Showing 30001 words to 33000 words out of 76905 words

Chapter 11 - TSINTACCIYAR MAGE BY AUFANA.txt

AUFANA   

12 Dec 2024

4303

tana kuka itama Amiran kuka take saboda ganin yanda MUFIDA tadawo tamkar wacca batada gata wacca kuma batada kowa a duniya, kuka take sosai dakyar Amira ta rarrasheta tadaina kukan tadubi Amira tace "Amira kinga yanda duniya tajuyaman baya ko bayan auren dole yanzukuma ga kazafin kisan kai Amira bansan wane laifi nayiwa ubangiji ba yake jarabtana da waennan mugwayen kaddarori..." bata k'arasaba Amira tarufemata baki tana juyamata kai alamar tai shuru sannan tace "MUFIDA kidaina fad'ar haka dik abunda kikaga yasami bawa to *MUK'ADDARI* ne daga ubangijinsa, yanzudai mudaina wannan zancen wannan shine lauyanda muka d'auka wanda zai tsayamana jibi a gaban alkali" saita nuna Rayyan tasake cewa "sunansa barrister Rayyan Al-mustapha inafatar kin shaidasa",,,....

Murmushi tai sannan tace "eh Rayyan abokin mr man" Amira tai murmushi sannan tace "eh shine lauyanda muka d'auka lauyane mai zaman kansa ba lauyan gomnati ne ba" kallonsa MUFIDA tai ta gaidasa ya karb'a sannan suka zauna suka fara tattaunawa yana mata tambayoyi tana bashi amsa,, saida suka gama sannan security d'in yazo yakoma da ita,,,....

Acikin kwanakin Rayyan yadinga bincike akan wannan case d'in a b'oye batareda momy tasaniba tindaga masu aikin gidan security's gateman da dai sauran masu aikin gidan, acikin k'ank'anen lokaci yafara samun kwakkwarar shaidarda zai gaba tar a kotu,,"...

Saura kwana d'aya ashiga kotu Rayyan ya ziyarci gidansu MUFIDA, bayan anmasa iso ankawomasa ruwa sai momy tashigo tazauna suka gaisa sannan yagabatarmata kansa "hajiya sunana Barrister Rayyan Al-mustapha lawyer mai zaman kansa nine lauyan MUFIDA nazone nad'anyimaki wasu tambayoyi" tinda momy taji yace shine lauyan MUFIDA ta tamke fuska tasha kunu,,,...

Wani mirmushi Rayyan yai sannan yace "hajiya lokacinda MUFIDA tashigo harta kashe Alhj shin kina inane sannan dawa dawa ne acikin gidan?" juya fuskarta tai sannan tad'ora k'afarta d'aya kan d'aya tamasa wani kallo sannan tace "ni lokacin ina kitchen gidan kuma bakowa munira na school mubina kuma na office sai mustapha yana bacci masu aiki kuma dik suna ghost house" yan rubuce rubuce yai sannan yacigaba "ok to kince kina kitchen to ya akayi kikaga lokacinda takasheshi ko wanine yagani yazo yafad'a maki?" a,a lokacinda tashigo bangantaba amma lokacinda zata fita na ganta lokacin kuma zanshiga gun Alhj ne. "ok to ya akayi kikasan itace takasheshi dakanki kika kamata kokuwa ya akayi ne?" a,a bankamata ba amma lokacinda take fitowa naga jikinta dik alamun mara gaskiya bandai yarda da'ita ba sai kawai nashiga ciki koda nashiga kuwa sainagansa kwance akasa tacafkamasa wuk'a acik....i" saita fashe da kuka,,,...

Kyaleta yai saida tad'an tsagaita sannan yamik'a mata ruwa takarb'a tasha sannan yacigaba da "hajiya lokacinda kikaga tafito kinga alamar jini ajikinta ko zufa?" nankam shuru tai tafara rabon idanuwa sannan tace "a,a banga komai ajikinta ba" rubutu yai sannan yace "ok nagode sosai hajiya amma dan Allah inaso nacire CCTV cameras dake cikin parlon nan dakuma d'akin Alhj" dasauri tad'ago idanuwanta tana zarosu, sam brain d'inta baitab'a kawo mata tinani akan camera's d'indake cikin gidanba amma badamuwa zansan yanda nai, yanayinda yaga tashiga hakan yak'ara bashi kwarin guiwa, badan tasoba tace "O....K...Ok toh" yai murmushi sannan yatashi yafita jim kad'an yadawo tareda masu cirarsu nan suka hau suka kwancesu suka bashi sannan yayiwa momy godiya yawuce,,"...

Aiki yake tukuru har kusan 2am yana binciken camera's d'in shiga da ficenda akai aranar, hankalinsa yad'auke yana kan aikinda yake kamar ance ya waiga saiyaga wani mutum yawurga ta k'ofar parlor, tashi yai yaje yad'auki wuk'a yafara tafiya ahankali sadaf sadaf domin,,,....

Har ya'isa cikin parlon baiga kowaba nan yafara dube dube har yabud'e k'ofar fita baiga kowaba yafita yadudduba ko'ina har bayan gidan amma baiga kowaba saiyadawo ciki yarufe k'ofar yakoma d'akinsa,,,....

Koda yazauna yajanyo laptop d'insa domin cigaba da aikinsa saiyaga anmasa delete all komai ya goge har abunda yad'akko acikin camera's d'in gidansu MUFIDA, mamakine yakamasa nan yacigaba da bincike amma haryagama baiga komai yadawoba tabbas yagoge nan ya tabbatar da wanine yashigo yad'auki hankalinsa "ohhh....shet!!!" yafad'a tareda kaiwa iska naushi cikin takaici da b'acin rai...........

Kuyi manage da wannan muhadu gobe zakusamu dayawa insha Allah





#/Vote
#/Share
#/Comment

'''AUFANA for life '''
  *I.W.A*🖋
_*TSINTACCIYAR MAGE....*_🌷
_a true love story_


_*BY ~ AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183_


® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚


_*Page 41/42*_
_Not Edited_

_*BISMILAHIR RAHMANIR RAHIM*_

Wayarsa ya d'akko yai dialing number na Amira cikin saa kuwa tadaga kasancewar itama takasa bacci sai nafiloli take tana kaiwa Allah kukansu daya taimakeso yatonu asirin dik wanda ya aikata wannan laifin kuma yacuci MUFIDA yasaka acikin wannan sarkar mai wahalar kwancewa,,,...

Tana dagawa batareda yamata ko sallama ba saboda yanda ransa yabaci yafara magana "Amira wallahi komai yajagule yanzu aka shigoman gida aka dauki hankalina naje naduba wanda yashigo koda nadawo saina tadda dik evidence d'inda nahad'a tin shekaranjiya izuwa yau komai angoge" Subhanallah. Amira tafad'a tai shuu tana jinjina wannan al'amarin can tace "tabbas dik wanda ya'aikata wannan abun olready dama bibiyarka yake saboda haka yanzu dole kakiyaye kanka" hmm....!!! yasauke numfashi sannan yace "tabbas hakane amma idan sunsan wata ai basusan wataba insha Allah bazan kwanta harsaina samu evidence d'inda zan gabatar gobe a kotu" murmushin jin dad'i Amira tai sannan tace "to Allah yabaka nasara ya taimakeki muma insha Allah bazamuyi bacci ba munanan muna kaiwa Allah kukanmu itama MUFIDA nakaimata Qur'an da sallaya tanacan tanayi" nandai suka gama sannan sukai sallama,,,....


Daren ranar gaba d'aya suduka hud'un, MUFIDA, Amira, munira dakuma Rayyan ba wanda yai bacci, acikin daren Rayyan yaje gidan marigayi Faruk sannan yaje station d'inda suka karb'i case d'in, saida ya tabbatar yahad'a kwararrun evidence sannan yakwanta lokacin kuma yai dai dai da 5am,,,....


Washe gari tin 8am Amira da munira suka zo Court gun MUFIDA suka kwantar mata da hankali akan karta d'imauce ta kwantarda hankalinta dik abunda aka tambayeta tabada amsarsa dai dai yanda tasani karta kuskura tafad'i abunda batasaniba saboda lauyan gomnati kwararre ne sosai zai iya rikitata har tafad'i abunda bashibane daga baya kuma abun yarikice saboda haka ta kwantarda hankalinta Barrister Rayyan zaiji da komai, saida ta sallar nafila raka'a biyu sannan suka fito suka barta,,"...


9:30am Barrister Rayyan yak'araso nan sukaje gunsa suna tattaunawa, su momy ma sun iso mubina ji take kamar ta daki munira saboda haushinta datakeji wato ita tafisan wannan *TSINTACCIYAR MAGE* akan mahaifinta, momy tace barni da'ita kawai mubina maganinta zanyi wallahi,,,"....

10am dot mai Shari'a yaiso akashiga, lauyoyi suka fara gabatarda kansu lauyan gomnati yafara "am ni sunana Barrister Sadiq Abubakar lauyan gomnati" bayan yagama Rayyan shima yamik'e tsaye yace "nikuma sunana Barrister Rayyan Al-mustapha lauya mai zaman kansa nine nake kare wacca ake tuhuma" yagama saiya zauna,, wani nan nakusa da mai shari'a yamik'e rike da wata takarda yafara karantata kamar haka "A yaune zamu cigaba da sauraran kararda ake shari'a akanta ta MUFIDA Ahmad Shitu wacca ake tuhuma akan takashe mahaifinta dakuma mijinta wanda wannan shine zama na biyu zai kuma dauke mu tsawon awa biyu kacal" yana kawowa nan yajuya yamikawa mai shari'a takardar sannan yakoma ya zauna,,,....

Bayan wasu y'an dak'ik'u sai mai shari'a yad'ago yace "lauyoyi zaku iya fara gabatarda shaidun ku" lauyan gomnati yamik'e yace "ya mai shari'a inaso kotu tabani dama nai waensu tambayoyi ga wacca ake tuhuma wato MUFIDA" sai mai shari'a yad'ago yace "kotu tabaka dama Barrister" olready dama tana nan tsaye an iso da'ita saiyamatsa kusa da'ita yakalleta sannan yafara mata tambaya kamar haka "MUFIDA meyasa kika kashe mahaifinki da mijinki da mijinki? Miye dalilinki nayin hakan? Ko dai wanine yasakaki aikata hakan? Kud'i yabaki? Ko akaran kanki kika kashesu domin ki mallake dukiyarsu kotu tana sauraronki" dasauri Rayyan yamik'e tsaye taredafadin "objection mai Lord yakamata Barrister yasan yanda zai rik'a jefawa wacca ake tuhuma tambaya saboda idan yai duba da wannan shine karo na farko da tafara zuwa kotu sannan yanayinda yake mata tambayar kamar yanasone tafad'i cewa eh itace takashesu bayan kuma tuhumarta yake bashida tabbacin itace ta aikata ko ba itace ta aikataba inafatar za'adubi k'orafina my lord",,...

Daga momy har mubina ji sukai kamar suzo su shake Rayyan yamutu, hakama Barrister sadiq, su Amira kuwa wani sanyi suka faraji a ransu,,,....

Mai shari'a yadubi Barrister sadiq yace "barrister a kiyaye" yace "ok my lord za'akiyaye nagode" sannan yacigaba "MUFIDA kotu tana sauraronki" basmala tai sannan tafara magana "ni dai banice nakashesuba sannan bawanda yasakani koya bani kud'i abunda nasani dai wallahi banice nakashesuba" murmushi yai sannan yace "MUFIDA wannan kalmar itace kiketa fada amma taya kike tinanin zaki rainamana hankali mu yarda da hakan bayan kuma dubbannin mutane sunkamaki dumu dumu rik'e da wuka a hanunki lokacinda kika kashe faruk sannan dika dika tazarardake tsakanin kisan Alhj Ahmad da faruk batafi 30mnts ba sannan kuma lokacinda kika kashe Alhj kika fito uwargidansa taganki fitarki dakusan 5mnts tashiga koda tashiga ta tadda kinkasheshi" saida ta sauke numfashi sannan tace "bazan daina cewa ni banice nakashesuba, eh tabbas anganni rik'e da wuk'a saidai tinaninda sukai bahaka yakeba, dama akwai sab'ani tsakanina da faruk saboda koda akamana aure bana sonsa bashine zab'inaba kawai nayi biyayyane na auresa, tsanarsa takarda ruruwa acikin zuciyata tin lokacinda nasan shi mashayi giya ne kuma manemi mata ma'ana mazinaci, dikda haka nai biyayya nai auresa, nayi nayi yadaina shan giya amma yaki, nacigaba da zama dashi kwatsam kuma wata rana saina taddashi yai raping d'in 'yar aikina harira,, da'abun yafaru yayi nadama sosai har fushinda iyayenmu sukai akansa yasauka danhaka akace nayi hakuri nakoma gidansa",,,....

Kwallanda suka zubomatane ta tsaya ta share sannan tacigaba,,"...


Bayan nakoma da kwana d'aya kacal kuma nadawo daga gun aiki saina taddasa shi da abokanansa Suhail da Nazir acikin parlor sunyi tatil da giya sai wari suke, raina yabaci sosai sai kawai najuya naje gida nafadawa dady na, a maimakon yad'auki mataki saiyace naje nai hakuri kowacce mace da tata kaddara rayuwa ni tawace ahaka amma naje gashinan yanzu zaizo, badan nasoba haka nafito, to lokacinda nafitone raina a bace saina hadu da momy zatashiga d'akinsa kasancewar raina yana a bace yasa bantsayaba nawuce,,,....

Koda naje gida saina tadda faruk kwance akasa ancaka masa wuk'a aciki, tsintsar tashin hankali yasa narasa yanda zanyi cikin bacewar dabara saina saka hanuna nacire wukar" saita dago kwallah nazuba daga idanuwanta takallesa tace "to kaji iya abunda nasani" murmushi yai sannan yace "to munji wato kinaso kice koda kika auri faruk nakyasonsa kenan wannan dalilinne yasa kika kashesa saboda kije ki auri wanda kikeso" Rayyan yamik'e tsaye dasauri yace "my Lord inason nayi tambayoyi ga MUFIDA inafatar kotu zata bani dama" sai mai shari'a yace "Barrister Rayyan kajira har Barrister sadiq yagama nasa tambayoyin" sai Barrister sadiq yace "nagama my lord zai iyayin nasa" saiya dawo ya zauna,,,....


Matsawa Rayyan yai kusa da'ita yakalleta yace "malama MUFIDA kince koda kika shigon gidan faruk shi da abokanansa kika iske to amma koda kika dawo kika taddasa ankashesa shine kintaddasu abokanansa kokuma shi kadai kika tadda" a,a koda nadawo shi kad'ai na tadda su bangansuba. "ok to ina sukaje kuma bakya tinanin anya basune suka kashe faruk ba" eh to hakan zata iya faruwa saboda gaskiya ba mutanen kirki bane dansunma taba yin fada har Suhail ya yankawa faruk wuk'a a hanu. "Good" Rayyan yafada sannan yajuyo yace "my lord ina rokon kotu ta daga wannan shari'a izuwa wani lokaci sannan tasaka akamo suhail da nazir domin su amsawa kotu tambayoyinda take dauke dasu agaresu, daga wannan karar kuma zai bamu damar sake samo kwararan hujjojinda zamu gabatar agabanta inafatar za'a karb'i k'orafina" yana gamawa yakoma ya zauna,,,...

Shuru yaratsa kotun natsawon wasu yan mintina, can mai shari'a yadago yace "andage wannan shari'a har izuwa 2 ga watan apirilu sannan laiyoyi suyi kara kwazo domin samun kwararan hujjojin" yana fadar haka yatashi kowa yamik'e sannan yafita,,,....

Wani irin dad'i was Amira taji hakama munira ganin nasara tafara tinkarosu, tasowa sukai suka rungume MUFIDA suna dariya itama tana dariya sannan Rayyan yazo, kallonsa MUFIDA tai tace "Rayyan banida abunda zan sakamaka dashi Allah yabiyaka da mafificin alkhairi yacikamaka burikinka na alkhairi yasa kagama da duniya lafiya" murmushi yai yace "ameen MUFIDA karki damu Allah dai yabamu saa yasa muyi galaba akan wannan shari'a" suka amsa da ameen munira tace "nasara tafara tinkaromu insha Allah komai yakusa zuwa karshe" Rayyan yace "yanzu zaaje neman su suhail sannan zanje na karb'o wuk'arda akai kisan da'ita sannan kuma sainayi scanning na hannayen dik wani wanda ke cikin gidan dady da faruk saboda hakan ne zai sauk'ak'amana wajen gano wanda ya'aikata kisan" murmushi sukai suduka sannan sukace "Allah yataimakeka yabaka nasara yakuma kareka" yace ameen sannan yawuce security's sukazo suka wuce da MUFIDA ciki sukuma su munira suka wuce,,,"....


***** *****

Ahalin yanzu komai yai zafi bincike ake sosai, tini Rayyan ya karb'o wuk'ak'enda akai kisan dasu kuma yasaka anyi scanning hanun dik wani dake cikin gidan dady da faruk saidai har aka gama ba'asamu wanda hanunsa yai dai dai tambarin hanun wanda yai kisanba daga baya ma koda Rayyan yakula ashe waennan wuk'ak'en an sauya su ba ainihin sune akai kisan dasuba, murmushi kawai baice komaiba,,"....

Tini aka kamo Suhail da Nazir nan aka dinga gana masu azaba fiye da wacca akayiwa MUFIDA domin su sufadi gaskiya amma sukaki,saida sukaci wuya sannan Nazir yace "wallahi basu bane suma sunfita su siyo masu abinci koda suka dawo saisuka taddasa ancaka masa wuk'a a ciki tsoron kar a zargesu yasa suka gudu amma akwai wacca suke zargi" jin haka yasa Rayyan yacemasu "matukar kuka fadaman gaskiya za'akyaleku bazaa maku komaiba amma idan kukai hmm kunsan karshen" sunsan irin azabarda aka masu danhaka nantake Nazir yace matso nafada maka sai Rayyan yamatsa dab dashi shikuma yaduko dai dai kunnensa yafada masa,, wani irin murmushi Rayyan yai sannan yacemasu "nanda anjima za'a sakeku amma idan inaneman wani abu zan kiraku" sukace toh sannan yafita,,,"....


Yana cikin bincike a gidan faruk saiyaga tsinin takalmi na mace yana d'auke da jini a jikinsa, daukansa yai yaduba sannan yasakasa acikin leda yafita,,,....

Yana fita yakira Amira yace su had'u yanzu kuma tazo tareda munira tace toh sannan yakashe wayar, kimanin 30mnts kuwa saigasu sun iso a gidansa nan yaciro tsinin takalmin yanuna masu sannan yace "nasami wannan ne a gidan faruk munira wakika sani acikin gidanku da irin takalmannan" tana dubasa ta tina tace "wallahi na mubina ne naga takalmanta d'aya tsininsa yacire dana tambayeta saitace musty ne yamata b'arnan" murmushi Rayyan yai sannan yace "wannan shari'a tana gab da kai karshe wannan shine evidence na biyu dana samu akan mubina na uku nake jira sannan nasaka akamata" munira tace "kenan akwai hanun mubina acikin aikata wannan kisan" Rayyan yace "bama da hanunta ba itace ta aikata saidai banida tabbacin dika kisan biyu itace ta aikatasu sai idan munkamata zamusan hakan" hmm....!!! Amira ta sauke nannauyan numfashi tateda fad'in "Allah i kyauta" suka ce ameen sannan suka tashi suka wuce,,,"....


****** *****

Yau saura kwana biyu kacal akoma kotu danhaka yanzu kullum Rayyan acikin aiki yake ba zama ba tsayi, Amira kuwa dabino ta siya da Qur'anai masu yawa ta bada a masallatai domin amasu addu'ah sannan suma kullum cikin yinta suke ba dare ba rana,,,....


Around 2am zaune yake acikin parlonsa yana aiki da system d'insa, kamar motsin mutum yaji saiya share yacigaba da aikinsa,, can kuma saiya sake jin motsi saiya tashi yasakawa laptop d'insa password tayanda bayanda za'a iya bud'eta amasa b'arna sai yatashi yabarta yashige bedroom d'insa,,"....

Kamar 15mnts haka saiya fito yana fitowa kuwa saiyaga mutum tsaye yad'auki laptop d'in yanata k'ok'arin yabud'eta, dasauri yadamk'o wuyansa yajuyosa yanunasa da bindiga, fuskarsa a rufe take da bak'in abu sai yace "bud'e fuskarka" k'in bud'e fuskar yai saiya fara matsowa danufin yafara kokuwa da Rayyan sai kawai Rayyan yaharbesa a k'afa aibashiri yazube k'asa yarik'e k'afar yana ihu nan shikuma yazo yabud'e fuskar,,,....

Kujera ya janyo yakamasa ya yazaunar akanta sannan ya d'akko igiya ya d'auresa, bayan yad'auresa sannan yace "waye kai? Waya aikoka?" shuru yai yana ihu yaki yin magana nan Rayyan yadaga bindigar yace "zaka fad'a ko saina sake harbe k'afar ne" da sauri yace "hajiya Fatima ce uwar gidan Alhj Ahmad shitu da dan Allah kabarni natafi karka illatani" wani murmushi Rayyan yai sannan yad'auki wayarsa yakira police cikin y'an dak'ik'u sukazo suka d'aukesa suka wuce dashi,, wani irin farinciki Rayyan yaji saboda yaga yakusa cin nasara dakuma kai karshen wannan case d'in,,"....


Washe gari koda yaje police sun cicci uban yaron yasha duka da bakar azaba nan yaita fad'awa Rayyan dik irin tuggu da makircinda momy kesakasu sunayi ciki hadda suje sushiga kotu su kashe MUFIDA bayan sun kasheshi shi rayyan, dik abunda yaron ke fad'a Rayyan recording nasa har yagama sannan yace sudaina azabtardashi yawuce,,,"....


********

2/4/2019~ 9am dot

Tin cikin daren ranar ake ana raya masallatai da karatun Qur'an domin neman samun nasara dacin galaba akan wannan shari'a, hakama MUFIDA da Amira da munira kwana sukai suna karatun Qur'an suna kaiwa Allah kukansu kuma Alhmdllh dan sunji acikin zukatansu insha Allah zasuyi nasara dan tinda safiya tawaye MUFIDA takejin kanta acikin yanayi mai dad'i,,,...


9:30am kowa ya hallara amma banda su momy harsu hajiya da Abbu da Abban ammar dik sunzo amma momy da mubina basuzoba, hakan baisa su MUFIDA sunyi mamakiba shi Rayyan dama yayi tinanin bazasu zo ba dansunsami labarin yakama yaronsu,,,"....

10am dot akashiga kotu mai shari'a ya'iso, bayan lauyoyi sun gabatarda kansu sai aka fara sauraron karar, mai shari'a yadago yace "lauyoyi zaku iya fara gabatarda shaidinku" nan Barrister Sadiq yai saurin mik'ewa tsaye yace "my lord inaso zanyi waensu tambayoyi ga wacca nake tuhuma wato MUFIDA inafatar kotu zata bani dama" mai shari'a yace "kotu tabaka dama barrister" nan yamatsa kusa da MUFIDA yakalleta yace "malama MUFIDA kince bake kika kashe Alhj Ahmad da Faruk ba amma a bincikenmu damukai a na'urorindake gidan Alhj da faruk wato CCTV camera's dinsu nuna kece kika kashesu sannan tambarin hanunda ke akan wuk'arda akai kisan da'ita tambarin hanunki ne saboda haka kidaina wahalarda shari'a ki karb'i laifinki saboda tabbas kece kika aikatasa" cikin nutsuwa MUFIDA tace "wannan wallahi dik karyane ba gaskiya bane ni bani nakashesuba saboda haka bazan taba amsar laifinda bani na aikatasaba" dole ki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login