Showing 39001 words to 42000 words out of 76905 words

Chapter 14 - TSINTACCIYAR MAGE BY AUFANA.txt

AUFANA   

12 Dec 2024

4293

a hankali, Rayyan ne yakab'a sallamarsu saboda yasan bazaiwuce twin's din sarki bane, cikin fara'a sukaje suna masa magana cikin harshen larabci suna fad'amasa waiga wasu y'an uwansu sunzo daga Nigeria zasu gaidasa, Rayyan yafara d'agowa yagansu tsaye suna kallonsa wani irin murmushi yai sannan yace "a,a kai maraba manyan bak'i mukai ashe sannunku da zuwa" Amira ce tace "Barrister sannu dai ya aiki" yace "Alhmdllh MUFIDA yakike" murmushi tai tace "lafiya k'alau Barrister ya aiki" yace Alhmdllh,,,...

Jin an ambaci sunan MUFIDA yasa yad'ago tareda juyoda fuskarsa ya kallesu yanayin tozali da kyakkyawar fuskarta yatashi zaune dasauri, tanayin tozali da fuskarsa itama tai saurin ja da baya tareda zaro dara daran idanuwanta cikin tsintsar mamaki tace "mr man" wani zama yai tareda kwantarda kansa saman kujera fuskarsa na kallon sama yafara magana cikin wani irin yanayi mai cike da tsintsar ban tausayi "MUFIDA kin wahalardani kin wahalarda zuciyata meyasa kika tafi kikai nisa dani meyasa kika bar zuciyarda take cike tsintsar so da k'aunarki" wasu zafafan kwallah ne suke zubomata ahankali tanatso kusa dashi sannan tafara magana cikin muryar kuka bakinta har rawa yake,,,....

"kaine yadace nayiwa waennan tambayoyin MUJAHID shin kakuwasan halinda katafi kabar zuciyata aciki lokaci d'aya zuciyata takamu da tsintsar k'aunarka saidai ina kariga dakamata nisa tashiga had'aruruka ba adadi dik a sanadin sonka" tasowa dakyar yasaukarda k'afuwansa k'asa ganin haka Rayyan yazo da sauri zai rikesa saiya dakatardashi yakama dakyar yamike tsaye Nasmat da Nasma suka zaro idanuwansu suka firfito dasu waje saboda mamaki mutuminda yake kwance tsawon shekara amma yau gashi yamik'e tsaye, ahankali ya tattako yazo kusa da'ita Rayyan nakusa dashi yakalleta yace "kinga waennan k'afafuwan yau kimanin shekara d'aya da wata bakwai kenan rabonsu dasu taka k'asa dik a sanadin sonki" kamo hanunta yai suka kama hanyar wani d'aki, suna isa Rayyan yasaka key yabude d'akin suka shiga, suna isa first abunda tafara tozali dashi shine wani k'aaaton hotontane manne a bagon d'aki tana sanye da abaya wankanda tai ranarda akai graduation d'insu MUJAHID a k'asansa kuma anrubuta My smole baby, k'arasawa tai ciki tana kallon bangon ginin d'akin koina da koina hotunantane dik waenda tai ranar wasuma batasan lokacinda tayisuba wasunsu a k'asansu anrubutu my JERRY wasu kuma my smole baby wasunsu kuma my one and only wasu kuma my MUFIDA, waigowarda zatai sai taga wani wanda yahad'a hotonta danasa k'asa yarubuta TOM AND JERRY,,,....

Waigowa tai ta kallesa tareda rufe bakinta da hanunta d'aya tana murmushi kuma tana kwallah sannan tace "nadade da d'aukan nikadai ce ke haukana nikadaice ke fama da d'awainiyar son ka ashe kaima hakane" baiyi maganaba murmushi kawai yai,,"....

Amira ce tamatso kusa da'ita tadafa shoulder d'inta tace "bakekad'ai bace Jerry, tin lokacinda kika kamu da son MUJAHID kuma kike shan fama da k'aunarsa nai alk'awarin saina had'aki da MUJAHID har kuyi aure, nafara shirin yanda zanyi nashawo kan MUJAHID ya'amince yakarbi soyayyarki, bayan mungama karatu mun rabu sainafara naman Rayyan saboda nasan zanfi samun sauki idan nahad'a baki dashi, cikin ikon Allah kuwa nasamu ganin Rayyan wani abun mamakin danasamu agun Rayyan shine, shima Rayyan din burinmu d'aya dashi nanyake fad'aman shima MUJAHID yakamu sonki, nantake mukafara shirin had'aku saidai kash koda nakiraki saikike sanardani ansaka ranar aurenku da faruk, nayi bak'inciki sosai saboda naso MUFIDA ku mallaki junanku kodon kuci ribar k'aunarda kukeyiwa junanku amma ina abun yafu karfinmu",,,.....

Lokacinda naji labarin faruk yamutu naji dadi saidai kuma dadin yakoma ciki saboda cewarda akai kekika kashesa, lokacinda nake neman lauyanda zai tsayamaki sai kwatsam Rayyan yazo yace indai zan amince nataimakasa wajen shawo kanki ki'amince bayan kingama idda ki auri MUJAHID to zai tsayamaki harsaiyatabbatar anwankeki daga zarginda ake maki yakuma bani labarin halinda MUJAHID yake ciki dik asanadin sonki har yakaiga baya iya tafiya da k'afafuwan sa yakasa auren kowacce mace dik wacca aka kawomasa saiyace batamasa ba, nan take na amince kuma Alhmdllh sai mukai nasara, shekaranjiya dana kiraki nace zaki rakani bikin k'awata bawani biki dazamuje dama nanne zan kawoki kiga irin halinda MUJAHID yake ciki dik a saboda sonki",,,,.....

Wani irin nannauyan numfashi MUFIDA ta sauke sannan tad'ago ta kallesa wanda yakafeta da mayun idanuwansa tai murmushi tajuya fuskarta sannan tafita, suma murmushin sukai Nasmat tace "dama yaya ciwonka ciwon so ne shine aka kasa samun maganinsa" dariya suka kyalkyale da'ita yajanyota ya rungume tareda mata rankwashi sannan suka fita parlor,,,....

Tindaga ranar wasan b'uya suka fara tak'i yarda su tsaya suyi magana wai kunyarsa takeji irin abunda tamasa a baya, saidai tsohuwar zumar soyayyarsu ta taso tadawo sabuwa gall yanzuma saitafi ta da d'in saboda wannan kunyar tata saima yaji k'aunarta tak'ara shigarsa..........






#/Vote
#/Share
#/Comment

```AUFANA for life ```
*I.W.A*🖋
_*TSINTACCIYAR MAGE.....*_🌷
_a true love story_


_*BY~AUFANA*_ _wattpad@Aufana8183_


® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚


_*Page 49/50*_

_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_

Washe gari bayan sunyi sallah sukai break saitai wanka tasaka wata abaya mai kyau tai rolling da veal sannan tasaka takalma tazauna tanajiran Amira tashirya, bayan Amira tashirya itama cikin abaya, kallon MUFIDA amira tai tasha kunu sai MUFIDA tai murmushi tace "yadai Amira" batace da'ita uffanba saitaje gun mirror tad'akko kwalli da jan baki tazo tamik'amata tace "karb'a ki shafa" murmushi tai ba musu ta karb'a tashafa, woww Amira tafad'a sannan tace "kingakuwa yanda kikai kyau gaskiya yanzukam tinda kinhad'u da TOM d'inki dole kidinga tsantsara masa kwalliya yanagani" dariya tai tace "kai Amira nifa kinsan kwalliyarnan ba damuna taiba" tab aikuwa yanzu dole ta dameki dan dole arik'ayiwa yayanmu. Tak'arasa maganar cikin tsokana MUFIDA batasake cewa komaiba tai murmushi sannan suka saka takalmansu suka fita,,,.....

Koda suka fito parlor momy da abban ammar suna zaune nansukamasu barka da safiya sannan suka wuce,,,.....

Kai tsaye fadar sarki sukawuce koda suka shiga kuwa yana kishingid'e yanakaratun wani littafe hisnul muslim nan suka durk'usa suka kwashi gaisuwa, yadubesu cikin fara'a ya amsa sannan suka fita, daganan suka wuce sashen tsohon sarki mai martaba suna isa suka taddasa da Abbu da gimbiya matarsa suna fira, cikin girmamawa suka durk'usa suka gaidasu sannan suka zauna suma akacigaba da firar dasu,,,".....

Sunjima anan sannan mai martaba yasaka aka kira Nasmat sukazo saiyamasu magana cikin harshen larabci sannan yajuyo gunsu MUFIDA yace "zakubisu kuzaga gari sannan sukaiku gidajen sauran y'an uwa kisansu daganan kuwuce gidan mahaifinki saboda matansa susanki kinji ko yata" bayanda MUFIDA taiya dole badan tasoba ta amsa da to sannan suka tashi suka fita,,"....


Wunin ranar gaba d'aya su MUFIDA basu zauna ba koina da ko'ina saida sukaje daga k'arshe dai suka sauka a gidan mahaifinta, acan suka k'arasa wuni kuma Alhmdllh matan sun karb'eta sosai sai nan nan suke da'ita saboda MUFIDA tanada shiga rai sosai dik wanda yaganta nantake zaiji tashiga ransa gatakuma tanada kama da mahaifinta sosai, sai dare sannan suka baro can suka dawo gida,,".....

Around 8pm tai wanka tasaka kayan baccinta saita saka katon hijab tafita, gun Abbu taje yana zaune acikin parlon mai martaba cikin sallama tashiga tagaidasa ya amsa sannan ta zauna, y'ar fira suka fara kasancewar dama MUFIDA da abbu suna shiri sosai, suna cikin fira saitace "yawwa Abbu dama inaso na tambayeka nifa gidannan nakasa gane kansa wallahi please kamun bayani yanda zan gane sosai" murmushi abbu yai sannan yatashi daga kishingid'enda yake yace,,,...

Wannan tsohon sarkin mai martaba kenan shine mahaifin sarki na yanzu wato Abdul samad sai tajudeen mahaifinki sai kanwarsu Sarah, Abdul-samad shine yahaifi Biryama wato MUJAHID sai k'anensa Ma'aruf wanda yake Cyprus yana karanta BIOCHEMISTRY sai k'annensa twin's Nasma da Nasmat sukuma anan suke karatu a wata University dake Madina, sai tajudeen mahaifinki shi bayan ke baisake haihuwaba sai kanwarsu Sarah wacca takeda yaya shida to kinji yanzukam" murmushi tai sannan tasake cewa "to Abbu ya zumuntarku take da mai martaba naga kai Nigeria ne family naka suke kuma su sunajin hausa gasu kuma basa garinda ake hausa" murmushi Abbu yai sannan yace,,,....

Eh sunajin hausa amma basosaiba yanda zumuntarmu take da mai martaba shine mahaifiyata da mahaifiyar mai martaba uwarsu d'aya yagaji sarautane ta gefen mahaifinsa wanda dama su asalin y'an BAGDAAZ ne yanajin hausane saboda a Nigeria yagirma saida akabashi mulki sannan yadawo nan gabad'aya amma har aka haifi su tajudeen dik yanazuwa yanzune dai da tsufa yakamasa yadaina zuwa suma kuma yaran yanamasu hausa shiyasa suke d'an yi amma basosaiba" eh naga ai basuma iyataba sosai musamman su Nasmat inma sunayi kamar kai dariya wallahi. Nandai sukacigaba da shan firarsu har mai martaba yashigo sukacigaba da yi, sai kusan 10pm sannan MUFIDA taje ta kwanta,,,,.....


Washe gari tin basuyi wankaba su Nasmat sukazo dole sukai wanka da sauri sukai break sannan suka fita,,....

Wata wasace suke gudanarwa a dik irin waennan ranakun idan sunzo kusan al'adar masarautarce, koda suka fito gaba d'aya ko'ina na gidan ciki da wajensa ansakamasa flower's da kyalli sai shining yake abun gwanin birgewa ga hadimai sai gyaran gidan suke, hannayensu sakad'e dana juna sukai can bayan gidan koda sukaje acanma gyara ake anzuba flower's da color's masu kyan gaske itatuwa suma ansakamasu kyalli, MUFIDA najuyawa bayanta tahango MUJAHID zaune a karkashin wata bishiya yana shan tufa sai kallonta yake yana murmushi, itama murmushin tai tabuya bayan Amira batareda Amira tasan abunda takenufiba,,,....

Jansu su Nasma sukayi sukaje can baya wurin wani lambu akamasu lalle ja a hanu sannan akayiwa su Nasma gyaran suma, saida aka gama masu sannan akafarawa MUFIDA kasancewar itace tace afaramasu kawai,, anacikin yimata saiga MUJAHID da Rayyan sunshigo, dasauri tad'auki mayafi tarufe jikinta sannan suka gaisa da Rayyan nan yataimakawa MUJAHID yazauna sannan yajasu Amira da Nasma suka fita,,,"....


Shuru yaratsa wajen sai kukan tsintsaye kakejiyowa, dakyar tabud'e baki tace "am dan Allah mr man kai hak'uri da abunda yafaru abaya wallahi sharrin shaid'an ne da bin san zuciy.....a" bata k'arasaba yamatso dab da'ita tareda kai yatsansa kan lips d'inta yafurta "Shiiiiitttt.....!!! is OK komai yawuce" k'urawa juna ido sukayi suna kallon cikin idon junansu cikin tsintsar so da k'aunar junansu had'eda kewar junansu, itace tai saurin d'auke nata idon saboda wata iriyar kunyarsa dataji tana shigarta taredayin murmushi, shima murmushin yai yana kallon kyakkyawar surarta, hanunsa yakai ya yaye mayafinda tarufe jikinta dashi nantake saiga sumarta tazubo mata gwanin birgewa har gadan bayanta, dasauri tad'ago takai hanunta zata kamo mayafin tana d'ora hanun sai kan nasa nan sukaji wani shork yajasu dasauri yarufe idanuwansa saboda wani irin yanayi dayaji,,....

Ahankali yabud'e idanuwansa yazubawa sumarta yana kallo sannan yakai hanunsa ya yayemata wanda yazubo yarufemata fuskarta nan suka k'urawa juna ido, matsowa yai yakai bakinsa dai dai kunnenta yamata rad'a a kunne banji abunda yaceba sai kawai tafashe da dariya harsaida fararan hak'oranta suka bayyana wishiryanta ta bayyana d'an dimples d'inta yalotsa shima yai murmushi sannan yakai hanunsa ya tallafo hannayenta yana kallon lallenda akamata, binsa tai da kallo ganin yanda yake kallon lallen kamar baitaba ganin lalle ba,,,".....

Ganindai abunsa yai yawa yasa tamike tsaye dasauri tana murmushi zata wuce da gudu yai saurin rik'o hanunta, mikewa yai tsaye yajanyota da k'arfi tafad'o kan k'irjinsa tareda jan numfashi, duk'oda fuskarsa yai kamar yana shinshinarta yakai hanunsa yaye sumarda ta rufemata fuska, yanayin yanda hanunsa ke tab'a jikinta yasa saitakejin wani iri taja numfashi tareda rufe idanuwanta, duk'owa yai dai dai fuskarta kuma dai dai kunnenta ahankali tamkar wanda bayason yin magana cikin wani irin yanayi muryarsa cikin taushi yace "my Jerry will u marry me" wani murmushi tai wanda yalutsarda dimples d'inta batareda ta bayyanarda hak'oranta ba tad'ago fuskarta takafesa da sexy eye's nata, shima kallon nata yake ganin irin kallonda takemasa, bai ankaraba yaji tashafa masa lalle a hanci sannan tagudu tana kyalkyala dariya, shima dariyar yai yana bin bayanta da kallo harta b'acemasa,,....


Around 10am kowa yashirya yafito gunda za'agudanarda al'adar hadimai sai yawo suke suna bama mutane coffee da shayin y'an Arab's, kowa da kowa yaiso har matan Abban MUFIDA tajudeen gimbiya Zainab ma tafito da tawagarta hakama gimbiya uwar gidan mai martaba, martaba da abbu da abban ammar dik sun fito sarki yaiso da fadawansa kowa dai yafito har anfara gudanarda al'adar,,....


Cikin shiga mai kyau ta alfarma irinta y'ay'an masu mulki MUJAHID da Rayyan suka fito yanzukam ma shike tafiya dakansa bamai rikonsa saidai da sanda yake, yai matuk'ar yin kyau yafito asalinsa na balaraben asali, MUJAHID dogone fari tass mamallakin fuska mai tsayi mai d'an fad'i wacca take d'auke da manyan idanuwana masu black eye lashes da baki mai d'an girma kuma red ne, hancinsa mai d'an tsayine amma bakamar na MUFIDA ba dan ita nata haryakusa cimma bakinta, faffad'an k'irji ne dashi atak'aice dai kyakkyawane na asali,,,....

Cikin kasaita irinta yarima mai jiran gado yake tafiya harsuka k'arasa, sarki na ganinsa yai murmushi, kujerarda aka tanadar dominsa ya zauna Rayyan yazauna gefensa suka fara kallon wasan saidai shi sam hankalinsa baya gun wasan yanacan gun naman inda idanuwansa zasuyi tozali da abar k'aunarsa, yanacikin dube dube kuwa saiya hangosu suna tahowa su hud'u cikin shiga iri d'aya sunyi matuk'ar yin kyau musamman tauraruwar tasa saima yake ganin itakad'aice ke haske acikinsu, wani irin murmushi yai wanda yakasa fassarasa yak'uramata sexy eye's nashi yana kallonta, har suka k'arasa suka zauna baidaina kallontaba harsataji ajikinta wani yana kallonta nantafara waige waige caraf tasauke iadnuwanta kansa yak'uramata ido yana kallonta, murmushi tai saita d'agamasa gira alamar yadai shikuma saiya kashe mata ido d'aya saita zaro idanuwanta tafirfito dasu waje tareda kai hanunta d'aya tarufe bakinta tana dariya, ganin yaki daina kallonta yasa ta tashi tasauya waje saita d'an lek'o taga yab'ata fuska alamar baiji dadi ba, dariya tai tacigaba da zamanta anan har akagama wasan,,,.....


Bayan amgama suka gudu rafinda ke cikin masarautar wanda yabi ta cikinta yawuce, wajen yanada dad'i sosai ga sanyi gakuma ruwa tsintsaye sai wasansu suke kanari mai dad'in sauti sai kuka yake wajen dai gwanin birgewa, takalmansu suka cire suka yaye rigarsu suka zauna suka saka kafafuwansu acikin ruwan suna fira, magana sukaji anyi a bayanzu saisuka waigo atare, MUJAHID ne da Rayyan sai wani kyakkyawan saurayi daganidai shima jinin sarautane, suna waigowa sai MUJAHID yanuna MUFIDA da yatsa yace "wannan itace" alamar dai yana nunawa abokin nasa MUFIDA ne,,,.....

Badan tasoba dole tace "barka da safiya" ya amsa mata "barka dai sarauniya ya hidima da jama'a" ta duk'arda kanta tace Alhmdllh nan suma su Amira suka gaidasa ya karb'a sannan suka wuce, jim kadan saigashi yadawo shik'adai yacewa su Nasma "Sisters kuje Ummi nanemanku" nan suka tashi tareda Amira suka wuce, har zasu wuce sai Nasmat tace "batawata ummi dake nemanmu kaidai soyayya kazo sha" tana fada suka kyalkyale da dariya sannan suka wuce,,,....

Itama mikewa tai tsaye takama hanyar wucewa saiyai saurin rik'o hanunta tareda fadin "haba my Jerry inakuma zakije ne bayan nazone muyi fira" k'in nuyowa tai tacigaba da tsayuwarta, sunanta yakira "MUFIDA" saita waigo nantake ta zaro daran daran idanuwanta ta firfito dasu waje tareda kai hanunta d'aya tarufe bakinta tana murmushi ganinsa durk'ushe a gabanta hanunsa rik'e da flower red tana d'auke da zobe mai shegen kyau, jin tai yace "my MUFIDA will u marry me please...!!! my only one answer me" rufe fuskanta tai tana dariya sannan tace "yes I will my heartbeat" wani irin murmushi yai yamike tsaye yakamo hanunta yasakamata zoben a yatsa sannan yai kissing d'insa yace "yanzu munyi engagement kenan zanje nasami Abi na ( means dady ) namasa magana azo asakamana rana ayi bikinmu" kallonsa tai tace "kacika zumud'i dawuri haka tin bamugama fahimtar junaba" hararanta yai sannan yace "eh naji ai dole nai zumud'i akan abunda nasha wahala akansa kan nasamesa kinsanfa hausawa sunce abari yahuce shike kawo rabon wani saboda haka gwanda nai sauri nafad'a karkuma wani yazo yakwaceman" murmushi tai tace "bama wanda zai kwacemaka rabonkane insha Allah" wani kallo yamata yace "Allah ko" tareda kashe mata ido d'aya tai dariya tareda juyawa tawuce,,,".....


Ahankali shak'uwa ke kara shiga a tsakaninsu yayinda wutar k'aunar junansu ke kara ruruwa acikin zuciyoyinsu,, kimanin satinsu d'aya da zuwa su abban ammar suka gano asalin garin mahaifiyar MUFIDA Turkish nan suka shirya hadda su MUJAHID sukaje, lokacinda suka isa antaryesu da kyau jin daga masarautar BAGDAAZ suke bayan sunhuta sun gama gaisawa nan Abban ammar yafad'amsu abunda yakawosu, nantake aka kaisu gidan hajiya shahida, tinda suka isa MUFIDA taita kallonta MUJAHID kuwa yana ganinta yatabbata itace mahaifiyar MUFIDA dan dikda MUFIDA nada kama da Abba taju amma kamarta tafi yawa da mahaifiyarta,,,"....


Tarba ta musamman tamasu bayan sunsha ruwa suka gaisa sai abban ammar yafad'amata abunda yakawosu, dajin abunda abban ammar yafada nantake komai daya faru a baya yadawomata sabo a brain nata, kuka tafara tana zubda kwallah sannan tace "inatake yarinyata" abban ammar yanunamata MUFIDA saitaje gun MUFIDA tashafa fuskarta tana zubda kwallah itama MUFIDA tana kuka sannan tace "kiyafeman yata wallahi badan banasonkibane yasa na yadaki tsoron halinda zan shiga idan iyayena da dangina sukaji abunda na aikata shine yasa na barki amma badan banasonkiba har izuwa yanzu dikna tina dake saina zubda kwallah zuciyata taita mun kuna dan Allah kiyafeman" banda kuka ba abunda MUFIDA keyi takasa cewa uffan sai sheshekar kuka take,,,.....

Shuru yaratsa parlon nawasu y'an mintina can abban ammar yace "to Alhmdllh dama fatanmu shine tasanki kema kuma kisan tana raye kuma kisan inda take yanzu tinda kinganta shikenan" basuwani jimaba sosai ba suka tashi zasu wuce saita rok'esu dan Allah sujira mijinta yadawo yaganta kuma tanaso suje gidansu gun iyayenta suma suganta, basumata musuba kuwa suka zauna har mijinta yadawo k'annenta su uku suka dawo daga School dik suka ganta sannan suka wuce can gun kakaninta, jin abunda yafaru a baya yasa ran iyayen shahida ya baci sosai har saida suka zubda kwallah saida abban ammar dasu MUJAHID sukaita rarrashinsu suna basu hak'uri sannanfa sukace sun yafemata nansuka janyo MUFIDA ajikinsu,,,......


Sunjima sosai anan daga bisani suka barosu suka kamo hanyar BAGDAAZ,,,....

Bayan sundawo MUJAHID da Rayyan suka sami Abbu sukamasa zancen soyayyarsa da MUFIDA, abbu yaji dad'in maganar sosai saboda koba komai za'ak'ara jaddada zumunci gashi shikuma abbu ba abunda yafi so kamar zumunci danhaka nantake yai na'am da maganar kuma yace su kwantarda hankalinsu aure kamar anyi angama insha Allah, dad'i kamar yasan yanda yai da MUJAHID sai faman murmushi yake yana godiya ga abbu yana sinne kai k'asa,,,.....

A

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login