Showing 33001 words to 36000 words out of 59470 words

Chapter 12 - UWA KO UKUBA MShakur HAUSA NOVEL

M SHAKUR   

28 Mar 2025

3083

zatai
amfani dashi gobe, yafito daga kitchen din yana tafiya ahankali yawuce gaban dakin ya tsaya yayi dan
jimmm, hannu yadaga yadaura kan kofan yayi knocking kadan he could hear minsharin Gwaggo daga
wajen, sake knocking yayi ahankali but still shiru yasake yin jimmm, ataushashe cikin yar kankanuwan
murya dake ratsa mind yace “Asma’u!” Firgigit Asmeey tafarka tabude idanunta dan har cikin zuciyanta
taji yanda aka kirata, da muryan bacci dake a hargitse tace “uhnn na’am” dan jimmm Hamad yayi, kusan
1️⃣0seconds sannan calmly dan yasan bacci take karya firgitata yace “open the door” tashi tayi daga
gadon dasauri ta sauko batare datama san dankwalinta baya kanta ba bata da kayan bacci anan so gown
din atampan ne ke jikinta ta taho wajen kofan kai tsaye tasa hannu daya tabude kofan while dayan
hannunta nakan idanunta tana murzawa sabida bacci, sauke gentle eyes dinshi Hamad yayi kan fuskanta
she’s not even looking at him sosa idanu take sabida bacci, idanunshi yadaura kan lafiyayen hadadden
kitson da aka mata dayayi kyau sosai da sauri yasauke kanshi ya maida kan fuskanta for the second time
ahankali yace “Asma’u!” Dasauri ta dago kanta takalleshi tana janye hannunta daga kan idanunta da
suka kada sabida bacci ga kumatunta daya kara ja inda aka mareta gabanta na faduwa sabida yanda
yakira sunanta, tsareta da idanu yayi na kusan 10secs dukansu babu wanda yayi magana this time
around shine yafara janye idanunshi daga kanta yamika mata bowl da ruwan ice ke ciki yace “put this a
fuskanki” bowl din itama ta kalla saita gyadamai kai ahankali tasa hannuwanta kan bowl din zata amsa
sai bai saki ba hakan yasa tadago kanta ta kalleshi ganin bai sakin mata ba, hada idanu sukayi yanda taga
yana kallonta yasa ta sauke kanta kasa da sauri har lokacin hannuwanta nakan bowl din tana jira ya sakin
mata, cikin yar kankanuwan murya da ita kadai zata iyajin maganan sa Hamad yace “next time if anyone
tries to slap you use your hands or elbow ki kare fuskanki,” dan dago kanta tayi tadan kalleshi har
tsakiyan zuciyanta takejin muryanshi dakeda bala’in dadi, ga kamshin dayake yi daya cika wajen, bawai
fuskanshi ko expression nashi shows he care bane but his words are so deep a heart nata that translates
as he cares, baiso yaga kumatunta sunyi jan mari, sauke kanta kasa tayi sannan ta gyadamai kai ahankali
tace “tom, thank you 4️⃣ d ice cream Ya Hamad” sakin mata bowl din yayi ta hanyar jaye hannayenshi
daga kai yajuya da sauri kaman wanda yaji kunya murya ciki ciki yace “Mamie na siyama not you”
yawuce dinning da sauri hakanan saita kasa komawa ciki ta tsaya awajen kaman an kafata he looks so
cute, godiyan datamai ne yabasa kunya? His shyness is charming, laptop dinshi ya dauka daya kashe da
ragowan ruwan bottle water daya rage yajuyo hada ido sukayi da sauri tajaye nata idanun gabanta na
faduwa takoma cikin dakin da sauri ta maida kofan tarufe, dauke kai yayi yawuce yakashe wutan parlour
kafin yayi stairs yashiga dakinsu Hameed yayi nisa a bacci, ijiye komi yayi yafada bayi yafito daure da
alwala, dadduma ya shimfida yayi nafila sannan yatashi yazo yahau gadon ya kwanta ahankali.

Tana maida kofan tasake jingina da kofan tayi shiru duk wani motsinshi a parlour tanaji harya gama
kashe wuta sannan tajuyo yarufe kofa dan bakajin walking step nashi what is wrong with her? Tayi
maganan ahankali, wucewa tayi gaban gadon ta zauna tadauki kankaran ta daura saman kumatunta but
saitaji sanyi da sauri tacire ta ijiye a bowl din tana kallo, sake dauka tayi takai kumatun kusan 3secs ta
ijiye takasa jure sanyin sai kawai ta ijiye bowl din ta kwanta sai tunanin Ya Hamad take da yanda yakirata
Asma’u da maganan daya mata muryanshi is so soothing she can’t even explain and so calm gawani irin
natsuwa da kwarjini da haiba da tunda take bata taba ganin namiji mai kalansa ba ga idanu kuma kwallin
dayake sawa namai bala’in kyau ahaka bacci yayi awon gaba da ita.

Wajajen 4️⃣:30 na asuba Gwaggo ta farka tana kunna wuta takalli Asmeey data dukunkune tace “ke ga jin
sanyi amman kin kasa tashi ki dauki abin lulluba” sauka tayi daga gadon ta wuce drawer taciro bargo
tazo tabude ta lulluba mata sannan tawuce bayi tace “bari na barta tadan kara bacci nasan taci bakar
wuya a hannun muguwar uwarta” salla Gwaggo tafito tayi tanakan dadduma tana kallon Asmeey data
kudundune a bargo harkai saijan charbinta take around 6 tafada bayi tayo wanka tazauna ta cicciro
abubuwan shafe shafen ta tafara shafawa masu wired kamshi abinda yatada Asmeey kenan tabude
idanunta tana yaye bargon ta tashi zaune ahankali tace “Gwaggo meke wari” kallonta Gwaggo tayi zata
zageta sabida yanda take kiran manta na wari tabuga salati. “Oh Innalillahi wa innailaihi raji’una
billahillazi idan uwarki bata rokeki gafara ba sai Allah ya soyata a jahannama, kalli suntumemen kumatu
kaman an zuba yeast” dasauri looking confuse Asmeey ke kallon Gwaggo dake surutu but ganin yanda
take kallon fuskanta yasa gently takai hannunta saman kuncinta da Mom ta mara saitaji ya kumbura
takai dayan hannun ta shafa na bangaren dama is normal hannunwanta kansu sai sukayi kaman ta daura
daya a tudu daya a flat surface sai kawai ta tashi da sauri tawuce bayin Gwaggo tana bude kofa ta tsaya
turus tana kallon madubi yanda kumatunta na haggu ya kumbura kaman tana ciwon hangum ko ciwon
hakori harda wajen lips da jaws nata saitai looking kaman ba’ita ba tai wani irin muni a idanunta wani
irin sosa mata rai abin yayi batasan sanda ta duka tafashe da kuka sosai ba like she’s feeling super hurt,
takai kusan 30min abayi Gwaggo tace “wai harna gama shiryawa tsaf nasaka kayan salla bazaki fito kiyi
salla ba” da kyar ta tashi idanunta sunyi jazur tafito kanta akasa tasaka hijabi tai salla tana idarwa ko
azkar batayi ba ta mike yafada gado taja bargo har saman kanta Gwaggo tace “yau naga ikon Allah tashi
kije kiyi wanka yanzu zanje chan dakinku na karbo kayan sallanki mutafi masallaci” taushe bakinta tayi
bataso Gwaggo tasan tana kuka ta danne tace “bazanje ba” tsuki Gwaggo taja tamike tace “nadawo
dakin nan bakiyi wanka ba sai an jimu agidan nan” tawuce tafita.
Wajajen 7:15 Gwaggo tadawo da leda a hannunta wanda Ramla tahada mata komi da zata saka dan
ka’ida rannan salla kowa kayan da Abban Kano ya dinkama kowa yake sawa ganinta har lokacin akan
gado gashi masallacin dasuke zuwa 8:00 ne salla yasa Gwaggo tace “au baki tashi ba bari kigani” kayan ta
ijiye tafito falo tana rapkama Abba kira. “Abubakar Abubakar, Madina kai Abubakar” koda Abba yabude
yashiga saukowa Mami biyeda shi ya shirya tsaf cikin manyan kaya da malunmalin ga agogon da Hamadi
ya siyamai wrist nashi Mamie ma tasaka lace mai kyau ta saka sarkan da Hamadi ya siyomata shima
Hameed yashiga saukowa yayi bala’in kyau cikin shaddan sa sky blue da akamai jumper da aiki mai kyau.

Abba yace “Gwaggo lafiya” rai abace tace “kaga nida Asama ne takemin bori uwa nice na kumbura mata
fuskan, wanka takiyi wai bazata masallaci ba sabida uwarta ta nakasa mata barin fuska” wani kallon
takaici Abba yama Gwaggo sai kawai yawuce dakin Mamie tabisa Gwaggo tabi Hameed dake kamshi
tace “kawa Allah sammin turaren nan daka fesa dake kamshi ja’iran chancewa tayi wai wari turarena
yake” Hameed yace “dama bakisan tsami turarenki yake ba Gwaggo” haderai waggo tayi tace “nidai zaka
tsammin ko bazaka tsammin ba”? Daidai Hamad yafito cikin exactly kalan kayan Hameed da sunmai
bala’in kyau yana saukowa daga stairs Hameed yace “turarensa ne ki tambayesa” tsayawa Gwaggo tayi
tana kallonsa yanda yake tafiya a natse tace “Oh Allah ka nunamin auren Hassan da Hussaini, kai Allah
yama Hamadi natsuwa inama haka Hameedu keda natsuwa” rai abace Hameed yace “me kikace”?
“Uban ka nace” ta amsashi tana murmushi tana kallon Hamad daya hada fuska.

Abba ne yafara shiga dakin da sallama yace “Husna” dawani irin sauri Asmeey ta tashi dan gidan nan kap
bataga wanda baya girmama Abba ba shine babba har Baba respecting Abba yake sosai kuma ya
manyanta yaye bargon tayi ta tashi ta zauna tace “na’am Abba ina kwana” daga Abba har Mamie
kumatunta sukabi daya kumbura gashi tai kuka sai idanunta suma suka tashi karasowa wajen gadon
Abba yayi yace “subhanallahi Doctor bai baki magani bane?” Ahankali tace “yabani nasha amman yace
nasa kankara jiya nafara sawa sai nayi bacci bansa da kyau ba” tana maganan sai hawaye suka sake
fadomata ta share da sauri ta sauke kanta kasa asanyaye Abba yace “ya isa tashi kiyi wanka muje
masallaci Doctor sai kara dubaki” gyadama Abba kai tayi ta tashi ahankali tawuce bayi Abba yawuce
yafita duk zuciyanshi ba dadi Mamie ma haka suka fito duk an shigo su Ya Mustapa kowa yaci gayu Abba
ya kalli agogon hannunsa yace “inaga masallacin 8:30 zamuje ko na 9 Doctor ahmm please kaduba
yarinyar nan kumatunta ya kumbura” dasauri Ya Mustapa yace “batasa ice bane” Mamie tace “tafara
wai sai tai bacci” Abba yabi duka yaran nashi da kallo sunyi kyau sosai kallo saya Hamad yama Mamie
yaga sarkan saya sayamata Abba yasa agogon Ya Mustapa ma yasaka agogon daya sayama hakan yamai
dadi sosai.

Bata wani jimaba tafito ta zazzage ledan harda cream Ramla tasa mata sharp sharp tasa kayan atampan
da Abba yamusu mai kyau gold atampa mai blue ne embellish an mata riga da skirt da suka zauna
ajikinta sosai, bata daura dankwali ba hijab kawai ta saka ta fesa turare tasake kallon madubi she feels
pathetic she feels down she’s feeling like the most ugliest girl in the world zuciyanta yayi baki kirin ba
dadi ta daga hannuwanta takalli lallinta da duk sun gwalje nothing is right about her banda kitso da dinki
she’s having a very very dark salla sai kawai taji tana kunyan ama ganta gashi batada nose mask anan
adakinsu akwai daga waje taji Mamie ta kirata. “Ma’u kingama” ahankali muryanta na cracking tace “eh”
takalmin sallanta wanda yake hill gold mai kyau sosai very expensive shoe tasaka sannan taja wuyan
hijabinta gaba sosai sannan takama hijab din tagaba tarufe kumatun tazo wajen kofa kanta akasa tafito
ahankali kowa na falon har Abba kallonta suke banda Hamad dayayi kaman baimasan wani abu na
faruwa ba Abba da baison wani yayi maganan fuskan yasata kuka yace “toh kumutashi muje muje muje
Husna” Hamad yafara tashi kai tsaye yawuce kofa abinsa yabude yafice, Gwaggo takoma daki taciro
gyalenta ja ta yafa wanda Hamad ya siyamata tace “billahillazi banga wanda yakaini kyau agidan nan ba

yau” fitowa sukayi sukai wajen motocin gidan da an wanke gasu Nana da Ramla duk an fito suma sanye
da irin kayan dake jikin Asmeey, Ramla sai kallon, ahankali ta tsaya gefe daya wajejen taki zuwa wajen su
Ramla Munir daya fito daga flat dinsu yana sanye da shadda hadade tasha guga idanunshi akan sister shi
yafara sauka yanda yaganta ita kadai tajawo hijabi gaba da sauri wajenta yafara zuwa ya tsaya yadan
leka fuskanta yace “mehaka Ya Asmeey kin rufe fus…..” kasa karasa maganan yayi lura da kumburin
fuskanta sai yayi shiru yana kallonta ahankali yace “na dauko miki nose mask?” Gyadamai kai tayi da
sauri yajuya yakoma flat dinsu daidai Mom na fitowa daga flat din tareda Mama dasu Ammi mugun
bugawa kirjinta yayi Mom ce kadai bata sanya kayan da Baba yamusu ba wani HKG atampa ta saka ta
daura designers after dress akai ta zuba gwalagwalai awuya da hannu tana tafiya kaman she owns the
floor rawa hannuwan Asmeey yafara tajuya tana kokarin zata zagaya ta bayan motan Ya Mustapa yace
“Asmeey” arude ta juyo yakalli Hamad ya mikamai key sienna motan Baba yace “all the children su shiga
this sienna drive them, get in Asmeey” dasauri kafin Mom ta iso wajen tawuce, ta shiga chan last roll na
motan Ramla itama tashigo tazo ta zauna kusa da ita sauran kannensu suka shiga motan kowa na shiga
motan Mom ta iso ta gaisa da kowa aka amsata banda Baba daya shige mota abinsa Mom tawuce ta
shiga motanta Mama ta shiga tareda ita, Mamie ta shiga mota daya da Ammi da Gwaggo Hameed ya
jasu Ya Faisal yaja matayensu shikuma Ya Mustapa yaja su Abba Munir yafito yazo ya shiga gaban motan
Ya Hamad yashigo ya rufe motan Munir yajuyo yaba Yusra nose mask yace “mikama Ya Asmeey”. Black
glass Ya Hamad yasaka yaja motan duk akabar gidan, hannu Ramla tasa ta karbi nose mask din tajuyo
tamikama Asmeey da ke kallon gefe daya ahankali tace “Asmeey take” juyowa Asmeey tayi batare data
kalleta ba tasa hannu zata karbi nose mask din dasauri Ramla tarike hannunta hakan yasa Asmeey ta
kalleta da rinannun idanunta sosai Ramla taji she’s feeling guilty barinma kumatunta data gani sai taji tai
nadama taruwa hawaye yayi a idanunta murya chan kasa tace “I’m sorry Asmeey kiyakuri kinji” shiru
Asmeey tayi tana kallonta tana tuna abinda tamata jiya tayi kokarin fizge hannunta Ramla tarike muryan
Asmeey na rawa sosai tace “ki sakeni” ta madubin gaban motan Hamad ya kallo bayan, yaran ma duk
suka juyo Ramla tace “kice kin hakura tukunna” ranta na tafarfasa tabude baki zatai magana takasa
tashiga kokarin fizge hannunta, Munir da iya shiganma yar uwanshi yace “Ya Ramla ki saken mata
hannu” ahankali Ramla tace “hakuri nake bata” cikin tsiwa Asmeey tace “bazan hakura ba and baruwana
dake kifita harkana you lied kince nace miki wawiya and I never said that, ai yanzu you are happy ko
daman kince nasaba shan mari a kumatu kema zaki karamin kumatun is swollen I hope you’re satisfied
niki sakeni” tafashe da kuka sosai datake rikewa sake kallonta Hamad yayi ta madubin sai kawai ya
dauke kanshi ya maida kan titi Ramla ta rungumeta da sauri tana kuka itama tace “Asmeey dan Allah
kiyakuri I’m sorry for whatever I said jiyan nan kiyakuri kinji” shiru Asmeey tayi sai chan ta gyadamata kai
Ramla tace “tsaya na samiki nose mask din” hannu rasa ta sharemata fuska sannan tasa hannunta a
hijabin tasa mata nose mask ahaka sukakai mosque kashe motan Hamad yayi Munir ya sauko yabude
musu duk suka shiga fitowa gabanta sai faduwa yake tadan kalli gaban motan ganin Ya Hamad na zaune
dauke kanta tayi da sauri tafita daga motan ahankali daidai Mom na zuwa wajen dawani irin sauri
tadawo cikin motan hakan yasa Hamad yajuyo hada idanu sukayi dauke kai tayi da sauri sannan tafita
daidai su Mom sun wuce tabi baya ya sauko yarufe motan suka wuce sahu tayi gefen su Gwaggo Mom
nadaga chan.

Sallame sallan sukayi kaman ance tadan juyo karaf suka hada idanu da Mom wani kallo da Mom tamata
ita kadai tasan meaning dinshi cikinta wani kuka yayi dasauri ta sauke kanta kasa tashi Gwaggo tayi tace
“kumuje Billahillazi yunwa nakeji dabino na yana mota shi zanci” hannunta Ramla takama tace “muje”
ahankali ta mike dasauri tabi Ramla suka wuce Mom tamata wani kallo ganin kallon data mata dazu
baisa ta tsorata tace a motanta zata koma gıda ba ko gaisheta ina kwana batayi ba tafarfasa zuciyanta
yashiga yi suka wuce itada Mama.

Wajen motarsu sukaje suka jingina suna jiran Ya Hamad da Munir ganin Mom na zuwa wajen wani kalan
dukewa tayi ta tsugunna dan kafafunta sun kasa daukanta ko kallonta Mom batayiba tawuce wajen tata
motar abinta tashiga ta kunna tana duke ahaka saiga Ya Hamad da Munir suna zuwa ahankali Ramla tace
“tashi muje”
Tashi tayi Munir yabude musu motan duk suka shiga tunda ta shiga motan tai shiru dudda anata hira but
Mom kawai zuciyanta ke kawo mata şundan bata lokaci kafin sukai gida parking akayi saukowa sukayi
ahankali tawuce flat dinsu Ya Hamad yadan kalleta yadauke kai mazan suka wuce wajen raguna dan
tanka su Mamie kuma suka wuce backyard daidai zata shiga flat dinsu Gwaggo tace “zonan Asama tunda
komawa inda ake neman kasheki kikeso kiyi” Dan waigowa tayi ta tsaya Baba dayake tsaye kusa da
Gwaggo yace “badake ake magana ba” juyawa tayi tayi hanyar flat dinsu Abba Mom data fito daga mota
takalli Baba dayayi kaman bai ganta ba zata wuce flat Gwaggo tace “eh aje acire kaya afito ayi aiki” ko
kallonta Mom batayiba.
Kananun yaran gidan tea aka shiga basu Ammi tace “Ramla kutashi kuje kuda su Nana ku jera carpet a
tsakar gida da kayan abinci anan za’aci” tashi duk sukayi, Asmeey na shiga dakin hijabin ta cire ta zauna
ahankali tana zare nose mask daga falo taji Gwaggo tace “kifo Asmeey an saku aiki” tasan aikin already
hakan yasa tadauki gyalenta na dakin blue ta yafa akai tadan zazzago dashi tafito slippers data gani so
well kept anan side na chair a falon ta zura kafafunta aciki sun mata yawa Ramla dake kallonta tace “jiya
da daddare saida nazo na ganki but Ya Twins bansan ko Ya Hamadi ko Hameed bane” da zuciya daya
Asmeey tace “maisa kwallin?”Gwaggo dake zaune ta buga salati tace “Hamadi kike cewa maisa kwalli
Asmeey ai gashinan yana jinki”? Dawani irin sauri daga Asmeey har Ramla suka juyo daidai yagama
saukowa daga stairs gashi bakajin footstep nashi, arude tajuya zata fice gabanta na faduwa calmly yace
“my flops” chak Asmeey ta tsaya saita sauke kanta ta kalli kafafunta da sukai dan firit a takalmin, awani
irin hankali tajaye kafafunta daga ciki sannan ta sauke kanta sadaf sadaf tafita ahaka Ramla tabita suka
shiga warware carpet suna shiryawa a compound din ga pillows sun jefa anyi setting sannan suka tafi
backyard su da matan yayansu nafito da abincin da aka dafa daban daban kusan 45mins aikin ya
daukesu su Baba kuma an gama gasa musu some part na layyan dasukayi duk akazo aka zauna dan cin
abinci Mama tace “bari na kira Maman su Aya”.
[03/01, 21:55] +234 806 229 2100: 💫UWA KO UKUBA?💫

✍💫M SHAKUR

EPISODE 1️⃣💫2️⃣💫

Babu wanda yace mata wani abu ta mike ta wuce Asmeey kanta na kasa Ammi da Mamie suka shiga
serving kowa saiga Mom tafito tareda Mama tasami waje ta zauna tana murmushi da Mama, Baba ya
tsareta da idanu she never cared about family nashi bata shiga harkansu, this is the measure reason yasa
ya karo aure lokacin, Gwaggo ta watsama Mom harara tace “aikin kenan bakar muguwa” wani kallo
Abba yamata yasa tace “ai nayi shiru uhmm tunda an hanani magana” abincin kowa yakeci banda
Asmeey data kasa ci sabida zuwan Mom, dan dago kanta tayi tana kallon Mom she just wish inama zata
mata murmushi she loves her Mom amman Mom murmushi take da Maman su Nana, dan karkato da
idanunta tayi karaf suka hada idanu da Ya Hamad dake kallonta shima bayacin abinci he’s not
comfortable, da sauri ta sauke kanta kasa tadebi rice takai baki kadan, Mom ta kallota ganin she’s eating
abinta ta dauke kai zuciyanta na radadi da suya, Ya Hamad yafara tashi kansa akasa yawuce babu wanda
yamai magana yamayi kokari yau yafito cus baitaba fitowa aci abincin tareda shi ba, Gwaggo tace
“makiyin abinci mai shegen zurfin ciki da rashin son jama’a” Ya Mustapa yakalli Asmeey yace “once you
finish eating go and put ice a fuskan nan take your drugs and

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login