Showing 27001 words to 30000 words out of 76905 words

Chapter 10 - TSINTACCIYAR MAGE BY AUFANA.txt

AUFANA   

12 Dec 2024

4285

suka jata,,,.....

Tsintsar mamakine ya bayyana a fuskar MUFIDA kwallah nazubarmata cikin mamaki tace "momy kina nufin kice dady na ma yamutu" mubina ce tai magana cikin kuka tace "to wazaki tambaya bayan kece da kanki kika kasheshi sannan kuma kikazo yanzu kika kashe hamma faruk kokina nufin kice rainama hankali zakiyi bayan ankamaki dumu dumu" cikin mamaki tace "ni kuma kina nufin kice nice nakashe dady da hamma" mubina tace "kece za'ayiwa wannan tambayar ba kece zakiyi tambayar ba saboda amsar tambayar tana gunk.." batako k'arasaba sukaga MUFIDA tazube k'asa somammiya, cikin tsintsar b'acin rai momy tace "kukira I.G da D.I.G da commissioner of police kufad'amasu sannan ku tsareta anan kamin su k'araso karku yarda tad'aga izuwa konan da toilet ne itakuma gawar za'aturo a d'auketa" suka amsa da "yes ma angama" saita juya ita da mubina suka wuce,,,,.....

Acikin y'an dak'ik'u kad'an zancen yakarad'e ko'ina da ko'ina acikin k'asar kebbi tini momy tasaka aje adakko munira school adawo da'ita, dika gidajen biyu banda koke koke da tsinuwa ga MUFIDA ba abunda akeyi momyn faruk kuka momy kuka su bilkis da mubina kowa kuka yakeyi gida dikya rikice sai koke akeyi, har and'akko gawarwakin sai Abbu yace ajira har gobe dai dai y'an uwa na nesa dana kusa sun iso sannan a sallacesu akaisu makwancinsu,,,"...

       Haka kuwa akayi, washe gari around 10am kowa ya'iso kusan dik rabin familyn gaba d'aya sun iso sai waenda ke nesa sosai ne kad'ai suka rage suma kuma sunakan hanya, Governor da PA d'insa I.G da D.I.G da commissioner of police da sauran shuwagabannin gomnati dik sunzo,,,....

      10:30am dot aka fito da gawansu, gidan sarki akamasu sallah sannan aka kira su momy sumasu addu'a sannan awuce akaisu makwancinsu na gaskiya, koda sukazo ma komai basu iyayiba banda kuka abban ammar ne kawai ya'iya tsayawa yamasu addu'oi shima sai zubda kwallah yake, Abbu da hajiya ma sunmasu addu'oi sannan akadaukesu akawuce mak'abarta aka binnesu,,"....

Allahu akbar kullu nafsin zaa'ikatul maut dady da hamma faruk anrigamu gidan gaskiya Allah yamaku rahama ya kyautata tamu idan tazo ameen,.

A b'angaren MUFIDA kuwa tini ta farfado sai kuka take matsananci idanuwanta dik sun sauya launi sunyi zajir sun kukkumburo saboda kuka ita bama kazafinda akamata yasa take kukaba a,a mutuwar dady saboda tasan yanzu tabbas tarasa gata har abada rayuwarta saidai wani iko na ubangiji,, gidan kuwa gaba d'aya ansakamasa tsaro gaba da baya ko'ina police ne da sojoji,,,....

           Bayan andawo daga mak'abarta su governor suka shigo gida sukayiwa su hajiya dasu momy ta'aziyya sannan suka wuce, suna wucewa I.G yawuce gidan faruk suka d'auki MUFIDA suka wuce da'ita izuwa station d'insu,,,....

Suna isa kuwa yasa akashigar da'ita wani d'aki inda suke magana da mai laifi kan su hukuntashi, bayan anshiga da'ita tana zaune itakad'ai saiga I.G yashigo tareda wata police mace k'atuwa, zama yai a kujerardake fuskantarta sannan yad'ago jajayen idanuwansa masu ban tsoro yakalleta fuskarsa tamke yafara mata magana "ke meyasa kika kashe mahaifinki da mijinki...? wane laifi suka maki...?" haka yajeromata tambayoyin atare,, wasu zafafan kwallah ne suka zubomata bakinta na rawa tace "Wallahi wallahi Allah banina kashesuba shin wace riba zanci idan nakashe mahaifina haba kudinga tinani mana kan kuyi magana mahaifinane fa shi kuma wanda banida kamarsa a duniy..." bata k'arasaba yadaka mata tsawa saida ta razana cikin kakkausar murya yace "ba wannan na tambayekiba kifad'aman meyasa kika kashesu waya sakaki ki aikata hakan" cikin kuka tace "nafad'a maka wallahi Allah banina kashesuba ni ko kiyashi bantab'a kashewaba bare mutum kuma ko mutum ma dady na da yayana" wani kallo yamata sannan yace "ohhkk bazaki fad'aba kenan Good A.S.P hafsat" matar dasuka shigo atare tace "yes sir" yace "kishiga da'ita kumata dik yanda yadace har saitafad'i gaskiya tai magana sannan kufito da'ita" matar tace "ok sir angama, ke tashi muje sha sha wacca batasan ciwon kantaba barin irinku acikin al'umma bala'i nema wallahi" MUFIDA tamik'e tsaye jiki ba kwari suka fita atare,,,,....

    Sai kusan 1pm sannan munira suka iso tin a k'ofar shigowa dataga y'an zaman makoki tafashe da kuka dakyar ta'iya k'arasawa cikin gidan, tana shiga tafad'a jikin momy tana kuka mai tsuma zuciyar mai karatu cike da tsintsar tausayi, da akafada mata wai MUFIDA ce takashe dady da faruk k'in yadda tai tace "kai ina wallahi k'aryane wannan sharri ne wanine kawai yakeson yasaka aunty MUFIDA acikin tashin hankali bayan wanda tashiga na rasa dady amma wallahi sam Anty MUFIDA bazata tab'a iya aikata wannan laifin ba" wata muguwar harara momy tawatsa mata batareda tace mata komaiba hakan yasa dole munira takama malamin bakinta,,"....

Wani d'aki mai duhu tashiga da'ita tana ganin cikinsa tagane gunda suke horasda masu laifine nantake k'irjinta yafara bugawa da k'arfi da k'arfi, wasu mata taga sunshigo su hud'u manya masu girma sosai kuma karfafa dan idan kagansu ma zakace maza ne kuma da'alamu dikansu ba musulmi bane A.S.P ce kawai musulma acikinsu, suna shigowa tacemasu "ku tub'eta kusakamata riga yanzu" nan suka kama MUFIDA tana kallonsu suka ciremata kaya suka maidata daga ita sai brez da pant saisuka sake d'akko wata y'ar best bak'a suka sakamata girmanta iya cinya sannan suka rufemata fuskarta da wani kyalle bak'i,,,...

Bayan sun rufe fuskarta sannan suka kamata suka d'ora akan wani abu suka d'aureta sannan suka d'akko wata bulala irin wacca ake dukan doki da'ita ba ice bace ita bulala ce nan suka fara dukanta su biyu suna zabgamata ita tako'ina na jikinta musamman cikin k'afafuwanta da tafukan hannayenta, kuka take tana k'ara mai sauti saboda azabarda takeji amma haka sukacigaba da dukanta tintana ihu tana k'ara har muryanta ya disashe, saida suka gaji sannan suka kyaleta suka kwanceta suka maidata zaune, A.S.P tace dai dai fuskarta tace "kifad'amana meyasa kika kashesu? waya sakaki?"  cikin shesheka tana haki tace "wallahi banina kashesuba bani bace dan Allah kudaina cutardani banmaku komaiba bani bace" wani murmushin gefen leb'e tai sannan tace "ok da'alamu har yanzu baki shirya fad'ar gaskiya ba gyaiz zaku iya cigaba da aikinku",,,....

Wasu karafa suka d'akko masu baki biyu sukazo suka kamo hanunta suka saka yatsunta bibbiyu aciki suka matsesu sosai, wata iriyar k'ara tai mai sautin gaske tareda fad'in "dadyyyyyyyyy......!!!" saisuka kyalkyale da dariya sannan suka koma a kafafuwanta suka sake saka yatsunta na kafa suka matsesu sosai da iya karfinsu tasakeyin wata k'arar sai kawai tasome saboda bak'ar azaba,,,"...

D'aukanta sukai suka dora kan wani table wai fad'i sosai suka watsa mata ruwa a fuska dole ta farfado numfashinta yadawo tafara tari tana numfashi sama sama, kyaleta sukai saida takusan 30mnts tahuta amma har yanzu yatsunta basu daina mata zafiba gashi sai zubda jini suke,,,"...

A.S.P ce tazo tasaka hanunta tadamko bakinta cikin mugunta tace "kin shirya fad'ar gaskiya ko har yanzu" yanzukam tariga data galabaita ko magana bazata iyaba danhaka shesheka kawai take sai matar ta tashi tsaye, matan sukazo suka danneta anan kan table d'in sannan suka rufemata fuska da wani towel k'arami sai suka d'akko ruwa cike da bucket suka fara kwararamata a fuska, juyi take tana neman d'auki amma ina haka sukacigaba da kwararamata su saida sukaga numfashinta nanema ya dauke sannan suka kyaleta tafara tari tana jan numfashi da k'arfi tana fitarda ruwanda suka shiga a hancinta da bakinta, ganin ta galabaita yasa suka barta haka amma badan sun k'are mata ponishment d'inba,,,..

Haka sukacigaba da gana mata azaba kala kala amma har yanzu tak'i tace itace takashesu yanzuma ko magana bata iyayi saboda bakinta ya kumbura sosai saboda dukanda suke mata jikinta dik tabo ne jini kam ba'amagana gashi har yanzu y'ar wannan best d'in itace ajikinta gashi tanajin sanyi saboda zazzab'inda take fama dashi gakuma yunwa da k'ishi saboda yanzu sau d'aya suke bata abinci ruwa kuma sau biyu kawai tini tafita hayyacinta dan idan kaganta sam bazakace MUFIDA bace fuskarta dikta sauya,,,"...

                *****  *****

Yau kimanin kwana hud'u kenan da mutuwarsu dady angama zaman makoki kowa ya watse saidai har yanzu gidan cike yake saboda bak'inda ke zowa daga nesa,,,....

Around 3pm momy tace akaita gun MUFIDA nan munira tace itama zataje saisukaje atare, suna isa aka kaisu gun MUFIDA munira tafashe da kuka saboda ganin halinda MUFIDA take ciki, dakanta tad'auki key tabud'e k'ofar dagudu tashiga ta tallafo ta tarungume tana matsanancin, MUFIDA kuwa "ruwa ruwa" kawai take fad'a ganin alamun kishi takeji saboda bakinta dikya bushe yai fari alamar dai kishi takeji, tashi munira tai taje tabud'e wani k'aramin fridge tagani tad'akko ruwa acikin gora tazo ta dagata tafara bata ruwan aikuwa zokuga yanda take karb'an ruwa tana hadiyewa kamar wacca tai shekara d'aya batasha ruwaba saboda tsabar kishinda takeji,,,"...

Batako gama shan ruwanba saiga A.S.P tashigo ta karbe ruwan ta watsar sannan takama hanun munira tafitar da'ita tarufe k'ofar, cikin masifa munira tace "wai ke matarnan anya kuwa musulma ce saboda ina kokonto akan musulincinki, wane irin rashin imanine wannan zaki kama baiwar Allah kudinga azabtar da'ita bayan kuma tafad'a maku ba'itace ta aikata wannan abunb..." bata k'arasaba momy tawanketa da mari sannan tace "amma dai wallahi munira kinji kunya dumu dumu aka kamata da wuk'a ahanu tagama kashe faruk sannan tabbas itace takashe Alhj amma dikda haka wannan bai isheki ki tsinewa wannan muguwar ba wato kenan ke bakya bak'inciki akan kashe maki mahaifi datai" d'agowa munira tai tareda fad'in "to amma momy" sai momy tai saurin dakatar da'ita dacewa "dakata munira bana buk'atar sake jin komai daga bakinki tinda ke kin nuna bakiji zafin kashe maki mahaifi dataiba" tana fad'ar haka takalli I.G tace,,,....

"I.G tinda tak'i tafad'i gaskiya kukawo d'in nasaka hanu sai shigarda case d'in court inaga acan zaifi tafad'i gaskiya cikin sauk'i" I.G yace "ok madam" sai yaje yad'akko yakawo mata tai signing sannan tace "bana buk'atar kukai file d'in gunsu hajiya harsaikungama komai lokaci kawai ake jira nafara shiga court" I.G yace "dik yanda kikeso haka za'ayi ur Excellency"  suna gama maganar tajuya suka wuce munira na kallon MUFIDA badan tasoba haka suka wuce sukabarta acikin wannan halin,,,,.....

Komai ya kammala nafara shiga court lokaci kawai ake jira sadai abunda yamasu matsala shine MUFIDA batada lawyer,,,....

24/3/2019 ~ 10:00am dot akafara gudanarda wannan shari'a a babbar cotun dake cikin k'asar KEBBI State, bayan lauyoyi sun gabatar kansu sai akafara sauraron k'ara, lauyan gomnatin shine yafara tambayoyi ga MUFIDA bayan yagama sai mai shari'a yace "idan lauyan wacca ake tuhuma yana kusa yazo yafara gabatarda shaidunsa domin kare wacca yake wakilta" nan aka shaidawa mai shari'a cewar batada lauya,,,....

Bayan mai shari'a yagama y'an rube rubensa sai yad'ago yace "duba da rashin lauya da wacca ake tuhuma batada andaga wannan shari'a har izuwa 27 ga wannan watan sannan tayi gaggawar samo lauyanta domin yakareta agaban kotu kan lokacinda aka d'iba yacika sannan acigaba da tsare wacca ake tuhuma" yana gama maganar yamik'e tsaye sai kowa yamik'e tsaye yafita,, police ne sukazo suka rik'e MUFIDA zasu fita, suna fitowa waje saiga y'an jarida kowanne sai jefowa MUFIDA tambayoyi yake itakuwa banda zubda kwallah ba abunda take takasa amsa kowa daga cikinsu tambayarsa, dakyar police suka samu suka wuce da MUFIDA,,,"....

Zaune take akan kujera tana kallon TV, wayartace a hanunta tana danne danne jin an ambaci sunan MUFIDA AHMAD SHITU wacca ta kashe mahaifinta da mijinta dasauri tad'ago kanta tamayarda hankalinta kan TV d'in, MUFIDA ce dai tagani an hasko tana kuka police sun rikota 'yan jaridu sun rufeta sai tambayoyi suke mata, dasauri tafara kiran "ummi ummi ummi kizo mana" wacca takira da ummi tafito daga kitchen dasauri tazo tana fad'in "haba Amira wannan kiran mafarautan fa" tace "ummi zo kiga k'awata MUFIDA gatanan wai itace takashe mahaifinta da mijinta",,,....

Zama tai ummin saida aka gama hasko abun sannan suka nannauyan numfashi atare Amira tace "wallahi insha Allah na tabba ummi wannan abun sharri ne saboda na tabbata MUFIDA bazata iya aikata wannan abunba" kallonta ummi tai sannan tace "Amira yanzu wani zamani yazo da ko iyayenka bazakayi shaidarsuba bare kuma aboki" cikin damuwa Amira tace "ummi nazauna da MUFIDA tsawon shekara hud'u nasan halayyarta mai kyau da mara kyau MUFIDA ko fad'a mukayi itace ke saurin sakkowa daga gadon fushi saboda bata iya gaba ko k'anwarta mubina data rainata wallahi kosunyi fad'a itace ke fara mata magana ummi na tabbata wannan sharri ne akamata kuma wallahi koma waye yamata wannan muguntar sai Allah ya toni asirinsa cikin gaugawa",,,....

Numfashi ummin tasauke tace "to Allah yafitar da'ita yakuma toni asirin wanda ya'aikata kada a yankemata hukunci batareda itace ta aikataba" Amira tace "ameen ummi gobe dole nayi sammako k'asar KEBBI kuma dan Allah ummi kitayamu da addu'ah Allah yatoni asirin dik wanda ya aikata wannan abun" ummi tace "insha Allah Amira kuma zansaka a masallatai atayamu da addu'ah" nan Amira ta tashi tashige ciki,,,....

Washe gari tin 8am dot tashirya tai'sa airport 10am jirginsu yad'aga izuwa k'asar KEBBI..............





#/Vote
#/Share
#/Comment

'''AUFANA for life '''
   *I.W.A*🖋
_*TSINTACCIYAR MAGE.....*_🌷
_a true love story_

_*BY~AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183_

® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚

  _*Page 39/40*_
   _Not Edited_

_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_

Kwance take a k'asa tarufe idanuwanta dasuka mata nauyi sosai saboda kuka, makyarkyata take alamar tanajin sanyi, wani police ne yashigo d'aya dagacikin masu tsaronta saboda yanzu ba hanunsu I.G da A.S.P takeba tana gidan tsaro na kotunda ake shari'ar, yanzu tadaina shan wuya andaina azabtar da'ita saidaifa ankara mata tsaro sosai ko d'akinda take ma soja shida ke gadinsa,,,....

Police d'inne yazo yabud'e k'ofa yakalleta yace "kizo ankawo maki ziyara" jikinta ba kwari ta tashi tamik'e tsaye kafafuwanta bako takalma, ita yasaka a gaba tana tafiya yanabin bayanta har suka isa, suna isa saitaga mubina ce tai mamaki sosai dan bata tab'a zaton mubina zata tina da'ita ba,,,...

Zama tai batareda tace uffan ba sai mubina takalli police d'in tace "plss malam kad'an bamu wuri inaso nayi magana da'ita ne" sai yace mata "toh amma 10mnts kawai nabaku" tad'aga kai alamar toh, juyowa tai takalli MUFIDA ta tsuke fuska sannan tafara mata magana "MUFIDA nazone naji dalilinda yasa kika kashemuna mahaifi da d'an uwa, MUFIDA meyasa kika kashe dady meya maki nawa aka baki danki kasheshi, hmm wallahi MUFIDA kinbani mamaki yanzu dik irin alkhairinda dady yamaki abunda zaki sakamashi dashi kenan ki d'auki wuk'a da hanunki ki kasheshi wallahi MUFIDA kinbani mamaki kuma kisani dik abunda kika shuka saikin girbesa nan bada jimawaba" zafafan kwallah ne suke zuba daga idanuwanta takasa ciwa uffan zuciyarta sai kuna take mata kalaman mubina sai k'ara tafarfasa mata zuciya suke, d'agowa kawai tai takalleta batareda tace mata k'ala ba,,,....

Ganin tamata shu yasa ranta yak'ara baci "MUFIDA kifad'aman memuka maki kika maidamu marayu dady yamaki komai a rayuwa yamaki abunda ko iyayenki bazasu tab'a iyamaki shiba shin ko dukiyarda yamallaka maki ce bata makiba shine kika kasheshi danki kwashe dukiyar gaba d'aya MUFIDA kinzama butulu kiyi abunda duniya gaba d'aya saita zageki daga k'arshe kuma kema kije inda kika kai mahaifinmu da d'an uwanmu hmm tabbas hausawa sunyi gaskiya dasukace *TSINTACCIYAR MAGE* BATA MAGE gashinan mungani acikin gidanmu" zuwan police ne yakatseta da cin mutuncinda takeyiwa MUFIDA saidai hartagama kalma d'aya MUFIDA bata mayarmata ba, haka ta tashi tawuce tana matsar 'yan kwallan da sukaki fitowa MUFIDA kuma ta tashi suka koma ciki,,,.....

   
                 *****  *****
Around 2pm dot jirginsu yasauka k'asar KEBBI suna isowa kuwa tanemi taxi tashiga, kai tsaye hotel tawuce takama d'aki bayan tahuta tai wanka taci abinci tashirya sannan tafito, tana fitowa tanemi taxi tashiga kai tsaye tawuce gidansu MUFIDA,,,....

Cikin sa'a kuwa koda tai'sa munira nanan nan munira ta taryeta suka shiga tayiwa su momy ta'aziyya sannan munira tashiga ita da'ita d'akinsu, cikin nutsuwa Amira takalli munira tace "munira wai abunda akace MUFIDA ta aikata gaskiya kokuwa?" shuru munira tai kwallah suka zubomata tajuyo takalli Amira tace "Aunty Amira wallahi ni koda dik duniya zasu taru suce gaskiya ne ni bazan yardaba kawaidai ba yanda zanyine yanzu hakama wallahi tanacan agidan tsaro na kotunda ake gudanarda shari'ar kuma kan sukaita can saida suka wahaldaita yanzuhaka idan kika ganta bazakice ita bace" hmm....!!! Amira tasauke numfashi sannan tace "shikenan Allah i kyauta yanzu kitashi muje naganta sannan muje mufara neman lauyanda zai tsayamana",,,....

Wani irin murmushin jin dad'i munira tai tace "abunda naketa tinani kenan yazanyi nasami lauyanda zai tsayawa Aunty MUFIDA saboda har yanzu bawanda yai zancenta kowa harkan gabansa yake momy kuma batun had'a shaida kawai suke basu zancenta" murmushi Amira tai tadafa shoulder d'inta tace "to ki kwantarda hankalinki insha Allah komai zai tafi dai dai daikon Allah sai asirin dik wanda ya'aikata wannan abun ya tonu mucigaba da addu'ah kawai" basuwani jimaba suka fita,,,....

Koda suka isa Court d'in sai sukai rashin sa'a akace bazasu ga MUFIDA ba saboda yanzu ba lokacin ziyara bane sujira har 5pm tayi, ganin zasu b'ata lokaci yasa Amira tace zasu tafi amma zasu dawo idan 5pm d'in tayi, munira bataso hakanba amma dole tasa suka juya suka wuce,,,,....

Wunin ranar gaba d'aya yinsa sukayi atsaye saida suka tabbatar dikwani abu na cike cike akan shari'ar sunyisa har lawyer sun d'auka Amira tabiya kud'i sunyi signing gobe 10am zai iso k'asar KEBBI domin fara bincike akan shari'ar, sai 6:30pm suka koma gida danhaka basusamu komawa gun MUFIDA ba, saida Amira tai sallar magrib sannan takoma masaukinta,,,"...

Washe gari tin 9am Amira tashirya taje ta d'auki munira suka wuce, kai tsaye office d'in lauyoyin suka wuce domin jiran isowar lauyanda suka d'auka,,,, 10:35am ya'iso wani abun mamakinda suka gani shine ashe lauyanda suka d'auka Rayyan ne abokin MUJAHID, ai saboda tsabar farinciki Amira da munira kasa magana sukai sai dariya kawai suka dingayi,,,....

Bayan yahuta sannan akamasu izini dasu shiga office d'insa, bayan sunshiga Rayyan yai murmushi sannan yace "ashe Allah yayi zamu sake ganin juna" Amira tai murmushi sannan suka gaisa sukamasa barka isowa lafiya, daga nan suka kara masa cikakken bayanin yanda case d'in yake, dikda wannan bashine farko agaresa ba dayai irin wannan case d'in amma abun daya kasance ga MUFIDA saiyai mamakinsa sosai,,,....

Bayan sungama komai sai yace yanaso suje yaga MUFIDA domin yamata waensu tambayoyi nan suka tashi suka wuce Court d'in,,,"....

Suna isa akai caking d'insu sannan akamasu umarni dasu shiga, zaune take akasa tai tagumi itakad'ai tana kallon sama, d'aya daga cikin masu tsarontane yashigo yace "kifito ankawo maki ziyara" jiki ba kwari tamik'e tsaye tafita, tana isa tahango Amira da sauri hadda d'an gudu taje tarungume Amira

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login