Showing 57001 words to 59470 words out of 59470 words
Hameed daya sunnar da kansa yana
sosakai na rashin gaskiya Abba yace “muna komawa gida za’akai kudin aurenka gidansu ita wacce kakeso
din tijararre” yawuce yafita, Ya Abdullahi yatashi yana kallon Hamad dahar lokacin yakifa kansa kan
guiwansa yace “ango, ango, ango Hamad” Faisal yace “wuhuhuuuu sai amarci ina gayamaka Ya
Abdallah” zokaga dariya harshi Ya Mustapa saida yadan kyakyata amman a fuske, Hameed yataso shima
yace “ku tsaya kuje Yaya” duk suka tsaya suna kallosa yace “yanzu kowannenmu zai dauki topic ne dazai
koyamai kan zaman aure, ni Hameed his twin brother i will take him kiss and hug” zokaga dariya, Ya
Faisal dan sune sako dagashi sai su yace “as yayan ango I will teach him tarayya” wani kalan tashi Hamad
yayi tsaye da duka hannunsa a fuska zai fice suka rikeshi suna ihu. “Angooo Angooo” kaman zai fashe da
kuka Ya Hamad har lokacin hannayensa nakan fuska yace “Yayaaaaa” Ya Mustapa na dan dariya ciki ciki
yazo ya karbesa yace “dalla ku cikasa wai mehaka kuna abu kaman yara”Hameed yace “damafa yadan
kyasa harda siyamata ice cream” kaman Hamad zaiyi kuka yace “ni banso” yajuya yafita daga masallaci
zasu bisa Ya Mustapa yataresu yace “wai sai kun sakashi kuka zaku huta? He’s in shock let him be” Ya
Abdullahi yace “Ya Doctor wai ya akayi Abba ya chanza”? Ya Mustapa ya harari Hameed yace “wannan
mara kunyan yanada babe so karya wahalan da Asmeey that is already going through alot shine aka
hada da Hamad, once we get to kano zamu mai gini a compound a flat da zasu zauna” Ya Faisal yace
“but Ya Doctor tayaya Hamad zai fara rayuwa da mace ku baku gansa ba? I’m still worried for Asmeey fa,
cus can heeeeeee?” Suka wani bushe da dariya, Ya Mustapa yayi shiru but duk sun gane maganan sa, Ya
Mustapa yace “well all I know is he’s a man, komujima komu dade zamuga yaransa” Hameed yayi wani
ihun iskanci yace “Yaya kaga dan Allah nima muna komawa kano washe garin rannan kuje gidansu Zee
wlh Yaya nakai 2more months banyi aure ba zaku iya rasani washhh” kunnensa Ya Mustapa yakama yace
“kaiko naughty boy” ihu Hameed yayi yana dariya yace “sorry Yaya Sorry” Ya Mustapa yace “lemme
warn you tundaga yanzu naga ka takurama Hamad koka samai ido ranka sai ya baci and that goes for
dukanku” yasaki kunen Hameed yanuna Faisal da Abdallah da duk ke gimtse dariya, yace “allow him to
get close to matarsa, banda sa’ido you know yanda Hamad yake wlh na kamaku in anyway ranku zai
baci” Faisal yace “Yaya bazan samai ido ba but wlh Yaya curiosity wan kee me I just want to see yanda
Hamad zaiyi coitus” Zokaga dariya Hameed harda faduwa akan dadduma cus ya dauka shi kadaine dan
iskan ashe Ya Faisal ma dan iska ne, infact yama fishi iya iskanci is the way he said coitus that killed him
finish, duk kawai yanda Hamad zaiyi abu akeso agani, Ya Mustapa yakallesu da Faisal da Hameed sai
kuma ya kalli Abdullahi dayaga shima rike dariya yake da kyar hannuwansa har zabura suke sabida
yanaso ya tuntsure da dariya yace “ohhh hardakai Yayansu akeso aga coitus”? Ya Abdallah yawani bushe
da dariya yana kama cikinsa yace “Ya Musty sorry, sorry, is not my fault, to Hamad din namune wlh ko
mace bata isa tanuna mai kunya ba, ni I can’t wait to see his wife with belly maybe aruwa zatasha, yaron
da a bayi yake chanza kaya yayi wanka how he go do the thing now? With clothes on or off”? Zokaga
dariya su ukun kaman mahaukata, ganin suna nema susa shima yayi dariyan babba dashi 40 something
years kawai Ya Mustapa yajuya yafice daga masallacin yace “yan iskan yara” sunma manta duk a
masallaci suke zama sukayi ciki suna gulma suna bude babin Hamadi.
[06/01, 15:27] +234 806 229 2100: 💫UWA KO UKUBA💫
✍💫M SHAKUR
EPISODE 2️⃣💫1️⃣💫
Tsaf Baba ya sanar da Yayan Mom Alhaji Mahmood abinda ke faruwa tundaga kan zancen fyade, wanda
already tun jiya ya sanar dashi awaya dakuma zancen karbe gidan gadonsu datayi, ran Alhaji Mahmood
yabaci yanaso yaje yasameta Baba ya hanasa yace “yabarta tayi yanda taga dama da gidan” sundanyi
magana kafin yawuce shima, Baba yawuce yatafi.
Baba na zaune dakin Gwaggo, Ammi ta shigo, Aya ta shigo, Gwaggo na zaune daketa washe baki, Mamie
ma haka, Baba yace “Aya na aurar da Asmeey!” Dasauri Aya ta kalli Baba tace “Baba Asmeey”?
Gyadamata kai yayi yace “ba’a dade da daura aurenta ba anan masallaci sabida inaso jibi su Yaya da
Gwaggo suka tashi wucewa su tafi da ita” ahankali Aya da gabanta ke fadi tace “waye mijin Baba”?
Murmushi Baba yayi yace “Hamadi!” Murmushi Aya tayi saikuma tayi wata cute dariya sanin Hamadi
sarkin kunya takalli Mamie tasake murmushi Mamie ma haka, Baba yakalli Gwaggo yace “Gwaggo bance
ki fitar da zancen nan ba Asmeey y’ata ne nakuma aurar da ita na sanar da Baffan ku Aya Alhaji
Mahmood hardashi wajen daurin aure, zuwa gobe idan Asmeey tadan sami karfi da kyau zan sanar da ita,
kafin kitafi inaso keda su Ramla ku hadamin kayanta tsaf da credentials nata da komi nata zaku iya
ciremata kaya kala biyu da zata saka gobe da shi jibin tayi tafiya, sauran zansa akai mota yau din nan
dasauri Aya tace “toh Baba” Ammi tayi murmushi tace “Allah sanya alheri Mamie” Mamie tace “Ameen
Ameen nagode” dan hira sukayi Aya sai wani dadi takeji.
Ranan sai yamma Ya Aya tatafi sai alokacin Asmeey tafara jin damuwa bataga Mom ba tana nan saita
fara tunane tunane Ya Hamad ma tadanyi shiru saita kalli kofa shima bata gansa ba duk saita farajin ba
dadin Munir ya shigo yana wani murmushi yahayo gadon yace “Asmeeeyyyyy” dan hararansa tayi tana
turo baki tace “sunana kake kira kai tsaye” dariya yasake yi yace “I am just happy sabida ke” “ni?”
Asmeey tadan tambayashi dasauri yace “wai Nana” dan murmushi Asmeey tayi bata kara magana ba
tadaura kanta kan pillow tana kallon yanda yake taba wayansa yana Instagram sai kawai Mom tasake
fadomata arai tace “Munir Mom na side dinta?” Yana jinta Munir yayi banza da ita hannunta mai lafiya
tamika ta taba Munir tace “Munir Mom fa”? Batare daya kalleta ba yace “kije takarasa karya dayan
hannunki duka kinga saiki huta” shiru tayi bata sake cewa komiba kanta na kan pillow tana kallon
wayansa tashiga lumshe idanu ahaka bacci yayi awon gaba da ita.
Sai wajajen 11 nadare yashigo gidan kawai dan kar ace this and that ne da yau yakoma Kano sabida
kunya shigowa gidan yayi yahayo sama zai shiga dakinsu Abba yace “Hamad” dago kansa yayi yasauke
yace “na’am” wucewa yayi gaban dakin Abba daya shiga yabisa abaya Mamie na zaune tana kallon wani
shiri da akeyi a tv takalli Hamad din daya kasa kallonta kasa akasa yace “Mamie ina yini” “sannu da
dawowa” Mamie ta fadi, Baba yadauki bandir na 1️⃣k din yadago yace “gashi dazu Baba yazo nemanka
yabaka bakanan, sadakin Asmeey ne karike mata idan tadan sami lpy saika bata lokacin muna kano”
kallon kudin yayi saiya kasa karba yasake sauke kansa kasa Abba yace “ha’a wai ba sako nake baka ba
koko cewa nayi kudin naka ne? Kudin matarka ne karba kaje ka ijiye” yana ahaka kansa akasa kaman mai
tsoro yadaga hannuwansa yamikama Abba duka biyun yakasa dagokai saura kadan Abba yayi dariya
yasamai kudin a hannu Hamad ya karba kaman flash yajuya dasauri yafita daga dakin, dakinsu yawuce
ahankali yabude kofan bakaramin dadi yaji dayaga Hameed na bacci ba shigowa yayi yamaida kofan
yarufe yatafi wajen akwatinsa yaduka yasaka kudin achan kasa sannan yatashi yafada bayi yafito yahau
kan dadduma sannan yadawo gadon ya kwanta yayi shituuuu ahaka bacci am yayi awon gaba dashi.
Surutun Gwaggo ma yau yasake tadata daga bacci bude idanu tayi ahankali Gwaggo na saman kanta
tana tafamata uban yawu a hannu wai addu’a take dauke hannunta tayi tana turo baki Gwaggo tace
“bazaki bari nagama miki addu’a ba bakiga kin denajin zafi ba” ahankali tace “ni har yanzu zafi yakemin”
baki Gwaggo tasaki tace “ahhhh lallai kin dace da Hamad dan bakin halinku daya Asama, ohh ni Allah
baya amsan adduata kenan ko bakina baida tsarki” tashi tashigayi Gwaggo tace “wai bazaki zauna
najarasa ba” ahankali tace “ni fitsari nakeji” tawuce bayi Gwaggo tabita da kallo tace “hartadan fara
kumari” zaki iya tsarkin da hannu daya konazo namikin tsarkin?” Juyowa Asmeey tayi ta kalli Gwaggo
tace “huu’um” Gwaggo ta kwashe da dariya tace “ai shikenan jeki abinki nima daman nayi maganan ne
amman ina tunanin warin dazan shaka idan kin hada da kashi” maida kofan tayi dasauri ta rufe tafito da
alwala tazo tahau dadduma ahankali take salla da hannun.
Yauma haka aka wuni agidan Hamad baya nan only God yasan ina yake zuwa ansan he will definitely do
that so babu wani cikin bothers dinsa daya nemesa.
Yau all through Gwaggo na dakinta hakan yasa Asmeey takasa zuwa wajen Mom but zuciyanta na zuci
zucin tunanin Mom, sai bayan Isha’i Gwaggo tasa Mamie takamata ta kaita kasa dantai bacci da asusuba
zata tashi tahada kaya tunda Allah baiyi zuwansu kauye ba sabida ciwon yarnan Asama.
Sallama Baba yayi hakan yasa Asmeey tadago kanta ganinsa yasa tashiga kokarin tashi dasauri Baba
yakarasa wajen gadon yakai hannunsa yadagata yana saka mata pillow abaya yace “sannu ya jikin”?
Ahankali tace “dasauki Baba” zama yayi bakin gadon yana facing nata yakai hannunshi ahankali yadauki
hannun nata da aka kulle yana kallo yayi shiru fuskanshi yayi wani iri kasan he’s hurting hakan yasa
gently Asmeey tace “Baba bayamin zafi yanzu wlh” dan kallonta yayi har yanzu fuskanta bai dawo daidai
ba kana ganinta kasan taci duka wlh, sai yaji kaman Allah zai kamasa for all the pain she went through,
Asmeey is the most beautiful daughter dayake dashi mai kyawun hali da hakuri da biyayya she’s going
through this pain duk baisani ba and yana gidan, ijiyan zuciya ya sauke yace “mesa baki sanar dani kalan
dukan da Mamanki ke miki ba”? Dan zaro idanu tayi tace “Mom bata wani dukana Baba sai once in a
while kawai idan na bata mata rai ne”lumshe idanu Baba yayi yabude yace “naga jikinki Husna, i saw
duka dukan, i saw hands naki” sauke kanta kasa tayi da sauri lips dinta yashiga rawa chan tace “nike
mata laifi Baba” ajiyan zuciya Baba yasauke anatse yace “Asma’u” hakanan taji gabanta yafadi tace
“na’am Baba” ahankali Baba yace “jiya da rana bayan sallan azahar na dauramiki aure da cousin dinki,
Yayanki Hussain, Hamad!” Wani wawan faduwa gabanta yayi dasauri takalli Baba gabanta na bugawa
beyond measure dan har Baba saida yagani yasa hannu yakama hannunta anatse yace “I dont know
mesa mahaifiyarki kemiki abinda take miki but ban haifeki dan wani ya kashemin ke ba and Munir ya
sanar dani komi dan yajuyo maganan datake gayamiki adaki kan tamiki miji da yanda tazage yan uwana
harda kiran mijin naki mara aiki da abinyi”Baba yace “amatsayina na mahaifinki ni da Yayana muka hada
aurenki da Hamad” kawai sai hawaye sharrr ya sauko daga idanun Asmeey tasauke kanta kasa tanaji
kaman mafarki take Baba yace “sadaki dubu dari nabawa mijin naki yarike miki kudin kukaje kano zai
baki, gobe da izninin Allah zaku tafi Kano aduk sanda komi yazama daidai za’a tsara lokacin da za’a kira
mutane ayi yinin biki wato walima, dazu nasaka yayarki Aya tahada kayanki tsaf itada Ramla ankai mota”
Baba yasauke ijiyan zuciya yana kallon ya da take share hawaye Baba yace “iya abinda nasani shine kin
gama university Asma’u, zancen zuciyanki law school lies a tafin hannun mijin naki sabida shine keda iko
dake, idan yaga dama yabarki kije idan yaga dama yahana shine mai iko dake yanzu” Baba yasake yin
shiru sannan yakai hannunsa yakama hannunta ahankali yasake daura dayan hannunsa saman kanta
yace “Asma’u nasan yanda kikeda tarbiya da natsuwa mijinki Hamad for now baida wani tsayayyen aiki,
ki zama mata mai tsoron Allah da kaunar mijinta domin Allah, kada ki takuramai da siyan abubuwan
kyalekyalen duniya siyamin kaza, siyamin kaza, ki zama mai godiyan Allah kiyakuri da abinda ya iya samu
yabaki, kada kice dan kinga matan yayyinsa da kaza sai kema yamiki kaza, wata rana sai labari shi arziki
na Allah ne, kuma yana bawa duk wanda yaso, Hamad nada kwazo zai kula dake iya gwargwado, iya
karfinsa kuma kinji” gyadamai kai tayi tafashe da kuka maganganun namata wani iri, Baba yace “Hamad
baida gida, yanzu kukaje kano a flat din Abba da Mamie zaku zauna kafin agama gina flat dinku, Abba
Yayana ne kuma matsayin mahaifina yake bazai taba bari ki cutu ba hakama Mamie, ki kula dasu Asmeey
kinga sun soma gajiyawa jiki ya tsufa ki zama mai taimaka musu da abubuwa da dama tundaga kan girki
da sauransu kinji Asma’u” Baba yasa hannu yaciro wayanta da Ramla takawo mai dazu yace “ga wayanki
nan nacire sim naki nada zan ijiye wajena zuwa nan gaba, nasaka miki wata SIM card danake dashi ki
dinga amfani dashi, Asma’u ina sonki nayafe miki duk wani abu dakika tabamin da Wanda na sani da
wanda ban sani ba sannan ina neman yafiyanki ina matsayin mahaifinki but i couldn’t protect you kalleki
yau Asma’u kiyafema Babanki kinji” dawani sauri Asmeey ta rungume Baba tana kuka murya kasa kasa
tace “Baba bakamin komiba baka tabamin komiba dan Allah kadena rokona Baba” tafashe dawani irin
kuka, Baba yadagota yakai hannu yashare mata fuska yace “I am sure babu wanda zai kara dukanki
agidan Yayana, Mijinki, Yayinki da Abba will shield you Asma’u thank you for being a good daughter to
me, me rufama iyayenta asiri, mai hakuri da juriya da kwazo, ina alfaharin zama mahaifinki” kara
rungume Baba tayi tana kuka, Baba yayi murmushi yana shafa bayanta yace “go and start a new life
kinji”? Dagowa tayi ahankali takalli Baba tace “Baba Mom tas….”? Baba bai barta ta karasa maganan ba
yace “mahaifiyarki mahaifiyarki ce har abada Asma’u but kaman yanda banda wani iko akanki yanzu
itama batadashi kina karkashin Hamadi yanzu ba muba kinji” gyadama Baba kai tayi gabanta na faduwa
ita kadai tasan ya zuciyanta ke mata sai wajejen 11 Baba yabar dakin ta kwanta tai shiru tana kallon
sama jitayi bakinta ya bushe dasauri tatashi zaune da kyar takalli side drawer tabi duka dakin da kallo
babu bottle water da dane data kira Mamie but hakanna saitaji tanajin nauyinta bamataso su hada ido,
ahankali tasauka dagakan gadon tamike tsaye tunda Baba yafita bataji any motsi ba maybe kowa yayi
bacci tunda gobe zasuyi tafiya, daya daga cikin gown din Ya Aya tasaka red mai botura agaba ya tsaya
mata a gabada guiwa but baikai har kasa ba, babu dan kwali akanta ko hula, rigan short hand garesa,
slippers tasaka tabude kofan ahankali tafito tana tafiya, hannunta always feels kaman kaya sabida nauyi
ko na daurin da aka matane oho, staircase tahau tasauka a first matakalan da kyar tana shirin sauka na
biyu…. “Ina zaki?” Chak Asmeey ta tsaya sabida muryan Ya Hamad dataji da kamshinsa duka at the same
time, wani kalan nauyi taji tajuyo balle ta kallesa yau, sai kawai tasauke kanta kasa lips nata yahau rawa
kaman yar baby tace “ruwa zanje kitchen na dauka” murya ciki kaman baiso yayi magana yace “go inside,
I will bring it for you” gyadamai kai tayi still taki kallonsa ta taka bene dayan data sauka akai tahayo nan
falon sama tawuce dakin Mamie, Hamad dake sanye da joggers ash color yana sanye dawani black tshirt dayamai bala’in kyau yawuce yasauka kasa, kitchen ya shiga yadauko bottle water marasa sanyi
guda biyu yahayo sama, kofan dakinsu yakalla sannan yawuce dakin Mamie ahankali yabude kofan
batare daya bar door din yayi kara ba ya shiga ciki.