Showing 1 words to 3000 words out of 86608 words

Chapter 1 - DIDDIGAR ƘAYA COMPLT Hausa novel

21 Aug 2024

18401

DIDDIGAR ƘAYA
(Mai Wuyar Tsincewa)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*

*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
And Now..
*Diddigar ƙaya... Paid*

*Shimfiɗa*

*PAID BOOK*

ƊANƊANO

**Assalamu Alaikum warahmatullah, tadaaaa ga Gureenjo da sabon littafi,salo,labari me kama zuciya.. Ba zan ce wadda baku taɓa gani ba sede in ce ya sha bam-bam da wadda kuka saba gani, Mallaki naki tun kan free pages su ƙare ki sha karatu cikin kwanciyar hankali🥰**


Wani mahaukacin gigitaccen Marin da yake barazanar ɗauke mata ji da gani ya sauke mata, wadda seda ta kai ƙasa dafe da kuncinta hawaye na aikin ambaliya kaman an buɗe lalataccen famfo bisa saman fuskanta.

"Rufe min baki! Shashasha,munafuka,marar hankali... Har kina Tunanin akwai wani banzan dalilinki da ze hana wannan ɗaurin auren? Ke har kina da bakin ja da wannan auren? Wato so kike ki nunawa duniya cewa ya tabbata ke ɗin tantiriyar marar kunya ce ko? Toh bari ki ji in faɗa miki ko da aljani ne be isa hana wannan aure ba, idan har ba shine ya zo yace ya fasa ba kin yi kaɗan ki hana wannan aure!"

Cikin matsanancin kuka me taɓa zuciya wadda be daaɗa shi me sauraron da ƙasa ba don ko a jikinshi ta fara cewa
"Na yarda baba Alhj....a ɗaura aurena jibi, na yarda ka zaɓa min miji a ko ina...! Ko yaya yake... Ko mai talauci ko nakasarsa,komai tsufa ko yarantarsa..! Komai fari ko baƙin halin sa zan zauna dashi akan da ku Haɗa aurena da Wannan azzalumin. Don Allah Baba ka taimakeni.."
Ta karashe da kuka sossai har tana shiɗewa.

Wani mugun kallo ya watsa mata yace
"ko mutuwa zaki yi se an ɗaura aurenki a jibi Da FAIZAN! Kuma ko me ze miki se kin zauna dashi wawuya, butulu baki isa kin sa na yi jayayya da yayana akan abunda yake taimakona ze yi ba! Na tabbatar shi karan kanshi Faizan ɗin ba son auren tantiyar ƴar iska irin ki yake ba..!"

Wani irin karyayyen kallo take yiwa mahaifin nata, kai tsaye yake kiranta ƴar iska a gaban idanunta, wani irin kuka me cin rai take yi ba laifin kowa bane laifin su ne iyayen nata, su suka jefa ta duk wani rayuwa da take ciki a yanzu amma taya zasu kasa yi mata adalci su Haɗa ta da wadda kap duniya babu wadda ta tsana irin shi? Wani irin zama zasu yi? Shima fa ya tsane ta fiye da yadda ita take tsanar shi.

Da gudu ta miƙe ta fice tana me tsananta kukanta, ba tare da ta damu da dumbin jama'ar da suka taru a gidan don sheda wannan mummunar kaddarar baƙin auren ba kaman yadda ta sa mishi suna, a kan cinyar mahaifiyarta ta zube tana kuka a ruɗe

"Ammi! Baba Alhj basa ƙaunata Ammi, Ammi don Allah kiyi wani abu kar su kasheni tun kwanana be ƙare ba! Ammi wallahi na tsane sa Ammi bana sonsa bana ƙaunarsa, ki tausaya min Ammi..!"
Shafa kanta Ammin take cikin baƙin cikin da yake daskare bisa zuciyarta, in akwai wadda ta tsana a rayuwar nan To mahaifiyar Faizan da Mahaifinshi me ze sa komai na rayuwarta da ahalinta se da umarnin su za'a aiwatar?

Allah kaɗai ya san irin zaman da suke yanzu da mai gidanta duk saboda su, me yasa ne ita bata da ƴanci a nata gidan da mijinta? Me suka fi su? Kuɗi ko suna? Me yasa Sulaiman a ko yaushe umarnin Prof shine gaba da na kowa? Ina soyayyar da Jaddah ke ikirarin tana yiwa Fauziyya ɗin?

"Fauziyya kiyi haƙuri, duk yadda zan yi wurin ganin na hana aiwatuwar wannan aure na yi sede babu nasara sakamakon hakan ma aurena rawa yake, ki daure zuciyarki ki bari ayi auren amma ba zan taɓa yi miki dole ki zauna ko kiyi biyayya ba... Wannan karo ma Aisha tayi nasara a kaina"

Sakin Ammi tayi ta sake mikewa ta fice da gudu, idanunta a rufe suke mafita kawai take nema, sashen Jaddah ta shiga a gigice Sam bata lura da mutanen da suke wurin ba, ta fara cewa

"Zan kashe kaina! Wallahi tallahi zan kashe kaina.... Duk ranar da aka yi Adu'ar aurena da Wannan azzalumin ina me rantsuwa zan mutu! Sede a kai gawata ɗakin sa.. Ku gafarceni Jaddah..."

Natsatsiyar muryar da take bayyana fushi da wani irin ciwo ne ta ratsa kunnuwanta, irin muryannan na no nonsense, muryar da ta tsana fiye da na kowa da komai a duniya, sautin da take jinshi kaman saukar aradu a kunnuwanta da ma gangar jikinta...

"Ka ji ba Baba? Ban taɓa yi muku jayayya ba a rayuwata, ban taɓa sauya fari zuwa baƙi ba idan har ku kuka furta Cewar farin ne, sau ɗaya dae ku dubi Allah karku tilastani yin abunda ba zan iya ba, zan iya shiga wuta aka yi min dole wannan aure saboda ba zan iya adalci tsakanin ta da Fatima ba, above all that baba bana fatan Haɗa jini da fasiƙa...! Idan har aka ɗaura wannan aure an cutar da ni da iyalina..."
Sauƙar gigitaccen mari ne ya hana shi ƙarasawa.

Jajayen idanunshi ya ɗago ya zuba mata na mintuna ba tare da ya iya cewa komai ba, karon farko da wayaunshi kenan da mahaifiyarshi ta sa hannu a kanshi duk akan wannan annoban, miƙewa yayi a zuciye ya fice kaman kububuwa...

"Menene hujjar ki na ƙin wannan aure?"
Jaddah ta jefa mata tambayar karon farko tana kallonta.

Shiru tayi tana kuka sossai don Kalmar fasiƙa da ya jefe ta dashi har tsakiyar zuciyarta take jin zafi da raɗaɗin shi.

"Baki da hujja? To fitar min daga ɗaki"
Kallon ban yarda Jaddahta bace a zaune anan take jefa mata kan ta yi baya baya ta fice da sauri tana kuka.

Dafe kai Jaddah tayi cikin jin ciwon wannan abubuwa da suke faruwa a cikin zuri'ar ta, idanunta ta kai kanshi yayi shiru cikin nazari da tunani, chan ya ɗago ya kalli Jaddah cikin girmamawa yace
"kwarai raina a ɓace yake kuma a ƙuntace hajiya! Ban taɓa yin abunda na muzanta ba irin wannan kab tarihina zuwa matsayin da na taka a yanzu, na kan Haɗa auren maƙota ma su karɓa cikin farin ciki bare na ƴaƴan cikina.."

Shiru ya ɗan yi kan ya kalli Mammi yace
"Ki sanar da ɗanki daga yanzu har a ɗaura auren nan idan na saƙe jin muryarsa da sunan mujadala da auren nan na yafesa har Abada!"

A razane duk suke kallon shi, kwarai ranshi ya ɓaci da wannan lamarin tunda har Baba prof ze iya furta kalma irin wannan.

Miƙewa yayi ya fice ba tare da ya sake cewa komai ba, a maimaikon yayi sashensa se ya nufi sashen ƙaninsa Sulaiman, sama sama yake amsa sannu da matan da suke daga farfajiyar har zuwa harabar na gidan Sulaiman suke mishi har ya isa zuwa parlornshi, da sauri Baba Alhaji da yake shirin cin abinci ya miƙe tsaye yana furta

"Yaya! Ai da ko a waya ka ƙirani ba se ka zo da kanka ba!"

Daga tsayen hannayenshi goye a baya yace cikin natsuwarsa na tsantsan ilimin addini
"Ba buƙatar hakan Sulaiman saboda ina so ka san saƙon me muhimmanci ne, ina so ka sanar da Fauziyya idan har kai ka haifeta na sake jin magana makamancin wadda ta zo dashi yanzu sashen hajiya ka yafeta wa duniya har Abada!"

Da sauri ya ɗaga kai ya kalli yayan nashi zuciyarshi na bugawa, dukda maganan yayi mishi tsauri sede zasu iya kaiwa ko wani mataki domin ganin mutuncinsu be zube ba kaman yadda ƴar wajenshi ta so zubarwa, mutuncin da tun kan a auri mahaifiyarta yake wanzuwa a idanun mutane..

"Kayi hakuri yaya in shaa Allah hakan ba ze sake faruwa ba"

"Allah ya sa!"
Baba prof ya faɗa yana Juyawa ya fice a lokaci ɗaya yana amsa saida safen da Baba Alhajin ke yi mai.

Ya jima bayan ya fita harabar gidan yana safa da marwa, kan ya nufi kofarshi bayan ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi...!


***Shin ya kuka gani? Menene hasashenku kan wannan sabon littafi? Su waye ne waennan ahali? Me yake faruwa a cikin wannan gida? Menene musababbin tsanar da suke yiwa juna? Meyasa kowa ya buɗe baki da kalmar fasiƙa yake jefan Fauxa? Wani irin zama zasu yi bayan Haɗa Wuta da Auduga inuwa guda? Akwai fa'ida a wannan aure ko babu? Za'a daura ko kuwa?***

Pls waenda suka fara biya should dm me sbd in saka su paid group.

One more thing comment matters pls, ba zan zauna ina wasting energy wurin typing ku ki yin comment in ji daaɗi ba, so show some love with ur wonderful comments🙏🥰


Duk ku biyo ni a cikin wannan littafi nawa me suna DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa)
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank

Karku sake a baku labari.


🖤Gureenjoh🖤

DIDDIGAR ƘAYA...
(Mai Wuyar Tsincewa)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
And Now..
*Diddigar ƙaya... Paid*

*Shafi Na Ɗaya*

*PAID BOOK*

ƊANƊANO

**WANNAN KARO COMMENTS ƊINKU NA DA MATUKAR MUHIMMANCI SOSSAI***

Idanunta da gabaɗaya suka jeme suka kumbure suntum har suka sauya mata kamanni ta sake saukewa kan agogon ɗakin karo na ba adadi, hasken dake ratsowa daga window ɗin ya bata damar kallon lokacin, karfe 12:30 na dare yunƙurawa tayi ta miƙe zaune tana jin kanta na mata wani irin nauyi kaman an ɗaura mata dutsen dala.

Idanunta ta kai kan handbag ɗinta cikin tsananin nazari da damuwa kan ta janyoshi ta zaro wani farin gora ta gimtse cikin hannunta, ɗakin su ta bi da Kallo, ɗakin dake ɗauke da rabi da kwata daga cikin tarihin rayuwarta, duk cikin waenda suke kwance babu wacce zata ce sun yi kusa kusa duk en uwan nesa ne waenda suka zo bukin nan da bata taɓa hasashen yiwuwarsa ba seda taga wankin hula na shirin kai ta dare, kai tsaye zata iya cewa biyar daga cikin ahalinta na ɗakin suna wurin mahaifiyarsu da itama tun zancen ya tashi basu da sukuni.

Ƴar uwarta kuma da suke ciki ɗaya ta ƙaura wa sashen sbd rashin son hayaniyarta, cikin dauriya ta miƙe tsaye jiri na shirin yar da ita, a saɗaɗe ta nufi kofa ta buɗe ta fice, babu kowa a tsakar gidan sede tana iya kallon haske daga sashen mahaifinta alamun idanunshi biyu har yanzu, hannunta har rawa yake wurin cire sakatar ƙaramin gate na sashen nasu ta fice tsakar babban gidan nasu dake ɗauke da sashuka masu ɗan dama.

Chan baya inda haske be cika yawa ba ta je ta tsaya idanunta zube bisa farin robar da aka rubuta sniper da zanen ƙwari a jiki, hawaye masu tsananin zafi ne suka saukar mata maganganun mahaifinta na ƙarshe gareta masu kaifi da ƙuna na amsa kuwwa a kunnuwanta kaman yanzu yake yin su...

"Fauziyya ban san cewa kin tabbata marar kunya fitsararra ba seda kika tsaya gaban su jadda da yaya kina ikirarin kashe kanki saboda abinda yake gata ze miki, kina Tunanin ko wasu iyaye ne zasu yardar ma ɗan su auren mace irinki? Ko ni.. (Ya nuna kanshi da hannu) da Farhan ze zo min da zancen auren mace me makamancin halayenki Fauziyya ina miki rantsuwa ba zan amintar mishi ba, in har kin haifu don Allah ki kashe kan naki in aka ɗaura, jaliha marar tunani.. Daga sadda kika kashe kanki daga sannan ni kuma na zare duk wata alaqa tsakanina dake, zan tsinewa gawarki tun kan a binneki, wanka da sallah ba de a gidana ba don ba zan taɓa yiwa kafira Adu'a ba, kaman yadda kika san hukuncin duk wadda ya kashe kanshi ya mutu kafiri... Don Allah karki faasa, fice ki bani wuri...!"

Kuka take yi sossai tana jin yadda zuciyarta ke mata ciwo, meyasa kowa ya gagara fahimtarta? Meyasa se ita? Hannayenta na rawa ta buɗe roban sniper ɗin ta nufi bakinta, duka jikinta na mugun rawa gwara ta mutu ta bar musu duniyan da wannan bakin cikin, motsin da taji a bayanta yasa tayi saurin juyowa se idanunsu suka sarƙe cikin na juna.

Hannunshi zube cikin wandon Fararen pajamas dake jikinshi masu sulbi da suka fitar da kirarsa na kakkarfan namiji me zaati da charisma, idanunshi masu kaifi ya fara saukewa kan hannunta kan ya ɗago ya tsura mata su na mintuna ya ɗaukesu tare da jan tsiririn tsaki, cikin takunshi na zaratan maza ya nufo ta har kaman ze goge ta kan ya ɗan ja kuta yace cikin muryarsa me rikitar da mata..

"Mutuwa se ta fi miki sauƙi da aurena! Rayuwar ƙabari se ta fi miki jin daaɗi idan kika mutu kafira da irin rayuwar da na tanadar miki muddin kika sake aka shafa Adu'ar aurena dake! Faizan be yi zina ba da yardar Allah ba ze taɓa auren mazinaciya ba, ki saka wannan a bayan thick lunatic skull na ki..."
Yana kai nan ya tsirtar da miyau ya wuce abunshi ba tare da ko waiwaye ba.

Fitinan da Fatima ta dasa mishi kaɗai ya ishe shi, idan ta mutu se ya fi kowa farin ciki wallahi, ihunta yaji hakan kuma be saka shi waiwayawa ba har ya shige sashen samarin gidan inda nan ɗakin shi yake tun kan yayi aure har yanzu.

A kan gwiwowinta ta zube tana kuka me cin zuciya wani irin jarababbiyar kaddara ce wannan? Wadda ake yi mata murnan samun shi kenan a matsayin miji? Wadda shine ya zama duk wani silar taɓarɓarewar farin cikinta, idan da be tsoma kanshi cikin tsarin rayuwarta ba da duk hakan bata faru ba..

Da sauri ta sake kai roban bakinta tana shirin apawa taji an yi chilli da robar, da sauri ta ɗago se taji sauƙan mari bisa fuskanta dake suntume already.

"Fauziyya??? Innalillahi wainna ilahi rajiun..!"
Ko bata ɗago ba ta san jadda ce daga muryar, fusgo ta tayi suka zagaya zuwa kofan sashenta suka shiga, tsallake mutanen dake parlorn suka yi suka wuce kofar ɗakin Fauza dake sashen wadda shima mutanen su na Maiduguri ne ciki suka shiga ɗakin jaddar, kan gado ta ajiye ta tace

"Fauziyya kina da hankali kuwa? Meyasa kike shirin kashemu tun kwanakin mu be ƙare ba? Ki bar mu muji da abu ɗaya mana! Kin kuwa san hukuncin ki daga sadda kika aikata abunda kika aikata kuwa? Wuta fa! Kin kuwa san menene dawwama a wuta na har Abada? Haba Fauziyya! Ina iliminki? Wani bala'i ne yafi na jefa kai ga halaka? Akan auren ɗan uwanki saboda laifin da ke kika janyo?"

Cikin kuka sossai take girgiza kai hannayenta gabaɗaya a kanta duniyar gabaɗaya yayi mata zafi ji take kaman an rufe ta ne a cikin kurkuku me cike da tsananin duhu da zafi, bata iya magana ba Jaddah ta sake cewa

"ba don naji ihun ki na fita ba da yanzu ba wannan maganan ake ba Fauziyya waye ya kawo miki wannan abu? Taya ya zo hannunki?"

Seda ta daka mata tsawa kan ta faɗa cikin dasashiyar muryarta..

"Sakinah!"

"Yanzu waennan ƙawayen arziki kenan Fauziyya?"
Sassauta muryarta tayi tace

"Fauziyya duk abubuwan nan da suke faruwa ki saka a Ranki Allah ne ya tsara hakan ba wai yin mu ba, ina me tabbatar miki kuma Faizan shine alkhairinki in har kinga an ɗaura auren nan to tun farko rubutacce ne daga sama! Wlh idan na ganki cikin wannan hali hankalina tashi yake"

Tana girgiza kai saboda babu wadda ze iya hango abunda take hangowa ta fara cewa
"Meyasa se Faizan? Meyasa Jaddah? Don Allah ki taimakeni Jadda, aure fa ba wai ana yinshi don gobe a fito bane a'a, ana so in ka yi shi ku kasance abadan abada har se mutuwa ta raba, taya kuke hango min farin ciki da zama na har abada daga Maƙiyi na wadda burinshi ko da yaushe ya ga hawaye bisa idanuna? Mutumin da be taɓa ƙaunata ko da na second guda ba, Jaddah idan kuka hana ni mutuwa tabbas zan gudu!"

Bakinta ta buge cikin faɗa tace
"Haba Fauziyya ke kam meyasa kike da taurin kai ne Haka? Auren nan se an ɗaura tunda har iyayenku sun riga sun zartar, tun farko wa ya janyo? A tarbiyarki ban taɓa Tunanin zaki aikata abunda kika aikata ba, gwara ki sakawa zuciyarki salama ki amshi wannan aure don ko gawarki ne na yarda a kai gidan Faizan da irin watsewar da zaki zauna ki mana, kuma babu uban da ze amince da aurenki in har yayi bincike akanki gwara tun wuri mu rufawa kanmu asiri, daga yanzu in kara ganinki ko da a kofar ɗakin nan ne ki gani..."

Tana kai nan ta hau gado ta kwanta tare da kashe wuta, anan Fauza ta cigaba da zama lokaci lokaci tana share hawaye zuciyarta baƙi kirin har bata san sadda bacci ya sureta ba kanta bakin gado tana zaune daga ƙasa.

Sam bata san an yi asuba ba don Jaddah bata tashe ta ba sanin bata sallah, don seda babanta yayi mata har gwajin ciki da HIV kan ya saduda da hana Faizan aurenta Dukda iyayenshi basu damu da duk wannan ba.

Hayaniyar da take ji daga tsakar gidan da salati ya sakata farkawa Sam bata so tashi ba amma jin hayaniyar kaman tayi yawa ne ya sakata mikewa tana yamutsa fuskanta da ya jeme ya rame saboda tashin hankali ta nufi waje, a iyakar sanin ta in har kaji ana hayaniya a gidan Baba Prof to da Fauziyya ne yau kuma to me ke faruwa?

Daga kofar gate na Jaddah ta ja ta tsaya tana kallon matan dake tsakar gidan wasu kuma sun fi yawa a kofar sashensu, tana shirin Juyawa don bata ga abunda ake ba se ta hangi tahowarsa da Fatima a hannu gabaɗayanshi a rikice kana ganin fuskanshi ka san al'amarin dake nufo shi baya kaunar ta ko na miskala zarratin, da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login