Showing 54001 words to 57000 words out of 61981 words

Chapter 19 - ABRAH Complete Hausa novel

08 Apr 2025

2303

ya shigo,


Dr shireem ne cikin shirin na zuwa Hospital Yayi Kyau so sai sai baza qamshi yake.

Men'parlour ya sauko kujera Atine taja mashi ya zauna black'tea shi ne ta fara had'a mashi sannan ta koma ta had'a mashi kunun gyad'a mai shinkafa wannan shi ne Abin da yafi so thank u Atine.
. Ur wlcm tace" da shi

Bayan ya karya ya ta shi ya haura zuwa d'akin Abban shi dan gai'she da shi suna zaune waje guda shi da Sweetheart tana mashi gyaran fuska

Sunkuyar da kan'shi yayi ya gai'she da su sun Amsa mashi cikin farin ciki .

Sweetheart ta Aje Abinda take ma Abba gyaran Fuska taje ta Rungume danta tai mashi kiss gefe da gefen kumcin'shi shima yai mata A goshi sannan yace" I'm goine to Hospital owk.

Bye tayi mashi Adu,a ya fita yau mulkin ya motsa sawa Yayi Akayi driving din shi tare da rakiyar manyan car's din shi wad'an da suke mallakin shi.

Motar"shi Ce tsakiya biyu baya biyu gaba ta fiya suke Ahankali cikin Natsuwa duk inda suka gitta sai An kalle su domin tsarin nasu Abin birgewa ne duka motacin farare ne ta shice kad"e blue wadda yake Aciki

Hon sukayi a get din Hospital din get man ya bude masu get jiki na mashi rawa sunyi parking inda ya dace suyi parking driver"n shi ne yazo ya bud'e mashi marfin motar cover'shuos din shi farare su su suka fara bayyana wato qafar shi ita ya zuro waje zuwa wasu mintina ya ida fitowa gaba daya ma aikatan wajan sunyi layi suna gai"she shi masu shara da bawa flower ruwa.

Office din shi ya nufa ya zauna bisa kushin irin mai juyawar nan documents din gaban table din ya jawo ya hau dubawa yana saying

.mintina kad'an ya ta shi.

Yafita zuwa duba ma jinya ta

Haduwa sukayi da Salome good morning sir. Salome tace" da shi cikin daure fuska ya d'aga mata hannu.

Bata da muba dan tasan halin mutumen Nata yana tafiya tana binshi hannuwan ta d'auke da fayil tana bashi labarin tawa mara'lafiya da Aka kawo cikin dare tana zubar da jini

Yana jinta Aman tanke bai tanka' mata ba ita kuma bata fasa gaya mashi ba biye take da shi.


*Wacece Salome?"*


Salomi dai ma aikaciya Ce A wannan Hospital din A salinta Yar jahar Ogun Ce

Ba bahausa bace yare ce Nursing ce babbar likita ce tanada gogewa Akan matsalolin da suka shafi mata.


Salomi Aboye mata'shiyar budurwa yar kimani shekara Ashirin da biyar

Salomi tana Matuqar son Dr shireem so sai .

Jiya ta dawo daga garin su ta jima Acan wannan kenan,


Duk d'akunan marasa'lafiya yabi yana shiga yana duba su wasunsu sunji sauqi ya Rubuta masu sallama haka sukai tabi suba dubusu Salomi na taya shi

Har suka iso d'akin matar da Aka kawo tana zubar da jini so sai take zubda jini

Bafulata bace bayan sun shiga cikin har'shen turanci Salomi tasake Yi mashi bayanin matsalar ta wai planing ne tayi na kwayoyi batabi qa'idar shi ba shine ya bata matsala sannan baya ga haka tanada matsala A gaban ta dolle sai Anduba ta

Dan jini sai wari yake
Dr yagi ko yawu bai iya hadewa ya dauki Abin Rufe Hanci da safar hannu yasa ya matso bakin gadon yace da ita tana kwance gyara A duba ki bude qafafunki

Yasa hannu zai yaye zanan ta
Aiko bafulatanannan tai maza ta ta shi zaune .

Ta gyara zamanta ta d'auki qafarta daya ta Dora kan daya tace " Aradun Allah likita da mai'shi.

Dr ya mai mai ta dan daga shi har Salomi basu fahimci bafulata'na ba Dr yace ki kwanta nace na duba matsalar ki

Aiko ta qara jawo zananta ta tura tsakan'kanu qafafunta tace" shin likita Aradun Allah bazan kwanta ba wallahi tallahi bazan bude maka wanga wuri ba dan Wallahi da mai shi . yo'idan Na bude maka hardo yagani fa Aiko naga boni wanga wuri ka ganshi Aman wullahi bazan bude shi ba sai dai kabani magani

Yanzuko sun fahimce ta Salomi ji take kamar ta maqare shegiya dan tabata haushi cikin zuciyar ta sai d"ura mata Ashar take mi Dr zaiyi da ita Abu haka cikin qazan"ta sai tsami da wari da qari take
Ko ita da take haka ai Dr bai kulata ba balle ita Yar daji.

Shiko Dr dariya ta bashi so sai yanda ta dage tana fad'in da mai'shi bayan da bayyi da ita Akan ya duba taba Aman taqi ita dai da mai'shi

Tambayar ta yayi INA mijin nata tace yana waje Salomi ya kalla yace taje ta kira shi
Cikin haushi ta fita mintina kaden sai gasu sun shiga

Dr ya dube shi da uwar sandar shi ga hannu yai mashi bayani yanda sukayi da matar'shi

Budar bakin mijin sai yace Aradun Allah likita nata ne .

Kai Fulani ba dai wauta ba😄😄 saura kice dake nake teemarh😄😄


Dr shireem yaga zasu 6ate mashi lokaci yace da mijin ya fita ya fita ya tsuke fuska ya daka mata tsawa yace gyara ai jiki na rawa ta kwanta ita da kanta ta yaye zanan ya dubata matsala ce so sai A mahaifar ta saka makon magani da take sha mahaifarta ta so lalacewa dan sai Am'mata Aiki so sai gare ta dan haka sai ya fad'a ma Salomi matsalar ya wakiltata da tai mata Aikin yanda ya kamata Shikuma ya fita ya koma office din shi

Salomi taci gaba da yimata aiki yanda ya kamata domin tanada kwarewa so sai Akan matsalolin mata .

Minitana 30. Ta gama ta fito kai tsaye office din shi ta nufa yana zaune da phone din shi yana duba chart din da sukayi da Abra jolley inji shi hello tace da shi ta samu waje daya daga cikin kujerun ta zauna Dr cikin zuciyar yake fad'in ta dawo fa yanzu ba sauran zama lafiya zata matsamani

Sa shi gaba tayi tana kallo ita dai Dr shireem ya mata komai na shi ya mata yana birgeta ba kad'an ba Aman yaqi bata dama akan soyayyarta ita fa ko ba Auranta zaiyi ba ya kama su d'an soye koda soyayyar shan minti ce.

Yanda take kallon shi duk ya tsargu dan haka phone din shi ya Aje shima ya zura mata ido yana qare mata kallo.

Salomi Baqa,Ce Amman taxi bilicin duk ya feso mata quraje man bai Amshe ta ba doguwa Ce tanada jiki so sai da manyan idanu bata gashi kai so sai dan ko yanzu kitson gashin doki ne tayi irin shi nan mai kala biyu Baki da bula Anzuboshi har ga baya Ansa roba An daure

Shiga suit Ce tayi farare masu guntun siket dawasu dogayan takalmi masu shegen tsini wuyan ta sanye da sarqa irin tasu ta Arna mai zanan kuros sai yar barima data maqala A kunnanta .

Hannuwanta ko nace yatsun hannuwanta sun sha Akai' fun roba Ta masu Ado da jan'farce Dr cigaba yayi da kallonta harya zuwa kan manyan nonuwan ta rusa rusa dasu itako ganin ya maido kallan' shi ga nonuwan"ta harda qara gyara zama yanda zai gansu da Kyau tana cin cingam yana kanne mashi ido guda sai wani qas' qas take da cingama fuskarta ya kalla sai kwarkwasa take mashi bai son haka take ba sai yau da ya qare mata kallo wani bajejan hanci ne da ita irin mai fadin nan duk ya cika mata fuska. Manyan lipes dinta sunsha lpes glass sai kyali suke ga urban Eye shadow ta sha hummmm yace tare da sauke Ajiyar zuciya ya tsani macce data cika kwalliya wai shi Salomi zata Ce tana so gaskiya ta cuce shi .

Telephone ya jawo Yayi kira Aman ga Alama bai samu Wanda yake kira ba.

Tsaki Yayi yace da Salomi cikin har'shen turanci da ta gyara takardun dake gabanta .

Aiko kamar jira take tasa air pis ga wayar ta ta kuna waqa ta liga air pis din A kunnanta ta dauki bro

Ta cigaba da aikin da yasata sai waqarta takebi mai taken doro doro buciyoyo doro doro doddodoro kai banfa iya waqar ba Aradu😝😄😫

Kallon ta yayi yanda take waqar doro kamar ita ta rerata

Dan Haka shi ta shi ta shima Yayi ya shigewar shi qurya ya kwanta kan bed ya lumshe idanun shi itako jin yata shi tabi shi da ido ji take kamar taje ta rungume shi. Aman badama.

Cigaba da ainta tayi har tagama ta jima tana jiran shi Aman shiru bai fito ba dan haka ta yanke shawara Shiva ciki ta isko shi shikuma barci ne yai gaba da shi tare da mafalkin Abin kaunar shi Abra wai yana kwance kan cinyarta ita kuma yana shafa sumar kan' shi

Yanata murmushi Salami tajima tsaye tana kallon shi yanda yake barci fuskar shi dauke da murmushi

Jitai kamar tai'ma cute lipes din shi kiss Aman badama dan haka ta kai hannuta bida lallausar sumar kanshi dan itace mai saukin ta6awa gareta jin Anashafa kanshi ya dauka duk A cikin mafalkinne sai wani qara gyara kwanci yake ita kuma jin taushi sumar shi tasa hannuta ciki taji sun lume cikin sumar har wani lumshe ido take tana fadin Ashe haka sumar take da laushi sai yamutsa mashi suma take shikuma jin Abin na yawa yasa shin kamar ba,a mafalki bane ita kuma dai dai ta dugo kanta Zara sumbaci sumar shi dai ya bude idon shi Yayi to zali da bajejen hancin ta zumul Yayi ya tashi zaune ita kuma taja baya wani mugun kallo ya watsa mata Wanda yasata fita bata shirya ba tana fadin sorry sir. Da idanun shi yabita wadanda sukayi jajir saboda baccin da ya dan dauke shi sai wani motsa mazauna take rumtsai idanun shi yayi tare da gilgiza kai yace" mata mata!!

Ta shi yayi ya shiga toilet ya watsa ruwa domin yau juma,a kuma yaga lokaci na qara towa ya fito ya gyara jikin shi tare da shafa mai ya sake kayan shi farar shadda yasa da farra hulla .

Yanada komai a office din shi kamar yana gida tarare yasa sannan ya fito dan zuwa masallaci Ahanya ya gadu dasu Sauban da Sudais suma zasu masallaci sun gai'sa kowa yayi wajan motar'shi .

Shima Dr ya shiga drive ya sahi kamar d'azun sukafita zuwa masallacin q'erau shi suka nufa domin halartar sallar juma,a


Abra sai shirya shirya tarbar Malam Bilal Ake domin yau ne yace"mata zai'zo in anfito juma'a tasanar da dadyn ta cewa malamin su yace zai'zo su gai'sa dady yace"to sai ya shigo .

An gyara dakin saukar baqi harda su tararen wuta komai ta kai na motsa Baki shi kawai Ake jirah momy dai sai binta da ido take domin itafa tafi son Dr da kowa kuma tana mata Adu,ar samun shi A matsayin miji.

Bayan Anfito juma,a kamar yana yace" gidan su Abrah yayi tsinke sai da yazo bakin get sannan yace mata gashi yazo A time din. Ita kuma suna tsakar cin Abinci ta dubi mahaifin ta dan shima sun rigada sun dawo daga masallacin shida hanif

Dady shinan yazo malamin mu owk Hanif jeka shigo da shi d'akin baqi hanif yafita yana turo Baki cikin ran'shi yace"sai ya kira Dr ya fad'a mashi .

Mai gadi hanif yace ya bude get shi kuma Bilal ya shigo da motar'shi hanif ya gai'she shi cikin girma mawa domin sun samu tarbiya mai'kyau

Ba laifi kyakyawa ne cewar hanif da yaqarema Bilal kallo .

Jagora yai mashi zuwa d'akin baqi sannan yaje ya sanar dasu .

Abrah ta jima bata ta shi ba sai da dadyn ta yace kin bar baqo shi kad'e maza jeku gai'sa ki dawo inada magana sake to'Dady tace " gabanta na tsaneta faduwa

Da sallama ta shiga yana zaune yasha lallausan yadin shi mai tsadar gaske ya hullarshi mai Kyau ya Murza .

Gai'she shi tayi ya Amsa yana binta da kallon so da qauna ..

Sundan ta6a hira soyayya inda yace mata zai'tafi hajir'su naji ranshi zai kai ta wani waje sukai sallama ya fito ita kuma tai cikin gida ..tayi karo da Dadyn ta shikuma zai fito .

Da sauri saboda kiran gaggawa da akai mashi wajan kasuwancin shi


Bilal gabi Dadyn Abra na tafowa yasa shi tsayawa su gai'sa sun gai'sa Amutunce inda Dady yace mashi yanzu sauri yake Aman zaine meshi Bilal yace to yai godiya kowa ya kama gaban shi ..



k'arfe 4 dai dai. Sirina Ce taxi kwalliya Abinta sai baza Qamshi take ..

Tace mommy na tafi sai na dawo mommy tace to Sirina ki gai'she man da su hajiya tace to zasuji

Sirina tama mommyn ta k'arya A kan zataje gidan kakaninta Alhalikuma bacan zata ba Hospital zata wajan Dr shureem kamar yanda taima kanta Alqawari

Tafe take cikin motar'ta zuwa Barhim inda Hospital din yake haka dai taci gaba da driveng din ta duk kuwa da gabanta na faduwa .

Har ta iso cikin Hospital din tai parking din car din ta kai tsaye ta tambayi office din Dr shireema A ka nuna mata .

Bakin office din taja ta tsaya na yan mintina kad'an tana wasu'wasi zuwa can tayi shahada tayi nocking yes comeng shine taji zazzaqar muryar shi mai'kama da busar sarewa tace sai' tai Ajiyar zuciya sannan ta shiga da sallama dago kan'shi Yayi dan gani wanene kyakyawar yarinya ya gani ei Sirina kyakyawace

Asalinsu ba yan nan bane Buzayene na Agadas

Wurin zama yanuna mata ta zauna tare da gai'she shi UA Amsa mata yana mata kallon kamar ya ta6a ganinta


Shuru sukayi bawanda Yayi magana shi yana jiran yaji mike tafe da ita ita kuma tana tunani ta INA zata fara ..


Gyaran murya Yayi yace mike tafe dake baiwar Allah mike da munki .


Kallon shi tayi ido cikin ido

Sannan tace mashi Abinda ke damuna bakomai bane Illa ciwon so ciwon so ke damuna matsalata ta so ce ciwon so ne ke damuna ba komai ba shine nazo kabani maganin shi.


Tunda tafara magana ya zaro ido shima yana kallonta kamar yanda itama take kallon shi

Kuma Abida ya fahimta bikin gaskiyar ta take fada mashi dan yaga hakan Acikin idanun ta .

Sai yace da it'a kinada hankaliko INA kika ta6ajin haka Aini bani bada magani ciwon so sai dai Na rashin lafiya .

Shima ciwon son Ai rashin lfy ne babba

Ta ci gaba da cewa ba komai bane ciwon so na illa kai kai ka haddasa man shi kai ne Make so Ina sonka Ina sonka so sai nake mugun sonka Dr shireem .

Ba Abu qarami bane zai'sa macce tace tana son Na miji gaba da gaba


Saboda kunya ta diya macce da Aka Santa da it'a Aman ba haramun bane dan kaga Abinda kake so kace kana son shi

Annabi yace duk Wanda kakeso to kafada mashi kana son shi .


Babbar matsalar munan hausawa ba mu dauki Kalmar so da mahimmanci .


Alhali kalma Ce babba mai matuqar mahimmanci Agurin Wanda Aka fada mawa da Wanda ya fad'i


Larabawa da turawa suna mutunta wannan kalma suna darajjata domin ingancinta

Kalmar so kalma Ce mai Nauyin gaske mai matuqar mahimman ci


Dan Allah kaso ni kamar yanda nake sonka

Dan Allah ko sau daya ne kace kana so na ta qarashe fada da hawaye taf idanta



*tofa komai Dr zai'ce da Sirina shin zai Ce mata yana sonta kamar yanda ta buqata ko sau daya ne*

*Shin koya zata kasan Ce*

*To dai kubiyoni sannu A hankali dajin ya zata kaya*


*More comments more typing*




Ammyn khairat Ce golden girl 😄💔💃🏻🥰
*♠ABRAH♠*

*Na*



Ammyn khairat
*Golden girl*


*Dedicated to Teemarh cute*

(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)



тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09


*PAGE3839*


Dr ta jinjina kai yace yi haquri dai na kuka aman Baki. Fada man sunanki ba

Sirinah ta share hawayen ta da bayan hannuta tace" sunana Sirinah Sirina Dr ya fadi sannan Yayi Ajiyar zuciya yace" Sirinah nan garin kike"?Sirinah ta daga mashi kai tace ei nan garin nake owk inji Dr.

Yace" Sirinah naji jawa"banki kuma na gode so sai dan baqaramin na mijin qoqari kikayi ba Abinda kikayi Abin Ayaba makine kuma Ajinjina maki dan kin zama jarimar macce ba duka mata bane zasuyi irin Abinda kikayi gaskya kin birge ni so sai!!!

Sai dai wani hanzari ba guduba shine. Kamar yanda kika buqata gaskiya bazaki samu soyayyata ba ina sonki so irin na musulinci Aman ba so na Aureba domin zuciyata guda Ce kuma na mallakama wata ita sai dai in maki fatan Alkairi Sirinah Allah ya Baki mijin nagari Wanda ya fini komai Wanda zai kula dake fiye dani

Sirinah ta fashe da kuka tace dan Allah Dr shireeeeeeem ka tausaya man wallahi INA. Sonka dab Allah ko ban kai macce da za,a soni ba mike makusata Dr ya sake kallonta da Kyau yace look Sirinah Baki da makusa ko kadan Aman kifahimci Abinda bake gaya maki kamar yanda kike so na haka nima nake mahaukacin son wata so ba nawa saba son da nake mata ya wuce tunani mai tunani dan idan har narasa ta zan iya rasa tawa Rayuwa baza iya Rayuwa babu ita ba dan ita itace Rayuwa ta itace komai nawa itace bugub zuciyata ke idan zan kwana ina gaya maki irin son da nake mata bazn ta6a gajiya ba na tabbata ke Baki man irin son da nake mata domin ke in kirasani zaki iya Auren wani Niko in narasata bazan'ta6a Aure ba har Abada dan haka Ban fatan Narasata dan rasata dai dai yake da rasa tawa Rayuwar !!

Baqaramin so nake mata ina maruqar son Abra so ba nawa saba so dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login