Showing 21001 words to 24000 words out of 59470 words

Chapter 8 - UWA KO UKUBA MShakur HAUSA NOVEL

M SHAKUR   

28 Mar 2025

3087

Hamadi”? Gyadamai kai yayi yadan
sauke kansa kasa tareda daga hannu yabashi paper bag din Mustapa yadan kalleshi sannan yasa hannu
ya amsa hakan yasa dasauri Hamad yajuya zaihau machine dinsa karaf Ya Mustapa yarikesa yace “ina
zaka? Tsaya wat is this? Nawaye?”
Kanshi akasa yace “is urs” dasauri Ya Mustapha yaciro akwatin agogon yabude da sauri yace “for me?
You got this for me Hamadi?” Daidai agogon ya bayyana is a minimalist agogo brown mai kyau, shiru
yayi yana kallon agogon saikuma yakalli Hamadi da kanshi ke kasa yace “an ina kasami kudi Hamadi?”
Very low calm voice yace “I design website for one cafe they paid me” dadan fada Ya Mustapha yace
“shine bazaka ijiye kudinka katara ba, why are you wasting money? Nacema I need agogo ne?” Har
lokacin kan Hamad akasa baice komiba, Ya Mustapa yayi shiru yana kallon agogon he’s feeling very
emotional cus duka kannensa saidai shi yamusu abu, He’s the first one so kwata kwata baitaba tasowa
dawani expectation na kannensa sumai abuba, bawai basason juna ba no they’re united kawai dai wai
wani cikinsu yasayo specific gift yabashi wlh basu tababa sai yau da Hamad yamai so abun ya mugun
tabashi he was even speechless saiya kalli agogon saiya kalli Hamad da kanshi ke kasa, gently Hamad yaji
Ya Mustapa ya rungume shi cikeda so yace “thank you Hamadi” wani irin kunya ne yakama Hamad
kaman zai nutse awajen yadan shiga komawa baya alamun ya sakeshi abinma sai yabama Ya Mustapha
dariya, yasakeshi yakai hannu yadanja kunnenshi yace “even a hug from you big brother kunya ko”

kanshi na kasa har lokacin bai magana ba, Ya Mustapa yace “thank you Hamadi, nagode” juyawa yayi da
sauri yahau machine ya kunna yabar wajen Ya Mustapa yabishi da kallo harya fita daga gate na hospital
na su, yasake kallon agogonshi yayi shiru sannan ya maida ya rufe yasa a jakan yawuce ya koma cikin
hospital din.
Wuraren 2 yakai gida a falo yaga Gwaggo tanacin alalen gwangwani da akayi da sunkai guda 6 da manja
ga kaji a gefe ga ruwa ga maltina na gwangwani tana ganinshi ta washe baki tace “oyoyooo Hamadi na
yadawo, yaka zokaci abinci” ga mamakinta saitaga yataho, yaune rana na farko datake kiranshi yazo
Hamadi yazo, ta shiga mikewa da sauri tana wani Irin murna tace “bara na daukoma cokali” tayi hanyar
kitchen zama yayi yaciro gyalenta ya ijiye mata yamike, daidai Gwaggo na dawowa taga bashi awajen
but ga gyalen awajen data tashi da sauri ta ijiye cokalin tadauki ledan gyalen tashiga warwarewa tace
“menake gani haka? Hameeda zo zo zo taho yau danki yayi abun arziki Hameeda” Gwaggo ta shiga
warware gyalen Mami na fitowa daga bangaren Abba tazo Gwaggo tace “kinga Hamadi ya sayamin
mayafin salla ni Madina oh dama yaron nan nada kirki da hankali haka dubi mayafin nawa fa” sosai
Mamie taji dadi tace “Masha Allah akashe lafiya Gwaggo” Gwaggo tace “ni nasan Hamadi yayi kudi na
more ba sauran gantalallun da matansu kadai suke kashema kudiba, jibi abinda yaron da baya aiki ya
siyamin na salla banda ke dakika bani atampan codivowel, shikuma Abubakar yamin leshi da atampa
gwara gwara likita yamin takalmi amman sauran ko hoda basu sayamin ba, kiga wannan gyale kaman
wata Amarya da Hamadi ya sayamin ohh Allah, Allah ka karama yaron nan lafiya ka kuma bashi aiki
sabida zamu huta, ahhh zamu huta Madina” Mamie murmushi tayi tace “cinye abincin ki toh Gwaggo”
dasauri Gwaggo tace “hakane ungo linkemin ki maidamin ita cikin leda zanje namai godiya kinga ya
sayamin mayafin amman kunya ya dingaji harya gudu banmai godiyaba” linkemata Mamie tayi tawuce
sama abinta takoma bangaren Abba tana hadamai kayansa tsaf ta gama tafito dakinta ta shiga saitaga
yar leda kan gadonta dasauri tawuce ta dauka tabude taga sarka mai kyau da dan kunne da warwaro
harda zobe, shiru Mamie tayi saikuma tafito kai tsaye tawuce dakinsu tabude kofa yana zaune akan
gadonshi yabude system dinshi ya daura kan cinya yana dandannawa jin anbude kofa yasa yadago
kanshi ganin Mamie ce ta maida kofan ta rufe tace “who asked you to spend money like this eh
Hamadi?” Sauke kanshi kasa yayi, Mamie tace “I’ve seen yanda kai aiki for days on this project yauda
kagama shine zakaje ka kashe kudinka kaida yakamata akara maka ma kudin so that you will establish
something shine kake kashemana eh” kanshi na kasa har lokacin baice komiba, shiru Mamie tayi tana
kallon sarkan saikuma ta tako ahankali tazo wajen gadon ta zauna gefenshi tasake kallon sarkan ta
kalleshi sai kawai taji hawaye sun zubo mata da sauri takai hannayenta tadaura saman fuskanta ta share,
jikin Hamad yayi sanyi sosai ijiye laptop dinshi yayi a gefe yadan juyo yakalli Mamie dake share hawaye
har lokacin fuskanta na nuna wrinkles kawai yau saiyaga Mamie shi tafara tsufa sai zuciyanshi yasake yin
wani iri, murya chan kasa mai taushi da sanyi da nuna so yace “You’ve done alot for me Mamie” yadan
sakeyin shiru kanshi akasa ahankali yace “I am always troubling you da rashin lafiya” ahankali yace
“you’re always constantly worried sabida ni” cikin kuka Mamie tace “shine aka cema ka you have to buy
something for me? You have to repay me? I’m your mother Hamad I don’t need gift sabida kullum ina
cikin dawainiya dakai, you’re my son Hamadi, it’s my duty to take care of duka yarana” dan juyowa yayi
yakalleta saikuma gently yakai hannunshi yadaura saman fuskanta ya share mata hawaye yace “don’t cry
Mamie” hannunshi tarike tana kallonshi tace “promise me bazaka dinga kashe kudin daka samu a aiki
hakaba save your money kaji, kai kadai ne baka da aiki, babanku karfin hali ne kawai baida jari yanzu,

yayyinka nada iyali duk ta yanda zasukai ga kula dakai wata rana zasu gasa barinma idan yara suka fara
tasawa, dama inada niyyan bayan salla zan saida gwal dina na baka saika bude cafe tunda ka iya
abubuwa da computer” ahankali yace “Mamie don’t sell your gold, just pray for me I can take care of
myself and you kinji” gyadamai kai yayi sai kawai sai kawai ta rungumeshi yayi lamoo ajikinta, inhar babu
kowa he accept hug din Mamie but da wani zai shigo dakin yanzu zai saki Mamie, sun dade ahaka
sannan tadago shi ta kalli sarkan tana goge fuskanta tana murmushi sosai tace “nagode Allah yamaka
albarka, Allah yabaka abinda kake nema, Allah yabaka nasara a ayyukanka Hamadi, thank You Hussaini,
Allah yamaka albarka” murya chan kasa yace “Ameen” sabida baiso Mami tasani daga baya tamai fada
yasa yace “I got wristwatch for Abba and turare for my brothers Mamie” sarai tasan yana fada mata ne
sabida kartazo taji daga baya tamai fada, dan shiru tayi chan tace “nawa aka biyaka for aikin dakayi?”
Ahankali yace “2️⃣50k” “nawa yarage yanzu?” Dan shiru yayi chan yace “2️⃣0k” saikuma dasauri yace “inada
wasu kudi a account” shiru Mami tayi tana kallonshi chan ta shafa bayanshi tace “it’s okay but next time
kada ka kara kashe kudin aikin ka haka duk sun fika kudi sunada tsayayyan aikin yi mai albashi kaji”
gyadamata kai yayi, daidai an bude kofan dasauri yafita daga jikinta dudda haka saida Hameed yagani
yawani zaro idanu yace “Mamie dama yaron nan na hugging naki ko gizo idanuna kemin” dawani kalan
sauri Hamad yatashi zai wuce bayi Hameed yashigo da gudu yarikeshi yace “so you can hug Mami
Hamad amman ni baka taba bari nai hugging naka to wlh sainayi yau” yataho zaiyi hugging nashi da sauri
Hamad ya fizge kanshi yace “Mamie” Mamie dake dan dariya tace “mehaka Hameed ka kyaleshi please”
dariya Hameed yayi yataho wajen Mamie tamikamai sarkan tace “kalli abinda ya siyamin yasami kudi
duka ya kashemana” murmushi sosai Hameed yayi yace “kafito daga bayi ina nawa?” Yakalli Mami yace
“ga Gwaggo chan takasa hayowa sama tana jiranku itama ta nunamin gyalenta” Mamie tace “bari naje
kuhada kayanku ku kuka rage” yace “toh Mamie” tawuce.
Fitowa Hamad yayi kana gani kasan wanka yayi but he’s still wearing kayan daya saka dazu sabida
damuwan Hameed bai bari yadauki wani kaya ba ko kallon Hameed baiyiba yazo wardrobe yadauki
jogger da t-shirt yawuce yakoma bayi ya shirya tsaf yafito yajefa kayan daya cire a laundry basket sannan
yazo Hameed yace “ina nawa Hamadi” jakan shi yabude yaciro nashi ya bashi yaciro na sauran yayi shi ya
ijiye a gefe Hameed was so happy with the perfume sai murmushi yake yace “tashi toh muhada
kayanmu” kwanciya kan gado yayi yace “I’m tired” hararanshi Hameed yayi yasauko da box nasu yahada
musu kayan tsaf yasama Hamadi kayan zama gida da jallabiya guda biyu da turarukanshi duka ciki da
takalman daya saya musu na salla da hula da agogo tsaf da sabulan wanka, yadebi few novels na Hamad
ya samai, ka’ida ne duk babban salla a Bauchi sukeyi 7days kuma sukeyi a Bauchi kafin su dawo, gama
hadawa yayi yawuce shima yaje yayi wanka.
Around 9 yashigo gidan daga mosque Abba yagani zaune kan carpet ga kwalin agogon daya siyamai ga
Gwaggo gefensa akasa ta kishinguda da gyalenta amman bacci ya kwasheta tsaresa da idanu Abba yayi
ahankali yace “sannu da dawowa Abba” murmushi Abba yamai yace “zonan Hamad” karasawa wajen
Abba yayi ya zauna ahankali, Abba ya kalli agogon saiya kalleshi yace “naga abinda ka siyama kowa
harda ni Allah yayi albarka, kaima Allah yasa naka yaran su maka abinda yafi haka sannan Allah ya
sanyama hanyar nemanka albarka, Allah yakawo tsayayyen aiki” gyadama Abba kai yayi murya chan kasa
yace “Ameen Abba” yatashi yawuce sama Abba yasake binshi da kallo sannan yakalli agogon kafin yakalli
Gwaggo dake munshari.

Around 7AM Ya Mustapa yazo gidan da matarsa da yaransa biyu Areef and Arfat, shima Ya Abdallah yazo
gidan da matarsa da yarsu Amra tasha lalle ta tafi wajen Mamie da gudu tana nunama Mamie lallinta
saiga Ya Faisal shima da matarsa ita har yanzu bata haihuba duk suna falo an gama loda kaya tsaf,
Hameed ya sauko yana sanye dawani ash color yadi mai kyau Abba dake wasa da jikokinsa yace “Ina
Hamadi? Shikadai ake jira” “gashinan zuwa Abba shiryawa yake” gyadamai kai yayi, Hameed yazo ya
zauna abinshi bai gaida kowa ba, kusan 10minutes saiga Hamad yana saukowa yana sanye da ash color
yadi exactly irin na Hameed sai kamshi yake, yadin yamai bala’in kyau bambamcinsa da Hameed is just
eyes, idanun kwalli garesa and it’s so obvious kansa akasa anatse yake tafiya daidai cikeda kamala da
natsuwa kuma, ya shigo cikin falon calmly yazo gaban Ya Mustapa da matarsa ke zaune kusa dashi
kanshi akasa yace “ina kwana Anty” murmushi tayi sosai tace “Alhamdulillah Ya Hamadi ya karfin jikin an
warware ko” gyadamata kai yayi yatako zuwa gaban ya Abdallah kanshi akasa anutse yace “ina kwana
Anty” cikeda so tace “lafiya lau Ya Hamad ya jiki” bai amsaba yadai gyada kai takawa yayi zuwa wajen Ya
Faisal yace “ina kwana Anty” kanta tasauke akasa cus Hamadi ya girmeta she’s just 2️⃣5 amman baida
girman kai tace “ina kwana Ya Hamadi” kasa amsawa yayi yawuce gently kusada Mamie duka yayyinshi
na binshi da kallo ya zauna, Gwaggo tashigo taci gayu wani bubu da zani da mayafi tasaka na hadari lace
tace “mutafi yaufa jajubari akwai go slow” tashi Abba yayi kowa yatashi aka fito Mamie takashe wutan
kowani daki ta tofa addu’a duka kulle gidan aka shishiga mota
Abba yaje yana sallama da mai gadi yabashi makullin gida da kudade da motoci hudu sukai tafiyan
motan Abba sai motan Ya Mustapa Ya Abdallahi Ya Faisal, motan Abba Hamad ya shiga gaba kusada
dreban Abba, Abba da Mami suka shiga baya, shikuma Hameed ya shiga motan ya Faisal, Gwaggo
tashiga motan Ya Mustapa suka wuce.
**
Bauchi

Shigowa gidan Munir yayi su Yusra dasu Amina da Ya Ramla duk suna kasan bishiya da aka shimfida
babban tabarma ga masu kitso da masu lalle duka ana musu, ga yaran maza da anriga an musu aski sai
wasa suke a tsakar gida Ammi sai up and down take itada masu aiki a backyard ana soye soyen su cincin
da kuma girki sabida su Kawu da Abba dazasuzo yau everyone looks happy the only person dabai gani ba
is Ya Asmeey wucewa yayi ya shiga flat dinsu babu kowa a falo banda tv dake aiki dan duka yaran suna
waje staircase yashiga hawa dakinsu Asmeey yawuce yabude kofa bata ciki hakan yasa yarufo kofan yayi
jimm cus yasan tana wajen Mom wlh ranan nan dayace he wish Ammi ce mamansu bawai karya yayi ba
cus look at yaranta they’re so happy anachan ana musu lalle suna tsalle tsalle a compound haba gobe
salla fa at least tabar Asmeey amata kitso da lalle like every other gurl but no itama tafito tayi aiki she’s
too big tayi Ammi ke handling komi, kullum Asmeey sai ramewa take duk tayi zuru zuru sabida jaraban
Mom he called Ya Aya da Ya Aysha akan suma Mom magana tadan sassautama Asmeey but sun kasa
kowa tsoron Mom yake ga Baba baicika zama ba baimasan wat is going on ba sai wanda yagani akan
idanunshi, ahankali yawuce side din Mom kofan yabude babu kowa a falo sai tv dake aiki falon na

kamshin turaren wuta tafiya yashiga yi yana shiga corridor dazai sadashi da bedroom din Mom yaji
muryan Mom na bala’i. “Kin kosan how important this property law practice yake a law school? Are you
dumb da kin kasa iyawa so nawa zan koya miki? See Asmeey idan kika fadi bar exam dinki just die kafin
kizo ki sanar dani kin fadi, what is so difficult about property law practice when kinada all materials duk
abinda za’a muku a law school na zaunar dake ina koyamiki did you know how lucky you are? Wlh kika
karamin shirme sai ranki ya baci give me requirement din ina jinki” muryan Asmeey yaji baya fita sosai
and it’s even shaking cus bayajin ma abinda take fadi wani irin yaji zuciyansa yamai har wani daci daci
yakeji juyawa yayi ahankali zai tafi sai kawai yaji karan saukan mari dakuma buguwan abu Mom tayi ihu
tace “idan bazaki iya zama ni ki gajeni ba just die Asma’u dan banga amfaninki a doron kasa ba” wajen
kofan Munir yayi da sauri zai bude yakasa sabida tsoro yakafa kanshi jikin kofan yanajin kukan Asmeey
kasa kasa sai kawai yajuya da sauri yabude kofa yafita ta nan window sama ya hango motan Baba
alamun yadawo hakan yasa yayi hanyar dakin Baba kai tsaye yabude kofan baima tsaya sallama ba
babban falo ne sosai mai bala’in kyau Baba na zaune kan kujera ko takalmi bai cireba magana yake
awaya yana sanye da faran shadda ganin idanun Munir sunyi ja yasa yace “Yaya saikun iso Allah kiyaye
hanya bari na kira Kawu” katse wayan yayi yakalli Munir yace “menene Munir”? Tahowa wajensa Munir
yayi yana kokarin magana sai kawai yakasa yafashe da kuka cikeda damuwa Baba yace “Munir what
happened meya faru”? Ina Munir yakasa magana, Baba yadagosa yace “Munir menene”? Da kyar ya
tsagaita kukan yana wani irin nishi na zuciya in a very childish way yace “Baba banso ace nayi gulman
mahaifiyata ko ace nafadi wani abu mara kyau akan Mahaifiyata, Baba just save Asmeey sabida idan
wani abu yasameta Baba harkai sai Allah ya tambaya ni shikenan abinda nazo na gayamaka” yana
maganan ya fizge jikinshi daga na Baba ya ruga da gudu yafita daga dakin Baba ya tsaya looking confuse
ya bisa da kallo yana maimaita kalaman Munir yakai kusan 2min ahaka sai kuma yamike, fitowa yayi
daga dakinshi yabude dakin su Asmeey dake next to him but babu kowa adaki sai kawai yashiga sauka
daga bene cus his believes Asmeey na waje, su Ammi da Mom na backyard suna girki yana sauka kasa
Ammi na fitowa daga kitchen yace “Asmeey na wajen lalle ne?” Da zuciya daya Ammi tace “a’a bata
waje ai tun safe datazo gaidani takoma sama ina ganin tana dakin Mamanta” dasauri Baba yace “Salima
bata tareda ku wajen girki ne” gyadamai kai Ammi tayi tace “eh tana sama bata sauko ba inaga wani
abun suke” Baba ji yayi ranshi yabaci sosai sai kawai yajuya yakoma sama Ammi kuma tawuce tafita
falon Mom yabude but bakowa ciki but yana jiyo muryan Mom daga ciki tana banbami, kai tsaye bude
kofan dakin yayi dadan sauri Mom tajuyo ko kadan bata dauka yanzu Baba zai dawo ba sai chan anjima
chak Baba ya tsaya yana kallon Asmeey dake zaune akasa gaban Mamanta ga uban files da manyan
textbooks agabanta gadan jini daya gani gefen lips nata which yana shigowa akan idanunshi yaga tagoge
da sauri but bata dago kai ta kalleshi ba, tashi Mom tayi tana sauke littafan dake kan cinyanta tace
“Alhaji kadawo” ko kallonta baiyiba idanunshi nakan Asmeeey yace “Husna” dan dago kanta Asmeey tayi
takalli Baba tareda kakalo murmushi asanyaye tace “Baba sannu da zuwa” wani irin faduwa gaban Baba
yayi ganin idanun yarinyar sunyi jaa gashi kuncinta shaidan hannu dayayi ja abunka da fara lips dinta
yadan kumbura Mom takalleta tace “Babanki na kiranki kitashi kin zauna” dasauri tace “toh” kokarin
tashi tashugayi kafafunta sunyi sanyi sai Mom tashiga gaban Baba ta kareshi tana murmushi tace “muje
falo ta biyomu an kawomin kayan sallan dana maka muje kaga dinkin” ko motsi Baba baiyiba kokarin
kallon Asmeey dake kokarin tashi yake Mom tasake kareshi takai hannunta takama nashi tace “muje
kagani” fizge hannunshi yayi yamata wani kallo yace “don’t touch me” yawuce gefenta yaje wajen
Asmeey data tashi, ahankali yakai hannunshi yakama kuncinta yana kallon wajen strictly Baba yace

“meya sami fuskanki yayi ja haka” washema Baba baki tayi tace “faduwa nayi dazu Baba” boyayen ijiyan
zuciya Mom ta sauke, Baba yace “to me kikeyi anan bakije kinyi kitso ba zo muje” riketa Baba yayi yasata
ajikinshi yashiga tafiya da ita ahankali sukabi ta gefen Mom suka fice dakinshi yawuce da ita kan
kujeranshi ya zaunar da ita yawuce fridge dinshi yabude laban yadauko me sanyi yakawo mata yabude
yabata ta amsa tana murmushi tace “nagode Baba” takai bakinta tadan kurba, gently Baba yasake kai
hannunshi gefen kuncinta anatse yace “tell me the truth Mamanki ne tadakeki haka”? Dasauri ta girgiza
kai tace “Baba faduwa nayi dazu Mom bata dakeni ba” shiru Baba yayi yana kallonta ganin haka yasa
tashiga shan madaran gabanta na faduwa, saida ta shanye Baba yace “tashi kije waje wajen kitso da lalle
kema amiki” tashi tayi tace “toh” tawuce tayi wajen kofa tafice yayi shiru sannan yadauki wayanshi yasa
a kunne kai tsaye yace “meet me in my room” ba’a wani jimaba Mom tashigo sai kamshi take dubawa
Baba yabita da kallo ranshi abace yace “Salima nina sa aka kira masu lalli har gida da masu kitso sabida
ama yarana mata akan wani dalili zaki ijiye Husna adakin ki bazaki barta taje tayi ba” Mom na kallonshi
tace “au haka tace maka”? Ran Baba abace yace “babu abinda Husna ta gayamin rannan nan I told you
kibimin yara ahankali wai shi karatun nan dole ne? Law school zata iya zuwa aduk sanda taga dama
akanme zaki tasamin y’a agaba? This is the last time dazan miki wannan maganan ba dole bane

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login