Showing 6001 words to 9000 words out of 59470 words

Chapter 3 - UWA KO UKUBA MShakur HAUSA NOVEL

M SHAKUR   

28 Mar 2025

3091

ita, dan jotter ta dake kan cinyanta ne ya fadi
kasa bata sani ba, alkali yawuce yafita aka tattashi a kotu ana, fita Mom tashiga magana da client dinta
itakuma Asmeey tashiga hada abubuwan su, tana kokarin sa komi ajaka taga an miko mata jotter ta,
wani black hand dake sanye da Rolex chak ta tsaya tanabin hannun da kallo dake sanye da suit black
saikuma ahankali tadago kanta ta kalli gabanta, wani dogon matashi ne yana sanye da suit black
kyakkyawa gaske yanada yawan gashi akai da dan karamin gemu yana kallonta gently yace “u dropped
this Asma’u” dan zaro idanu tayi jin yanda yakira sunanta kuma bata sanshi ba daidai lokacin Mom
tajuyo takallesu anatse tace “Fawaz” dasauri matashin yakalli Mom hakan yasa itama Asmeey tajuyo ta
kalli Mom dataji takirashi tasa hannu ta amsa jotter batare data sake kallonshi ba, saikuma ta sauke
kanta tacigaba da hada kayan shikuma matashin yawuce wajen Mom datai sallama da client nata Fawaz
yakarasa gaban Mom cikeda girmamawa yace “Mom ina yini” murmushi Mom tamai cikakke tace “your
Mom told kadawo you will come and see me today, I told her I will be in this court, muje let’s go Son”
takalli Asmeey dahar lokacin nahada files tace “let’s go uwar kwainani common hada files kaman kina
hada nation” gyadama Mom kai tayi da sauri ta goya jakanta abaya takai hannu zata dauki files din
Fawaz yarigata yace “allow me to help” dasauri Asmeey takalli Mom data dauke kai abinta tace “muje

Son” binta Fawaz yayi sukai gaba Asmeey na binsu abaya suka fice wani office Mom tabude tace
“kushiga nan kujirani, i have a meeting with the judge” Fawaz yafara shiga office din, Asmeey zata shiga
Mom tamata wani kallo tace “review those two yellow files”gyadama Mom kai tayi tace “toh” tashiga
office din tana tafiya ahankali, Fawaz na zaune kan couch dake office din yana danna wayanshi iPhone
16 pro max Asmeey tawuce tazauna kan wata single chair dake wajen dake facing dinshi, tasa hannu
tadauki yellow files din tabude tafara dubawa, ahankali yajaye idanunshi daga kan wayanshi yadaurasu
akan Asmeey dake dube dube, pink lips dinta suna motsi alamun karatu take, kana ganin yarinyar kasan
irin yaran nanne da iyayensu did a good job bringing them up sannan an killace su sosai, tundaga kan
takalmin kafafunta yake kallo har zuwa fuskanta gadan gyalenta daya zame baya yana hango gaba gaban
gashinta dake nan a kwance yayi kyau. Jin kaman ana kallonta yasa tadan dago kanta sama karaf suka
hada idanu dasauri ta sauke kanta kasa, gently Fawaz yace “whats with the case Asmeey?” Murya chan
kasa kaman mai tsoron magana tace “it’s confidential” murya chan kasa yace “give me ur number” dan
kallonshi tayi saikuma ta sauke kanta tace “Mom forbid me, I’m in school ba aure zan yi ba yanzu” the
way she talks sincerely shows she’s just a Mommy’s gurl, like she went straight to point, murmushi yayi
yace “baki sanni ba ko? Tun kina jaririya nasanki” dan kallonshi tayi da manyan idanunta sai kuma ta
sauke kanta kasa tace “but I don’t know you, I’ve never seen you” murmushi yamata yace “do you want
to know me?” Girgizamai kai tayi alamun no yace “why” tace “Mom tace I have no business with men
that are not my family” ahankali yace “but I’m technically your family, I’m Mom’s best friend son bakisan
Maryam kawar Aya ba” dasauri tace “Ya Miemie?” Gyadamata kai yayi yace “yes ni yayansu Miemie ne”
sosai mamaki ya kasheta saikuma tasake maida kanta kan abinda take karantawa yadinga kallonta kusan
20min saiga Mom tashigo office din Asmeey ta dago kanta da sauri Mom tamika mata key mota tace “je
mota kijirani I am coming” karba tayi tawuce tafita daga office din, Mom takalli Fawaz tace “I believe
Mommy dinka told you everything Fawaz, like I told her right from the first time kace kanason Asma’u
zan baka aurenta but kabari tagama Law school, kaga babban salla saura 2weeks immediately bayan
salla list zai fito, inaso taje law school, I don’t want any distraction na maza kona soyayya in her life, I
refuse to give her room for that cus she’s a small girl, batasan komiba, everyday tana taredani, I’m
training her, bawani kokarin kirki Asmeey kedashi ba soyayya at this junction can mess with her IQ, I will
send her number to you but can I trust you bazaka sa tai deviating ba?” Murmushi Fawaz yayi akunyace
yace “Mom I promise you in sha Allah” “good” Mom tafadi tace “nima I trust you, I know you want wats
best for Asmeey, beside kaima Barrister ne, you are in the same profession da ita, so you will help her
and guide her through and through” gyadama Mom kai yayi akunyace, Mom ta yagi paper tarubuta
number Asmeey tamikamai tace “gashinan tashi muje” ahankali yasa hannu ya karba yace “thank you
Mom” murmushi tamai tace “you are welcome Son muje” tamike, atare suka fito Asmeey na zaune a
mota taga sun fito tareda Mom ita batasan ya akayi ba dudda sunsha zuwa gidansu Ya Miemie bata taba
ganinshi ba sai yau, no wonder taga Mom namai murmushi ashe yaron Besty ta ne, har wajen motan ya
karaso sannan yama Mom sallama yawuce yashiga cikin wata 2024 mad Benz ya kunna yabar wajen
Mom tashigo motan ta tada taja sukabar wajen.
Around 3 suka shigo gidan Mom tai parking gateman yazo yana gaisheta yashiga kwashe kaya sannan
suka wuce ciki suna shiga yaran dake falo suna video game dukansu suka taso wajen Mom suna gaisheta.
“Mommy welcome welcome Mom” murmushi tamusu kadan tace “ya school an dawo” jakanta tabude
taciro packet na chocholate data sayo musu tabude taba kowa bibbiyu, yaran Ammi ne dukansu su

bakwai Ramla ce farko, sai Yusra, Amina, sai Maza four Areef, Ahmad, Kamal sai autan giran Ibraheem,
sai karba suke suna godiya Ammi tashiga saukowa daga staircase da murmushi kan fuskanta tace “an
dawo” ahankali Asmeey tace “ina yini Ammi” “lafiya lau sannu ku da zuwa” for the second time takara
kallon Mom tace “sannu da dawowa Maman Aya” ba yabo ba fallasa Mom tace “yauwa” sannan tawuce
sama Asmeey ma tawuce sama, dakinsu ta shiga kaya tacire ta daura towel tafada bayi dantai wanka tai
salla tasan yanzun nan Mom zata kirata kitchen cus Baba na dakinta yau.

KANO
Wuraren 3 nadare yabude idanunshi, gently yatashi zaune yana yaye bargo he feels great and strong duk
zazzabi yatafi hannunshi ya tattaba yadauki wayanshi yataba screen din yayi haske ya haska yatashi yana
tafiya ahankali yawuce wajen wardrobe nasu yabude shima ahankali yaciro wani farin jallabiya mai kyau
da new singlet and boxer da hula yawuce yatafi bayinsu tareda kunna wutan bayin, yakai kusan 30min
aciki dan da dabara yayi wankan bai bari ruwa yataba wajen ba sannan yafito ashirye tsaf ya ijiye
kayanshi cikin laundry basket yazo ya feffesa turare dakin yadauki kamshi sannan yahau kan dadduma
yayi sallan ish’i sannan yatashi yafara kiyamun Layl.
Gentle and very soft kira’an shi kasa kasa yatada Hameed duk gidansu babu wanda yakai Hamad ilimin
addini ya haddace Al Qur’ani kawai shi baiyi choosing rayuwan jama malamai baki da sauransu bane cus
baison shiga mutane sabida yanayin shi ne but babu wani book dazaka kawoma Hamadi dabazai koyarda
kai ba, gashi he loves novels but only Arabic novels yake karantawa. Tashi yayi shima ahankali yawuce
bayi alwala yadauro yazo ya shimfida dadduma kusada shi ya tsaya yabishi sallan around 4:30 suka idar.
Hameed yatashi yakunna wutan dakin yadawo kan dadduman yana kallon Hamad yace “yajiki?” “I’m not
sick” Hamad yafada ciki ciki, hararanshi Hameed yayi yace “kaida ke kuka jiya pretender kawai” hade
fuska Hamadi yayi, cikeda tsokana dan kawai yasashi yayi magana yace “ohh bakasan sanda kayi kuka ba
ko wen u were having pains saiga hawaye sharrr a idanun yaron Mamie” tashi daga dadduman Hamadi
ya yunkura zaiyi da sauri Hameed yarikeshi yace “yakuri yakuri toh! Zauna lemme go and make coffee
for you” dauke kai yayi yay banza dashi Hameed yawuce yafita yasauka kasa ya shiga kitchen yasa ruwa
a heater yadauko musu cups guda biyu ya zuzxuba instant coffeee ruwan na yafasa ya tsayaya yasamusu
sugar da spoon yadauko yahayo sama yashigo dakin ya ijiye agabansa shima ya zauna, gently Hamad
yasa hannu yadauki coffee yakai bakinshi ya kurbi kadan Hameed ma haka ahankali yace “an biyamu jiya
nasama kudi a account” dasauri yakalleshi hade fuska yayi sosai bana wasaba, Hameed yayi murmushi
yace “ni wlh bantaba ganin mutum abaibai irinka ba Allah idan da nine bana aiki kai kana aiki I swear
ATM card dinka ma dani zai dinga zama tsabagen yanda zanci kudinka kaiko u hate nabaka kudi, you
hate kaci kudina why eh Hamadi? Am I not your twin? Why do you hate taking money from me”?Kaman
bazaiyi magana ba saikuma murya chan kasa yace “save your money kayi aure da Zainab” wani irin zaro
idanu Hameed yayi, wlh, wlh Hamad baitabamai magana hakaba sai yau, dauke kai Hamad yayi kaman
bashi yayi magana ba yakai tea bakinshi, Hameed yawani kwashe da dariya yace “Hamadi daman kasan
ina soyayya da Zee? Duk wayan damukeyi kana pretending kaman bakasan komiba dama kasani? Iyye
ikon Allah har wani so kake nayi saving kudi for aurenmu” dariya Hameed yahauyi sosai yana kallon
Hamad da kaman bashi yayi maganan ba coffee yake kurba abinsa kuma yaki kallonsa, dan tsagaita

dariya Hameed yayi yace “jiya I don’t know what got over me I almost kissed her” ijiye mug na coffeee
Hamad yayi kawai ya yunkura zai mike da sauri Hameed yarikeshi yace “Hamadi wai I can’t gist with u, if
I don’t tell you wats going on in my life wazan gayamawa? Besides ma idan baka koyi all this ba how will
you get married? Tayaya zaka raya sunnan ma’aiki da iyalinka”? Fizge hannunshi Hamad yayi dasauri
yayi hanyar kofa, Hameed ya kwashe da dariya yace “wlh matarka ba kunya zataci ba atoh banza kawai”
bugomai kofan Hamad yayi da karfi, habawa me Hameed zaiyi inba dariya ba abun Hamad is too much
shifa Hamad ko kallon mata baya iyayi, you will never see Hamad with any friend aduniya, you will never
see Hamad a inda ake maganan banza, ko abu zaiyi on google idan irin advert din banzan nan yayi
popping up yahakura kenan wlh, just look at yanzu because of conversation na kiss yagudu yatafi
masallaci, Wlh he’s not sure Hamad yamasan yanda ake sex taraya da iyali, he remembers suna yara a
fiqhu duk ranan da za’ayi wani baabi na wani abun kunya he will leave the class, Allah yama Hamad
kunya da jin nauyin anything raw and bad he just can’t stand it, he just wants to see ranan da Hamad
zaiso wata ko ranan aurenshi kai he will love to see matan Hamad da ciki cus yanaso yasan tayaya zaima
matanshi ciki ko a ruwa zata sha Hamad fa ko kaya baya iya cirewa gabansa hmm, Allah ya kyauta.

Bayan sallan asuba kowa yadawo banda Hamad daya tsaya muraji’a sai wajejen 9 ya shigo gidan the way
yake tafiya ka kalleshi saika kara kallonshi, yana taku cike da izza da natsuwa da haiba da kuma kwarjini,
farin jallabiyan jikinsa nawani irin sheki, yau Saturday ko maybe saisa yaga motocin yayyinshi agidan dan
yawanci on a Saturday sukanzo suyi breakfast tareda Abba ayi catching up rannan ba aiki.
Gently yayi sallama yashiga falon dukansu suka amsa Abba ne zaune akasa kan lallausan carpet dinsu
yana sanye da jallabiya da yar hula akansa ga charbi a hannunsa yana kallon Hamad din, sai Ya Mustapha
dake zaune kan kujera kusada Abba, sai Ya Abdullahi shima sanye da jallabiya zaune kan 2 sitter, ya
Faisal na zaune kusada shi, sai Hameed dake zaune akasa kusada Abba, ga upan atampopi da lace sunkai
kusan 50, each da shaddodi anan tsakiyan dakin, ahankali yakarasa cikin falon har zuwan gaban Abba
anatse yace “ina kwana Abba” kanshi Abba yashafa yace “yaya karfin jikin?” Kanshi akasa yace “dasauki”
tashi yayi yabama Ya Faisal hannu cikeda girmamawa yace “ina kwana” murmushi yamai cikeda so yace
“ya jikin” gyadamai kai yayi yabama Ya Abdullahi shima yacemai “ya karfin jiki” hannu yabama Ya
Mustapha kanshi akasa yace “good morning Ya Mustapha” anatse yana kallonshi yace “how are you?
Wat time katashi?” Ahankali yace “3” yajuya zai wuce Abba yace “dawo kazauna cikin yan uwanka” ba
musu yadawo ahankali yazauna kusada Ya Mustapa, Ya Abdallah yayi murmushi kawai daidai Mamie na
shigowa falon duk suka gaidata Abba yace “Maman Dr zoki zauna kicirema kowa nasa inaso da safen nan
Faisal ya aika da komi Bauchi” Gyadamai kai tayi tace “toh Masha Allah” Abba yace “Doctor tashi
kadauki naka danasu Areef” gyadama Abba kai yayi yatashi yadauki shaddan su yadi goma ya isheshi
shida yaran yace “Allah amfana Abba”.
[03/01, 07:38] +234 806 292 7511: 💫MOTHER OR CURSE? 💫

✍💫M SHAKUR

OYA JOIN GROUP DINA INDA NAKE POSTING UWA KO UKUBA IDAN KINA CIKIN 1-8 DONT JOIN 9 PLEASE
https://chat.whatsapp.com/HOfjHAh3gw5502DZ5uJTWn
EPISODE 3💫
Around 10 nadare Hameed yashigo dakin wuta ya kunna yana kallon Hammad dake bacci mai nauyin
gaske yawuce bayi ya watso ruwa yafito daure da towel yaje yasa boxer kadai yazo zai kwanta ya tsaya
yana kallon Hamad, saiya tashi yakai hannu yasake gyaramai bargon dayake lullube dashi sannan ya
kashe wuta yahau gadonshi, ya kwanta daidai wayanshi na ringing ya daga yakai kunne murya chan kasa
yace “Zeezee” daga tachan bangaren tace “Ya Hameed baka kirani ba why is your voice so down haka
kaman you are not happy wat is it”? Dudda akwai duhu juyowa yayi yakalli gadon Hamad ahankali yace
“my brother is sick Zee” dasauri tace “subhanallah your twin? Wanda akama operation last
week?”Gyadamata kai yayi yace “yes!” Murya chan kasa tace “ayyahhh so sorry Allah yabashi lpy, Ya
Hameed kanason twin brother ka sosai” murmushi kadan yayi kaman bazaiyi magana ba yace “I don’t
even love him as much as he loves me! Hamadi na sona sosai fa, he’s not much of a talker but actions
nashi speaks love, anytime I’m sick baya bacci he stays all night yana kula dani, before nace kaza or
nafurta i want kaza Hamad yamin is as if he reads my mind, kokuma my mind na jikinshi ne I don’t know
but kaman magic, saisa anytime he’s sick jinake rayuwana ba dadi, sai narasa ina zansa kaina naji dadi,
most times he knows we all get worked up idan baida lafiya saisa baya fada mana, he’s always sick ne
yau mura, gobe kai gata kaza, he feels bad yana unnecessary damunmu shi ba sikla ba, even today
bansan he was sick ba cus bayaso mu damu, and bansan why I didn’t noticed ba cus I’m always the first
to know whenever he’s sick, I’m feeling very bad Zee I don’t give dan uwana dsame kind of love and care
he gives to me” Zee tace “don’t say that, kanason brother ka sosai saisa ma har kakejin guilt din nan,
anyways shi kadaine ban sani ba agidanku, bantaba ganin twins da ba’a san daya ba sai akanku” dariya
Hameed yayi for the first time yace “Hamadi baya hoto, he hates pictures, he hates cameras, bayason
mutane, Grandama dinmu tace mutum daya kadai Hamadi keso aduniya” Dasauri Zee tace “waye?”
Ahankali yace “Mamie! Idan kinga yadanyi few magana ko hira to da Mamie ne, gashi you will never
hear meyake cemata kaman munafuki, Gwaggo always call him makiri takadirin yaro” dukansu sukahau
dariya yadan tsagaita yace “don’t worry bari yaji sauki zan jawoshi muzo zance gidanku tare” murmushi
tayi tace “okay” ahankali yace “bari ki kwanta we will talk tomorrow agaida Mama bye” bye.
**

Bauchi!

“Wai bazaki tashi ba Asmeey?” Wata doguwar matashiya fara dake tsaye gaban wani gado haka mai
kyau 6/7 tahau dukan wacce ke nannade cikin bargo da ba’a ganinta tace “kowa yatashi anyi salla an tafi
aji banda ke, bazaki tashi ba sai Baba yashigo gida daga masallaci wai Husna” ko motsi batayiba, baccin
ta takeyi lafiyayye, bude kofan dakin akayi hakan yasa wacce ke tsaye gaban gadon ta juyo da sauri, wata
hamshakiyan mace ce tsaye gaban dakin mai jiki yar gajera haka dan batada tsayi ga farin glasses a kan
idanunta tana sanye da dogon hijabi har kasa mai kyau ga charbi a hannunta, tanada jiki, fuskanta babu
alamun wasa, kana ganinta kawai kasan no nonsense mutane ne hakan yasa yarinyar dake tsaye gaban
gadon cikin whispering tana kallon wacce ke cikin bargon ta side na idanu tace “ai ga Mom nan” awani
mahaukacin zabure yarinyar dake nannade cikin bargon tawani yaye bargo ta taso da mugun gudu
akuma firgice tana dirkowa daga gadon har tana neman fadi sabida baccin dake idanunta jikinta ba karfi
amman ta dafa gado ta tsaya da kyau tana goge idanunta da gefen bakinta da duk miyan bacci, daga ita
sai yar rigan bacci daya tsaya mata a knee fari fari, kanta babu dankwlali gashinta dayake a tsefe baki
sidik yayi biji biji ya sauko har gadon bayanta, fara ce sosai like asalin fara dan tafi wacce ke tashinta
haske ma, ba siririya bace tanada dan kiba unlike dayan da siririya ce sosai saidai tafi wacce ta tashi daga
baccin tsayi da matured face alamun kaman ta girmeta, sannan wacce ta tashi na bala’in kama da matar
dake kofa kaman tayi kaki ta tofar, har yanayin rashin tsayin saidai yarinyar da dan tsayinta ba laifi but
bawani sosai ba dan akafadan wacce ke tashinta daga bacci tsawonta ya tsaya, strictly matan dake kofan
babu wasa kan fuskanta cikin wani thick powerful voice tace “okay ita Ramla bata isa ta tasheki ba kinaji
ana tashinki kinyi shiru right”? Baki tabude zatai magana babu wasa kan muryan matan tace “idan kince
uppan sainazo wajen nan na daura miki mari stupid girl!” Shiru taja bakinta tayi gabanta na faduwa dum
dum dum, matan tace “nabaki 3min do whatever you want to do kifito kiwuce aji kona saba miki”
dawani irin sauri tajuya tayi bayin dakinsu matan ta kalli dayan budurwan da kanta ke kasa tace “kekuma
me kike jira? Oya bacemin daga sight kiwuce kitafi aji kema” dasauri yarinyar tace “toh Mom” hijab nata
dake kan gadon ta dauka tasaka da sauri tawuce gaban dressing mirror su tadauki Al Qur’anin ta tazo
wajen sai kuma takasa wucewa, babu wani yaro in this house da baya shakkan Mom kawai ajininta abin
yake, she’s so scary cus bata da wasa and batason nonsense even a bit, ganin haka yasa Mom tajuya
tawuce tabar wajen itakuma Ramla tafito, Babban gidane sosai tashiga sauka kasa ta sauko falo tabude
kofa tafita gidansu is a very biggggg house, ga flats daban daban chan tawajen masallacinsu akwai wani
katon class tawuce direct tabude kofa tashiga yaran gidan su ne ciki, 6boys ne awajen akwai dan 20yrs
sai sauran duka kanninshi ne sai kuma mata yan 8yrs, da 9yrs sai ita datashigo ta zauna tana sauke ijiyan
zuciya ganin Malamin su bai shigo ba yar 9yrs din tace “Ya Ramla ina Ya Asma’u?” Yar 8yrs tace “hmmm
Ya Asmeey ai bata tashi ba, Allah yasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login