Showing 3001 words to 6000 words out of 59470 words

Chapter 2 - UWA KO UKUBA MShakur HAUSA NOVEL

M SHAKUR   

28 Mar 2025

3093

carpet dinsu tana kallon Hamad still tace “kaman kasani yau nahayo benen nan yafi
akirga sabida wannan yaron dabaison mutanen, kai Hameed duk matar da Husainin nan naka zai aura
zatasha fama” mikewa Hamad yayi, hakan yasa Hameed yakalleshi yadanyi dariya yace “common seat”
ko kallonsu baiyiba yawuce wajen kofa Gwaggo tace “tohh ni wanan yaro dabaku yan biyu bane da
sainace ba Abubakar bane ya haifesa ba yoo wannan wani irin hali ne yaro sai miskilanci ga kin jama’a,
ga, ga, ga eh dan ubansa ya dauka nazo ganin fuskan nan nasa mai kama dana mata ne?” Dan murmushi
Hameed yayi Gwaggo tace “atoh da lafiyansa kalau ai babu abinda zanzoyi inda yake dan ba kaunata
yake ba, Hamad ya tsaneni narasa menamai uwarsa kawai yaron nan yakeso, dazaran nazo waje zai tashi
yabar wajen, ya tsaneni ina dalili saisa da Babanku zai dawo dani nan naki biyoshi sabida nasan Hamadi
baya sona Uwarsa Batula kawai yakeso duk tabi ta hure masa kunne” ta rushe da kuka, ahankali Hameed
yace “Gwaggo mehaka kidena kuka, mesa zakice Hamadi baya sonki ke kadai yakema haka eh? Mu yan
uwansa kulamu yake? Ni yanzu kinga ya kulani? Eh”? Dankwali Gwaggo ta kwanto daga kanta ta

warware tana goge fuskanta ga gashin kanta dayama kare sunyi fari kal tace “nagani kam” Hameed yace
“to kingani akan mene zaki dinga kuka, haka Allah yayo Hamad kitamai addu’a, amman bai tsani kowa ba
kinji Gwaggo kinga baida lafiya, kina kukan nan kara tadamai da hankali kike dena toh” rushewa tasakeyi
da kuka sosai tace “yooo ai yanason Uwarsa Fatimatu Batul, nida na tayata rainanku ana haihoka na
karbeka na rike, saida tasake nakuda nakusan awa guda cur sannan ta haihosa shima na amshesa, baka
gansa ba lokacin gabaki dayansa yayi kalan ruwan kwai wai jondus (jaundice) aka haifesa da ita, ga
uwarsa ba lafiya haka nina dinga lura daku har taji sauki, kai kasha madara amman akai juyin duniya shi
yasha yaki hakafa uwarku na cuta da bamata hayyacinta aka kamasa aka daurasa kan mama yasha,
halama saisa yake cuta kullum sabida ya zuge na jikin uwarku alokacin, saida aka cire mata mahaifa
gabaki daya kuma shine yakusan kasheta dan yaki fitowa daga ciki, kuma shine tundaga asibiti har yau
yake damunta da cuta daban daban ai ban manta dakomi ba, nida nai wahalar sa wai nine yanzu zai taso
ya tsana bayaso” dariya kawai Hameed kerike wa yace “toh kiyakuri Gwaggo” Mamie tadade tsaye
gaban dakin sannan tabude kofa tashigo Gwaggo ta watsamata harara Mamie ta kalli Hameed tace “ina
yake?” “He left the room Mamie” Mamie tadan kalli Gwaggo tace “Gwaggo kiyakuri tashi muje” kaman
jira Gwaggo take tace “ohh Allah kana gwadamin ni kike cema nazo nafita daga dakin jikokina eh Batola
kin rabani da Hamadi yanzu da Hassan zaki rabani shima” dan lumshe idanu Mamie tayi tabude tace
“bahaka bane Gwaggo kiyakuri daman na dauka zaki sauka kasa ne bari naje” ihu Gwaggo tahau yi tace
“eh kitafi wlh duk abinda akemin agidan nan zan sanar da Abubakar duk anbi an rabani da jikokina”
ijiyan zuciya Mamie ta sauke tawuce tafita direct dakinta tawuce tabude tashiga Hamad na kwance kan
gadonta jin an bude kofa ya kallo kofan daure fuska Mamie tayi tareda folding hands a kirji tace “wat are
you doing here? Ba cewa nayi zan kawo muku abinci kaida Hameed ba”? Dan sauke kanshi kasa yayi
yace “I’m not hungry” karasowa dakin Mamie tayi zuwa gaban gado tadan sassauta murya tace “mesa
kabar dakin sabida Gwaggo? Cinyeka zatayi? Why do you always make her cry eh Hamadi? Can’t you see
how she deeply loves you eh? She was worried sick sabida kai, the least you could do is kadan zauna ko
bazaka kulata ba seeing you makes her happy, Hamadi why are you like this eh? When will you stop
giving me headache? Yaushe zaka chanza halin nan eh? We are your family idan kayi haka awaje it’s
okay but us fa, banda mu wa kake da shi? Mesa kake gudun Gwaggo not just she kowa ma why why why
Hamad? Kullum ina daga kafa ina cewa ka girma zaka dena idan yanzu your 33 baka chanza ba sai kakai
50yrs zaka chanza eh?” Kanshi na kasa yana sauraron Mamie murya ciki ciki asanyaye yace “sorry
Mamie” cikin fushi tace “I don’t want your sorry katashi kaje kuci abinci and tell her sorry” gyadamata
kai yayi yatashi zaune ahankali sannan ya sauka daga gadon gently sabida ciwo yawuce ta gefen Mamie
yafice tabishi da kallo tai shiru tana nazarin sa, Hameed na zaune yafaracin wainan Gwaggo namai zuba
Hamad yabude kofan da sallama chan kasa ya shigo daga Gwaggo har Hameed suka bishi da kallo, Ya
tsaya awajen yakasa tahowa ciki Hameed yadauke kai yacigaba da cin abinci abunsa Gwaggo tace “taho
zokaci abincin ka kona maka fura zaka sha?” Girgiza mata kai yayi yana tsaye bai kalleta ba, wani washe
baki Gwaggo tayi tace “yauwa toh dan Albarka zoka zauna kaci ko guda daya ne kaji” ahankali ya shiga
tahowa Gwaggo ta matsamai da sauri gently yazo ahankali yashiga zama yadan kama gefen cikinsa
Hameed yabishi da kallo Gwaggo tace “Wajen aikin ka kema ciwo?” Girgiza mata kai yayi yajuyo yasa
hannu yadauki spoon ya gutsiri masan kadan yasa a miya yakai baki dan yatsine fuska kadan yayi
Hameed yace “is it too spicy for you?” Girgizamai kai yayi yana taunawa kaman wanda akasa dole yaci,
Gwaggo dake kallonshi batako kyafta idanu tace “miyan yayi yaji ne”? Girgiza mata kai yayi daidai ana
bude kofan wani magidanci dake kama da Ya Mustapha yashigo rikeda yaro a hannunsa yana kallon

Hamadi yace “Hamad ya jikin?” Dan kallonshi yayi daidai yaron yasauka daga jikin Babanshi yataho
wajen Hamadi da gudu daukanshi Hamad yayi for the first time yasaki murmushi sosai dimples dinshi
suka fito da white fararen hakoransa yaron ma ya k
washe baki, Gwaggo tace “Areef narasa meya gani a jikin Hamadi dayake sonshi haka” karasowa cikin
dakin Ya Abdallah yayi yace “ai ba Areef ba harsu Akram da Abdool dukansu haka sukeson Hamad, Areef
oya come Uncle Hamadi is sick today” makema Babansa kafada yaron yayi, Hameed ya ballama Areef
harara aiko ya tsala ihu yana shiga jikin Hamad garin haka ya takemai ciwo wani kalan runtse idanu da
karfin gaske Hamad yayi dayasa Hameed da sauri yadaga Areef yana karbansa, Abdallah yace
“Subhanallahi Hamadi, sannu, Hamadi” Gwaggo tace “shikenan Areef yatakemai wajen aiki duba kagani
ko wajen na jini Abdullahi” jin haka asauri Hamadi ya daura hannunshi awajen murya chan kasa dake fita
da kyar yace “I’m fine” bottle water Abdallah yadauka yabashi amsa yayi yakai bakinshi yasha kadan duk
sukai shiru suna kallonshi barinma Gwaggo, akufule da karaman murya yace “kudena kallona”
“mundena” Gwaggo tace amsa da sauri, Hameed yatashi yana sauke Areef yawuce bayi, yace “it’s time
for magrib” Gwaggo tace “Abdullahi kaga nima kamani ka kaini kasa” kamata yayi suka fice, Hameed
daya fito yajira Hamad shima yadauro alwala suka fito suka wuce masallaci.
Suna magrib suka dawo gida da sallama suka shigo falon, Abba suka gani zaune a falo dayake kokarin cin
tuwonsa na dare, duk yayyinsu na falon, Hameed yawuce dinning yazauna tareda Faisal suna danna
waya, sai Ya Mustapa zaune wajen Abba tareda Abdallah sai Mamie dake zaune a gefensu, karasowa ciki
yayi dukansu suka kalleshi harda Abba daya dakatar da abincin dayake ci ya tsareshi da idanu irin kallon
da uba kema dansa na nazarin yanayinsa din nan da kula, sauke kansa kasa Hamad yayi yakaraso har
wajen yadan duka cikin muryanshi mai cikeda natsuwa yace “sannu da zuwa Abba” anatse Abba na
lurada shi yace “jikin yahanaka zama karatun dakukeyi a masallaci bayan magrib ne?” Gently ya
gyadama Abba kai batare dayayi magana ba, Abba yadan jinjina kai yace “Maman Doctor yaci abinci
kuwa?” Anatse Mamie tace “kowa yaci abinci banda shi” kallonshi Abba yayi babu wasa kan fuskanshi
yace “zonan kaci abinci, Doctor bani maganin dazaisha na dare” ba musu yataho yazauna gaban Abba
kanshi akasa Faisal da Hameed suka kalleshi, Hamad yadan dago kanshi yakalli Ya Mustapa daya kawo
maganinshi Ya Mustapa yamai wani kallo yace “eat my friend” maida kanshi kasa yayi Abba yabashi
spoon dayakecin tuwon dashi ya karba ahankali shi Abba yasa hannu yace “oya bismillah ci zakasha
magani” ahankali yafara ci Mamie na kallonshi yaci kusan 5spoons ya ijiye spoon din ahankali, Abba yace
“ka koshi?” Gyadamai kai yayi Abba ya wanke nashi hannun tsaf yadauki ruwa yasha ya ijiye cup hakan
yasa ahankali Hamad ya mika hannu zai dauki plates din da Abba yagama cin abinci dasu yakai kitchen
Abba yace “barshi bakada lafiya” sai kawai Abdallah yatashi ya dauka dan yaran sunada tarbiya da kyau,
yana dauka Hameed yazo da sauri ya karba yawuce kitchen, Abba ya tsare Hamad din da idanu da kansa
ke kasa anatse yace “meke maka ciwo yanzu eh Hussain?” Kanshi na sunne akasa yace “bakomi Abba
naji sauki” Abba yakalli Ya Mustapa bawasa kan muryansa yace “meke damunsa likita ance kaduba sa
dazu? Tell me menene matsalan?” Ahankali Ya Mustapa yace “Abba he got infection, rashes sun fito
wajen stitches dinsa, I think maybe from ruwan wanka or sabulu or it could be anything, nayi dressing
wajen dazu I will still do it yanzu sai yasha maganin” Abba ya maida dubanshi ga Hamad da kansa ke kasa,
cikin murya mai tsauri yace “bakaga kuraje a wajen ba da bazaka fada ba eh Hamadi? Bazaka iya kiran
Yayanka ka gayamai ba ko Mamie ko ni? Kana kallon ciwo jikinka kaki magana kai yaro ne wai? Inda

wajen ya rube fa? Halaka kanka kakeso kayi? Bazaka dena abubuwan nan ba ko mutuwa kakeso kayi
kahuta mesa kake haka ne”? Murya chan kasa kanshi akasa yace “kayakuri Abba” dan ijiyan zuciya Abba
ya sauke yace “tashi muje Doctor yamaka dressing din aka gama saikasha maganin, tashi” ahankali
yatashi ba musu bai kalli kowa na dakin ba yawuce stairs Mustapa yawuce yadauki jakar dake kan kujera
daya ijiye yawuce sama Abba yabisu bayan ya dauki ledan magungunan.
Yana shiga dakinsu kwanciya yayi akan gadonshi ahankali daidai Doctor na shigowa dakin yazo wajen
gadon yana kallonshi yace “how are you?” Ahankali yace “Yaya key the door pls” wani kallo Dr yamai
sannan yabude jakan yashiga ciro hand gloves nashi daidai Abba na shigowa dakin da sallama.
“Assalamu Alaykum” Hamad ya sauke kanshi kasa kaman yayi disappearing yakeji, ahankali Abba yazo
wajen gadon ya tsaya yana kallon Hamad din dayaki kallonsa yayi folding hannuwansa a kirji, Mustapa
na hada komi sannan yazo gadon yakai hannunshi zai dage riganshi Hamad yadan rikemai hannu sabida
Abba, Abba dake kallonsu yace “wai mehaka Hamad” sakin hannun Ya Mustapa yayi ya runtse idanu
kawai, Dr yadan dage t-shirt nashi sama zaija wandonsa kasa kadan Hamad yarike hannunshi yadan kalli
Abba daya haderai yace “sakenmai hannu yayi aikinshi kadade bakaji kunya ba shirmen banza da wofi,
kunyan ai shi yasaka a wannan condition, da tunda kaga abin kabi Yayan naka asibiti yabaka magana da
tuni anyi an wuce wajen, cikamai hannu nace” sakin hannunshi yayi ahankali, Ya Mustapa yaja
wandonshi kasa maranshi yafito har zuwa wajen walls nashi ga hair kadan akwance ana gani ya runtse
idanunshi sosai kunya kaman zaiyi ihu, Abba dayaga ciwon cikin bacin rai yace “look at wat he did to
kanshi bakasan kunya na halaka mutum ba, kuraje na fitowa haka ajikinka ka kasa fadama kowa alhalin
kanada Yaya likita, ga sauran yan uwanka, ga mahaifiyar ka, gani duka, wannan wani irin abune
wandonka za’a cire gabaki daya dakake irin halin nan kaniyanka da abinda kake boyewa” daidai Ya
Mustapa yafara goge ciwo mugun ijiyan zuciya ya sauke dayasa Abba yayi shiru da fadan dayakeyi ganin
abin namai ciwo sosai yadena fadan yahakura, Doctor ahankali yace “sorry” daidai lokacin aka bude
dakin duk yanda yakejin zafi saida yakai hannu yaja wandonshi zai rufe Abba yace “wai mehaka Hussaini
eh”? Abdallah ne yashigo dakin sai Faisal biyedashi tareda Hameed suka maida kofan suka rufe, cikeda
masifa Abba yace “cigaba da aikinka kaji sun ganshi din ba yan uwansa bane” da kyar cikin karfin hali
yace “sufita! I want my privacy” dan murmushi Ya Mustapa yayi kana ganin Hamadi haka kaman ka
samai y’ata baisan yanda ake taunawa ba silent rigimamme ne wlh, Abba da ranshi yagama baci yaci
“kaci me garinku da privacy, babu inda zasu hukuncin ka kenan, next time wani abu yakara samunka kaki
fadi haka duk zamu taru akanka idan kuma bakason haka kabi yayanka asibiti kuyi abunku ku biyu” sai
kawai Abba ya zauna abakin gadon yana karbe hannunshi daga wandon yarike yace “bude ka cigaba
Mustapa” ahankali Ya Mustapa yaja wandonshi da boxer nashi kasa but this time sai baija kasa sosai ba
ganin yanada kunya and yan uwan shi are there, dudda Abba ya lura da abinda Mustapa yayi sai baice
komiba hasalima hakan yamai dadi tunda haka Allah yayo Hamad da shegen kunya, cigaba Mustapa yayi
kowa tsaye daga yanda Hamad keyi da kafa kasan da zafi Hameed yayi wani iri da fuska idanunshi sukai
jaaa, yana kan gyara stitches din sai kawai ga hawaye sun fito daga idanunshi na azaba dasauri Hameed
yajuya yafita daga dakin idanunshi sunyi ja, hannu Abba yasa yakai yasharemai fuskanshi, saikuma ya
sassauta murya cikeda so yace “ya isa kadaure Mustapa ka kusa gamawa ko”? Gyadama Abba kai yayi
yana karasa dressing din su Abdallah na kallo, Faisal ma yakasa daurewa yajuya kawai yafice, Abba
yakara sharemai hawaye sannan aka gama idanunshi sunyi jaaa, Mustapa yamai allura aka bashi magani
yasha Abba na zaune dashi ahaka yace “sannu kadena rufe wajen da wando dan Allah Hamad ciwon ya

warke, dagakai sai yan uwanka agidan nan kumama duk aiki suke zuwa kai kadai ke wuni so kafinga bari
yanashan iska” gyadama Abba kai yayi Abdallah yace “sannu Hamadi” gyadamai kai yayi duk suna tareda
shi ahaka bacci yayi awon gaba da shi sabida alluran Abba yace “yatashi yayi isha’i” Mustapha yace
“kada kadamu Abba nan da 3 days ya warke” gyadamai kai Abba yayi yace “kuwuce kuma kutafi gida”
bargo Ya Mustapa yasa ya rufamai sannan suka kashe wuta suka fice.
[03/01, 07:38] +234 806 292 7511: 💫UWA KO UKUBA? 💫

✍💫M SHAKUR

https://chat.whatsapp.com/HOfjHAh3gw5502DZ5uJTWn

EPISODE 4️⃣💫
Knocking Asmeey tayi tareda sallama, murya ciki ciki Mom tace “shigo” kofan tabude tashigo ciki anatse
Mom tace “dau gyle kihada jakanki kije kisa takalmi gani nan zuwa” gyadama Mom kai tayi tawuce
tadauki gyalen tazo tahada komi na jakanta tadauka tafice, dakinsu tawuce taga Ramla harta hau gado
abinta tana bacci sai kawai tadan turo baki kadan, kaman tai bacci itama haka takeji amman ba hali,
wani black Zara cover shoe tadauka tasaka tai rolling gyalen da kyau sannan tai backing bagpack dinta
abaya, she looks very smart and elegant kaman wata yar secondary school dan bata da wani tsayin kirki
55/56 ne length nata har a abaya ma, tadauki wayanta kiran iPhone 11 normal tafito, duk kudin Baba
kwata kwata bai bata yaransa ba cus shi bai taso cikin kudi ba, dayan flat na left tawuce tabude shima
dakin na kamshi an kunna turaren wuta bakowa a falo hakan yasa tawuce bedroom din tai knocking tace
“Ammi” bude kofan da sauri Ammi tayi cikeda fara’a tace “za’a tafi kotun ne our fresh Lawyer”
murmushi tayi dake kawatar da fuskanta sosai tace “eh natafi” gyalenta datai rolling Ammi takai hannu
ta shiga gyara mata shi da kyau tace “toh adawo lpy Allah bada sa’a, ki kiyaye kada ki batama Mamanki
rai koda wasa kinji Husna” gyadama Ammi kai tayi tareda dan murmushi tajuya tafice Ammi tabita da
kallo tai murmushi.
Sauka kasa tayi tafice waje, Mom tagani na kokarin bude wani black jeep mai kyau da sauri tayi wajen
motan Mom ta kalleta tadauke kai tashiga ciki abinta ta zauna, baya tabude ta ijiye jakanta sannan
tadawo gaba tazauna tasaka seat belt dan baka shiga motan Mom bakasa seat belt ba, Mom taja motan
daidai ana kiranta tashiga magana da client nata itakuma tajuya tana danna wayanta da babu anything
fun aciki, Mom tahanata tiktok, instagram, the only application takeda shi is watsapp shima sabida

family da irin class group na school, Mom is very strict she watch them closely, tiktok saidai ta kalla
awayan Ramla kuwa, wayan ma akwai hours datake amfani dashi, for example yanzu suna kaiwa kotu
that is the end of taba waya sai kuma idan an koma gida zata taba kadan su yi aiki Mom can call her
anytime for a case hakadai so in a way bata taba waya for good 3hours wlh saidai tsakar dare, tana cikin
daddana wayan Mom tace “drop that phone and pick the case file dana baki” ahankali tace “to” jakanta
tajawo dake baya ta saka wayan tadauki case file din tashiga dubawa har sukakai court Mom tai parking
takashe motan suka fito ta goya jakanta tana rike da case file din, Mom tafito tasaka gown nata duk
Asmeey na kallonta, Mom is so elegant and charismatic and very intelligent, she really wants to make
Mom happy and be like her but tana ganin kaman bazata iyaba even though she’s trying but she is not
as brilliant as Mom, she’s not as smart as Mom, gama saka gown din Mom tayi tajuyo ta kalleta ba
rahama tace “me kika tasani a gaba kina kallo” dan murmushi tayi gabanta na faduwa ahankali jikinta da
dan sanyi tace “wlh Mom ina sonki” dan kallonta Mom tayi sai kawai takara tamke fuska tace “I don’t
want your dumb love, make me proud that’s how you show Mahaifiyarka kana sonta, that’s all I require
from you, not your nonsense love words wawiya kawai” sauke kanta kasa tayi ahankali ga few people
here and there na wucewa, Mom tadauki handbag nata tarike tace “kwaso files a back seat” bude bayan
mota tayi ta kwaso files dayawa tarike Mom tarufe motan tana rike da hadadden jakanta na Hermes
suka shiga cikin court din, nan da nan client nata suka taso former controller general ne yace “barka da
zuwa Mrs Saraki” gyadamai kai Mom tayi majestically tana murmushi yadan kalli Asmeey dake biyeda
Mom hakan yasa ahankali Asmeey tace “good morning Sir” murmushi yayi yace “wowww wat a voice,
wannan Mrs Saraki junior ce Masha Allah, you are so lucky to have this woman as your mother young
lady, mahaifiyarki itace real definition na beauty and brains” itadai Asmeey na kallonshi bataso tai
magana Mom tai fushi, Mom tai magana dashi kafin su shiga court room aka fara case Mom tafito
Asmeey tadauki pen da jotter tana kallon mahaifiyarta. Mom is just great, Mommy is just who she thinks
she’s like the woman dominate the courtroom, Mom tafara magana u must listen dole ne kawai, anya
zata taba iya zama kaman Mom kuwa? Mom wants her ta gajeta she’s scared cus tasan bazata iyaba.
Almost 1hour akai a kotun bayan kowani party ya bada evidence alkali yayi ruling client na Mom as not
guilty yasa other party su biyashi sum na 500000 charges sai murmushi Mom keyi, Asmeey sai kallon
Mom take cus hardly Mom ke kallan murmushin nan da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login