Showing 6001 words to 9000 words out of 76905 words

Chapter 3 - TSINTACCIYAR MAGE BY AUFANA.txt

AUFANA   

12 Dec 2024

4287

suke suyi maganar kada MUFIDA tanemi ta had'iyesu saboda sunsan halinta,,,....

Har suka iso School tai parking bawani mai mostin kirki acikinsu musamman ita gogar datakejin jikinta dik ba dad'i kasala ga danga diksun mata yawa aciki,,,....

Yauma haka tawuni tana raba idanu kozata hango MUJAHID amma shuru ko motarsa bata hangoba bare shi, harsukagama zana exam suka fito suka wuce bata gansaba saitaji dik ba dad'i a kwana biyun nan dabata gansa sukayi rigima ba, haka suka wuce gida batada wani kuzari sosai.........




#/Vote
#/Share
#/Comment

```AUFANA for life ```
*I.W.A*🖋
_*TSINTACCIYAR MAGE....*_🌷


_*BY~AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183_


® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚


_*Page 11/12*_

_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_

Zaune yake ak'asa cikin makeken parlon sa ga tarin litattafai agabansa yad'aga kansa sama yad'ora hanunsa d'aya akansa d'aya kuma akan hanun kujera,,...

Rigimarda suke da MUFIDA ce yake tinawa itace take dawomasa tana masa yawo acikin kwakwalwa, d'ank'aramin bakinta yake hangowa yanda take tujayasa tana masa masifa,, wani k'ayataccen murmushi yai yace "hmm smole baby kenan",,....


Cigaba yake da tino dik irin rigimarda sukai tin ranarda ta maresa har ranar k'arshe data fasa masa taya tad'auka baisan itace tayiba, yai zurfi sosai acikin tinanin har yakaiga baisan shigowar Rayyan da mubashir ba saida Rayyan yadafasa sannan yai firgigit yadawo hayyacinsa,,,....

Rayyan yace "haba Prince mekake tinani haka sai zuba sallama muke tin a k'ofar shigowa har muka iso kusa dakai amma dik bakajiba ka lula cikin tinani kai zurfi" murmushi kawai yai yashafa lallausar sumarsa" zama sukai sannan suka gaisa MUJAHID yakalli mubashir yace "muby inafatar ka kammala aikinka gaba d'aya" cikin girmamawa yace "eh nakammala ur Highness ga komai a rubuce cikin wannan file d'in cikakken sunanta dakuma address d'insu da garinsu" karb'an file d'in yai yaduba sannan yad'ago yace "good aikinka yayi kyau zaka iya tafiya" nan yatashi yafita,,,....


Fira suka fara a hankali shi da Rayyan suna cikin firar sai rayyan yadubesa yace "wai Prince shuru nadaina ganin mutuniyarka kundaina buga game" murmushi yai yace "ai ita tagama nata wasan yanzu nawa time ne yafara saidai kasan yanayin karatunmu naso naso wallahi na ladabtarda yarinyar nan nakoya mata hankali sadai exam tahana saidai nayiwa kaina wani alk'awari wanda nikad'ai nabarwa kaina shi" murmushi kawai rayyan yai sanna yace "gaskiya nidai naso naga k'arshen wannan game d'in naku amma nasan bazan ganiba tinda dika dika kwana nawa yarage muyi bankwana da juna, sadai ina rok'on Allah yasa wannan game d'in naku tasauya salo takoma love dan wallahi kun matuk'ar dacewa da juna Prince har kamanninku ma d'aya yanda halayyarka take itama haka tata take miskilanci dakuma jiji da kai sadai ita tafika jiji da kan zaku matuk'ar yin marching idan kuka zama masoya",,,....

Tinda yafara maganar MUJAHID kemasa wani mugun kallo har yagama, bayan yagama yakallesa yace "kagama" murmushi kawai yai sai yace "to malam plss idan kagama kafita kabarman gida tin kan nasaka afitar dakai yanzu yanzinnan" yai maganar cikin tsintsar bacin rai fuskarsa ba alamun wasa, ganin haka kuma rayyan yasan halinsa sarai hakan yasa yatashi yana murmushi yace "Allah yabaka hak'uri yarima mai jiran gado nidai nasan gaskiya nafad'a kuma inarokon Allah yasa maganata ta tabbata tazama gaskiya" binsa yai da gudu shima yafita dagudu yana kyalkyala dariya yashiga motarsa yawuce shikuma yadawo ciki yana huci kamar kumurcin maciji yana zara idanuwansa,,,....


***** *****

Kwance take akan makeken gadonta tai shuu itakad'ai ga tarin littafai agabanta tarasa meke mata dad'i a duniya dik inda tajuya fuskarsa take gani tanamata gezau acikin idanu, tashi tai a zaune tai tagumi tana mamakin abunda ke shirin faruwa da'ita, acikin zuciyarta tace "to wai meke shirin faruwa danine ohh ni MUFIDA kardai maganar Amira ce keshirin zama gaskiya agareni son mr. Man kenan zuciyata keyi hmm tabbas inkuwa hakane ina cikin babbar matsala da tashin hankali",,,...

Can kuma sai taji tsintsar tsanarda tamasa ta taso mata acikin zuciya sai tace cikin tsananin b'acin rai "kai noo wallahi bazai tab'a yiwuwaba hakan bazata tab'a kasancewa ba natsaneshi wallahi zuciyata k'arya kike bazan tab'a barin wannan abun ya zama gaskiya ba" haka taita surutai itakad'ai harta gaji takwanta bacci b'arawa batasan lokacinda yai awon gaba da'ita ba,,,....


Washe gari haka taje school jikinta dik ba walwala dik inda sukaje sai dube dube take kozata hango MUJAHID amma harsuka dawo ko walk'iyarsa bazata ganiba, hakan kuwa bak'arin k'ara sakata acikin damuwa yakeba gashi batada damar ta tambeyasa saboda aganinta hakan zubda girmanta ne da ajinta aji ita da kanta tana nemansa bayan irin cin mutunci da bala'i da musifarda tadinga masa kai ina hakan bazata tab'a kasancewa ba, hmm nikwa nace yo ina ruwan so dawani class hhh Lol,,.....

Haka tawuni a school d'in amma bataga walk'iyarsa ba har suka koma gida,, su kansu mubina da munira sunga sauyi sosai ga MUFIDA a yanzu takoma tamkar wacca batada lfy idan tana tafiya kamar wacca kwai yafashewa a ciki gashi dama tafiyar ta yanga ce bare kuma yanzu, a school ma idan sunje batayin kamar yanda takeyi a da yanda take hura hanci tana d'aga kai sama kamar wata y'ar shugaban k'asa dik tadaina yanzu daga class sai restaurant sai gun hutawa saikuma gida, saidai basuda halin tambayarta abunda ke damunta saboda sanin halinta,,,....


***** ***** *****
Kwance yake akan gadonsa yai shuu,kyakkywar fuskarta yake tinowa da d'an k'aramin bakinta yanda take juyasa idan tana rashin mutunci ji yai kamar ace tana kusa dashi yakame bakin yatsotse shi saima a yanzu yake mamakin kansa dakuma jin haushin kansa dabai damk'eta yamannata da k'irjinsa yatsotse bakin nata datake rashin mutunci da rashin kunyaba dashiba, afili yace "amma bakomai yanzuma bata b'aciba akwai sauran lokaci ai",,,....

Rayyan ne yafito daga wanka saiyajiyosa yana magana kamar acikin mafarki, tsaye yai yana kallon ikon Allah a ransa yace "yarinyar nan tana nema tazautar man da friend sai maganarta yake shikad'ai kodai yatsunduma ne wai hhh" yai dariya yace "mujedai zuwa ai garin ba nisa sannu a hankali zaka gasgata maganata",,,....


Matsowa yai kusa dashi yadafasa saiyai firgigit yadawo hayyacinsa sannan yasauke numfashi "hmm wai Prince meke damunkane kwana biyun nan nalura dik bakacikin hayyacinka nalura kwana biyun nan dik so so silent kake plss tell me what's rong with u" shuru yamasa can kuma saiya tashi yashige toilet batareda yace dashi uffan ba, murmushi rayyan yai saboda inda sabo yasaba da halin MUJAHID wannan bazai damesaba nan yacigaba da abunda yake yakyalesa tinda bayasan yafad'a masa damuwarsa idan tai wari yaji,,,...


***** *****

Abun duniya yataru yayiwa MUFIDA yawa tarasa ina zata saka kanta taji sanyi, a yanzu kam ta yarda da abunda zuciyarta take fad'a mata ta tabbar da zuciyarta tagama cika da tsintsar k'aunar MUJAHID saidai ita kanta tasan wannan babban al'amarin da zuciyarta ta rarumomata bak'aramin al'amari bane kuma tasan dole tafuskanci k'alubale akansa,,,...

Zaune suke acikin wajen hutawa dake cikin school d'insu tai shuu talula acikin zurfin tinaninsa, Amira da Nusy sai shan firarsu suke amma itakam tai shuu tana ware dara daran idanuwanta tana kallo masu shigowa da masu fita acikin school d'in,,,....

Tinda suka zauna Amira takula da yanayinda MUFIDA take ciki saidai tashareta takyaleta,, tana cikin dube dube kamar ance ta waiga a gefenta na dama tana waigawa kuwa sai tai tozali da kyakkywar fuskarsa acikin wata dalleliyar mota dake shigowa cikin School d'in,,,...

Dasauri tamik'e tsaye tawashe fararan hak'oranta tana dariya fuskarta d'auke da tsintsar farinciki, mamakine ya bayyana tsintsarsa a fuskokinsu ganin yanda tai kamar zautatta, gunda take kallo suma suka juya domin ganin abunda take kallo.......



Ance ina shagwab'aku sosai 😅 saboda haka yanzukam nadaina maku 2pages kullum kuyi manage da wannan




#/Vote
#/Share
#/Comment

```AUFANA for life ```
*I.W.A*🖋
_*TSINTACCIYAR MAGE....*_🌷


_*BY~AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183_


® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚


_*Page 13/14*_

_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_

Ganin MUJAHID tareda Rayyan suna k'ok'arin fitowa a cikin dalleliyar motarsu yasa suka gane cewa su d'inne take kallo,, dasauri Nusy tarik'ota suka zauna cikin b'acin rai da masifa tace "haba feedom mekikeyi hakane so kike kibamu kunya ne" shuru tai takafe idanuwanta gu d'aya sai kawai sukaga kwallah sunfara zubomata daga idanu,,,....

Mamakine har yanzu cike fam a zuviyoyinsu dakuma tarin tambayoyi ga MUFIDA, ahankali tad'ago ta kallesu sannan tace "friend's ina cikin matsala ina cikin damuwa" subhanallah feedom meke faruwa dake ne...?? Nusy ta tambayeta,,,....

Shuru tai can kuma tafara magana kwallah nabin kuncenta "ina cikin matsala friend's abunda Amira tafad'a naga laifinta hadda fushi nai da'ita yau yazama gaskiya ya tabbata akaina" murmushi Amira tai saboda tini tagano kwanan zancen takuma fahimci inda yadosa, "mekenan feedom?" sake kallo nusy tai tace "Nusaiba zuciyata ta tsunduma tsundum acikin kogin k'aunar MUJAHID bansan ya akayi hakan tafaruba wallahi bansaniba" tak'arasa cikin fashewa da kuka, dasauri nusy tajanyota ta rungume tana rarrashinta,,,....


Shuru yad'an ratsa wurin sai she she kar kukan MUFIDA kake jiyowa kasancewar wurin kowa sha'anin gabansa yake yasa basuwani damuba, Amira ce tace "tin farko dakuka fara wannan rigimar naji a zuciyana akwai wani abu dazai shiga a tsakaninku shiyasa namaki magana akan ki sausauta tsana dakuma irin tarin rigimarda kika shirya kiyi da shi saboda irin haka tasha faruwa daga k'arshe saikiga ankoma dana sani" Nusy tace "yanzudai dik abar wannan zancen mufara neman mafita akan matsalarda take shirin fuskantomu" wani irin murmushi Amira tai batareda tasake cewa komaiba saidai dagani kasan akwai magana acikin bakinta tadaiyi shuru ne kawai,,,.....

Yaukam basu wani jimaba suka wuce 5pm tawuce gida saboda rashin jin dad'in jikinta datake ga wani a zababben zazzab'i datakeji,,,....


***** *****

Kwance yake akan gadonsa yad'aga kansa sama hanunsa d'aya akan kansa, yalula sosai yai zurfi acikin duniyar tinani idanuwansa sunyi jajir saboda tsananin zazzab'inda yakeji, Rayyan ne yashigo tareda mubashir dakuma wani doctor Ayman,,,....

Suna shigowa suka zauna MUJAHID yagaisa da doctor sannan likitan yafara duba lafiyarsa,, bayan y'an gwaje gwajenda yamasa sannan yahad'a injection yamasa yakuma doramasa drip saboda yalura yanada buk'atar su,,....

Saida yagama komai sannan yazauna yadubi su Rayyan yafara magana "am to nayimasa gwaje gwaje sosai bawata cuta dake damunsa kawai yawan damuwa da yawan tinani dakuma yawan zama acikin kad'aici shine yamasa yawa yakekuma nema ya haddasa masa hypotention yanzu hakama jininsa yahau yakai 70% shiyasa ma namasa wannan injection d'in saboda jinin yasauka yakoma normal but idanfa bai rage yawan damuwa da tinani ba jinin zai sake hawa zai kuma iya fin hawanda yai yanzu idan kuma hakan tafaru tofa komai zai iya faruwa wallahi saboda haka dole a kiyaye" shuru sukai suka rasa mema zasuce dakyar Rayyan yace,,,....

"Ok Thanks doctor insha Allah za'akiyaye mungode sosai" nan yahad'a kayansa yafita mubashir yabisa domin masa rakiya,, juyo da kallonsa izuwa ga MUJAHID rayyan yai cikin b'acin rai yace "kaga abunda kake nema ka janyowa kanka ko to wallahi idan baka daina wannan damuwar ba Allah saina kira mai martaba nafad'amasa" murmushi yai sannan yajuya fuskarsa yace "hmm rayyan kenan wallahi dan bakasan irin yanda nakeji acikin zuciyata bane shiyasa kake wannan maganar" murmushin gefen lebe rayyan yai saboda shifa tini yagano damuwar MUJAHID acikin zuciyarsa kuwa tsintsar farinciki ne fall saboda tini yadad'e dayiwa MUJAHID sha'awar auren MUFIDA saboda sunmatuk'ar dacewa da juna to yanzu tinda abunda yake rok'o yatabbata wato MUJAHID yatsunduma a k'aunar MUFIDA dole yayi iya yinsa domin ganin yahad'a su fatansa Allah yataimaka masa yashawo kan abun cikin sauk'i har Allah yasa aure yashiga a tsakaninsu,,,.....

Saida mubashir yadawo sannan rayyan yadawo daga tinaninda yake,, bayan drip d'in yak'are aka cire sai suka had'amasa ruwan d'umi yai wanka yai sallah sannan yashirya sai rayyan yace yazo sufita domin yad'an mik'a kafa saboda yarage tinani, haka kuwa akayi bayan yasaka kaya sannan suka fita,,,....


***** *****

Yau kimanin kwana biyu kenan MUFIDA bataje school ba hakan yasa tai missing exam's biyu, saidai su Nusy sunyi matuk'ar mamakin abunda yasa MUFIDA batazo school ba dasuka tambayi munira saita fad'amasu batada lafiya ne,,,....

Bayan sungama exam saisuka shirya suka nufi gidansu MUFIDA, koda suka isa tana cikin d'aki a kwance itakad'ai, dasauri Amira tahau kan gadon tad'agota tana tambayar abunda ke damunta, mamakine ya bayyana a fuskarta ganin wata iriyar muguwar rama da tai a y'an kwana biyunnan,,,....

Subhanallah Amira tafad'a "MUFIDA meke damunkine haka kwana biyu kikai wannan muguwar rama" bataiya cemata komaiba sai kwallah datake zubarwa daga idanuwanta masu zafin gaske, cikin tsintsar tausayi tazaunar da'ita koda tabud'e cikinta yayi tamkar babu ciki a jikinta da'alamu yunwace takeji dasauri tace "nusaiba je kitchen kihad'o mata tea mai zafi yanzi yanzinnan" nusaiba tace toh tafita da sauri,,,....

Cikin y'an mintina nusaiba tahad'o tea d'in takawo nan Amira tad'aga ta tabata, dasauri takarb'a tafara sha dikda zafinsa amma haka taita shansa saida ta shanye gaba d'aya sannan tasauke nannauyan ajiyan zuciya tareda lumshe idanuwanta,, can kamar 5mnts saita tayunk'ura gefe d'aya kan gadon nantafara shek'a aman jini, tsoro yakama su Amira sosai dasauri Amira tarik'ata taita shek'a aman jinin saida tagama sannan takamata suka wuce toilet,,,....

Wanke mata jikinta tai tabata ruwa ta kuskure bakinta sannan tarik'ota suka dawo d'akin, koda suka dawo har nusaiba tacire wannan bedsheet d'in tasaka wani, kwantar da'ita tai sannan tabud'e wardrobe tad'akko mata wata doguwar riga ta taimaka mata tacire wacca ke jikinta sannan tasaka wannan d'in,,,.....

Zama tai kusa da'ita nusaiba kuma na a gefensu tarik'o hanunta d'aya cikin kulawa tace "MUFIDA waimeke damunkine....?" Amira ta tambayeta, shuru tai dakyar tabud'e bakinta tace "tin shekaranjiya damuka rabu daku a school bansake yin lafiya ba dama koda naje banajin dad'i bayan nadawo ne abun yakaru" shuru sukai bawanda yasake cewa komai,,,....

Can sai Amira tace "MUFIDA kodai har yanzu baki cire MUJAHID a rankibane?" kwallah ne sukaga sunfara gangaromata sai kawai tafashe da matsanancin kuka, bata hanataba ta kyaleta saida tai mai isarta, ahankali tafara magana cikin muryar kuka "wallahi Friend's inacikin mawuyacin hali inacikin Matsananciyar damuwa son MUJAHID nanema yazameman baraza a rayuwata nayi iya yina amma nakasa ciresa a zuciyata sonsa saima dad'a k'aruwa yake a zuciyata nakasa ciresa yafi k'arfina" tana kawowa nan tasake fashewa da sabon kukan,,....

Wani irin tausayinta ne sukaji yakamasu nusy kasa jurewa tai har saida tazubda kwallah, Amira ce tace "hak'ika nasan irin halinda kike ciki MUFIDA nasan irin rad'ad'inda kikeji saboda nima natab'a tsintar kaina acikin irin halinda kike ciki a yanzu shiyasa tin farko nafara tsoron irin wasanda kuke a tsakanink...." amanda MUFIDA tafarayi ne yakatse maganarda take,,,....


Dasauri tarik'ata takamata suka wuce toilet, abun kamar wasa sai cigaba yake aman jinin ne yanzuma take tintanayi da k'arfinta hartafara gajiyawa can kawai saita zube a jikin Amira somammiya..........



Hmm....!!! tbd rikicos inji y'an bokon k'auye 😂 lallai mufida kin taro ruwan dafa kanki da kanki, to shikuma gogan kenan shima dai yatsunduma tsundum to lallai kuwa tasu salon soyayyar kenan hhh Lol, muje zuwa reader's 🏃‍♀🏃‍♀😜





#/Vote
#/Share
#/Comment

```AUFANA for life ```
*I.W.A*🖋
_*TSINTACCIYAR MAGE....*_🌷


_*BY~AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183_


® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚

*αѕlm mч fαn'ѕ jíчα αnmun αвundα чαѕα nαjí dαd'í ѕσѕαí nαkumα чí fαríncíkí nαѕαmu tαввαcín mαѕσчαnα kunα вíвíчαtα ѕσѕαí, jíчα wαtα tαвíní pc tαmun gчαrα tαfαd'αmαn nαчí míѕtαkє αcíkín ruвutunα nα jíчα, índα nαcє jínín mujαhíd чαhαu чαkαí 70% míѕtαkє nє jínínmutum ídαn чαkαí 120 nє чαhαu вα 70 вα ѕαmα 120 k'αѕα kumα 90 ѕσ nαjí dαd'ín hαkαn ѕσѕαí kumα ínα gdч ѕσѕαí dα wαnnαn cσrrєctíσn d'ín, dα'αcє αnα hαkα dα αn rαgє ѕαmun kurα kurαí α ruвutu ѕhínє αmfαnín чín ѕhαrhí tαhαkαn nє mukє gαnє índα mukαí kuѕkurє, ѕσ nαjí dαd'í ѕσѕαí kumα αkσdαчαuѕhє k'σfα tα α вud'є tαkє dσmín kαrв'αn kuѕkurє nα nαgσdє ѕσѕαí thαnkѕ αlσt єr uwα*

*mαmαn khαdíjα ínα gdч ѕσѕαí dα k'αunα jíчα nαgα αnвudє ѕαвσn grσup tѕíntαccíчαr mαgє fαn'ѕ 😍 nαjí dαd'ín hαkαn ѕσѕαí ínα gdч dα k'αunα αllαh чαвαr zumuncí tnх σnєcє αgαín much lσvє u dєαr*💘


_*Page 15/16*_

_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_

Tsintsar tashin hankaline yak'ara bayyana a fuskar Amira, dasauri takwallawa Nusy kira a rikice tazo, tana ganin irin halinda MUFIDA take ciki hankalinta yak'ara tashi,,,....

Cikin sauri Amira tace "nusaiba wannan abun yayi zafi sosai mud'auketa mukaita asibiti kar tasamu matsala" toh nusy tace fuskarta cike da tsintsar tashin hankali,,,....


Cikin sauri suka d'auketa suka saka a motar nusy nan suka wuce a wata private hospital dake kusa dasu,, dazuwansu kuwa ana ganin irin halinda take ciki akai saurin karb'an ta domin bata taimakon gaugawa, I.C.U aka wuce da'ita kai tsaye, cikin gaugawa suka fara taimakamata domin dawo da numfashinta, tajima sosai kan numfashinta yadawo sannan suka sakamata oxygen domin taimaka mata wajen cigaba da numfashi da kyau bayan sunsakamata oxygen suka had'a wasu injection suka mata tareda d'ora mata drip a hanu d'aya d'ayan kuma jini saboda tazubarda jini sosai lokacinda take amai,,....

Acikin drip d'in ma saida suka saka wasu medicine's aciki waenda zasu taimaka mata domin tasamu k'arfin jikinta,, ....


Tinda aka shiga da'ita d'akin Amira takira munira a waya tashaidamata halinda MUFIDA take ciki hakama mubina takirata ta fad'a mata amma saitai kamar bata damuba tad'aga kafad'a irin ko'ajikinta dinnan,, munira kuwa suna gama exam bako tsattsayawa tahawo taxi tazo hospital d'in, ganin dak'in da akace MUFIDA take ciki dakuma ganin yanayin fuskokinsu Amira yasa hankalinta yak'ara tashi saita fashe da kuka saida Amira tajanyota jikinta ta rungume tana rarrashinta,,,....

Saikusan 4pm sannan akamasu izinin suganta koda suka shiga kuwa har yanzu bacci take oxygen yana a hancinta hannayenta dika biyun sanye da jini dakuma ruwan jiki, cikin tsintsar tausayi sukai zaune suna jiran farkawarta munira sai kuka take,,,....


Around 6:30pm bayan sunyi sallar magrib Amira na zaune munira da nusy sunje siyomasu abinci, ahankali tafara juya fuskarta tana karanto kalimatush shahada tana bud'e idanuwanta, dasauri Amira ta taso cikin murmushi tazo kusa da'ita, bayan tabud'e idanuwanta Amira tace "sannu MUFIDA" tad'aga mata kai yunk'urin tashi tai sai takasa Amira tai saurin rik'eta saigasu munira sundawo, dasauri sukayo gunta cikin fara'a sunamata sannu ta amsa nan munira taje tashaidawa doctor farkawar ta,,,....

Atare suka shigo nan yafara y'an gwaje gwajenta yacire mata drip d'inda yak'are saura jini sannan yasake mata wasu injection sannan yajuyo garesu "to Alhmdllh komai yazo da sauk'i yanzu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login