Showing 45001 words to 48000 words out of 59470 words

Chapter 16 - UWA KO UKUBA MShakur HAUSA NOVEL

M SHAKUR   

28 Mar 2025

3081

kara kunnenshi yana wani irin nishi ya bubbuga kofan
yace “Asma’uuuu!” Buga bucket din Asmeey tayi a kofan bayin da dan karfi saida bucket din ya tsage
sake manna kanshi sosai Hamad yayi jin kara adakin dasauri yace “Asma’u!” Da yar muryanta tace “Ya
Hamad!” Tasake buga kofan dawani Irin sauri Ya Hamad ya murza kofan but a kulle rudewa yayi yarasa
yazaiyi yashiga tattaba jikinshi baida anything kawai saiya shiga gudu a corridor fire extinguisher daya
gani anan corridor yawuce yadauka kawai yadawo yabugama handle din balle handle din yayi sannan
yahada karfin kan fire extinguisher yayi wani murde murde harsai da hannunshi yaji ciwo sannan ya iya
ya bude kofan yawani shiga cikin dakin yabi dakin da kallo babu kowa sai gyalen Asmeey daya gani ga
pant da aka barka akasa ga kwalba ga wine dahar yasoma bushewa gakuma jini akasa, gabansa yashiga

faduwa yashiga juye juye adakin yace “Asma’u” ahankali da galabaitacciyan murya tace “na’…..am”
dawani sauri yayi wajen bayin yakama handle din ya murza gabansa na faduwa sosai ya kafa kunnenshi
jikin kofan yace “Asma are you in there”? Gyadamai kai tayi tana kuka sosai mara sauti takasa motsi
cikeda tashin hankali Hamad tace “okay I’m coming” wucewa yayi gaban dakin inda ya yarda fire
extinguisher din yadawo yadaga murya ahankali yace “ki matsa daga around bangaren kofan” da duka
karfinshi ya buga kofan dayake banzan kofa katako ne a door kawai ya fashe kofan da sauri yasauke
hannunshi kasa ya leka ramin Asmeey yagani zaune agalabaice a bayin ta kankame jikinta, ga jini jini a
jikinta fuskanta lips dinta sun kumbura taci duka ga gaban riganta data hada ta rike da hannu biyu dan
ya barke, tsayawa yayi yana kallonta suka hada idanu wani kalan kuka tafashe da shi tana kallonshi,
dauke idanunshi yayi daga kanta Asmeey na kallonshi yashiga buga kofan yana banbarewa yana zufa
yana balballe katakon da hannu, tana ganin yanda he’s getting injury a tafin hannunshi but bai dena ba
sannan yasamu yashigo ta kofan forcefully kana gani kasan wood na wajen sun karcesa ajiki dawani irin
sauri yazo wajen sai kawai yaduka yana kallonta zufa na ketomai a goshi kaman yanda take kallonshi
cikin idanu, baimasan mezaice ba kawai he’s looking at her, kusan 1️⃣0secs suna kallon juna kafin cikin
raunanniyan murya mai taushi dake cike da tausayi that sounds very deep also with lot of emotions yace
“are you okay”? Sosai Asmeey ke kallonshi in the eyes tana kuka mara sauti kawai saita yunkuro da kyar
tanajan hannunta da baya motsi akasa and just hugged him da hannu daya tasa kanta a kirjinshi tana
wani irin kuka da duka dan karfin dayake tattare da ita.
Lumshe idanu Hamad yayi ya tsaya chak without touching her, zuciyanshi na radadi, yana kuna, yana zafi,
cikin wani yanayi da shi kanshi baisani ba ya fuzar da ijiyan zuciya mai bala’in zafi, ahankali and calmly
yace “it’s okay! It’s not your fault!” Ihu Asmeey tayi sosai akirjinshi maganan dayayi ta rikeshi gam da
hannunta mai lafiya, she’s feeling something da bata tabaji ba in her life game da Ya Hamad, bataso ta
sakeshi, she wants to stay like this with him, ahankali yana ahaka calmly yace “can you let me go”?
Gyadamai kai Asmeey tayi tasakeshi ahankali tana komawa baya hakan yasa gaban riganta dayake a
yage da boobs nata sukai flashing a eyes nashi dawani irin sauri yadan koma baya ya maida kanshi gefe
saikuma yatashi tsaye da sauri ya mike hannu yadauki towel daka kan rag abayin ya warware ya kare
fuskansa ajiki Asmeey nawani irin kallonshi, yaduko ahankali ya daura mata towel din a shoulder to
shoulder sannan ahankali yakama hannunta daya luradashi, fashewa da kuka tayi hakan yasa yakama
kafadunta zai dagata wani irin fashemai da kuka tayi yakalli fuskanta ganin she’s really in pains yasa
ahankali yadauketa chak a hannunshi wayanshi yahau ringing da hannu daya yasa yadauka baima tsaya
jiran maganan Hameed ba yace “I’ve seen her come to room 4️⃣1️⃣4️⃣” ya katse wayan yafara tafiya da ita
yasa sakata yabude yafito daga bayin da ita daidai Fawaz na shigowa dakin ga jini duk fuskanshi tareda
wasu lalatattun securities guda biyu marasa kiba kaman sanduna.

Dawani mahaukacin sauri Asmeey ta kankame Hamad tarushe da kuka Fawaz ya shigo dakin yana wani
kallonta yace “ohh ina mijinki kika dauki wayana kina kiran saurayinki to come to your rescue look at the
damage dayama sabon hotel dina” yanuna kofofin da Hamad yafasa wani irin kallon Hamad yamai
sannan yajuya ahankali yabude kofan bayin ya sauketa awajen yace “stay here”

zai janyo kofan tarike hannunshi da sauri saida yaji wani shock baisan sanda ya kalleta ba suka hada ido,
he felt something from her gaze, girgiza mata kai yayi yana mata wani gently look hakan yasa tasake shi
yajawo kofan but still ya tsaya around wajen cus yariga ya balla tsakiyan kofan, juyowa yayi yakalli Fawaz
dake kallonshi yashiga folding hannun riga Fawaz ya matsa gefe yace “kubashi kashi ku shemeshi na
dauki matata nayi gaba” tahowa sukayi kan Hamad sukayo kanshi cikin wani skills Hamad yadaki
kuyangin habar daya wlh saida hakoransa biyu suka zubo yayi baya daya yawani zube akasa, na biyun
yakawoma Hamad naushi ya kauce sannan yabiyoshi ta baya ya daki gefen cikinshi yafadi akan cylinder
fire extinguisher security yayi ihu Hamad azuciye ya kwashesu ya watsar kan Fawaz, dukansu ukun sukai
kasa Fawaz zai tashi Hamad yarikeshi yashakemai wuya ya bugashi da bango yace “how dare you touch
her!”? Dariya Fawaz yayi jini yana fita daga bakinshi yanama Hamad din wani kallon isgilanci yace
“wowww i see jealousy in your eyes haushi kaji narigaka”? Ihu Hamad yayi kaman mahaukaci yawani
juyar dashi ya zubar dashi akasa yafadi close to barkakken pant din Asmeey, Fawaz na wani nishi yakalli
Hamad dake zuwa kansa yace “look at how I ripe that pant from gabanta kyaaaaaa!” “I will kill you! I will
kill you!” Ashe Hamad mahaukaci ne yahau ihu da saida Asmeey ta leko ta ramin ta mugun tsorata ganin
yanda Ya Hamadi yashiga dukan Fawaz ta ko’ina yana sassaukemai punches a fuska Hameed dasu Baba
suka shigo dakin sukai kan Hamad ganin yahaukace Abba yana “Hamad Hamad zaka kasheshi” yana
rikeshi ina Hamad yaki barinsa dukansa yake da kyar Baba da Abba suka dauke shi Hamad yadauke pant
din Asmeey batare da kowa yama lurada pant dinba yasa a aljihun wandon a aljihunsa Abba na rikeshi ya
bala’in tsorata baitaba ganin Hamad hakaba sai kallon Fawaz yake jijiyoyin jikinshi duk sun fito da
wuyanshi yace “zan kashesa, i will kill him, i will kill him Abba” Abba da kyar yafito dashi wajen corridor
yace “Hamad, Hamad kalleni” ina kallon dakin Hamad yake still yana furta saiya kashea kawai rungume
sa Abba yayi ganin kaman baimasan meyake ba, hawaye masu mugun zafi suka fito daga idanunshi Abba
yace “kace La’ilaha Illalla Muhammadu Rasullullah” da kyar Hamad yace “La’ilaha Illlalah Muhammadu
Rasulullah, Hasbunallahu wa nieemal Wakeel” yadan sami natsuwa Abba zai cirosa daga jikinsa da sauri
yaciro kansa yajuya ma Abba baya yana goge fuskansa yace “I am fine Abba ka koma ciki” kallonsa Abba
yayi sosai sannan yawuce yakoma dakin shikuma Hamad yawuce kawai yafita.
💫UWA KO UKUBA?💫

M SHAKUR

EPISODE 1️⃣💫5💫

**
Akwai mutane da more police da motoccinsu akasa, babu wanda ya kalla yawuce yafita kawai yayi gate
yana fita yatare abin hawa kawai yabar wajen idanunshi sunyi jawur.

Kama Fawaz police sukayi suka samai ankwa, Hameed yakaimai nushi aciki, Baba yabude bayi ahankali
saiyawani irin tsayuwan ban tausayi yahade hannayensa biyu akan cikinsa yana kallon Asmeey Abba
yazo wajen yana kiran sunayen Allah yaduka yakama Asmeey Munir da idanunshi sukai ja yazo zai kama
hannunta ihu tayi na azaba, Baba yaduka dasauri yakalli hannun ahankali yace “ta karye” fashewa da
kuka Munir yayi kawai ya rungume Asmeey, Hameed yaduka yadauki gyalenta da dankwalinta dake
wajen yazo wajen ahankali ya warware yasake rufa mata ya lullube harda fuskanta murya chan kasa
yace “I will carry her kira Ya Mustapa Abba” chak yadaga Asmeey data kasa kallonshi yawuce yafita da
ita Munir yabisu abaya da Kawu, Motan su Baba Hameed yasaka ta yana kallon fuskanta yanda take kuka
har lokacin ta bala’in galabaita yadan koma baya ahankali, Baba ya shiga bayan Kawu yashiga gaban
motan Abba dake bin wajen da kallo yakalli Hameed yace “ina Hamad? Banganshi ba call him” wayansa
Hameed yaciro yakira Hamad but baidagaba ahankali yace “Abba let’s go I’m sure yatafiyansa ne kasan
shi” dan jimm Abba yayi sannan yashiga gaban motan kusa da Kawu Hameed yawuce yashiga mota shida
Munir suka tada motan akabar wajen.
Sosai Baba ya rungume Asmeey baya iya magana but kana ganin fuskanshi kasan kukan zuci yake sosai
ahaka sukakai private clinic dinsu, suna zuwa aka karbeta akai ciki da ita Baba yabi doctors dinsu akace
ya dakata tukunna dawowa yayi sai kawai yasami waje yadaura hannuwansa aka duka biyun Munir
kuma yana tsaye sabida kawai dauriya ne da cijewa yasa baiyi ta kurma ihu yana kuka ba, zama Abba
yayi kusada shi hakama Kawu duk suka dafashi kanshi ahaka ayanda yake cikin wani irin murya mai rauni
yace “Yaya mezan gayama Allah? Mezan cema Allah? Y’ay’ayan mu amana ne garemu, nakasa killace
amanan da Allah yabani dubi abinda wani d’a namiji yama y’ata Yaya” Yayi maganan yana dago kansa
idanun Baba kaman zai fashe da kuka ahankali Hameed yakalli Munir dake goge fuskanshi yamai alama
yazo suka wuce sukabar wajen, murya chan kasa yace “ko bai mata fyade ba wanda nake gani da kyar
ma in baiyiba yariga yabatama diyata rayuwa ya barka suturan danama diyata ya yaye lullubin dana
mata domin killace al’auranta” Baba yawani fuzar da iska, yana girgiza kai gwanin ban tausayi yace “Yaya
Salima tasan waye yaron nan, wannan yaron yayi suna anan garin Bauchi, ansan yan gidan ko diyata Aya
lokacin saida nahanata zuwa daman sabida mahaifiyarta take kawance da yar gidan Maryam kowa ya
sansu m…..mesa Salima zata aikamin diya tareda su? Mesa Salima ta tsani y’ata yar cikinta yarda muka
haifa tare ta sunna da soyayya”?Murya chan kasa yace “Yaya kunsani banyi makaranta ba da kyar na
lallaba nagama sakandire shima bazanyi karyaba bawai nasan wani abu bane hakan yasa duk wani
harkan karatu makarantan boko dai kap a hannun Salima yake duka yaran gidan ita ke sakasu a
makaranta tayi komi ni nawa tafadamin adaddin kudin da ake bukata na bata tabiya shikenan bani cikin
lamarim ta daura buri kan Asma’u saita zama lawyer irinta saita gajeta daganan duk tsanan yafara”Yayi
shiru chan yace “dasafe nake fita naje kasuwa sai mangariba nake dawowa bana sanin meke faruwa

amman Yaya namaka alkawari duk wanda nagani agabana ina shiga na dauki mataki, Salima tacika fushi
da fada da sauri hannu masifaffiya ce duk nai hakuri sabida mun zama daya shekarunmu talatin da aure,
akan wani dalili zata hada yarinyar nan da mutanen nan suje gidansu?Meyake faruwa ban sani ba”
daidai lokacin Ya Mustapa yashigo asibitin yazo wajen shima Dr su Baba na fitowa duk sukai wajenshi
Baba yanuna Mustapa yace “ga dana shima Dr ne dan Allah yimai bayanin komi” gyadamai kai yayi Dr
yawuce tareda Ya Mustapa suka shiga dakin su Baba duk suna tsaye su Hameed ma sun fito, kusan
1️⃣5min sukayi sannan Ya Mustapa yazo wajensu Baba, ahankali yace “yaron baici nasaran bata mata
rayuwan ta ba” dasauri Abba da Baba da Kawu duk sukace Alhamdulillah, ahankali Mustapa yace “but ya
karya mata hannu sannan akwai lot of ciwo ajikinta signs na she was physically abuse ya daddaketa
gaskiya” duk kallon Ya Mustapa suke ahankali yace “an daure mata hannun nace dazaran tagama shan
drip a sallameta sabida muje gida zan cigaba da mata treatment agida” atare kowa yace “Alhamdulillah”
dan shiru Ya Mustapa yayi saikuma ya matso dab da Baba hakan yasa Baba yace “yi maganar ka Doctor”
dan ijiyan zuciya yayi yace “Baba ba hurumina bane ince this, nasan awasu wajen dan mahaifiya na
dukan yaransu it’s fine is okay, Baba banda dukan da yaron nan yamata yau akwai ciwuka da tabo da
dama ajikin Asmeey abin yayi yawa” yadanyi shiru yanajin nauyin maganan dazaiyi but hakan yasa yace
“Baba please ka duba lamarin nan kayi binciken abinda ke faruwa a rayuwan Asmeey da wanda bata
fadamaka kar watarana mu wayi gari babu Asmeey cus ciwukan jikinta sunyi yawa kaje dakin kagani da
kanka, she’s a girl what will her future husband think of us? Haba ciwukan yayi yawa” Ijiyan zuciya Baba
ya sauke ahankali yashiga tafiya wlh he’s feeling so down and unhappy dakin yabude ya shiga, rigan
asibiti yasani cus an ciremata riganta daya yaga hannayenta yafara kallo duk tabon ciwo baijin yataba
ganin Asmeey da riga mai karamin hannu ba ashe saisa takesawa ga gefen wuyanta ma duk ciwo da
kanshi yadaga riganta yana kallon bayan jikinshi na mutuwa da sanyi yadawo tagaba yana dubawa yaga
cikinta haka ya lumshe idanu sai kawai ya kifa kansa jikin gadon yakai 10min ahaka sannan yadago kansa
yana kallon fuskan yarinyar sannan yatashi yafita yasami waje ya zauna Ya Mustapa yadawo dawani tshirt sabiwa yabama nurse tasa mata duk suka zauna, Ya Mustapa yayi clearing bill din. Within 30min
ruwan yakare Nurse ta tayata sa rigan bata iya amfani da hannunta daya sannan aka sata a wheelchair
nurse tafito da ita Asmeey takasa kallon any of them sabida kunya da jin nauyi, She was even wishing
inama tamutu agadon asibitin ganin yanda takeyi yasa babu wani wanda yacemata wani abu banda
Munir daya kasa daurewa yayi wajen bai damu da duk mutanen wajen ba dukawa yayi agabanta hakan
yasa nurse din ta tsaya shiru yayi yana kallon fuskanta duk ja da bruises na ciwo gefen lips dinta har
bandage an saka ga hannunta adaure an lullubeta da bargo dakuma gyalenta taki kallon Munir din tayi
wani iriiii rawa bakinshi yakeyi ahankali yace “As…..s….m….Asmeeey” gangarowa hawaye sukayi daga
idanunta hakan yasa Baba yace “tashi muje gida Munir” dagasa Baba yayi yamike da kyar yana kallon
Asmeey da just around two dazu na rana she was fine but yanzu dukta chanza, sukai mota da ita Baba da
kanshi yadagata da Munir tashiga mota ya zaunar da ita Munir yashiga yazauna kusa da ita kawai saiya
kama hannunta me lafiya yarike Asmeey tai shiru she looks lifeless, Hameed yaja motan suka baro
asibitin shima bini bini yana kallonta ta madubin gaba zuciyanshi namai zafi.
Wuraren 5:30 suka isa gida yanda sukabar matan a tsakar gida haka suka shigo gidan, daga Gwaggo,
Mamie, Ammi, Ya Aya, matan su Mustapa da yaran dukansu şuna waje banda Mom, motocinsu na
shigowa duk suka mike Aya tafara tafiya Gwaggo da sauran duk suka biya abaya.

Baba na bude kofan yafito Aya ta tsaya turus ganin kanwarta ta chanza gabaki daya kana ganinta kasan
taci duka hannuwanta biyu tadaura abaki takasa motsi Gwaggo tai wajen hankalinta atashe. “Abubukar
meya saman mini jiki? Muhammadu Sani meya sami Asama? Eh ku sanar dani” Mamie da Ammi suka
tsaya duka babu wanda ya iya motsi da kyar Abba yace “yanzu ba lokacin magana bane bari mu kaita
ciki” ahaukace Gwaggo tace “nace ku gayamin abinda akama jikata tadawo haka? Lafiya kalau tabar
gidan nan me aka mata?” Ijiyan zuciya Baba yasauke ahankali yace “Gwaggo bata mata rayuwa yaron
yaso yayi amman cikin ikon irin na ubangiji bai cimma burinsa ba yanzu haka yana hannun yan sanda”
“Fawaz ka mikama ga yan sanda”? Dukansu sukaji magannan Mom wani irin kankame Munir Asmeey
tayi jikinta yashiga kyarma sabida muryan Mom dataji Hameed dake gaban motan zaune yabita da kallo
ta mirror hakama Munir dukansu speechless, dukansu juyawa sukayi suka kalli Mom dataci gayu cikin
abaya tafito ga wannan farin glasses din a idanunta tarike handbag idanunta kur kan Baba tace “client
dina ka mikama yan sanda Baban Aya”? Baba na kallonta yace “har kotu saina shiga dashi I will get
justice for y’ata can you see abinda yama Asmeey look at your daughter Salima! Look at her” yanuna
Asmeey dake cikin mota tarike Munir gam ta manna fuskanta awuyan Munir hannayenta na rawa, Baba
da ranshi ke tafarfasa yana ihu yace “bakiji komi azuciyanki ba? Waye baisan Fawaz dan gidan Taurari
agarin nan ba? Yaro Mara tarbiya da da’a zaki aikamin diya wani waje dashi and ko ajikinki infact fita ma
zakiyi daya lalata mata rayuwa fa”? Mom na kallonshi babu ko dar cikeda girman kai da isa tace “ita taso
ai! Kaga ba wannan bane agabana I need to get my client out of cell” tawuce, azuciye Baba yace
“Salima” tsayawa chak Mom tayi batare data juyoba, Baba yace “wlh kika kuskura kikai bailing yaron nan
abakin aurenki!Dasauri kowa ya kalli Baba, Abba zaiyi magana rai abace Baba yace “wlh Yaya bazan
saurareka ba ta kuskura ta fiddo yaron nan abakin aurenta saki daya wlh! Bantaba ganin mahaifiya mara
kaunar yarta irin Salima ba, Yaya kasan yanda nakejin ciwo wani dan iska yama y’ata wannan abu?
Kamata yayi duk ciwon danakeji ita taji sama da nawa tunda itane mahaifiyarta amman kaga ciro yaron
zatayi wai toh wlh wlh taje abakin aurenta” shiru Mom tayi na kusan one good minute saita daga
kafanta zatai tafiya dasauri Aya tace “Mommm” juyowa Mom tayi ta kalleta dawasu kalan idanu tace
“wallahi kikace tak Aya sai ranki yayi masifan baci yau!” Tana maganan tajuya tawuce wajen jeep dinta
ran Baba nawani irin suya yanda Mom ta dizgasa agaban duka yaransa da yan uwansa da masu aikinsa
yan gadi na gate ta kunna mota taja aka bude mata gate tafice, da kyar Abba ganin Baba bazai iya
magana ba yace “Aya dake dasu Ammi da Mamie ku taimaka mata tayi wanka” yakalli Ya Mustapa
dashima yayi mutuwan tsaye yace “kabasu maganin dazata sha doctor” saiya kama hannun Baba
yawuce dashi flat dinsa zuwa dakinsa asama Kawu yabisu.
Gwaggo tace “ni yar gidansu Tasiu wace kalan annoba Muhammadu Sani ya auro, Hameed!” Takira
Hameed daya fito daga mota tana sallallami tace “kodai sato yar nan tayi ba tata bace lokacin cikinta
cikin roba take sawa? Ku kunduba”? Wucewa abinsa Hameed yayi boys quarters ganin duka mata ana
flat dinsu dan nan aka wuce da Asmeey, Ya Abdullahi dasu Faisal ma duk suka bisa abaya.

Mom babban Barrister ce da ansan da zamanta a Bauchi, and police station waje ne da take zuwa every
now and then saidai idan any of her client is not in trouble, and she made good friends and connections
da alot of people a police it takes her just one call to wani babban dan sanda tagano wani police station

aka kai Fawaz tana shiga headquarter nan da nan tai magana tayi some paper works tawuce office na
babban su suna magana sai gashi an shigo da Fawaz daya daku sosai hannun Hamad, Mom ta tsayar da
maganan tabishi da kallo kaman yanda Fawaz din ya kalleta yadauke kai ya zauna Mom tajaye kanta da
kyar ta kalli ISP tace “as I was saying ISP Kamal is just misunderstanding yarinyar y’ata ce and har gida
yazo ya dauketa nina bada izini baban baisani bane, please I want the case closed and gone nobody
need to know no trace no record” shafa kansa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login