Showing 18001 words to 21000 words out of 54681 words

Chapter 7 - Mutallab Asad Part 2 Complete Hausa novel

05 Oct 2025

44

tafasashi tare da ganyen beji kina zaunawa." "To Aunty nagode Allah ya saka da alkhairi agaida Abba." "Zai ji." TafaWa tana ficewa daga gidan.

Koda Afrah takoma ciki kallonta t?nte tayi haWe da cewa, "Kiga ikon Allah baiwar Allah nan kamar ba ita ba ta sauya sosai wallahi." "T?nte dama can tun farko bata fiye matsala ba kamar Umma, wasu abubuwan ma wallahi ita take sakata amma kinga yanzu data gane gaskiya tana nuna mana so kamar ?a?anta su Walid, sannan kina ganin Abba ma ya samu natsuwa ta Sangarenta ba kamar lokacin da ba." "Haka ne, itama waccan Win Allah ya shiryar da ita tagane gaskiya kafin lokaci ya ?ure mata." "Cab! Wai t?nte Umma kike cewa? Ai wallahi tayi nisa bata jin kira, kina ga fa yadda ta hana kanta zama lafiya gatanan duk ta ?are saboda dai kishi, shiyasa nake jin takaicin matar ya Mutallab data shige masa kuma laifin ya Mutallab Win ne daya ?yaleta." "Allah ya kyauta itama ya dawo da ita kan hanya." t?nte tafaWa tana dakatar da zancen don bata don abinda zai haWata da Meenal Win balle har tayi mata rashin kunyar data saba.

***********
Oga gayen nan fa shegene, kana gani fa duk yadda agabansa shagunan nan nasa sukayi ?urumus da tarin dukiyarsa aciki bai girgiza ba ko kaWan, asali ma abun kamar ko a jikinsa, wanda aka kira da oganne ya furzar da iska ta baki alamun bakin ciki Sacin zuciyarsa yace, "Ka ?yalesa idan yasan wata baisan wata ba, ko yanzu ba ?aramin asara ya tabka ba kawai ya tara kudinne shiyasa yasa bai ji wannan ba, amma zan yimasa abinda zai girgizasa ya kuma fitar da dukiyar da sai yaji ajikinsa, bana son ganin farinciki a fuskarsa dan haka kowace hanya zan bi naga na da?ile wannan farincikin sai nayi." "Sai oga." Suka faWa suna sa dariya kafin ya mi?a masu kuWin aikinsu yabar wajen..

***********
Al'amarin Jamal abu ya haya?a yanzu dan case dinsa ya wuce ?aramar kotu ya koma a high court, gbaWaya yafita hayyacinsa tamkar ba shi ba, ga wani irin ba?i da yai saboda tsabar wahala daya sha, gaba Waya yarda madara a rayuwarsa, ya rasa mai taimakonsa kasancewar Abba ya cire hannunsa a lamarinsa ta kuma hana Mutallab ya taimakesu acewarsa har sai ya gane kuskuren daya aikata, a dayaSangaren iyayen matarsa sun zo har gida sunce lallai-lallai dole ya saketa bazata zauna zaman jiran tsammani ba tunda ba'a san lokacin da zai dawo ba, Abba yayi basu ha?uri har ya gaji umma kuwa sai zage-zage takeyi tana cewa su butulu ne sun manta da ?ar tasu aka ci dukiyar amma dan tsabar yaudara yanzu zasu ce sai an saketa, ganin abun na shirin kawo tashin hankali tsakaninsu yasa Abba yace su tafi zaiyi magana da shi ya bata takardarta, nan umma ta sake yin tsalle tace baza ayi hakan ba sai in hulWi zasuyi masa, hararar da Abba ya aika mata tasa ta kama bakinta kafin sukayi sallama suka tafi akan mahaifinta zai dawo ya karSar mata takardarta ta saki nan da kwana biyu.

Karo na farko kenan da Abba ya gyara yaje prison wajen Jamal, haWin Wa da mahaifi kallo Waya ya yimasa yaji zuciyarsa ta karye, dan gabaWaya ya sauya kamar ba shi ba, ga wasu ?uraje da suka feso mashi jiki wuWanda da likita ya dubashi cikin gidan yarin ya tabbatar da cewa na cutar ?wayar HIV ce data damesa, ba tare da Abba ya nuna yanayin daya shiga ba yace, "Jamal nazo wajenka ne saboda iyayen matarka sun zo suna nemawa ?arsu takardar saki." "Abba Bama sai na rubuta ba taje na saketa, ni yanzu takaina da lafiyata nakeyi Abba ka taimakeni kafitar dani a wajennan, ina shan wahala sosai." Ya?are zancen yana fashewa da kuka haWe da durkushewa agaban mahaifin nasa." "Ni ba abinda zan iya yimaka Jamal, kai ka zaSawa kanka wannan rayuwar duk da so da fatar dana nuna maka, haka ka rufe idanuwa kayita cutar dani kana kwasar dukiyata kana yin yadda kake so, to da tawa Win ce kaWai da sauki amma kaje ka haWa data mutane ga abinda kajawo maka, zanyi magana da Wan uwanka Mutallab amma ba yanzu ba saboda yana cikin ?ar damuwar shagunansa da suka ?one." Abba na gama magana yami?e ya juya zai tafi Jamal ya tsaida shi, Abba dan Allah ka yafe mani?" Ya faWa cikin muryar dake nuna yayi kaishi dan kimanin watanninsa uku kenan wajen yana karSar nau ukan azaba kala-kala banda ciwon dake tattare dashi, sai da Abba yai ajiyar zuciya hannayensa duka na zube abaya sannan yace, "Kayi ?o?arin fara tubarwa Allah da kuma halayenka sannan kadawo gareni." Yana jin yadda Jamal ya fashe da kuka amma yayi tafiyarsa, har ga Allah ya yafe masa amma akwai bu?atar yafara gyara halayensa da neman gafarar Allah shiyasa ya furta masa haka, Abba mutumne mai sanyin halin da don iyalansa, shiyasa ake saurin samun nasara kansa ga wasu abubuwan, yanayin shiga da ficen Umma na bokaye ne da aka sukayi tasiri akansa suka mayar dashi mafaWacin mutum yanzu. Ko daya koma gida Aunty Amarya ta tambayesa ya Jamal Win yake amsa mata yayi da sauki amma yana cikin yanayin da yake bu?atar taimako, cikin nuna tsantsar damuwarta tace, "Abba kayi ha?uri kabari Wan uwansa ya taimaka masa yafito dashi." "Ban?i ha?a ba yanzu, sai dai ba yanzu ba sai ankwana biyu shima ya sake gane kuskurensa, zuwa lokacin ana gama hidimar Afrah." "To Shikenan Allah ya kaimu lokacin yasa muna da rayuwa, ga abincinka can yana jiranka." Ta?are zancen tana mi?ewa Abba kuma yabi bayanta, sai data zuba masa abincin ya soma ci sannan yace, "Ina ita mahaifiyar tasa?" "Wallahi ban sani ba tunda ina can Sangarena ina aikin abinci." Kai ya kaWa haWe da ?walawa Asiya kira ta taho yace, "Ina Ummanku? Kira mani ita" "Bata nan Abba tafita." "Tun yaushe?" "Kana fita itama tafita." Cokalin hannunsa ya ajiye tare da kallon Asiya yace, "Rayuwar da mahaifiyarku ta zaSa kenan ko? Sannan ke baza kiyi hankali kifitar da wani mijin ki aura ba kinfi so ki zauna kina cigaba da kwasar mugwayen halayenta." "Kayi ha?uri Abba wallahi babu wanda ke nemana yanzu." "Allah ya kyauta, ina ita Jiddah Win take." Shiru Asiya tayi dan batasan amsar da zata ba mahaifin nata ba tunda tana can abuge tasha ?wayunta tayi tatil kar yace takirata ta rasa yanda zatayi, don idan yasan hakan ma zai iya jawo ya koreta gidan daga ita har Jiddah Win "Ba dake nake magana ba?" Abba ya faWa a tsawace yana Wan bata rai, inda inda tafarayi kafin can dubara tazo mata tace, "Abba bacci takeyi." "Idan ta tashi kifaWa mata tazo ina don ganinta, tashi kije." "To Abba." Asiya tafaWa tana mi?ewa tare da barin wajen tana sauke ajiyar zuciya ganin ta sha.

Daidai lokacin Afrah tafito ta nufi kitchen zata kai plate din data gama cin abinci, ganin mahaifin nata da bata san ya dawo ba yasa ta nufi wajen murmushi Wauke a fuskarta cikin Wan girmamawa tace, "Abba ina wuni sannu da dawo." "Yawwa Afrah lafiya kalau Afrah kina lafiya?" "Lafiya kalau Abba." TafaWa tana barin wajen, kallon Aunty Amarya hai haWe da cewa, "Yaushe ta shigo baki faWa mani ba?" "?azu ne, na bari ne har ka kammala cin abincin sai na yi maka zancen, dama kasan ana ?an gyare-gyare namu na mata shine nace tadawo nan kafin satin bukinta sai takoma can." Wani sanyi Abba yaji a ransa, yana matu?ar jin daWin sauyawar amaryar tasa musamman yadda yaga tajawo yaransa ajiki yanzu tamkar itace ta haifesu, murmushi ya saki tare da cewa, "Naji daWin hakan sosai Allah yayi Mali albarka, dama nakan ji ba daWi aduk lokacin da naga Afrah ta shigo gidannan tafita alhalin gidan ubanta ne, zanyi magana da yayan nata ya bar mani ita ayi hidimar bikinta anan ko ya kika gani." "Hakan ba laifi indai ya amince tunda gidan mahaifinta ne." Da haka Abba ya?are cin abincin ya koma palour ya kira Afrah Win suna fira cike da jin daWi.

Sosai Aunty amarya ta dage wajen gyaran Afrah ciki da wajenta tamkar ?ar cikinta, Walid ne ke bata duk wasu kuWaWe da take amfani dasu acewarsa shima yabada tashi gudun mawar ga ?ar uwar tasa. Wani irin farinciki Afrah ke ji aduk lokacin data ganeta cikin ?an uwan nata suna fira, dan daga Khalid har Walid da matarsa idan sun zo haka suke sakata tsakiya suyita fira Asiya ma da taga tsabbace kanta da takeyi bazai yimata ba tafara shiga cikinsu ana fitar ba tare da tayi la'akari da ita yayarsu bace, Jiddah kaWai ce ke boye kanta cikin Waki bata fitowa saboda yadda damuwa tayi mata yawa, idan ta gaji da zama kuma ta jawo ?wayunta tasha, Umma tayi masifar tayi jidali da ita tadena wannan Wabi'ar har tagaji amma ta?i bari, abun duniya duk yabi ya isheta ga Asiya tadena saurararta takoma wajen makiyiyarta dan kusan can take wuni, shiyasa idan suka haWu da Aunty amarya ta dinga yadda mata magana kenan wai makwaWaiciya dan taga abun duniya shine ta jawo Afrah a jiki tana kuma so ta gabata da ?arta dan mugun hali da munafunci bayan tagama rabata da mijinta to tajira martani dan sai ta sata tayi nadamar yimata haka tunda tana da bokayen itama da malam, murmushi Aunty Amarya kawai zatayi tace ni Allah nari?e banda boka ban kuma da malam, duk abinda kuma kika iya kike kiyi ni dashi na dogara kuma ina da ya?ini akan zai bani kariya ni da mijina da kuma yaranmu. Ako yaushe haka take bata amsa cike da kwarin guiwa dan tasan yadda suke tsaye wajen addu'o'in kariya da kuma nafilfilin dare babu abinda zata iya yanzu.






#Mutallab Asad
#?an Tagwaye
#Nana Diso
#Billy s fari
*MUTALLAB ASAD*
Book 2

SHAFI NA GOMA
??
? Arewabook:- billysfari
?
? ? Paid book ne, N500 via ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A, Gt bank, sai shaidar biya ta +234 704 040 2435 ko +234 809 845 6130 Ga masu son vip post 1k ne.


Ana saura sati Uku bukin Afrah yau Farouk yakira Mutallab yana zaune gefen gado ya sanar dashi za'a zo aka kawo lefen Afrah, fuskarsa a sake yace, "To Allah ya kaimu sai a kaishi can gidan Abba Win." "To Shikenan yaya." Farouk YafaWa cike da tsokana yana dariya, "Kai dai ka sani ranka shi daWi." Mutallab ya bashi amsa yana dariya shima, "wato ka rama anyi 1-1 kenan". Fadar farouk haWe da yimasa sallama ya kashe wayar yana ?ara ganin kimar Mutallab a idanuwansa daga shi har Afrah da yace yakai lefenta agidan Abba dan itama da sukayi zancen cewa tayi agidan Abba zai kawo amma suyi magana da yaya Mutallab, duk arzi?in mutum indai nagari ne zai so ya yi bugun gaba da gidan mahaifinsa, wannan abun yasa ya ?ara jin cewa tabbas ya samo mata a inda ya dace. Bayan sun gama wayar Mutallab ya kalli Meenal dake kwance saman gadon yace, "Farouk ne ke sanar dani yau za'a kawo lefen Afrah, saboda haka dame-dame kike tunanin ya dace ayi." "Je ka tambayi matar so wacce suke shiri da ita, ni meye ruwana a ciki yarinyar da gabaWaya ta gama renani." "Wannan tsakaninki ne da ita wannan kuma tsakaninmu ne a matsayin ki na matata nake shawararki." "To ban sani ba." Ta bashi amsa tana mi?ewa daga kan gadon ta nufi sashenta. (Hmmm mata muri?a kulawa, duk yadda kike da matsala da dangin miji ki danne haka alokacin da yabaki wani girma da muhimmanci akan wani sha'ani nasu da yake da iko akai. Ina kika ce a'a zaki Wauki fadan dake tsakaninki dasu ki sanya a tsakaninku da mijinki tofa tabbas kin yadda girman daya baki a idanuwansa, idan kuma wani abu ya taso gaba to ai dai yayi da wata ba keba tunda kince ba ruwanki da lamarinsu, kina gani za'a ri?a yin hidimarsu ba dake ba an batseki gefe."


"Allah ya kyauta." Shine abinda Mutallab kawai ya iya faWa tare da mi?ewa ya feshe jikinsa da turarukka don dama gama shirinsa kenan zai fita farouq Win yakirasa, sashen A?cha ya nufa ya sameta a kitchen ta gama haWa kunun garin sabaya dake gyara jikin macce da cikota zata sha.

Kayan hada SABAYA

1. Ridi gwangwani 2
2. Hulba original gwangwani 2
3. Gyada gwangwani 2
4. Waken suya rabin Kwano
5. Shinkafa rabin Kwano
6. Alkama rabin Kwano

Gyada da ridi zaa soya su sama-sama
Shinkafa da alkama zaa jika su na awa 5 sai ashanya su bushe
Sai ahada su waje guda dukkansu a ni?o a tankaWe. Yadda ake shansa za'a dinga damawa ne sai a saka madara da zuma cokali 3 duk mutum 1 yasha.

Ga Amfaninsa kamar haka:

1. Gyara nono
2. Gyara fata
3. Lafiya jarirai
4. Ciko da mai rama
5. Dauke rama gamai azumi
6. Samar da ingantacciyar lafiya naa gaban maza
7. Samar da lafiyayyan maniyyi
8. Samar ga niima ga duk macen dake da karancin niima.

Macen dake da ciki ko mai shayarwa ma zata iya sha haka ma ga mazan dake bukatar jikinsu yayi kyau du zasu iya sha. WuWan da bazasu iya haWawa da kansu ba to su nemi wannan lambar *+234 907 927 4454* zasu samu hadi mai kyau ingantacce tamkar ke kika haWa a wajenta.

"Ma ch?re morning an tahi lafiya." A?cha ta faWa tana juya kunun a cup, sai daya rungumota ajikinsa yana sha?ar ?amshin dake tashi ajikinta Waya gauraye da wani sassan ?amshin turaren wutar data saka a Wakin sannan yace, "Lafiya kalau Mon Amour, me kike haWawa haka naga yayi kyau tun a fuska su ?amshin madara ke tashi." Dariya ta saki haWe da Wago kai ta kallesa tace, "zaka sha na zuba maka?" "Eh da gani zaiyi daWi." "M? Ch?ri ba dai iya salo ba zakayi mun wayo ka shanye abu." TafaWa da Wan wasa tana jawo wani cup ta zuba masa shima tare da Wauka ta juyo tami?a masa nashi ita kuma tafara kuSar nata, anan cikin kitchen ya jawo kujerar dake gefe mai tsawo ya zauna yana sipping a hankali saboda zafi yana faWin, "Mon Amour yau za'a kawo lefen Afrah gidan Abba, me kike ganin Yakamata ayi?" With so much excited A?cha tace, "Wow Masha Allah Allah ya nuna mana ma ch?ri nayi farinciki, yanzu kai meye ?arfi ka?" "Duk abinda kika faWa ina da karfin yinsa." Mutallab yafaWa yana sake kai cup din abakinsa don ba ?arya hasashensa ya zama gaskiya kunun yayi masa daWi sosai, sai data ajiye cup Win sannan tafara yimasa lissafi da yatsun hannunta, "Za'a soya naman kaji inda hali a haWa masu da rago, ayi snacks drinks sai kuma ruwa da abubuwan daya dace a?ara masu akai." "Kamar me kenan!" "KuWi da duk abinda zaka iya." "Shikenan za'a kawo gasashshen rago da drinks da ruwa, snacks kuma zan baki kuWi sai kiyo masu odar tunda wuri ya ?ure, kaji kuma nasan zaku iya soyawa anan ko kuwa?" "Eh hakan yayi kayi magana da Aunty Meenal?" "No bata jin daWi ita, inaga kuyi magana da matar Walid idan tana da dama sai ku haWu kuyi, ana dafa masu abinci?" "Eh mana m? Ch?re amma wannan zan iya ni kaWai kafin zuwa anjima, Allah ya?ara buWi da wadata." Ya amsa da amin yana ajiye cup din Dan ya shanye kunun tas akan carbinant din kitchen, wayarsa ya ciro yayi transfer Win 300k sannan ya maida cikin aljihu yana faWin. "Ki duba natura maki dubu Wari uku na snacks din, idan basu isa ba kiyi mani magana, sannan ki duba abubuwan da babu da zaki bu?ata na ganin cin da za'a yi koyi Mani list ki turo mani, zansa Khalil ya siyo ya kawo tare da jakin." "To Shikenan ma ch?re Allah ya?ara arzi?i." TafaWa tana bin bayansa, sai data kaishi bakin ?ofar sashenta sannan ta dawo ta Wauki wayarta, lambar chef deejerh berver da kwanaki ta shiga wani class Winta na kayan mata da tayi online ta kamo murmushi Wauke akan fuskarta dan ba kaWan take son matar ba takira, tana Wagawa suka gaisa cikin girmamawa da karamci da iya mu'amala da abokan kasuwanci irin na Chef Win suka gaisa, sai data yaba mata akan class Win da sukayi yadda tayi masu bayani dalla-dalla da turo masu vedios da audios na yadda zasu hada komai sannan tace, "Dama snacks muke so Hajiya za'a kawo lefen ?anwar mijina shine nace to tabbas ke zan nema." Kuma ku Meta ta wannan lambar *+234 907 927 4454* dan samun duk abinda kuke so daga wajenta cikin girmamawa da mutuntawa, so da Chef tayi Murmushin jin daWi haWe da godema Allah daya sa mutane ke son kasuwancinta da mu'amala da ita sannan tace, "To Hajiya dame-dame kuke so." Nan A?cha ta lissafi mata duk abubuwan da take bu?ata ta faWa mata kuWin sannan sukayi sallama tana cewa, "Nagode da karamci da ragin da kika yimani chef, zakiga na ?aro 5k akai na class Winki na Ramadan da naga kina tallah zan shiga saboda mai gidana nason homemade drinks kala-kala kuma naga haddasu zaki koyar bayan kalolin girke girke da na gani masu sau?i da kuma burgewa." "Eh haka ne amma zan maido maki da dubu biyunki saboda RAMADAN CLASS Wina dubu uku ne kacal ba dubu biyar ba Nagode sosai." "Haba ba komai ai Kinci fiye da dubu biyar ga abubuwan da zaki koyar wallahi, kawai dai nasan kin saukaka ne saboda har marasa ?arfi su samu su shiga, amma online class gasu nan muna gani dubu goma dubu bakwai har ma fiye, kuma ba wani cikakken bayani Allah dai ya saka maku da alkhairi." "To Nagode hajiya sai kin jini, pick ne ko delivery?" "Eh to bari na turo a karSa sai ki ajiye Mani address Win." "Ba damuwa." TafaWa tare da kashe wayar. (Ga masu bu?atar shiga wannan aji na musamman wato RAMADAN ONLINE CLASS, zaku biya dubu uku ? 3000 ne kacal, PAY 3K ONLY into: Deejarh Berver Enterprises
2041774069
Firstbank And SEND YOUR RECIEPT TO 09079274454 ..AFTER PAYMENT)

A?cha na gama waya da ita takira Imam ta sanar da ita zancen aikin, Fannah ma duk da tayi nauyi ta sameta a wajen t?nte ta sanar da ita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login