Showing 18001 words to 21000 words out of 163158 words

Chapter 7 - KAUNA DA SO COMPLETE Hausa Novel

M SHAKUR   

06 Sep 2025

8171

mahimmaci a motan taduba ko ina, saita dauki handbag nata tabude drugs tagani cikin wani roba haka na drug holder anyi arranging kaman magungunna dazata sha da rana ne ko dare dan gasunan daban daban, saiga wayanta iphone 16 taciro call log nata taduba, Son1 and Son2 sune the only contact datake waya dasu like almost all the time especially Son1, ajiyan zuciya Ziora ta sauke sannan ahankali tafara dialing number Son 1 amman kwata kwata bai shiga ba kusan sau uku, bayama ringing ne, sannan network basa cewa komi is as if number yashiga flight mode, sai kawai tai dialing Son 2 bai shigaba shima, tana dialing tana duba magungunan a roba suke so babu ma suna, jakan takara dubawa idanunta ne ya sauka kan wani kati haka plastic card, ansa I m a Cancer Patient! Gaban Ziora yafadi dummm! Dawani irin gudu tasauko daga motan tabar wayan ciki tai cikin asibitin tana zuwa tafada dakin emergency room din inda Ya Chidi da nurses ke kanta dasauri tace  Ya Chidi look, I think she s a cancer patient I saw this card and this drugs in her purse dakatawa Dr Chidi yayi yazo ya karbi drugs din yabude anatse yana kallo kafin ya kalli Matan da har lokacin bata dawo hayyacinta ba, anatse tace  that explain everything thank you Smart Ziora you just save her life, excuse us now ficewa tayi daga dakin tana kara satan kallon matan saita zauna anan wajen dakin tai shiru tai tagumi gabanta kawai sai faduwa yake tawani kalan damu na ban mamaki, cancer data gani ya tsayamata arai, bude kofan akayi dasauri ta dago kai Ya Chidi ne yace  have you spoken to her family? Girgizamai kai tayi, Moh ya tsareta da idanu yace  call them again yajuya zai wuce dasauri tace  Ya is she aw& ..awa& ke? Tai maganan muryanta na breaking tana shirin fashewa da kuka, Chidi yawani tsareta da idanu he s not trying to blame her infact she did the right thing na saving life din mutum, but Ziora is so soft she easily get attach, ga tausayi da saurin kuka yace  when you know bakida zuciyan why didn t you let saloon people to take her to the hospital? Ba saloon dinsu taje ba ? Bayan hannu takai tayi share fuskanta tass tahana kanta kukan karya mata bala i sannan tace  I know you re the best Dr saisa nakawota wajen yayana hararanta yayi yace  kikamin kuka anan saina tattakaki my friend go and call her family gyadamai kai tayi tajuya yace  ina zaki? Ahankali tace  wayanta na motanta tana maganan tawuce tana goge hawayen, tawuce waje wajen parking space tabude motan ahankali tadauki wayan tana danna screen saitaga 3 missed call from Son1 dasauri tai dialing number back ringing daya aka daga wani nutsassiyar tattausan murya dake cike da izza dakuma dan tsauri kadan yace  Mami nah! Hakanan gabanta yafadi sai kawai taji maganan datake shirin yi ya karare a wuyanta, and voice din kaman ta tabaji somewhere but she is not certain, sauke ijiyan zuciya tayi mai kara.  uhmmmmm shiru daga dayan bangaren akayi ba ace komiba kuma ba a kashe wayan ba, daurewa Ziora tayi anatse cikin turenci tace  my name is Ziora, I am with your Mom in hospital, I actually brought her her& & .  Which hospital! ? Mutumin ya tambaya babu babu wasa kan muryansa, hakanan kawai saitaji kaman she s in trouble kirjinta wani kalan dum! Dum! Dum! Yake mata, ahankali tace  ka& .. kawai taji shiru dasauri tacire wayan daga kunnenta taga wayan yamutu ba chaji, Innalillahi yanzu mezata cema Ya Chidi? Ijiiyan zuciya ta sauke kawai ta ijiye wayan ta fito tadawo cikin hospital din direct dakin tawuce danta gayama ya Moh wayan matan ya mutu daidai lokacin matan tashiga bude idanunta Chidi na juyowa yakalli Ziora datazo da sauri wajen gadon sai kawai takama hannun matan tarike sosai cikeda damuwa tace  Mami cus taji haka danta yakirata, bude idanunta gabaki daya Mami tayi tadaura idanunta dake nuna rashin lafiya sosai akan Ziora da idanunta suka cicciko da hawaye ga gyalenta ya zame kasa, kannan rabi daya a tsefe bari daya ba a tsefe ba, ahankali Ziora tace  do you remember me Mami in the saloon? I m Ziora, you fainted u were having nosebleed shine I drive you to hospital na Yayana, this is my brother Dr Moh Chidi, he s my elder brother, I tried calling your children ta wayanki but wayanki yamutu ba charge, can you give Ya Moh number su yakirasu? Lumshe idanu Mami tayi tabude kafin ahankali ta yunkuro zata tashi tana salati ahankali.  La ilaha illallah Muhammadu Rasulullah riketa Ziora tayi ta tashi zaune anatse, Ziora duk tai wani iri idanunta na cikowa da hawaye sabida yanda jikinta yayi zafi, anatse Mami ta kalleta tace  mesa baki tsaya an gyaramiki kai ba ? Kallon Mami Ziora tayi the woman looks so strong dudda she s sick amman she s talking about kanta da ba a gama tsefewa ba, hawaye sake ciccikowa a idanun Ziora yayi Mami tai murmushi ganin bata amsaba yasa takalli Chidi tace  thank you for saving my life Dr Muhammad, I see inda Amrah ta dauko kirki da kuma taimako murmushi kadan Ya Moh yamata, cikeda girmamawa yace  how are you feeling Ma? Ahankali tace  Alhamdulillah! I have Cervical Cancer tadanyi murmushi kadan tace  ina last stage already, banson needles, kowani damuwa danasan za a kawoni asibiti ma na hana, I don t want hospitals again, Doctors said I have 6months to live so I m just waiting for time yanda Ya Chidi ke kallonta haka Ziora ke kallonta idanunta sunyi ja and matan looks so strong, ga addini, ga karfin imani, how can you be this strong and comfortable kasan duka duka wata shidda or less yarage maka a duniya? Zuciyan Ziora, ahankali Chidi yace  how can we contact your family Ma ? Murmushi tayi tace  no need yarana duk suna wajen aiki yanzu, discharge me, Amrah kawo jakana akwai card dina kizo kibiya dasauri Moh yace  you don t have to pay Ma, lemme just write the discharge papers and sign, but how will you get home? I won t let you drive in this condition dasauri Ziora da muryanta harya dan dishashe sabida tausayi tace  I will drive her home Yaya dan kallon Ziora yayi itama Mami ta kalli Ziora da idanunta sukai ja, duk babu wanda yayi magana yashiga rubuta papers din Ziora ta mike tace  na dauko wheelchair Yaya? Gyadamata kai yayi da sauri tawuce tafita Mami tabita da kallo, ahankali Chidi yaja kujera yazauna gaban Mami hakan yasa ta kalleshi, ahankali yace  why will you give up so early? I know wani good trial I can enroll you maybe the outcome will be good Hajiya sosai Mami ke kallonsa saikuma ahankali tace  no wonder kakeda kanwa that s very very caring da tausayi just like you, look at how worried she is sabida ni da bata sani ba tasake murmushi tace  I am just so tired! Kasan tun yaushe nake battling da cancer? Tun yarona yana 18yrs old today he s 35yrs, he s also a doctor like you, Oncologist and a Surgeon, but I guess haka Allah yaso ya ganni, and I m very grateful to Allah dayama bani tsawon rai cus I thought bazankai this stage ba daidai Ziora na bude kofa tana shigowa da keke, tazo har wajen gadon tamika mata hannu tace  Mami zo ahankali Mami tace  toh yar Mami dasauri Ziora ta kalleta saitaji kunya kawai tasa hannu takama Mami, Mami ta kalleta sosai saita taso shima Chidi sai kallonsu yake, zaunar da ita tayi a keken sai Chidi yace  let me gungurata yayi har wajen motansu tare sukasa Mami a baya, yakalli Ziora da zata shiga gaba anatse yace  be careful kikai dropping nata take a taxi back home I still have patient here yazaro kudi a pocket 5k yabata na hawa taxi ta karba tace  thank you Ya Doctor tashiga gaba ta tada motan Chidi ya tsaya saida yaga fitansu yajuya yakoma ciki.

Suna shiga hanya tace  Mami where is your house ? Ahankali Mami tace  GRA 1st Avenue house number 10 she knows GRA thanks to Mommy datake rakawa unguwa haka tasa wuta bini bini tana tuki tana kallon Mami ta madubi dake lurada ita, har sukakai hadadden layin suka shiga, unguwan shiru kaman ba mutane, gidan dataga number 10 tawuce tace  Mami nan? Ahankali Mami data lumshe idanu tabudesu tace  eh nan ne, yi horn horn Ziora tayi ko sakan uku ba a karaba aka shiga bude gate din wani maigadi ne dake sanye da uniform na security, gidan babban gidane sosai kusan girman gidansu ga lafiyayyun motoci anyi parking, ga Imam tsaye a tsakar gidan dake sanye da 3quater da t-shirt yayi folding hannu a kirji yana kallon motan saikuma yashiga zuwa while Ziora tawuce wajen parking tai parking daidai Imam na karasowa wajen, Ziora tasa hannu tabude kofan tafito batama lurada Imam ba, tundaga kafa yake kallonta zuwa jean da riga dake jikinta da mayafin dake kanta da yake a zame ga gashinta awaje, kallo daya yamata yaganeta dan yanada gane mutane, yahada fuska sosai yana mata wani kallo da hakanan saida Ziora taji kaman ana kallonta tajuyo dasauri suka hada idanu, faduwa gabanta yayi tana kara kallonsa trying to understand waye kuma wannan wani kallo yake mata haka, sai kawai taji dauke kai ta taho baya zata budema Mami kofa kawai Imam yasha mata gaba.

=ث?KAUNA DA SO=ث?



'

EPISODE =??
Chak Ziora ta tsaya tadago kai ta kallesa takasa motsi sabida yanda ya tsaya mata agaba yana kallonta, sai kawai tadauke kai tace  excuse me! Cikin kakkausan murya Imam yace  why are you here? Dawani irin sauri Ziora ta kallesa kaman ya why is she here, baki tabude zatai magana kawai yadaka mata tsawa.  What s a girl like you doing a motan Mamana? Why are you with Mami? Kafin Ziora tamace wani abu Mami ta lallaba tabude kofan ta dayan side din tunda yatare side din daya kamata tafito da, dasauri dukansu biyu atare suka kalli kofan hango Mami tabude kofa struggling tafito yasa Imam yayi wajen dasauri yaduka kawai agabanta yakai hannunsa kan fuskanta yace  Mami? Meya sameki? Wait? Yar shaye-shayen nan tabugeki da motan ta ne komeya faru? Kafinma Mami tayi magana kawai Imam yataso yakalli Ziora data zagayo itama wajen amman bata matso kusada Mami ba sabida yana wajen yace  yauma kinyi shaye shaye ne like the other day a golf club? Me kikama Mami? Why is she with you ? Zafi ran Ziora yayi sosai though bata ganesa ba but maganan golf club dayayi made her realizes cewa yaganta hala dasuna golf club taredasu Mira zatai magana dan ranta yabaci Mami ta lallaba tafito daga motan ahankali tana dafa mota tace  Maheer! Imam! Juyowa yayi dasauri yakalleta zatamai magana Ziora itama cikeda bala i tana bankama Imam din harara gaban Mami tace  Mami I m going! I wish you quick recovery and May Allah grant you Shifah tai maganan zata wuce abinta karaf Mami takama hannunta tace  Amrah wait! Tsayawa Ziora tayi takalleta zata turo baki kuma saita fasa dan matan look weak and sick she needs rest, cikin rashin kuzari Mami tace  don t mind all abinda Maheer yace, you can t trek back home ai, inane gidanku? Ahankali takama dayan hannun Mami in a very loving way tace  Mami Ya Chidi gave me money for taxi nakai road I will take taxi back home dasauri Mami tace  no! Take this car with you, gobe saiki kawomin I want to see you tommorow okay tsayawa Imam yayi yana kallon Mami da wannan yarinyar dayagani a golf club tareda mahaukatan kawayenta irinta Mami na nan nan da ita kaman tasanta da dadewa, sauke kanta kasa Ziora tayi ahankali jin abinda Mami tafadi kana gani kasan bataso ta dauki motan, maganganun yaron sun mata zafi, kaman Mami ta lurada hakan takalli Imam daya tsaya yana kallonsu kaman yasami TV ta hararesa tace  you dont talk to my guest like that Imam sauke kansa kasa yayi, Mami takalli Ziora tai murmushi tace  don t mind Maheer haka bakinsa yake ba filter kinsan footballers, don t take any abu daya fadi to heart, he s a good person once u get to know him okay Ziora kin cewa komi tayi, Mami tajuyo takalli Imam dake kallonsu strictly tace  apologize to Amrah right now! Without her help I would ve been dead by now, she saved my life, she saved me shiru Imam yayi yana kallon Mami, there s nothing dabazai iya yima Mami ba hakan yasa yadan kalli Ziora da batama kallon direction dayake yace  I take back my words sorry Amrah! Hakanan Ziora taji gabanta yafadi dahar saida tadan dago kanta ta kallesa suka hada idanu ta ballamai harara tareda make kafada tace  I forgive you because of Mami if not saina rama ashagwabe tai maganan tadauke kai sabida faduwa da gabanta yayi takalli Mami sai kawai tai hugging Mami tsam batare datamasan dalili ba, murmushi Mami tayi ta shafa bayanta ahankali tace  I m fine! Start going kar Dr yadamu same with ur Mom nasan hala tadawo Saloon daukanki dagowa Ziora tayi daga jikin Mami ahankali tace  take care ko Mami, take your drugs, karki kara fita sosai Mami ke kallonta kowa na cemata take care take your drugs, but kalman karki kara fita mutum daya ne rak ke fadamata shi a duniya sai Ziora yau tazama tabiyu murmushi Mami tayi mai taushi tace  tom bazan karaba Amrah, shiga mota bude motan Ziora tayi batare data kara kallon Imam ba, ta shiga ta kunna Mami duk na kallonta tace  banda gudu gyadama Mami kai tayi ta juya da motan saida tazo daidai saitin Imam takara kallonsa hada idanu sukayi ga mamakinsa ballamai harara tayi harda juya idanu sannan tafice daga gate din da aka bude mata Imam yabi motan da idanu yana mamakin yanda ta ballamai harara, Mami tace  sai muje ko Oga Imamu mara kirki dan shafa kai yayi yataho yana kamata yace  Mami what are you doing with a Christian girl? This child na shaye shaye kinga yaran datake yawo dasu ne karuwai ne fa& . Wani kallo Mami tamai tace  banson karajin maganan nan, she s a Muslim, kodama she s a Christian I don t care, what matters is heart, ina kaunar Amrah .


Da gudu take driving daidai tana kokarin shan kwana tafita daga layin wata babban Range Rover sport baka kirin na tahowa da mahaukacin gudu da saida sukai clashing yadaki gaban motanta, ihu Ziora tayi sosai tana taka wani mahaukacin brake, tunda tafara driving bata taba accident ba, hannunta saida yabuge sosai tai maza ta kashe motan takasa dawowa daidai ga hanyar ba mutane tadauka unguwansu ne ba mutane but yau for the first time taga unguwar dayaci uban nasu arashin ganin mutanen, bude gaban Range Rover akayi dasauri ta kalla tana mamakin waye ganin mai Range Rover bai reversing back ba, wani black matashi ne da wlh tana kallonsa taga Mami tsaf kawai ita Mami fara ce, amman kaman tayi kaki ta tofar unlike she Imam data gani a gidan baiyi kama da ita ba shi fari ne but baya kama da Mami, hakanan taga kaman ta taba ganinsa, yanada cikan jiki kadan kaman body builder, yanada saje bakin kirin da gemu baki shima daya taru a fuskansa, yanada pink lips that looks kaman ciwo but they re dead gorgeous exactly kaman mutumin data gani a mall kawai wannan baisa glass ba, gawani dogon hanci da manyan idanu round masu dogayen eyelash ga gashin gira baki kirin, yanada suma akansa baki sunyi coils sosai sunada yawa kana ganinsa kaga bafulatani, bahaushe ne oho dai, ga uwa uba tsayi kana ganinsa akalla zaikai 35yrs yana sanye dawata riga da wando kafafunsa crock ne ga lab coat ajikinsa fara kal an rubuta Dr AH ajiki, fuskansa na dauke da damuwa sosai yana kallon motan yaga wacce ke ciki ba yar gidansu bane cus motan Mami ba tinted bane, while Ziora har lokacin jikinta ke rawa, calmly yakarasa wajen kofan baiyi knocking ba direct yabude kofan inda take dasauri tajuyo ta kallesa jikinta na rawa hakama bakinta sai kawai yayi shiru ya tsareta dawasu irin idanu da tunda take aduniya bata taba ganin wani yamata kalan kallon ba kamshin turaren dataji rannan na ratsa hancinta mai bala in dadi, dauke kanta tayi da sauri gabanta na fadi ahankali da muryanta mai shegen zaki nan that looks like na baby tace  Ma& .Mami is at home with your brother Imam jin shiru baice komiba saita dago idanunta karaf suka hada idanu still kallonta yake, maida kanta kasa tayi takai hannu taja gyalenta daya sauka a bayanta tarufe kanta, ahankali Ziora tace  she asked me to go with this car and bring it back tommorow shiru har lokacin baiyi motsi ba, sake kallonsa tayi zata kauda idanu for the first time tunda yazo wajen cikin wani husky voice that s not that loud and it s very calm yace  which hospital did you take Mami to? Idanunsa kaman wuta haka yake mata ajiki ga muryansa dadi kuma a natse yake mata magana unlike dayan Imam dakeyi kaman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login