Showing 27001 words to 30000 words out of 59470 words

Chapter 10 - UWA KO UKUBA MShakur HAUSA NOVEL

M SHAKUR   

28 Mar 2025

3090

Mom ce ta mareta yazatayi? Mom ai saita kusan kasheta, baya magana so ba lallai
yafada ba but idan yafada fa? Sai lissafi daban daban take aranta ana mata kitson, kusan 10mins da
zamanta awajen hakanan kawai ta dago kai ta kallo gaban flat nasu karaf suka hada idanu yabude kofa
yafito daga flat dinsu Ya Hameed biyedashi dasauri ta dauke kanta kasa shima haka baimasan mesa ya
kallo wajen bishiyan da baida wani nisa da gaban flat dinsu ba yawuce abinshi, hakanan Asmeey taji
takasa daurewa samin kanta tayi da sake juyowa tabishi da kallo tundaga yanda yake tafiya anatse
kanshi akasa Ya Hameed kuma na danna waya yana magana dashi, “he’s o quiet” tafadi aranta, saida ya
shige flat dinsu sannan tadauke kanta tayi shiruu bamatasan mesa taki dawowa daidai ba in something
daya faru within just 1min a flat dinsu, hancinta takai wajen kafadanta sai taji kaman tana kamshin dataji
a jikinshi, dasauri tace “Mairo dan Allah kunji ina wani kamshi?” Mai kitson tace “kamshin mene
Asmeey?” Tsare mai kitson tayi da idanu dan sun dakatar da kitson saitai shiru wondering why is she

even asking this kind of question sai kawai ta dauke kai dasauri tace “uhm ni banmasan mesa nai
tambayan ba barshi kinji” dan dariya mai kitson tayi tace “ai ke koda yaushe kina kamshi bantaba zama
namiki kitso naji kina wari ha Asmeey kin tuna nataba rokonki turare har kika bani” dan murmushi kadan
tayi hakanan sai ta manta she’s sad ma sai tunane tunane kawai take.

YA HAMAD YASAN MARINTA AKAYI??💫
💫UWA KO UKUBA?💫

✍💫M SHAKUR

EPISODE 💫
Wuraren biyar saura aka gama mata kitson dayayi yayi bala’in kyau, yan kanana aka yaryada mata su, sai
fuskanta da goshinta suka fito sosai, ga gashin yayi tsayi, su Nana daman an gama musu lallin nasu da
komi itane daman tarage kuma Mom tace bazatai lallen ba, mai lallen tace “Ammi tace idan an gama
kizo ki karbo mana abinci” gyadamusu kai tayi ta tashi tareda sa dan gyalen nata ta yafa tarike na sa a
hannunta tawuce backyard inda Ammi take tareda Mama dasu Anty Nafisa da Anty Mims da Anty
Meena matan su Ya Mustapa Ya Abdullahi da Ya Faisal dakuma matan dake asalin aikatau din da aka
dauko, Anty Nafisa tace “an gama kitson Asmeey?” Gyadamata kai tayi tace “eh an gama Anty” Mamie
ta kalleta tareda murmushi idanunta suka sauka kan hannayenta da kafafunta dasuke nan farare kal tace
“lalle fa? Kowa harmu tsofaffi munsha lalle balle ke yar yarinya” hannunta ta kalla saikuma ta kakalo
murmushi batai magana ba, da zuciya daya Anty Mims matan Faisal tace “ko masu lallen basu iyaba ne?
But naga wanda akama Nana yayi kyau ko Mama”? Dasauri Mama tace “yayi kyau sosai kam daga jan
har bakin ai saisa duk babban salla basu yarda suyi lalli a Gombe saisun iso nan Bauchi” dan dago kanta
Asmeey tayi ganin duk kallonta suke yasa cikin innocent voice tace “bayan salla zanje law school saisa
banyiba is not allowed a law school” tana maganan saiga hawaye nataruwa a idanunta da sauri tajuya ta
goge hawaye saikawai tawuce dasauri muryanta nadan rawa tace “Ammi wai akai musu abinci masu
lallen” tabar backyard din all of them knew she was crying so no one bothered to call her back wucewa
tayi tafito daga backyard din ganin hawayen yake tsayawa yasa tayi chan parking space nasu dan gidan
ko’ina da mutane dukawa tayi gaban daya daga cikin motocin wajen bawai kuka take wiwi ba but
hawaye ke fitowa daga idanunta sosai sai sharesu takeyi da bakin gyalenta, she’s feeling sad again wlh,
she’s not happy, tasan wani yaganta tana kuka can be a problem especially idan Mom tasani, bude kofar
mota akayi hakan yasa tadago rinannun idanunta da sauri dakuma tsoro, Munir tagani yafito daga
motan Abban Bauchi, maida kanta tayi ta sauke kasa ganin shine tana goge fuskanta, karasowa wajen

yayi cikeda damuwa saiya duka gabanta yace “wat happened Ya Asmeey? Mesa kikazo nan kika boye
kina kuka? Mom ta dakeki ne”? Kallonshi tayi yanda yake kallonta cikeda damuwa dakuma so sai kawai
yanzu kukan yataso mata tafashe da kuka sosai tana kallon Munir, ja idanunshi yayi cikeda bakin ciki
yace “Mom ne ko?” Gyadamai kai tayi cikin kuka tanunamai hannuwanta tace “kowa yayi lalli agidan nan
banda ni Munir” har wani daci zuciyan Munir yakeyi, kowa is happy agidan nan banda sister shi, kowace
yarinya in this house da mata tayi lalle banda sister shi cikeda bakin ciki yace “hala sabida shegen law
school din nan ne, komi law, law, law, wlh I hate abinda Mom keyi” tashi yayi yace “bari naje na gayama
Baba yaza’ayi kowa yayi lalli har ita Mom din an mata banda ke sai kace gobe ne law school din look at
you salla ake but you’re the only one that is sad today with red kumatunki and it’s all her doing” dawani
irin sauri Asmeey tarike hannunshi tace “Munir karkaje” a zuciye yace “sainaje ki banni naje kafin masu
lallin su tafi ba’a miki ba” hawaye gangarowa daga idanunta sukayi cikeda tsoro da tashin hankali tace
“Mom will be angry Munir, I don’t wanna be the reason for her anger dan Allah kada kaje please please
kaji kaga ni nama dena kukan I’m not sad wlh, dan Allah karufamin asiri” tashiga share fuskanta da
gyalen tana kallon Munir da red eyes nata na kuka, Munir yamata wani kallo kaman ya maketa yana
hararanta sai kawai tafashe da dariyan dole dan kawai ya yarda dan tasan halinshi tace “haba Nana
boyfriend” zaro idanu Munir yayi yahaderai tareda fizge hannunshi yace “kika kara hadani da wata Nana
that small girl ranki zai baci” hararanshi Asmeey tayi ganin yanda Allah yama Munir shegen son girma
tace “kaganta wani jin kanka kake eh Dr Munir kana wani iyayi da kankamba I know u love her” yowa
kanta Munir yayi dasauri tawani kurma ihu na tsoro. “Babaa!” Ta kwala kara, chak Munir ya tsaya ta
kwashe da dariyan tsokana taredamai gwalo tace “Nana’s boyfriend” tawuce flat nasu da sauri tana
tafiya tana waigowa dan karya biyota kadakai kawai yayi yakoma cikin motan ya zauna yace “Yaya yafara
aiki?” Gently Hamad dake screwing headphone da Munir yabashi yatayashi dubawa cus ya daina aiki ya
kalleshi saikuma ya maida kanshi kasa baice komiba, dan fuzar da iska Munir yayi kadan yace “Ya
Hamadi Gwaggo never tells you no dan Allah zaka iya gayamata tasa masu lallen nan suma Ya Asmeey?”
Dan dago kai Hamad yayi yamai wani kallo dayasa Munir ya sassauta murya yace “pleseeeee Ya Hamadi
Mom ce tahanata yin lalle wai sabida law school dazata bayan salla and is not really immediately bayan
salla fa sometimes it takes weeks karfin list din yafito but tahanata yi, kowa yayi lalle is only my sister
that is looking different” yasake dan shiru yana kallon Ya Hamad dake abinda yakeyi cikeda damuwa
yace “kaga Ya Asmeey always got my back, always protecting me I feel like a bad brother nakasa doing
anything for her” yayi maganan yana kallon Hamadi dayayi kaman badashi yake magana ba daidai
yagama komi yadauki wayanshi ya kunna yayi connecting yasa Qur’ani ganin yayi yasa yamikamai anatse
yace “take” karba Munir yayi yana murmushi sosai yace “wow thank you so much Ya Hamadi harzan
wurgar fa nace tunda zakuzo salla bari na barshi tukunna i know yanda kasan this stuff” bude kofa
Hamadi yayi yafita daga motan yawuce flat nasu Munir yabishi da kallo yanda yake tafiya ahankali you
can never understand Ya Hamadi, he hardly talk, baya wasa da yara, but then he’s the most intelligent
person daya taba sani arayuwanshi, Ya Hamad yasan computer kaman maye, and he knows anything
wayan wuta, anything technology wlh yasani ya iya he can fix anything, silent genius ne.

Flat dinsu ya shiga zuwa dakinsu da babu kowa, ko ina Hameed yayi oho?Bayi yafada yayi wanka yafito
daure da towel yawuce yasa key a kofan sannan yabude akwatinshi kayanshi yaciro komi yasa a

wardrobe Hameed yasamai duk abinda yake bukata ya shirya tsaf sannan yaciro laptop dinshi daga
bagpack ya kunna yana zama kan gado saikuma yayi jim kafin yakalli wayanshi dake gefenshi sai kawai
yadaga wayan…….
Gwaggo na zaune anan falo tana surutu duk wani abinda yafaru a Kano yaran nan take bama labarinshi
ko gajiya batayi ba, yaran suma sun zagayeta anajin dadin labari harda na takwaran da aka mata
wayanta yahau ringing da sauri ta taba wayar dake cikin lalita akasan zanin tace “yooo wa yake kirana ko
su Munarin Kauye ne”? Warware zaninta tashiga yi tasa hannu taciro wayan daga lalita takalli screen din
kaman ta iya karatu tace “tohh wannan lamba ce batada suna” ta danna dauka takai wayan kunnenta
murya ciki ciki akufule Hamad yace “kuma karki kira sunana! Yarinyar chan batai lalleba” yana maganan
ya katse wayan Gwaggo tace “wace yarinyar? Ham….” Saikuma tai shiru da sauri tuna yace karta kira
sunansa, tashiga bin yaran da kallo daya bayan daya tana sauke wayan daga kunnenta kawai tazare
idanun ta mike tace “duk kutashi kuzo ku nunamin kunshin sallan ku daya bayan daya”faduwa gaban
Asmeey yayi dake zaune kusa da Ramla cus tasan Gwaggo taga batai lalle ba she will cause trouble tai
maza ta mike zata wuce Gwaggo tace “zonan kafin na cimiki mutunci Asama” tsayawa Asmeey tayi tana
boye hannunta abaya, Gwaggo tace “mehaka naga kafafunki farare tasss kaman na zabiya! Jibi yara anan
ku takwas gasu Hajar hudu ku shabiyu, maza sunsha aski mata sunsha lalli banda ke sai kace yar riko” har
lokacin Asmeey taki nuna hannunta ahankali tace “Gwaggo makaranta zani bayan salla saisa an hana lalli
a makarantar” dakuwa Gwaggo tamata ta daga murya tace “kinci mai garinku da makaranta yo ko kirista
suna zuwa hutun salla balle ke musulma ke baki gajiya da boko sai kace uwarki iyyee? Kinada tabbacin
zakiga sallan badi? Babban salla guda hannayenki da kafafu fari sol kaman aljana ina masu lallen wuce ki
kiramin su Amina idan basu tafi ba, ke ko sun tafi sai an kirasu” wucewa Amina tayi da gudu ta tafi,
Asmeey gabanta na faduwa dumdumdum tace “Gwaggo dan Allah ni bazanyiba ni ki barni” tai stairs da
gudu Gwaggo tace “kiramin ubanku Munir” dan shima Munir na falon, tsayawa Asmeey tayi tajuyo da
sauri ta kalli Munir daidai yawuce abinshi da sauri Hamda ta sauko tazo wajen zatai magana Baba ya
shigo ga Amina da masu lalle da kitso sun shigo falon suma, Gwaggo na daga murya sosai tace
“Muhammadu Sani tun kana dan kankani kataba ganin salla tazo da bansa kunshi ba?” Dasauri Baba
yace “a’a Gwaggo” cikin fada Gwaggo tace “toh wani dalili zaisa kaf cikin yaran gidan nan Asama ce mara
kunshi sai kace wata bare wannan mukai baki ai sai ace mun tsaneta ne ba yar gidan bace” kallon
Asmeey Baba yayi da sauri ta sauke kanta kasa zaiyi magana sukaji muryan Mom cikin harshen turenci
tace “you know she’s going to Law school bayan salla Alhaji that’s why”kafin Baba yayi magana Gwaggo
tace “to yar boko ke duk inda kike saikin nuna mutanen dake wajen basusan komiba kene kikasan komi,
ke ba abin kunya bane yarki ta fita daban cikin sauran yara? Komi boki komi boko da boko za’a lahira
dazaki hana yarinya yin adon salla? Yin ado da salla sunna ce danko Annabi tsira cewa yayi ranan salla
musa kaya mafi kyawu muyi ado mai kyau amman ina zakisan haka sai ilimin yahadu kika sani bana
arabi” Mom zatai magana strictly Baba yadaga mata hannu hakan yasa tai shiru, cikeda girmamawa Baba
yakalli Gwaggo dake huci yace “Gwaggo kiyikuri yanzu za’a mata” cikeda rigima Gwaggo tace “ai gamasu
lallin nan na aika Amina taje ta kirasu anan gabana za’a mata kafin yar boko ta zaga tahanata yi kekuma
zauna da shegun idanunta masu kama dana jemage” tanuna Asmeey da atsorace tadan dago kanta ta
kallo Mom data mata wani mugun kallo, da sauri ta sauke kanta kasa Mom tajuya daga sama zata koma
daki Gwaggo tace “saukowa zakiyi kije kema kisa hannu abayan gida ayi aiki ba daraja kikafi sauran dake
wajen ba bakina kima kika fisu ba dan sunfimini ke so dubu” wani kallo Mom tama Gwaggo saikuma ta

kalli Baba daya mata kallon baison rigima tayi abinda tace yajuya yafita itama Mom din badan taso ba ta
sauko tawuce tafita, Gwaggo tabita da harara, ran Munir fess kaman ya rungume Gwaggo dan dadi aka
shiga yima Asmeey lallen dake cikin tsananin tashin hankali duktai zuru zuru sauran yan uwanta harda
Munir suka zagayeta suna kallon yanda ake lallen Munir harda matsar da kanninsa baya karsu gwaljema
yayarsa lalle, kana ganin Asmeey kasan hankalinta baya jikinta Gwaggo ta buga tsaki tace “Allah
yahadaku da jarababbiyan uwa ga yara har yara Allah yabata inba haukan bama yarinya haka kaman
Asama wani yahanata yin lalle ba abun tai fada dashi bane amman ita ke hanawa da kanta yarinya
kyakkyawa haka son kowa kin wanda yarasa” itadai Asmeey ta saukar da kanta kasa.
After magrib aka gama lallen gabaki daya both baki da ja, ta kwanta anan kan doguwan kujera dan ba
halin salla suna kallon film tareda sauran yaran, Gwaggo kuma ta fita tsakar gida wajen su Baba tana
magana dasu ganin an gama lallen, bude kofa akayi aka shigo Ya Mustapa ne da sauri yaran sukai
wajenshi suna gaidashi Ramla ya kalla yace “come here Ramla” dasauri Ramla ta taso taje wajen kofa
dayake, jakunkunan ice cream din hannunshi yabata yace “gashi ki raba muku” gyadamai kai tayi
dukansu sukai godiya yawuce yafita Ramla tashiga rabon ice cream din na supreme manyan robobi
tanaba kowa nasa, tazo gaban Asmeey hakan yasa Asmeey tace “kibani strawberry” Ramla tarike last
strawberry tace “nawane shi vanilla zan baki” dasauri Asmeey tace “ai kafin ki dauki strawberry nace
miki ni shinakeso” Ramla tace “to baza’a bayar ba” kallon Ramla Asmeey tayi cikin ido sai kawai ta dauke
kai tace “ki hada duka ki shanye banso” ran Ramla baci yayi jin abinda Asmeey tace, cikeda masifa tace
“ohh kullum akaina ne kikeda bakin rashin kunya ko”? Dasauri Nana tace “Ya Ramla kiyakuri” tashi zaune
Asmeey tayi daga kwancen ta harari Nana tace “wayace kisa baki? Da ke akayi?” Akufule Ramla tace
“wai ba Baba yace kidenamin rashin kunya ba? Dani kike magana kaman kinyi da sa’an ki? You’re a rude
stubborn girl wawiya kawai” ran Asmeey yabaci jin zagin da Ramla tamata tace “ni dai ba wawiya bace”
hannu Ramla tasa ta dungure mata kai saida Asmeey takoma baya tsabagen yanda Ramla ta dunguruta
tace “okay nine wawiyan kenan? Ki kara magana kiga wlh sai kinsha mari akan kumatun nan naki daya
saba shan mari”dasauri Yusra tai wajen kofa tabude tafice ganin Ya Ramla da Ya Asmeey na chachan baki
akan ice cream….
Ganin bataga su Baba ba yasa tai wajen motoci inda taga Ya Mustapa tsaye tareda Ya Hamad tai wajensu
tana haki tace “Yaya ga Ya Ramla chan da Ya Asmeey suna fada a falo sabida ice cream” “because of ice
cream”? Ya Mustapa ya maimaita, gyadamai kai tayi tana zaro idanun gulma tace “she prefers
strawberry itakuma Ramla tace vanilla zata bata tace bataso shine Ya Ramla tashiga dungure mata kai
tace mata wawiya wai zata mareta akan kumatunta da suka saba shan mari” Ya Mustapa yace “wuce
muje” binta yayi zai wuce daidai nan sai ga Mom data zagayo daga backyard tashiga flat din hakan yasa
Ya Mustapa yace “ga Mom chan tafi kawai bari basai naje ba” wucewa yayi yakoma inda Hamad yake
tsaye dan shi baiyi motsi ba daman.
Mom na shiga dakin tagansu suna chachan baki hade giran sama da kasa tayi yaran kowa yayi tsit kaman
anga dodanniya gaban kowa na faduwa harda ita Ramlan ganin Mom, maida kofan Mom tayi tarufe
takaraso falon yaran kowa na komawa baya, Ramla ta kalla strictly tace “what is going on here”? Ice
cream na hannunta Ramla ta nuna mata tace “Mom Ya Mustapah ne yazo yabani ice cream yace
narabamana, kingani nabama koya shine nazo naba Asmeey this Vanillah agaban kowa agaban yaran
nan tahaumin rashin kunya harda cemin wawiya wai kawai dan ban bata strawberry b……” Kafin

takarasa maganan Asmesy ta tari numfashinta muryanta na rawa tace “wlh Mom karya takemin itane
tafara cemin wawiy……..” tassssssss! Mom ta dauke Asmeey da lafiyayyen mari da saida ta ijiye
kafafunta na lallen kunshi akasa saman tiles hands nata suka kwalbe ajikin chair, ita kanta Ramla saida
kirjinta yabuga bata taba kawowa Mom zata daki Asmeey over this silly ice cream issue ba, idanun
Asmeey harwani baki sukayi gashi a left side Mom tamata marin inda tamata dazu da safe, Mom namata
wani mugun kallo cikin kakkusan murya tace “is this tarbiyan dana baki? Are you stupid kike kiran
yayarki dake gaba dake makaryaciya! Are you stupid Asmeey!” Mom ta daka mata tsawa da saida falon
ya amsa idanun Asmeey sukai jaaa ga duka kannenta awajen, she felt embarrassed, baki tabude zatai
magana amman kuka yasa ta kasa magana cus tana bude baki zata fashe da kuka ga kanninta awajen,
Mom dake huci sosai tana kallonta tace “okay I’m talking to you kin sauke kanki kasa ni ga shashasha
eh?” Dago kanta tayi ta kalli Mom sai kawai jikinta yahau rawa ganin idanun Mom tace “so….s……”
saikuma sorry yakasa fitowa sabida kuka, ran Mom yayi masifar baci tawani fizgo gaban rigan Asmeey
haka yarinyar ta taso fuuuu kafafuwanta sukai daba daba akasa skirt nata ya sauka kan black lallin Ramla
naso tabata hakuri cus she’s regretting telling Mom amman tsoro take ahada da ita, Mom tashiga daga
murya tana jijjiga Asmeey yace “don’t you know how to apologize Asmeey ko saina daddakaki zaki bada
hakuri” rawa bakinta yashiga yi idanunta sunyi fiki fiki sun kankance daidai lokacin Gwaggo tabude falon
ta shigo tundaga lallin da taga ya kwalbe akasa ta shiga kallo da yanda Mom tarike yarinyar tana kallon
yanda hannayen Asmeey da jikinta ke kyarma kawai Gwaggo ta kurma mahaukacin ihu tana bude kofa
da saida gidan kap ya amsa. “Ihuuuuuuuu zatai kisan kai jama’a ataimaka zatai kissan kai!” Tundaga su
Mamie da Ammi dake backyard dasu Ya Mustapa da Hamad dasu Baba dake masallaci harda Ustaz da su
Ya Hameed saida aka fito da gudu ana yowa flat din jin ihun Gwaggo, Mom ta dauke kai daga kallon
Gwaggo dake ihu babu ko dar a zuciyanta ta shake wuyan rigan Asmeey dake kyarma tace “I said
apologize now!” Ta daka mata tsawa ahankali cikin muryan ban tausayi jikinta na rawa sosai tace
“so….so…sorry” “Sorry Wa ne”? Mom ta sake dauketa da mari a same kumatu for the second time
mercilessly, Gwaggo tai ihu ta taho tana ture Mom tace “wai ke yarnan bataki bace ko yar riko ce?”
Mom dako gezau batayi ba da tureta da Gwaggo keyi tana rike da Asmeey tace “speak!” Bakinta na wani
kalan rawa tace “so……sorry Ya Ramla” daidai lokacin su Ya Mustapa na shigowa falon Ya Hamad biyeda
shi, awani kalan zuciye Mom ta hankada Asmeey saitin center table dake tsakiyan falon da mugun karfi
sai kasa tamugun buge da center table

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login