Showing 75001 words to 76905 words out of 76905 words

Chapter 26 - TSINTACCIYAR MAGE BY AUFANA.txt

AUFANA   

12 Dec 2024

4304

su Amira sunzo hakama su munira nan aka hade ana zumunci, sai bayan kwana biyu da biki sannan kowa ya watse,,,.....


Haka rayuwa tacigaba da tafiya inda MUJAHID wanda yadawo Abban jawaad itakuma ummin jawahir yake bama iyalinsa cikakkiyar kulawa, abulkhair nada wata bakwai da haihuwa Abban jawaad yakammala ginin tamfatsetsen gidansa sabo gall ginin kasar England wanda turawa suka gina, ni kaina danaga gidan saida hankalina yatashi saboda tinda gyatuma tajefoni duniya idona baitaba ganin irinsaba hhh Lol, ranarda suka tare acikinsa saida MUFIDA tai walima saboda farinciki da murna, a yanzu matsala d'aya suke fuskanta itace rashin haihuwar munira sunyi yawon asibiti anyi gwajen gwajensu har ba adadi amma har yanzu shuru, likita ya tabbatarmasu da dikansu lafiyarsu kalau kawai dai lokacine baiyiba,,,...


Yanzu har munira tagaji tabarwa Allah, dikda munira keda matsalar amma MUFIDA tafita damuwa musamman dataga ma'aruf yanda yadamu sosai saboda yanason yara, matsalar tana matukar damun MUFIDA dik yanda MUJAHID yakeson ya kwantar mata da hankali amma yakasa saboda shi kansa matsalar tana damunsa, ganin yanda MUFIDA takasa kwantarda hankalinta yasa yabiyamasu umrah suje kozata dan rage damuwa sosai, aikuwa taji dad'in hakan sosai dan dik ibadardasukai fiyeda rabinta rokon Allah take akan yamagance masu matsalarsu,,,....


***** *****

Bayan sundawo daga umrah MUFIDA tasake samun wani cikin lokacin kuma abulkhair nada shekara biyu Afza kuma nada shekara biyu da wata bakwai Amira tasake samun wani cikin, wannan cikin kam ALHMDLLH batasha wani wahala ba kamar cikin Afza, haka suka sake haifar yayansu MUFIDA tahaifi da namiji amma saidai wannan haihuwar kam da matsala don saida akamata operation aka cire babyn, tasha wahala sosai ganin haka yasa MUJAHID yace adaure mahaifarta saboda wahalan yai yawa yana tsoro kar watarana yarasata gaba d'aya, Amira kuma tasake haifan baby boy wanda yaci sunan abban Rayyan sukamasa inkiya da Affan, dan MUFIDA kuma yaci sunan sarki Abdussamad suka masa inkiya da Anwar,,,,.....


Kwatsam Anwar nada wata biyar a duniya wata rana munira ta tashi da zazzabi, abu kamar wasa sai cigaba yake, ganin abun yafi karfin tinaninta yasa takira ma'aruf, yana zuwa baiyi sanyaba kuwa yadauketa sukaje asibiti, tin a gwajin farko aka tabbatar masu da cikine natsawon wata biyu, abun kamar a mafarki haka suka gani, saida result yafito sannan suka tabbatarda gaskiyan abunda doctur yafada aikuwa dasauri ma'aruf yakira MUJAHID yafadamasa, kankace me kowa yaji murna da farinciki agun MUFIDA baya misaltuwa hadda sadaka saida tai dan farinciki,,,....


Cikinta nakai wata rana ciff suka dawo BAGDAAZ anan ta haihu inda ta santalo kyakkyawar yarta mai kama da ma'aruf, ranar wuni sukai cike da farinciki MUFIDA sai nan nan ake da munira, bayan kwana d'aya da haihuwa aka wuce da ita Nigeria saboda hajiyar dady tamatsa saidai amaidata nan doke kuwa akayi mata haka,,,.....


Ranar suna babyn taci hajiyar dady wato fatima sai sukamata inkiya da khairat, saida sukai wata hudu cif sannan suka koma BAGDAAZ,,,, haka rayuwa tacigaba da gudana cikin tsintsar farinciki da kaunar juna,,,......


****** ***** ******

Shekaru na tafiya watanni na shudewa yau kimanin shekara goma sha biyu kenan da auren MUJAHID da MUFIDA inda jawahir da jawaad kuma keda shekara goma da haihuwa, yaran sungirma sosai gwanin birgewa MUFIDA kuma yanzu anzama babbar mace kuma uwa,,,....


Sarki tsufa yakama sosai yanzu yana wahala wajen gudanarda sarautarsa saboda tsufa, ganin tsufa yakamasa yasa ya yanke shawarar sauka daga kujerarsa yabama dansa MUJAHID, bayan yagama yanke shawara da mahaifinsa mai martaba da mahaifiyarsa dakuma matarsa saiyakira MUJAHID yamasa bayanin komai, dikda MUJAHID bashida raayin yin mulki amma dole yakarba saboda bazai iyayin musu da mahaifinsaba, haka ya amince da karban mulkin,,,....


Bayan sungama magana da maraice kowa yahallara mutanen fada nan sarki yasanardasu zaiyi murabus yabama dansa MUJAHID, kowa yai na'am dahakan saboda MUJAHID mutum ne wanda kowa ke alfahari dashi da kyawawan halayensa da dabi'unsa nan kowa yai na'am taredayiwa MUJAHID mubaya'a,,,....


Bayan wata d'aya dayin maganar kowa yaji sai sarki yatara mutane a fadaa, bayan kowa yahallara nan yacire rawaninsa sannan yasauka daga kan kujera MUJAHID yahau sannan yabasa rawanin da sandar mulkin nan aka nada MUJAHID sannan mai shela yai shaidawa mutan gari MUJAHID yanzu shine sarkin kasar BAGDAAZ shine sarkin babbar masarautar BAGDAAZ,, bayan wata uku dafaruwar haka sannan akai gyaren gyaren masarauta akai sabon fenti aka sabunta komai nacikin masarauta tareda yin sababbin gini acikinta wato inda sabon sarki zai zauna da iyalinsa kenan sannan aka sabunta komai nagidan tindaga bed's kujeri kayan sakawa na sarki da gimbiyarsa kayanda tsofaffin sarakuna ke sakawa har izuwa abincin gidan da dai komai da komai saida aka sauya,,,....


Bayan angama gyare gyare sannan aka saka ranarda zaa nada sabon sarki, ana saka ranar MUJAHID yace shima ranar zai nada MUFIDA amatsayin gimbiyar masarautar BAGDAAZ, hakan kuwa yayiwa kowa dadi kuma kowa yai farinciki dahakan sosai,,,"....


Ranarda zaayi nadin kuwa hmm taro ne akai nagani na fada iya kallonka bazaka iya kai karshen adadin mutanenda sukazoba su Rayyan kuwa sune agaba, acan bangaren MUFIDA kuwa anacan anamata shiri namusamman su Amira da munira suke tarbon baki, 12pm dot aka nad'a MUJAHID amatsayin sarkin k'asar BAGDAAZ bayan angama nasa nadin kuma anan shima yanada uwar gidansa amatsayin gimbiyar masarautar BAGDAAZ,,,bayan angama kuma abban MUJAHID wato tsohon sarki yashirya gagarumar liyafa inda aka ci aka sha akai hani'am aka rarraba kayan biki sannan kowa ya watse,,,....


Tindaga ranar MUJAHID yacigaba da kula da k'asar BAGDAAZ inda MUFIDA ketayasa gudanarda mulkin tahanyar basa kyawawan shawarwari domin taimakamasa amatsayinta na matarsa kuma gimbiyar masarautar,,,....


***** *****


Rayuwa tacigaba da tafiya inda MUJAHID da MUFIDA girma yafara kamasu, jawahir da jawaad ayanzu sun kammala secondary School har sun shiga University abulkhair da Anwar kuma suna secondary School kasancewar basuda wani tserayya atsakaninsu sosai,,,, A b'angaren su Amira da munira kuwa Afza nagab da kammala secondary School Affan kuma yana ss 1 sai k'annensa biyu mata kuma suna jss section, khairat kuma na jss 3 sai k'annenta biyu Amir da Aryan suna jss 1, Alhmdllh zuriya ta yawaita komai natafiya normal zumunci sai k'ara kulluwa yake,,,....


Jawaad da jawahir na 200level a jamiar dake madina inda ma'aruf ke lecturing Afza tashiga itama tafara 100level, yaran matukar kaunar junansu kaikace uwa d'aya uba d'aya suke, ahankali soyayya tashiga tsakanin jawaad da Afza inda yatashi daga yaya yakoma masoyi, jawaad baiyi sanya a guiwaba yatinkari ma'aruf yafadamasa yana son Afza, ma'aruf yaji dad'in hakan sosai nanshima yakira sarki MUJAHID da Barrister Rayyan yafadama, kankace me maganar takarade koina,,,....


Bayan sundawo hutun zagon farko na karatu MUJAHID yakira Afza yatambayeta shin tana son jawaad, cikin yanayin kunya tace eh nan yace "to Alhmdllh dama inaso naji daga bakinkine tashi ki tafi Allah i maku albarka" tace ameen sannan tafita,, sati d'aya kacal yakara akaje Nigeria neman aure, ma'aruf baidawoba saida aka bada auren Afza ga jawaad hakan kuwa yayiwa kowa dadi kowa yai farinciki,,,Acikin dan kankanen lokaci akasha shagalin bikin Afza da Jawaad amarya ta tare agidanta,,,,".....


_________________


Gimbiya MUFIDA ce zaune acikin katafaren parlonta tana hutawa kyawawan yaranta zaune a gefenta khairat da Anwar da Amir saiga d'aya daga cikin hadimai mata tashigo, cikin girmamawa tadurkusa tace "Allah yajima da ranki gimbiya barade ne yazo yace wai gawata mata tazo tsohuwa tace ke takeson gani yanzu anyi anyi ta tafi hadda dukanta anyi amma taki tafiya" tashi tai daga kishingid'enda take sannan tace "kubarta tashigo" tana fadar haka sai hadimar tace "to angama ranki yadade" sannan tawuce,,,....


Batafi 30mnts da fitaba saigata tashigo da wata tsohuwa mai bak'ar kama tana wani irin wari mara dad'in ji itama hadimar rufe hancinta tai suna tafiya tana fesa tirare saboda warinda tsohuwar keyi, tana shigowa dasauri su khairat suka rufe hancinsu Amir yace "Subhanallah wannan wane irin warine haka" k'arasowa tsohuwar tai sannan tadurkusa kwallah nazuba daga idanuwanta tace "MUFIDA yata kece acikin wannan daular haka" cikin tsintsar mamaki dakuma rashin shaida wannan tsohuwar tace "baiwar Allah wacece ke?" kwallah sukaga suna zubowa daga idanuwan tsohuwar tace "MUFIDA nice momy momyn musty" dasauri MUFIDA tamike a tsaye cikin tsintsar mamaki tareda fadin "momy kece" tace "Eh nice MUFIDA kinga yanda Allah yayi dani ko kinga yanda duniya tajuyaman baya ko" kwallah ne suka fara zubowa MUFIDA su Amir da khairat da Anwar naganin haka saisuka taso tsaye sukacewa MUFIDA "ummi wacece ita Hala" cikin harshen larabci suke mata magana sai tace masu "itace ummin ammin ku munira ummin khairat" saisuka zuba mata idanuwan suna kallonta cikin tsintsar mamaki, daganan sai MUFIDA tai umarni daashiga daita ciki nan hadimai suka shiga daita,,,,.....


Saida suka tsabtaceta taci abinci sannan sukaje suka fadawa gimbiya MUFIDA sunkammala,,, cikin sallama MUFIDA da munira sukashigo, zaune take akan gado tai shuu sai suka karaso suka zauna, kallonsu tai tace "dan Allah MUFIDA narokeki ki yafeman abunda namaki natabbata abunda na aikata maki da dadyn MUFIDA shine yake bibiyar rayuwata, narasa komai nawa dik tarin dukiyarda na mallaka ta halak data haram dikta kare komai yakare ga mubina tamutu yayana dik sun gujeni hatta mustapha danaje gunsa guduna yai" saita kalli munira tace "munira kiyiman magana ko sanyi naji dan Allah" daga munira har MUFIDA kuka suke sosai, dakyar MUFIDA tadago takalli momy sannan tace "shikenan momy yaisa haka kidaina kuka dan Allah nayafemaki dik abunda kikaman ni dama can wallahi ban rikeki azuci ba kinemi yafiyar ubangijinki saboda shine babban wanda kikayiwa laifi saikuma dady wanda shi ba'abunda zamu iyacewa akansa saboda datin farko kunkarbi hukuncin Court dadik wannan matsalar batafaruba" hmm....!!! Momy tasauke nannauyan numfashi sannan tashare kwallanda suka zubomata tace "hakane sai a yanzu ne nake girban abunda nashuka bankarbi hukuncin Allah ba yanzu gashi yana hukuntani dakansa tinkan naje gunsa wannan kadai yaisa yazama *EZNAH* gasauran masu halayya irin tamu, mubina anyi mutuwar wulakanci" saita fashe da kuka MUFIDA da munira ma kukan suke sosai,,,,......


Shigowar su Anwar ne yasa suka tsagaita da kukanda suke, cikin sallama suka shigo sai momy tadago tashare kwallanda suka bata mata fuska sannan tace "waennan sune jikokin nawa" MUFIDA tace "Eh sune wannan shine Anwar sai wannan abulkhair saikuma waennan sune yaran munira khairat da Amir sauran k'annensu suna makaranta, saikuma akwai yayyensu mace da namiji tagwaye jawahir da jawaad, jawaad yai aure ya auri yar uwarsa yar Rayyan da Amira kawata yanzu hakama tana d'auke da juna biyu suna karatune a University dake madina" murmushi momy tai sannan tace "masha Allah ubangiji ya albarkacesu yakara zaman lafiya atsakaninsu" sukace ameeen,,,....


Daganan bayan sarki MUJAHID abban jawaad yadawo daga rangadi aka kaita gunsa, bayan sungaisa sai MUFIDA tanemi farmar MUJAHID yabari momy tazauna taredasu saboda tanaso su nemamata maganin ciwonta ko Allah zaisa tawarke, MUJAHID baihanaba kuwa haka suka zunduma wajen nemawa momy magani saidai amaimakon taji sauki ciwon sai karuwa yake,,,,....


Haka dai akacigaba da nemamata magani badan lafiya tana shigowaba, haka kuma rayuwa tacigaba da tafiya inda alkhairai keta shigowa acikin ahalin MUFIDA da MUJAHID..




ALHMDLLH ALHMDLLH ALHMDLLH

Taammat bihamdillah, to masoya dika dika anan nakawo karshen wannan labari nawa inafatar Allah yayefaman kura kuran da nai aciki yakuma bani ladan abunda na rubuta ameeen


Saikuma mun hadu a sabon littafena mai zuwa after sallah insha Allah nagode



Zaku iya samun littafaina complete a
WhatsApp@AUFANA4real

Wattpad@Aufana8183

Facebook@Aufana ummi jawahir Aufana

Nagode




```AUFANA for life ```
*I.W.A*🖋

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login