Showing 51001 words to 54000 words out of 163158 words

Chapter 18 - KAUNA DA SO COMPLETE Hausa Novel

M SHAKUR   

06 Sep 2025

8189

ita yana christa tazauna dashi akanme Ziora bazata iya zama da christa ba batasan how addininku works ba, ganin Mommy taki bude kofa fashewa da kuka kawai Ziora tayi Daddy yabar wajen kofan yataho wajenta yace  why are you crying kekuma cikin kuka tace  I ve made you and Mommy angry, Mommy is angry with you Daddy and Mommy never gets angry with you Dasauri Daddy yayi hugging nata yace  don t worry she will calm down okay okay now go to your room and observe magrib Daddy yayi maganan yana kaita dakinta yabude kofa yasata aciki yakalli su Chidi yace  let s go wucewa sukayi suka tafi duk Mommy na jinsu, itama Ziora kasa tabuka komi tayi jin sun fita yasa tabude kofa tafito tazo wajen kofan dakin Mommy ta tsaya gaban dakin tafashe da kuka sosai tace  Mommy I m sorrry, I didn t mean to hurt you Mom, please open the door I want to hug you My Mommy Mommy you re my everything I love you okay Mommy na jinta tai banza da ita tana parking kayayyakin ta tana hadawa a box nata saita ta kwashi komi datake bukata she needs to give them space dukansu make them realize how important she is in their lives even though ita Christian ce, zata nuna musu this Christian woman is very important to them, wayanta tadauka da bibble dinta da cards nata tajawo wani drawer na dakinta ta debi just 2 wrappers na 100 dollars da na yan 1k guda daya kawai tabude kofan Ziora dake kuka taga Mommy da akwati rawa jikinta kawai yafara tace  Mommy where are you going ? Ko kallonta Mommy batayi ba tawuceta tashiga jan akwatin zuwa staircase, Ziora tafashe dawani mahaukacin kuka tazo da gudu tai hugging nata tabaya tace  Mommy where are you going? Cikin fada Mommy ta tureta tace  your mother is a Christian I hold no value nor importance arayuwanki dana yayyinki dana Babanki toh what am I doing here? I will go and meet my Son Micheal and become his mother only him dawani irin sauri Ziora tadawo tagabanta tunda Mommy take bata taba ganin Ziora na irin kukan tashin hankalin nan ba, idan kuka ne Ziora itace queen of cry but duk kukan datake na banza ne da iskanci but yau Mommy saw that fear tace  Mommy I ve never ever spend a day in my life without you, where are you going? Why are you leaving me who will be my Mommy ? fizge hannunta Mommy tayi ta nunata da yatsa tace  kika kara tabani saina daukeki da mari, I don t care who will be your mother ai kinada step mother dakikeso, na haifeki kin gagareni menake cewa kiyi kiyi eh, menake cewa kiyi kiyi? Nabar muku gidan yanzu ga ubanku me the only Christian person in the house is leaving, you the Muslims should enjoy your life in peace Mommy tai gaba Ziora tashiga binta da gudu tana kuka.  Mommy I will do anything you want Allah jan jakanta Mommy tayi zuwa wajen motanta tabude baya tasa jakanta aciki tawuce zata shiga gaba Ziora tabita yanda Ziora ke kuka da ihu su Hassan da step Mom saida suka bude bude kofa suka fito, Mommy tadan a wani irin horn aka bude mata gate taja motan da mahaukacin gudu Ziora nabin motan da gudu har waje yarinyar tafito tana gudu Mommy tana kallonta ta mirror glass, wani mugun faduwa Ziora tayi sai kasa saida Mommy tadanci burki, har cikin jinin dake bargon kashinta taji faduwan kaman tai reverse tadawo but no, gata yama Ziora yawa batasan me rayuwa is time tashiga hankalinta tabugama motan wuta taja tabar anguwan while security gate nasu yataho da gudu zuwa inda Ziora take akasa tana kuka yace  stand up Miss Ziora daidai lokacin su Daddy sun fito daga masallaci hango Ziora akasa da Dady yayi saida kirjinsa yabuga yataho da gudu yace  wat happened to her, Princess menene menene ? Yaduka yakama Ziora zuwa jikinsa Obinna da Chidi na zuwa wajen da sauri suma ganinta awaje.

=ث?KAUNA DA SO=ث?




'

EPISODE 2?? 9??


SUBSCRIBE TO MY YOUTUBE CHANNEL AND LISTEN TO KAUNA DA SO AUDIO
https://youtu.be/q3kNkMVipuY?si=SqD9S_hg9YEJytWI



EPISODE 2?? 9??





Chidi yakalli security yace  what happened to her ? While Daddy da Obinna na daga Ziora sama knees dinta na jini, Security yace  she followed Madam car that just left dasauri dukansu suka kalli security, sai kowa dai yayi shiru suka kama Ziora daka takawa da kyar tana dingishi suka shigo da ita ciki tana kuka ba kakkautawa, Daddy na kallon wajen motocin dan baiga motan Mommy ba hankalinsa yatashi, suka kama Ziora suka shigar da ita ciki Daddy yama rasa ina zaisa kansa Ziora dake kuka sosai zai lallasa ko Mommy zai fita ya nema, Chidi yawuce sama yadauko first aid box danta kurje a knee sosai, Daddy yaciro waya yana dialing number Mommy but ta kashe wayan hankalinsa yatashi ya ijiye wayan ya rungume Ziora kawai yace  stop crying your Mommy will come back okay cikin kuka numfashinta har fizfizgewa yake tace  I& & I& want& ..my Mommyyyy Daddy yace  I know, I know, stay with your brothers kidena kuka lemme go and get her yakalli su Chidi yace  please stay with her kunlallasheta tadena kukan nan kar zazzabi yakamata you know how she gets idan tai kuka too much, treat her knees, I m coming bari nabi Mamanku duk suka gyadamai kai Daddy yawuce dasauri yafita yashiga motansa.

Ya matukar damu cus Mommy is not the type datake irin wannan fushin shi baima santa da daukan zafi haka ba, yamata abubuwan dayafi wannan bata barsa ba sai yanzu ne over karamin issue haka kan Ziora zatai fushi tabar gidansa, Church nasu yaje dan nan yafisa rai zai ganta amman batanan wlh kuma gashi bawai tana zuwa gidan kawaye bane, rayuwanta is just church then home, but dudda haka yan few members daya sani na church da Mom ke mutunci dasu yakira su ko Mommy tazo duk akace batazo ba. Where could she possibly go to this night?
Wasa wasa duk wani wanda suka sani a Abujan nan Daddy yaje ko yakira Mommy bata nan, saiya fara tunani to tafi gida ne? Florence is from Enugu zata iya zuwa airport ta koma garinsu da gaske, yarasa yazaiyi saiya tafi airport din he has few contanct nan da nan yace adubamai duk wani flight zuwa Enugu daya tashi daga 7:30 zuwa yanzu wajejen shadaya agani ko wata Florence Ogenechuku tayi boarding, it took almost 45min kafin azo office din afadamai yes tabi jirgin Obom Air to Enugu daya tashi 9:05 agogo ya kalla Mommy by now dayake 12 something ma tuni ta tsufa a Enugu maybe ma takai gidansu.
**

Wasa wasa har 11 nadare Mami takasa bacci sabida Ziora da bata kirata ba nor watsapp her, tun da yamma Mami ke kiranta taji kotakai gida lpy amman shiru ba a dauka, Mami tamata voice note a watsapp takirata video call duk bata dagaba hankalin Mami yatashi, duk Aliyu na lurada ita amman baice komiba, har wuraren 11:30 yazo dakin danya kwana yaga tana dialing number Ziora tasa a kunne amman ba a dagaba sai idanun Mami suka cicciko da hawaye, dauke kai Yayi yamaida kofan yarufe yadauki bargo ya shinfida akasa kawai ya kwanta abinsa, ya lumshe idanu wannan wace kalan yarinya ce data shigo rayuwan mahaifiyarsa ta fitineta ne haka? Why will Mami zata dauki son duniya yadaura akan yarinyar da basu santa ba, basu dan usulinta ba nor daga ina tafito banda yau dashi yakaita gida da kanta shima he intentionally did it just to know daga inama this girl ke zuwa, he s not liking this kawai ba yanda zaiyi ne, by now yakamata tayi bacci, he s very happy BP ta yazama normal yanzu zata fara damuwa BP yatashi, yana cikin xancen zucin yaji sheshekan kukan Mami saiya bude idanu yataso yazauna yakalli Mami dake kuka saiya taso dasauri yazauna bakin gadon dab da ita yace  Mami menene yanzu why are you crying cikin kuka sosai tace  something yasami Amrah tsare Mami yayi da idanu, Mami tabasa wayanta tana kuka tace  I ve been calling her tun biyar da hamsin na yamma bata dagawa har yanzu and that s so unlike her, I ve watsapp her bata dagawa, nakirata video call bata dagawa that s so unlike her wlh wani abu yasameta yanda Mami ke kuka abin shakar dashi yayi yace  Mami why would you be crying akan wacce baki santa ba eh? What if something happens to you? Me ruwanki da yarinyar nan dazaki hana kanki bacci kina kuka sabida ita? Maybe ma tanachan ta manta dake ke kina nan kina kuka that some thing tamasan menene sha kuwa balle so maybe tama mance ki wani kallo Mami tamai dayasa ya hadiye maganan tace  tashi kabar gidan nan ka koma gidan ubanka daman halinku daya marasa mutunci wanda basuson farin cikina, kadauka kowa ne mai kalan zuciyan karfe irin naka, Amrah is not like that, bata mance dani ba, I know who that girl is dudda ban santa da dadewa ba, something happens to her Mami ta rushe da kuka bana wasaba dayasa Aliyu ya matukar damu zuciyansa namasa zafi cus yasan kukan nan datakeyi baza a kare lpy ba, saiya kalli number a wayan Mami data bashi yayi dialing wayan na ringing amman harya gama ba a dagaba, saiya ciro wayansa daga aljihu yashiga kwashe number Ziora yayi dialing yakai kunne shima yafara ringing ba a dagaba yasakeyi still ba a dagaba, saiya kalli Mami cikeda lallashi yakama hannayenta yace  Mami maybe tayi bacci tagaji or wayanta na silent, I believe tamayi bacci bakiga rawan kanta da tsalle tsalle ba irinsu daman sukai bacci kaman sun mutu ne, she must have slept, ki kwanta gobe I will go and find her okay please calm down ki kwantar da hankalinki Mami da kyar ya lallaba Mami ta kwanta bacci ya saceta ya zauna yayi shiru yana kallon Mami datai bacci saiya kalli wayansa, ahankali yasake dialing number ta but harya katse bata dagaba he saw sanda tashiga gida or something happened ne? Ya tambayi kansa bacci da baiyiba kenan yawuce kawai yaje yadauro alwala shimfida dadduma yana nafila.
**


Sai wajajen 1 nadare Ziora tai bacci shima ajikin Ya Chidi afalon sama, du kansu yaran babu wanda iyacin abincin dare ko yayi dinner shigowa gidan Daddy yayi yataho flat nasu yabude kofa yashigo ahankali yahayo falon saman ganin haka Ya Chidi ya kwantar da Ziora anan kan kujera ahankali duk suka tashi sukabi Daddy zuwa dakinsa yazauna kan kujera yana share zufa, Chidi yace  where did she go Daddy? Ahankali Daddy yace  Enugu, and I m calling her wayanta akashe, I will call her Elder Sister tommorow karku bari Ziora tasan Mamanta taje wani gari, I know Maman ku is just angry but nasan she will come back even if not for anyone of us she will come her for her little girl, I will be going to Enugu nima tommorow we need to sit down and talk Chidi dayayi shiru yana kallon Daddy yace  Daddy I know Mommy feels kaman bamu mata adalci ba, but ba a compromise a addini, I m sorry to say but the thing that got her angry hartabar gidan is something that will never happen that s Amrah marrying a Christian so just make it crystal clear and stand your ground kafin kudawo Obinna yace  exactly Daddy yace  no problem kubarta wajen nan kada ta tashi yana maganan yawuce bayinsa yayi wanka yasa yafito yasa pajamas yafito Ziora ce kawai a falo sai Chidi dake zaune yana aiki da laptop ganin Daddy sai kawai yatashi ya shiga dakinsa Daddy yazo ya zauna yana kallonta yana shafa gashinta ahankali ahaka azaune bacci yayi awon gaba dashi.

Wuraren 5 Daddy yashiga bude idanu gabaki dayan Ziora ta shige jikinsa ta chukuikuyeshi ya shiga cireta daga jikinsa ahankali yazame yawuce yayi knocking dakin yayyinta yawuce nasa dan shirin salla yafito duk tare suka fita babu wanda yatasheta, wuraren 6 take bude idanunta Daddy kadai tagani kusada ita dasauri ta tashi zaune idanunta sun kumbura takallesa cikin wani irin shagwaba tace  where is my Mommy Daddy? Tana maganan idanunta na ciko da hawaye.

=ث?KAUNA DA SO=ث?




'

EPISODE 3?? 0??


SUBSCRIBE TO MY YOUTUBE CHANNEL AND LISTEN TO KAUNA DA SO AUDIO
https://youtu.be/q3kNkMVipuY?si=SqD9S_hg9YEJytWI


EPISODE 3?? 0??




Cikin muryan kuka tace  Daddy I want my Mommmmm Daddy yayi hugging nata tace  where s my Mommy Daddy? Ahankali Dady yace  I will go and bring your Mom, kallon Daddy tayi tace  where did she go to? Ahankali Daddy dan baimaga amfanin boye mata ba yace  she s in Enugu tana Aunt Ngozi s house murya chan kasa tace  I want to follow you Daddy dasauri Daddy yace  no stay at home, stay with your step Mom I will come back before 1na rana, now stand up go and pray and shower okay gyadama Dady kai tayi duk jikinta yayi ba dadi Daddy yadagata har daki zuwa bayinta sannan yafito shikuma yawuce dakinsa ya shirya fitowa tayi tahau dadduma tai magrib da isha i na jiya sannan tai subhi batamayi wankan ba takara fitowa tanadan dingishi guiwowinta zafi sabida ciwon dataji, direct tabude dakin Daddy tashiga taga su Chidi na wajen dukansu, Daddy daya kalleta yace  banace kiyi wanka ba ahankali tazo ta zauna tana kallonsa tsaf ya shirya yace  shower and go to step Mom dinki do breakfast awajen don t go anywhere today, while Obinna go to the company and handle things, Chidi go to hospital, your Mommy is just angry but that doesn t mean she can abandon you all, so banson naga wani is sad okay, I m going come here princess tasowa tayi kuka na zuwan mata kafinma ta iso wajen Daddy takara fashewa da kuka tace  Daddy I want my Mommmm Daddy yayi hugging nata yace  kinamin kuka haka so kike na rasa yanda zanyi da kaina eh princess? Oya stop crying karkisa nai missing flight dina gyadama Daddy kai tayi da kyar tai shiru Daddy yasaketa yawuce tana kallonsa Chidi yakalleta yace  dalla wuce kije kiyi wanka kina abu kaman wata yar 5yrs raurau tamai da idanu tawuce tafito tabude kofan tawuce dakinta tamaida kofan tarufe tana goge kwalla today is the first ever time takejin batajin dadin rayuwanta, kuka tayi sosai sannan tawuce tashiga bayi wanka tayo tafito hakanan kawai taji kanta na masifan ciwo tana rawan sanyi kuma bude kofa tayi tafito sai kawai tazauna bakin gado ahankali tana goge kwalla, ringing taji wayanta nayi dube dube tashigayi agaban mirror ta taga wayan hakan yasa tamike ahankali kanta na sarawa tawuce wajen tasa hannu tadauki wayan Mami tagani hakan yasa taji wani sabon kuka yazo mata tadanna wayan takai kunne kafin tai magana taji muryan Mami tace  Alhamdulillah Alhamdulillah, Amrah na ina kika shiga? Eh? Ina kika shiga tun jiya nake kiranki I ve been so worried about you, lafiyan ki kalau? Are you okay eh Amreery? Wani irin kuka Amrah tasakin ma Mami mai jiniya tace  Mami Mommyyyyyyy Mami kawai tamike tsaye tana dafa kirji tace  meya faru? Meya sami Mommyn ki? Why are you crying like this eh? Aliyu dake saukowa daga bene yakalli Mami kadan yadauke kai kawai, Mami tace  Amrah ya isa, ya isa, yimin magana menene ? Cikin kuka Ziora tace  my Mommy left meeeees, she and Daddy fought because of me Mami tace  keda waye yanzu agidan? Ahankali tace  Daddy left to airport he s traveling to bring her back, he told me to go to my step mom my brother are going to work cikeda so Mami tace  kinci abinci to? Girgixama Mami kai tayi tace  a a Mami tace  turomin address na gidanku zan turo a daukomin ke yanzun nan, kizo nan gyadama Mami kai tayi ta katse wayan Mami takalli Aliyu dayaje dinning ya zauna ga coffee gabansa yana taba waya yana sha, tace  Aliyu dan Allah ga wayana Amrah zata turo address a gidansu jeka daukomin ita baice komiba ya karbi wayan kawai ba yanda zaiyine yamike yafita yashiga mota yaja motan, breakfast Chidi yakawo mata yace  eat kije wajen Step Mom I have emergency I need to go to the hospital now, stop crying okay, once nagama emergency I will come back home and pick u up mufita kinji gyadamai kai tayi ya manna mata kiss a goshi yace  stand up and put on clothes tashi tayi tawuce wardrobe nata shikuma yafita, pant tasa red sannan tadauki wani floral gown mai spaghetti hand daya tsaya mata a kasan guiwa da kadan red yanada flowers blue mai bala in kyau, gashin nan nata kaman na mahaukaciya amman hakan makes her even looks prettier, tadawo ta zauna tana tunanin Mommy hawaye na gangarowa daga idanunta kanta nawani kalan ciwo zuciyanta ma yana tashi kaman zatai amai, ko kallon breakfast din batayiba, kusan 15min tana ahaka wayanta yayi ringing takai hannu tadaga ahankali, Mami tagani hakan yasa takai wayan kunne cikin muryan kuka da shagwaba daya shake tsabagen kuka tace  Mamiiiii shiru Aliyu yayi yakai kusan 1min har saida Ziora tace  hello sannan adikile yace  I m outside kifito and don t waste my time wani rawa rawa kirjinta yake jin muryansa, mikewa kawai tayi ita tama mance wani kalan kayane jikinta and

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login