Showing 18001 words to 21000 words out of 76905 words
murna da farinciki,,,"....
MUFIDA kuwa yau farincikinta baya misaltuwa, ana gamawa suka wuce gidan hajiyar dady su munira kuwa anacan ana yawo tareda k'awaye,,,....
Suna zaune acikin parlon hajiya plate d'in abinci na kan cinyarta tanaci saiga faruk yashigo, bilkis naganin yashigo ta tashi tafita bilkis nafita itama tamik'e tsaye zata wuce saiya fizgota tafad'o k'irjinsa, wani mugun kallo tamasa sannan tace "kasakeman hanu malam" murmushi yamata sannan yace "am sorry my lovely wife, tin lokacinda abunnan yafaru naketa neman nasamu dama nabaki hak'uri amma saikikaki bari naganki kika hanawa idanuwana ganin kyakkyawar fuskarki, haba k'anwata kiyi hak'uri mana Allah ma munamasa laifi murokesa kuma ya yafemana bare mu y'ay'an adam ajizai" wani irin murmushi ne yasub'ucemata batareda tama saniba saboda mamaki takallesa tace "Allah sarki ashe kazama malam asshekh bansaniba katuba kenan to mezai hana kakoma islamiyya kadinga koyarwa watakil acan wa'azinka zaifi karbuwa amma nankam sam bazai tab'a karbuwa ba bare har yashiga kunnena, kad'auka salon yaudarar taka zai tasiri akaina sanin kankane ni sam ba'irin sauran 'yammatan nan bane" tana gama fad'ar haka tacire hanunsa daga k'ugunta tajuya tawuce tabarshi tsaye sololo yana kallonta,,,".....
Batawani dad'e ananba takira mani driver yazo yad'auketa suka wuce gida,,....
***** *****
Rayuwa tacigaba da tafiyarmata bayanda takeso ba saboda har yanzu momy bata kula da'ita kamar yanda take kula dasu mubina wulak'anci mubina da raininta izuwa gareta sai dad'a k'aruwa yake saidai ita sam bata biyemata bare sudunga fad'a kullum,,,.....
Watansu uku da dawowa aka saka ranar bikin MUFIDA da faruk sannan MUFIDA da mubina suka fara aiki a katafaren company na Abban faruk, hakan kuwa bak'aramin dad'i yayiwa faruk ba saboda koba komai zai dinga ganinta kullum kasancewar shine manager a camfanin,,"....
***** *****
Kimanin sati d'aya kacal yarage afara shagalin bikinsu MUFIDA tini aka kawo lefe wanda Maryam yayar faruk tahad'o daga DUBAI, tinda aka kawo lefen MUFIDA ko kallonsa batayiba aranarda aka kawowasa kuwa kwanatai kuka dan kwata kwata ranar batai wani baccin kirkiba wato dai tanaji tana gani za'amata auren dole,,,....
Dady da Abban Ammar sunbude bakin aljihunsu sai b'arin naira suke tamkar basusan zafinta ba tini dady yai order na kayan d'aki k'asar Italy, gidajen biyu kuwa gaba d'aya ansauya masu fasali anyi sabon fenti ansaka sababbin kaya,,"....
Wata ranar Tuesday ne MUFIDA tadawo daga aiki koda tazo saita tadda Aunty maryam, cikin fara'a kuwa tazauna suka gaisa saitacemata "kishiga kishirya zamu fita yanzu driver yana jiranmu" batai musuba kuwa tawuce domin ta shirya,, batawani b'ata lokaciba tafito taje gun momy tafad'a mata zasu fita, cikin fara'a tadubeta tace "to adawo lafiya" tace to tawuce, a y'an kwanakinnan tana mamaki sosai yanda momy tasake mata fuska tamkar baita bace tsawon shekaru kotace tin tashinta har izuwa girmanta momy bata tab'a yimata kamar yanda takemata yanzu ba abun yamatuk'ar bata mamaki sosai,,,"....
Kai tsaye gidan maryam dake unguwar ghesse phess 1 suka wuce suna isa gateman yabud'e masu gate suka shiga, suna isa cikin parlor sai MUFIDA taga wasu mata su uku daganinsu manyan mata ne wayayyi, gaidasu tai cikin girmamawa suka karb'a cikin fara'a d'ayar tace "a,a itace amaryar tamu" aunty maryam tace "eh itace" masha Allah barakallah. d'ayar tafad'a itadai MUFIDA jinsu kawai take,,"....
Basufi 30mnts dazuwaba aunty maryam takirata bedroom d'inta koda taje saitaga wasu manya manyan robobi cike da abubuwan kayan mata anandai tafahimci gyaran amare ne za'amata, wani irin takaici da bak'inciki ne taji sun mamaye zuciyarta kamar tatsala ihu, bawasa matan suka fara mata gyaran jiki suna hadeta da tsime kala kala da tirarikan saka maigida ihu, hhh Lol,,,"....
Kimanin kwana uku suka d'auka sunamata gyaran jiki kala kala irinna matan kebbi, ita kanta MUFIDA tasan ta canja gyaran yamatuk'ar k'ara fito da tsintsar kyanta da kyan surarta, fatarta tai kyau takara fari sai kyalli take kamar hasken rana, acikin kwanaki k'alilan suka kammala mata gyaran jiki,,,....
***** *****
Yau takasance Wednesday kuma itace ranarda za'afara gudanarda bikin yau ne za'ayi kamu, tin 10am aka wuce da'ita domin yimata lalle da saloon, bak'in lalle da ja akamata sannan aka gyaramata sumarta tasha mayuka kala kala bayan angama sannan suka dawo,, around 3pm dot akafara mata make up da shirin kamu, sai 3:30pm sannan aka kammala komai 4pm aka wuce izuwa gunda za'ayi kamun,,,"....
Koda suka isa kuwa tini wurin yagama cika taff da mutane waenda aka gayyata dama waenda ba'a gayyata ba, matan manyan y'an kasuwa da masu gomnati dik sunzo,,, kamu yayi kamu taro yayi taro sai kusan 7pm sannan aka gama driver's sukazo suka d'auki amarya da aunty maryam da bilkis kasancewar ba k'awar amarya ko d'aya hakan yasa dole bilkis ce tamaye gurbinsu,,,"....
Washe gari akai mother's night tin 10pm aka fara sai 1am aka gama, wannan event d'in yafi kamu had'uwa da tsaruwa kuma yafi samun mutane sosai dan harda matan governor of kebbi state sunje hjy Aysha da hjy Zainab kasancewar ranace ta uwaye, MUFIDA tasamu kyatutuka sosai daga matan shugabannin gomnati da matan abokanan Abban Ammar, bayan angama aunty maryam tadaukesu suka wuce gidanta kasancewar tin lokacinda akamata gyaran amare take acan tahanata fita ko'ina ko wani abu takeso saidai tasaka munira taje tamata,,,"....
Tinda bikin yagabato hankalin MUFIDA yatashi takasa samun nutsuwa kullum cikin kuka take da bak'in cikin auren faruk dazatai kullum kuma cikin sallolin nafila da azkar take tana rok'on Allah idan aurensa shine alkhairi agareta to Allah yabata ikon yimasa biyayya idan kuma bashine alkhairi ba to Allah yayi gaggawar watsardashi ya tarwatsashi, kullum haka take kwana tana addu'oi, tin ranarda akai kamu mubina tasake zuwa kowanne event ba shima dolece tasaka taje y'an office d'insune sukazo sukace tare da'ita zasuje hakan yasa dole badan tasoba tashirya sukaje, munira kuwa hmm sai inda k'arfinta yak'are dan tinda akafara gudanarda bikin bata zaunaba dik abunda MUFIDA keso itace kezuwa tamatashi,,,"....
Washe gari dinner, dawuri suka tashi aka d'auketa izuwa gidan hajiyar dady saboda takira tace akawomata ita taganta, dasukaje guntama kayan matane tasakata a gaba tadinga bata wurin ranar haka MUFIDA tayisa hajiya naturamata su wasu tasha wasu kuma tazubar saboda tagaji da shansu sosai harshenta harya sauya kala saboda shaye shayen kayan mata,,,......
Bayan sunyi sallar isha sannan aunty maryam tazo ta d'auketa suka wuce gidanta, acan mai make up tacimmasu tafara tsantsara mata had'adden make up saboda ranar yau taci uban kowacce don ango zaizo da abokanansa...........
#/Vote
#/Share
#/Comment
```AUFANA for life ```
*I.W.A*🖋
_*TSINTACCIYAR MAGE.....*_🌷
_A true love story_
_*BY~AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183_
® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚
_*Page 27/28*_
_Note Edited_
_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_
Saikusan 9pm sannan aka gama had'e amarya cikin wata tsadadiyar wedding gown blue and white color har k'asa take, takalmanta da jakarta dakuma d'an kwalinta dik silver color ne tahad'u matuk'a takoma tamkar y'ar tsana kamar ka d'auketa ka gudu sai kyalli take tana shining tamkar hasken farinwata acikin sarararin samaniya aunty maryam da k'awayenta sai d'aukanta pic's suke hakama munira da k'awayenta,,,.....
10pm dot motocin ango dana abokanansa sukazo domin d'aukan amarya nanfa MUFIDA tace bazata shiga motarsu ba atare da aunty maryam zataje, dik yanda sukazo tashiga motar angonta fafur tak'i dole badan sunsoba suka tafi suka barta ran hamma faruk a b'ace suka wuce, a ransa cewa yake "yarinyar nan dole na gyara mata zamanta saboda nafuskanci rainani takeso tayi bari kawai Allah yakaimu gobe zaki bambance tsakanin aya da tsakuwa badai ni kike wulak'antawa a gaban abokanainaba hmm zakiyi nadamar yin hakan" haka yaita tinani dakuma tsara yanda zai hukuntata da salon muguntarsa,,,"....
Bayan sunwuce aunty maryam tad'auketa a tata motar da k'awayenta suka wuce, dasuka isa tsayawa sukai domin jiran karasowarta saboda kowa ya hallara ango da amarya kawai ake jira, suna nan kuwa suma suka iso nan su aunty maryam suka sakasu a tsakiya su munira da bilkis da k'awayen munira tareda k'awayen hamma suka shiga gaba wasu kuma suka tsaya baya sannan suka kama hanyar shiga holl d'in,,,....
Tinda suka danno k'afafunsu aka taso akafara basu zafafan pic's da DJ kuma yasake sautin amarya da ango, har suka isa gunda aka tanadar dominsu ba'adaina basu pic's ba, bayan sun zauna MC yazo yatsayarda masu d'aukan pic's d'in sannan yafara gudanarda abunda yatarasu,, bayan yayi yan maganganunsa sannan akace yanzu ango da amaryarsa zasu yanka cake danhaka kowa yamayarda hankalinsa nan sannan yabada attention nasa nan DJ yasaka sautin kida mau d'auke da sassanyar waka irinta masoya,,,, aunty maryam ce tazo ta taso da MUFIDA sannan shima yataso aka bud'e cake d'in sannan aka basu suka matar commissioner ce ta taso takarb'i microphone tafara karanto kalmomin dake cikin I LOVE U d'aya bayan d'aya saida takai U sai suka yanka cake d'in nan aka d'auki shewa ana tafi nan yadiba yasakamata a baki itama ta d'iba zata kaimasa abaki sai tai tsaye tana kallonsa tana murmushi kwallah nazuba daga idanuwanta,,,".....
Siffar MUJAHID taga yakoma mata yanda yake murmushinnan nasa nan takaimasa abaki yakarb'a tareda d'an cizar yatsunta, dasauri tacire hanun tana fad'in "aaashhh....!!!" alamar taji zafi tana yarfarda hanun nan akaita dariya ana kallonsu, shima dariyar yake a zatonsa MUFIDA tasauke karan tsanarda tamasa ganin hadda murmushi take masa nan kuwa baisan ita abunda take nufi dabanba, bayan sun yanka cake aka jasu izuwa wani gu da aka tsarasa acikin holl d'in tamkar lambu gun shak'atawa DJ yasakamasu wata waka wacca JAWAAD yayiwa ZULAIHERT d'insa mai suna WAIT FOR ME MY HUBBY ZULAIHERT, k'ugunta yarik'o yad'ora hanunta kan shoulder d'insa sannan shima yad'ora nasa kan gefen k'ugunta d'aya suka fara rawar jajayen fata,, hmm hamma faruk wallahi kai d'an duniyane na k'arshe hhh Lol,,"....
Ahalin yanzu dik siffar MUJAHID itace take gani ga faruk hakan yasa dikta susuce tadawo tamkar wacca tai loosing memory dik yanda yajiyata can take tafiya, hakan yabama hamma faruk mamaki sadai yaji dad'in hakan sosai, sundauki y'an mintina suna rawar sai d'aukansu ake ana video recording nasu abun gwanin birgewa sannan akace suje su zauna akacigaba da shan shagali ana cashewa,,,, sai kusan 2am sannan aka gama dinner d'in kowa ya watse,,,".....
Har suka koma gida munira nacike da mamakin yanda MUFIDA ta sauya itadin ma haka mamakin kanta take yanda tasake masa jiki yau kamar baitaba,,,"....
Washe gari Friday around 3pm bayan ansakko daga masjid dibban jamaa suka shaida d'aurin auren MUFIDA da UMAR FARUK akan sadaki mafi tsoka nai dubu d'ari, bayan angama d'aurin auren dady yashiryamasu walima akatafaren holl dinnan mai suna ROYAL SPECIAL HOLL, angon kuwa yau garinciki agunsa ba'amagana shima bayan andaura auren yakwashi abokanansa izuwa gidansa dayake alfasharsa sukaje suna cashewarsu da holewa,,"....
A b'angaren amarya kuwa tinda aka d'aura auren tagudu gidan hajiyar dady batareda kowa yasaniba ko acan dinma dataje dikda d'inbin jamaar dake cike famm a gidan bata bari kowa yaga shigowartaba tashige d'akin bilkis tarufe kanta taita darzan kuka tana fad'in "wayyo Allah na kaicona kaicon rayuwata meyasa zuciyata takasa bayyana sakonta izuwaga mr man dayanzu shine wanda zai malleka meyasa rayuwa ta juyaman baya meyasa rayuwata ke tafiya ahaka, wallahi hamma banasonka bana k'aunarka kuma babu ranarda zan so ka natsaneka kuma natsani rayuwarda zanyi dakai wayyo Allah na kajikaina kashiga lamari na" tak'arasa tareda fashewa da matsananci kuka mai ban tausayi mai raunana zuciyar wanda yajisa,,,"....
Haka taita rerasa tin muryarta nafita harta disashe,,,....
Lokacinda aunty maryam ta ankara da MUFIDA bata cikin gidannan bak'aramin tashi hankalinta yayiba nantake aka bazama nemanta acikin gidan amma dik wani lungu da sak'o na gidannan annemeta anrasa, hankalin maryam yak'ara tashi hakama dik wani dake cikin gidan hankalinsa yatashi nantake maryam takira dady tasanardashi, hankalin dady ma yatashi ba kad'an ba nantake yakira gidan hajiyarsa yasanardasu abunda ake ciki sannan yasaka akafara nemanta acikin gida,,,....
Ananma ko'ina saida aka duba amma ba'agantaba, bak'aramin tashi hankalin dady yayiba nantake yakira commissioner of police yasanardasu abunda ake ciki nanfa akafara nemanta akasaka tattsauran tsaro acikin unguwar ghesse phess 1 dakuma G.R.A,,, ana cikin nemanta kamar ancewa momyn su faruk tabud'e d'akin bilkis aikuwa tana bud'ewa saitahango MUFIDA kwance akan gado, dasauri taje gunta ta tallafota saitaga ashe bata numfashi, cikin tsintsar tashin hankali momyn faruk tad'auki wayarta takira abban Ammar tafad'a masa nan shima yakira dady yafad'a masa,, cikin y'an mintina suka iso gidan a firgice dady yaje yad'auki MUFIDA ganin bata numfashi yasa hankalinsu gaba d'aya yatashi nantake cikin sauri suka kama hanyar hospital,,,"....
Daisarsu kuwa ba b'ata lokaci aka karb'eta domin bata taimakon gaggawa,kasancewar dama likitan yasan matsalarta yasa hankalinsu bai wani tashi ba kuma nantake suka shawo kan matsalar tadawo cikin hayyacinta, saida likitan yafito yafad'a masu ta farfado sannan hankalin dady ya kwanta ya sauke nannauyan numfashi,,,"....
Dik wainarda ake toyawa faruk baisaniba yanacan suna holewarsu a gidansa saida lokacin d'aukan amarya yai yaga harma yawuce dan har 11pm tayi sannan yake yiwa hajiyar dady magana wai har yanzu lokacin d'aukan amarya baiyiba,, wata iriyar harara hajiya ta wurgamasa kan tace "kana nufin kace bakasan abunda yasameta ba kenan" dasauri yataso daga kan kujerarda yake zaune tareda zaro idanuwansa yace "meya faru da'ita hajiya" kallonsa tai sannan tace "to natacan asibiti anyi admitting nata tin d'azu" dasauri yamik'e tsaye yad'auki carkey d'insa yafita, kallo hajiya tabisa dashi tace "ohh yaran zamani ba kunya yanzu fa can zashije bako kunya watakil ma yace acan zai kwana",,,....
Kai tsaye hospital d'in yawuce koda yaje harta farka tana zaune dady nabata abinci a baki tanaci yamata firar barkwanci tana dariya, cikin sallama yashigo yagaidasu dady suka amsa sannan yakalleta yacemata "sannu MUFIDA yakarfin jiki" batareda ta kallesaba tace "dasauki" ganin faruk yazo yasa dady yatashi yacewa abban ammar suwuce, dasauri tarik'o hanun dady cikin shagwab'a tace "plss dady karka tafi" murmushi yai sannan yace "karki damu my dear zan dawo kinji" ya sumbaci goshinta sannan yawuce,,"....
Ganin suntafi yasa yazo zauna gefen gadon yad'auki plate d'in abincin yadiba yakaimata baki saita juya fuskarta tak'i karb'a tareda watsa masa harara, murmushi yai sannan ya'ajiye plate d'in, matsowa yai dab da'ita yahard'e k'irjinsa da nata sannan yakai hanunsa yarik'o hanunta yana kallon lallenda akamata yana murmushi, dasauri tafizge hanunta cikin masifa taso ta turesa da hanu d'aya saboda d'ayan mak'ale yake da drip sai kuma takasa,,"...
Goshinsu yahard'e gu d'aya har suna shak'ar numfashin juna suna kallon cikin idanuwan junansu, ture gishinsa tai da nata cikin tsintsar b'acin rai yayinda tsanarsa kuma ke k'ara cika zuciyarta, bata ankaraba kawai taji bakinsa acikin nata yana tsotsar yawunta cikin salon yaudara sannan yacusa hanunsa acikin k'asan rigarta yakamo brez d'inta hanunsa d'aya kuma yadinga shafar surarta cikin wani irin salon yaudara, cikin sauri tayunk'ura da dika hannayenta dikda jikinta bayada kwari amma nantake taji k'arfi yazomata taturesa harsaida allurar dake cikin hanunta ta drip tafita da k'arfi jinin yadinga zuba,,,.....
Cikin masifa tanunasa da yatsa ta zaro dara daran idanuwanta tace "wannan yazamemaka na k'arshe dazaka sake tab'a jikina idan bahakaba kuma wallahi zan iya zama ajalinka" shima cikin b'acin rai yanunata da yatsa yace "ba ubanda ya'isa yahanani morarki saboda dagake har abunda kika mallaka nawane k'udi nasaka nasiya saboda kinyi kad'an wallahi ki hanani na more naji dadina" au hakama zakace to shikenan ni da kai shege ka kafasa. Fita yai fuu yawuce ransa a b'ace itakuma takoma kan gado ta kwanta tareda dafe kanta dakemata ciwo,,,"....
Kwananta biyu kacal aka sallameta suka koma gida nan akafara mata shirin wucewa izuwa gidanta, a ranarda zata wuce kuwa saida dady yamata nasihohi masu ratsa jiki akan biyayyar aure taita kuka, daga nan akawuce da'ita gidan hajiyar dady suma suka d'ora daga inda dady yatsaya, sai 10pm sannan aka d'auketa izuwa gidan mijinta dake unguwar ghesse phess 2 tareda y'an aikinta guda biyu da dady yabata domin sutayata aikin gida, aunty maryam ce dasu munira sai gwaggonsu k'anwar su dady hajiya Amina da y'ay'an ta biyu twin's Afra da Afza sune sukayiwa MUFIDA rakiya suna isa kuwa basu wani jimaba suka fito suka barta..........
Kuyi manage da wannan 👏
#/Vote
#/Share
#/Comment
```AUFANA for life ```
*I.W.A*🖋
_*TSINTACCIYAR MAGE.....*_🌷
_a true love story_
_*BY~AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183_
® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚
_*Page 29/30*_
_Not Edited_
_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_
Bud'e mayafinda aka rufe mata fuska dashi tai ta tashi tafita parlor, kallon yanda aka narka mata dukiya acikin parlon take aranta tace "hmm wallahi dama dady yasani da bai wahalarda kud'insaba a wannan k'azamin gidan mara tsabta wanda yake cike da k'azanta" sauran d'akunan tawuce tashiga, 3bedrooms ne da 2parlors sai d'akin y'an aiki d'aya wanda yake kusa da kitchen, d'akinsu harira 'yan aikinta tashiga cikin girmamawa suka gaidata tareda tambayar ko akwai abunda take buk'ata tacemasu aa nan tamasu saida safe tawuce,,,"....
D'akinta takoma tacire kayanta tadaura towel tashiga toilet, wanka tai ta d'auro alwala sannan tafito, bayan tafito tashafa mai takunna AC sannan tasaka wata doguwar riga bak'a mara nauyi tasaka hijab tashimfid'a prayer met tafara sallah,,, tanacikin sallah yashigo ganin tana sallah yasa yafita,,"....
Tana k'are sallar tai saurin d'aukan key tarufe k'ofar sannan tadawo tacire hijab ta linke prayer met tamayar cikin wardrobe sannan takashe fitilar dak'in tahau gado ta kwanta taredayin addu'ar kwanciya bacci, batafi 15mnts da kwanciya ba taji yana bubbuga k'ofar amma tai shuu kamar batajisa ba, haka yaita bubbuga k'ofar yana kiranta harya gaji dole yawuce nasa dak'in ya kwanta,,"....
Washe gari bayan tai sallah saita sake komawa bacci, sai kusan 12pm sannan tafarka tashiga toilet tai wanka tafito tasauya kaya izuwa atamfa sket da riga, batai make up ba tadaura d'an kwali sannan tasaka wasu plat shue tad'auki key tabud'e k'ofar tafita parlor, koda tafita saita tadda su harira a kitchen suna girki nan suka gaidata sannan tace "hamma faruk yafita ne" harira tace "eh yafita tin d'azu yake zaune parlor yana jiran fitowarki dayaga baki fitoba shine saiya fita" wani irin dad'i taji acikin zuciyarta harsaida tad'an murmusa sannan tace "ok to me kuka girka mana ne" harira tai murmushi tace "naki breakfast yana can kan dining kekadai yake jira" tai murmushi tawuce, bayan tagama break tafito tacewasu harira "kudafa dik abunda kukeso shima kudafamasa nasa" suka amsa da to sannan tawuce d'akinta tasaka key tai kwanciyarta,,,"....
Idan ran faruk yai dubu to yab'aci ba'asababa b'ata masa rai kamar daren jiya ba, yakasa zama yakasa tsayi sai zarya yake acikin d'aki yana tinanin irin