Showing 18001 words to 21000 words out of 59470 words

Chapter 7 - UWA KO UKUBA MShakur HAUSA NOVEL

M SHAKUR   

28 Mar 2025

3089

kifa kanta a kirjin Ramla tace “Ya Ramla I’m a bad daughter I hurt my Mom, bai
kamata na tsaya inata sauraron abinda Munir yaketa fada gama da Mom ba, a good daughter bai
kamata ta tsaya and listen to any magana ko kalamai marasa kyau akan mahaifiyarta ba, and nadinga
tarema Munir da zata dakeshi i didn’t even know why I did it kawai yabani tausayine, banso ta dake
shine, da Mom ta daki Munir gwara ta dakeni, he said all he said out of anger but ai Munir is a good boy,
he always care for me he shares everything he has with me” ahankali Ramla tace “konine bazanso adaki
Munir ba, stop crying hakanan, Mom zata hakura ya isa, you are hurting yourself Asmeey” ijiyan zuciya
kawai take ita kadai tasan yanda takeji a zuciyanta, maganganun Mom sun zauna aranta waye ita zataja
da authority Mamanta? Was she trying to show Mom tafita son Munir bayan Mom ne ta haifeta? She is
feeling so bad and guilty, ahaka baccin da batayi last night ba ya kwasheta ajikin Ramla, Ramla ta
kwantar da ita she’s feeling very bad even though sunada different mothers but sunason junansu
regardless saisa ma Baba ke hada yaransa waje daya su kwana kuma kusada dakinshi. Tashi tayi ahankali

tafito daga dakin tawuce dakin Ammi tabude kofa, Ammi na zaune a falonta wani wa’azi takebi a Sunna
tv Ramla ta shigo hakan yasa ta kalleta dasauri ta maida kofan tawuce wajen Ammi ta zauna kusada ita
dab sai kuma tayi shiru Ammi tace “menene? Meya faru?” Kaman bazatai maganan ba takasa rikewa
murya chan kasa tace “Ammi mesa Mom batason yaranta especially Asmeey kaman yanda ke kike
sona?” Tsareta Ammi tayi da idanu tace “idan gulma yakawoki tashi kibarmin daki” kaman zatai kuka
tace “wlh Ammi Asmeey tausayi take bani sosai, Ammi kinga ke baki dakinmu baki kwana tareda mu, I
use to see wat she’s going through kullum, Ammi idan Mom tabata manya manyan files din nan nasu na
kotu idan yarinyar tazo bata iyaba ko bata gama abinda Mom tasata ba kaman zata zare kaman zata
haukace wani zubin har zawo takeyi wlh kaman zatai hauka, Ammi all of us zamuyi bacci banda ita
sabida she’s trying to read duka abinda mamanta tasata, saisa most of the time saina tashi nabar dakin
cus idan ina kallonta zuciyana breaking yake wat kind of mother is Mom Ammi? Why is she making her
daughter go through so much pain? And Asmeey can’t react sabida she feels abinda Mom kemata is
okay and is normal, Ammi batada lokacin kanta sabida Mom kanta ba kitso sabida Mom, time din dazata
zauna ta kula da kanta takasa sabida tunanin files din Mom, what kind of mother is Mom eh Ammi?”
Murmushi Ammi tayi tace “the best mother but mai worst approach, Allah ya kyauta ke banson
maganan baruwanki kicire idanunki akansu yanda nakeyi dake dasu Yusra ba dole ne sai Mom tayi haka
da nata yaran ba so mind your business” hawaye ne yataru a idanun Ramla ahankali tace “Ammi please
ki gayama Baba azaban da Asmeey is going through cus bai sani ba, Ammi the worst part is Asmeey can
not even show cewa she’s sad! Wlh bantaba ganin sad young girl kaman Asmeey ba, waya babu any
social media sai watsapp, waya babu any contact saina sisters nata da yan gidanmu, friend kwara daya
Mom tahana, ba saurayi, school Mom takasa ta tsare ita ke kai yarinya tadawo da ita, Ammi wlh I hate
Mo….” Wani kallo da Ammi tamata yasa takasa karasa maganan, strictly Ammi tace “tashi kifita daga
dakina” ahankali ta mike tawuce tafita daga dakin.
Around 11 Asmeey ta farka gently ta tashi zaune har zazzabi zazzabi takeji bathroom nasu ta wuce
tahada ruwan zafi sosai tai wanka tajuya tana kallon bayanta ta madubi da sheda tako’ina sunyi ja
abunka da faran fata, ijiyan zuciya ta sauke sannan tafito tazauna gaban madubi tadauki mai tafara
shafawa tana cikin shafa man taji wayanta na ringing har mantawa take tanada waya, da sauri ta juyo
akan gadon taga wayan hakan yasa ta tashi ahankali tasa hannu ta dauki wayan tana kallon number
which is new, ganin sabon number ne saitaki dauka anata kiranta chan wayan yasake ringing tana
dagawa taga Mom dasauri ta dauka kirjinta na bugawa sosai ahankali tace “Mom” Strictly Mom tace
“when did you become deaf and dumb? Are you blind da bakiga anata kiranki awaya ba? Fawaz ne call
him back kuyi magana” gyadama Mom kai tayi kaman tana gabanta tace “t…toh” Mom ta katse wayan
dailing number tayi back harya katse ba’a dagaba sai number yakirata back ahankali tadaga tace “Hello
Mom tace nakiraka” shiru akayi kaman ba mutum adayan bangaren hakan yasa Asmeey tace “hello”
cikin wani husky voice yace “da Mom batace ki kiraba da bazaki kiraba?” Ahankali tace “eh” anatse yace
“why?” Ahankali tace “sabida Mom forbid me from talking to kowa banda my family” dan murmushi
Fawaz yayi muryanta bala’in dadi, yadan murmusa yace “ai nima yanzu I’m part of the family since I’m
going to be your husband!” Hakanan Asmeey taji gabanta yafadi dumm! Takasa magana kawai tunaninta
ya tsaya chak, Fawaz yace “Mom choose me to take care of her last baby gurl, I’m your husband to be
Asma’u” abu taji ya tsaya mata awuya sai taji kaman kuka takeji saikuma takasa, murya chan ciki yace “I
love you Asmeey” sauke kanta kasa tayi this is the first time wani ke gayamata yana sonta, anatse Fawaz

yace “zan dinga kiranki wifey daga yanzu” shiru still tayi ahankali yace “I will be going to London gobe it’s
a 2️⃣days trip idan nadawo I will come and see you okay Wifey” shiru tayi jin batayi magana ba yasa yace
“are you there” rasa abinda zatace yasa tace “wayana zai mutu my battery is low zansa charge” dasauri
tacire wayan daga kunnenta ta katse ta yarda wayan tareda kifa kanta agado tana sauke ijiyan zuciya.
Kusan 3mins tayi ahaka sannan ta tashi tawuce wajen wardrobe nasu tabude wani atampa taciro gown
tasaka green yamata so simple a jiki tasaka hijab sai kawai tahau kan dadduma.
Around 3 Mom ta shigo gidan kashe motanta tayi ta shigo falo Ramla tace “Mom sannu da zuwa” ko
kallonta Mom batayiba tawuce daki abinta Ammi tafito daga dakinta takalli Asmeey datagani gaban
dakinsu tana kallon bangaren Mom sai kawai tazo tawuceta ta tafi dakin Mom kai tsaye tasa hannu
tabude kofan da sallama Mom na zaune tana kokarin ciro iPad mata daga cikin jakanta ganin Ammi saita
tsaya tana kallonta Ammi ta maida kofan tarufe tazo ta zauna kan kujeran dake facing na Mom anatse
tace “Maman Aya nasan maganan dazan miki ba lallai ta miki dadi ba, sannan ba hurumina bane but all I
know shine d’a na kowa ne! Asmeey da Ramla da Munir duk daya suke awajena” Ammi ta danyi shiru
sannan ta kalleta ido cikin ido tace “Salima yaran nan mune muka haifosu amman kisani amana ne su
agaremu wanda Allah yabamu rannan gobe kiyama Allah zai tambayemugame dasu, hakkinsu na kanmu,
idan muka cutar dasu Allah zai saka musu sannan zai hukuntamu! Kene mahaifiyar yaran nan kinsan me
kike musu kinsan ya fushinki yake aransu, nasan sun miki laifi but yanda kika sharesu is torchuring them,
tun jiya they couldn’t eat sabida ke! They couldn’t sleep sabida ke, Asmeey tun jiya takasa saka
lafiyayyen abinci abakinta same with Munir dudda Babansu yatasashi agaba yatafi school tun safe, I’m
sure ba lallai yama gane abinda ake koyarda su a makaranta ba! Gabaki daya yaran kin barsu agantale
duk sun zama wani iri, idan ciwon zuciya ya samesu ko hawan jini I’m sure you will not forgive yourself
Salima! It’s okay for us mothers to be angry but kinfi kowa sanin mai fushinki yakema yaran nan I don’t
even know wat I’m doing her but seeing them is breaking my heart, what is so big dazakima Asma’u
kalan tabon da hala yaran dazata haifa nan gaba zasu gani a jikinta? Aganina me wacce zatai fada ne da
duk wanda zaiyi inflicting such pain ajikin yarki mace ba ke kimata dakanki ba, wallahi Allah zai tsayar
dake akan yaran nan, amman kiyakuri idan na shiga huruminki” Ammi na maganan ta tashi tawuce kofa
tabude tafita, Mom tabita da kallo ranta ya dagule, yau Aya da Aisha duk saida suka kirata kuma tasan
Babansu ne yakira ya sanar da su, kafafu ta kada tai dan ijiyan zuciya ta sauke anatse tace “Lami” da
sauri yar aikinsu Lami tashigo dakin anatse tace “gani Hajiya” “kiramin Asmeey” Mom tafadi atakaice
hakan yasa Lami tafice. Asmeey na zaune kan gado idanunta sunyi jazur Lami tabude kofansu tace “kizo
Maman ki na kiranki Asmeey” dasauri Asmeey ta mike tsaye ta gyadamata kai gabanta faduwa yake,
tafito tana tafiya ahankali tawuce side na Mom ahankali tabude kofa, babu kowa a falo hakan yasa
tawuce bedroom din tai knocking da sallama daga ciki Mom tace “come inside and lock the door” kofan
tabude ahankali babu kowa a dakin gadai kofan bayi a bude maida kofan tayi tarufe tasa lock ta tsaya
awajen, daga bathroom Mom tace “zonan” wajen bayin Asmeey tayi gabanta na faduwa sosai taje
gaban bayin ta tsaya, Mom na tsaye wajen tap ga bucket tana tara ruwa tama Asmeey wani kallo tace
“zonan” wani irin nishi Asmeey tafara tana kallon Mom, yanda kirjinta ke motsi zaka dauka fashewa zaiyi
sai kawai hannayenta suka fara rawa jikinta ma haka takasa magana, tadan shigo ta gaba gaban bayin sai
kuma taji knees nata sun kasa daukanta tadafa bango zatai kneeling bakinta na kokarin furta magana.
“M…..Mo….Mom….” Taku daya Mom tayi tazo wajen tasa hannu tawani fizgota cikin bayin Asmeey zata
tsala ihu Mom ta bugata da bangon bayin takai hannayenta kan wuyanta ta shaketa da bala’in kyau

idanunta na kadawa tace “because of you mutanen da basu kai komi ba, in educational level i think NCE
gareta but tanada audacity da zatazo tana gayamin maganan banza ana cewa Allah zai tambayeni sabida
ke, kedin banza da wofi, Babanki bai kwana anan ba dudda yana bangarena and still yabiyoni yacimin
mutunci akanki this morning, are you showing people ina making naki sad eh? Are you showing mutane
I’m hurting you”? Girgixamata kai Asmeey tayi tana tari idanunta sunyi ja kaman zasu fito, Mom nawani
irin kallonta tace “nina haifoki and I can kill you babu abinda zai faru, Shegiya wulakantacciya sabida ke
anata kirana, wani daraja gareki Asma’u dan Maman ubanki” wani Irin kyarma tafara idanunta na juyawa
kaman zata mutu ganin haka yasa Mom tasaketa Asmeey ta zube awajen tana wani irin tari tana
bankarewa tana dukan wuyanta, Mom ta tsaya tana kallonta zuciyanta na tafarfasa sai kwai ta juya ta
sunkuci bucket na ruwan datake tarawa ta daga ta juye akan Asmeey tai wani irin ihu da baya fitowa
sosai Mom tace “Shegiya jaka kawai duk sanda akamin magana akanki sai kinji ajikinki” zata ijiye bucket
din sai kuma ta daga bucket din ta shiga bugama Asmeey tana rafka mata duk ta inda ta samu Asmeey
na wani irin kuka tana kare fuskanta da hannayenta akasan bayi, Mom ta jefar da bucket din daya fashe
tajuya tafita daga bayin tarufe bayin tana huci sosai.
Kaya tawuce ta chanza sannan tafita daga dakin tawuce kitchen dan yauma Baba na side nata.
Kusan 1hr tana akasan bayin ahaka sannan ta dafa bango ta lallaba ta tashi ta zauna ta kankame jikinta,
this is the reason jiya she tried to protect Munir cus bataso Mom tafaramai Irin wannan dukan gwara ita
ayita mata dan tama fara sabawa, sosai takejin sanyi but unless Mom ce tazo ta budeta bata isa ba tafito
da kanta ba, wani irin zama tayi kaman almajira tana kallon window bayin hawaye na fita daga idanunta
kadan kadan har wajajen 5:30 na yamma sannan taji an shigo flat din.
Tana wajen akazo aka bude kofan bayin dasauri takalli Mom jikinta na rawa muryanta baya fita sosai
tace “I am sorry Mom” wani kallo Mom tamata ta daka mata tsawa tashi kicire kaya, zabura tayi tamike
tsaye da kyar tana dafa bango ta shiga cire kayan Mom na kallonta hawaye sake kwararo mata daga
idanu sukayi Mom tace “yayyinki basu taba ja da dokana ba and look at them they’re living a very fruitful
life, I will say this to you for the last last! The next time zan ce kiyi abu ki kiyi, na hanaki abu kikiyi,
konace kiyi abu ki kiyi wlh wlh zam share sunanki daga cikin yaran dana haifa Alhamdulillah bake kadai
gareni ba” daidai tacire rigan yarage sauran pant and bra hannayenta duk ciwo sabida yanda tadinga
kare fuskanta dasu da Mom na bugamata bucket, Mom ta mata wani mugun kallo tace “ko ina zakikai
girman nono oho jaka kawai saina kaiki an ciresu cus suke saki feeling kaman kin girma bakisan zan iya
tattakaki ba kokinkai shakera dari, juya nagani” juyawa tayi Mom tabi bayan nata da kallo duk shaida na
dukan shekaran jiya juyawa tayi takoma daki chan ta dawo da magani a hannu ta bude tafara shafamata
tana fada tace “kunyi waya da Fawaz”? Gyadama Mom kai tayi alamun eh, Mom tadanyi shiru chan cikin
kakkausan murya tace “I choosed him for you! Shizaki aura, shi kadai ne namijin dana yarda dashi in
your life kuma bance you should get distracted da soyayya ba, tsakani ki dashi biyayya, your top
pariority shine ki gama Law school da good grade, sai bayan kin gama law school zan turashi yaga
Babanku asa rana ko ayi biki kinakan NYSC ko bayan NYSC so ki saki jiki dashi yarone mai tarbiya i
choosed him for you jiya nina kirashi kotu dan yazo ya ganki dudda ya sanki tun kina little gurl, sister shi
kawar yayanki Aya ne u remember right?” Gyadama Mom kai tayi jikinta har sannan rawa yake Mom
tace “shima I told him banso yayi distracting naki da soyayya focus on your goals am I clear” ahankali
tace “yes Mom” Mom tace “all the files dana baki gobe zaki bani summary kowani case I don’t bloody

care how u will do it, get out of my bayi” dasauri ta dauki riganta tadan juyama Mom baya tana maida
riganta Mom na kallonta kusan Asmeey tafi yayyinta duka nono har Ramla datake gani tanada shi, ina
zatakai nono haka God she’s just turned 2️⃣1️⃣ batason hakan ko kadan, wucewa tayi tafita daga bayin tana
tafiya kadan kadan tafice gwanin ban tausayi tana fita Munir na shigowa da sauri tayi gefe zata wuceshi
yakama hannunta chak ta tsaya tadan sauke kanta kasa yana kallonta yace “why did u cry? Did Mom
beat u again? Are your clothes wet? Ruwa ta watsa miki?” Fizge hannunta tayi da sauri ta kakalo
murmushi tace “bayi na wanke ma Mom yes I cried but sabida ta hakura, jeka bama Mom hakuri kaima
Munir” Dan Jim Munir yayi yana kallonta tausayin Asmeey yakeji sosai hakan yasa ta turashi ganin yana
kokarin magana yawuce side na Mom itama tawuce.

ABINDA MOM KEYI TA KYAUTA?????

COMMENT DANAKE GANI TAKO’INA YASA NA KARA MUKU💫
PISODE 8💫

KANO

Two days to salla
Yau tun safe shirye shirye ake agidan, Abba is a very cultured and family man baya wasa da zuwa garinsu
babban salla, a kauye suka taso bayan mahaifinsu yayi kudi yadawo dasu cikin birnin Bauchi, so duk salla
anan Bauchi sukeyi, rannan salla na biyu kuma sai suje kauye ziyara.
Mamie is very busy da shirye shirye, Gwaggo da sai yau ta zauna agida dan tunda aka mata takwara
agidan mai jego take zama rainon takwaranta, itama nata aikin take uban kayan da Gwaggo tahada na
tafiya zaka dauka bazata kara dawowa gidan ba, a manya manyan gana masgon tahada komi, Abdallah
kawai ake jira yadawo da motoci daga service a jejjera komi gobe da safe zasu shiga hanya.
Gently yashiga saukowa daga staircase yana sanye dawani wando black sai maroon t-shirt daya zauna
ajikinsa da kyau, yasaka pcap black akai sai black shade a idanunshi ya goya black bag pack abaya, he
looks damn handsome and huge, babu kowa a falon sai kamshin turaren wuta dake tashi, muryan
Mamie dayaji a kitchen yasa yatafi wajen baitaba fita bai sanar da mamanshi zai fita ba, a gefen kitchen
din ya tsaya cus baimaso yaga matan dake tayata aiki, murya kasa kasa yace “Mamie!” Dasauri Mami
tajuyo jin muryan Hamad, ganin bata ganshi ba yasa takalli matan Ya Mustapa dake wajen tace “ina

zuwa Ummi” tafito daga kitchen din ganinshi tsaye a gefe ya shirya tsaf kanshi na kasa yayi kyau sosai
yasa tadan tako dab dashi tace “ina zaka Hamadi”? Murya chan kasa yanda dagashi sai Mamin shi zasu
iyajin meyake fadi yace “zanje na sama wani cafe software ne dasuka sa nai musu rannan salla zasu bude
cafe”murmushi Mamie tayi sosai tace “Masha Allah, Alhamdulillah Allah bada sa’a, Allah yacigaba da
kawo maka aiki haka, kayi gudu ahankali kasan titi acike yake sabida salla saika dawo” gyadamata kai
yayi yajuya yafice Mamie tabishi da kallo harya fice sannan takoma kitchen. Compound dinsu yafito ya
goge machine dinsa yahau kai yatada aka budemai gate yafice, cafe da dan nisa but haka yaje, he install
it for them ya nunama Ogansu yanda ake amfani dashi sukai test running akai order from site din sannan
Ogan yamai godiya yabiyashi payment nashi 250k ya karba yafito lokacin around 12:50, awani masallaci
ya tsaya yayi salla sannan yafito yahau machine nashi wani babban plaza yaje yayi parking sannan
yashiga cikin mall na wajen he wants to buy something for Mamie, Abba da Ya Mustapa tunda yau
yasami kudi, wajen agogon maza yaje wasu agoguna yazabo masu kyau guda biyu 50k each na Micserah,
sai yaje bangaren mata ya tsaya turus yarasa mezai sayama Mamin shi, baitaba sayan wani abu na mata
ba, idanunshi ne suka sauka kan set na wani sarka da dan kunne da warwaro is 35k dauka yayi sai ga
wani red veil babban gaske hakanan Gwaggo kawai tafado ranshi baitaba really siyama family shi wani
abu ba cus baya aiki saidai su subashi kudi, kawai dauka yayi yaga 15k gyalen, yabiya kudinsu 150k, yasa
kowanne aka packing daban yafito yasa komi ajakan bayanshi yahau machine nashi sai yawuce shagon
dayake sayan turare ya saima kanshi da Hameed sai Ya Abdullahi da Ya Faisal saida yakashe 80k ashagon
yarage saura 20k kacal a kudin sannan yahau machine yabiya filling station yasai fuel na 5k a machine
sannan yawuce hospital din Ya Mustapa yayi parking yaciro wayanshi yayi dialing number sa wayan na
gab da katsewa ya daga yace “Hamadi!” Anatse cikeda girmamawa yace “ina waje Yaya” yana maganan
ya katse wayan Mustapa yasan Hamad bazai taba shigowa ba he’s even use to it dudda baicemai yazo ba
cus bazai taba iya cewa Yaya kazo ba but he knows yana jiransa awaje ne, akwai that respect in Hamad
sosai fitowa yayi ya sameshi yana tsaye awajen goye da jaka gawani paper bag a hannunsa na micserah
watches yakaraso wajen yace “hope everything is fine with you

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login