Showing 60001 words to 63000 words out of 76905 words

Chapter 21 - TSINTACCIYAR MAGE BY AUFANA.txt

AUFANA   

12 Dec 2024

4305

kimanin wata goma kenan da aurensu, wani abun mamaki da MUFIDA ke gani shine cikinta sai girma yake har yanzu bobbs d'inta basu huceba basu daina cika ba sannan tinda tai bari har yanzu bata al'adartaba tazo ( period or menstruation) abun yana bata mamaki kuma yana d'agamata hankali saboda ko lokacinda tana budurwa taba tsallaken wata dik wata saitaga al'adanta amma yanzu har kusan wata uku amma shuru, a zuciyarta tace "dolene nasanarda MUJAHID muje asibiti inba wata matsala bace",,,....


Tana cikin wannan tinanin sai wayarta tai kara nanta d'akko, tana dubawa saitaga sunan (my Lil Sis M ) akan secreen d'in wayar aikuwa dasauri tadaga tak'ara a kunne cikin zumud'i, daga 'dayan bangaren akai sallama sannan akace "haba my big Aunt haka akeyi dankina makale da masoyinki shikenan saiki manta da y'an k'annenki" dariya MUFIDA tai sannan tace "habadai my Little Sister munira wace ni dazan iya mantawa da y'an kannena abun k'aunata wallahi kullum kuna raina yanzu hakama kullum cikin maganarku nake kwanan nan harma nayiwa yayanku magana muzo mu gaidaku to shinedai baice komaiba shiyasa kukajini shuru amma insha Allah acikin kwanannan zaku ganni" murmushi munira tai sannan tace "to shikenan da har munyi fushi mundauka kin manta mune amma yanzukam munyi hak'uri" saitai murmushi tace "yawwa y'an kannena ina sonki ina alfahari daku wallahi ina my Lil bro musty" munira tace "yanzu suka fita tareda uncle hashim yazo kinga aunty MUFIDA kusan time by time sai musty yaita tambayana momy da aunty mubina sainarasa amsarda zanbashi wallahi",,,...


Shuru MUFIDA tai sannan tasauke nannauyan ajiyan zuciya, ganin haka yasa munira ta kauda zancen da fad'in "am aunty dama nakirane nafad'a maki gobe insha Allah zamuzo BAGDAAZ su Abbu ne sukace kar afadamaki abari muyi surprising naki shine nikuma nazo a boye nakiraki nafad'a maki" wani irin dad'i MUFIDA taji tace "kai dan Allah munira dagaskiya kike" munira tace "Allah kuwa gobe zamuzo" aifa nan MUFIDA taita tsalle tana murna,,,....


Sunjima sosai suna waya daga bisani sukai sallama, sunayin sallama takira MUJAHID tafad'amasa nan shima yaita murna sannan yamasu addua da fatan sauka lafiya,,,...


A daren ranar bayan MUJAHID yadawo daga office saiya d'auketa sukaje gida, koda sukaje saisuka tadda ana shiryen shiryen taryan mutan k'asar Cyprus wato MA'ARUF kanen MUJAHID dake can yana karatu yanzu yagama shine zai dawo gobe, kasancewar har yanzu ummin MUJAHID batasake mata fuskaba yasa tai zamanta a sashen jaddati bataje sashentaba hakama MUJAHID baitarukataba akan taje saboda shi bayaso yaga anawulk'antamasa ita shiyasa yanzu kosunzo bayacewa taje sugaida ummi saidai shi yaje dikda koya gaidata d'in ba karb'amasa takeba dan har yanzu fushi take dashi saidai ya zauna suyita fira da k'anensa idan suka gama yadawo sashen jaddati, su Nasmat ma sunaso suje gun MUFIDA ko kwana d'aya suyi amma ummi tahana,,,....

Sunjima sosai anan kasancewar idan ana wani biki a gidan to kowa nagidan baya bacci any time kamar ba dareba mutane sai zirga zirga suke hadimai kuma kowa na nasa aiki, sai kusan 11pm sannan suka koma gida,,,"....


Washe gari around 10am dot akaje dauko Ma'aruf airport dasu munira kasancewar jirgin lokaci 'daya suka shigo sai aka raba biyu MUJAHID da sauran dakaru sukaje dauko ma'aruf mai martaba da wasu dakarun sukaje d'akko su munira su MUFIDA kuwa aka fake gida ana jiran isowarsu,,,....


Su munira ne suka fara isowa nanfa su MUFIDA aka had'e sai murna ake ana tsalle, bayan sun iso ne su ma'aruf suka iso nan gida yacika da mutane y'an uwa dakuma abokan arziki, abban MUFIDA ma yazo tareda matansa,,,,....

Tinda ma'aruf suka iso yakyalla idonsa ga munira yakasa d'auke idonsa sai kallonta yake, shi abunda ma yafiso yasani akanta shine ya zumuncinsu yake dasu,,,...


Ma'aruf kyakkyawane kamar MUJAHID amma MUJAHID yafisa tsayi da fad'in fuska kuma yafisa fari sosai amma shima dai very handsome gyai ne gashi d'an bokone yanaji da boko sosai d'an gayune nabugawa a mujallah,,,"....


Bayan sunhuta angama gaisawa da juna sai sarki ya shiryamasu kasaitacciyar walima ta murnar dawowan ma'aruf da kammala karatunsa wacca zaagudanar a babban parlonsa na taryan manyan bak'i, zaagudanarda walimar 2:30pm bayan angama sallan azahar,, daganan MUFIDA takwashi su munira suka wuce gidanta, acan sukai shirin zuwan walima bayan sunshirya sannan suka fito domin suwuce, harsun fito suna jiran isowar driver saiga ma'aruf yadanno hancin motarsa shi da friends d'insa, bayan yaiso yai parking saiyafito cikin fara'a da dariya suka gaisa da MUFIDA sannan yakalli munira itama suka gaisa yana mata wani irin kallo da'ita saida tadan ji ta tsargu, ganinsu sunfito kuma yasan can gun walimar zasuje yasa yace suzo mana yakaisu shima can zasu,,,...


MUFIDA batamasa musuba kuwa suka shiga suka wuce, acanma ma'aruf sai kallon munira yake dik inda tai saita gansa dazasu zauna ma kujerardake kusa da'ita ya zauna, bayan angama komai MUJAHID yazo yadaukesu yawuce dasu gida.............







#/Vote
#/Share
#/Comment

```AUFANA for life ```
*I.W.A*🖋
_*TSINTACCIYAR MAGE.....*_🌷
_a true love story_

_*BY~AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183_

® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚

_*Page 69/70*_
_Not Edited_

_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_

Suna isa wanka su MUFIDA sukai shikuma MUJAHID yawuce bedroom d'insa, bayan sunyi wanka sannan sukafito parlor humaida takawomasu abinci nan suka zauna sunaci sunashan firar yaushe gamo,, bayan sungama sannan sukai zaune munira tafara bama MUFIDA labarin abubuwanda suka faru bayan tafiyanta, sunjima sunashan fira har kusan 7pm ganin ankira sallar magrib yasa suka tashi suka shiga ciki domin gabatarda sallah,,,....

Bayan sungama sai MUFIDA tafita tabar munira anan, kai tsaye d'akin MUJAHID tawuce,,,"....

Cikin sallama tabud'e k'ofa tashiga, zaune yake akan gado yana tsara kaya acikin traveling bag, yanajin sallamarta yad'ago fuskarsa cikin fara'a da murmushi yakarb'amata, k'arasowa tai itama cikin murmushin tazauna kusa dashi tana fuskantarsa sannan tace "barka da hutawa habiby na" yai murmushi tareda rik'o hanunta sannan yace "barka dai my only one da harnace yau my only anhad'u da k'anwa anmanta da habiby" dariya tai tace "laa a,a wallahi kasan anjima ba'ahad'uba shine muketa shan fira amma kana raina dama so nake nai sallah sannan nazo gunka",,,.....

Murmushi yai sannan yamatso dab da'ita yalakuci tsinin hancinta cikin tsokana yace "to me za'abani yanzu kishi nakeji amma na matana" murmushi tai tasinne kanta k'asa cikin yanayin kunya batareda tace komaiba, shima murmushin yai yace "hmm only na badai kunya ba bansan lokacinda wannan kunyar zata fitaba gabadaya amma nasan dik laifinane daban cireta ba gaba 'daya tin a first night" hararansa MUFIDA tai sannan tace "a first night ai mugunta kai" dariya ya kyalkyale da'ita sannan yace "my only ashe dai haryanzu baki mantaba" "inafa zan manta kuwa idan mai tutu ya manta ai wanda ke kwasansa bazai mantaba" gyara zamansa yai yana kallonta yace "nimafa naci wuya aranar" hararansa tasakeyi tace "bawani dad'i dai kasha" yai dariya sannan yajuya yacigaba da aikinsa,,,,.....

Kan gadon tahau dakyau tana fad'in "am habiby wai inazakaje ne naga kanata harhada kaya haka" mikewa yai tsaye izuwa wardrobe d'insa yana fad'in "wallahi wata tafiyace takamani" cikin mamaki tace "tafiya kuma zuwa ina?" "Nigeria, zamuje neman aure Amira ne wa Rayyan" zaro daran daran idanuwanta tai ta firfito dasu waje tace "Ehhh....!!!" cikin tsintsar mamaki, yanda tai sai abun yabasa dariya yace "yess insha Allah kuma munada hope d'in baza'ahanamu ba kinga nanda after sallar azimi saimusha biki",,,,...

Tsintsar mamaki da farinciki yagama cika MUFIDA tama rasa mezatace kawai tasakko daga kan gadon tazo tarungume MUJAHID tareda bashi hot kiss a hab'a sannan tace "wallahi naji dad'in wannan abun nai matuk'ar farinciki sosai" janyota yai yatallafo fuskarta da dika hannayensa cikin murmushi yace "ai nasan zakiji dad'i kuma zakiyi farinciki shiyasa nai k'okarin hada wannan abun domin kiyi farinciki, jibi insha Allah zansauka Nigeria zanyi kwana uku a can sai angama komai sannan zan dawo" wata iriyar dariyar farinciki tai tasake rungumesa tana fad'in "ina sonka ina matuk'ar k'aunarka mijina" yai dariya yace "nima ina k'aunarki matana",,,....

Daganan cigaba tai da had'amasa kayan dakanta saida tatsara komai ta harhahada komai sannan tagyaramasa d'akinsa sai shan fira suke suna barkwanci da junansu, bayan tagama sannan sukafito atare suka dinner tareda munira,,,....

Washe gari bayan sunshirya sai MUJAHID yadaukesu yakaisu can gida, koda suka isa ma'aruf na harabar gidan yana buga game shi da friend's d'insa cikin game were's, yana ganinsun fito yazo cikin fara'a da murmushi suka gaisa da MUJAHID sannan yagaida MUFIDA, bayan sungaisa sannan yakalli munira itama suka gaisa, atare suka wuce ciki yabar friend's d'insa,,,....

Saida MUJAHID zai fita sannan suka fito atare, basuko gama buga game d'in ba yace atashi nan suka wuce side d'insu, wanka yatsala cikin English were's had'addu sai kamshin daddadan tirare yake, bayan yagama shirin yakalli kansa a mirror ya tabbatar yagama had'uwa sannan yafita,,,....

Kai tsaye side d'in jaddati yawuce koda yaisa dik suna zaune sunashan fira, cikin sallama yashigo yana fara'a yazo ya zauna kujerardake kusa data munira akacigaba da firan dashi,,,....

Sunjima sosai anan anansuka wuni sunashan fira dasu Abbu musty sai tsalle yake ajikin MUFIDA tamkar itace mahaifiyarsa koda yake hausawa sunce babbar yaya uwa ce, saida MUJAHID yadawo daga office sannan yazo yad'auki MUFIDA suka wuce kasancewar munira anan suka barta,,,"....

________________

Around 7:40pm MUFIDA na a zaune bayan tagama sallan magrib saiga kiran munira yashigo a wayarta, ahankali tad'auki wayar sannan tadaga tareda kara wayar a kunnenta, bayan sungaisa munira tace "am aunty MUFIDA inataso muyi wata magana d'azu amma yaya MUJAHID yahana" cikin kulawa MUFIDA tagyara zamanta sannan tace "Eyyah menene hala" itama gyara kwanciyarta tai sannan tacigaba "wallahi aunty tinda mukazo ma'aruf yamanneman kaman cwingom narasa yanda zanyi dashi, yauma d'azu bansan a'ina yasami number na ba saigashi yakirani wai yananemana a lambu, bayan najene yake fad'aman wai shi sona yake kuma da aure yake sona dan Allah karnace a,a wallahi tinda yaganni yaji sona yashiga zuciyarsa" tak'arasa maganar cikin dariya, MUFIDA ma dariyan tai sannan tace "ai tinda naga yana wani sinne sinne yana sadda kai idan zai gaidani hadda wani d'an risinawa nasan dawata ak'asa, to munira naji dad'in hakan kuma nayi farinciki sosai, saidai munira gaskiya ni ban amince ki amincewa tayin soyayyar sa ba saboda banaso ki auresa" jin abunda MUFIDA tafad'a yasa dasauri ta tashi daga kwancenda take tace "meyasa aunty MUFIDA" d'an shuru MUFIDA tai sannan tacigaba "munira nikaina dakikagani ummi mahaifiyar MUJAHID bataso MUJAHID ya aureni ba hakan yasa yanzu haka fushi take dashi saboda kin bin umarninta dayai yaki aurar y'ar uwarsa y'ar kanwarta ya auren" nandai takwashe komai daya faru tafad'amata sannan tak'arasa dafadin "a yanzu haka ummi bata k'aunar ganina bataman magana tahana kowa nata yakusanceni hatta k'annen MUJAHID dasuke uwa 'daya uba 'daya sai ma'aruf ne kawai shima kuma nasan batasan yana zowa nanbane, saboda haka munira banason kema kishiga acikin halinda nake kuma banason kiyi saurin shiga acikin soyayyar ma'aruf saboda inatsoron kar mahaifiyarsu tace bazai aureki ba,, munira kawai kibama ma'aruf hak'uri yaje yanemi wata kema kuma Allah yabaki wani",,....

"Hmm....!!!" munira tasauke numfashi sannan tace "shikenan Aunty dama banbashi amsa ba yanzukuma tinda haka abun yake zanbasa hak'uri yaje yanemi wata kawai" MUFIDA tace " shikenan Allah yabaki wani nagari shima kuma Allah yabasa wata tagari" tace ameen sannan sukai sallama,,,....

Waigowarda zatai sai kawai MUJAHID a tsaye yana kallonta, juya fuskarta tai cikin jin kunyar maganarda tafad'awa munira abunda ke tsakaninta da ummi saboda tasan yaji dik zancensu",,,...

Ahankali yak'araso fuskarsa d'auke da fara'a wacca tabama MUFIDA mamaki saboda a zatonta zataga tsintsar b'acin rai ne a fuskarsa amma saitaga akasin hakan, zama yai dab da'ita cikin sakin fuska yace "MUFIDA sam baidace kifadawa munira abunda ke tsakaninku da ummi ba ma'aruf yaganta kuma yaji yanasonta itama kuma na tabbata kila tanasonsa to meyasa zakiyi haka amatsayinki na yaya agaresu, hakan dakikai baidaceba sam" shuru tai tana kallonsa cikin mamaki baidamuba yacigaba "ma'aruf yafad'aman yana son munira kuma nai na'am dahakan nai farinciki sosai kuma insha Allah zanyi tsaye da kafafuwana har sainaga wannan auren ya tabbata" dasauri MUFIDA ta taresa dafadin "MUJAHID karkai hakan wallahi banason munira itama tashiga acikin halin rayuwarda natsinci kaina aciki inaso naga munira nafarinciki inaso naga sirikar munira tana alfahari da'ita kuma tanasonta dan Allah narok'ek'a kabar wannan zancen please....!!!" takarasa cikin magiya kwallah nabin fuskarta,,,,....

Juya fuskarsa yai sannan yace "MUFIDA kidaina fadar waennan maganganun kema insha Allah ummi zatasoki watarana kawai dai raunine da ummi irinna mata bata fahimceki bane kidauka aranki wata rana zata soki sannan kadace zaki hana ma'aruf y'ar uwarki idan kikamana hakan sam baki kyauta mana ba kuma bazanji dad'i ba shima kuma haka saboda yariga daya fad'a tarkon sonta kuma kinsan zafi da rad'ad'in rasa masoyi" shuru kawai tai batasake cewa komaiba sai yacigaba "abunda kawai nakeso dake shine, kimasu addua dakuma fatan alkhairi arayuwarsu sannan ki rik'o Allah yafahimtarda ummi tagane gaskiya dakuma matsalar raba masoya ko shiga atsakaninsu" ganindai har yanzu takasa sakewa yasa yamatso dab da'ita cikin murmushi yajanyota tadawo jikinsa tareda yin kissing nata,,"....

D'agota yai cikin murmushi yace "pleace my only ki saki jikinki mana banaso inganki acikin irin wannan yanayin dan Allah" y'an kwallanda suka zubomata ta share sannan ta k'ak'aro murmushi tace "shikenan nadaina" yai dariya yace "yawwa my only one Allah i maki albarka" tace ameen itama cikin murmushi, jin kiran sallar isha yasa yamik'e yafita izuwa masjid,,,....

Washe gari tin 8am MUJAHID yashirya yafito tareda MUFIDA, atare sukaje airport saida jirginsu yad'aga sannan suka dawo cikin kewar abun k'aunarta,,,...

Kimanin kwanan MUJAHID biyu da tafiya su munira suka koma Nigeria sukabar MUFIDA cikin tsintsar kewa,, MUJAHID kuwa ranarda yasauka washe gari akai baikon Amira da Rayyan tareda saka ranar bikinsu, abun yamatuk'ar yiwa MUJAHID dad'i Rayyan kuwa farinciki tamkar yakashesa, bayan anyine MUJAHID yakira MUFIDA yafad'amata, farinciki da tsintsar murna baya misaltuwa agun MUFIDA nantake takira number d'in Amira, tana d'agawa nan taita tsokanarta suna dariya daga bisani ta tayata murna sosai, sunjima suna fira daga bisani sukai sallama,,,"....

Kwanan MUJAHID uku a Nigeria sannan yadawo gida BAGDAAZ, koda yadawo saiya tadda MUFIDA na zazzabi, cikin kulawa ya zauna sannan yad'orata kan cinyoyinsa, tallafo fuskarta yai saiyaji jikinta yai zafi sosai, kallonta yai sannan yace "my only one meke damunki ne?" dakyar tabud'e idanuwanta sannan tace "najima sosai lokaci bayan lokaci zazzabi yana tasoman saidai danasha magani yake kwantawa to yanzuma dai nasha magani" ganin yanda takeyi alamar tanajin zazzabin sosai yasa yakwantar da'ita sannan shima yakwanta a bayanta,, hanunsa tarik'o 'daya tadora kan cikinta sannan takallesa tace "habiby tin bayanda nai bari bansake ganin period dinaba kuma nasan banida ciki amma kuma abun mamaki wani lokacin idan na kwanta sainaji abu yanaman motsi aciki nidai habiby ka kaini asibiti inajin tsoro" murmushi yai yashafa fuskarta sannan yak'ara matsota acikin jikinsa yace "karki damu my only one insha Allah bawata matsala bace gobe zankira doctur Aysha tazo saitadubaki kinji ko" saitai murmushi tace to,,,"....

_______________

Washe gari kuwa kamin yafita office yakira doctur Aysha d'in tazo nan tafara yiwa MUFIDA y'an tambayoyi tana bata amsa, bayan tagama sannan tamata y'an gwaje gwaje, abunda dai doctur ke tsammani shine yake tabbata, murmushi sukaga doctur d'in nayi, bayan tagama sannan tacewa MUJAHID tanaso suje hospital nasu domin tayiwa MUFIDA wani babban gwaji wanda zai tabbatar mata da abunda take tinani,,,....

MUJAHID kuwa baiyi musuba yace MUFIDA tashirya nantashirya suka shiga mota suka wuce, bayan sun isa saita d'ora MUFIDA kan wani gado acikin babban dakinsa sukeyiwa mata masu ciki awo, na'urori takunna sannan tad'ora wani abu akan cikin MUFIDA nantake saiga d'a baby ya bayyana a naura kwance acikin mahaifar MUFIDA, tsintsar mamakine ya bayyana a fuskokinsu wanda yasaka MUJAHID yakasayin shuru saida yai tambaya, acikin harshen larabci yace "doctur ya akayi wannan rikitaccen al'amari yafaru mai cike da ban mamaki da al'ajabi" murmushi likitar tai sannan ta zauna tafara masu bayani "sau dayawa irin waennan matsalolin suna faruwa wanda idan likita baiyi kwakkwaran bayaniba hakan na'iya zama matsala atsakanin ma'auratan biyu, lokacinda matsalar tafaru cikin bai zubeba tadaiyi zubar jinine sannan suma likitocin basuyi kyakkyawan bincikeba koda yake irin wannan matsalar bakowanne likitane ke iya magancetaba saboda haka dai babyn ku bai bareba yana nan saidai yana buk'atar kulawa sosai" wani irin farincikene yarufesu sai aka rasa wanda zai fara magana acikinsu dik sai dariya kawai suke suna fara'a,,,....

MUJAHID ne yace "mungode sosai doctur amma yanzu watansa nawane" saida taduba tamata awo sannan tace "yanzu watansa bakwa ne da kwana hud'u" yai murmushi, nandai sukamata godiya yabata kudin aikinta sannan yad'akko MUFIDA suka wuce gida,, ranar wuni sukai acikin tsintsar farinciki musamman MUFIDA, tindaga wannan lokaci MUJAHID yad'ora daga inda yatsaya na bama MUFIDA kulawa ta musamman yanzuma saiyafi da d'in dan yanzu aikin komai yahanatayi saidai shi yamata kokuma tasaka hadimai sumata itakuwa ma batason hakan saitakejin dikta takura ba dad'i amma dole take hak'ura saboda MUJAHID yace a,a,,,"....

***** *****

Rayuwa tacigaba da tafiya inda MUFIDA da MUJAHID ke rainon cikinsu cikin kulawa ta musamman yanzu yashiga wata takwas yaturo fiyeda da yafito kuma saiyamata kyau sosai,,,....

Saura sati 'daya afara azimi MUJAHID yazowa MUFIDA da daddadan albishir sarki yace zasuje suyi umrah atare dashi da ummi, MUFIDA taji dad'i sosai nantaita yiwa sarki kyakkyawar addua saidai dayace da ummi zaaje sai murnarta taragu har MUJAHID yafahimci hakan a fuskarta,,,.....

Saura kwana uku afara azimi jirginsu yad'aga izuwa Saudi Arabia domin gudanarda UMRAH............

*kumin afuwa najina shuru kwana biyu NEPA namuce tasami matsala shys amma yanzukam komai normal insha Allah*



#/Vote
#/Share
#/Comment

'''AUFANA for life '''
*I.W.A*🖋
_*TSINTACCIYAR MAGE.....*_🌷
_a true love story_


_*BY~AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183_


® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚


_*Page 71/72*_
_Not Edited_


_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_

*****2pm dot jirginsu yasauka k'asa mai tsarki, suna sakkowa dakaru sukazo da dalla dallan motoci suka d'aukesu izuwa masauki, kasamcewar sarki babban mutum mai gudanarda gaskiya wanda aka sansa da tausayi dakuma son talakawansa, girmansa dana kujerarsa yasa kowa ke girmamasa kuma yake martabasa data kujerarsa hakan yasa dik kasarda yaje a yankin arab's ake bashi girma ake martabasa sosai,,,"....


Kai tsaye wani k'ayatacaccen gida aka kaisu mai d'auke da part uku sai sarki da ummi suka shiga d'aya MUJAHID kuma da MUFIDA sukashiga d'aya 'dayan kuma a rufe yake, suna isa MUFIDA tawuce toilet tasakarwa kanta ruwa tai wanka sannan tafito, kasamcewar a gajiye take yasa wata gown kawai tasaka tabi lafiyan gadon kankace me har bacci yai awon agaba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login