Showing 24001 words to 27000 words out of 59470 words
Husna
saita gajeki ba! Ni dan kasuwa ne mesa bance Munir dole sai yazama dan kasuwa kaman ni ba? Kibar
yara suyu abinda sukeso, the next time zaki takurama yar nan wlh saina dauki mummunan matankin da
saiya baki mamaki! Imagine yau baki zanyi mahaifiyata da yan uwana suna hanya keçe babba agidan nan
amman bata ayyuka da abincin da zasuci kike ba, I will not say anything ku cigaba da halinki gida biyu
maganin gobara kada ki komi ko yaya kikeso kiyi amman yarana kidena takura musu na gaya miki”Mom
na kallonshi tace “shine kakemin ihu”? “Wacece ke da baza’amiki ihu ba” yana maganan yawuce ya
shiga bedroom dinshi ya barta nan tsaye.
[03/01, 07:38] +234 806 292 7511: 💫UWA KO UKUBA?💫
✍💫M SHAKUR
https://chat.whatsapp.com/HOfjHAh3gw5502DZ5uJTWn💫💫💫💫
[03/01, 07:38] +234 806 292 7511: 💫UWA KO UKUBA?💫
✍💫M SHAKUR
https://chat.whatsapp.com/HOfjHAh3gw5502DZ5uJTWn
EPISODE 9💫
Dakinsu ta shiga bayi tashiga tai wanka dan batai wanka ba tun safe fitowa tayi tabude sip taciro wani
gown na atampa mai kyau yanada blue floweres shiryawa tsaf tayi tasaka sannan tazo gaban madubi
takalli fuskanta har lokacin fuskan yayi ja sai kawai taji har kunya kunya takeji ma tafita mai ta dauka ta
shafa a fuskanta sannan tazo dauki kwalli tasaka duk dan tai looking normal hakan saiya rage redness na
fuskanta amman saitayi bala’in kyau gashinta ta warware a wanke yake har tsakiyan bayanta gashi baki
gwanin kyau batada full gashi sai tsayi but is scanty and silky combing tayi sai kawai ta dauki blue veil ta
yafa tadan fesa bodyspray dinta ta tashi ta kalli madubi murmushi tayi saita fito ta sauko kasa babu
kowa a falo saita fita tana tafiya ahankali zuwa wajen masu kitso Ramla dahar an gama mata kitso tace
“wat happen to fuskanki?” Zama tayi kan tabarma tace “faduwa nayi laaaa lallinki yayi kyau Ya Ramla”
tai maganan da sauri dan ta kauda maganan, takalli lallin Yusra tace “Yusri iyyeee Irin naki za’a min”
Yusri ta washe baki Amina tace “Ya Asmeey kiyi irin kitsona” dasauri tace “shiko zanyi” Yusra tace “ga
Mom tafito” wani kalan faduwa gaban Asmeey yayi da sauri ta sauke kanta kasa Mom tashiga tahowa
wajen fuskanta kaman bata taba dariya aduniya ba tana sanye dawani simple gown na Cotten irin na
Egypt din nan masu manyan mayafi sai wani mashahiurin kamshi take idanunta akan Asmeey dataga tai
wanka harda chanza kaya, Yusra na ganinta tayi murmushi tace “Mom saura ni ana gamama Amina
za’amin kitsona asamin beads” Amina tace “Mommy lalle na yayi kyau” dan murmushi kadan tayi tace
“yayi sosai” takalli Asmeey da kanta ke kada cikeda authority da isa da iko tace “ayi miki kitso only banda
lalle” ba Asmeey kadai ba hatta su Yusra yara da su masu lallen da masu kitson da Ramla saida suka kalli
Mom, wani iri Asmeey taji cus tanason lalle duk salla Allah yasani lalli da kitso da saka sabon kaya are the
measure things she looks forward too, amman saita gyadama Mom kai ahankali muryanta nadan
breaking tace “tt….toh Mom” strictly Mom tace “good! You’re going to law school bayan sallan nan,
henna kowani iri is not allowed” sake gyadama Mom kai tayi ahankali kanta akasa, Mom tajuya tawuce
abinta batare data kara kallonsu ba tana tafiya kaman itace mai gidan masu lalle da kitso suka bita da
kallo asace ana mamakin gadaran matan, duk yanda Asmeey taso ta daure takasa kawai saiga hawaye
sharrr dasauri takai bayan hannu ta share kafin wani ya lura dan kanta na kasa, me lallen tace “menene
law school Ramla?” Ahankali Ramla tace “makarantan dakake zuwa kazama cikakken lawyer, da gaske
ba’a barin lalle” mai lallen tace “amman ai yanzu lalle nan da nan yake gogewa kuma shampo na goge
lalle lokacin yayi aisaita goge lallen” Ramla tace “tunda Mom tace kartayi kartayi mubar maganan nidai”
Asmeey tai shiru zuciyanta baya mata dadi kawai kitson ma kaman kartayi but tasan Baba zaiyi magana,
haka aka gama na Yusra sai akahau mata kitso shiku mai bala’in kyau yan kanana ana cikin mata Kawu ya
iso daga Gombe.
Tashi duka yaran sukayi bata tashi ba Ramla tace “tashi muje mu gaida su Kawu” ahankali ta tashi suka
wuce wajen motansu, wani magidanci na mai kama da Abba na Kano sosai tareda wata mata da yara
mata, Matar tace “ana kitso ne Asmeey ba’a gama ba” dasauri Asmeey tace “eh Mama” ta rungume
“Nana da Baby tace “Nana, Babyyyy” suma suka rungumeta Nana is 1️⃣5, Baby kuma 1️⃣2️⃣ sai sauran yaran
Maza ne guda hudu, daidai nan Kawu ya gama magana da masu gadi yazo wajen yaran duka suka
gaidasa idanunsa nakan Asmeey yace “meya sameki a fuska Asma’u”kafin tai magana Yusra tace
“faduwa tayi Kawu” ahankali yace “sannu bakiji wani ciwon bako” gyadamai kai tayi tayi murmushi still
ya tsareta da idanu dan kaman mari daidai Baba na fitowa daga flat, Mom da Ammi kuma suna zuwa
daga backyard, wani kallo Mom tama Asmeey hakan yasa tajuya ahankali tawuce takoma wajen kitso,
Baba yayi hugging dan uwansa cikeda farin ciki suka shiga gaisawa while masu gadi na kai kayansu side
nasu, Asmeey takoma wajen kitso tazauna aka cigaba tana kallon yanda kowa ke murna, su Nana suka
taho wajen basuyi lalle ba suma Ramla tace “kuje kuhuta ku chanza kaya kar lallen yabata wannan sai
kuzo amuku” wucewa sukayi dan chanza kayan.
Suna chanza kaya suka dawo, suna cikin kitson Munir yazo wajen kaman bacci ma yayi dan idanunsa yayi
ja bakaramin dadi yaji dayaga Asmeey ana mata kitso ba dudda yana ganin fuskanta yasan aikin Mom ne
yazo wajen yadan harari Nana dake kallonshi yace “ni tsaran wasankine kike kallona” kallon Ramla
Asmeey tayi Ramla ma takalli Asmeey suka wani kwashe da dariya bakaramin dadi yaji dayaga Asmeey
tayi dariya ba, Ramla tace “sannu Ya Munir itakuma Nana jibi yanda tawani sunnar dakai kaman irin Ya
Mustapa asalin Babban yayanmu namata magana” hararan Ya Ramla yayi yasake tamke fuska sosai shi
adole babba sannan yakalli Asmeey yace “Mom is calling you” yajuya abinsa, faduwa gaban Asmeey yayi
sosai ta tashi da rabin gashi akitse tawuce Nana tadan saci kallon Munir da tun tana yar karama take
sonshi Ramla tace “dalla kidena tsoronshi” murmushi tayi tace “cikamin ido yake Ya Ramla” baki Ramla
tabude tace “Munir din ahhh babban magana” shigowa falon sukayi ga Baba da Kawu akan carpet
sunashan shayi dake kamshi sosai Baba dake kallon Asmeey tun shigowanta yace “ina zaki da gashi haka
ba kallabi” da sauri ta taba kan tace “Mom ke kirana yanzu na manta da kallabin wajen kitso ne”
gyadamata kai Baba ta wuce sama afalon Mom taga Mama, Mom na shiri da Mama sosai da Kawu but
Mamie kano ne dai basu cika shiri ba dakuma Abba suma bawai fada suke ba kawai dai haka suke sunfi
shiri da Ammi su, Mama dakecin samosa tace “Hajiya Salima I trust you dan Allah Asmeey ma ki sama
mata gangariyan miji gaskiya dan matar manya ce yarinyar nan ga kyau ga diri dudda naga sai karewa
take maybe zullumin zuwa law school ne” akunyace Asmeey tadan sauke fuskanta kasa, Mom tahade
fuska tace “zonan” rawa hannayenta suka fara har Mama saida ta lura amman taja baki tai shiru kafin ta
shiga black book din Mom, wucewa Asmeey tayi gaban Mamanta wani kallo Mom tamata tace “wuce ki
daukomin kayan dana dinkama Maman ki da wanda na dinka miki dasu Nana” wucewa tayi bedroom din
Mom, Mama tace “ohh baki gajiya Hajiya Salima! Nagode Allah ya saka da alkhairi Allah kara girma da
daraja” kawo kayan Asmeey tayi bakin Mama har kunne Mom nada kudi so manyan exclusive atampopi
ne Mama tace “Allah dai yaja zamaninki wlh Babansu Aya shi kanshi yasan yayi dace saisa har yau har
gobe kece yar gaban goshi, Aya zatazo namata godiya ko, mijinta ya fitar da zakka dubu dari biyar ta
aikamin wlh” murmushi Mom tayi na isa irin abin nan takeso Asmeey ta kalli Mom tace “Mom natafi”?
Mom tace “yaron nan has been calling you go and talk to him kafin ki koma” wani iri Asmeey taji,
badaman yakira bata dagaba saiya kira Mom, wucewa tayi tafita daga dakin, dakinsu ta wuce ta zauna
kan gadonsu tadauki wayan taga 5miss calls nashi, instead of takirashi back sai kawai ta kwanta ahankali
kan gadon tarike wayan a hannu within 2mins bacci mai dadi ya kwasheta cus tun asuba data tashi bata
koma bacci ba tana wajen Mom, kusan 1hr tana bacci sannan wayanta ya shiga ringing firgigit tabude
idanu tana tashi zaune tana mamakin yanda bacci ya saceta haka, daukan wayan tayi takai kunnenta
ahankali tace “hello” “Wifey how are you”? Abu taji ya tokare mata wuya she hates d name sosai, da
kyar tace “fine” yana murmushi da tana iyaji a muryansa yace “sorry banzo ba har yau ban dawo garin
ba sai yau, ya shirye shiryen salla ni da Mommy na zamuzo washegarin salla” gyadamai kai tayi batace
komiba cus bama tasan mezata ce ba, matse murya yayi yace “I can’t wait to see you my wife Asma’u”
wani iri jikin Asmeey yamata ta runtse idanu, Fawaz yace “kullum sainaga fuskanki a bacci, I don’t know
why I love you this much, me kikamin”? Kin magana tayi Fawaz yace “wai yaushe zaki dainajin kunyan
mijinki eh? Relax and talk to me babu abinda yakai muryanki dadi arayuwana”? Murya chan kasa mai
dari dari tace “kitso akemin zan koma akarasa” dan shiru yayi he feels kaman bata sonshi but he don’t
care, ahankali yace “okay kije toh zan kira anjima take care” dasauri ta katse wayan ta ijiye wayan akan
gado tanemi another blue veil karamin veil tadaura saman kanta sannan tafito Ammi tagani tana fitowa
daga dakinta kaman itama ta hauro tai salla ne ganin kanta bangare daya himm bangare daya a kwance
tace “meya faru ba’a gama miki kitso ba har yanzu Asmeey kowa yayi nashi kitson agidan nan?”ahankali
tace “Ammi bacci ne ya kwasheni a daki” hararanta Ammi tayi tace “wuce ni kafin in mangareki awajen
nan yarinya kaman mage”wucewa tayi tafita sauka kasa Ammi biyeda ita tabude kofa tafice Baba tagani
da kanshi yana bude gate murmushi yalwace a fuskanshi, motan su Abba na danno kai dan nasu ne
agaba hakanan gaban Asmeey yawani fadi shigowan motan zaro idanu tayi tace “Ammi Gwaggo ta iso”?
Daidai nan yaran wajen lalle harda su Ramla da Munir dake wajen dasu Nana suka kwaso da gudu suna
ihun. “Gwaggo oyoyo! Gwaggo oyoyo! Gwaggo oyoyoooo” Kashe motan akayi Abba ne yafara fitowa
yana sanye da manyan kaya da charbi a hannunsa atare duka yaran gidan sukai kan Abba. “Abba
oyoyoooo!” Abba yabude hannunshi dukan uban yaran ya rungumesu, Mamie ma tafito ta zagayo ta
dayan bangaren yaran suka saki Abba ta zago ta gaban motan suka rungumeta, Ammi dahar ta wuce
tajuyo takalli Asmeey dake tsaye tace “wuce muje kiyi gaisuwa” hakanan kawai saitaji tabajin kunya da
nauyi tadajan gyalenta gaba, tawuce wajen Mamie data tsareta da idanu, sai kawai Asmeey taji tanajin
kunyan su Mamie suga fuskanta dan jawo gyalenta gaba tayi tadan tsaya gaban Mamie, Mamie dake
kallonta tasaki yaran tace “Ma’u kene haka zonan” batai wata wata ba dan tana bala’in son Mamie taje
ta rungume Mamie tace “Mamiee” murmushi sosai Mamie tayi tace “Asmeey” Ramla ma tazo aguje
dasu Nana suka rungume Mamie, Baba yabudema Gwaggo mota yakamota tafito dan kafafun sunyi
tsami tace “Muhammadu Sani wai Bauchin nan kullum kara nisa yake
Ne?” Yaran najin muryan Gwaggo duk suka arto, Gwaggo Gwaggo sun kusa kada Gwaggo, Baba yamusu
tsawa. “wai bazaku bi Gwaggo ahankali ba” saukowa kowa yayi su Ya Mustapa da matayensu duk sai
gaisawa ake, Mom da Mama suka fito atare sai gaishe gaishe ake everyone looks so happy har lokacin
Asmeey na tsaye kusada Mamie, Baba yashiga bin ko’ina da kallo
Abba dake lura da shi yace “me kake nema Muhammad” Baba dake kalle kalle yace “Yaya naga tundaga
kan Mustapha har Hassan nagani amman banga Hussaini ba, ina Hamadi”? Kawu yace “ai wannan ka
sanshi” girgixakai kawai Abba yayi yace “yana mota” anatse Baba yawuce wajen motan kai tsaye yabude
kofan gaba yace “Hussaini har yanzu dai halin nan na nan to sauko, fito” kowa na compound din juyowa
yayi jin maganan da Baba yayi, ahankali Asmeey dake tsaye kusada Mamie gaban motan da Baba yabude
tajuyo daidai Hamad na fitowa daga motan kanshi akasa cike da bala’in natsuwa sai kawai gently akuma
natse yaduka ahankali gaban Baba yace “ina yini Baba!” Dawani irin sauri Baba yataroshi yace “tashi
tashi Son ya gajiyan hanya yakuma karfin jiki? Aikin ya warke ko”? Gyadama Baba kai yayi still kanshi na
ahaka yace “Kawu ina wuni” Kawu na murmushi yace “Hamadi lpy lau ya karfin jiki Allah dai ya
karamana lafiya gabaki daya” dan shafa kanshi yayi kadan saikuma yatako kadan zuwa dan nesa da Mom
dake tsaye tareda Ammi da Mama sai kawai ya duka yace “Mommy ina yininku” bayabo ba fallasa Mom
tace “barka da zuwa Hamad” Ammi tace “tashi tashi kaida bakada lpy mike” mikewa tsaye yayi sai yadan
waiga, Gwaggo dake kallonshi tace “yanzu zai nemi Maman shi” aiko aka kwashe da dariya harda Mamie
sai kawai ya sauke kanshi akunyace, Baba yace “kumuje kumuje bismillah”
Yaran suka shiga gaida yayyinsu, Asmeey takalli Hameed tace “ina yini Yaya?” “Wat happen to your
face?”Juyowa Mom tayi ta kalli Hameed sannan ta kadakai tai wucewarta Asmeey tace “faduwa nayi”
dan hararanta yayi tasauke kai dasauri tajuya zata gaida Ya Hamad yawuce abinshi ko kallon inda take
baiyiba instead of yaje flat dinsu Baba sai kawai yawuce flat din dinsu m Ya Mustapa ya kalleshi saikuma
ya kyaleshi, dan satan kallonshi Asmeey tayi Ramla taja hannunta tace “muje ciki” suka wuce flat nasu.
Duk zama akayi Baba yakalli kowa na falon ganin babu Hamad yasa yace “ina Hamad”? Ya Faisal yace
“yawuce chan side din” hada ido Asmeey tayi da Mom data ℳ
💫💫💫💫 wani mugun kallo mikewa tayi da
sauri zata fice Baba yace “ina zaki?” Ahankali tace “zanje akarasamin kitso ne” Baba yace “je flat din
Abban ku ki kiramin Yayanki Hamad kafin kije wajen kitson” gyadama Baba kai tayi tajuya tawuce
hakanan taji gabanta ya fadi, duk babban salla anan Bauchi sukeyi every year tana ganinshi sau daya tun
tana yarinya amman shi kadai ne cikin yayyinta magana bai taba hadata dashi ba, shine ma wanda ba’a
ganinshi, shi kowa ne bayama magana, kullum yana daki saidai ranan da za’a kauye, hartakai gaban flat
dinsu gabanta faduwa yake hannu tasa tabude kofan falon babu kowa ciki banda akwati nan su dake nan
falon da masu gadi suka kawo.
Gently tace “Assalamu Alaykum” but shiru sai eco na muryanta da flat din yadauka staircase tafara hawa
tana wucewa sama daidai nan falon sama ta tsaya ahankali tace “Ya Hamad!” Shiruu kaman babu kowa
a side din, dan tafiya tayi zuwa gaban first room dakenan falon saman ahankali tace “Ya Hamad!” Jin
shiru yasa ta wuce second door din saitadan taba tareda knocking tace “Ya Hamad!”
Shiru babu amsa hakan yasa tace kodai ba nan ya shigo ba wani flat yaje ko boys quarters, maybe tafita
taje boy quarters taduba tana tunanin ta juyo Ya Hamad tagani tsaye abayanta awajen mummunan
faduwa gabanta yayi sosai har tana neman kurma ihu tahana kanta da kyar ta daura hannuwanta duka
biyun akan kirjinta ta saman gyale tana wani kalan mummunan numfashi sabida tsorata datayi ta jingina
da bangon wajen da sauri tana numfashi sosai kaman kirjinta zai fita tana kallonshi fuskanshi da ruwa
gashin giranshi yawani kwanta sabida lema, dogayen gashin idanunsa sun tattare sabida ruwa pink lips
dinshi sunyi wani pink sosai jikinsu duk lema hakama sajenshi a jike ga hannayenshi daya nannade
hannun rigan dake jikinsa zuwa sama tafukan hannayensa ajike da alamu dai he was in the bathroom
yana wani irin kallonta, hakanan kasa jure kallonshi tayi sabida yanda taga yanada wani irin kyau
barinma yanda kwallin idanunsa yamai kyau, tunda take bata taba tsayawa this close to Ya Hamad ba,
idanunshi namata wani iri dasauri ta dauke kanta, kawai bakinta yahau rawa, cikin wata yar
kamkanuwan murya da bamatasan tanada kalanta ba dayake so scattered sabida tsoro tace
“ahhhmmm…..uhmmm dama daman…..” saikuma ta dafa bango kaman zata suma sabida yanda taji
yacika mata gaba and he smells damn good raspberry dawani oud da lavender da sandal wood da vanilla
takeji yake mata, softly murya ciki ciki yar karama mai wani irin taushi yace “who slapped you?” Dawani
irin sauri tadago idanuwanta ta kalleshi today is the first ever time tunda dai tai girma tayi kuma hankali
da Ya Hamad ke mata magana, cus he doesn’t talk to them, yaune rana na farko datakejin muryansa
agabanta, kallonsa take kaman yanda yake tsaye shima yana kallonta bazaka iya tantance ya yanayinsa
yake ba his eyes looks warm calm serious harsh sexy kai komiba, bala’in kwarjini taji yamata idanu lips
dinta rawa suka shigayi sai ta shiga wasa da yatsunta tana kallon yatsun murya chan kasa tace “faduwa
nayi akasa” to her biggest suprise saitaga Ya Hamad ya matso gabanta dab da ita da sauri tadago
idanunta ta kalleshi bai kalli kwayar idanunta ba duko da kanshi yayi daidai tsayinta yashiga sauko da
fuskanshi wajajen fuskanta da mahaukacin sauri Asmeey ta kulle idanunta daidai saitin fuskanta Hamad
ya sauke fuskanshi yana kallon wajen dayayi sauka idanunshi sukayi kan kwantaccen gashin sajenta mai
kyau zare idanunshi yayi daga wajen ya maida idanunshi kan fuskanta yana kallon yanda ta kulle
idanunta lips dinta na rawa tana fidgeting fingers nata sosai hakan yasa yadan koma baya ya tsaya getly
yace “who slapped you?” “Mom” ta amsa kai tsaye dawani kalan sauri tabude idanunta cikeda
mahaukacin mamaki jin yanda tafadi gaskiya what did he do to her? Dago idanunta tayi suka hada idanu
again yai mata wani kallo sai kawai yajuya zai koma first room na wajen data fara zuwa dataga kofan
abude dasauri tace “Baba yace nakiraka!” Kaman bada shi tai magana ba dakin ya shiga ya maida kofan
yarufe batare daya juyoba tabi kofan da kallo tasake kai hannayenta tadaura kan kirjinta dake bugawa
none stop saikuma tasake kallon kofan dakin daya shiga sai kawai tawuce harda dan gudu gudunta
tashiga sauka daga staircase din har lokacin kirjinta bai dawo daidai ba tayi kofa daidai zata bude aka
rigata budewa Ya Hameed ne chak ta tsaya tadan sauke kanta kasa yace “kin gayamai Baba na kiransa?”
Gyadamai kai tayi, Hameed yace “meyace?” Kallonshi tayi tace “baice komiba” sama ya kalla saikuma ya
kalleta yace “did u put anything a face dinki?” Girgizamai kai tayi alamun a’a, cikeda kulawa yace “put
ice okay” gyadamai kai tayi tace “toh” wucewa abinshi yayi yawuce stairs itakuma takama kofan tafice
da sauri tayi wajen mai kitso tazauna aka cigaba da mata kitso har lokacin takasa dawowa daidai she’s
just feeling somehow sai taba kirjinta take tana feeling heartbeat nata da har lokacin bai dawo daidai ba
tanajin muryanshi a kunnuwanta da bata tabaji ba, for as long as tasan kanta Mom bata taba wani abu
ta gayama kowa ba hatta Baba, but wat happened data gayamai Mom ce ta mareta yanzu idan ya sanar
da wani akasan