Showing 12001 words to 15000 words out of 76905 words

Chapter 5 - TSINTACCIYAR MAGE BY AUFANA.txt

AUFANA   

12 Dec 2024

4288

MUFIDA sai raba ido take tana kallon waje tana shak'ar daddad'an iska mai sanyi, suna isa gateman yabud'e gate aka danna hancin motocin aciki, suna tsayawa akai saurin zowa aka bud'e masu murfin suka fito sannan jamian tsaro sai take masu baya suke har suka isa k'ofar shiga babban parlor sannan suka koma sukuma suke wuce ciki,,,.....

Suna shiga cikin parlon saisukaga mutanen gidan ashe surprising nasune akeso ayi, dariya suka kwashe da'ita gaba d'aya dadyn su yazo yana fad'in "wlcm back my lovely daughters" tana murmushi taje cikin shagwab'a tashige jikin dadyn ta shima yana murmushi yarungumeta yana fad'in "ohhh my sweetheart i really miss u so much" tace "mee too my dad" momy ce tamatso tareda ammin su da yakumbon su da matar k'anen dady dakuma mahaifiyar hamma faruk da k'annensa sukazo sunamasu barka da dawowa,,,....

Wani irin takaici mubina taji yatirniketa yanda dady ke nunamasu bam banci a fili tsakaninsu batama jira komaiba tawuce ciki batareda ta damu da mutanendake cikin parlon ba, hakama momy dan kawai akwai mutane acikin parlon ne shiyasa takyalesu,, munira kuwa murmushi take sosai itama taje tashige jikin dady yahadasu ya rungume tareda sumbatarsu a goshi,,"...

Bayan angama masu barka da dawowa sannan suka wuce ciki domin su huta,,,"...


Wanka sukayi suka sauya kaya izuwa material Blue color, 2am dot kowa yahad'u lambu domin yin launched, girke girke ne akayi kala kala masu matuk'ar birgewa da dad'i ma'aikatan gidan sai hidima suke, bayan angama had'a komai sannan aka zauna akafara launched d'in,,,"....

Kowa sai faraa yake ana wasa da dariya ana raha da barkwanci amma banda mubina, MUFIDA nakusa da dady munira ma na gefensa hamma faruk na kusa da MUFIDA sai kallonta yake yana janta da fira itakuma ko kallonsa batayi hankalinta sam baya garesa, batareda angama launched d'in ba mubina tabar wajen momy nakallonta amma batace da'ita uffan ba har saida aka gama sannan tabi bayanta,, MUFIDA kuma bayan angama launched d'in MUJAHID yad'aukesu suka fita yawo, wani katafaren gun hutawa da shak'atawa dakuma holewa yakaisu mai suna PLUS CENTER sukaci kayan maku lashe sukayi kallon halittun daji sannan suka shak'ata,,,....


Zaune take a gefen gado zuciyarta sai zafi take mata saboda tsintsar b'acin rai, momy ce tashigo tazauna gefenta sannan takalleta tace "mubina nafad'amaki kidaina saka kanki acikin damuwa kada kijawa kanki wata matsala" d'ago da jajayen idanuwanta tai takalli momy tace "haba momy meyasa bazan damuba bayan kema dakanki kina ganin yanda dady ke nunamana bam banci a fili tamkar mu ba y'ay'ansa bane itakad'ai ce y'ar sa plss momy kifad'aman wai kodai dady bashine mahaifinmuba" dasauri momy tace "kiyi gaggawar fitarda wannan banzan tinani acikin zuciyarki vice shine ubanku shine yahaifeku kawaidai banzan raayinsa ne yasa yake nunamaku haka kuma ki kwantarda hankalinki insha Allah zai daina kinji ko" numfashi tasauke sannan tace "hmm momy kenan wannan matsalar batin yanzu muke fama da'ita ba a gidannan bana tinanin dady zai daina abunda yake saidai kisani wallahi bazan cigaba da jurar ganin haka ba dole ne nad'auki mataki saboda yanzu na mallaki hankalin kaina nasan zafin ciwo nasan dad'in lafiya" itadai momy kallonta kawai take saboda tasan maganarta gaskiya ce abunda dady yake sam baya kyautawa amma ba yanda zatayi tinda tayi iyayinta tin suna yara amma yak'i yadaina yanzu gashi sungirma sunfahimci komai,,,.....

Saida tad'an kwantar mata da hankali sannan tafita tabarta,, sai 6pm sannan su MUFIDA suka dawo agajiye, bayan sunyi wanka sukai sallah sannan suka kwanta munira tad'akko wani hausa novel *BARKIN'DO* tafara karantawa, MUFIDA kuma wayarta tad'akko takira Amira sukai waya sannan takira nusaiba,,,.....


Sunjima suna waya da nusy daga baya sukai sallama takashe sannan ta tashi tai sallar isha, bayan sunyi sallah sannan suka fita dining sukai dinner, batawani ci komaiba sai juya cokali take daga k'arshe ma tawuce bedroom takwanta,,,"....

Koda munira tashigo tana kwance tai shuu sai zubda kwallah take tana sheshekar kuka, zama tai kusa da'ita sannan tace "aunty MUFIDA kefa musulma ce yakamata kiyarda da k'addara soyayyarki ga MUJAHID *MUK'ADDARI* ce daga Allah idan kuma Allah yayi zaku sake had'uwa saikiga kun had'u watakil ma harda rabon aure a tsakaninku, nidai nakeso agareki shine dan Allah kicire damuwa a zuciyarki kada kisake fad'awa halinda kika shiga kwanan baya a school" wani irin murmushi tai wanda yafi kuka ciwo sannan tace "wallahi munira da inada yanda zanyi nacire mr man a zuciyata da nayi da akwai maganinda zaasha acire mutum acikin zuciya wallahi da ko nawa yake saina siyesa saboda nacire mr man a zuciyata, ahalin yanzu nikad'ai nasan irin azabarda nakesha a zuciyata saboda son mr man" hmm....!!! munira tasauke nannauyan numfashi sannan tace "zancigaba da tayaki da addu'ah Allah yasake had'aki dashi koda a aljannah ne" tai murmushi tace ameen, dahaka sukai shirin bacci suka kwanta,,,....


Washe gari bayan sunyi sallah taje dak'in dady tamasa barka da safiya sannan tawuce d'akin momy, kamar ko yaushe yanda momy ke mata da fuska hakama yau tamata tadai karb'a kawai ta tashi tafito, akowane lokaci MUFIDA na mamakin yanda momy kemata wani lokacin sai zuciyarta taita cemata kodai ba'itace mahaifiyarta ba saboda yanda take mata dik wanda yagani zaice ba'itace ta haifetaba amma idan ta tambayi dady saiyace wai dan tana y'ar farine shine take mata hakan saidai har yanzu zuciyarta bata yarda da hakan ba,,,....

Tana fitowa daga d'akin momy saiga mubina bata kulaba kawai taji tamata wata wawiyar bangaza harsaida takusa fad'uwa kuma tana d'agowa sorry kawai tacemata tawuce abunta, ji tai kamar tanarka mata dukan tsiya saikuma wata zuciyar tace shareta karkibiyemata ajiku k'anwar kice danhaka sai kawai tawuce takyaleta saidai batajin dad'in yanda mubina ke mata amatsayinta na yayarta tana kyaleta ne kawai saboda nasiharda dadyn ta kemata amma badan hakaba dasaita raina kanta,,,"....

Wanka sukai suka sauya kaya, 10am driver yad'aukesu izuwa ghesse pes 1 gidan mahaifan dady wato kakanninsu MUFIDA, suna isa bayan anyi parking suka fito suka wuce cikin gidan, dasauri munira tawuce dak'in hajiya Inde kakarsu tana fad'in "hajjaju mutan makka kina inane" daga cikin bedroom d'inta ta amsa "a,a kai maraba da y'an makaranta y'ar gidan hajiya andawo kenan" dasauri taje tafad'a jikinta suka rungume juna, hajiya tace "ina sarkin miskilai ko bada ita kukazo ba" munira ta kyalkyale da dariya tace "kai hajiya aunty MUFIDA gatanan shigowa" ah to nasan halinta shiyasa daga gun dady ba inda take zuwa aidai jefata zamuyi gidan miji muhuta ak'aratacan da miskilancin. Munira tai dariya saigasu sunshigo,,,....


Cikin fara'a ba kamar yanda tasabayi ba tazo tadurk'usa tace "hajiya barka da safiya" tsaye hajiya tai tana kallon ikon Allah tace "ikon jallah jaka cikin jaka yaukuma y'ar zamani da wannan salon kikazo kodai shi uban nakine yafara koyamaki tarbiyya yanzu" murmushi MUFIDA tai batareda tace komaiba ta tashi tawuce side d'in su hamma faruk,,,"...

Tana shiga taci karo da musty autansu ashe dama yananan gun aboki Ammar sa'ansane aikwa da gudu yazo yarungumeta yana fad'in "oyoyo oyoyo Aunty feedom" itama tana dariya tad'aukesa hamma faruk da Bilkis dake zaune parlor sunajin musty yace Aunty feedom suka fito atare bilkis tazo suka gaisa takalli hamma tagaidashi fuska a d'aure sannan suka wuce ciki ita da bilkis,,,".....


Wunin ranar gaba d'aya a nan sukayisa faruk sai shi shigewa MUFIDA yake itako sam batason hakan saboda itafa bata tab'a jin sonsa a zuciyarta ba,, saida Abbu yadawo kakansu sannan takoma side d'in hajiya ita da bilkis saboda dama tafi shiri da Abbu akan hajiya ita hajiya saitaita mata fad'a da masifa tana cemata miskila shiyasa basa shiri amma Abbu saisu zauna suyita fira abunsu,, sai 7pm sannan driver yazo yamaidasu gida,,,....

A y'an kwanakinda sukai daga dady har momy sunfahimci MUFIDA komai nata ya sauya mashi chasa'in acikin d'ari na d'abi'unta sunsauya musamman girman kanta da miskilancinta yanzu saima wasu halaye data aro kamar son zaman kad'aici rashin son damuwa zama so silent rashin son rigima sannan kusan kowanne lokacin idan ka kalli fuskarta zakaganta a kumbure kamar wacca tai kuka idan dady ya tambayeta saitace bakomai ba abunda ke damunta,,,"....

Yau kimanin watansu d'aya da dawowa tana zaune acikin d'aki itakad'ai wayarta na a hanunta tana juyata kanta na kan pillow saiga musty yashigo da gudu yafad'a kanta takwabe fuska tace "ohhh Lil bro zaka karyani" ya kyalkyala da dariya sannan yatashi a zaune yace "Aunty dady ne yace nakiraki yana parlon sa" dady kuma. Yace eh "to shine kuma zaka karyani kan kafad'a man sak'on" yatashi yasauka k'asa yana dariya nan itama ta tashi suka fita atare............



kuyi hak'uri da tyaiping error ba lkc editing ne wlh 👏





#/Vote
#/Share
#/Comment

```AUFANA for life ```
*I.W.A*🖋
_*TSINTACCIYAR MAGE....*_🌷


_*BY~AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183_


® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚


_*Page 21/22*_
_Note Edited_

_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_

Atare suka shiga parlon hanunta na rik'e dana musty sai tsalle yake, cikin sallama suka shiga dady na zaune akan kujera momy na gefensa tana yanka masa fruit's yanasha,,,....

Cikin fara'a yakarb'a yana murmushi taje tazauna kusa dashi musty yahau kan k'afafunta yazauna, cikin ladabi tace "dady musty yace kana kirana" yai murmushi yace "eh magana nakeson nayi dake mai muhimmanci" murmushi kawai batareda tasake cewa komaiba shima yacigaba da shan fruits d'insa, saida yagama sannan yagyara zamansa yana fuskantarta cikin murya mai taushi yakalleta yace "MUFIDA inaso ki fuskanci maganarda zan maki yanzu sannan kimata kyakkywar fahimta a duniya banida burinda yawuce naganki kina farinciki kina dariya sannan ba abunda nafiso kamar farincikinki" murmushi tai tad'ago tace "nasani dady nasan hakan tin ina y'ar k'ank'anuwata kuma abune wanda nasani saboda haka basaika fad'a ba" murmushin jin dad'i yai sannan yacigaba da magana,,,"....

"MUFIDA dan Allah inaso ki kwantarda hankalinki karki tada hankalinki akan abunda zan fad'amaki yanzu wallahi babu hanuna aciki aikin Abbu da Abban Ammar ne (mahaifinsu hamma faruk ) dakuma hajiya banso hakan ba amma dole ba yanda naiya kema kuma dan Allah ki daure kiyi biyayya kinji ko" kallon ban fahimci abunda kake nufiba takemasa tace "dady har yanzu ban fahimci abunda kake nufiba fa kasani acikin duhu" takaicine yacika momy kamar tai magana dan haushi k'aramar yarinya kamar MUFIDA kuma y'ar cikinsa zai tsaya yana shakkar fad'amata magana kamar wata uwarsa, wani d'an siririn tsakai tai mara sauti saidai batasan dady yajiba,,,....

Cigaba yai da fad'in "MUFIDA Abbu yahad'a aurenki da FARUK a yau akayi baikonku bayan kin kammala karatunki za'ayi bikin" dasauri tad'ago takalli dady tareda mik'ewa tsaye nantake kwallah suka cicciko mata tace "what.....!!! Dady meyasa za'amun haka meyasa baza'a tambayi raayina kan a yanke hukunciba haba haba yanzu anmun adalci kenan kanasi wallahi bantab'a jin son hamma faruk a zuciyata ba bana sonsa taya zan amince da aurensa, yanzu dady kanaji kana gani za'amun auren dole kodai kadaina sonane dady" tasowa yai cikin damuwa yarik'o hanunta yace "No no my dear wallahi bahaka bane banida hanu acikin wannan lamarin nima saida aka gama komai sannan aka sanardani kidaina cewa nadaina sonki" janye hanunta tai cikin kuka tabud'e baki zatai magana sai kuka yakwace mata tajuya da gudu tafita,,,".....

Itadai momy kallonsu kawai take batace uffan ba dan itama da'akwai abunda take ji a zuciyarta akan wannan abun da Abbu yakulla,,,....

D'akinsu tawuce tafad'a kan gado tana rera kuka mai raunana zuciyar mai karatu, acikin kukan take fad'in "wai meyasa duniya ta sauyaman ta juyaman baya komai nawa yanzu a jagule yake tafiya narasa mr man namijinda farko da zuciyata takamu da k'aunarsa bayan kuma itace ta tsanesa komai nawa ya sauya asanadin haduwata da mr man nakamu da masifaffen sonsa saikuma kwatsam yatafi yabarni batareda na'isarmasa da sak'on zucitaba yanzu kuma ga wannan matsalar auren dole nikam nashiga uku wallahi mutuwa zanyi dan bazan taba iya auren faruk ba kuma natabbata suma dan basusan asalin halin faruk ba shiyasa zasu had'ani dashi da dady na yasani bazai bari ahad'ani dashi b.....a" tasake fashewa da wani kukan,,,,......

Munira ce tashigo tazo tazauna kusa da'ita takai hanunta ta dafata cikin sassanyar murya tace "Aunty MUFIDA dan Allah kiyi hak'uri kidaina kuka ki rungumi k'addara dik abunda kikaga yafaru da bawa to acikin k'addararsa yake taki k'addarar ce haka na tabbata da dady yasan asalin halayyar hamma da bazai bari a aura maki shiba hamma faruk zalwajahaini ne" dasauri tad'ago cikin mamaki tace "munira kinanufin kema kinsan halinsa" tad'aga mata kai alamar eh tace "nasani aunty MUFIDA amma su dady basusaniba saidai natabbata dole wata rana zasu sani kisani wallahi dady bashida laifi shima jiya ne suka kirasa Abbu yafad'a masa kinsan yanda dady ke gudun fushin iyayensa shiyasa dole baimasu musuba yace Allah yasanya alkhairi, tin jiya yake tinanin yanda zai kiraki yafad'a maki amma yakasa" zafafan kwallah ke zuba daga idanuwanta a yanzu dikkanin siffar MUJAHID itace take mata gezau a idanu, murmushi tai wanda yafi kuka ciwo tace "Allah sarki mr man Allah yasake had'a fuskokinmu koda a aljannah ne" munira tace ameen, cigaba da kwantar mata da hankali munira tadingayi saidai dik yanda taso ta kwantarda hankalinta abun yaci tira sai kuka take zuciyarta takasa samun nutsuwa MUJAHID taketa gani a idanuwanta k'aunarsa kuma sai dad'a ruruwa take acikin zuciyarta,,,"....


Momy ce zaune acikin d'akinta tana danne dannen laptop saiga mubina tashigo da gudu tana kuka tazo tafad'a kan momy,, dasauri momy ta'ajiye laptop d'in tarik'ota tana tambayarta abunda ke faruwa,,,....

Cikin kuka tafara magana "momy wallahi saina kashe MUFIDA saina kashet..." dasauri tarufe mata baki cikin masifa tace "ke kinada hankali kuwa meta maki dazakizo kina wannan banzan zancen naki" d'agowa tai da jajayen idanuwanta tashare kwallah da majina sannan tace "momy wai anyiwa MUFIDA baiko da faruk d'ina meyasa zasuman haka momy meyasa kinsan wallahi faruk shine zab'ina shine wanda nakeda muradin aure shi nakeso momy kuma kinsani meyasa zaki bari amun haka momy, to wallahi bazan tab'a bari hakan tafaruba bazan bari ta aure shiba" janyota momy tai tarungume tana rarrashi cikin tsintsar tausayinta,,,"...

D'agowa tai takalli momy cikin kuka tace "wai meyasa akeman haka momy ita komai saita kwacaman takwace man dady ta kwace man tsohon saurayina Abdul na school d'inmu wanda nasoshi kamar nafadawa ubangiji yanzu kuma zatasake rabani da faruk bayan kuma ita kanta tasan shi nakeso kuma dady ma yasani to wallahi bazan bari ta auresa ba saidai komai zai faru yafaru" numfashi momy tasauke sannan tace "mubina ki kwantarda hankalinki sannan inaso ki kawarda tinaninda kike a zuciyarki MUFIDA y'ar uwarkice sannan komai kikaga yafaru *MUK'ADDARI NE* daga Allah" hakadai momy tacigaba da tausan zuciyar mubina badan itama taso hakan tafaruba,,,"....


Yau kimanin kwana uku kenan dayin baikon MUFIDA da faruk kusan kullum saiya kirata a waya amma bata d'auka daga k'arshe ma saita saka number d'insa black list,, kwance take akan gado dak'in momy saiga musty yashigo yai tsalle yahau gadon yana dariya, murmushi tamasa tace "my Lil bro yatake ne" yai dariya yace "hakan take my Aunt hamma faruk ne yazo momy tace nakiraki yana parlon bak'i" b'ata fuska tai tajuya kamar takwallah ihu dan bak'inciki da takaici ganin haka shikam yasauka yawuce abunsa yana tsalle,,,".....

Zamanta tai tak'i fita saiga momy tashigo a fusace tace "ke bakiga na aiko mustapha ba yafad'a maki faruk yanajiran a parlor ba" tashi tai jiki ba kwari tawuce d'akinsu, tana shiga tabud'e wardrobe tad'akko k'aton hijab zindimeme har k'asa tasaka,,, hmm abunda bata tab'a yiba kenan dan tama manta rabonta da hijab k'ato zundimeme haka saidai k'arami shima dan sallah ne data gama zata cire saikuma wata sallar,,,....

Bayan tasaka sannan tasaka wasu plate shue tabar wayarta anan tafita, ahankali tabud'e k'ofar parlon fuskarta a tirnike babu walwala ko alamun murmushi bare dariya a tattare da'ita, murya k'asa k'asa tai sallama sannan tak'arasa tazauna nesa dashi takuma juya fuskarta tamaida hankalinta kan TV d'inda ke kunne yana aiki,,,"....


Dakyar kamar bata iyayin magana tamkar wacca bakinta ke ciwo tace masa "Barka da wuni" murmushi yai yakalle kyakkyawar fuskarta yace "barka dai k'anwata ya gida" lafiya kawai tabashi amsa, munira ce tashigo tareda hadiman gidan d'auke da abinci da abunsha kala kala, dikda dai shi ba bako bane amma yau bako yake a gidan tinda tad'i yazo saboda haka dole a karramasa,,,"....

Cikin fara'a munira tace "barka da zuwa yayana" shima cikin murmushi yace "barka dai munira a,a harda hidima haka dayawa to nagode sosai" tai murmushi tace ai bakomai sannan suka fita, juyowa yai gun MUFIDA wacca kanta yake duke tana kallon k'asa yakira sunanta "MUFIDA" batareda ta d'ago ba ta amsa masa sannan yace "MUFIDA yakamata kibani aron hankalinki anan saboda koba komai ni yayan ki ne kuma d'an uwanki yanzu kuma K'iris yarage nazama mijinki uban y'ay'anki" yana fad'ar haka tad'ago dasauri ta kallesa idanuwanta suka cicciko da kwallah bai damuba yacigaba "MUFIDA inaso kisani wallahi nadad'e ina dakon son ki azuciyata kuma kema kinsan hakan dan Allah ki daure kikarb'eni a matsayin mijinki domin muji dad'in gudanarda rayuwar aurenmu cikin farinciki da jin dad'i" sai yataso daga kujerarda yake yadawo dab da'ita, matsawa tai dasauri tana hararansa yayinda idanuwanta ke zubda kwallah,,,....

"please MUFIDA kidaure ki k'aunaceni wallahi ina sonki har cikin b'argo na" yakai hanunsa yarik'o nata, dasauri cikin masifa tamik'e tsaye tazaro dara daran idanuwanta tace "a da ina ganin girmanka amma tin lokacinda ka furtaman kalmar so na tsaneka kuma wallahi babu ranarda zuciyata zata so ka saboda tariga data kamu da son wani kuma kasani zaka aureni ka mori gangar jikina amma zuciyata da ruhina gaba d'aya suna ga wanda zuciyata tafara k'auna faruk banasonka bana sonka bana k'aunarka Allah wadaran da masu irin halayenka, hmm wato dankaga su Abbu da dady basusan mummunar halayyarda kakeyi ba shine ka lallab'o ka kitsa masu magana kamasu dad'in baki har suka amince to kasani komai daren dad'ewa akwai ranar tonon asiri akwai kuma ranar k'in dillanci ranarda hajjin mai gari ta b'ata, ranarne kuma zaka gane kurenka, faruk kak'ara sani kuma ka k'ara ji bana sonka bana k'aunark...." bata k'arasa ba yataso cikin zafin nama yawanka mata mari ya zazzaro idanuwansa yanunata da yatsa jikinsa na rawa kamar d'an dambe yace "idan kinacin k'asa ki kiyayi ta shuru karki sake kice zakiman rashin kunya wallahi yanzu sainai b'alla b'alla dake",,,,.....

Wata iriyar dariya ta kyalkyale da'ita sannan tace "kasani wallahi ni nafi k'arfinka kuma idan kasake kasaki marina wallahi saika bambamce tsakanin aya da tsakuwa kuma nasake fad'a bana sonka kuma bazan tab'a sonkaba saboda wani wanda yafika yariga daya mallake zuciyata da ruhin...." bata k'arasa ba yajanyota ya manne da k'irjinsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login