Showing 51001 words to 54000 words out of 59470 words

Chapter 18 - UWA KO UKUBA MShakur HAUSA NOVEL

M SHAKUR   

28 Mar 2025

3080

Hamad, yanzu kuma ta tashi lips dinta na motsi but batajin metake cewa, ahankali
takai kunnenta saman fuskanta tayi shiru tana kokarin jin abinda take fadi Asmeey cikin bacci da mafarki
tace “Ya Hamad! Ya Hamad” dasauri Aya ta kalleta she’s still calling Ya Hamad dasauri tadaura hannunta
saman kanta ko zazzabi take but babu zazzabi ajikinta, ijiyan zuciya tayi tadan jijjigata hakan yasa tai
shiru tamaida lips nata tarufe, Aya tasauka daga gadon ahankali batare datai motsi ba kada ta tadata ta
rufamata bargo tawuce bayin Mamie tadauro alwala tafito ta shimfida dadduma tahaukai, yau gabaki
daya prayer point nata is her sister, she just turn tana kallonta tana mata addu’an Allah ya tsareta, yauta
kubuta Fawaz bai lalata mata rayuwa ba, but gobe fa? Jibi fa? Gata fa? Zata kubuta? The solution is Allah
ya shigo lamarin tasan ko duniya zata hade after wat happened today Baba bazai taba aurama Fawaz
Asmeey ba, but wat next? Will Mom give up? Will Mom backdown? Ga yarinyar batada any saurayi balle
tamasaka baki ta zuga Baba ya mata aure to hell with d law school, tayi agidanta, but she has no one! No
any man, Mom da bata bari tazo gidajen su wat will even happen? What kind of life is this? Why is Mom
like this? Kanta ya kulle batasan how she can save her little sister ba, bataso tace su Abba ko Kawu na
Gombe sutafi da ita, Mom are literally enemies da mutanen, she’s a sworn enemies dasu, so is
impossible but wat next? What will she do? Tayi shiru tanakan dadduman.
Around 5 na asuba Gwaggo ta shigo dakin tana haki taduka takama guiwowi, Aya ta tashi daga kan
dadduma dasauri tace “Gwaggo benen kikahau?” Kaman jira Gwaggo take tafashe da kuka tana haki har
lokacin kaman tafito daga yaki tace “Wallahi wallahi runtsawa nan banyi ba Aya sabida yarnan” tanuna
Asmeey dake kan gado tace “najama uwarku da yaron nan Yaseen yafi kafa sittin da shidda, wani irin cin
zaline wannan uwartaku tamikata da kanta aje amata fyade?” Ahankali Aya tace “Gwaggo hala Mom
batasan hakan zai faru ba tunda tace gidansu suka tafi” Gwaggo tace “dalla matsa uwarku duk ta muku
fitsarin asuba a kwakwalwa baku gane abinda ke faruwa, ta tsani yarnan, ta tsani Asama kaman
makiyarta, ai tasan waye kwalandan yaron nan, kuma da gangan tabasa ita ya lalata mata rayuwa Allah
ya hana ai addu’a ta ba banza ba”Gwaggo tai maganan tana sharce hawaye tabuga tafi tace “toh bari
kuji, wlh wlh karya tasha karya ke duk uban durun uwar abinda zai faru ya faru amman saina raba Asama
da wanchan muguwan Salima wlh kuwa” Gwaggo ta buga kofan da karfi cikin fushi kaman zata karya
kofan tar Asmeey ta bude idanunta kawai saitaga Fawaz asamanta zaihau jikinta wani irin mahaukacin
ihu tasaki da saida gidan gabaki daya ya dauka da Aya da Gwaggo dake magana sukayo kanta Aya tace
“Asmeey Asmeey mune kalla kalli, menene? Stop screaming” ina Asmeey bamatasan me akeyi ba tawani
irin kankare ihu kawai takeyi Gwaggo ta buga salati. “Innalillahi Wa innailaihi raji’una, Asama ke ke” Aya
tahau gadon tana kokarin dagota but wlh takasa cus Asmeey ta sankare sosai tana ihu, Mamie tashigo
dakin da gudu tana “meke faruwa” bama aji sabida ihun Asmeey daya cika dakin, Abba yashigo sanye da
jallabiya hannunsa rike da charbi yazo wajen gadon shima yana kokarin dago yarinyar yakasa ihu kawai
take. Yace “kira Dr Aya” Aya tarude batamasan da waya zata kirashi ba kawai tayi waje Baba yashiga tofa
mata addu’a, Aya na fita taga su Yaya Mustapa harda su Faisal da Munir duk zasu masallaci, Baba shima
yana fitowa ganinta tana kuka kawai sai suka taho Baba yataho da gudu duk sukai sama tundaga kasan
falon ihun Asmeey akeji Ya Mustapa yazo gadon da sauri ganin suna kokarin daukanta yace “don’t
forcefully try to carry her or take her zata karye, Mamie rub her hair” Baba yashigo dakin da gudu wlh
wlh yarude gabaki daya yace “Asmeey Asmeey, Husna, ke Husna” yakalli Abba yace “aljanu gareta Yaya?

Meya sameta”? Girgizamai kai Abba yayi Ya Mustapa yace “is just fear” tsayawa ahankali Hamad yayi
jikin kofan dakin wanda baiso yazo ba but yakasa daurewa saida yazo, duk suka shiga mata addu’a
Hameed ahankali shima ya jingina da bango yana kallonta. Ahankali Asmeey tafara sakin jikinta Mamie
na shafa mata kai Baba yace “Asma’u bude idanunki gani nan, ga Baba” bakinta ne yayi motsi cikin
rashin karfi da yar karaman kofa tace “waya buga kofan? Wanna mutumin ne”? Atare duka sukace “no”
Gwaggo tace “nice na buga kofa bansan zaki firgice ba Asama” ahankali Asmeey tace “Baba” dasauri
Baba yace “na’am Husna, gani” murya chan kasa tace “Munir” dasauri Munir yazo gaban gadon yace
“na’am Asmeey I am here, open your eyes” is as if she wants to be sure da gaske tana tareda su kafin
tabude idanunta tayi shiru kusan 2️⃣min duk suna kanta suna tofa mata addu’a kafin gently tace “Ya
Hamad!” Dasauri kowa na dakin yajuya yana neman Hamad suka ganshi tsaye jikin kofa yasauke kanshi
kasa da sauri gabansa yawani fadi jin takira sunansa,Ya Mustapa yace “answer her she’s in shock”kasa
magana Hamad yayi kaman zai nutse akasa da kyar yabude yace “uhmm” yana maganan yafice da sauri
daga dakin, gently Asmeey tabude idanunta tasaukesu akan Baba hakan yasa tai relaxing jikinta tamika
hannunta mai lafiya tabama Baba dasauri ya karba fashewa tayi da kuka ahankali tana kokarin tashi
Mamie ta taimaka mata ta taso tazauna ta rungume Baba tace “Baba I am scared” ahankali Hameed
yajuya yafice daga dakin, Baba yashafa bayanta yace “babu abinda zai sameki duk ba gamu ba, ga
yayyinki kuma, waya isa yataba ki ” gyadamai kai tayi ahankali tace “Baba ina Mom?!” Kowa na dakin
saida ya kalleta, murmushi Baba yayi yace “tana dakinta, bari muje muyi salla, Aya taimaka mata tayi
alwala” gyadamai kai Aya tayi da Baba da Abba da sauran mazan duk suka fice.

Wuraren 9 yashigo gidan daga mosque. Yaji karfin jikinsa he’s not running temperature zai shiga flat
dinsu Munir daya fito daga Bq yazo wajen yace “Ya Hamadi Abba na BQ yace ne daman na kiraka daga
mosque zanje wajen Asmeey” shiga flat dinsu Munir yayi yaje wajen Asmeey, shikuma Hamad yawuce
BQ din, wucewa yayi wajen ya shiga falon baida wani girma, Abba ne aciki sai Mami, sai Kawu, dakuma
yayyinsa, wajen Ya Mustapa yaje ya zauna duk suna kallonshi yasauke kai kasa yace “ina Kwanan ku”
Abba yace “lpy lau yaya katashi yau”? Ahankali yace “fine” yayi shiru sannan yadan gyara murya yadubi
duka yaran nasa yace “akwai very important magana dayasa nataraku, Baba bayaso ya zauna anan
sabida baiso wani yaji kunyarsa yakasa magana or yafadi ra’ayinsa” Abba yayi shiru sannan yace
“Muhammad Sani na so ya aurar da Asama’u!” Abba Yayi maganan yana kallon yaransa dayaga babu
wani wanda yayi motsi cikinsu, Abba yace “Asama’u batada wani manemi ko daya balle ace yafito” yayi
shiru na kusan 3min kowa na kallonsa, ahankali Abba yace “inaso ka aureta Hassan!” Dasauri Hameed
yadago kansa yakalli Baba cus baitaba kawo kansa maganan zatayo ba, Kawu yace “ka aureta Hameed!”
Kallon Hamad Ya Mustapa yayi dake kusada shi asace batare da kowa ya lura ba, kansa na kasa but
fingers dinshi yaga sunyi motsi more like rawa sai calmly yaga yaharde hannun nasa biyu yarike ya ijiye
kan cinyarsa, Ya Mustapa yadauke kai kaman bai kallesa ba, Abba yakalli Hameed yace “bakace komi ba
Hameed bawai tursasa ka nakeba saisa ma Baba yaki zama anan sabida kar kunyansa yasa kuyi abinda
zaku cutar da kanku” Hameed is an upright person, he’s outspoken saisa ake cemai baida kunya shi a
inda Hamad yake, kai tsaye yace “Abba ni inada budurwa wacce nakeso sunanta Zainab, Yaya Mustapa
yamayi magana da ita awaya” Abba na kallonsa yace “and so? This is kanwarka ake magana dan kanada
wata budurwa, nan da yan shekaru masu zuwa idan Allah ya budamaka kaga zaka iya rike mata biyu sai

kayi” mikewa tsaye Hameed yayi da sauri Abba ya kallesa kowa ma haka banda Hamad da kansa ke kasa
har lokacin, Hameed yace “Abba I am sorry gaskiya the same reason dayasa tundaga kan Ya Mustapa, Ya
Abdullahi and Yaya Faisal basu taba marmarin auren yaran matan nan ba nima I am no exception” duka
yayyinsa kallon Hameed suke, Abba dake kallonsa cikin natsuwa da magana irinta manya yace “and wat
is that reason Hameed danni ban sani ba” rai adan bace Hameed yace “Abba have you seen yanda yaran
matan nan ke tsoron mahaifiyar su? Tundaga kan Aya down to Munir? Abba kana ganin na auri yaran
matan nan will I ever be husband to her? No no no Abba wlh Mom dinsu ce mijin, Mom dinsu ce komi
tasu, they fear mahaifiyarsu kaman me, she’s in total control of lives nasu” Hameed yace “Abba idan
Mom takira Asmeey tace Asmeey karkima Hameed girki bazatayiba” Hameed yayi magana da muryan
Mom da saida Yaya Abdallah yayi murmushi cus he’s saying the truth wlh, Hameed yace “idan tace shigo
mota kizo bauchi yanzun nan wlh they no born those children ko Asmeey takejin maganan! Kafin
nadawo daga bank Abba Asmeey ta tafi” Hameed yadan lumshe idanu yace “Abba ni bazan taba iya
auren wacce uwarta ta maida robot ba, she’s always ready to obey command, this is abinda yayyina
suka gani basu taba kwadayin ko marmarin hada zumuncin nan ba cus it will never end well, banda haka
that woman hates Mamie na alot! She hates us, she also hates y……” hannu Abba yadagamai hakan yasa
Hameed yayi shiru, Abba yace “I don’t care idan she hates us or like us, Muhammad Sani kanina ne and I
will always be yayanshi, zumunci is the most important thing to me” Kawu yace “kwarai Yaya” Baba yace
“koba kanina araye ni mai daukan Asmeey na aurar da ita ga miji nagari ne, so idan wayannan ne
dalilanka ban karba ba inaso ka auri Asmeey Hameed!”.
[06/01, 15:27] +234 806 229 2100: 💫UWA KO UKUBA💫

✍💫M SHAKUR

EPISODE 1️⃣💫8💫

wa.me/+2347012181461
Baki Hameed yabude ganin da gaske Abba yake fa dan haka shima dole yayi da gasken, hakan yasa
yahade rai yace “Abba nifa bazan auri wacce wani yarigani ganin jikinta ba!”Dasauri kowa ya kalleshi
adakin da fuskan bacin rai sosai banda Hamad da har lokacin kansa akasa, Abba ya dakamai tsawa yace
“what are you saying Hassan”? Cikin kunkuni Hameed yace “karya nayi Abba sabida baici nasara ba
doesn’t mean bai mata wasu abubuw……” enough! Abba yafada rai abace, yanunamai kofa yace “fita!

Get out” wucewa Hamee yayi fuuuu yafita daga dakin, Abba yadanyi shiru saiya kalli Hamad dakansa ke
kasa anatse yace “Hussain zaka auri Asma’u”? Tashi Hamad yayi akufule yace “no!” Kawai yawuce yayi
kofa yafice daga dakin Abba yabisa da kallo haka kowama na dakin Abba ya sauke kai tareda dafa kai
yayi shiru chan Abba yadago kansa yace “wai nakalli Hameed shine mai dan hankali dazai iya zama da
mace compare to Hamadi dakeda kunya bayama son mata na kallonsa, kuma naga Hameed shine yadan
kama aiki a hannu zai iya rike mace da albashinsa, shi Hamad har yanzu bai sami aiki ba, amman jibi
rashin mutuncin da Hameed yamin” ahankali Kawu yace “yanzu yaya zamuyi Yaya? Bazamu iya samo
wani mu basa auren Asmeey ba gaskiya daga waje wanda bamusan yanayin halinsa ba, gwara yaranmu
da suna gabanmu kuma mu muka tarbiyantar dasu” ahankali Ya Abdallah yamike yace “Abba reasons na
Hameed are valid, I’m not talking about the last statement dinshi wannan hauka ne kawai yake but
statement din mahaifiyarsu yaran dayayi is true, very very true, Abba auren yaran matan nan ba zaman
lpy bane and idan kun shirya yi ku shirya ganin drama da damuwan uwarta daban daban cus kunsan
gaskiya bawai mahaifiyarsu na sonku bane ko tana shiri daku ba she hardly talks to Mamie, Abba think
about it please” ahankali Abba yace “to ya kukeso mu ceci Asma’u eh? Abdullahi idan ni mahaifinta
Yayan kuma mahaifinta banyi ba who will? Do you have a better solution mu barmata yar ta kashe?
Mubar innocent Asma’u ta mutu sabida halin mahaifiyarta sai muzo mukaita kabari nan gaba?”Shiru Ya
Abdallah yayi sai kawai yawuce yafita shima, Faisal yamike yabisa abaya cus the truth is they don’t hate
Asma’u infact babu wata kanwarsu da suka tsana tundaga kan Aya kawai they don’t want problem na
mahaifiyarsu saisa dukansu bama su taba gigin neman yaranta ba duk sukaje suka auro matayensu
awaje.
Dakin yarage daga su Abba sai Ya Mustapa, tasowa Ya Mustapa yayi yazo kusada Mamie yazauna
dukansu suka kalleshi ganin magana yakeso yayi, Abba yace “me kakeso kafada Doctor? Kaima bayan
kanninka zaka bi”? Girgiza kai Ya Mustapa yayi yace “Abba ku aurama Hamadi Asmeey!” Dukansu
kallonsa sukayi jin maganan dayayi, Abba yace “Doctor Hamad! Da kanka kake fadin abama Hamad
Asmeey? Ta ina kake ganin Hamad zai fara zaman aure da wata eh? Baka gansa bakaga kalansa ba”?
Anatse Ya Mustapa yace “Abba sabida yanayin Hamadi sai muyita kallonsa bazaiyi aure ba? Hameed
nada budurwa Zainab yariga yabama wata zuciyansa, koya auri Asmeey bazata sami zuciyarsa ba, so I
support kar Hameed ya aureta but for Hamad baitaba soyaya ba just like Asmeey bata taba ba, Hamad is
shy and calm, Asmeey is calm too and sad and lonely girl with zero friends, so I think a unionship nasu
they will find solace and comfort in one another, they will learn to love ajunansu and unite, they will
build not just love har friendship da companionship, Hamad zai chanza within a blink on an eye and be
free da matarsa” Abba yayi shiru duk suna kallon Ya Mustapa dake magana hakama Mamie, ahankali
Mamie tace “rike mata, rike gida, ciyarwa da sauransu fa doctor? Hamad bai kama sana’a ba kwakkwara
yaya zai lura da ita?”Murmushi Ya Mustapa yayi yace “Mamie Hamadi is not that jobless da bazai iya rike
mata ba yaron nan yanada sana’an sa, Hamad is genius, gifted, he works and he earns money, ana gobe
salla they paid him 2️⃣50k for a job dayayi that’s albashin Hameed na one month ya samesa in a day,
Mamie kudenama Hamad kallon baida aiki trust me cikin duka yaranku Hamad shine ma yafimu aiki ga
potential, akwai wani gasa daya shiga na Microsoft idan yagama yaci Mamie wlh kudin da yaron nan
zaiyi sai kunyi mamaki and they will invite him to kasan waje ranan kaddamarwa zaku gansa a TV saisa
na siyamai desktop rannan cus dashi yake aikin nashi ya lalace, Hamad is not lazy kuma ba lallai ma
yajira mu mumai wani abuba, kumai addu’a kusamai albarka Mamie and wish him well, aure na bude

kofofin arziki Allah bazai taba hanasa abinda zai ciyar da Asma’u ba banda haka I’m still here, gasu
Abdallah ga Faisal ga Hameed we will all support our brother, Mamie Asmeey bazata taba wuni without
a meal ba I promise you that” Duk shiru sukayi suna kallonsa Abba yace “na yarda toh doctor, inada
wata miliyan daya muka koma kano sai atada gini a musu flat yasata agidan, bazan turasa gidan hayaba
karya zaman mai wani burden akai biyan kudin gida duk shekara, kuma ayanda Hamad yake gwara suna
gabanmu muna kwabamai, muna nunamai ga yanda akeyi dan yaron sai ahankali” Baba da Kawu duk
sukai na’am Ya Mustapa yace “Baba karka damu zan dauki nauyin ginin in sha Allah” ahankali Mamie
tace “Idan mahaifiyar ta tafara bura’uba fa? Hamad baida bakin fada ko fitina da tashin hankali? Nasan
maganganun Hameed yayi shirme amman kuma yafadi gaskiya dayawa, idan Asmeey Hameed zata aura
bazan waniji tsoro ba Hameed nada jan wuya dazai tsorata Asmeey ta natsu tasha ruwan jikinta idan
mahaifiyarta na abubuwan data saba, but Hamad fa? Ta ina zai iya da jaraban matan nan?” Murmushi Ya
Musty yayi yace “one problem at a time Mamie, and Mamie kinsan mene kinga yaran nan biyu Asma’u
da Hamad idan sukazo suka kulla soyayya ba mahaifiyar Asmeey da idan duka danginta ne Asmeey zata
yakesu sabida mijinta, babu abinda so baya sawa Mamie kawai mubisu da addu’a” Abba yace “wannan
gaskiya AlMustapa, idan muka tafi da ita kano saitai haukanta aurenma sirri ne, so maganan nan ta tsaya
tsakanin mu, bari na kira Muhammadu Sani” Baba yadaga wayansa ba’a wani jimaba saiga Baba yashigo
ya zauna Abba ya sanar dashi komi sun dauka bazaiso hadinta da Hamad ba cus baida aiki amman Baba
yace “wlh wlh nafison Hamad! Nafison Asama’u da Hamad Yaya, nasansa da kunya da jin nauyi yasa naki
zuwa nan amman shinake mata kwadayi dama, arziki kuma Allah ke badashi ga wanda yaso, ni da inada
arxiki? Rana daya Allah yasama kasuwata albarka, zan sayamai gida a kanon sai su zauna ciki” Abba yace
“kadakata tukunna su zauna agabanmu muna kallonsu kasan yanayin Hamad we have to groom him and
teach him zaman aure” Ya Mustapa yace “Hamad bazai taba yarda ma ya zauna agidan da zaka basa ba
Baba yanada zuciya da kwazo fa bayason irin abubuwan nan, ko ginin da zamumai yanzu zakuga yanda
za’ayi dashi sai munyi daga” Waya Baba yadaga yakira Yayan Mom, Yakira wasu abokansa guda biyu,
dawani babban Malami daya sani karfe biyu a masallacinsu na nan cikin gida.

Shigowa dakinsu Hameed yayi dan tuntuni yana waje yayi wani bako dan shi yanada friends anan Bauchi
yana shigowa daidai Hamad na fitowa daga wanka yasaka wani ash yadi but idanunsa sunyi ja da sauri
Hameed yace “meya sami idanunka haka kuka kayi?” Da sauri Hamad ya dauke kai yace “soap” gabansa
Hameed yasha yana kallon idanun yace “soap? Yaushe kafara sa soap a idanu wajen wanka? Did you cry
Hamadi?” Kokarin matswa gefe Hamad yayi Hameed yabisa yace “why did you cry”? Dan lumshe idanu
yayi saikuma ahankali ya nunamai shoulder shi, dasauri Hameed yazo yadan daga rigansa yaga ciwon
yace “you got hurt wurin nan jiya ko?” Gyadamai kai yayi Hameed yace “sannu kasha magani”? Maganin
ya nunamai dake gefen gado kawai yawuce yahau gadon yadauki laptop dinsa ya kunna Hameed yabisa
da kallo zuciyanshi na kokonton abinda yasashi kuka, Hamad is very soft tun yana yaro he cries for ciwo
especially idan da zafi, but could this small ciwo be abinda yasasa kuka abayi? But wani abin ne? But
mene toh? Wani abu yabatamai rai ne? Wat happened? Yayi shiru cus yakasa kawo wani abu
Sai yazo bakin gadon ahankali ya zauna ahankali yace “Hamad” juyowa Hamad yayi yakallesa, murya
chan kasa Hameed yace “I love you!” Wani irin dauke kansa Hamad yayi da gudu yadauki filo yana kare
fuskanshi adikile yace “wat is this”? Kaman mace Hameed yawani shake murya yace “Wallahi I love you

Habiby na Hamadi fine boy” dawani irin sauri Hamad ya yunkura zai tashi Hameed yarike shi yana
hayowa gadon yace “wlh bazakaje ko’ina ba, wai kai bazaka koyi irin abubuwan nan ba, hakafa kai aure
matanka zata dinga gayamaka, I love you Hamad” yawani make murya yana kanne idanu uwa mace,
juyawa Hamad yayi yakifa fuskanshi akatifa sosai kaman zai shige ciki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login