Showing 9001 words to 12000 words out of 59470 words

Chapter 4 - UWA KO UKUBA MShakur HAUSA NOVEL

M SHAKUR   

28 Mar 2025

3086

Malam yamata dukan latti jiya daman ta dakeni” ballamata harara
Ramla tayi tace “zan fasa miki baki fa, wayace ki taba mata hoda ba saisa ta dake ki ba” turo baki tayi
tajuya ta cigaba da karatunta daidai nan Malaminsu ya shigo wani Ustaz ne da dingilallen wandonshi
yasa hula akai ga dorina akan kafadarshi ko kadan baya ragama anyone cikinsu wanda hakan umarnin
Baba ne saisa suke tsoronshi ba wasa duk wacce tai latti ko takasa bada hadda akwai duka although
hadda Saturdays and Sundays suke bayarwa, baice komiba yawuce gaban aji ya zauna zauna.
Tana shiga bayi ko brush batayiba tafito tasa hijabi tai salla ko azkar batayi ba ta mike tsaye tadauki
daddumanta ta ijiye kan gadonsu tadauki Qur’anin ta tazo kofa tafito gabanta na faduwa sosai ta shiga
sauka kasa tafito tawuce class ta window ta leka ganin Malam yana aji haba saita kasa shiga idanunta
take sukai ja, masallacinsu ta kalla tasan Baba na ciki but dazaran tawuce zata shiga masallacin Malam

zai hangota hakan yasa tajuya takoma flat nasu tabude tawuce kitchen nasu tana bude kofa taga wata
mata but bata dazu ba wannan looks exactly like Ramla tareda wasu mata da kana ganinsu kasan yan
aiki ne binta da kallo matan tayi hakan yasa arude idanunta sunyi raurau tai wajen matar kaman zatai
kuka tace “Ammi” wani kallo matan tamata tace “yauma kin sake latti ko Husna” saiga hawaye kaman
jira take tace “Ammi dan Allah kisani kowani aiki zanyi I will even cook abincin lunch din su Yusra
saikicema Malam kene kika sani aiki yau su Gambo basajin dadi basu tayamu aiki ba kinji Ammi wlh
dukana zaiyi” Ammi na kallonta tace “inaji ana tashinki fa kikai shiru Asma’u? Mesa bakiji kullum kece ke
latti eh kinsan idan Baban ki yazo yaganki a kitchen din nan ranki harda nawa saiya baci da safen nan dan
haka wuce kitafi kibama Malam hakuri kinji” girgizama Ammi kai tayi kawai tasaki kuka zatai magana
cikin kakkausan murya akace “Asma’u” juyowa tayi arude ganin Mom ce saida kirjinta yayi mugun
faduwa kawai tafashe da kuka sosai taboye bayan Ammi tace “na shiga uku wayyooo Allah Ammi
Mommy zata dakeni mari na zatayi Ammi” dan murmushi Ammi tayi tace “Mommy dan Allah kimata
hakuri kada ki tabata yanzu zata tafi kinsan Asmeey akwai tsoron duka” Mom zatai magana duk sukaji
muryan Baba. “Meke faruwa awajen nan?” Duk juyawa sukayi daidai Baba na karasowa wajen ya tsaya
dab da Mom yana kallo kitchen din yana jiyo kukan Asmeey, yan aiki duka suka gaidashi but baima iya
amsawa ba yace “meke faruwa? Meya faru Asma’u ke kuka? Mesa bataje makaranta ba”? Cikin kuka
Asmeey tace “Baba Mommy” dan kallon Mom yayi dake kallonta rai abace saikuma yakalli Asmeey dake
lekowa daga bayan Ammi yace “zonan” ba musu ta taho ahankali tana goge fuskanta da tasan Baba
bazai taba dukanta ba baya dukansu, agabasa ta tsaya kanta akasa yace “mena gayamiki kan zuwa aji
latti da asuba” ahankali tace “kace nadena?” Baba yace “so danazo na tadaku kika tashi kika kalleni ina
wucewa natafi daman bacci kika koma?” Fuskanta tashiga gogewa takasa magana, Baba dake kallonta
yace “kinaso ki gamu da fushina ko”? Girgiza kai tayi tace “Baba bazan karaba kayakuri” shiru yayi yana
kallonta saikuma yace “zoki wuce kitafi” bakinta na rawa tace “Baba Malam zai dokeni” saikuma ta rushe
da kuka Mom tamata wani kallo dayasa tayi kan Baba zata shige jikinshi Baba ya kalli Mom hakan yasa ta
dauke kanta tawuce tashiga kitchen din shikuma yace “wuce muje” ba musu tabishi suka fice tana
murmushi, har ajin nasu yayi sallama Malam ya amsa yana tasowa Baba yace “basai ka tasoba Malam
kaga Asma’u sai kuka take sabida tasan tayi latti amata afuwa adaga mata kafa nayau gobe tayi latti
amata hukunci” murmushi Malam yayi yace “shikenan Alhaji ta shigo” Baba yakalli Asmeey dake
gefenshi data share fuskanta da sauri tanamai murmushi mai bala’in kyau yace “da idanunta awajen
kaman na mutanen da wuce kishiga” murmushi tayi ta shiga tana ballama kannenta harara dake kallonta
barinma su Yusra.
Dan saurayin dake 20yrs yana kama da ita sosai yajuyo yakallota yamata gwalo kirne fuska tayi Malam
yadawo ya zauna kowa ya natsu suka cigaba da karatu.
7:00 daidai na safe aka tasosu duk suka fito dayake almost dukansu yaran suna zuwa school Asmeey ne
kawai da Ramla basa zuwa su sun gama university Ramla NYSC zata yanzu ita kuma Asmeey law school
duk suka wuce cikin gidan, zama all the children sukayi anan babban falo su Gambo da Ammi na bama
kowa breakfast, Asmeey tawuce sama da sauri dakinsu tawuce taje tai wanka tai brush tafito tai shafe
shafen ta sannan ta dauko wani white shirt mai boturi tasaka sannan tadauki black skirt daidai ita tasaka
tadauki black veil tai rolling daya mata kyau ta dauki wani LV bag mai kyau ta hada yan abubuwa da
wasu books da jotter ciki ta feffesa turare sannan tafito daga dakinsu, gidansu is big flat da akwai 2more

flat ciki, flat din dake left and right sai dakin Baban su at the center sai dakinsu na mata agefe na maza
ana dayan gefen babansu, right flat din tawuce da saurinta da dan kunne a hannunta tabude kofan
ahankali ta shiga ciki.
Gambo ce kadai a falon tana goge goge ansaka turaren wuta dakin na kamshi sosai, ahankali tace “ina
kwana Gambo” murmushi tamata tace “Asmeey an shirya” gyadamata kai tayi da saurinta tawuce
bedroom na Mom tai knocking ahankali kusan 1️⃣min akace “come in” bude kofan tayi ahankali ta shiga
ciki, dakin Mom yahadu iya haduwa komi nata is well organized, ga bango guda da duk books ne acikin
shelf, Mom ce zaune kan wani couch mai bala’in kyau taci gayu sosai tasaka wani lace mai kyau hadadde,
ga glass akan idanunta tana aiki dawani iPad dinta, harta karaso wajen kanta na kan iPad bata dagoba,
dukawa tayi agabanta cikin muryanta mai sanyi and very fresh tace “Mom Good morning” dagowa Mom
tayi tabita da kallo daga sama har kasa fuskanta ba walwala, wani irin murmushi mai kyau tama
mamanta tace “Mom bazan kara makara ba sorry karki fushi” dan hararanta Mom tayi cikin muryan
kasaita da iko tace “kinyi breakfast?” Girgiza mata kai tayi tana mikama Mom dan kunnenta tace “Mom
samin” karba Mom tayi tanabin dankunnayen da kallo dasauri Asmeey ta tashi tahau kan kujeran ta
daura kanta ajikin Mom tana shakan kamshin da mamanta keyi mai dadi tawani sauke ijiyan zuciya
kaman irin yaron dayayi shekara baizo jikin mahaifiyarsa ba, tai lamo ajikinta, dan kallonta Mom tayi for
few seconds sannan tasamata dan kunnen, cikin kakkausan murya tace “dagani” dasauri Asmeey ta dago
daga jikinta Mom tasake kallon yarinyar saikuma takai hannunta ta daga black veil nata tana kallon
gaban white shirt nata tace “banace anytime kikasa white shirt haka ki dinga sa singlet ba aciki can’t u
see yanda bra naki ke showing” dan komawa baya kadan tayi da mahaifiyar tata gabanta na faduwa
hankali kaman mai tsoron magana tace “Mom duka sunyi datti ne but yau duk zan wanke” wani kallo
Mom ta mata hakan yasa tasake matsawa daga kusa da ita dasauri, girgiza kai na takaici tayi tace “be
very very careful Husna or you will not like me kikai provoking din kinsanni very well stand up open that
drawer ki dauki sabon singlet” tashi tayi dasauri ta tawuce wajen drawer tajawo sabon singlet taciro
tabude shi daga leda black ne mai kyau sai kawai ta cire rolling na gyalen tabude shirt nata tadan kalli
Mom ganin bata kallonta yasa tacire rigan ta ijiye kan gado zata dauki singlet tasaka authoritatively
Mom tace “zonan Husna” dasauri Asmeey tajuyo takalli Mom dataga ta tsareta da idanu saikuma tadan
kara singlet din gaban kirjinta cikeda kunya ta taho ahankali har gaban Mom, muryanta har rawa yake
tace “g…gani Mom”
Mom irin iyayen nan ne masu lura da yaransu sosai, masu sa ido, ga basu tarbiya, yaranta must do
abinda takeso ne dukansu haka ta rainesu har yarage saura biyu gabanta yanzu da Asma’u da Munir,
wuyanta Mom takai hannu ta taba tace “yaushe eczema yakamaki?” Zaro idanu Asmeey tayi cus ita
bama tasani ba tace “ni Mom an ina”? Wuyanta gabaki daya Mom tashiga dubawa zuwa bayanta
saikuma ta juyo da ita hannunta tasa, tashi daya ta karbi singlet datake kare kirjinta dashi ta ijiye a gefe,
Asmeey tadan sunnar da kanta kasa, ahankali Mom tabi saman kirjinta da kallo tace “stand up” tashi tayi
dasauri agaban Mom, Mom tabi cikinta da kallo sannan da masifa tace “eczema ko’ina a jikinki dame
kike wanka? Ina soap naki?” Murya chan kasa gabanta na faduwa tace “yakare” Mom aharzuke tace
“tun yaushe”? Gaban Asmeey faduwa yake bana wasaba tace “the 3rd day dakika bani” Mom namata
wani kallo tace “mesa baki gayamin ba”? Dasauri tace “Mom ai munada sabulu dayawa a bathroom
dinmu anyone nagani sainai wanka dashi” shiru Mom tayi saikuma chan cikin kakkausan murya tace

“you’re very stupid, wawiyan yarinya kawai mara wayau, shashasha” sauke kanta kasa Asmeey tayi
ahankali hannunta yahau rawa, Mom tace “wani irin stupidity zaisa ki kasa gane cewa you’ve always had
a sensitive skin? Waya cemiki u can use just anything kika gani kiyi wanka dashi eh? Why do I waste my
money ina saimiki separate abubuwan skincare batare da bari kinyi using sabulan da mayukan da
Babanku ke kawo muku ba, If you ever made that kind mistake again saina sabamiki shashasha kawai,
bacemin daga gani ki wuce ki maida kayanki kizo kiyi briefing dina on case file dana baki last lemme see
idan kinyi wannan” gyadama Mom kai tayi asanyaye duk tayi wani iri tawuce ahankali tasaka singlet din
sannan tasaka shirt dinta, bata maida veil dinba tazo wajen tabude jakanta taciro file da Mom tabata jiya
tabude tadago kanta takalli Mom kirjinta na dukan uku uku, Mom tace “bani distinction na case din but I
prefer persuasive brief, inason statements of facts, then give me substantive issues and procedural
issues” gyadama Mom kai tayi hannunta nadan rawa tasake bude jakanta tadauko wani book nata datai
jotting komi, tabude zata karanta, Mom tamata wani kallon uku saura kwata tace “kikaje law school
haka zaki dingayi? Reading from book? how many days nabaki case din nan nace kiyi reviewing?” Murya
chan kasa irin na mara gaskiya tace “7days” Mom tahada fuska tana karkada kafa tace “idan kikamin
shirme awajen nan ranki zaiyi masifan baci Asma’u, drop that book I’m listening” gyadama Mom kai tayi
saita ijiye book din gently and calmly tafara briefing Mom voice nata narawa, tun tana yi Mom na aikinta
harta juyo ta natsu tana kallonta she really tried, saida takai procedural issues ne takakare Mom tamata
wani kallo hakan yasa hawaye yafado daga idanunta tace “sorry Mom” Mom tace “okay wat is
procedural issues?” Anatse tace “ Procedural issues shine irin wat is the appealing party claiming the
lower court did wrong example kaman ruling on evidence, jury instructions, granting of summary
judgment, etc” Mom ta gyadakai cikeda gamsuwa tace “okay if you know this then a case file dana baki
menene Procedural issues na wajen” shiru tasakeyi cus bata karanta yakai wajen ba, Mom na karkada
kafafu tace “7days but bakiyi going through this case file dana baki ba sabida kwana biyu nadan daga
miki kafa! This should be the last time you will try this wlh kika kara ranki zaiyi masifan baci! I want you
to be the best lawyer in this entire Nigeria, I want you to pass bar exam naki, you’re my daughter no
body a Bauchi can mention law ba akira sunana ba Mrs Turaki and kece magajiyata my successor, you
just have to work hard you have no option, you must study Asma’u dole ne ba negotiation am I clear?”
Ahankali Asmeey tace “yes Mom” Mom zata sake magana aka bude kofan tareda sallama Baba ne ya
shigo yana sanye da wata lafiyayyan gizna datasha aiki yabi Asmeey da kallo dake zaune akasa kan
carpet gaban mahaifiyarta idanunta sunyi ja kaman ma tai kuka yace “kinyi breakfast Ma’u?” Girgizama
Baba kai tayi ahankali tace “a’a” agogon hannunshi ya kalla sannan yazo wajen yasa hannu yadagota
yace “wuce kije kiyi kari, je Ammi tabaki abinci Ma’u na” murmushi tayi sosai Baba daban ne kawai he’s
very sweet, caring, and very affectionate, ahankali tace “toh Baba” wucewa kofa tayi yabita da kallo
tafice shikuma yakaraso wajen ya zauna gefen Mom, cikeda nuna rashin jin dadi yace “why are you so
hard on this girl? Jibeta kaman ba Hamda na yar bakutu ba duk ta rame haba! Kin addabeta, finally
tagama makarantan at least let her rest, all this damuwa yanzu na menene ita da ko list nasu bai fito ba”
rufe iPad nata Mom tayi tadauki Hermes bag nata tanasa iPad din ciki tace “Alhaji I don’t know why you
are saying all this now! I’ve always been like this to all yarana and Alhamdulillah kai karan kanka you are
proud of my upbringing, Asma’u is my daughter, no one loves her better than I do” anatse Baba yace “of
course I know that Barrister and ina alfahari da tarbiyan da kika bama yaranmu Aya is a Nurse, Aisha is a
journalist working with BBC, ga Asma’u kice dole saitazama lawyer irinki while Munir na MBBS, my point
is all yaran nan baki samusu pressure dakike sama Ma’u ba, kwata kwata baki la’akari da she’s still a

small gurl, burin dakikasa akanta yasa I don’t even know wat you did dahar Asma’u tayi WAEC at 14yrs
tafara university at 1️⃣5yrs she’s 2️⃣1️⃣ yanzu wai harta gama LLB, please go easy on her, stop pressuring her,
karatu is a gradual process all this things dakike forcing nata takoya yanzu she will learn it gradually a
law school, karatun dakike sata da menene menene sukesa idan tayi bacci da kyar take tashi da asuba,
batada lokacin kanta, bata da lokacin kula da kanta kowace yarinya a gidan nan da kitso akanta banda
Asma’u sabida rashin time, please and please I don’t want this! Kibimin y’a ahankali, boko ba dole bane,
ba dole Asma’u saita gajeki ba we have other kids agidan ai, allow this girl to be herself please” Baba
yafada calmly yana kallon Mom, Mom takalleshi sai kawai ta dauke kai tace “naji” tamike zata tashi yasa
hannu yarikota tadawo takalleshi tace “menene kuma”? Murmushi yamata yace “yau ina side naki baki
tambayeni mexanci ba” dan lumshe idanu tayi tabude tace “mezakaci Baban Aya”? Murmushi yayi yasa
hannu a aljihu yaciro bandir na yan 1️⃣k guda uku yabata yace “make anything, gashi this is for you” takalli
kudin he’s mutum da baya kallon kudin matansa he always gives them money, murmushi tayi tace
“thank you” manna mata kiss yayi a goshi yace “natafi, kibimin yarinya ahankali a kotu” ahankali tace “to
adawo lafiya me y’a.” Dan dariya Baba yayi yafice daga dakin.
[03/01, 07:38] +234 806 292 7511: 💫UWA KO UKUBA?💫

✍💫M SHAKUR

https://chat.whatsapp.com/HOfjHAh3gw5502DZ5uJTWn

EPISODE 5💫
Abba yace “Abdallah saikai” tashi yayi yadauki 5yard yace “Allah amfana Abba Allah kara budi” Abba
yace “Faisal” tasowa Faisal yayi yadauki 5yrd shima yace “Abba Allah saka da allhairi” Abba yace “Hassan
sai kai” tashi yayi ahankali yadauki 5yard” Abba yace “zabi another one ku baku da iyali so kala bibbiyu
zan muku” murmushi Hameed yayi yakara another color daya yace “nagode Abba” Abba yajuya yakalli
Hamad dake zaune kusada Ya Mustapa yace “saikai Hussaini” tashi yayi ahankali yadaura hannunshi
yadauki the first two shadda dake in line Mamie tace “iri dayane duka change color” cikin calm voice
nashi yace “Mami zaban mini” Hameed yace “toh yaron Mamie” Abba yace “ina ruwanka” hararansa

Mamie tayi tasa hannu ta zaba masa irin na Hameed ya karba kanshi akasa yace “Jazakallah Abba”
murmushi kawai Abba yayi yace “to cire mata naku Hajjaju ina Gwaggo”? Mamie tace “taje makota anyi
haihuwa wai an mata takwara” Abba yadanyi murmushi kawai tadauki atampa daya lace daya tace
“gana Ramla” tasake ciro wasu biyu tace “gana Asma’u” “Yusra da Amina” Abba yace “to kwasan ma
mazan ma Shadan su su Munir” haka Mamie tacirema duk wani yara na danginsu kayan salla sai mai
aikinsu Lami da yaranta Faisal yahada kayan a babban gana masgo yafita yakai mota yadawo Abba
yakalli Mustapa yace “yau salla saura sati biyu ko” Abdalla yace “saura 1️⃣3days Abba” Abba yace “okay
ina ganin ana gobe salla zamu wuce Bauchin akwai abinda zanyi” yakalli Abdallah yace “next week sai
akai duka motoci ayi musu service ko” Abdallah yace “toh Abba” Abba yace “Masha Allah” yataba
aljihunshi yaciro 50k guda biyu yabama Hameed daya yace “gashi kudin dinki da kudin takalmin salla”
dasauri Mustapha yace “Abba don’t worry about that zan basu please dawainiyan yayi yawa” dasauri
Hameed ya karbi nashi 50k yace “Ya Mustapha kudi baya yawa” Abba ya girgiza kai yakalli Hamad yace
“Hamad zo ga naka” kin motsi yayi tausayin Abba yakeji sosai baida arziki kaman da kuma sai kashe kudi
yake anatse yace “Abba kabarshi inada takalmin salla” atare dukansu sukace wanne?” Dan kallon Abba
yayi kadan yace “Ya Mustapa bought sabon takalmi last week for me dashi zanyi amfani” Abba yace
“dudda haka amsa wannan nina baku nace kusaya take it” kasa tashi yayi yadan kalli Ya Mustapa
dayamai alamu da idanu ya amsa hakan yasa yatashi yasa hannu biyu ya amshi kudin ahankali yace
“nagode Abba” Abdallah yace “zansa mai dinki na yazo ya amshi kayan ya aunaku I will pay for the 2 of
you” Mamie tawuce aka kawo breakfast kunu ne lafiyayye da kosai Abba kuma aka dumamai tuwo cus
he can’t do without tuwo, ko half cup na kunnun bai iya sha ba yawuce yatafi sama kowa ya kalleshi but
aka barshi gamaci Ya Mustapa yayi yawuce sama Hamad na zauna kan gadonshi yana taba laptop dinshi
Ya Mustapa yashigo gently ya ijiye laptop din, Ya Mustapa yakarasa wajen yace “too much sitting is not
good for you allow system dinka to rest okay, da lafiya ake komi”zama yayi yaduba ciwon is looking very
good magani kawai yabashi da allura sannan ahankali yace “do you need anything?” Girgizamai kai yayi
Ya Mustapha yace “zamuyi tafiya next week going to family house for salla you know how you get so tell
me idan kana bukatan anything for traveling din” ahankali yace “bakomi” gyadamai kai yayi yace “okay
zanje hospital yanzu anjima i will call you sai muje tare na siya maka desktop dinka tunda na da ya
lalace” Dasauri ya kalli Ya Mustapha hancins a Mustapha yaja yace “dudda you will never say it out loud I
know how much all this su system and desktop dinka daya lalace means to you, my tech little bro so we
will get it today anyone kakeso” baki yabude zaiyi magana Ya Mustapha ya harareshi yace “yimin shiru
just complete project din daka fara and send it to Microsoft muga abinda Allah zaiyi, in sha Allah you will
win, I also speak to wani friend dina za’a nema maka aiki idan an samu any slot, idan kuma babu I think I
will just enroll you

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login