Showing 15001 words to 18000 words out of 76905 words
yahard'e bakinsu gu d'aya yafara tsotsa tareda saka harshensa yana tsotse yawunta, takarfin tsiya yakaita kan kujera ya kwantar sannan yasaka hanunsa yakai kan bobss d'inta yafara matsasu da k'arfi, dadika k'arfinta ta yunk'ura ta tallafeshi tai jifa dashi k'asa sannan ta Mike tsaye tana mayarda numfashi,,,....
Cikin tsintsar masifa tawanka masa kyawawan marika har biyu sanna tanunasa da yatsa tace "Allah yafika mugu azzalumi hak'arka bazata tab'a cimma ruwa a kainaba" tana gama fad'ar haka tajuya tafita tabarshi zaune akan carpet,,,"....
Tin daga wannan ranar faruk baisake zuwaba koma yazo bazaiga MUFIDA ba dan bata fitowa a waya kuma tasaka number nasa black list,,,.....
A b'angarenta kuma kusan kowanne lokaci cikin kuka take da takaicin auren faruk dazatayi gakuma k'aunar MUJAHID dake dad'a k'aruwa acikin zuciyarta tarasa yazatayi da rayuwarta gashi ba Amira da nusy dake bata shawara munira yarinyace bakomai tasaniba mubina da momy kuma dama basune abokan shawarartaba dady ne dady kuma yanzu basuda zama kullum sai 8pm yake dawowa idan kuma yadawo agajiye yake yana buk'atar hutu, haka dai tacigaba da rayuwa cikin k'unci dikta rame tai bak'i batacin abincin kirki sai zaman kad'aici da tinani,,,....
Wata ranar assabar ne koda munira tashigo d'aki taganta tana aman jini kwance a k'asa, cikin tashin hankali taje da gudu tafad'awa dady da momy, a rikice dady yazo yana zuwa yaga halinda take ciki kawai yad'auketa yafita, yana fita yabud'e mota yasakata baijira driver yazoba bashida ko takalma yashiga momy ma tashiga yatada motar sai hospital,, wata k'asaitacciyar hospital yawuce da'ita mai suna EQUITY SPECIAL HOSPITAL, dazuwansa yai parking yafito yad'auketa yai cikin asibitin,,,"....
Kasamcewar vice governor kowa yasanshi danhaka nantake cikin gaggawa aka karb'eta akawuce I.C.U da'ita, tinda suka fita mubina tafito parlor takunna TV tai kwanciyarta munira kuwa carkey tad'akko tabi bayansu,,,....
Saida aka kwashe kusan 1hour akanta sannan aka samu tadawo normal nan sukamata injection na bacci suka doramata drip da jini, bayan likitan yagama sannan yakira dady office yamasa cikakken bayani akan matsalar MUFIDA, hankalinsa yamatuk'ar tashi dajin MUFIDA na d'auke da ciwon hawan jini hypotention, nandai doctor yamasa k'arin bayani akan irin kularda za'adinga mata dakuma medicines d'inda zata dinga amfani dasu,,"....
Saida takwashe sati d'aya ana kula da'ita a hospital sannan aka sallameta,, satinta biyu da dawowa suka koma school,,,....
Bak'aramin jin dad'in komawarsu school taiba saboda zatafi sakewa yanzu kuma zata rage yawan tinani da damuwa dakuma rage tinanin mr man musamman idan tana kallon inda sukai rigima saitaga kamar komai yadawo baya wani lokacin idan tana kallon gunda take parking motarta saitaga kamar MUJAHID fitowa zaiyi tai murmushi sannan tawuce,,,....
Haka rayuwa tacigaba da tafiyarmata cikin k'unci, ahalin yanzu komai na MUFIDA ya sauya gaba d'aya rayuwarta ta sauya kamar ba MUFIDA ba mai jin kai da jiji da kai dakuma masifa tadawo so so silent yanzu, daga class sai gun hutuwa saikuma gida yanzu ko yawo tadainayi, su kansu y'an school d'in abun yabasu mamaki sosai saidai ba halin yin magana dan har yanzu shakkarta suke........
#/Vote
#/Share
#/Comment
```AUFANA for life ```
*I.W.A*🖋
_*TSINTACCIYAR MAGE....*_🌷
_*BY~AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183_
® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚
_*Page 23/24*_
_Note Edited_
_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_
Lokacinda su Amira sukaji anyiwa MUFIDA baiko saida sukai kuka musamman nusy saboda sunsan yanzukam MUFIDA tarasa MUJAHID har abada, tausayin rayuwarda zatayi a gidan mijinta ta rashin sonsa yasa suka zubda kwallah,,,"....
Ahalin yanzu kam karatu suke gadam gadam saboda yanzu final year suke suna gab da k'arewa, hakan yasa yanzu MUFIDA tarage damuwa da yawan tinani sosai saboda kusan kowanne lokaci sunacikin karatu ga tilin lectures dake gabanki basuda hutu hakan kuma yasa tama manta dawani zancen faruk saidai MUJAHID danshi dik lokacinda take zaune itakad'ai zakaganta tai shuu tai tagumi tana tinaninsa dakuma irin rigimarda sukai a baya,,,....
***** *****
Kwanci tashi asarar mai rai yau saura wata d'aya kacal su MUFIDA su kammala degree d'insu danhaka yanzu kusan kullum suna school suna karatu,,,....
Kwance take a parlor munira na gefenta tana danne dannen waya mubina kuma na lambu tana hutawa, su Amira ne suka shigo ta tashi tana dariya suka gaisa sannan suka zauna, nusy takalleta tace "feedom tashi ki shirya yau zamudan motsa kafa muhuta tinda yau weekend ne kuma yaune kad'ai mukeda enouf time" murmushi tai tace "a,a yau dai kice abun ya motsa kenan" tafad'a tana mik'ewa tsaye,,,"....
Amira ce ta kalli munira tace "a,a munira ana nan ana wannan ibadar ta chart ba'ako ajiyewa ahuta adan yi karatu" dariya munira tai tace "aunty Amira ai ba chart ne nakeyiba wani novel ne nake karatu *BARRISTER ALEEYAH* wlh yayi sweet sosai lbr yana torching hert sosai kamar nai kuka nakeji",,,.....
Dariya nusy tai tace "aikuwa bakida aikinyi indai ina kibiye ta novel to hawayenki zasu k'are" MUFIDA ce tafito sanye da wandon Jeans da t-shirt fara anmata zanen flower's bak'i da fari kanta sanye da veal bak'i sai takalma hills masu belt bak'ak'e,,,....
Tana fitowa nusy tace "woww feedom kinga yanda kikayi kyau kuwa inama ace mr man yana kusa na tabbata dasai ya yaba da wannan kyau dakikayi" murmushi kawai tai batace komaiba suka tashi suka wuce, guraren hutawa da shak'atawa suka zaga can sai suka wuce gidan zoo, suna cikin kallon halittun daji sai MUFIDA tahango wasu masoya suna tafiya suna shan love daka gansu kasan masoyan junane,,,....
Kuruuu tai da ido tana kallonsu cikin tsintsar sha'awa a ranta tace inama ace itace da mr man d'inta kai ta tabbata dasaisunfi waennan birgewa, saida Amira ta dafata sannan tadawo hayyacinta suka wuce,,, sai kusan 5pm sannan suka koma gida,,"....
***** ***** *****
Alhmdllh yau takasance Monday kuma itace ranarda su MUFIDA suka fara zana jarabawa ta kammala degree d'insu, zaune suka acikin restaurant sunacin abinci suna firar yanda exam d'in tabasu kashi kamar basumata shirin kanta ba, basuwani jimaba suka tattara suka wuce gida,,,".....
Ahankali suke cigaba da zana jarabawan saidaifa sunashan wuya saboda malam basa tausaya masu gashi kullum biyu sukeyi hakan yasa yanzu basuda zama basuda tsayi any time sunacikin karatu kuma cikin ikon Allah suna samun nasara,,, yau saura biyu kacal suk'are wacca kuma sai ranar Monday mai zuwa zasu zanasu,,,....
Yau takasance Saturday tana zaune waje agun shak'atawa mujallah na hanunta tana karantawa saiga mubina, batareda tace mata komaiba tamik'a mata waya tace "karb'i hamma ne yakeson yin magana dake" tai maganar tana kallon sama alamar jin kai, saida takai aya sannan tad'ago tawatsa mata wata muguwar harara sannan tace "nagayamaki ina buk'atar yin magana dashine dahar zakizo kiman tsaye a ka saboda tsabar kin rainani ko" shekeke ta kalleta sannan tace "Ah kajiman MUFIDA to ai banice nakirasa nace yayi magana dakeba shine yakira dakansa saboda koya kiraki bata shiga" to bazan karb'a ba kuma kitafi kibani waje tinkan na sab'a maki kamanni wallahi ko don kinga ina kyaleki dik irin iskancinda kikeman to ba tsoronki nakeba wallahi yanzinnan sai nai k'asa k'asa dake anan. Sanin halin MUFIDA batada mutunci yasa dole taja kafa tana kumbure kumburen baki tana guna gani had'e da watso mata harara tabar wajen,,....
Around 6pm MUFIDA tahad'a kayanta tawuce gidan Amira saboda tafi jin dad'in karatu a can,,.....
Ranar Monday tin 6am suka tashi sukai sallah sannan suka shiga kitchen suka had'a breakfast sannan suka fito, bayan sungama break suka d'an gyara gidan sannan sukafara shiri, MUFIDA tafara shiga wanka sannan Amira koda Amira tafito tini MUFIDA harta shirya cikin wata tsadaddiyar Arabian gown black color mai d'auke da flower pink asamanta, yaukam tai make up abunda takusa yin shekara batayiba d'an k'aramin bakinta tashafamasa jan baki pink sannan tashafa kwalli da powder kana tafeshe jikinta da tiraruka sannan tai rolling da veal na rigar bak'i,,,,"....
Nantake tsintsar kyanta ya bayyana dikda bawata make up neba tai amma kyanta ya bayyana sosai, Amira tadubeta tace "umm pretty kenan kinga yanda kika had'u kuwa wannan ai sai k'asar larabawa za'asami wacca tafiki kyau amma ba k'asar Nigeria ba inama inama hmm inama ace mr man ne zai mallaki wannan kyakkyawar surar natabbata dasaiya dawwama yana godiya ga ubangiji daya mallaka masa ke" murmushi kawai tai tareda share y'an kwallanda suka zubomata tad'auki phone nata tafita,,,"....
Cikin sauri Amira tashirya tafito suka wuce, da har MUFIDA tace yau ita zatai driving saboda yau kusan shekararta d'aya da barin driving tin lokacinda ta fasawa MUJAHID taya yau kuma taso tai saboda murnar zasu kammala degree amma Amira natinamata da MUJAHID saitaji dik kasala ta saukarmata danhaka dole Amira tajasu,,,"....
koda suka isa tini nusy tajima da zuwa ganin yanayinda fuskar MUFIDA ke d'auke dashi yasa ta tsaidasu tace "yau ranarace ta farinciki agaremu saboda haka sam b'acin rai da damuwa basu kamata a gansu a fuskokinmuba pleace MUFIDA ki daure kisake fuskarki ko muma maji dad'in yin walwala" murmushi tai tace "karki damu nusaiba muje kawai" itama murmushi tai suka rik'a hanun juna suka wuce ciki,,,"....
4pm dot suka gama zana jarabawan k'arshe suka fito, farinciki agunsu MUFIDA ba'amagana itadasu Amira haka sukakoma tamkar k'ananun yara sai wasa suke suna shafawa fuskokinsu fent kowa yafito sai murna da farinciki suke suna selpie,, ranar sai 6pm sannan suka koma gida,,,"....
Bayan sati d'aya da kammala zana jarabawansu school d'in ta shiryamasu biki, kwana d'aya saura ayi bikin dady da hamma faruk da muk'araban dady sukazo aikuwa murna agun MUFIDA ba'amagana saidai a b'angare d'aya sam bataji dad'i ba da akazo da hamma faruk sadai inda tad'an ji dad'i shine a hotel zasu zauna saboda haka bazai dameta ba,,,"...
Washe gari around 10am aka fara gudanarda bikin, anjima sosai anasauraron jawabai daga bakin shuwagabannin school d'in dakuma manyan bak'i da sukazo ciki kuwa hadda dady, daga nan akayaba kwazo da k'ok'arin d'alibbai sannan aka bada kyautuka ga gwarazan dalibai wanda MUFIDA takarb'i kyauta biyu hakama su Amira sun karb'a, daganan kuma akabar dalibai sukacigaba da shagalinsu, sai 2pm sannan aka kammala komai akai hotuna akai musayar number sannan kowa ya watse,,....
Daren ranar MUFIDA taredasu Amira ta kwana kasancewar gobe zasu wuce saboda dady yanada meeting gobe, daren ranar kuwa basuwani yi baccin kirkiba saboda kwana sukai suna shan fira, sai kusan 2am sannan suka kwanta bacci,,,"....
Washe gari tin 5am suka tashi sukafara shiri, 9am suka kammala komai suka wuce izuwa hotel d'inda su dady suke, 9:30am suka wuce izuwa airport taredasu Amira da nusy, saida jirginsu yasakko zasu wuce sannan su Amira sukai bankwana da juna nusy da MUFIDA harda kwallah suke dakyar Amira tacire nusy ajikin MUFIDA suka wuce har jirginsu yad'aga MUFIDA nakallonsu saida tadaina hangosu sannan tarufe window tajuya tana share kwallah,,,"....
2pm dot jirginsu yasauka k'asar Nigeria a Abuja city daga nan suka sake shiga jirgi wanda zai kawosu KEBBI State,,, sai 4pm sannan suka iso kebbi suna isowa motocinsu sukazo suka d'aukesu izuwa gida,,"....
Koda suka iso gida kuwa momy tashiryamasu had'addiyar liyafa domin tarbansu dakuma tayasu murnar kammala karatunsu, bayan sunyi wanka sunsauya kaya sannan suka fito domin gudanarda liyafar, cikin tsintsar farinciki sukai liyafar kowa sai farinciki yake amma banda MUFIDA da mubina, batawani ci abincin dayaba ta tashi tawuce kallo kawai momy tabita dashi mubina kuwa wani mugun kallo tarakata dashi wanda batamasan ma munira da dady sunganta tanayi ba,,,".....
Satinsu d'aya da dawowa dady yashiryamasu k'asaitacciyar walima ta murna da farinciki dakuma tayasu murnar kammala karatunsu wacca za'ayi ranar Thursday mai zuwa...........
_Banyi editing ba kuyi hak'uri da tyaiping error idan komai yadawo normal zandinga maku sbd jin dad'in ku ngd_
_WhatsApp reader's zan daina maku posting sbd bakwamin comment d'inda nakeso y'an wattpad da Facebook sunfiku yawan comment so bazan cigaba dayin aikin banzaba sbd banga halamar sak'onda nakeso na'isar a gareku ya'iso ba sbd haka idan kun gyara zancigaba da turomaku ma'assalam_🤚
#/Vote
#/Share
#/Comment
```AUFANA for life ```
*I.W.A*🖋
_*TSINTACCIYAR MAGE....*_🌷
_*BY~AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183_
® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚
*I dedicated diz page to diz gyaizz, maryam momyn Afrah yaya mero 😜 eeshan Aufana my dother, really in lobi naku over, my yaya mero kina k'ok'ari sosai wajen yin comment amma banda wajen yimana tyaiping hhh Lol, ina gdy sosai Allah yabar k'auna*
*My wattpadians kuma ban manta dakuba naku page d'in yana nan zuwa ammafa kusani kuma ina k'aunarku sosai k'auna mai tsabta kuma ina gdy da soyayyarku agareni tnx so much one love💘*
_*Page 25/26*_
_Note Edited_
_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_
Kwance take akan gadon momy tana karatun wani hausa novel *MUHIBBAT* na marubuciyar zamani SAINAH UMMUN MEENAL saiga kiran Amira yashigo a wayarta, cikin murna da zumud'i tad'aga wayar tareda fad'in "aminiyata k'awar arziki" can daga d'ayan b'angaren akai magana sainaji tace "eh mun iso tin d'azu ma jibi ranar Thursday za'ayi walimarmu dan Allah Amira kizo" can daga d'ayan b'angaren akai magana sannan tace "kai gaskiya banji dad'in hakan ba amma bakomai Allah yadawo daku lafiya" bayan anyi magana daga d'ayan b'angaren sannan tasake cewa "ok badamuwa bye bye" saikuma takashe wayar, kallon wayar take tana juyata tana kuma murmushi can dai ta'ajiyeta tacigaba da karatunta,,,".....
Yau takasance Wednesday danhaka tini akafara shirye shiryen walima, tini gidan yafara cika da y'an uwa da abokan arziki ma'aika kowa sai aikinsa yake adora wannan a sauke wancan, a daren ranar dady yadawo daga tafiyarda yai domin siyomasu kyaututtukan da zai basu, around 4pm mai k'unshi tazo tazanamasu lalle ja sannan aka masu saloon,,....
Washe gari tin 8am mai make up tazo ta tsantsara masu make up hmm naso kuga tauraruwar tamu irin rantsattsen kyanda tai, hakama mubina tai kyau munira ma anmata da bilkis k'anwar faruk, wasu tsadaddun arabian gowns suka saka red and black color, mai make up ce tamasu wani sabon rolling da'ake yayi yanzu,,"....
Tini ma'aikata suka gama tsara gidan dakuma gunda za'ayi walimar, wuri yafara karb'an manyan mutane ciki kuwa hadda Governor of kebbi state dakuma amaryarsa hjy zainab manyan commissioner's da sauran mutanen gomnati,momy ta'iso cikin fara'a suka gaisa sannan tad'auki hjy zainab suka shiga ciki, saida aka fara gudanarda walimar sannan MUFIDA tafito su mubina tini suka fito gun k'awayensu itakuwa abunda yahanata fitowa shine tin d'azu bilkis tafad'a mata hamma faruk yana nemanta wannan dalilin yasa tak'i fitowa,,,.....
Cikin salon takonta mai rikita hankali mai kallo take tafiya tana amsa waya, juyowarda zaiyi k'iris yai tozali da kyakkywar fuskarta tana d'auke da murmushi, saida takammala wayar sanan taje gun dadyn ta yahadata da abokanansa ta gaidasu tagaida governor hjy zainab tajanyota ta zauna kusa da'ita tana sanya mata albarka dakuma tayata murnar kammala karatunta, da mubina tahango MUFIDA zaune kusa da hjy zainab suna fira sai dariya suke ji tai kamar taje tashaketa ta mutu dan takaici da bak'in ciki,,"....
Momy ce ta'iso da muk'arabanta tazo suka gaisa da governor dakuma sauran bak'inda sukazo, ganin wani irin kallo da momy kemata yasa dole ta tashi tabata wuri ta zauna,,,,......
Saida akafara gudanarda walimar sannan dady yamik'e tsaye yakarb'i microphone yafara magana "Assalamu Alaikum y'an uwa dakuma abokan arziki, hak'ika naji dad'i kuma nayi farincikin karb'an gayyatata dakukayi nagode nagode sosai Allah yabar k'auna, sannan ina mik'a d'immin godiyata ga governor of kebbi state dakuma hjy zainab Atiku Bagudu dakuma sauran manyan bak'inmu nagode sosai, then after that kuma ina buk'atar ganin MUFIDA da mubina anan" yai maganar yana murmushi,,,.....
Tasowa sukai daga gunda suke sukazo yakamo hanun MUFIDA yana murmushi yafara magana "waennan sune yarana dana shiryawa wannan walimar MUFIDA da mubina y'ay'an dady, a saboda jin dad'i dakuma farincikin kammala karatunsu zan basu wannan gagarumar kyautar" yakalli MUFIDA yai murmushi itama tai murmushi sannan yacigaba "nabama MUFIDA kyautar sabuwar mota k'irar Honda wato LANGEROVER da sabon gida acikin unguwar G.R.A mai girman eka hud'u had'e da k'udi naira millions biyar domin tasaka credit" kuwa wajen yad'auka da shewa dasauri MUFIDA ta rungumeshi cikin tsintsar murna da farinciki tana fad'in "nagode nagode sosai dady na Allah yak'ara maka arziki mai albarka yakareka daga sharrin makiya da mahassada yasa kagama da duniya lafiya THANKS SO SO MUCH my dady I really love u more than my life my dady" shima cikin jin dad'in addu'ointa yasumbaceta yace "don't worry my dear ke jininace zan iya mallaka maki komai dana mallaka" hadda y'an kwallan farinciki MUFIDA tai,,"...
Takaici da bak'in ciki kamar yakashe mubina momy ji take kamar tazo tawanke MUFIDA da dady mari sai aikamasu da harara take, bayan nan yacigaba "saikuma mubina k'anwarta itama nabata mota k'irar Honda wato AVENSIS da kud'i naira million uku da dubu d'ari takasa credit Allah ya albarkaceku yasa kuma kuci amfanin karatunku" nan aka amsa da ameen sannan yabada microphone suka sauka,,,"....
Daga nan akacigaba da gudanarda walimar har izuwa 12pm sannan aka watse,,,....
Momy ce tashigo d'akin mubina saboda ko'ina tadubata kuma tasaka andubata amma ba'agantaba hakan yasa tayo d'akinta watakil tananan, zaune taganta akasa tana sharb'an kuka, k'arasowa tai kusa da'ita tadurk'usa tadafa shoulder d'inta cikin sigar rarrashi tafara mata magana "nafad'amaki kidaina kuka kina zubda kwallanki akan MUFIDA" dak'arfi tad'ago takalleta da idanuwanta dasuka sauya launi izuwa zajir tace "ai dole koda banaso na zubda kwallah momy hatta a fili agaban jama'ah dady nunamana bambamci yake a tsakaninmu kiduba abunda dady yau a bainar jamaa" k'ara matsowa tai kusa da momy tace "pleace momy tell me shin dagaske dady shine mahaifina shiya haifeni saboda ina tamtama sosai lallai idan ba dady ya haifeniba to saina kashe MUFIDA saina shafeta daga doron k'asa" wani irin tausayintane yatirniketa momy nan ta zauna tagyara zamanta tace "gyara zamanki nafad'a maki wani abunda zaisakaki farinciki naso nacigaba da taya dadyn ku b'oye wannan sirrin amma tin lokacinda yafara nuna bambamci a tsakaninku dama ni kaina naji bazan iya cigaba da b'oye saba" dawowa tai gaban momy tana kallonta cikin kaguwa tace "inajinki momy" kallonta tai tai murmushi sannan tace "inaso kisani mubina MUFIDA ba y'armu bace ba mune muka haifetaba dik wannan gatan da mahaifinku ke nunamata yanayin hakan ne dik saboda kartaji aranta bamune iyayentaba" dasauri tamik'e tsaye tareda zaro idanuwanta tace "are u shure momy" tai murmushi tad'aga mata kai alamar eh,,,.....
Wata iriyar karar farinciki tatsala tana kyakyata dariya, dasauri momy tarufemata baki tace "ke kinada hankali kuwa" ta k'ara kyalkyalewa da dariya tarungume momy tana fad'in "ina k'aunarki momy na daga yau tak'aremaki MUFIDA" jakarta ta d'auka tashare kwallanda suka b'ata mata fuska sannan tafita da sauri tana