Showing 54001 words to 57000 words out of 77995 words

Chapter 19 - karayar arxiki COMPLETE

12 Jul 2024

9238

Abbah dai yayi shiru, dan tsorone fal ransa, idanfa Umar baisamu kud'innanba dolene shizai nemosu, tundadai mufida diyar cikinsace, atsarima shiya halatta yayimata kayan d'akin. Wani haushin Abubakarne ya kuma tunik'e zuciyarsa.
Agefe kuma dariya na cin zuciyar inna da Harris, dan sunsan ya Umar yanayin pretending ne kawai.
Rafi'a da mufida kam sai ballama ya Abubakar harara sukeyi, karma mufida taji labari, dan zuciyarta akuntace take, wai itace za'akai gidan miji da kayan gado nawajen halladu kafinta?.
Ita bamatasan yanda ya Abubakar ya tsanetaba. Tafashe dakuka Wanda yadawo da hankalin kowa akanta, cikin kuka ta ce, "Abba aidai kai kanada kud'in yimini, kowadai yasan halin da ya Umar yake aciki? Inhar ba'a tausaya masaba to ai ba'a tsine masaba. Niko wlhy Indai kayan wajen halladu kafinta za'a kaini dashi to na hak'ura da auren, ta tashi fuuuuu tafita tana kuka.
Babu wanda ya iya cewa komai, daga nan ma suma taron ya watse.
Ya Umar ma gidansa yakoma yay kwanciyarsa, dama kansa namasa ciwo.
Asma'u kam tana gidan bikin, bama tasan wainar da'ake toyawaba.
Sudai makwafta suka hau gyara abinda yasamu, masu gulma nayi masu tu'ajjibi nayi, harda masu dariyar mugunta dan kowa yasan mugun halin mama a anguwar.
Zuwa bayan isha'i aka kammala miyar dataji uban alayyahu ko kayan miyar ba'a gani saboda yawan alayyahun.
Tun adaren aka kusa shanye rabin miyar ma, mama tamkar tayi hauka dan bak'in ciki, tarasa inda zata tsoma kanta taji sanyi, gashi batada ko sisi, dan bata ta6a tunani ajiye wasu kud'iba saboda aurennan, tasaki jiki komai Abubakar zaiyi.
Abba madai hankalinsa atashe yake, dukda shida yanada 'yan kud'insa amma mak'o da ganin k'yashi yahanashi fiddosu afita kunya.

Adaren mama da inna sunkira ya Umar yafi sau hamshin-hamsin amma yak'i yad'aga, hakama Abba yakirashi yafi ak'irga amma bai d'agaba.
Hankalinsu dukya tashi, musamman ma inna.
Ita duk zatonta ya Umar yayi pretending ne, fitar dayayi zaije yayo sayayyane, amma har shad'ayan dare babushi babu alamarsa.
Ya Umar kam yana kwance agidansa, kuma duk kiran dasuka masa yana kallo ya sharesu.
Duk kiran daya shigo saiyayi murmushi sannan ya ce, "inna mama Abba kufayi hak'u wannan ba Umar d'in dakuka Sani bane, na yanzu ya canja, yasan dad'in dukiya shima, ni babu abinda zan muku, koma wajen d'aurin auren babu mai ganina.
Wannan zai zamemuku izina aii.
Inna ki gafarceni wannan karon kema bazan saurarekiba.
Dayagaji dajin wringing d'in wayar saikawai yamaida wayar salient........



*_washe gari_*
Har kusan 11 babu wani canji agidan, mutane sun sami abun tsogumi sai gulma sukeyi, harda cikin 'yan uwan mama danasu inna.
Zuwa yanzu mama tayi lak'e-lak'e, tayi kuka da nadama har babu iyaka, tasandai yau kunya zasu shatane bata wasaba kam.
Amaryama kuka takeyi rurus, ko wanka tak'i yarda tayima, ta tubure akan tafasa aurenma gaba d'aya, anyi lallashin duniya tak'i sauraren kowa.
Har shabiyu babu wani bayani, gidakam haryama fara d'inkewa da mutane, wasuma badan ALLAH sukazoba, sunzo ganin kwakwafne tunda tun ajiya labari yafara zaga anguwar.
Mutane na tsaye tsirko-cirko akan mama data suma. Dan tashin hankali, ko abincin daza'aci agidan babu to, d'an Wanda Ya Abubakar yakawo ana gama dafawa tun'a gindin murhu mutane suka kwasheshi. Wannan 6acin ran yasaka mama zubewa.

Ana cikin haka sai akaji k'ugin motoci ak'ofar gida. Kafin mutane suyi wani yunk'uri anfara shigowa da manya-manyan kuloli na abinci. gefe kuma ana shigiwa da kayan gado na gani na fad'a.
Ai sai mama ta tashi tashiga jerin 'yan kallo.
Saida aka shigo da kula kusan d'ari ta abinci, gakuma kayan gado na nunawa a sa'a, saikuma ga kayan kichin suma akwalayensu.
Inna dai data kasa hak'uri saida tamatsa tana tambayarsu waya aikosu?............





Kuyi manage da wannan.





*_(((S)))........2017_*
*_I Love you all_*
[12/28/2017, 6:35 PM] ~πŸ‡© ' πŸ‡― πŸ‡¦ πŸ‡· πŸ‡­βœ: πŸ‘©πŸ»β€πŸ’».........



πŸ’Ž *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* πŸ’Ž


*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*


*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_


*_NIKA'DAIπŸ‘ŒπŸΌ WRITER ASSO.....😜_*

*_page→59-60_*


..........Kai daga ina? Waya aikoku kuma?.
Wani a cikin masu sauke kwalayen ya ce, "Alhaji Umar ne.
Kowa baki ya hangame sama dan mamaki, tuni fuskar mama da inna ta washe, mama kukan farinciki takeyi sa6anin da datakeyin na bak'inciki.
Sunan tsaitsaye tamkar an dasasu saiga ya Umar yashigo, sanye yake cikin kananun kaya, yayi k'yau sosai, kwarjininsa da k'yawun haibarsa sunk'ara bayyana saboda gyaran fuska dayayi.
Mama tak'araso da sauri ta rungume ya Umar. Shima dai yau ya kar6i Maman tasa 100%, kukan dad'i takeyi, haka shimad'in hawayene kebin kumatunsa.
Innace tamusu magana sannan suka koma ciki.

Acan k'uryar d'akin Abba ya Umar ya ce, " mama inna dan ALLAH kugafarceni saboda rashin d'aukar wayarku danayi jiya.
Wlhy mun yafe maka, mun yafe maka umaru, mamace take maganar a cikin kuka.
Inna ma ta ce, "tayafe masa."
Ana haka Abba ya iskesu a d'akin, cike da farinciki ya rungume ya Umar. albarkadai yashata har babu adadi.
Daga nan hidimar biki tacigaba da gudana cikin farin ciki, bakin mak'iya, masu gulma da dariya kuma anrufeshi ruf🀐.
Mufida kam jitayi aduk duniya batada kamar ya Umar.
And'aura aure da k'arfe 2:30pm.
Ango yayi shar dashi, sai washe baki yakeyi yana gaisawa da jama'a.
Hakama amarya mufida a cikin gida, tayi k'yau harta gaji, dangi da k'awaye suna zagaye da ita.
Mama da inna ma dai suna cikin farin ciki mara musali.
Hakama Abba ba'a barsa abayaba, shima yau ya aurar da d'iyar farko a cikin 'ya'yansa.
Ya Abubakar kam bak'aramar k'ullatar ya Umar yayi ba, ko'a awajen d'aurin aure da sun had'a ido saiya d'auke kansa.
Shidai ya Umar saidai yayi murmushi kawai.

Zuwa yamma taro yarage na mata a cikin gida.
Can na hango muku Asma'u itama taci kwalliyarta cikin wani ubansun less pink da ratsin milk, bak'aramin k'yau tayiba gsky, tana tareda matar yazeed da Anty Saddiqa matar muktar.
Zuwa dare aka mik'a amarya d'akinta dayasha Jere da su Anty sa'a da Anty Saratu, saikuma wasu a cikin danginsu na uwa dana uba dasuka biyosu, tun wajen k'arfe d'aya akayi, dukda dai sai yamma lik'is suka gama, ko d'aurin auren basu halartaba.
6angaren abinci kuwa babu Matsala, anci har an barsa, komai ya wadatar da jama'a, dan abincine kala-kala aka kawo, tundaga jalof d'in shinkafa, fankasu, waina, tuwo, gurasa, alala, kai komaidai yawadata, ga ruwa shima, hakama lemuka kowa yasha iya gwargwadon iko.
Bayan ankai amarya akace sushirya za'a dinner da abokan Ango suka shirya.
Su Asma'u anata shiri saitaji wayarta na wringing, d'agawa tayi da hanzari dan ganin ya Umar.
Ko amsa sallamarta baiyiba ya ce, "kin shirya?."
Eh, tafad'a cikin rawar kai.
Cikin dariyar mugunta ya Umar ya ce, "kisameni awaje to."
Aida hanzarinta ta kammala shirinta tafito. Waige-waige taketayi dason hangoshi.
d'it-dit taji motar kusada ita ana mata horn.
Kallon motar tayi saita hango ya Umar aciki. Idanu tad'an fiddo waje dan mamaki, ko'a ina yasamo mota?.
Da wannan tunanin tak'arasa inda yake.
Zagayo mana yafad'a tana bud'e mata k'ofar gefensa.
Babu musu tazagaya ta Shiga ta zauna, wani k'amshin dad'i da sanyi suka ratsata, ta shak'a talumshe idanunta.
Duk ya Umar yana kallonta, dariya kuma nacinsa azuciya, ga wani k'yau da kwalliyar tata tamasa.
d'agowa tayi tana kallonsa, ya Fharuk wannan motarfa?.
Gira yad'age sama yana kallonta da ido d'aya, ta aroce yafad'a cikin wani salon magana.
Amma fa motar tahad'u wlhy cewar Asma'u tana shashshafa kujerun motar na baya.
Saida yatada motar sannan ya ce, "kokinasone?."
Asma'u tarik'e ha6arta, ya Fharuk rufamin asiri, inani ina Mota? Nida ko keke ban iyabama.
'Yar dariya yayi yana k'ara dafe sitiyari dan harsun fara tafiya.
Kedai inhar kinaso kifad'a kawai?..
Tab indai maganar soce kam aii inaso, amma a ina zan samu? anan gizon ke sak'a aii.
Murmushi yayi kawai batareda ya ce, "da ita k'alaba.
Daga nan motar tayi shiru nawasu mintuna.
Wani gurin hutawa yakaita, yasa aka kawo musu abubuwan motsa baki, itadai Asma'u cikawai takeyi, amma hankalinta nacan wajen dinner, kad'an-kad'an saita kalli agogon hannunta.
Duk abinda takeyi idon ya Umar na kanta, amma saiya basar yanata danne-danne awayarsa.
Candai Asma'u takasa daurewa, tad'ago tana kallon ya Umar daketa murmushi yana latsa waya, dan hotuna yaketa mata batareda tasaniba, wajen yak'awatune da hasken lantarki tamkar rana. Itafa dabadan kar ace ta zura k'aryaba dasai tace ba'a 9ja sukeba.
Wajen babu hayaniyar, mutane ma d'ai-d'aine keta shawagi awajen, daka gansu kuma kasan masoyane, saidai asamu banbanci namasu aure da masu zuwa sa6on ALLAH.
ya Fharuk tara saurafa?.
batareda yad'agoba ya ce, "kingaji mutafi kenan?."
Bawai nagaji baneba, amma nasan yanzu anfara dinner d'in.
Fuskarsa yad'an yatsine, ad'age ya ce, "dinner kuma? A ina kenan?.
Sosai tawaro idanunta waje, saikuma ta kwa6e fuska, kai ya Umar kafasan za'aje dinner, kuma nazatama ka d'akkonine dan mutafi.
Kai! Shima yafad'a yanad'an zaro ido. Husna yaushe nacemiki wajen dinner zan kaikai? Nibammasan za'ayi dinner ba gsky.
Shiru tayi masa dan tak'ulu sosai, jitake tamkar tamakeshi dan haushi.
Dukda yakula dayanda tacika tayi fam dan haushi, saiya share, dariya yayi cikin zolaya ya ce, " dinner aii ta 'yammatace bawai cus irinkuba.
Baiyi zatoba saiyaga hawaye sun gangaro akumatunta, wai ita ya Umar kekira da cus!.
Tashi tayi zata bar wajen ya damk'o hannunta. Ta tirje tana fad'in nika sakeni, badai nice cus ba?.
Ina bafa dake nakeba, haba ma'una sorry yeee. Yafad'a yana jawota tafad'o saman cinyarsa, dukda mutsu-mutsun kwacewa datakeyi amma takasa, yaymata k'yak'yk'yawan rik'o, ganin zata tara masa mutane saikawai yafaraπŸ’‹ d'inta.
Muk'us kakeji Asma'u tayi shiru.
Dasalon soyayarsa da wayo irin nasa ya lalla6ata tahak'ura da zuwa dinner d'in.
Dama bayaso taje shiyyasa yaje ya d'akkota.
Sai wajen goma suka bar wajen.
Gida suka nufa, amma tun amota Asma'u tayi barci.
Koda suka isa gida saiya d'auketa cak yashiga da ita ciki.
Tayi matuk'ar gajiyane, dan duk yau batayi barciba, rabonta dashi tunna dare, tundaga sallar asuba batasake komawaba.
Da kansa yacanja mata kayanta zuwa nabarci, yayi mamakin dabata farkaba, dan yasan Asma'u batada nauyin barci. dukda yanatareda uzurinsa haka yahak'ura shima yay shirin barcin ya rungume matarsa suka lula duniyar barci..........



_______________________
A6angaren su Lubna kam an raba musu gadonsu, saboda matsawar dasu Safwan sukayi, ran momy ya6aci matuk'a, amma babu yanda zatayi tunda hak'k'insune.
Tunda akayi addu'ar arba'in suka addabi kowa, dole aka raba kowa yad'auki kasonsa.
Ba k'ananan kud'i da kaddarori suka samuba kuwa, dan mahaifinsu babu laifi yatara musu.
Hummm tunda kowa yakwashi kasonsa saiya kama alk'ibilar data dace dashi kuwa.
Babu Wanda yanemi Sana'a acikinsu kuwa. Dan basu iyaba, ba'a koya musuba, abinda suka Sani kawai shine sukashe kud'i komin yawansu, dasunzo dady zai basu wani. To yau babu dady, yatafi yabarsu cikin babban fili na gwagwarmaya, wato duniya.

Basu Lubna ba kawaiba, hattada mama karenta takeci babu babbaka, sunkoma rayuwarsu tamkar da, kamarma babu abinda yata6a zuciyarsu abaya.
Su Lubna kam aii likafa taci gaba itada Suhaima, murzar kud'insu sukeyi tamkar babu gobe. Sun sayi motoci na garari, hakama sitturu yanzu sai shigar dasuka gadama. To mom dake musu fad'a ada itama ayarta take shek'ewa ayanzu, tataka Wanda taso babu mai abin fad'a tunda tanada 'ya'yan banki masu magana da kowa.
Maganar aurema babu ita a ajandar rayuwarsu, daga bin club sai bin k'awayen banza da boy friends masu tatsesu cikin dabara.
Mom bata bincikar kowa akan dukiyarsa dan acewarta hankali yazoma kowa, idan ka6ata kaikasani, idan ka adanama nakane.
Safwan dayafi kowa rawar kai kam aii inasa-inasa ya had'a yabar k'asarma gaba d'aya. acewarsa yawuce da ajin zaman 9ja yanzu.
Ameer ne kawai zamu iya cewa ALLAH ya taimakesa, ya had'a shi da mace tagari, nuna masa tayi yaraba hannun jari kawai tundashi bai iya kasuwaba.
Dayake yana sonta saiyabi shawararta kuma taimasa amfani. Dama ko a bayan aurensu dataga tarbiyyarsa bata cikaba saita duk'ufa wajen gyarawa, dukda tasha hantara da wulak'anci awajensa hakan baisa tabariba saida taga yadawo hanya d'od'ar. To yanzu haka tanada tsohon ciki haihuwa yau ko gobe.
Lubna da Suhaima ne ke sakkowa daga saman benen gidansu suna taku d'ai-d'ai. Jikake kwas! Kwas!! Kwas!!! Takalmansu nabada sauti.
Ba mamaba hattada Amrah da Afrah dake zaune a falon saida suka d'ago suna kallonsu.
Sanye suke cikin matsatstsun kaya, wandone mai mannewa ajikin nan, sai wata 'Yar mitsilar riga wadda dukansu dazasuyi kwakwkwaran motsi duk sai anga cibiyoyinsu.
Lubna tad'an yane k'aramin gyale, amma Suhaima ko'a jikinta dan ko hula babu a kanta.
Suduka cingom ne abakinsu, kowa nata tauna k'as-k'as. Idan ka gansu basuda maraba da karuwaiπŸ˜₯.
Mom ta d'auke kanta cikin matuk'ar 6acinrai, amma batada damar musu magana.
Afrah da Amrah ne suka taso suna fad'in momy muma zamuje.
Lubna ta yatsine fuska tana harararsu, zakuje gidan ubanwa?!! Kujimin yara da d'aukar dala babu gammo.
Dallah kutashimin agaba kafin jikinku yay tsami.
Jiki a sanyaye Amrah da Afrah suka matsa baya.
Lubna da Suhaima suka d'agama mom dake zaune tamkar gunki tana kallonsu, hannu, mom bye...
Basu jira cewartaba suka fice, kowa motarsa yashiga yanufi inda zaije.
Amrah da Afrah kam dasuka fara wayo sosai, dan ayanzu haka shekarunsu takwas, gefe suka koma suka zauna, zuciyarsu cikeda sha'awar abinda sukaga momynsu da k'anwar tata sunayi.

Mom kam hawaye takeyi sosai, jitake mutuwar mijinta tadawo mata sabuwa fil yau.
Afrah da Amrah kam saisuka cigaba da wasansu hankali kwance........






*_duk naga sak'onninku na addu'a ga baba, ngd sosai ALLAH yabada ladan zuminci, masu kiranama ngd sosai wlhy. Kuyi hak'uri, wad'anda sukamin maganaba ta groups zasuga ban amsasuba, messages ne sukamin yawa ta PC wlhy, kunsan nakwana biyu bana online. Kumin afuwa duk naga messages naku INA godiya harbabu adadi 'yan uwana._*
Luv you so much allπŸ’‹

Bilyn Abdul d'inkuceπŸ‘ŒπŸΌ










*_(((S)))........2017_*
*_I love you aall_*
[12/30/2017, 4:54 PM] ~πŸ‡© ' πŸ‡― πŸ‡¦ πŸ‡· πŸ‡­βœ: πŸ‘©πŸ»β€πŸ’».........



πŸ’Ž *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* πŸ’Ž


*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*


*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_


*_NIKA'DAIπŸ‘ŒπŸΌ WRITER ASSO.....😜_*

*_page→61-62_*


..........A daddafe Asma'u tayi sallar asuba takuma zamewa akan abin sallah ta kwanta. Kafin ya Umar yadawo daga masallaci tuni barcinta yayi nisa awajen.
Kansa kawai ya jinjina yad'auketa cak yamaida kan katifa tareda zame mata hijjabin, shima barcin Yakoma.
Sai kusan goma suka tashi, Asma'u cema tafara tashi. a gaggauce ta afka kicin tana k'ok'arin had'a musu abin kari mai sauk'i.
Cikin 'yan mintuna kad'an kuwa ta kammala, sosai talura da yanda gidan yay datti amma takasa d'aukar tsintsiya tayi koda sharace. Wannan k'azantar data aureta a kwanakinnan tana damunta, tasan ya Fharuk ko kad'an bayason k'azanta. Dantasha ganin 6acinransa sanda yana tareda Lubna kafin ita kuma ya aureta.
Tana zaune afalo sai k'ulla wasik'ar jaki takeyi na yanda zata tashi tarage aikin. Motsin datajine abayanta yasakata juyawa, ya Umar sanye cikin wando dogo da vest yacire jallabiyar dayaje masallaci kenan.
Asma'u ta ce, "Yaya katashi?."
Bai bata amsaba, saidai bin ko'ina na falon yakeyi da kallo a yatsine.
Duk sai Asma'u tasha jinin jikinta.
fuskarsa da alamun 6acin rai, saidai kwarjininsa ya6oye kaso mafi tsoka a 6acin ran nasa. Husna wai wane sabon hali kikeson koya akan tsaftar gidannanne?.
Kallafa kigani, gida Yakima tamkar turken dabbobi, nifa banason k'azanta kuma kinsani sarai.
Sosai idanunta suka cikada kwalla, amma tayi jarumtar rik'esu......cikin rawar murya ta ce, "kayi hak'uri Yaya zan gyara, insha ALLAH bazan sakeba daga yau.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login