Showing 36001 words to 39000 words out of 54681 words

Chapter 13 - Mutallab Asad Part 2 Complete Hausa novel

05 Oct 2025

54

numbar Mutallab amma bata shiga hakan yabata mutukar mamaki takira yafi sau goma amma bamata shiga kwatakwata. Nan tashiga aika masa da text tana fadin " Idan kagama fushin naka kazo ka daukeni malam dan bazasu kasheni da aiki kamar jaka ba ta aika tana zaune tana jiran reply amma taji shiru kiranta dataji abba yanayi ne ta bata fuska tana fitowa hade da fadin tana tafe " Wakika barwa yagyara gidan?" Da dan mamaki ta kallesa tace " Nifa Abba ko agidana bana aikin nan tsakani da Allah tayaya zan iya wannan bautar?? Nidai gaskiya bana iyawa tafaWa..." saukar mata da da lafiyayyan mari yayi yace " idan nakara gayamiki mai yakamata kiyi agidannan sai na zaneki wallahi nagayamiki ki kama kanki kije ki gyara gurin yafada yana jan tsaki. " tana kuka haka ta dakko mofa tashiga aiki.

Bakaramin shagali akayi asunan fannah ba ta inda yarinya taci sunan Mahaifiyar su jalil Ana kiranta da Anam. Fannah dake tsaye tana kallon Aicha tace yanzu saboda Allah sai yanzu zaki shigo? Tun yaushe nake jiranki tunfa ranar suna baki kara lekomu ba." Murmushi Aicha tayi tana zama tace " Yi hakuri mum anam wallahi abubuwan sunmin yawa sai da nasamo house help amma dattijuwa ce sai ?ar karamar yarinya ga school nafara zirya kuma kinga su dada sai jiya suka tafi ga batun mai gidan duk da sun tafi umara yau sudasu tante da dada kuma nasan sati biyu zasuyi, Nariga nasaba sai bayan kwana niyu yake gurina yanzu kuma kinga kullum ne." " Ai wallahi kokarinki yana burgeni yadda baki hada mijinki da kowa Anty A?cha shiyasa nake koyi dake wallahi " To ba dole ba inada wanda yafeshi ne ai ko ciyarwar nan Anty fannah bakaramin abu baniba ballantana ga muhalli ga wasu hidindimun yau da gobe ba zagi ba duka ai kam sai abun agirmama idan kika biye ta batun kishinsa saboda ?an mata bazaka taba zaman lafiya ba fannah dan wallahi Namiji ko mahaukaci ne akwai macce dake sonsa da haukansa shiyasa kullum nake addu'a ina faWin Allah kada yabawa wacce macce sa'ar sabawa Allah kokuma sakashi acikin fitintunan nan na zamani." " Hakane anty Aicha nima Wallahi Bana damuwa da wasu yammata nasan mijina yadda yake dole asamu masu sonsa Allah dai yabarmu tare dasu yakuma tsare mana danAllah Abani sirrin da zanyi yanzu mana yar'uwa ." Murmushi Aicha tayi tace " wanne sirri." " Kai anty aicha." Dariya tayi tace " Kinyi ciccibi? Kada ?anta tayi alamar A'a nadaiji ummata tanafadin data iya datayimun dan ana faWin kyansa sosai." " To ki samu kiyi ciccibi ki aika gurin masu nama kice abaki gaban saniya su wanke su gyara miki ayanko miki daga can sai ki dorashi akan wuta ki bashi wuta sosai dan yanada wahalar dahuwa sai ya dakko hanyar dahuwa kiyi jajjage ki zuba sannan ki daka ridi ki zuba ki zuba minannans sannan ki saka maggi kayan kamshi ki zuba nonon rakumi idan kina dashi ki barsu su game ruwan ajiki. Ciccibi sai kici." Kallonta fannah tayi tace na matse fa." ai ciccibi yana matsi sosai fannah sai dai kikara da wannan asiyomiki alimun amma shi ?adan ake sakawa da kaninfari da bagaruwa da sassaken bagaruwa da Wan gishiri da ganyen magarya ki dafasu kiyi sati kina shiga ciki zaki ban labari." " aikam wallahi Nagode sosai sai tsumi danAllah tafada tana karya wuya." Wai ...." " DanAllah nidai ki bani mijina yanason kulawa da shinfida wallahi shiyace ma nagayami komai asiyo inyi gyara bayaso in zauna haka ban kula da jikina ba." " To fannah ai sakarar macce zata zauna bata gyara wallahi ai jikinmu sai da kulawa idan bahaka ba sai asamu matsala ai dole mutum ya dage ya kula bama bayan haihuwa. Kinsam cucumber maganin mata ce sadidan a zamanance har ma da likitance to kisameta ki samu abarba ki samu kankana ki samu minannas ki samu kaninfari kisamu cinnamon kisam ki haWesu ki dafasu sai ki markada ko ki murje kisha zakiga ikon Allah fannah." " NAgode sosai wallahi Allah yabarki da oga." " Bari naje inda aji karfe 2 sai nadawo tafaWa tana barin gidan.

Ni wallahi umma kidinga alama idan zakiyi kashi akan wane dalili zaki dinga kashi awando gaki da nauyi ke jidda Asiya tafada tana fadin wallahi Nagaji sai dai ki gyara dan ni ba baiwarku bace ba haba fitsari anan kashe ma hakama fa jiya ina bata abinci dai amai kuma ajikina." Harararta jidda tayi tace " Ai nayi aikina naga da safe wallahi ke zakiyi." Anty Amarya dake jiyosu tace " Menene hakan kukeyi saboda rashin tarbiya? Ba mahaifiyarku bace ba idan bakuyi mata ba wazaiyi mata kamar naku? Bakwaso rayuwarku tayi albarka ? Duk lallacewar uwa uwace kuma wallahi sai Allah yayi fushi daku ahakan zaku samu naku masu tausayi ko abunda kukeyi zakujo dadi idan yaranku keyi muku shi? Narasa gane ?anku kwana biyu aikin ladafa kukeyi ko dankunga abba baya gari to sai na sanar dashi ta waya, Ai yanzu yakamaceku ace kun tausayamata kun dubata bawai ku tsya haka ba kuna ganin dai Alhaji mutallab Abba ya lallabasa yafito da Jamil daga gidan yari gashi can asubuti shima yana fama da jinya yakukeso tayi saboda Allah? Ita kuwa kome tazama girmamata akeyi sai kuyi hanzarin gyara gurin Nan kunji yan albarka ke Jidda bakincemun zakije gidan afrah ba." " To ai babu mai kaini Anty." " Ki shirya kije akwai driver gidan yayanki sai ya kaiki ai kema yakamata kicigaba da makarantar idan ya dawo kisameshi ki lallabasa kinji." " Allah dai yabiya yaya mutallab gaskiya munyi dacen Wan uwa wallahi." Jidda tafada tana nufar gurin zata gyara nan asiya tace " A'a bari nagyara ke jiki taya anty Aiki.

Rungume yake ajikinta yana aika mata da sa?onni masu rikita kwakwalwa tun tanajin kunya har yakai da bashi martanin da ya zame mata sai kace yaro saboda shiririta nan tashiga aika masa da nasa karatun har sai da tabbatar ya haddaceshi. Ahankali yashiga sauke numfashi yana faWin " Afrah na ina kaunar wallahi. " kamin tabashi amsa wayarsa tayi kara yasanya hannu ya dauka yana karawa akunne haWe da saita muryarsa." Dady barka da asubahi yafada suna gaisawa " " Farouk afwan na kiraku da safe ya diyata dafatan kuna lafiya," " Lafiya laou muke dady Allah yasa nan kalou." " Maganar wanda suka sace afrah ne daman nakeso nayi maka ankama wani yaro yanzu haka yana hannun hukuma." " Really dad?" " Sure farouk yanzu dai suna hannun hukuma idan kasamu dama sai kaje ko?.. " Badamuwa dad zanje inshaaAllah."

****
Muje ki gyara da?in ko? Mumy tafada tana kallon meenal hakan yasaka tabita abaya tana dan kunnunai haka mumy tatsaya akanta ta nuna mata yadda zata gyara da?in hatta bedsheet sai daya koya mata yadda zata gyarashi duk da sai da sukayi gyaran kusan sau 5 kamin meenal din tayi daidai da yadda mumy takeso sannan ta kyaleta nan ma bandakin sai data tsaya akanta ta nuna mata yadda zata wanke ko'ina daki daki. " Wash wallahi mumy nagaji." " Kema kyaji dadi ajikinki meenal ba'a san macce da son jiki ba."

****

Akwana atashi babu wuya agurin Allah ?an saudia sun dawo inda karatun Aicha yafara zafi sosai, haka kuma matar walid itama tasamu karuwa ta haifi Wa namiji wanda aka saka masa sunan Abbanta anyi budiri itama ba kadan ba. " menene naga kinyi tagumi?" " Anya wannan matsalar haihuwa ba daga gareni take ba ma ch?ri??" " Nace miki kidaina damuwa ko? Ai ita haihuwa lokaci ne Amma kamar yadda kikace zamuje muga likitan Amma ba ke kadai ba tare zamuje adubamu duka dan sai ta iya yihuwa matsalar ba ke kadai bace ba hardani kokuma ni ne ma.
*MUTALLAB ASAD*
Book 2

SHAFI NA GOMA SHA TAKWAS
??
? Arewabook:- billysfari
?
? ? Paid book ne, N500 via ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A, Gt bank, sai shaidar biya ta +234 704 040 2435 ko +234 809 845 6130 Ga masu son vip post 1k ne.

Zaro idanuwa A?cha tayi jin abinda ya faWa cike da mamaki, taya zai ce kilan matsalarsu ce bayan matarsa ta taba samun ciki har sau biyu?, ssannan su maza basu fiye yarda cewa matsalarsu ce idan mace bata haihu ba shiyasa sam basa son zuwa asibiti, Waidaikunsu ne kaWai keda ilimin gane cewa ita matsalar rashin haihuwa wato (Infertility) a turance takan iya zama daga wajen namiji ko kuma wajen mace, wani lokacin duka mata da mijin za'a iya samun matsalar daga wajensu, shiyasa a ?a'idance idan ana don magance ta ko samun waraka to dukansu ya kamata suje koda kuwa Waya daga cikinsu Win ya taSa samun haihuwa a baya. "Min Amour ya akayi naga kin shiga dogon tunani haka?" Taji Muryar Mutallab ya faWa yana dafata, sai data sauke ajiyar zuciya cikin sanyin jiki sannan tace, "Mon Amour me zaisa kace ?ilan matsalar taka ce bayan sau biyu ana samun ciki agidan nan." Runtse idanuwa yayi tunowa da wannan miji haWe da cewa, "Hakan bazai zama hujja aguna ba da zan tattara duka laifin na maida akanki koda ace ma an haifa mani yara agidan, kawai kishirya zuwa ?arfe sha biyu zanyi waya da Dr Hussain abokina ya haWa mu da kwararriyar likitan mata da zamu gani." "To Shikenan bari na hakura da zuwa school yau tunda dama lecture Win sha biyu zamuyi." "No Bari nasake kiransu miji ko zata iya bamu wani lokacin." Ya?are zancen yana mi?a mata hannu ta Wora masa wayarsa dake hannunta, cikin mintuna biyar ya kira Dr khadija sukayi magana, nan tace masa ba damuwa ta sake saka masu appointment zuwa ?arfe goma yayi mata godiya sannan ya kashe wayar yana kallon A?cha dake faman turare closet din kayansa data gama shiryawa da aka kawo masa wanki, "To kin ji zamu iya tafiya nan da ?arfe goma, kinga zuwa ?arfe sha biyu Win idan muka kammala sai mu wuce n ajiyeki school ko kuwa?" "Eh hakan yayi ranka ya daWi." A?cha tafaWa tana murmushi, kamo ?ugunta yai ya janyota ya yimata mazauni akan cinyarsa haWe da cewa, "Ina son ?amshi A?cha turaren nan ya yimun daWi sosai." Ya Wago hannunta yana sumbatar thaWe da kallon cikin idanuwanta. Murmushi ta saki tana shafa gefen fuskar tasa da Waya hannun nata kafin tace, "M? Ch?ri ai ?amshi rahamane, wannan haWin musamman nakoyesa dan kai kaWai, kuma ina da tabbacin mijina kaWai ne akeyiwa amfani da irin wannan ?amshin." Hannunta da take shafa gefen fuskar tasa ya janyo yai masa kiss tare da cewa, "I love everything about you Mon Amour." "Me too m? Ch?ri tashi' muje muyi breakfast kafin lokaci ya karasa." Ta mi?e tana ri?e da hannunsa har zuwa kan dining ta janyo masa kujera ya zauna, bayan sun kammala ya fice zuwa sashen t?nte da ayanzu take ita kaWai ita kuma ta koma ciki ta Wauki mayafinta da handbag Winta ta same shi acan, "A'a A?cha yau ba'a fita dawuri ba?" "Eh t?nte bana da lecture Win sassafe shiyasa, ina kwana?" "Lafiya kalau A?cha, Allah ya tsare yabada ilimi mai albarka" "Amin T?nte." TafaWa tana bin bayan Mutallab daya fice yana yiwa t?nte sallama.

Zaune suke gaban Dr khadija dake rubuce-rubuce a file kafin ta Wago kanta tana ajiye biron hannunta haWe da gyara zaman gilashi idanuwanta tace, "Ok naji duk bayananka Alhaji Mutallab dana ita uwar gida, ita wannan matsalar ta rashin haihuwa kamar yadda kuka sani ba sabon abubane da zaisa ku tayar da hankalinku ko ku shiga damuwa saboda Allah shi yake badawa aduk lokacin da yaso a kuma lokacin da yake ganin ta dace, wani lokacin matsalar na zuwa ne daga wajen macce idan aka jurewa zuwa asibiti sai kaga daga baya itama andace ta samu haihuwar, wani lokaci daga namiji ne kuma wanda mafi aksari sunfi bada matsala da rashin bada haWin kan da za'a shawo matsalar a asibiti saboda basa don zuwa, wanda da ace zasuyi hakuri su rika daurewa suna zuwa ana dubasu kamar yadda matan keyi sai kaga ?ar damuwar data hana haihuwar kaWan ce kuma ana maganinta sai haihuwar ta samu, ko kuma ya kasance duka miji da mata kowa nada matsalar, idan suka tafi asibiti tare aka dubasu sai a magance matsalar cikin sau?i wanda hakan ne yakamata ace duk wasu ma'aurata dake fama da wannan matsalar sunyi kamar dai yanda kukayi Win nan." Sai data nisa sannan taci gaba da cewa, "Yan zu akwai gwaje-gwajen da zamu baku kuke dakai da ita duka kuyi sai ku kawo mana sakamako mu gani, amma kafin nan zan rubuta maku magungunan daya kamata kuje kufara sha dukanku, "Ok Dr muna godiya." Mutallab yafaWa yana gyara zamansa, gwaje-gwajen da zasuyi tarubuta takira wata nurse ga mi?a mata tace taje dasu lab, wuWanda kuma ake bu?atar sai sunje gida tami?a masu a hannunsu tace zasu iya zuwa ko wani wajen ne da suke bukata suyi sukawo mata result. Godiya yayi mata sosai sannan sukayi sallama suka tafi, sai da suka fara zuwa lab aka diSi jininsu da sauran abinda ake bukata daga wajen A?cha kafin suka tafi ya ajiyeta makaranta shi kuma ya wuce shago..

***********
Kwance Mommy take yau tana fama da zazzaSi sosai dan har Asiya tazo dubata, Meenal ce a kitchen tana girki Asiya na tayata suna fira sai ga Kamal ya shigo, yana jin tashin Muryar mutane a kitchen din ya nufi can, atare suka juyo ita da Asiya jin motsin mutum a bayansu, "Sannu da zuwa ya Kamal" "Yauwa Asiya, shigowar yaushe?" "?azu." Ta bashi amsa ata?aice tare da wanke hannunta data gama tu?a tuwon semovita da take nunawa Meenal, kallon Meenal Kamal yai haWe da cewa, "Ke kam kinji mugunta Meenaluwa, daga zuwan yarinya har kin sata aiki?"

"Da Mommy zakayi ita data sakata bani ba." TafaWa tana balla masa harara, sai da yayi dariya idanuwansa nakan Asiya sannan yace, "Ba dole ta sata ba tunda ke baki iya ba, ko da yake ba laifi yanzu naga kina koya." "What ever dai ba gareni farau ba itama koya tayi." Ta bashi amsa tare da sakin tsaki tana barin kitchen Win cikin jin haushin yadda yayan nata ya yarfata, Asiya dai bata ce komai ba ta shiga gyaran kitchen Win dan sun gama girkin, tuwon kawai take jira ya sake silala sai ta kwashe, magana kamal ke son yimata Amma ya kasa, tsawon watanni biyar kenan yana don tunkarar yarinyar ya bayyana mata soyayyarsa amma yakasa saboda rashin samun fuska daga wajenta, ko yaushe zasu haWu zata gaishesa cikin girmamawa amma fuskarta a haWe, wanda hakan ke saka shi jin tayi masa wani irin kwarjinin da bazai iya fuskantarta ba, wani lokacin ma sai yaga fuskarta ta koma tamkar ta Mommy idan tana cikin yanayin rashin wargi tattare da ita, wata irin ragguwar ajiyar zuciya ya sauke yana kallon yadda Asiya ke aikinta cike da natsuwa kafin ya aro jarumtar da shi kansa baisan yana da ita ba haWe dayin gyaran murya yace, "Amm.. nazo na tayaki aikin tunda ta tafi?" Yadda ta Wago kai ta zuba masa idanuwa jin abinda yafaWa ya sashi jin gabansa faWuwa tare da Waga hannuwa yace, "Oh! So.sorry." yana Wan ja da baya kamar mai tsoronta, dariya ya bata dan haka sai kawai ta juya tana murmushi, tana sane da yadda ya kwaye mata amma ya?i basa fuska don kar yaga damarta duk da itama Win tana sonsa, muryarsa taji yana cewa, "Pls can i get your number Dan Allah? Akwai maganar da nake so muyi dake mai muhimmanci pls." Allah daya haWata dashi ya sata juyowa ba tare data ce masa komai ba ta sinne kanta ?asa, da sauri ya ciro wayarsa yami?a mata ta saka masa lambar ta mi?a masa wayar, "Thanks." Ya faWa tare da juyawa yabar kitchen Win yana sakin ?ar ?arar jin daWi haWe dayin tsalle yana jinjinawa kansa da hannu, ita kuma ta saki dariya tana buWe tukunyar tuwonta daya gama nuna, dai-dai lokacin Mommy tafito, "Kamal lafiya?" Ta tambaya ganin irin tsallen da yayi, cikin jin kunya ya sosa kai yana ficewa ta bishi da kallon mamaki tana shiga kitchen Win, yanayin Murmushin data gani a fuskar ?ar tata yasa tafara tunanin wani abu amma sai tayi shiru tare tana shan alwashin sake sa masu idanuwa dan tabbatar da zargin ta, sai gashi cikin kwana biyu da Asiya tayi gidan ta lura da ala?a mai ?arfi ta shiga tsakanin ?ar tata da Kamal, baza tace bata ji daWi ba dan Kamal ya sauya fiye da tunani tun rasuwar mahaifiyarsu, babu wani aibi tattare dashi a yanzu da zata ?yamaci alakar ?ar tata dashi in har suna son junansu tunda yana da sana'arsa takansa yanzu bai dogara da abun mahaifinsa ba, haka ma tuni ya kammala ginin gidansa yana kan haWa lefe, dan haka sai kawai ta bisu da addu'a idan alkhairi ne Allah ya tabbatar da tare su, idan kuma babu alkhairi Allah ya rabasu cikin sauki ba tare da rayuka sun Saci ba, dan wani bangare na zuciyarta idan yana tuna mata wahalar data sha a gidan sai taji bata fatan ?arta ta shigo ta fuskanci irinta tunda dai su ?a?an so ne basa laifi.

Wasa-wasa sai ga ?aramar magana ta zama babba, dan tuni Kamal ya sanar da mahaifinsa zancen soyayyarsa da Asiya ya kuma ji daWi ya amince da zancen Wari bisa Wari, da yayiwa Mommy zancen nuna masa tayi itama sai abakinsa take ji tare da tabbatar masa da cewa ba tada abun cewa indai suna son junansu kuma mahaifin ita Asiya ya yarda da auren tana yimasu fatan alkhairi, nan take kuwa Abba ya sanar da ?an uwansa cike da mutuntaka suka je nemawa Kamal auren Asiya, da farko sam iyayenta basu amince da zancen ba sanin kowaye Kamal da sukayi ada, Wanda Wabi'unsa da Asiya ke faWa suna yiwa Mommy da ita kanta momyn da takeyi na daga cikin dalilan daya sa suka ki amincewa har sai daga baya da sukayi bincike sosai suka tabbatar da canzawar halaye da Wabiun Kamal Win, dan har ciwo sai daya kwanta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login