Showing 30001 words to 33000 words out of 59470 words

Chapter 11 - UWA KO UKUBA MShakur HAUSA NOVEL

M SHAKUR   

28 Mar 2025

3088

din a gefen cikinta daidai kan idon Baba dasu Mama da kowa
hadda matan su Ya Mustapa, Mom tajuya fuuuu tawuce stairs Baba kawai yayi mutuwan tsaye yakasa
magana ganin yanda Mom ta buga yarsa da center table mugun buguwa ma, Gwaggo ganin yanda yarta
sandarewa tayi ta kankame awajen cike da mamaki kowa na falon was freeze har ita Mama yar fadan
Mom,
Mamie ce ta iya motsi cikin kowa takarasa tsakiyan dakin ta duka tasa hannu ta dago Asmeey data kasa
motsi idanunta har lokacin duhu duhun mari suke mata, ahankali Mamie tace “Ma’u sannu tashi, kinji
ciwo”? Jikinta na wani irin kyarma totally destabilize ga lallen da aka mata ya dame duka har center
table yabaci shima da lallin da sauri ta girgizama Mamie kai har lokacin bata gani da kyau ga kunya
yagama kasheta ga jikinta rawa kawai yake, tajuyo tana kokarin neman Mom dabata gani a falon ba
kowa na kallonta, ahankali Mamie tace “Doctor zoka dubata” dasauri Asmeey ta kalli Mamie jikinta na
rawa yana kyarma amman takakalo murmushi muryanta ciki ciki yayi rauni tace “babu abinda kemin
ciwo ai ban buge ba” dasauri Yusra tace “duk Ya Ramla taja Mom ta daketa and she lied cus Ya Hamad ai

bata cemiki wawuya ba kene kika kirata wawiya because of ice cream” ran Ammi taji yabaci tashigo
tsakar falon tace “are you the reason aka daketa haka? Ramla do you even love your sister? Kalli
kumatunta, kalli lallinta, kalli yanda jikinta ke bari, bakida imani ne Ramla ke ba mai marba Asmeey ice
cream bane bakene babba ba? Wace kalan muguwa ce ke”? Tadaga hannu zata daketa Abba yace
“dakata! Karki daketa!Yarane ba’a raba yara da irin kananun fada haka musamman wajen rabo amata
afuwa, Husna” da sauri Asmeey ta kalli Abba idanunta sunyi firfirr ba hawaye tace “uhmmm na’am
Abba” magana Abba zaiyi but sai yayi shiruuu ganin yanayin yarinyar yace “kaita ta wanke hannayenta
da kafafun Maman Doctor, Nana ku gyara inda yabaci da lallen” yunkurin dagata Mamie tayi tace “tashi
muje” Asmeey takasa tashi bakinta zaiyi magana sai kawai ta kasa sai hawaye yataru a idanunta ta juyar
da fuskanta irin na neman inda zata saka kanta dinnan Mamie ahankali tace “zo Asmeey come” Mamie
zata kamata Asmeey zata fita daga jikinta takasa da sauri ta shige jikin Mamie duk yanda takeso ta daure
ta danne takasa tafashe da kuka sosai jikin Mamie mara kara sai shesheka da jikinta dake motsi irin
kukan nan mai taba zuciya tana huci mai bala’in zafi a jikin Mamie, Baba ya yunkura zai wuce sama Abba
yarikemai hannu alamun no dan yaga yanda Baba ya zuciya kuma babu kyau hukunci acikin fushi hakan
yasa ya tsaya, Munir yawuce ahankali wajen ya tsugunna kusa da Mamie da Asmeey ke jikinta yadaga
hannunsa yadaura saman bayan Asmeey yayi shiruu idanunsa sunyi jazur, ahankali Hamad yajuya yafice
daga falon yarufo kofa, Gwaggo da sai alokacin tadawo daidai tace “toh wlh wlh tunda dai abinda akema
yarnan agidan nan kenan zan tattarata natafi da ita, kuma dagayau tabar shashin nan, idan uwarta ta isa
tazo inda nake ta tabata, bantaba ganin muguwa Uwa irin mahaifiyarta ba, wlh kekuma sarai ai kinsan
halin uwarta koda tamiki laifi ai sai ki rufamata asiri ba yar uwarki bace? Kuma ai kina sane ai haushi
takeji ansata tayi lalli alhalin tahana ba dole ta dirketa ba, ga lallin nan tasa yabaci hankalinta ya kwanta,
Mara Imani da idanunta kaman na mutan da, saisa Allah yahanata tsayi kaman in kifeta da kwando,
muguwa dunkulen magi kawia ai gajeren mutum akwai bakin hali” Gwaggo na fadin haka ta karaso
takama hannun Asmeey dake jikin Mamie tace “tashi muje” fitoda ita daga jikinta Mamie tayi tace “tashi
kuje Asmeey” idanunta akasa taki kallon kowa ta kasa tashi, rai abace Baba yace “badake ake magana ba
tashi” ahankali ta tashi da dauriya da kyar, Gwaggo tariketa tajawota aka mammatsa suka taho Ya
Mustapa yabi yanda ke tafiya da kallo dakuma gefen cikinta suka fice sai kawai Mamie itama tabisu
abaya haka sauran matayen, Mama kuma tawuce sama abinta wajen Mom danta bata hakuri Ya
Mustapa yajuya yafito kowa ma yafito.
Flat din su Mamie Gwaggo tashiga da ita har lokacin fada take sosai dakin dake kasa tawuce dan ita duk
dakunan kasa nakowani flat nata ne cus duk inda taga dama take kwana tabude tashiga tace “wuce kije
ki wanke hannunki” wucewa tayi ahankali ta shiga bayin ta maida kofan tarufe takarasa wajen wash
hand basin tadaga hannuwanta da akama lalle duk sun gwalje both baki da jan tai shiru sai kawai
hawaye suka sauko daga idanunta tabude tap din ta wanke hannayen tasss and lallin yayi mata bala’in
kyau inda ta gwalje ne yayi wani iri, lallin yayi dan ja, Kuka takeso tayi but saita hana kanta gabanta har
lokacin faduwa yake, Mom sai fadomata take arai bazata taba kwana anan ba sabida kar ran Mom
yabaci zata bari Gwaggo tai bacci saita tafi wanke, kafafunta tayi suma tass ta dauro alwala dan batai
salla ba ta kalli kumatunta da sunyi jaa sosai abunka da fara ko yaya aka mareta kalan fatar fuskanta
saiya chanza towel na bayin tasa ta tsane fuskanta sannan tabude bayin tafito Mamie tagani tsaye kusa
da bayin tace “alwala kikayi?” Dasauri ta gyadama Mamie kai tana kakalo murmushi tace “eh banyi salla
ba shizanyi yanzu” Mamie na kallonta tace “babu abinda ke miki ciwo?” Gyadama Mamie kai tayi

Gwaggo tace “wannan ai ko zata mutu bazata fadi ba uwarsu yanda kikasan ta tsafesu ni zoki salla muje
falo muci abincin dare yunwa nakeji”dan takowa Mamie tayi dab da ita gently takai hannunta ta daura
saman kumatunta dayayi ja tana kallon idanunta, wlh tunda Mom ta mareta koda yanzu tai alwala tasa
ruwa a fuskanta bataji sanyin dataji kaman sanyin dataji yanzu da Mamie ta daura hannunta kan
kuncinta ba sai jikinta yayi sanyi sai taji jikinta ta ciki yadaina radadi cikin murya mai sanyi dakuma so
Mamie tace “ya isa! Calm down zanma Mamanki magana dakaina kinji, next time koma menene karkima
nagaba dake rashin kunya, kinfi kowa sanin mahaifiyarki macece mai bama yaranta tarbiya yanda
yakamata bata yarda danta ko yarta ya taka na gabansa ba, next time respect Ramla kinji no matter
what don’t talk back at her just like yanda Mom bazata bar su Yusra ko su Nana sumiki rashin kunya ba
kema bazataso kima na gabanki ba, but ya isa okay” gyadama Mamie kai tayi idanunta na cicciko da
hawaye, ahankali Mamie takai hannunta gefen cikinta tace “wajen namiki ciwo nasa Doctor yakawo miki
magani?”Girgizamata kai tayi tace “a’a bayayi” Mamie tace “to yi salla abinki” Gwaggo taja tsaki tace
“wlh takara taba yarnan tagani yo ita ubanwa naga tana girmamawa? Girmamani take? Mata sai girman
kai jitake tafi kowa sabida tayi boko, bokon da agidan d’ana tayi kuma da kudinsa banza kai shashasha
muzuba ni da ita zan nuna mata matsayinta”
Mamie dai tawuce tafita Asmeey ta dauki hijabin datagani kan gadon wajen tasaka tai salla magrib da
isha’i ma da akayi Gwaggo da tunda tafara salla take kallonta tace “kiwa Allah Asama kitashi kicire
hijabin nan muje muci abinci cikina sai kuka yake” tashi tayi ta cire hijabin tawarware mayafinta tasa aka
yadan sauko mata shoulder Gwaggo tai gaba ta biyota abaya su Ya Mustapa duk suna falon Ball ma suke
kallo a tv falon da Ya Abdallah da Ya Faisal da matarsa ke basa abinci, shi kadaine be ciba sai Ya Hameed
shima.

Hameed yakalli Asmeey fuskanshi ahade yace “kawomin ruwa” hararansa Gwaggo tayi tace “bazata
kawoba bakaga kalan dukan data gamaci ba” tabe baki yayi yace “inda sabo ai tasaba yanzu” wani
mugun kallo yayyinsa sukamai, yadanyi murmushi, haushin Mom yakeji sosai aransa, he hates the
woman wlh sabida yanda take da duka, da girman kai da fadinrai, haka su Ayah suka wahala a hannunta
shi besan me Baba yagani ajikinta take zaman aure da irin matar nan ba, wucewa fridge Asmeey tayi a
kitchen tana tafiya ahankali tasa ruwa a tray da cup tafito dashi tazo falon kanta akasa tazo gabanshi ta
ijiye. “Gashi Yaya” zata juya Mustapa yace “zonan” faduwa gabanta yayi ta gyadamai kai tazo gabanshi
babu wasa kan fuskanshi like a big brother yasa hannu a aljihunshi yaciro wayanshi ya kunna flash
yanuna mata gefenshi yace “sit” zama tayi ahankali Gwaggo tace “yauwa dubamin ita” hannunshi
yadaura saman kanta ya juyar da fuskanta yana haska kumatunta Mamie ma tafito ta tsaya kansu
sannan yasauke wayan yace “inda kika buge namiki ciwo?” Girgizamai kai tayi tace “a’a Yaya” hannunshi
yakai ahankali yataba gefen cikin ta saman riga da kyau jin wajen is not hard yadan sauke ijiyan zuciya
yana kallon yanda take runtse idanu she need drugs, hannunshi yacire dan murmushi yamata tareda
shafa kanta yayi cikeda kauna ta dan uwa yace “it’s okay okay don’t fight with ur sister again, i will buy
another ice cream for you gobe” Abdallah yace “wani flavor kikeso nima zan siya miki” Faisal yace “akan
strawberry flavor tayi fada nima zan siyamata gobe” Hameed yadan harareta yace “sweetthooth kawai i

will also buy for you” murmushi kadan tayi feeling so loved, ahankali tace “nagode Yaya” Mamie tayi
murmushi tana kallonta Gwaggo tace “sauko muci abincin” Ya Mustapa yace “jekici abinci zan fita
nakawo miki drugs” tashi tayi zuwa kujeran da Gwaggo take ta zauna suka faraci tanadan jin nauyin
yayyinta dan ba koda yaushe take ganinsu ba, but kuma tana sonsu sosai sunada kirki sosai and suna son
kanninsu suma.

Parking yayi ahankali tareda kashe motan ya kalli paper bag dake gefen sa kan kujera yayi jimmmm sai
kawai yatashi yakai hannu yadauka tareda bude kofan yafito yarufe yafara tafiya zuwa flat nasu ko
kadan baisan yayyinshi kowa na falon ba hakan yasa kai tsaye yabude kofan yashigo tsayawa yayi ganin
kowa harda Mamie duk a falon ga Gwaggo da Asmeey datai tsuri gefen Gwaggo ana kallon ball Baba ne
kawai baya falon, duk juyowa akayi ana kallonsa banda Asmeey da tana ganin shine ya shigo ta maida
fuskanta tv, ganin yanda kowa kallonshi yake yasa da sauri yaboye abun hannunshi abaya yajuya dasauri
zai fita daga falon Mamie tace “Hamadi!” Chak ya tsaya hakanan gaban Asmeey yafadi batare data
dauke kanta daga tv ba, Mamie tace “ina zaka daga shigowan ka? Ina kaje ban ganka ba tun dazu?
Come” dan jimm yayi sai kawai yasa hannu ya maida kofan yarufe yahade rai kanshi akasa yafara takowa
zuwa wajen Mamie Mamie tabi paper bag din da kallo tace “meka sayo?”Agefenta ya ijiye paper bag din
da sauri batare dayace komiba kawai yajuya kowa na falon yabishi da kallo yawuce stairs, Gwaggo tace
“mara mutunci meya kawo miki banda ni? Koni ba mutum bace” Mamie tasa hannu tabude paper bag
din fari ba logo ajiki kawai saita dago kai takallo sama harya shige dakinsu sai kawai tasa hannu taciro ice
cream a babban cup strawberry da akai breaking cone da chocolate da so many orishirishi ciki ga cokali
takalli Asmeey da idanunta ke tv tace “Ma’u gashi yayinki yasayo miki ice cream” kowa na falon saida
mamaki ya kashesa barin ma Hameed daya wani zaro idanu irin na gulman nan, Asmeey ta kalli Mamie
saita kasa tashi ta amsa Gwaggo tace “tashi ki amsa Hamadi ya siyamiki yaga kinci bakar duka uwa jaka”
tashi tayi zuwa wajen Mamie akunyace tasa hannu takarba ice cream din Mamie tace “kije daki kisha
abinki” batai musu ba tawuce dakin Gwaggo tana kallon ice cream din daya dadada mata rai, dan satan
kallon sama tayi kafin tabude dakin Gwaggo ta shige.
Gwaggo tace “Doctor kaika aikashi ya sayo abin ne?” Girgizamata kai Ya Mustapa yayi ya mike tace “bari
na sayo mata magani” su Abdallah suma sukama Mamie sallama suka fice flat nasu.
Hakan yasa dasauri Hameed yatashi yazo wajen Mamie cikin whispering yace “Mamie Hamadi buying ice
cream for a gurl this is unbelievable” hararanshi Mamie tayi tace “munafincinka yakesa Hamad baya
shiga harkan kowa cus u give meaning to anything me dan ya sayama Asmeey ice cream? Ba agabansa
taci duka ba yanada tausayi” Hameed yana wani murmushi yace “Mamie kodai kodai he he….”
Tallabemai keya Mamie tayi tace “kaga saida safe” ta tashi tana murmushi tayi stairs abinta ta shige
dakinta shima yatashi yace “bari naje na sami dan iskan nan” dakinsu Hameed yabude Hamad baya ciki it
seems yana bayi kayan jikinshi yarage dagashi sai singlet da boxer yazo gaban bathroom din ya jingina da
bango yayi folding hands nashi yana jiran yafito, kusan 5min yayi awajen Hamad ya bude kofa yayi
wanka yana sanye dawani ash color joggers da white t-shirt na polo mai kyau ga kayan daya cire abayi a
hannunshi, hada ido sukayi da Hameed dakemai wani kalan kallo da sauri ya dauke kai ya fuske yafito zai
wuce karaf Hameed yasha gabansa yace “wat is that you did earlier?” Chak ya tsaya batare daya kalleshi

ba yace “I don’t know wat u are talking about” dariya ke neman kufcema Hameed yace “karya kake
munafuki why did u buy ice cream for Asmeey?” Tambayan kaman zaisa ya nutse akasa sai kawai yama
juyama Hameed baya kaman zai kara komawa bayin Hameed yarikeshi ya fashe da dariya cikeda iskanci
yace “so you are in love” watsar da kayan hannunshi yayi akasa yace “stop Hameed leave me alone”
tsabagen son yakureshi Hameed yace “to kaida bama kasan ya ake sex ba how would you be intima……”
wani kalan tura Hameed yayi da karfi kaman zaki yawuce da sauri ya sunkuci laptop dinshi zai fice daga
dakin Hameed yadaga murya yace “google wat is sex and start learning tun yanzu kafin asami matsala
bayan aure” da sauri Hamad yafita yana bugo kofan me Hameed zaiyi inba dariya ba dariya haryana
faduwa gaban bayi is not like Hamad baisan sex ba but he can swear baisan yaya akeba wlh kuwa kunya
irin na Hamad daban ne aduniya, he hates maganan banza, he hates looking at abubuwan banza ko
iskanci ko tsiraici ko maganan kiss baiso ayi a inda yake yanzu sabida dan maganan nan zai iya harsu
koma Kano yadena zama dakin nan kenan yadinga avoiding nashi, ba lallai yanason Asmeey ba bama ya
tunanin tsokanane kawai yasan tausayi yarinyar tabashi yasayo mata ice cream kaman yanda suma
sukace zasu saya mata, da kyar yagama dariyan yaduka ya kwashe kayansa yaje ya ijiye masa yafada
gado abinsa sai bacci.
Babu kowa a falo hakan yasa yawuce dinning kawai yama ijiye laptop dinshi yawuce kitchen yadauko
ruwa yaja kujera ya zauna yabude ruwan yasha yana sauke ijiyan zuciya sannan yafara aiki.
Almost 30min shi kadai afalon yana aiki aka bude kofan aka shigo hakan yada yadago kanshi karaf suka
hada ido da Ramla wacce tana ganinshi taci burki gabanta na faduwa hakanan cikin duka yayyinsu ba ita
kadaiba all of them sunfi shakkan Ya Hamadi cus babu wacce yake wasa da ita babu wacce ta taba ganin
hakorinsa baitaba mata magana ba, gashi yanada kwarjini wani kallo yamata dayasa batasan sanda ta
sauke kanta kasa ba tace “uhnnn dama…..daman wajen Asmeey nazo” bayabo ba fallasa yace “get out!”
Har tsakiyan kanta taji muryanshi kusan tunda tasan Ya Hamad this is the first maganan dayake mata
wlh kuwa gyadamai kai tayi tace “tom saida safe Yaya” tajuya tabude kofa tafice.

Wuraren 11:30 Asmeey tafarajin munsharin Gwaggo sosai ahankali ta lallaba ta sauka daga gadon batare
datai making sound ba tana rike da veil nata a hannu tazo wajen kofa kaman barauniya tabude kofan
ahankali tafito tana maida kofan tarufe tajuya da sauri tana tafiya ahankali ahankali sadaf sadaf tana
warware gyalen tana kokarin yafawa danta rufe gashinta tai wajen kofa daidai takai kofa tasa hannu zata
bude kofan taji saukan zazzakan murya that is so calming and soothing a kunnuwanta. “Where do you
think you’re going”? Amahaukacin firgice tajuyo karaf suka hada idanu da Ya Hamadi dake zaune a
dinning ga laptop gabanshi da bottle water a gefe ya tsareta da crazy eyes nashi kawai saitaji ta dimauce
jikinta yayi wani iri, she couldn’t stand his gaze at all tama kasa magana gabanta sai faduwa yake sai
kawai tajuyo ta wuce hakanan saita sake samun kanta da so ta kalleshi dago idanunta tayi kaman mara
gaskiya ta kallonshi hada idanu sukayi mugun faduwa gabanta yayi tabude kofan dakin Gwaggo da sauri
ta shiga daidai Ya Mustapa na shigowa da ledan magani a hannunshi dinning ya wuce ya zauna yana
kwalama Asmeey kira. “Asma’u Asma’u” daga ciki Asmeey tace “na’am” fitowa tayi ganin Ya Mustapa a
dinning a yasa taje wajen ta tsaya gefensa batare data yarda ta kalli inda Ya Hamadi yake ba, magunguna
guda biyu yaciro yace “2️⃣ 2️⃣ zakisha, duba fridge idan akwai ice kisa a kumatunki karya kumbura idan babu

kisa ruwa a leda yayi kankara zuwa anjima” gyadamai kai tayi tawuce kitchen shikuma yatashi yakalli
Hamad dake aiki yace “good night” gyadamai kai yayi Asmeey tafito da bottle water ganin babu Ya
Mustapa duk sai taji wani iri magungunan tadauka daga dinning tawuce dakin Gwaggo da sauri.

WAYYO ASMEEY💫💫
AFADI GASKIYA MAMIE HAMADI YA SIYAMA ICE CREAM KO ASMEEY??
[03/01, 21:55] +234 806 229 2100: 💫UWA KO UKUBA?💫

✍💫M SHAKUR

GAYAMIN ME KIKEFI SO GAME DA THIS BOOK +2347012181461

EPISODE 1️⃣💫1️⃣💫

Tana shiga cikin dakin Gwaggo ta maida kofa tarufe ta jingina da kofan hannayenta biyun dake rike da
bottle water da magani duka ta daura kan kirjinta dake bugawa nonstop, why is her heart racing sabida
Ya Hamad? Saikace yauta fara ganinshi toh kodan bai taba mata magana bane? Anytime sukazo salla ma
hardly take ganinshi dan baya shiga mutane, wani zubin daga ranan dazasu zo sai rannan salla take kara
ganinshi, takai almost 2min tsaya awajen sannan tawuce ta zauna bakin gadon tabude maganin tabude
ruwa tasha, at first batason magani but dukan Mom yasa ta koyama kanta shan magani da kanta, cus
drawer su na daki Baba na ijiye musu basic magunguna haka irinsu paracetamol, Ibuprofen maganin
ciwon mara da first aid kit she learn to take care of kanta, kallon gadon tayi yanda Gwaggo ke maka
uban minshari abinta ta rakube ta kwanta gefe dudda ga uban space tai shiru gabanta sai faduwa yake
she wanted to go back to side nasu hakan zaisa laifinta yaragu gashi an hanata fita anan and she knows,

Mom tasan ba’a side nasu ta kwana ba, hannunta takai saman kumatunta da taji yana mata zugi takai
hannunta saman cikin nata shima dake mata zugi saitai shiruuu hawaye ya gangaro mata bata taba iya
bringing kanta to ask her self maisa Mom is always beating her? Mom bata tausaya mata, Mom hit her
kaman she’s not her Mom, tana son Mom but Mom bata sonta, dazu data rungume Mamie she wished
Mom ta rungume haka, hawaye ta kara sharewa ahaka tagama tunane tunanen ta bacci yayi awon gaba
da ita.
Around 1:00 yagama abinda yake dan har Abba saida yashigo still bai gamaba kashe system dinshi yayi
yadan kalli kofan dakin Gwaggo saikuma ya mike tsaye ahankali yawuce kitchen freezer yabude yadauki
ruwan data saka dayaga yayi kankara yadauka yadauki bowl yasa, yasa wasu ruwan a freezer incase

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login