Showing 9001 words to 12000 words out of 76905 words
sab'anin d'azu jininta yadawo normal sab'anin d'azu dayahau sosai wanda hawarda yaine ma yai sanadinda take aman jinin,, dik waennan matsalolin dasuka faru gareta sunfaru ne a sanadin tention d'inda yamata over damuwa yawan tinani gakuma saka abu a ranta wanda yake k'ara haifarmata da damuwa dakuma yawan tinani, zaman kad'aici yana bada babbar gudumawa wajen wanzuwar yawan tinani dakuma shiga damuwa, damuwa da yawan tinani shike kawo hawan jini wanda idan jinin mutum bayada k'arfi sosai saiyafara aman jini kokuma yafad'i b'arin jikinsa yamutu yadawo baya aiki wato paraliasation mutuwar b'arin jiki d'aya, so gaskiya bazan b'oye makuba tana gab da kamuwa da ciwon hawan jini wato hypotention matuk'ar jininta yasake irin wannan hawar da yai to komaima zai iya faruwa so saboda haka dole a kiyaye tadaina shiga damuwa da yawan tinani saboda gujewa matsala domin kuma kariyar lafiyarki Allah yabaki lafiya" dakyar suka iya amsawa da ameen saboda dik jikinsu yamutu sosai,,,....
Bayan yafita norse taciremata oxygen da jinin da aka doramata yak'are, brush tai tawanke bakinta sannan suka had'a mata tea tasha bayan tasha sannan akabata magani tasha takwanta, bayan ta kwanta suma sukaci abinci sannan sukai sallar isha,,,....
Suna zaune sai Amira tad'auki phone d'in MUFIDA takira PC d'insu koda yad'aga cikin farinciki yad'aga wayar azatonsa itace gogar saboda kullum saidai yakirata ko plss call me bata masa saikuma gashi yanzu yaga kiranta, bayan yad'aga tareda rangad'a mata sallama had'e da kiranta da sunanda yasaba kiranta wato baby,,,....
Dasauri Amira tai saurin katseshi da "sir barka da dare nice Amira Nasir Aji k'awar MUFIDA nakira ne nafad'a ma halinda MUFIDA take ciki a yanzu haka tana a private hospital dake kusa da School dinmu" bayan tagama fad'a masa yace "subhanallah ok ok ganinan zuwa" saiya kashe wayar, kallonta MUFIDA tai tace "meyasa kika kirasa da wayana Amira kinfasan banasan hakan bana sonsa haka kuma bana san kiransa a wayana kuma bana son komai nasa" murmushi Amira tai tace "nayi hakan ne saboda wata manufa, kinsan kinyi loosing exam's biyu yanzukuma gaki kwance akan gadon asibiti kinga ko gobe bazaki iya zuwa School ba so nasan idan yazo dik yanda za'ayi zaiyi saboda yaga kin rubutasu" murmushi kawai tawai batasake cewa komaiba,,,....
Haka kuwa akayi bayan yazo yamata sannu tareda kawo kayan jinya sai yace badamuwa insha Allah zata rubutasu tai masa godiya su Amira ma sukamasa,, washe gari saida suka shirya komai tai wanka taci abinci tai sallah sannan suka fita suka barta tareda norse, lokacin exam nayi saiga malaman School d'insu da jamian tsaro har uku sunzo anan aka bata Question's paper ta karb'a da laptop tai exam d'in tagama sannan tai submitting suka wuce,, saida tai kwana biyu anamata haka aranar na uku ne aka sallameta suka koma gida,,,....
A kwana biyunda tai Amira da nusy sunyi matuk'ar k'ok'ari sun nunamata su aminaine nagari dan ko y'ar uwarta batai mata abunda sukaimata ba, tin ranar farko da mubina taje batasake zuwaba shima bawani jimawa taiba tawuce abunta, munira kuwa dik abunda akai atare da'ita, acikin kwanakin sunyi matuk'ar k'ok'ari wajen ganin sun sakata acikin nishad'i saisuyita mata fira mai cike da barkwanci taita dariya suna nishad'i dikdan kawai tad'an samu tarage damuwa kuma Alhmdllh tasamu sauk'i sosai saidai tarame sosai daman bawani k'iba ne da'ita ba bare kuma yanzu datai ciwo,,...
***** *****
Yau kimanin kwana biyu kenan da dawowarta daga hospital taji sauk'i saidai har yanzu takasa daina tinanin MUJAHID dik lokacinda tazauna itakad'ai to zaka ganta tai tagumi tana tinani ko tai shuu kamar mara lafiya,,,,....
Zaune take itakad'ai akan kujera cikin class saigasu Amira sunshigo, fira sukad'anyi kan lokacin shiga exam yayi, bayan sunyi exam sungama suka wuce restaurant domin cin abinci,,,....
Bayan sungama sai suka tashi domin sud'an mik'a kafa anan acikin School d'in,, suna cikin zagayawa saisuka hango MUJAHID da Rayyan suna tafiya suna fira sai dariya suke suna wasa da'alamu sunajin dad'in firarsu,,,....
Tsaye tai tadazk'are anan tai tagumi tana kallonsa tana murmushi kamar yanda shima yake murmushin saikuma kawai taji kwallah nazubomata, nusy ce tai saurin rik'o hanunta tajuyo da'ita gefe d'aya lokacinda sukazo zasu wuce ta gefensu kusa dasu karsugane sune suke kalla, saida suka wuce tai saurin kwace hanunta tajuya tana kallon bayansa, wani irin kyau taga yak'ara mata saidai taga yarame sosai kamar wanda yakwanta jinya, murmushi take sosai har fararan hak'oranta suna bayyana saidai kuma kwallah nazuba daga idanuwanta,,,....
Tsintsar tausayinta ne yamamaye zuciyoyinsu nusy tace "MUFIDA kiman izini naje na bayyana soyayyarki a gun masoyink...." bakinta da MUFIDA tai saurin rufewa ne yahanamata k'arasa maganarta tace "hakan bazata tab'a faruwaba nusaiba koda kuwa sonsa zaima ajalina amma bazan tab'a iya tinkaransa nafad'amasa cewar ina sonsa ba koda kuwa sonsa ne zaizamto ajalina abunda kawai nake nema agareku amatsayinku na aminaina shine kucigaba da tayani da addu'a Allah yarageman zafin k'aunarsa acikin zuciyata yakuma bani juriyar cigaba da b'oye k'aunarsa har izuwa lokacinda rai zaiyi halinsa amma fa bazan tab'a iya tinkaransa nafad'a masa ina sonsa ba" janyota nusy tai tarungume cikin tsintsar tausayinta,,,....
Kasa yin yawon sukai kawai suka wuce izuwa gida,,...
*********
Yau takasance Thursday ranarda suka kammala zana exam y'an class d'insu MUJAHID sunfito sai murna suke suna nuna tsintsar farincikinsu da Allah yanuna masu wannan ranar dasuka kammala degree d'insu,,,....
Hamma faruk na gefe d'aya tareda abokanansa dasu MUFIDA suna tayasa murna, acan wani gu tahangosa zaune shikadai yana danne danne phone nasa, wani irin murmushi ne yakub'e ce mata batareda sanintaba saikuma tai sauri tajuya kar yaganta,,,...
Yana a zaune saiga Rayyan yazo fuskarsa dikta baci da kala wacca sukaita shafawa jikinsu, murmushi yai tareda zama sannan yace "MUJAHID gafa y'ar gidanka nan smole baby a kusa dakai mezai hana kasameta kafad'amata sak'on zuciyarka saboda wannan itace damar k'arshe agareka idan kabari ta kub'cemaka to bazaka sake samun irintaba" murmushi yai sannan yace "aikuwa saidai ta kub'ceman amma bazan tab'a aikata abunda kaceba" shuru rayyan yai yayi tagumi yana kallonsa shi tinda yake a rayuwa baitab'a ganin miskilin mutum kamar MUJAHID ba, yanda yai abun saima yabama MUJAHID dariya yai dariya yamik'e tsaye tareda buga shoulder d'insa irindai yanda gyaiz sukeyiwa junansu yawuce abunsa,,,...
Kallo rayyan yabisa dashi can saikawai wata dabarar tafadowa rayyan, dasauri yatashi yaje yanemo paper d'aya da ink yazauna yafara tsara letter irin wacca ada maza keyi idan namiji zai fara neman tayin soyayyar mace yakuma fad'a mata cewar yana sonta,,,....
Saida yatsarata tsab harda kalaman soyayya masu dad'in gaske masu sanya zuciya tai taushi sannan yalinketa yasaka acikin wani gu mai kyan gaske yahad'a da flower red colour had'e da zobe na zinare mai shegen kyau yai murmushi sannan yatashi yawuce,,,....
Wajen yacika sosai sai farinciki da murna suke, nan yakutsa yafara neman MUFIDA saidai ina iya ganinsa yaduba bai gantaba, can kawai saiya hango mubina tareda k'awayenta saiyaje gunta yamasu sallama suka amsa sannan yace dan Allah tad'an bashi 10 mnts yanaso yai magana da'ita nan tace ba komai suka keb'e,,,...
Bayan sun keb'e yamata bayanin abunda yakeso tamasa tace ai bakomai saiya bata yace takaiwa MUFIDA MUJAHID ne yace abata, karb'a tai a fili tana murmushi amma a cikin zuciyarta tsintsar bak'inciki ne da haushi dakuma takaici, bayan takarb'a yamata godiya yawuce...........
*ina buk'atar addu'oin ku wlh banida lfy sosai kilama bazanyi tyaiping gobeba*😔
#/Vote
#/Share
#/Comment
```AUFANA for life ```
*I.W.A*🖋
_*TSINTACCIYAR MAGE....*_🌷
_*BY~AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183_
® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚
_*Page 17/18*_
_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_
Wani mugun tsaki tai tareda binsa da harara, k'awayentane suka k'araso kusa da'ita, bud'e takardar tai tafara karanta abunda ke k'unshe acikinta saida suka karanta komai tabuga wani mugun tsaki zuciyarta namata kuna tace "aikin banza aikin wofi to sak'on bazaije guntaba bare har taji dad'i tayi farinciki" sai kawai tayaga takardar tayaga flower d'in shikuma zoben tabud'e jakarta tasakashi acikin,,....
Hmm wallahi sunma rainamaki wayoi wato kece y'ar aikensu ko yafa kamata kifara d'aukan mataki akan yarinyar nan ki nunamasu kemafa big lady ce. cewar anisa k'awar mubina, "eh wallahi dan daga MUFIDA har k'awayen nata sunmugun rainaki" inji najma k'awar mubina,, wani mugun murmushi mubina tai tace "karku damu lady's nakusa kawo k'arshen wannan iskancin nasu domin nafara gano sirrin abun wato yanzu dai gaba d'aya MUFIDA taluuuula acikin kogin soyayyar d'an samrayi MUJAHID" tai maganar cikin kyalkyalewa dawata muguwar dariya suma k'awayen nata suka kyalkyale da dariyar "so kunga nasami makamin da zanyi yak'i da MUFIDA" of course my k'awa muk'arasa gida domin sanin yanda zamu tsara abun. cewar najma nan suka wuce izuwa gidansu mubina,,,....
Rayyan nabata yawuce suka cigaba da celebrating d'insu,,"....
Around 4pm akafara gudanarda shagalin bikinsu MUJAHID domin tayasu murnar kammala karatunsu, cikin shiga mai kyan gaske ta alfarma MUJAHID da rayyan sukashigo acikin k'aton holl d'inda ake gudanarda shagalin sanye da graduation gown, tamasu kyau sosai idan kagansu kai kace jinin Arab's ne sak kirarsu da siffarsu kamanninsu gaba d'aya na arab's ne musamman MUJAHID,,,....
Bayan manyan bak'i professers da dai sauran manyan shuwagabannin k'asar sunzo sai akafara gudanarda bikin, anjinjinawa shugaban makarantar sosai irin namijin k'ok'arin da yake wajen ganin ansamu cigaba ga d'alibbai hakama d'aliban anjinjinamasu sosai saboda irin jajircewarda suke wajen karatu domin fitowa da result mai kyau, bayan nan sai akabada kyaututtuka ga gwarazan d'alibbai wanda hadda MUJAHID aciki yakarb'i kusan kyaututtuka uku da kyautar littafai guda biyar waenda wani professor yarubutu, rayyan ma yakarb'a, bayan angama sannan d'aliban suka fara nasu shagalin,,,.....
A can gefe d'aya MUJAHID yahango MUFIDA tareda k'annenta da hamman su cikin wata iriyar shiga mai d'aukan hankali, tai masifar yin kyau Arabian gown ce ajikinta tai rolling da veal d'in rigar k'afafuwanta sanye da wasu hills shues d'an k'aramin bakinta yasha janbaki red color, dariya take sosai fararan hak'oranta sai bayyana suke dimples d'inta sai lotsawa yake, murmushi yai yashafa sumarsa saboda wani irin shauk'i dayaji jiyake kamar yaje yarungumeta yafara tsotsar lips d'inta gasu pink sunsha janbaki gwanin birgewa da d'aukan hankali, saidai ina girman kai bazai bariba hhhh Lol,,,"...
Saikusan 6pm sannan aka gama akai pic's domin tarihi sannan kowa yanemi yafiyar d'an uwansa aka watse,,....
Zaune yake akan gado yai shuu yad'ora kansa akan pillow yana kallon sama mubashir na harhad'a masu kayansu, rayyan ne yashigo d'auke da jakar takalman MUJAHID,,,....
D'ayar jakar takalmansa yajanyo yasakasu aciki sannan yacigaba da taya mubashir, har suka kammala had'a komai baisanma rayyan yashigo d'akinba saida yatab'a shoulder d'insa sannan yai firgigit yadawo daga duniyar tinaninda ya lula, murmushi yai yashafa sumarsa yatashi yawuce toilet, binsa da kallo rayyan yai batareda yace komaiba yafita,,,....
Washe gari tin 6:30pm basu sake kwanciya ba, bayan sunshirya sannan suka fito sukai breakfast, sunacikin cin abinci rayyan yadubesa yace "prince yau itace damarka ta k'arshe karka bari ta kufcemaka" shuru yai nayan wasu second's kan yace "ban fahinci inda zancenka ya dosa ba" wani kallo rayyan yamasa na mamaki shikam yana mamakin hali irinna MUJAHID kana suma kana farfadowa akan abu amma kuma saboda girman kai ka kasa samarwa kanka wannan abun,,,....
"Hmm ina nufin kaje kasanarda MUFIDA kanasonta" Murmushi yai yahad'iye ruwan tea d'inda yakurba sannan yakallesa yace "rayyan kenan ayanzukam tabbas na tabbatar zuciyata tariga takamu da son smole baby saidai kasani bazan tab'a tinkararta na fad'amata ina sonta ba wannan maganace dana fad'a a baya yanzu kuma nasake maimaitawa, zan iya hak'uri nacigaba da binne sonta acikin zuciyata nakuma cigaba da rok'on Allah daya mantar dani k'aunarta yacire man ita acikin zuciyata amma bazan tab'a furtamata kalmar so ba koda kuwa son natane zaizamo ajalina" kallonsa rayyan da mubashir keyi har yagama maganarsa,,,....
Nannauyan numfashi rayyan yasauke hakama mubashir suna jinjina girman wannan al'amarin dandai tinda suke basu tab'a ganin irin saba basukuma san mezasuyi akaiba, saidai fa har yanzu k'udurinda rayyan yai bai mantaba yakuma d'auki alk'awarin cikasa kodon ya jadadda k'arfin abotakarsa da MUJAHID,,,"....
Haka suka kammala cin abincin batareda kowa yasake cewa uffan ba, bayan sungama sannan suka kwashi kaya suka saka acikin mota sannan suka fito aka rufe gidan sukabama gateman Key's tareda masa bankwana sannan suka shiga mota rayyan yajasu suka kama hanyar airport kasancewar flyt d'in 10am zasubi,,,.....
***** *****
Munira da Amira ce zaune akan dining suna break itakuma tana kan kujerar parlor a zaune tai shuu tak'urawa littafe idanu,, nusaiba ce tashigo da gudu suna ganin yanayinda tashigo bako sallama saisuka taso da sauri sukayo gunta,,,....
Cikin haki tafara magana "ga MUJAHID can nagani a airport suna jiran flyt d'insu ya'iso yanzu munje raka yayan k'awata nagansa shi da abokinnan nasa, MUFIDA dan Allah kitashi muje kibayyana masa sak'on zuciyarki kokuma kimana izini muje musanardashi" wasu irin zafafan kwallah ne suka zubomata a lokaci d'aya tareda murmushi mai zafin gaske "ahalin yanzu inaji ajikina tabbas narasa mr man har abada soyayyarsa takusa tazama tarihi agareni zancigaba da b'oye ta acikin zuciyata inkumayi k'ok'arin binneta saidai na tabbata aduniya zuciyata bazata tab'a son wani d'a namiji a duniya kamar mr man ba koda kuwa shine number 1 acikin masu kud'in dik duniya kuma koda shine yafi kowa kyau a duniya" juyowa tai takalli nusy tai murmushi sannan tace "nusaiba tabbas ku k'awayene nagari masu damuwa da damuwar wani amma nusaiba kiyi hak'uri wallahi bazan iya tinkarar mr man nafad'a masa ina sonsaba i can't i can't nusaib...a" saitafashe da matsanancin kuka mai tsintsar ban tausayi mai raunana zuciyar mai karatu,,,"....
Carkey Amira tad'auka afusace takalli nusy tace "tashi muje nusaiba" nan nusy ta tashi munira ma ta tashi suka fita suka barta kwance akan kujera,,,....
Kai tsaye airport d'in suka nufa cikin sauri Amira sai gudu take sosai da motar, suna isa sukai parking suka fito da sauri nusy tajasu izuwa gunda taga MUJAHID da rayyan da mubashir zaune saidai kash koda suka isa basugansuba suntashi,,,"....
Tsaye sukai suna dube dube nusy tad'ora hanunta d'aya a goshinta d'aya kuma tarik'e k'ugunta saboda damuwar da take ciki, Amira tadubesu tace "inaga mushiga ciki muduba watakil suna ciki saboda sai 10am jirgi zai d'aga kamar yanda naga sun rubuta acan" tanunamasu wanu k'aton allo fari da akai rubutu akansa,,,"....
Wucewa sukai ciki suka fara dube duben inda zasu hangosa, sunkai kimanin 30mnts suna zaga wajen harsuka gaji sukai tsaye kusa da wasu jamian tsaro dake kula da wajen,,,....
Can kamar ance nusy ta waiga tana waigawa kuwa tahangosu suna tafiya izuwa gun flyt yasakko domin sushiga suwuce, dasauri tajuya tacewa su Amira "Amira gayacan zasu shiga jirgi" dasauri harda gudu suka kama hanyar zuwa gunsu.........
*kuyi manage da wannan 😍 kunsan bangama warwarewa ba*
#/Vote
#/Share
#/Comment
'''AUFANA for life '''
*I.W.A*🖋
_*TSINTACCIYAR MAGE....*_🌷
_*BY~AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183_
® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚
_*Page 19/20*_
_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_
Dasauri harda gudu suka kama hanyar zuwa gunsu saidai kash suna kaiwa dai dai wajen masu tsaron hanyoyi saisuka taresu suka hanamasu wucewa saboda dokace bawanda yake wucewa daga nan zuwa gun flyt sai waenda zasu shiga jirgin,,,....
Cikin magiya nusy tafara masu magana "pleace dan Allah kuyi hak'uri kubarmu mushiga gun yayanmu zamuje plss" kallonsu yai d'ayan yace "ina card's d'inku" kallon juna sukai nusy tace "kaga a uzurce muke wlh bamuda card's plss kubarmu muje" bindiga suka fiddo cikin masifa suka nunasu sukace "idan bakubar nan ba zamu harbeku wlh kokuma mukaiku station d'inmu" badan sunsoba haka sukabar wajen suna kallonsu MUJAHID har suka shige jirgi suka d'aga suka bar wajen,,,....
Wani naushi nusy takaiwa iska tareda fad'in "ohhh...!!!shettt" munira kuwa ji take kamar tai kuka tsabar takaici Amira kuwa shuru kawai tai tajuya sukabar wajen,,".....
Saida sukai ban kwana da juna cikin fara'a sannan yashiga jirgin shi da mubashir, saida jirginsu yad'aga sannan rayyan yawuce izuwa gidansa yana kewar amininsa,,,.....
Har jirginsu yabar k'asar UGANDA MUJAHID nakallon k'asa ji yake kamar yai tsuntsu yaje yad'akko MUFIDA sutafi atare saidai ina bahalin yin hakan,,"....
Acikin mota suna tafiya kowa yai shuu zuciyoyinsu cike da takaici da b'acin rai, koda suka isa gida tana kwance akan kujera tai shuu mubina na gefenta tana danne dannen system, suna shigowa ta tashi dasauri tana kallonsu, a yanayinda taga fuskokinsu dakuma irin yanayinda suka shigo dashi shine ya tabbatarmata da amsarda take nufin tambayarsu ma'ana ba'adaceba,,,....
Wani murmushi tai wanda yafi kuka zafi tace "baku gansaba ko bakugansaba dama nasan bazaku gansaba shikenan narasa mr man narasashi narasashi har abad....a" tafashe da matsanancin kuka maicike daban tausayi munira da nusy ma kukan sukeyi munira tazo tarungumeta tana rarrashinta, wani mugun kallo mubina kebinsu dashi can kawai tad'auki earpiece tasaka a kunnenta sannan tamik'e tsaye tana waka tawuce abunta,,,"...
Kallo kawai suka bita dashi basuce mata uffan ba, sunjima acikin wannan halin daga k'arshe nusy da Amira suka fita suka wuce munira taja MUBINA suka shige ciki, wanka sukai suka sauya kaya sannan munira tabama MUBINA maganinta tasha takwanta,,,,"....
Washe gari around 8am suka gama shiri tsab, zaune take akan gado tad'ora hanunta a kanta tai shuuu idanuwanta suna kallon sama, mubina ce tashigo rik'e da akwatinta a hanu tana yatsine fuska tace "hamma yace kufito muwuce gashican acikin mota yana jiranmu" tana gama fad'ar hakan tai gaba abunta itako munira ko k'ala batace da'ita ba MUFIDA kuwa dama talula a duniyar tinani, bayan munira tagama komai tai rolling da veal d'in rigarta saitazo ta dafa shoulder d'inta dak'arfi tadawo hayyacinta cikin murmushi munira tace "am sorry big aunt hamma yafito yana jiranmu" murmushi tai tashafa fuskarta sannan tasakko tasaka takalmanta taje gun mirror tai rolling na veal d'in rigarta kasancewar kaya iri d'aya suka saka ita da munira Arabian gown red color,,,,.....
Bayan tagama sannan tad'auki jakarta da phone nata da jakar takalmansu suka fita, suna fita saigasu Amira nan suka rungume juna sannan sukai bankwana suka rakasu har gun mota,saida suka shiga suka wuce sannan su Amira suka wuce kasancewar su sai gobe zasu wuce,, suna isa airport basu wani dad'eba jirginsu yad'aga izuwa gida Nigeria,,,....
*KEBBI CITY.....*
1pm dot jirgunsu yasauka a katafaren filin jirginnan mai suna AHMADU BELLO INTERNATIONAL AIRPORT BIRNIN KEBBI, KEBBI STATE, suna fitowa saiga bodyguard's d'insu sun iso suka karb'i kayansu sannan suka wuce, wasu galla gallan motocine nahango bak'ak'e wulik sai shining, tinda suka sakko MUFIDA tafiddo glass d'inta no respect tasaka, suna isa aka bud'e masu murfin mota suka shiga ga jamian tsaro gabansu da bayansu,,....
Kai tsaye katafaren gidansu dake G.R.A birnin kebbi aka wuce dasu