Showing 30001 words to 33000 words out of 61981 words
zun yace" bazaki mutu ba gimbiya insha Allahu sai lokaci yayi" ina cikin damuwa mai tarin yawa akan wannan ciki naki" ban ta6a jin ko ganin cikin da yai wannan watannin ba a haife shi ba daman ciki na kai wa wannan lokacin haka koko dai sai nakine ya kai wannan lokacin
Abinda yafi dau reman kai shine" yanda likitoci basu da muda yawan watanni da cikin yai atare dakeba? Kowa sai dai yace "man lafiya ina cikin damuwa" sosai"
Ita" kanta " gimbiya wasu zafafan hawayene " suka cika mata ido daurewa kawai take" domin ita" kade tasan halinda take ciki" ita"kanta" ko a labarai ko afilm bata ta6a samun wanda ciki yai kusan shekara biyu baa haife shiba" kuma bai motsi " kuma yana girma" sannan ace wai lafiyar sa lau"
wani lokaci har tunani take anya kau ciki ne" take dauka" abin na daure mata"kai sai inda hankalinta" ke kwanta wa shi ne likitoci suna shaida mata" cewa abinda ke cikin" yana cikin qoushin lafiya" da ba mutum bane" da sungani" ko suga wata Alama"
hawaye" suka zubo mata masu zafi da daci" lalai wanna jarabtace" Allah ya daura mata kuma" ina roqon"Allah yabani" ikon" chanyeta
Muhammad yace" amee" ita duk atunanin ta cikin zuciya take zancen ta bata sanko duk abinda take fada" muhammad najin ta kuma kyaletane yayi" domin yabata damar gama tunaninta"
Sannan yace" mata abinda nake so dake" shine ki rage tunani dan shima wani ciwon ne na daban duk kuwa dana son tunani dolle ne a gareki aman ina roqonki da ki rage shi" kibarwa Allah komai" dan shine magani komai" kuma babu abinda ke dauwama sai ikon rabbi komai yai farko to yanada qarshe mu dage da adu'a muna gayawa Allah buqatummu dan shi mai jine mai gani kuma shine gafururahim ne"
Babu abinda ya gaga reshi shine mai kumfayakun wanda in yaso abu ya kasance zai kasan ce kinji kiyi haquri ki rungume kadaraki da hannu biybiyu ki kuma yima Allah godiya" a kowane hali ina roqon Allah yasa kaffara ne a gareki kuma nima zan dage da tayaki adu'a ba dare ba rana insha Allahu"
"gimbiya ta nisa tace" mashi to na gode" my da nasiha ka agareni" zan dage sosai wajan gayawa Allah insha Allahu" kuma kamar yanda kace babu abinda ke dauwama sai ikon Allah" wanna haka yake warana komai zai zama labari na gode kwaire mijina Abin alfahari agare suka" rungume juna su cikin shauqi da so da qauna" game da tausayin" junan su"
Suna"cikin wannan haline" sarauniya" ta kira muhammad sai" ya daga" Bayan sun gaisa sai"take" cemashi ya ake ciki" me likitocin sukace" sai" muhammad yace" mata sunce komai lafiya lau bata da wata matsala kuma" na roqi da sufa sata sufida mata cikin sunce a a"
"ok inji sarauniya "sai tace" kuyanki tikiti" yanzu" kutafo nan dan a kwai wani kwararen likita da nai ma magana zai duba man ita sai"yace to insha Allahu" sai mun tafo" tace" to Allah yakawo ku lafiya suke"amme"
Ya dubi gimbiya dake sauraran su yace" kinji abinda sarauniya tace" yanzu zamu tafi can mesira insha Allahu gimbiya idanu" sun cika da hawaye ita dai gaskiya tagaji da gani likitocin nan dama zasu qyaleta da yafi" tace mashi to"
yafita yaje yai ma likitocin bayani" akan suba shi takarda sallama zasu tafi sai" suka rubuta mashi" tare da basu wasu kwayoyen da zatai amfani dasu" wadan da zasu tai maka mata wanja tage kumburin da itayi dan shine matsala"
Airport *MESIRA* dandazon jama,a ne ta ko ina gasunan sun cika airport din du kuwa da girman shi aman cike yake da mutane daban da ban musamman ma masu kaya na gidan sarauta gasunan maza da mata yayin da ga kwalaye nan ga hannuwan su anyi rubutu da manyan baki"
kamar haka" *Ur WELLCOME GIMBIYA ZEENAT* shine abinda ke rubuce gefen su kuma wasu mutane ne da bindigu a hannuwan su suma sanye suke da kaya iri daya suit fuskar su kuma sanye da gilashi biki fuskar nan tasu ba alamun dariya tatare da ita
sai busar Alagaita ke tashi da kuma jiniyar motoci mintina kadan sai ga jirgin su ya sauka fasinja sunfara sau kowa kowa sai baza ido yake yaga wanda yazo dau ka da ga ciki ko harda masu dauke da kwali sao qara da gashi suke sama suna waqa" da baitika da kirari na diyan sarauta"
shuru kowa ya gama fito wa aman ban da su dalin qin futowar su kuwa shine" qafarta ta ruqe ta kasa daga ta kuma muhammad yace" ya dauke ta tace" a a shiya sa har kowa ya fita ban da su ganni kowa yafita kuma qafar bata saki ba" ba tau auneba ya sabeta yai mata dauka jarire" ba dan taso hakan ba taso ace da kanta tafita saboda ta taga ta ga anzo daukar ta"
koda ya zuro qafar shi yafara fito wa sai suka gansho dauke da gimbiya su kansu hankalin su yata shi cikin sauri tunka fin ya ida sau kowa suka shinfida wani qaton kafet ja wanda atsakiyar shi shima anyi rubutu da manyan baki wellcome gimbiy zeenat "
ta saman shi muhammad ya tako yayin da na ga wasu bayi dauke da wasu irin tururuka masu shegen kyau dauke a hannu su cike da fulawoyi masu kyau muhammad na tafiya suna watsa masu fulawoyin tare da rera masu waqoqi harya zuwa bakin mota inda nanne qarshe kafet din
wata zungureriyar motace hadadda mai shegen kyau ita aka buda masu gidan baya ya ajeta sannan shi ma ya shiga ya zauna suka tafi inda akasa motar su tsakiya na bayen su motocine da yawa sai jiniya suke wadan da muhammad ke tunani na sugaban qasa ne duba da mutanan da ke jan motocin
duk ta inda sukabi sai kaga mutane na kawo gai suwa wasunsu kuwa harzubewa suke qasa suna gaisuwa lallai muhammad yaga sarauta da mulki" tunkafin ma suje gidan ita dai gimbiya ta lafe ga jikin shi tana ta kanta bata san abinda kefa ruwa muhammad shida ke baqo shi ki kalle kallen shi
Sun isa *masarauta mesira* babbar masarauta ce ta gani ta fada masarauta mai cike da dumbin tarihi masarauta mai dauke da izzar mulki aman duk da hakan sarkin ya kasance mai adalci shiya yake da mutane talakawan shin nasan shi domin shi mai kirkine da tausayi agare su shiya suke girma masho so sai bama iya shi dade ba duk wanda ke wannan masarauta sun girma mashi"
musamman ma yanzu da aka kawo sauye sauye da tsare tsare saka makon na da sarauniya karima da akayi tasake kawo cigaba so sai awannan masarauta kuma suna jindadin mulkinta saboda itadin mai adalicice agare su tayi gado wajan mahaifin ta"
koda motocin suka tsaya sai" aka bude masu tasu suka futo dan zuwa cikin gida nana ma tun daga bakin motar aka sake shifida wani kafet din ga kuma wasu bayi maza da mataa sunyi layi haggu da dama sunsa kafet din tsakiya ga wata kalar busa da suke mai nuni da iso warsu yanzuko da kanta ta tako hannuta ruqe da mashi sun tafiya ana masu kirari bayin kuwa sai duqawa sume suan kawo gai suwa gare su kai inka ga tsarin abin sai ya birge ka"
farba ta musamman akai masu masauki biyi aka basu gimbiya guda shima guda yau sarauniya ba zaman fada wannan rana ta yar tace" sunci sun sha sannan
Aka kai su wajan mai martaba tsohon sarki suka gaishe shi ya amsa cikin farin ciki inda gimbiya ta aza kanta bisa qafafun shi shikuma yana shafa gashin kanta yana mata sannu ya tau saya mata ba kadan ba sai fira suke da muhammad sosai shi kan shi muhammad yayi" mamakin yanda suke ta hira dashi abinda yanura sarki yanada saukin kai yayin da ita kuma gimbiya bacce ga jiya ya dauke ta muhammad ya kalle ta yanda take bacce da ka gani kasan baccen wahala ne bana jindadi bane yace ita wanna ma tayi bacce ko akai ta daki"
mai martaba yai murmushi yace" kyale ta ta tuna quruciya ai inta zonan bata da wutin bacce sai saman qafafuna barta har sai tata shi duk da na tsufa ina iya dau karta muhammad shima" yai dariya ceto bara nima najai na huta yace" inji mai martaba
muhammad yanufi" masaukim shin dan hutawa kuma ya shiga yana qarema masukin nashi kollo komai yaji wuri ya hadu an shirya ma duniya kamr baza amutu ba lallai masarauta ta burge shi ta hafu iya haduwa nan ya watsa ruwa yayi sallah ya kwanta sai bacce
acan kuma mai martaba ya sa jikan yar tashi gaba yana kallo yanda ta koma tafita haya cinta ga qaton ciki kamar ya fashe yafito da kanshi bai ta6a gani girman ciki irin wannan ba sai ga jikan yarshi hankalin shi ba qaramen tashi yayi ba yana tausaya mata so sai gashi cikin farko abu ga qaramar yarinya shima idanu sun cika da hawaye sai gangarowa suke bai sani ba jin dumen wani abu kamar ruwa yasa tata shi taga kakannata na kuka kuma yana ta kallon ta shima ita yake kallo ta girgiza mashi kai alamar yai shuru
Cikin barkonci tace" ina bacce na zaka tadeni da kukan ka ko so kake nima nayi kuka ko ka tuna da tsohuwar matar ka margayiya shine kai zaune kana kuka to inka tunata kabi sai dariya take yanda taga hawayen shi suqin tsayawa da dai taga abin bana lafiya bane itama sai ta fashe da kuka wanda yafina shi daman ita kullum cikin qunci take daurewa ne kawai take da kuma qarfin adu,a da take itace samun sauqinta
gani kukan da take yafi nashi sai yace" ke kukan mekike halankin tashi kinga baki ga mijinki ba to bai tafi ba yana can yan bacce shima yamai da abin wasa yace" haba matar ishuru mana kinji mijinki bai tafi yabarki ba dan gayanzu kinfi sanshi dani yayi kalar tause sai ya bata dariya tace ba kai bane ba ni bara ma naje nai sallah
yai dariua yace" kije dai ki gano mijinki zakice ta Eh shi zangano kaima bayanzu kagama kukan matar kaba katuna ta ta tashi da kyar ta taka zuwa masaukin su ko ta kalme yanzu bata sawa saboda kumburin qafar ta mai martaba yabita da kallo yanda take ta fiya cikin duk ya janye ta ita daban cikin da ban Banyan ta watsa ruwa tai sallah
ta nufi wajan mahaifiya tata ta ta da ita zaune tana futawa gefen ta kuma wani kyakyawan mata shine zaune suna hira tunda ta shigo wannan mata shi ya qura mata ido yana ta kallon ta ko kyftawa bai yi har tasamu wuri ta zauna ta gaishe da sarauniya tace" mata barka da hutawa
tace" yauwa tare da jawo gimbiya kusa da ita tace yanzu mike maki cieo mekike so kin jin yuwa ta kama qafafun ta dakan ta tana mam matsa matasu gimbiya tace" banji yunwa ba abinda keman ciwo
ta kai duban ta ga wannan mata shi tace Ammar bako magana sai aita kallona wanda ta kira ammar yayi dariya yace bari nai ki huta sannan yakike ya qafin jikin tace" da sauqi Alhamdulilla
Sarauniya tace" ku shirya keda mijinki ga Ammar nan kuyake jira mahaifinki zai aiko dau karki yanzu zuwa gidan shi tace to " bari nata shirya sai na fada mashi ta ta shi tai daki dan shirya
Sun shirya motoci sun zo an dauke su zuwa fadar sugaban kasa muhammad tunda suka gaisa da Ammar basu sake magana ba da ma sun had ido da shi sai ammar ya harare shi yarasa da dalilan haka dalilli kuwa shine ammar dan waziri ne da yaso gimbiya shine muhammad yai mashi shirgar sauri mafarin harare hararen kenan
*♠ABRAH♠*
*Na*
*AMMYN KHAIRA*
(GOLDEN GIRL)
*PAGE 19*
(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/
TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
*kyautar page ga proficienat writers association*
Agurguje
Motoci"ne" da yawa sukazo dau karsu" dan zuwa fadar sugaban kasa" fadar sugaban kasa" fadace ta alfarma " am masu iso har wurin shi" ya tarbe su hannu biybiyu
Cike da farin ciki" sai murna yake" da ganin yar ta shi Bayan sun gaisa muhammad yace rankai dade" muna qara" ta" yaka murna" abisa wannan nasara" da kasamu" Allah yasa Alkairi ya kuma baka ikon yin Adalci "Ameen" sukace su duka"
"Ambasada ya dubi" yar shi cikin tausayawa; yace "yanzu wanne hali" ake ciki"? game da cikin nata da kuka zuyarci likita"? mesu kace"?
Muhammad ya shaida da mashi yanda sukayi" da likitoci"
Ambasada banga" taza maba" kutashi mutai" taga manyan likitoci nan" sai ammar yace" da man akwai likitan da zan kaita" wajan shi yanzu ya duba ta munyi magana" da sarauniya daga nan zamu wuce can wajan shi"
Sai Ambasada yace to mutafi can din muji Allah yasa a dace sukace "amee" suka fito gaba dayan su tare da rakiyan manyan motoci" na Alfarma
"shahararan hospilat ne" mai zaman kanshi suka nufa na Dr shuwab kwararen likita da yasan aikin shi" yayi chakin dinta yanda yaka mata" bai samu matsalar komai ba "
haka yai masu bayani dukan su sun shiga da muwa da qarin" Al ajabi na" wannan lamari haka suka dawo gida ransu ba dadi;
Daret gidan sarauta suka nufa" mai martaba sai murna yake da gani sirikin shi" kuma sugaba na wannan qasa" Bayan gaishe gaishe"
suka sake tau tau nawa akan matsalar gimbiya nan mai martaba yace" wannan abu abin al,ajabi ne" nai dai ko a labarai ban ta6a cin karo da irin wannan b"
Ace ciki kusan shekara biyu" haihuwa shuru wannan yarinya ina tausa; ya mata
So sai Allah dai ya rabata da shi" lafiya "ameen inji Ambasada yace" dolle a tausaya mata" matuqa"
Bayan Ambasada ya fito daga wajan mai marta ba sai ya nufi cikin gida inda sarauniya suke zaune da gimbiya
Da sallama ya shiga sarauniya ta amsa mashi" murmushi dauke a fuskar ta" shima murmushin yake jifar ta" da shi sai kallon love suke ma juna" Ambasada ido ya rufe yaje ya rungume mata shi yana kissn dinta ta ko ina itama ta biye mashi tana mai da mashi" da martani
Gimbiya sai kallon" su take mahaifan nata" na burge ta" haryanzu" soyayyar su suke suna cin duniyar su da" tsinke"
Gani sun manta" ta da ita" zaune yasa tai gyaran murya suka" saki junan su suna dariya" sun jima sun hira inda aka kira" Ambasada Ana nai manshi nan yai ban kwana dasu" sai gimbiya tace mashi" gobe zasu koma" yace" Allah ya kai mu" ya tafi"
Tun Asuba" suka shirya kasan cewar jirgin safe za subi" Bayan sunyi kari suka yi ban kwana da masarauta da inda gimbiya tai ta kuka kamar ranta" zai fita tana mai neman gafar sarauniya tana cewa ta yafe mata"
Sarauniya "tace na yafe maki duniya da lahira baki man komai ba ki dai dage da adu,a nima zan tayaki insha Allahu komai zai zo da sauki ina maki fatan Alkairi
Sarauniya ita ma idanun ta sun cika da kwalla ba dan ta so yar tata za ta tai tabar taba" taso ace gaban ta zata haihu" tana matuqar tau;santa sosai da tana da iko da tace muhammad yabar mata yarta" aman bata da wannan iko akan ta sai dai a matsayi na na uwa nabita da adua"
Gimbiya sai kuka" take kamar ranta zai fita gani take ahalin da take ciki kamar ba zata sake" dawowa wannan masarauta ba shiya sa take kuka tana qare mata kallo"
Bayi duk sun futo kowa dake gidan sarautar sai da yafito suma wasu daga "cikin su masu taushin; zuciya sai zubar da hawaye suke"
mai martaba yace" yar ta kiyi haquri kiba kuka kinji kije Allah yai maki Albarka kina tare da adu,armu ba abinda zai sameki"
Gimbiya "ta rungume shi tace to" na gode kuyafe man du abinda nai maku muza mu tafi inda rabon musake ganawa zamu gana inkuma rai yayi halinshi kubini da adu,a tasaki mai marta ba tajuya zata tafi qafar ta ta ruqe ta kasa da gata
sai sarauniya "da kanta ta kama ta zuwa bakin mota aka bude mata ta zauna sarauniya "bata bari sunqara koda hada ido bane tai cikin gida da gudu ta fashe da kuka na tausayin yarta da kuma halin da take ciki
ita gani take kamar mutuwa za tai cikin kuka ta daga hannu sama "tace ya ubangiji ga bai warkanan dubi lamuran ta kara bata da wannan ciki lafiya dan girman Al,arahin ka dan darajar manzon mu annabi muhammad (s.w.) ta shafa mai martaba dake bayan ta yana jinta "yace "ameen" wannan itace adu,ar da ya kama taki mata a matsayinki na uwa" ba kuka ba"
tau murmushi tace "insha Allahu yace" kokefa"
Aerport nan suka tarda Ambasada da tawa garsa suna jiran su shima gmbiya rungume shi" tayi tana kuka tana nai man gafara shi yana shafa kanta" yace na" yafe maki" bakiman komai Allah yai maki Albarka
*jirgin su ya daga a najeriya*
sun samu tarba ta musamman ga Atine saboda bada ita suka tafi ba ta shirya masu komai kan abinci da na sha
Dan dazon mutane da ke zama" qofar gidan shi" sai sannu da zuwa suke masu yayin da wasu ke tausayawa gimbiya dan gani ta dawo da cikin kamar yanda tatafi da shi dan yanzu ya qara girma ba kamar daba cikin tausayawa; sai sannu suke mata da adua Allah ya sauke ta lafiya
Ita kanta Atine ta tausa ya mata ba tai tunani gani