Showing 63001 words to 66000 words out of 76905 words
da'ita, MUJAHID kuwa yanacan gun sarki koda yadawo tini tai bacci,,,....
Murmushi yai sannan yazauna yad'akko k'afafuwan ta yad'ora kan cinyoyinsa yafara mata tausa cikin tausayi yana murmushi, wata iriyar mika tai tareda gyara kwanciyarta tacigaba da bacci saboda dad'in tausanda yakemata, murmushi yai saboda yanzu wani irin tausayinta yake Kara shigarsa tinda cikinnan yakai wata takwas yanzu batada juriyar zirga zirga sosai nantake take gajiya k'afafuwanta suyita ciwo sai anmata tausa,, saida ya tabbatar baccinta yai nisa sosai sannan yatashi yacire kayansa shima yashiga toilet, bayan yafito yasaka jallabiya da hula tab'a kasha hadisi sannan yazo ya sumbaceta a goshi sannan yafita,,,".....
Kimanin kwanansu biyu dazuwa akafara gudanarda UMRAH donhaka MUFIDA da MUJAHID sarki da ummi suka raba hanya, MUJAHID yakoma side d'insu ummi tareda sarki ummi kuma tadawo side d'insu MUJAHID tareda MUFIDA saidai fafur tak'i yarda tazauna d'aki d'aya da MUFIDA tashiga 'dayan d'akin dake kusa dana MUFIDA, ran MUFIDA bai baciba saboda yanzu inda sabo tasaba,,,,.....
Ahankali suka fara gudanarda ibadarsu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, dawowar ummi side d'insu yasa tai amfani da wannan damar tafara cusa kanta agareta tahanyar yimata hidima batareda tasaniba, da asuba idan zasuje masjid bazata tafi itakad'aiba saita jira ummi sannan sutafi dikda kuwa bamagana takemata ba idan kuma gama sallah har gunta take zuwa tamata barka da safiya dole badan tasoba take karbawa,,".....
Ahaka ahaka ahankali ahankali tin ummi bata kulata harta fara kulata saboda irin hidimarda take mata dikda bakulata takeba, ganin haka yasa MUFIDA tak'ara himma wajen cusa kanta agun ummi, y'an kayanta idan sukai datti saita dauka batareda sanintaba taje tawanke saidai kawai taga takawomata a wanke sannan idan suka dawo gida domin cin abinci sai tai amfani da wannan damar tashiga kitchen tamasu girki, abun yanabama ummi mamaki wani lokacin saitarasa shin aka wane daliline ma yasa take k'in yarinyar nan, itadai d'an zamannan dasukai bataga aibintaba yarinyace mai nutsuwa hankali dakuma uwa uba tarbiyya da ladabi, dikda k'aton cikinda take d'auke dashi amma baihanata yin ayyukanta ba amatsayinta na mace komai itakeyiwa kanta bata tarshe ba tace komai sai ammata tinda cikine da'ita ba dikda kuwa tasan irin sonda sarki da MUJAHID kemata komai takeso zasumatashi amma hakan baisata tazama raguwa ba wajen kula da kanta harma da wani sab'anin asma'u wacca ko wanka badan yazamemata dole ba dazatace shima adingamata,,,....
Nantake acikin k'ank'anen lokaci raayin ummi da k'iyayyarda takeyiwa MUFIDA tafara sauyawa akan MUFIDA yanzu tafara sakewa MUFIDA fuska harma idan tagaidata tana amsamata acikin fara'a da sakin fuska, hakan yabama MUFIDA mamaki matuka acikin k'ank'anen lokaci Allah yakarb'i adduarta wacca tajima tanayi, hakan yasa tak'ara yin d'amara dakuma Kara k'aimi kozata samu fada agun ummi,,,....
Tacigaba da cusa kanta agun ummi yayinda kuma take Kara samun shiga agunta yanzu har zama sukeyi gu d'aya dikda bawata fira sukeba, MUFIDA takan baro d'akinta tazo d'akin ummi tazauna tamata shara ta gyara mata gado sannan tazauna tai karatunta idan dare yai tamata saida safe tawuce,, ahankali ummi tasake da'ita yanzu har fira suke, idan zasuje masjid har Qur'an MUFIDA ke rik'amata sai insunje sannan tabata takarba cikin fara'a da murmushi,,,".....
***** *****
Alhmdllh yau saura kwana d'aya kacal sukammala ibadarsu wanda yau kuma itace daren sallan azimi, around 12pm bayan sundawo tai wanka tashirya tawuce d'akin ummi, koda taje tana zaune tana karatun Qur'an, cikin sallama tashiga tazauna saida ta kammala sannan tagaidata ta amsa cikin fara'a tareda tambayarta kwarin jiki tace Alhmdllh,,,....
Suna nan zaune dakyar cikin in ina tafad'amata abunda yakawota, murmushi ummi tai sannan tamata na'am da abunda tazo dashi, tsefa tamata sannan tazauna tamata kitso, bayan sungama sannan tamata lalle ja, wani irin dad'i ummi keji yanda MUFIDA ke kula da'ita tamkar yarta data haifa acikinta, bayan tagama zata wuce sai tadubeta cikin murmushi tace "kai nagode sosai MUFIDA sannu da k'okari Allah imaki albark......" saikuma tai shuu bata k'arasaba, murmushi kawai MUFIDA tajuya tawuce abunta,,,,......
Washe gari tin 5am tafarka tashiga kitchen tafara girki, abinci tagirka nagani na fad'a wanda kuma tasan ummi da sarki sunfiso dan yanzu ma batadamu data farantawa MUJAHID ba kamar yanda tadamu ta farantawa ummi da sarki, girki tai har kala uku sannan tahada juices kala biyu, bayan tagama sannan takoma ciki tai wanka tashirya cikin wata tsadaddiyar jallabiya black color ammata zanen flower's da red color saikuma wasu Stone's da'aka manna silver color, veal d'in rigan tai rolling dashi sannan tasaka nik'ab da takalmanta tad'auki jakarta da phone d'inta sannan tafita,,,"....
Kai tsaye d'akin ummi taje koda taje itama tashirya nanta gyara mata bedsheet d'inta takwashe kayanda tacire nan ummi tak'arasa shiryawa sannan sukafita izuwa masjid domin yin sallar eid_el_fitr,,, sai kusan 11am sannan suka koma gida koda suka koma su MUJAHID basu shigoba danhaka sai MUFIDA tajuya domin tafiya d'akinta, harta juya sai ummi takirata tace tazo su zauna anan mana harsu MUJAHID sushigo, batamata musuba kuwa tadawo tazauna, ahankali ahankali kad'an kad'an suked'an tab'a fira harsu MUJAHID suka dawo,,,....
Cikin farinciki da fara'a da nishad'i suka gaisa sannan sukayiwa junansu barka da sallah dakuma fatan ubangiji yakarbi ibadunsu, bayan su MUJAHID sun zauna saitamike tsaye tafita, jim kad'an saigata tadawo d'auke da food flask akan faranti, dasauri MUJAHID yazo yakarb'amata saboda sunmata nauyi kayan hanunta har rawa yake, yana karbawa tasake komawa tad'akko wasu har biyu da plate's da cup's da lemonda tahada sannan tazo tasaukesu,,,....
MUJAHID ne yabude abinci nantake wani irin daddad'an k'amshi yadaki hancinsa yai murmushi, tsintsar mamakine yakama ummi saboda sam batasan lokacinda MUFIDA tai wannan girkin mai yawaba "kai lallai wannan yarinyar akwai k'okari akwaita da hak'uri aiki bata gajiya dikda cikinda take d'auke dashi amma kamar bata d'auke da komai kamar batajin wahalar aiki" ummi ke fad'a acikin zuciyarta,, haka suka zauna suka kwashi daddadan girkin MUFIDA sarki da MUJAHID sai sanyamata albarka suke ummi kuwa murmushi kawai take amma zuciyarta cike take da tsintsar mamakin kanta yanda ta tsani MUFIDA batareda tatsaya ta zauna da'ita taga yanda halayenta sukeba,,,"....
*________________*
Bayan kwana hud'u dayin sallah sukafara shirin dawowa gida nan suka shiga kasuwa domin yin tsaraba, k'udi sarki yabama MUFIDA masu yawa yace tak'ara tasiyi abunda takeso nan taita masa godiya dakuma kyakkyawar addua,,,....
Washe gari rana ta biyar jirginsu yad'aga izuwa BAGDAAZ, 3:30pm dot jirginsu yasauka, ma'aruf da mai martaba da dakaru ne sukazo tarbansu ma'aruf sai tsokanar MUFIDA yake yana fad'in "gaskiya babbar yaya kink'ara kyau muma gaskiya next year damu zaaje" nan akaita dariya, kai tsaye su MUFIDA gidansu aka wuce dasu aikuwa suna isa tai wanka tai sallan la'asar taci abinci saita kwanta nantake tai bacci saboda gajiya,,,"...
Bayan kwana uku da dawowarsu sannan suka shirya sukaje gida, ma'aruf sukafarayin karo dashi zaune tareda dakarunda ke kula da k'ofar shiga sunashan coffee kasancewar ma'aruf mutum ne maison mutane tin yana yaro inkagansa gida to yunwace tamaidashi amma idan bahakaba to yanacan waje tareda mutane sunashan fira shiyasa yasaba dasu har girmansa sab'anin MUJAHID da daga gida sai gida saikwa gun sarki ko mai martaba,,,...
Yana ganinsu cikin fara'a yazo ya taryesu tareda masu barka da zuwa, bayan sungaisa kuma yakoma gun abokanan firarsa sukuma suka wuce ciki, sashen jaddati suka wuce kamar yanda suka saba suna isa MUFIDA tai zamanta anan, hartai kwanciyarta sai MUJAHID yace "my only na tashi muje mugaida ummi ko" shuruu tamasa tana tinani can dai ta tashi tareda fad'in "toh" tasaka hijab d'inta sannan suka wuce,,,...
Koda suka isa sashenta tana zaune kan sallaya tana jan carbi saboda haka suka zauna itadai MUFIDA diktasha jinin jikinta cike take da tsoro tarike hanun MUJAHID gam, bayan tagama saita juyo cikin fara'a da sakin fuska nan suka risina suka kwashi gaisuwa saisukaga tana amsa masu cikin fara'a da murmushi, abun yabama MUFIDA mamaki matuka harsaida mamakinta yakasa b'uya ya bayyana a fuskarta, zama sukai ak'asa sai MUJAHID yatashi yaje yadiboma MUFIDA kayan itatuwanda takesha yazo yafara fere mata yana yankamata tafara sha, suna zaune saiga su Nasmat sunshigo ganinsu MUFIDA a zaune har sunashan fruit's yabasu mamaki sosai nan suka gaisheda MUJAHID sannan suka kama hanyar shiga d'akinsu,,,...
Har sunjuya sai sukaji ummi tace "a,a bazaku gaisheda yayar takuba ko bakugantabane?" aikuwa sunajin haka sukazo da gudu suka rungume MUFIDA cikin farinciki, aranar anan sashen ummi MUFIDA tawuni saida dare sannan MUJAHID yazo suka wuce,,,"....
Tindaga wannan lokacin MUFIDA tasamu sakewa da ummi saidai har yanzu bawata doguwar fira sukeba sosai amma ita MUFIDA hakanma yamata dadi sosai tinda yanzu su Nasmat har gidanta suke zuwa suwuni kuma su kwana toko ahaka aka tsaya Alhmdllh,,,"....
***** *****
Kimanin satinsu biyu da dawowa ma'aruf yadami MUJAHID dan Allah yaje yayiwa sarki maganarsa da munira, MUJAHID kuwa baiyi k'asa a guiwaba yaje yasami sarki yamasa bayanin komai, sarki yaji dad'in zancen matuka yanuna farincikinsa nan yacewa MUJAHID yaje zaije gun mai martaba yafada masa dik yanda sukai zai kirasa shima yafad'amasa nan MUJAHID yai godiya sannan yawuce, kai tsaye sashen ummi yawuce itama domin yafad'amata saidai itakam yana shakku yana tsoron fad'amata saboda yanatsoron yanda zata karbi zancen,,,....
Baiyi sanyaba cikin girmamawa kamar yanda yasaba yarisina yagaidata ga mamakinsa saiyaga ta amsa masa bakamar da ba, hakan yabashi mamaki matuka nandai dakyar cikin in ina yasamu yafad'amata, murmushi yaga tayi sanna tace "ai ma'aruf yafadaman komai Allah i kyauta i sanya alkhairi" tsintsar mamakine ya bayyana k'arara a fuskarsa wanda yakasa boyewa har saida ya bayyana fuskarsa, baki sake yace "ameen" sannan yatashi yawuce,,,....
Bayan sarki yasami mai martaba yafad'amasa, mai martaba ma yai farinciki sosai yanuna jin dadinsa sosai nantake suka yanke shawarar yanda abun zaikasance,,,, acikin kwanakin maganar ta bayyana ta bazama kowa yaji, lokacinda MUFIDA taji tai matuk'ar mamakin yanda abun yakasance musamman dataji abunda ummi tafad'a, tai mamaki sosai yanda ummi tasauya acikin k'ank'anen lokaci,,,....
Acikin kwanakin mai martaba yakira a gida Nigeria yasanarda Abbu zasuzo kuma ga abunda zai kawosu, shima abbu yai matuk'ar jin dad'i ganin zumuncinsu zai Kara k'ulluwa,,,"...
Kimanin satinsu MUFIDA biyu da dawowa su mai martaba suka shirya sukaje Nigeria, tarba ta musamman akamasu wacca basuyi zatoba nan abbu yasaka aka kira masa munira yatambayeta shin dagaske tanason ma'aruf, dafarko shuru tai ganin haka yasa abbu yasake tambayarta nan tafara basa labarin komai, tabbas tanason ma'aruf saidai tanatsoron aurensa, cikin kulawa abbu yasake tambayanta saboda me, nan takwashe labarin yanda ummi keyiwa MUFIDA sam bata k'aunarta tahanata kowa nata ya kusanci MUFIDA hatta MUJAHID dake danta batamasa magana fushi take dashi kawai saboda ya auri MUFIDA yaki aurar wacca takeso ita ya aura wato asma'u,,,....
Murmushi abbu yai sannan yace "y'ata munira wannan dikba matsala bace indai har dagaske kinason ma'aruf saboda gimbiya zainab ba'itace zata zauna dakeba ba'itace zata aurekiba kuma bataisa tahanamu yin abunda mukesoba saboda itama a karkashin ikon wani take saboda haka ki amsa man eh kinasonsa kokuma a,a bakyasonsa" duk'arda kanta tai takasa cikin yanayin kunya tace "EHH" sai abbu yace "to Alhmdllh dama abunda mukeso muji daga gareki kenan shikenan tashi kije Allah yamaku albarka" ta amsa da ameen sannan tawuce,,,....
A ranar abbu ya'aika d'an aike yaje yafada a gidansu momy mahaifiyarsu munira gobe za'ayi baikon munira saboda a fitarda hakkinsu, haka kuwa akayi washegari around 10am akai baikon munira da ma'aruf dakuna sadaki naira dubu d'ari a kudinmu na Nigeria da jajayen rak'uma biyar da dawakai dakuma d'aurin dabino goma, anan MUJAHID yaroka da'ataimaka asaka lokacin bikin dai dai danasu Rayyan, baamasa musuba kuwa abbu yace ai shima uban d'ane zai iya sakalokacinda yafi so nan aka saka k'arshen wannan watan wanda kuma yake 15th na watan turawa, bayan angama aranar su MUJAHID suka wuce gida BAGDAAZ,,,....
**********
Rayuwa tacigaba da tafiya inda MUJAHID da MUFIDA sukacigaba da bama cikinsu cikakkiyar kulawa doctur Aysha ma tana nata k'okari sosai wajen kula da lafiyar MUFIDA dakuma abunda ke cikinta,,,"....
Alhmdllh yau sati 'daya kacal yarage afara gudanarda shagalin bikin ma'aruf da munira, Rayyan da Amira, tini MUFIDA taje taciro kud'inda dadynta yabarmata a accaunt naira dubu d'ari biyar domin yin hidimar biki dayiwa munira dik abunda takeso saboda yanzu itace uwa agareta, bayan tacirosu kuma MUJAHID yasake bata wasu naira dubu dari uku yace tak'ara yayiwa munira dik abunda takeso aikuwa nantaita masa godiya da kyakkyawar addua,,,....
Washe gari takeso tawuce Nigeria saboda kiranda munira da Amira keta kwala mata tazo tazo gashi kuma tanaso taje da munira kasuwa, bayan tashirya komai saita shirya taje masarauta domin tamasu bankwana zata wuce, kwatsam koda taje saita tadda asma'u tazo, wani irin wulak'antaccen kallo asma'u tabita dashi kamin tawuce tareda buga wani mugun tsaki da kallon "zaki gane kurenki nan kad'an", itakuwa ko kallon inda take bataiba taje gun ummi tacemata gobe zata wuce Nigeria nan ummi tamata Allah kiyaye hanya tareda kyakkyawar addua sannan tawuce,,,...
Washe gari hartagama shiri tana jiran MUJAHID yagama suwuce kasamcewar shine zaikaita airport saitaga kiran wata new number a wayarta, al'adar MUFIDA ne bata daga kiran new number saboda haka tacilla wayar tafita abunta, koda tadawo har kusan 6 miss call's akamata da wannan number d'in kasancewar tana sauri yasa batamabi ta kan kiranba tafita,,,....
Saida jirginsu yad'aga sannan MUJAHID yadawo gida cike da kewar abar k'aunarsa dakuma d'an babynsa dakullum yake manne dashi.............
Aslm reader's kuman afuwa dan Allah jiya bakuga posting ba bayan kuma namaku alkawari wlh harnayi har kusan 6 read more kawai ina hawa online message's suka fara shigowa daga grps dayawa sai kawai wayar tai restored komai ya goge, kuyi hkr dan Allah wlh banso hkb nima 👏😥
#/Vote
#/Share
#/Comment
```AUFANA for life ```
*I.W.A*
_*TSINTACCIYAR MAGE.....*_🌷
_a true love story_
_*BY~AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183_
® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚
_*Page 73/74*_
_Not Edited_
_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_
3pm dot jirginsu yasauka gida Nigeria a katafaren filin jirginnan na AHMADU BELLO INTERNATIONAL AIRPORT dake cikin babban birnin k'asar kebbi, koda jirginsu yasakko tini munira da uncle hisham dasu musty dakuma bodyguard's sun iso domin tarbanta, tana sakkowa acikin jirgi dagudu su munira sukaje sunamata oyoyo oyoyo itama cikin fara'a suka rungume juna cikin tsintsar farincikin ganin junansu, daga nan kai tsaye suka shiga motocinsu suka wuce izuwa gida,,,"......
Koda suka isa gida kuwa tini baba mai tuwo tsohuwar y'ar aikin hajiyarsu dady tamata had'adden girkinda takeso, cikin fara'a taje tarungume hajiya itama hajiya tana dariya cike da kewar y'ar jikar tata, bayan sungaisa sannan suka wuce ciki ita da munira, suna shiga tacire kayanta tad'aura towel tashiga toilet, wanka tai sannan tad'auro alwala tafito, bayan tafito tasaka kayanta sannan tagabatarda sallan azahar, bayan tagama kuma tahau kan gado sai bacci,,,....
Sai kusan 5:15pm sannan tafarka tana farkawa tai sallan la'asar sannan tafito waje, girkinda baba tamata tazauna taci bayan tagama sannan tawuce side d'insu momyn hamma faruk suka gaisa, anan tazauna har dare abban ammar yadawo suka gaisa sannan takoma side d'in hajiya,,,.....
Da dare kuwa kashe dare sukai ita da munira suna firan rayuwar yau da gobe yanda komai ya sauya, yau ba dady ba momy ba mubina gaba 'daya gida yatarwatse dik hadimai da na'aikata da security's da bodyguard's kowa ya watse gidan yakoma tamkar kufai bakomai acikinsa sai tsintsaye, sunjima sosai suna fira har kusan 2am sai can sannan sukai addua suka kwanta,,,.....
Washe gari kuwa bayan sunyi breakfast sai suka shirya munira da MUFIDA da uncle hisham suka wuce kasuwa Central market, kusan wuni sukai acan dik wani abu da munira ke bukata saida suka siyeshi kuma Alhmdllh sai kud'in suka ishesu har suka gama siyayyar, 4pm suka baro kasuwa suka dawo gida,,,.....
_________________
Gida yafara cika da bak'i na nesa dana kusa daga kauyuka da birane, aunty maryam tai'so dan haka tini tafara aikinta na gyaran amarya, saura kwana hud'u agara gudanarda shagalin biki mutan BAGDAAZ sukazo suka kawo lefe abun mamaki da MUFIDA tagani shine hadda k'annen ummi mata guda biyu da mahaifiyar asma'u da k'anwarta da matan abban MUFIDA biyu sai jakadiya da dakaru hud'u had'e da hadimai mata hud'u waenda sukamasu rakiya, abun yayiwa MUFIDA dad'i sosai tai farinciki sosai, hakama munira wannan ya tabbatar mata da gaskiyar abunda MUFIDA tafad'a mata cewar ummi tasakko yanzu tadaina fushi da'ita,,,".....
Zaune suka acikin d'aki anayiwa munira halawa da dilka sukuma sai shan fira suke ana kwasan dariya, jin karar wayarta yasa hankalinta dawowa kan wayar, wata new number ce tagani donhaka tamayarda hankalinta kan firarsu, bayan kiran ya tsinke saikuma wani yasake shigowa, tai mamaki sosai ganin ana kiranta da new number kasancewar layin Nigeria ne acikin wayarta bana can yankin arab's bane, bayan wannan Kiran ya katse ma saikuma akasake kira sai kawai tasaka wayar silent tacigaba da abunda ke gabanta,,,".....
Washe gari around 10am dot tawuce garin habuja gun Amira saboda kiranda taketa kwallah mata a waya tazo tazo,,,....
Saikusan 3:30pm sannan suka isa garin habuja suka kama hanyar gidansu Amira, tinda suka iso takira Amira tashaidamata sun iso Amira take cike da tsintsar farinciki sai shirye shiryen tarban MUFIDA take, saida suka kwashe kusan 30mnts sannan suka iso gidansu Amira,, wani tantsararren gidane suka gani mai hawa biyu ga manya manya sojoji na gadin gate d'in shiga hakama kuma gida gabad'aya azagaye yake da sojoji kowanne rik'e da bindiga Ak 47, daisarsu saida akafara masu tambayoyi sannan akai checking nasu dadik wani abu dasukazo dashi sannan akabarsu suka shiga ciki "hmm wato saboda tsaro ko badan tsoro ba hakan nadakyau",,,.....
Suna shiga ciki sukai parking suka fito tahango Amira can tsaye da kawayenta suna jiran isowarta, cikin tsintsar farinciki tak'arasa gunsu Amira kuma naisowa gunta suka rungume juna cikin tsintsar farinciki da d'auki ganin junansu, kallonta Amira tai saita zaro dara daran idanuwanta ta firfito dasu waje cikin murmushi da sigar tsokana tace "a,a a,a malama feedom kicemana ahe kin tsufa" saita fara mata waka cikin tsokana tana dariya "mai ciki wallahi banisan sunan nan...mai ciki sunan uwar mijina kenan....mai ciki uhum uhum uhum...um um um" sai suka kwashe da dariya MUFIDA takaimata dukan wata takauce, daga