Showing 36001 words to 39000 words out of 76905 words

Chapter 13 - TSINTACCIYAR MAGE BY AUFANA.txt

AUFANA   

12 Dec 2024

4297

tausayi yace "MUFIDA dan Allah inaso ki d'auki wannan al'amarin a matsayin k'addara kibarsa a matsayin *KUNDIN K'ADDARA* ki tabbas komai yasami bawa to *MUK'ADDARI* ne daga ubangiji dolene saiya sameka" Sam bata fahimci abunda yake nufiba danhaka saiyacigaba da maganar,,,....

"Tabbas MUFIDA ba y'arsu bace basune suka haifetaba" dasauri MUFIDA ta d'ago kanta ta kalli Abban ammar nantake idanuwanta suka cicciko da kwallah, cigaba yai da magana "MUFIDA y'ar amininsace Alhj TAJUDEEN ABDUSSALAM d'an d'an'uwanka Abbu sarki Abdussalam tsohon sarkin k'asar BAGDAAZ yankin Arab's,, shekara ashirin da biyar da suka wuce a makarantar TURKEYSH INTERNATIONAL SCHOOL dake k'asar TURKEY wato makarantar yaya Ahmad yakammala karatunsa nazama cikekken likita, anan ne yahad'u da abokinsa tajudeen, cikin k'nk'anen lokaci shak'uwa tashiga tsakaninsu kasancewar abu d'aya suke karanta, sun shaku sosai dik inda kaga yaya Ahmad to zakaga tajudeen anan idan kana neman d'aya kaga d'ayan to kamar kaga d'ayan ne saboda komai nasu d'aya ne saidai inda sukeda bambamci shine tajudeen yana neman mata sab'anin Ahmad, yaya Ahmad yayi iya k'ok'arinsa dan yaga tajudeen yadaina neman mata amma yak'i gashi kuma gida anyi anyi yafitarda mata yai aure kuma yace saiya kammala karatunsa sab'anin yaya Ahmad dahar ansaka masa rana",,,,.....


Suna cikin karatu akai auren yaya Ahmad da Fatima idan baku mantaba ma har tajudeen yazo shine yamasa babban aboki a auren kuma su sarki dik sunzo, bayan angama shagalin bikin suka koma school suka cigaba da karatunsu,,,, suna gab da kammala karatun tajudeen yahad'u da wata budurwa mai suna SHAHIDA it's shuwa Arab ce amma mahaifiyarta yar turkey ce, yafara soyayya da'ita kasancewar tajudeen akwai wayou yasan dik yanda zaiyi yaja hankalin yarinya nantake yasiye zuciyar Shahida tafad'a tarkonsa saidai ita son aure takemasa sab'anin shi dayake mata son sha'awa, ahankali ahankali yafara Jan hankalinta harta amince dashi yafara kusantarta batareda sunyi aure ba, lokacinda yaya Ahmad yaji zancen nanfa yai cikinsa yanamasa masifa meyasa shi baya tinani meyasa bazaiyiwa kansa wa'aziba yadaina wannan banzar rayuwar k'azamar rayuwa idan dai har dagaske yake toya aureta mana, amma kasancewar tajudeen yariga yai nisa bayajin kira saiyai banza dashi yawatsarda zancensa",,,.....

Haka sukacigaba da wannan bak'ar rayuwa batareda sunyi aure ba, Shahida bata ankaraba kwatsam saiga ciki ya bayyana a jikinta, hankalinta yamatuk'ar tashi nantake taje tasami tajudeen tafad'amasa, shima hankalinsa yatashi sosai saboda dik y'ammatanda yake mu'amala dasu gwangwazajjin matane basa yarda su d'auki ciki amma ita wannan shine ya tirsasat dole badan halayyarta bane to yanzu yazaiyi da'ita, nantake dabara tafado masa saiyacemata kawai a zubda cikin daga baya saisuyi sure nanfa tace ita wallahi ita tinda tasab'awa Allah nafarko bazata sakeba bazata zubda cikinba saidai yasan yanda zaiyi saboda idan gidansu akasani wallahi tashiga tara mahaifinta ko kasheta zaiyi, hankalinsa yatashi sosai dan shid'inma tsoron nasa iyayen susani yake musamman dayakasance gidansu gidan mulki da sarauta ne sarki mahaifinsa sarki zai iya korarsa",,,....


Nadama iya nadama Shahida tayita ta d'ora hanu a ka tana kuka sosai saboda tasan tariga data rusa kyakkyawan ginin rayuwarta, tashi tai tafita batareda sungama yanke hukunciba saidai itakam tariga tayanke nata hukuncin,,"....

Yaya Ahmad na zaune tajudeen yazomasa da zancen nan yaya Ahmad yaketinamasa maganarda yamasa a baya amma yaki yanzu gashi tace bazata zubda cikinba kuma tabbas idan tahaihu shi zata kawowa jinjirin,, tin ranar basusake ganin shahida ba har saida suka kai saura sati d'aya suyi graduation sannan tazo da katon cikinta tafad'amasa yazama da shirin karban babynsa dan bazai tafi yabarta dashiba,,"...

Bayan sunyi graduation batareda sanin yaya Ahmad ba tajudeen yawuce abunsa saima wata letter kawai daya barmasa shidai yaya Ahmad murmushi kawai yai, bayan sunyi graduation sai yaya Ahmad baiwuce gida ba yana jira ya karb'i notification d'insa sannan yawuce, kwatsam wata rana yana zaune saiga shahida tazo tana Neman tajudeen saboda ta haihu zata bashi y'arshi tawuce nan yaya Ahmad yakefad'amata yawuce garinsu shima baisan lokacinda yawuceba sai yar k'aramar letter daya barmasa, kuka tadingayi sosai tana tsinewa tajudeen Ahmad yadinga bata hakuri",,,.....


D'agowa tai tana share kwallah tacemasa yunwa takeji dan Allah yabata abinci taci nanyatashi yashiga kitchen domin d'ibomata abinci, koda yad'ibo yafita saiyaga ba'ita ba labarinta tagudu ta'ajiyemasa baby akan kujera, a rikice yafita yana nemanta amma harya zagaye school d'in baigantaba dole yadawo yad'auki babyn wacca taketa baccinta, hankalinsa yatashi sosai yarasa yazaiyi da babyn cikin ikon Allah dabara tafad'omasa nan yashirya yad'auki babyn yadawo gida",,,....

Kasancewar lokacin ba'a kebbi yake zaune da matarsaba yasa plan d'insa yai dai dai, lokacinda yakawowa Fatima jinjiran kuka tadingayi wato ita tana nan tana killace kanta tana daraja aurensa ammashi yanacan yanacin amanarta to wallahi bazata karb'i yarkowa ta rainaba kasancewar har lokacin basusami haihuwaba, dakyar da sud'an goshi yasamu yashawo kanta takarb'i jinjiran suka fara rainonta suna shayarda'ita da madara,, bayan sati d'aya sai kawai suka kira a gida Fatima ta haihu tasafka lafiya tasamu y'a mace,,,....


Abun yamatuk'ar bama kowa mamaki saboda bawanda yasan tanada ciki kasancewar tayi kusan wata shida rabonta datazo gida ashe baiwar Allah cikine da'ita, nan Ahmad yake fad'amasu ai surprising nasune sukayi saidai shi bayason bidi'a kawai aturomata tsohuwarda zatazo takula tasu amma baza'ayi bikiba zai turamasu kud'i su sayi sa ko saniya su yanka suyi sauran kayan yarkacen shi dagananma Australia zaitafi da matarsa da babynsu saboda su huta, gida basu yarda daba haka itama Fatima iyayenta basuyardaba nan hajiya tace yamaidota gida idan tagama jego saiya d'auketa sutafi nanfa yakafe yace inba hakaba saidai surabu, dole badan sunso hakanba suka kyalemasa matarsa aka tura baba maituwo garin Abuja domin takula da babyn da mai jego",,,...


Yana kawowa nan yad'ago yakalli su Abbu yace "bayan ni baba mai tuwo ma tasan da wannan Sirrin saboda dataje yaya Ahmad yafad'amata gaskiyar zancen, kasanvewar baba mai sauk'in kaice tace " insha Allah bawanda zaitab'a jin wannan zancen a bakinta, haka sukacigaba da binne wannan al'amin inda yaya Ahmad da Fatima da baba sukacigaba da bama baby *MUFIDA* cikakkiyar kulawa, wata d'aya kacal baba tai acan yaya Ahmad yakwashesu suka wuce kasar Saudi Arabia suka gudanarda umrah dik saboda MUFIDA, acan ne yarok'i Allah daya tayasa rik'on wannan yarinyar saboda yai alk'awarin bazai tab'a Neman iyayentaba harsai su sunnemeta da Kansu zai cigaba da kula daita kamar yanda zai kula da y'ay'ansa waenda zai haifa nangaba zaikuma rik'eta tamkar y'ar cikinsa" yana kawowa nan yakalli Abbu da zufa ke ketomasa ta'oina na jikinsa sannan yace "to kaji gaskiyar wannan lamarin" MUFIDA ce tamik'e tsaye kwallah na xubadaga idanuwanta tamkar an bud'e famfo bakinta na rawa tace "wannan wace irin k'addara ce yanzu kenan ni shegiyace wacca aka Haifa batareda aure b...a" bakinta na rawa takarasa maganar tareda fashewa da matsanancin kuka, munira ce tajanyota ta zauna tafara rarrashinta itadinma dai kukan take,,,....


Shuru yaratsa parlon nawasu y'an mintina can Abbu yad'ago yafara magana "tabbas wannan wani al'amarine mai cike da ban al'ajabi saidai babu abunda zamuce sai addu'a dakuma fatan samun kyakkyawar lahira ga Ahmad saboda badik mutum ne zaiyi abunda yaiba kuma insha Allah idan ita MUFIDA tagama takaba zamuje BAGDAAZ domin taga mahaifinta sannan yafad'i inda mahaifiyarta take itama taganta" dasauri MUFIDA tad'ago tamik'e tsaye tace "ni ba'inda zanje Abbu tinda su basunemeni ba nima bazanje gunsuba" tana fadar haka tawuce dagudu tana kuka Abbu yai murmushi sannan yace "kowa zai iya tafiya" nan kowa yatashi yawuce yana jinjina wannan lamarin,,"....


Wunin ranar gaba daya MUFIDA acikin d'aki tayisa tana kuka datagadai wannan bashine mafitaba saita tashi tai alwala tazo tad'auki Qur'an tafara karantawa nantake taji zuciyarta tafara sanyi, saida taji tasami nutsuwa sannan tarufe nantafara korawa dady addu'a tana nemamasa gafara a gun ubangijinsa, tad'auki tsawon lokaci tana yiwa dady addu'a sannan tashafa taje ta kwanta,,,....



***** *****

Rayuwa tacigaba da tafiya inda MUFIDA kecigaba da takabar mijinta faruk, yanayinda yanda take saka damuwa a ranta yasa dikta rame yanzu daga d'aki sai parlor kawai take zama saikuma cikin lambu tai karatun Qur'an, munira takoma school ga bilkis itama tana school ga Amira takoma Abuja tini danhaka yasa batajin dad'in gidan sai idan su musty sundawo daga school shikuma batason zama dashi saboda saiyaita tambayanta momy yanacewa takaishi gun momy, tin tanamasa karya yanzu hartarasa mezatace masa idan yatambayeta saidai taita kwallah tarungumesa tana rarrashinsa,,,....


Haka rayuwa tacigaba da tafiyarmasu cikin k'unci da kad'aicin rashin iyaye,,....


***** *****

Alhmdllh yau itace ranarda MUFIDA tagama takabar faruk nan momyn su faruk tasaka akaimata kitso da lallen Hausa bak'i hajiya tasiyamata sababbin kaya Abban ammar yabata kud'i da wata abaya mai shegen kyau taitamasu godiya tanamasu kyakkyawar addu'ah,,,"...


Sati biyu da gama iddarta takoma aiki inda Abban ammar yabata matsayin mijinta tamaye gurbinsa wato manager,,,.....

Tini akafara shirye shiryen tafiya kasar BAGDAAZ saidai itakam MUFIDA sam batason tafiyar hakan yasa batawani shiri saima harkan gabanta take, tana zaune saiga kiran Amira yashigo nanta d'aga cikin murna suka gaisa nan Amira take cemata tashirya jibi tananan zuwa tanaso tarakata wani waje ne, kamar Amira tasan MUFIDA neman abunda zaisa tak'i tafiya BAGDAAZ take nantake cikin murna tace mata "ok Allah yakawoki lafiya" tace ameen sannan sukacigaba da firarsu,,,....


Ranarda Amira tazo washe garine tafiya izuwa BAGDAAZ yankin Arabs danhaka zancen tafiya aka fasashi saima akai shirin tafiyar da'ita tinda tazo, saidai batasan wace iriyar tafiyace za'ayiba danhaka ta tambayi MUFIDA shin inane zasuje, nan MUFIDA tafad'amata komai bats b'oyemata ba saboda yanzu Amira tawuce k'awa aminiya tazama y'aruwa agunta, Amira tayi mamaki sosai saidai ta jinjinawa dady matuk'a saboda abunda yai badik mutum ke iyayinsaba, nantake tafara shirin tafiyar itama,,,....

Washe gari 8am drivers d'in gidan da bodyguards d'insu suka d'aukesu izuwa airport, 10am jirginsu yad'aga izuwa k'asar BAGDAAZ,,,...


*MASARAUTAR BAGDAAZ*

Sai kusan 2:30pm sannan jirginsu yasauka kasancewar saida jirgin yabi ta Jidda yasauke fasinja sannan suka wuce, koda suka isa kuwa tini aka aiko da driver's da hadimai su d'aukesu jirginsu na sauka kuwa suka d'aukesu izuwa masarautar kasancewar hadiman sunsan Abbu yasa suka durk'usa suna kwasan gaisuwa, kai tsaye masarautar suka wuce dasu,,".....


Masarautar Bagdaaz babbar masarautace babbar daulace wacca aka gina tin kakannin kakanni,,....

Suna isa a k'ofar shiga masarautar hmm baki na sake ina kallon ikon jallah hausawa sukace jaka cikin jaka, wani katafaren ginine akayiwa masarautar Wanda dakagansa kasan tsohon ginine amma ginin ya karb'i sunansa na gini, k'ofar gidan dik dakaru ne zagaye daita kowanne rik'e da bindiga wasu na zarya suna dube dube wasu kuma tsaye suke kawai wasunsu kuma suna zaune gefe d'aya,,,....

Sunaganin motocinsu Abbu nantake da sauri suduka suka taso suka durk'usa suna gaida Abbu sunkumayiwa su MUFIDA barka da sauka lafiya nan cikin sauri aka bude gate motocin suka danna ciki, ko acikin filin gaban gidan saida sukai yar tafiya mai nisa sannan suka isa gunda ake ajiye motoci saboda girman gidan, bayan motocin sun tsaya sannan suka fito suna fitowa saiga dakaru sunzo suna welcoming nasu suka kwashi kayansu suka wuce dasu izuwa masaukinsu, tinda suka iso su MUFIDA ke ware dara daran idanuwansu suna basu hakkinsu gaba d'aya tsarin masarautar yatafi da tinaninsu kaikace masarautar k'asar ingila ne iya kallonka bazakaga karshen gidanba,,,.....


Kai tsaye hanyarda zata sadasu da fadar sarki akawuce dasu, kamar ancewa MUFIDA waiga aikuwa tana waigawa saita zaro daran daran idanuwanta takafe Wanda tagani da mayun idanuwanta..............


Kuyi hakurin jina shuru 2day's NEPA namune yasami yar masala amma yanzu Alhmdllh komai normal zakucigaba da jina akai akai kamar da insha Allah ngd ❤👏





#/Vote
#/Share
#/Comment

```AUFANA for life ```
*I.W.A*🖋
_*TSINTACCIYAR MAGE.....*_🌷
_a true love story_


_*BY~AUFANA*_ _wattpad@Aufana8183_


® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚


_*Page 47/48*_

_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_

Kai tsaye hanyarda zata sadasu da fadar sarki akawuce dasu, kamar nacewa MUFIDA tawaiga tana waigawa kuwa saita zaro dara daran idanuwanta takafe wanda tagani da mayun idanuwan nata,,,.....

Tsintsar mamakine ya bayyana k'arara a fuskarta ganin Rayyan tsaye tareda wasu kyawawan y'ammata twin's larabawa shar dan ko hausardasuke ma dakaji kasan basu iyataba, kasancewar baigantaba yasa tajuya fuskarta tacigaba da tafiya,,,,"...


K'ofar shiga fadar ma tsare take da dakaru hud'u kowanne rik'e da bindiga nan Abbu yashiga gaba sukuma sunabin bayansa, cikin sallama suka shiga ciki mutanen fada suka amsa masu cikin sauri sarki yataso yazo yadurk'usa cikin fara'a yakwashi gaisuwa gun Abbu nan Abbu yad'agosa suka rungume juna sannan abbu ya sumbacesa a goshi nansuka gaisa cikin yarensu na larabci,,,.....


Bayan sungaisa da Abbu sannan yajuyo yabama Abban ammar hanu sukai musabaha sannan suka sumbaci juna a kunce, bayan sungaisa yajuyo yakalli su MUFIDA yafara masu magana cikin harshen larabci nanfa su MUFIDA akai tsuruu ana kallon juna, Abbu dariya yai sannan yafad'awa sarki ai su basajin yaren saidai hausa yai dariya sannan yamasu hausa nansuka gaidasa, tinda MUFIDA taga sarki taketa kallonsa a zuciyarta tace "wannafa mai kama da mr man d'ina kaddai ace shine mahaifinsa kuma shine mahaifina wayyo Allah Allah yasa bahaka bane dansuma twin's d'inda nagani a waje kamarsu d'aya da mr man to kodai nanne gidansu" hakadai taita sak'e sak'e a zuci,,"....

Bayan sungama gaisawa sai aka masu iso izuwa cikin gida, sashen tsohon sarki da matarsa wato d'anuwan Abbu aka wuce dasu, suna isa sarki yataso yana dariya yazo suka rungume juna shi da abbu suna gaisawa bayan sungaisa sannan su Abban ammar dasu MUFIDA suka durk'usa suka kwashi gaisuwa, bayan sungaisa saiga gimbiya matarsa hajiya zainab tafito nansuka gaisa da abbu sannan su MUFIDA suka gaidata, suna anan sashen saiga wata kyakkyawar mata tareda kyawawan y'ammatanda MUFIDA tagani tareda Rayyan sun shigo dakaru mata guda hud'u suna bayansu, nansuka shigo suka gaisa, y'ammatan nan sukazo sukaja hanunsu MUFIDA suna dariya suka fita itakuma momyn faruk sarauniya Sainah tawuce da'ita izuwa sashenta su abbu da abban ammar kuma aka kaisu masaukinsu,,,.....

Sai dare sannan su MUFIDA suka dawo masaukinsu nan sukai wanka sukai sallah suka sauya kaya sannan suka kwanta, around 8pm aka aiko da wasu hadimai hud'u suka kawomasu abinci, girke girke ne kala kala sai wanda kakeson ci hadda na gida Nigeria, 9pm sarki mai ci yanzu yashigo suka gaisa sannan yace sufito sashen sarki za'ayi magana nansuka shirya sannan suka fito atare,,,,".....

Kai tsaye sashen sarki tsoho suka wuce, suna isa MUFIDA tahango wani mai kama da sarki na yanzu nantake taji gabanta ya fad'i, bayan sun isa sunzauna sai Abbu yafara magana "to Alhmdllh kamardai yanda kukaji tajudeen shine mahaifin MUFIDA kuma shi kansa yasani saidai asakamon wani laifi daya aikata shiyasa bai fad'amaku yanada ita ba kuma yamanta da'ita dikda kuwa da tsawon shekarunda yakwashe bai haihuba, MUFIDA" Abbu yakira sunanta wacca kwallah sukariga sukagama wankewa fuska tad'ago ahankali takallesa yace "wannan shine mahaifinki doctor tajudeen",, taju ne yace "Abbu kana nufin kace wannan y'atace" murmushi abbu yai sannan yace "tabbas kuwa y'arkace MUFIDA wacca ka haifa da shahida kukagudu kukabarta" duk'arda kansa yai kasa nantake kwallah suka fara zubomasa, mai martaba ne yace "mufa kunsakamu acikin rud'ani kumana kyakkyawan bayani saboda mufahimta" abbu yace "yanzu kuwa zakuji" nantake yabasu labarin komai tin had'uwarsa da shahida har girman MUFIDA da irin rayuwar jin dadinda tai a hanun dady,,,"....

Labarin yamatuk'ar bama su sarki mamaki da al'ajabi dan tinda suke da taju baktab'a basu wannan labarinba, shikuwa banda zubda kwallah ba abunda yake hakama MUFIDA kuka take sosai,sarki mai martabane yafara magana "hak'ik'a tajudeen kayi abunda yamatuk'ar b'atamin rai sannan ka aikata babban kuskure wanda badan MUFIDA tasami kyakkyawar rayuwa ba da bazan tab'a yafemakaba amma yanzu zakaci darajar Ahmad" abbu ne yaisaurin karb'an zancen "yanzudai ai Alhmdllh dama abunda mukeso kusanta kusan jininkuce sannan shima yasan yanada y'a itama kuma tasansa sannan yafad'amana inda mahaifiyarta take domin akaita taganta dikda basunemetaba",,,....


Taju ne yad'ago fuskarsa yace "hak'ik'a nai nadamar abunda na'aikata kuma natabbata abunda na'aikatane yake biniyana tsawon shekara ashirin da wani abu dasuka wuce, tinda nai aure bansami haihuwaba matana biyu uku muka rabu saboda bana haihuwa amma kowaccensu bata tab'a yin b'ariba har izuwa yanzu, naje school d'inda mukai karatu naita neman shahida amma harnadawo bangantaba kuma bansami wanda yace yasantaba haka nagama yawona nadawo, MUFIDA dan Allah kiyafeman ki yafemana dan Allah" MUFIDA kasa cewa uffan tai saboda kukanda takeyi, Abbu ne yace "kadaina kuka yarona komai yawuce ai Allah dai yak'ara shiryarmana da zuriyarmu" suka amsa da ameen, d'agowa taju yai yace "abbu to ina doctor Ahmad ne bakuxo atareba" duk'arda kai abbu yai sannan yasauke nannauyan numfashi yad'ago yace "Ahmad Allah yamasa rasuwa Ahmad yarigamu gidan gaskiya asanadin matarsa data kashesa" nanfa Abbu yabasu labarin komai har irin wahalarda aka ganawa MUFIDA, sun jinina lamarin sosai taju hadda kwallah saida yaita zubarwa saboda tsintsar tausayin halinda MUFIDA tashiga asanadin laifinda bata aikataba,,,"....

Tajudeen yad'ago yashare kwallanda suka b'atamasa fuska sannan yafara magana "Shahida mahaifiyar MUFIDA bansan asalin gidansuba ammadai nasan ita y'ar k'asar Turkish ce sunanta kuma Shahida Safraz shik'adai nasani agameda ita" abban ammar yace "insha Allah zamusameta inada wani abokin business d'ina dayake k'asar zannemesa namasa magana" daganan dai sukacigaba da tattaunawa harsuka yanke MUFIDA zata zauna anan BAGDAAZ izuwa wani dan lokaci saboda tasan y'an uwanta suma su santa,,,"....

Wasu hadimai mata mai martaba yakira su hud'u suna zuwa sai yace "kukaisu sashen gimbiya Zainab gunsu Nasma da Nasmat akaita gun Biryama shima tagansa tasansa takuma gaidashi da jiki gobe saisuje suzaga gari suje gidajen sauran y'an uwa" nan hadiman sukace amsa sannan su MUFIDA suka mik'e tsaye suka fita,,,....

Kai tsaye sashen gimbiya suka wuce dasu bayan sun isa su MUFIDA suka durk'usa suka gaidata nan dasauri su Nasmat suka taso suna murmushi suka kamasu MUFIDA suka wuce d'akinsu MUFIDA sai kallonsu take itadai suna mata kama da mr man d'inta, Amira tace "waye biryama hala" Nasmat tace "yayanmu ne shi" kasancewar tafi y'ar uwarta jin hausa sosai sai Amira tace "to sarki yace kukaimu gunsa mugaidashi" sukai murmushi saisuka mik'e tsaye suka fita hanun Nasmat nasakad'e dana MUFIDA,,,,....


Cikin sallama suka shiga tareda bud'e k'ofar parlon, wani katafaren parlor ne naji da gani daka gansa kasan bana k'aramin mutum bane kodai yarima kokuma shi kansa sarkin, atare suka kutsa suka shigo yana a zaune kan kujera 3seater kafafuwansa kan matashi Rayyan kuma na gefensa yana b'are masa aiba yanabashi yanaci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login