Showing 27001 words to 30000 words out of 54681 words

Chapter 10 - Mutallab Asad Part 2 Complete Hausa novel

05 Oct 2025

45

Innalillahi wa'inna illahirrajiun yau naga diyar banza wannan yarinya inane alkiblarta ko tsoron Allah batayi kai amma batada hali ." Tante tafada tana rafka salati " Amma bata kyauta ba wallahi duk yadda yakeson cikin nan to saboda me itakam." Afrah da ko ajikinta tace " Jahilci ." " babba ma dan kuwa takashe rai ai tunda inaji anfara halitta ki duba uban jinin da yake zuba akan gadonta kai yarinyar nan Allah ya shirya to wai dole ne auren nasu." Aicha tace " Mama kuskure tayi Sai dai Allah ya kiyaye gaba." " To diyar nan will ba wannan ne na farko ba." Duk da mamakin da yacikata sai cewa tayi " Allah yayi mata afuwa." Nan Afrah takira jalil yasanar musu fannah ta sauka tasamu baby girl hakan yasanya su dunguna gaba dayansu dan daga nan zasu huce kwalliya anty aicha yanaga kin tsaya?" " Afrah kada na fita yayi fada kinga nakirashi bai daga ba kuma kinga halin da yake ciki nasan halinsa akan cikin nan wallahi bakaramin damuwa za'a shiga ba." " kiji danAllah to me yayi miki zafi danAllah zomuje wallahi bazai hanaki ba." " To dazu ai yahanani." " Tawo kishigo Aicha bazaiyi fada ba tante ta fada hakan yasa ta shige suka tafi asubuti gurin fannah MashaaAllah tabarakallah itama yaran gidansu sun cika da manya hakan yasa tante tace su shige su tafi ita zata zaunar mata har su koma haka Aicha tashige cikin su afrah da kawayenta akasha kwalliya duba da saima sun koma gida tacan angwayen zasuzo da sauran kawayen nata.

Zama yayi batare da motsi daga inda yake ba ga bakin ciki yazo masa nan bayason kallon meenal din ma wata kalar tsanarta ke saukar masa firgit ya dago yana kallon doctor din haWe da faWin " Are you okay sir." " Meke damunta kawai ya iya fada." " Wannan abun da kukeyi kuskurene yanzu da kabara maganin miscarriage har tasha fiye da ka'ida banida tabbacin zata sake haihuwa agaskiya dan ko da zata iya samun cikin sai dai ayimata aiki, kai bama lallai dan mahaifarta ta tabo yafaWa yana kallon Mutallab da gaba daya yanayinsa ya sauya idonsa yayi jajir ya saka hannunsa a aljihu ya mikowa likitan kwalin maganin daga kai yayi yace tabbas shine maganin zubda ciki wanda yake da mutukar haWari dan shi a akida idan aka sha daya ba'a kuma sha sai bayan 12 hours shikenan Amma kaga gaba daya tasha. BuWe idanuwan da meenal kiyi ne yasanyashi faWin kiji gidanku Na sakeki. A dan haukace ta ri?e mararta tana kuka dan abune da bata taba tsammani ba. Shikuma kamin yakai kofa tuni yazube agurin da yasa likitocin hanzarin bashi taimako zuwa wani da?in harma da saka masa ruwa.Likitan dake tsaye da'ita ne yace " ke kuwa menene na aikata haka? Yanzu kin cutawa kanki da lafiyarki." Ciki da karamar masifarta dake gauraye da azabar ciwo tace mai yayi maka zafi?."

Ihun da jidda takeyi da yadda Abba ke du?anta sai da yadagawa kowa hankali agidan, Daman asiya tagayamata idan batadaina wannan shaye shayen ba tofa ita sai tagayawa Abba shiyasa ta sameshi da asuba tagayamasa shi kuma da yashiga cikin tashin hankali yarasa me ma zaiyi dan Asiya ma sai da yayi mata kyawawan maruka. Kasancewar yanuwa ancika yasanya kowannen su hankali tashe yashiga bashi hakuri Ana riko jidda Umma dake wanka haka ta zura kaya da kumfar ajikinta kamin ta inda karasawa bakin kofa ta zumale ta waWi akasa wanda hakan yasa bayanta yayi kara da kafarta da hannunta guda daya gashi buguwar datayi da ka yasanya idanuwanta rufewa wani ihu tasanya da kowanne mai rai na cikin gidan yaji hakan yasa Anty Amarya dake kan jidda gudu bangaren ta da matan yayan abba suma suka shiga Ciki Nan suka tarar da umma kamar bata numfashi ha?an nr yamaida hankalun kowa har abba yabar jidda wanda tana ganin haka ta gudu sashin anty Amarya ita kuma Umma aka taimaka akayi asubuti da'ita likitoci ne sukazo hade da shiga bata again gaggawa anan nr abba yakira Mutallab yagayamasa Nan yasanar mai matarsa ba lafiya suna asubuti jalil kuma yana gayamasa yace yana gurin su fannah zqta haihu hakan kuma yakara daga hankalin kowa.

Jalil yakira awaya yace yazo yatafi dashi yace masa ai fannah ta haihuwa dakyar dai yake magana haka yayi masa Allah yaraya yakuma kaara kiran Abba awaya ganin missed call dinsa rututu " Abba yafada da wani calm voice." " Mutallab menene yasamu Iyalin naka." Baisan sanda yasaka kuka ba first time da abba yaji wickness dinsa yace " Ta zubarmin da ciki akaro na biyu Abba batajin maganata bata girmamani bata darajtani sai wulakantani dani da yanuwana Na sawwake mata Abba." " To ai ba kuka zakayi ba Mutallab hakuri zakayi babu ta inda Allah baya jarabtar bayinsa kayi addu'a Allah yasa kaci wannan jarabawar daman kuma yarinyar ana fadan dabi'unta to yanzu kuma gashi ta hadu da ummanku wanda tunfari nayi maka magana akan karabasu tunda itama wata babbar shaidaniyarce ina tunanin ko da halin yarinyar da hudubarta ko ta kawaye kayi hakuri ka dauki hakan amatsayin jarabawa Allah yabaka wasu masu albarka kana asubutin nazo nadaukeka." " A'a kazauna nan Abba jalil zaizo yakaini gida." " Ayi hakuri ayi hakuri dai." Tunda jalil yatawo hanya sai yasamu guri yafaka motarsa Numbar mumyn meenal yashiga dannah ita kuma lokacin suna tare da abba suna hira " A'a kamar jalil kanin mijin Afrah" mumy tafada tana kallon Abba. " Dauki mana kiji ko lafiya." Dauka tayi haWe da sakashi a speaker tana sallama " Mumy barka da rana dafatan kuna lpya." " Lafiya kalou jalil ya mai dakin tayi nauyi ko?" " Wallahi tama sauka yau ansamu mamata." " To mashaa Allah barka barka Allah yadayyiba." " Ameen mumy daman magana nakeso muyi dake akan Meenal danAllah kitsaya ki fahimce ni nakiraki ne dan naga hakan shine kadai masalaha duk da dai mai faruwa yariga ya faru amma maganar tawa zaisa kudubata da kyau." Duk jikinsu sanyi yayi sukace " Ina jinka jalil mai kaunarka ai shine ke cewa diyarka ya gyara." " Tabbas kuwa mumy gaskiya meenal tana bukatar karatu sosai akan zamantakewa ta aure dama duniya kinga tunda akayi auren nan bazance dan uwana yana samun farin ciki Agurinta ba sai dai shi yafaranta mata komai tasaka agaba yana tafe da'ita Amma wulaknci yau daban nagobe daban mumy hatta tante dake da matsayin mahaifiyarmu bata kyale ba wallahi afrah kowa hatta Aicha haka takeyiwa kowa rashin da'a nikuma mumy nasanki Nasan inna wallahi diyar inna sai hamdala Amma meenal nakasa gane kanta gaba daya yanzu ma ta zubar masa da ciki suna asubuti dukansu abunda tayi yasa shima sai da suka kara masa ruwa dayake likitan abokina ne yacemun har ya sawwake mata." " Innalillahi wa'inna illahirrajiun " mumy tafada tana kau da kanta haka Abba ji?insa sai yaji kamar an watsa masa ruwan zafi ." Nan yasanar mata asubutin shikuma ya huce gurin Mutallab din ko da ya daukeshi gida yayi dasu inda sukayi daidai da shigowar su Afrah wanda yazuba masu idanu taci?in mota Nan yaga su da kawayensu sun sakko aicha na ci?insu tasha ado tayi kyau sosai da ankon ji yayi gaba daya ransa ya baci wato shi yana nan yana jimamin Abunda yafaru dashi ita ko aji?inta harda shiga kamar yammata ganinsu dada bangaren tante ta ruga aguje tana murna ta rukunkumeta." Jalil nan shima yafito Mutallab kuwa zagayawa yayi yashiga part dinsa sosai ransa Saci Ganin Aicha yana hangota ta sama yadda taketa jan dada har suka shige sashinta kamin yayi ajiyar zuciya. " Ke jaira irin wannan kyau haka dada tafada. Ina mijin naku? " takara jifanta da tambaya Nan takwashe komai tagayawa dada nan tashiga masifa tana kwashwq meenal albarka suna zaune taga wayarta tayi kara " Wallahi kika sake fita bada izinina ba." Adan firgice tace " Wayyo Allah na nashiga ukuna." " ke menene " " Dada wai nazanje ba duk kwalliyar danaci tasaka kuka." " To ke baki tambayeshi ba kikaje kina baWa wannan hodar? Sai kace diyar aljanu ." Afrah datashigo ce tace ita suke jira nan tagayamata ya hanata. Duk yadda suka tambaya mata Mutallab yace babu inda zataje haka tacika tayi fam saboda ba?in ciki dada sai faWa take mata Amma ko ta?anta batabi ba.

??
*MUTALLAB ASAD*
Book 2

SHAFI NA GOMA SHA HU?U
??
? Arewabook:- billysfari
?
? ? Paid book ne, N500 via ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A, Gt bank, sai shaidar biya ta +234 704 040 2435 ko +234 809 845 6130 Ga masu son vip post 1k ne.


Rai a Sace ta nufi sashenta tana kwaSe kayanta Waya bayan Waya tana ?walla dan har ga Allah tasa ranta zuwa wajen bikin nan amma ya hanata, da Meenal ce ta tabbata jiki na rawa zai barta, bakin gado ta zauna tana share ?walla tare da goge lips Winta da suka sha jambaki tana sake share kwallan, wayarta ce dake ajiye gefe ta sake Waukar ?ara ta juya taga mai kiran nata, tamkar shi Win ne agabanta ta Salla ma wayar harara tana kauda kanta gefe ba tare data Waga ba har ta tsinke, sake kira yayi akaro na biyu tagoge ?wallan da suka sake zubo mata sannan ta mi?a hannu ta Wauko wayar ta Waya tasa a kunne ba tare data ce uffan ba, "Kizo ki haWa mani ruwan wanka." Mutallab yafaWa tare da katse kiran, wani ba?inciki ne da takaici lokaci Waya ya rufeta, wato ma baiga abinda yayi mata ba har cewa yakeyi tazo ta haWa masa ruwan wanka? Yi tayi kamar baza taje ba sai kuma ta tuna da yanayin da yake ciki ta Wan turo baki tana cewa, "Badon halinka ba wallahi." Sannan ta mi?e ta nufi Wakinsa tana haWe rai, ganin baya cikin palourn nasa yasata nufi bedroom Winsa ta sameshi zaune bakin gado ya dafe kansa da duka hannayensa. Kallo Waya tayi mashi ta Wauke kai ta nufi toilet Winsa, ganin akwai ?ar datti yasa sai data fara wankesa sannan ta haWa masa ruwan wankan tafito, "Na haWa." Ta bashi amsa tare da nufar ?ofa zata fita, Wari kai yai yana kallon bayanta haWe da cewa, "Ki fiddo Mani da kayana kafin nafito." Yami?e yashige toiletbatare daya jira amsar da zata bashi ba, kamar zata saka kuka A?cha ta buWe closet din na kayansa ta ciro masa kayan ta ajiye masa akan gado tabar Wakin da sauri dan kar yafito tana ciki saboda haushinsa da take ji. Bayan yafito ya gama shiryawa ne ya sameta a Wakinta kwance, tana jin shigowarsa tayi masa banza har ya?araso ya zauna bakin gadon ta makama bayansa harara, dai-dai lokacin ya juyo yana kallonta tayi saurin rufe idanuwanta tamkar mai kwana, "Yunwa nake ji akwai abincin da zanci ko naje waje na siya." YafaWa cikin sanyin muryar da tasa jikin A?cha yin sanyi ta mi?a zaune tana cewa, "Babu amma ka bani mintuna kaWan bari na haWa maka." Ta?are maganar tana sauka daga kan gadon ya bita da idanuwa har ta fice yana sauke ajiyar zuciya, "Tabbas Annabi yayi gaskiya daya ce ka auri mace dan addininta, ba dan nasaba ba ko kya??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????u ko kuma dukiya saboda duka zasu ?are, ya tabbata da Meenal tana da addini abubuwan da tayi mashi duk yadda takai ?ololuwa da Saci rai baza tayi mashi su ba, tabbas kyan Meenal da surarta na daga cikin abubuwan dayasa yafara sonta tun aganin farko, yayi tunanin zata sauya itama dalilin don shi da takeyi shiyasa ya ajiye zancen Wabi'unta agefe yaji tausayinta ya aureta ba tare da sanin cewa zata zo ta salwantar masa da jini ba har biyu, wane irin kuskure ne haka ya tabka ya Wauko flower a juji da zata gurSata masa rayuwar ?a?a idan ma tabari ta haifa masa su?" Ya tambayi kansa hawaye na cika masa ?walla ya dafe kansa dake wani irin sara masa, A haka A?cha data dafa masa taliya da soyayyen ?wai ta dawo ta iskesa, hankalinta a Wan tashe ta?araso wajen da yake dafe da kai tana cewa, "Lafiya ya Mutallab." Bai iya tankata ba sai matso ?wallan ba?i cikin dake das?are azuciyarsa da yayi ko zai samu sassauci, hakan yasa ta matso ta zauna kusa dashi tana Wora hannunta saman cinyarsa haWe da cewa, "I'm Sorry m? Ch?ri samu da rashi duka na Allah ne, kayi ha?uri ina sha Allah zaku samu wani Babyn idan ta samu lafiya." Runtse idanuwa yai jin malamin daya fito daga bakin A?cha kafin ya buWesu akanta yana cewa, "It Over A?cha, bazan iya ci gaba da zama da Meenal ba, bata sona bata don jinina taya kike tunanin nan gaba zata amince mu sake samun wani?" ?asa A?cha tayi da kanta dan baza ta nufi kallon fuskarsa ba a yanayin da yake ciki, hannuwanta taji ya ri?o ya rum?e cikin nasa yana cewa, "Pls A?cha kada ki?i jinina aduk lokacin da Allah ya baki, ina matu?ar son haihu shiyasa Meenal ta zaSi ta horani ta wannan fannin saboda aurenki da nayi." ?ago kai A?cha tayi ta kallesa jin abinda yafaWa, kenan wai saboda ya aurota Meenal ke kashe ?a?anta? Wannan wane irin rashin hankaline da rashin sanin ciwon kai? Tabbas yau ta yarda jahilci na Wawainiya da ita kuma Allah ya shiryeta ya ganar da ita, tayi maganar cikin zuciya kafin azahiri tace, "Kayi addu'a Allah ya bamu masu albarka m? ch?ri, duk da ance haihuwa da wahala amma zan jure ko nawa kake so na baka." "Da gaske kikeyi A?cha." "Me zai hana tunda kana so kuma nima..." Sai ta kasa ?arasawa tayi ?asa da kanta, wata irin runguma taji ya kai mata yana sanya mata albarka sai kace ma tasamu cikin har ta haifar masa, murmushi ta saki tana sauke ajiyar zuciya kafin tayi ?o?arin zare jikinta haWe da cewa, "Ka taso ga abincin can na haWa maka." Tami?e tare da ri?o hannunsa zuwa palourn tana danne Saci ran da take ji nasa a zuciyarta suka nufi wajen dining, sai data zuba masa yaci ya ?oshi sannan ya kalleta haWe da cewa, "I'm sorry A?cha da duk abubuwan dana tayi maki adalilinta, sai Waga baya na gano ashe sharri ne da makirci takeyi maki amma idanuwana suka rufe nakasa gane haka saboda yadda na ?wallafa gina akan Wan cikinta, sai gashi duka ban tsira ba sai data hanashi takowa duniya." "Ba komai haka Allah ya tsaro." TafaWa tana ?afarsa cin abincinta da takeyi.

*************
Buki ne na manya da ?awatuwa akeyi a babban ball Win da hamsha?an masu kuWi kawai ne da suka amsa sunansu ke iya kama wajen da kuma manya-manyan ?an siyasa da ?usoshin gwamnati masu faWa aji, duk inda ka duba jami'an tsaro ne tako ina suna faman mazurai dan ba ango da amarya kariya daga farmaki da aka taSa kaiwa na sace Afrah, wanda ba dan dangin ango da suka matsa dayin program Win ba da babu wani shagali da za'a gudanar inji amarya Afrah dan ba ?aramar tsorata tayi ba alokacin da aka dauketa, dan ma Allah yasa babu abinda akayi mata kuma ana bata ci da sha mai kyau acikin wuni biyu da kwana Waya da tayi awajensu. Sosai ango da amarya sukayi kyau ?an uwa da abokanan arzi?i sai tayasu murna akeyi haWe da yimasu liki, musamman dangin ango da suka buWe bakin aljihunsa cike da farincikin auren suna zubar da kuWi tare da kwasar rawa. Ba'a watse bukin ba sai misalin ?arfe goma da wasu mintuna ango da masu bashi kariya suka yowa Afrah rakkiya har gida, murmushi Afrah tayi lokacin da suka iso tare da kallon angon nata tace, "Sai da safe hubby, ka kula mani da kanka fiye da yadda kuka bani kulawa kai da jami'an tsaron ka." "Zanyi hakan har lokacin da kika dawo hannuna kulawar ta dawo hannunki dan ramawa kura aniyarsa." Lumshe idanuwa tayi tare da buWesu akansa tace, "Ba kada matsala Allah ya kaimu lokacin". Tana kai hannunta a jikin mabuWin motar sannan ta buWe tafita, sanyayyar ajiyar zuciya Farouk ya sauke bayan gama ?are mata kallon da yayi har tafita, ya zaiyi idan ya rasa Afrah dan wata irin soyayyarta yake ji mai tsanani na ?ara shigar masa a zuciya da sam baya don abinda zai rabashida ita ko kuma ya taSata, wannan dalilin yasa ya Wauki alwashin duk wanda keda sa hannu wajen Wauke ta da akayi sai ya bincikosa ya kuma hukuntasa akan haka, saboda adalilin hakan ne duk wani tsimi da tanadin da sukayima wannan bukin nasu suka soke shi, wanda yana da tabbacin ba haka Win Afrah taso ba kawai ta tsorata ne shiyasa ta zabi daga program Win yau babu wani abu da zatmsu sakeyi sai Waura aure kawai ta tare Wakinsa. Yana wannan tunanin ne yaga ashe tuni sun fice daga gidan sun kama hanyar zuwa gida, alokacin ya tuna kuma da al?awarin da yayi na cewa zai bada miliyan Waya ga duk wanda yakawo labarin inda za'a samu Afrah, wannan yasa ya ciro wayarsa ya kira Aryan dake tare da Mahmoud daya zo bikin Afrah a palournsa suna cin abinci, sai da suka gaisa bayan ya Waga kafin yace, "Aryan ka turo mani account number dinka na turo maka kuWin da nayi al?awarin bayarwa ga duk wanda yakawo mana labarin inda za'a samu Afrah. " "A'a ranka ya daWe, ai Afrah ?anwata ce, banyi Wan kabani komai ba tundaa wajen MAM ma aka samu duka baya nan " "No al?awari mukayi kuma ya zama dole mu cika, saboda haka ka turo mani da ita." "Shikenan ranka ya daWe godiya nakeyi bari nakira MAM ya tayani godiya." "No need don Allah Aryan ai anzama Waya." Farouk yafaWa yana kashe wayars." Shiru Aryan yai kafin ya kamo lambar Mutallab ya sanar dashi yana ?arawa da cewa, "MAM da Farouk yabar kuWinsa tunda cikin hidima yake kada ya takura." "Ba wani takura Aryan kawai katura masa tunda al?awari yai, amma kai kuma ka saSa al?awarin mu tunda nace kada kafaWawa kowa." "Kayi mun afuwa kaina kasan dole na faWa masa saboda alokacin shikaWai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login