Showing 21001 words to 24000 words out of 77995 words
*↓*
*_hii Umar Fharuk_*
_Hummm abin mamaki da al'ajabi._
_hhhhh Umar nasan abinda zaku fara ambata kenan kaida matsiyatan danginka da Mayyar matarka a yayin da kuka shigo kangon gidanka kuka tarar babu komai a cikinsa, hhhhhh to kasan wacece ta shirya wad'annan abubuwan mamakin da al'ajabi kuwa?. nice nan Lubna, nayi hakane saboda bazan ta6a barin kacigaba da morar wani Abu daga dukiyarmuba, bazan ta6a barin wannan shegiyar matar taka jin dad'in rayuwa da kaiba wlhy Umar, nice nan na kwashe komai nagidannan kuma nayi k'yauta dasu, Ku k'arata acikin talaucinku dama ahaka kuka taso kuma ahaka zaku k'are, Dan matiyaci ko'a tulun manshanu kasakashi haka zaifito bai dangwali komaiba, nasoka tamkar babu wani namiji aduniya, mahaifina yamaka gata tamkar shine ya haifeka, amma saboda butulci irin na talaka karasa dami zaka sakamin saida wata abar banza wai kishiya, tom ga fili gamai dokinan, saura kuma sukuwa ko?, ALLAH yabada sa'ar cin gabbaza mukan nagaba yayi gaba nabaya sai labari, abinda yasa zan barka katsira da gidan dakake cikima saboda yazama tukuyci wa tsaron dukiyar mahaifina dakayi abayane kawai, afrah da amrah kam kasaka aranka baka ta6a haihuwar wasu 'ya'yaba aduniya, nikam kamanta dani hakan zaifi yimaka sauk'i._
_wassalam matarka ada😜._
Ajiyar zuciya Asma'u tasauke, k'irjinta har wani d'agawa yakeyi sama saboda bugawar da zuciyarta takeyi da k'arfi, tadafe k'irjin tareda lumshe idanunta hawaye na zurara akumatunta, wani tausayin ya Umar ne yaketa walanked'uwa azuciyarta, ashe dama duk abubuwanan saboda ita yake faruwa dashi?, haba Anty Lubna miyasa zakiyi hakane?, gara'ace kin rabani da ya Fharuk da'ace kin cutar dashi da k'untata rayuwarsa sabodani, inason ya Fharuk banason wani Abu dazai ruguza duk wani cigabansa, ya ALLAH ka kawoma wanan bawa naka d'auki, tazame ta zauna k'asa da6ar tamkar wata mai shirin hawa bori.
Tadad'e a wajen tana kuka kamar wadda akace inna ko baba sun mutu, ganin babu sarki sai ALLAH tamik'e tawanke fuskarta, hijjabinta ta d'auka tasaka tafito.
Hartaje k'ofar fita saikuma ta fasa, komi ta tuna?, dawowa tayi tazauna a tsakar gidan tanabin k'adangaru daketa guje-guje da kallo.........
Ya Umar kam yanacan yanata bulayin Neman aiki, duk inda yasan yanada wata alfarma ada saida yaje, amma k'alilannema acikinsu suke Nuna sun ganeshi, wasuma nunawa sukeyi basuta6a ganinsaba, murmushin takaici kawai yakeyi yatafi, har yamma lik'is babu wani cigaba saima wahalar kishirwa da yunwa data addabesa, ganin magriba takawo kai yahau mashin yanufo gidansu.
Atsakar gida ya iske Mufida da Rafi'a suna hada-hadar girkin dare, Rafi'a dake wanke naman kaji tad'ago tana kallonsa da murmushi, yaya Sannu da zuwa.
Yauwa Rafi'a, aiki kukeyi?.
Eh yaya INA yini.
Lfy lau ya makaranta?.
Alhmdllh yaya.
Mufida itama ta gaisheshi.
Amsa mata yayi itama cikeda kulawa, Dan itama yanzu tausayinsa takeji tunda ya kwanta a asibiti.
Ya ce, "mamafa?".
Tanan ciki itada ya Abubakar.
Okey shima yazo gidanne?.
Eh yaya.
Cikin falon yashiga da sallama, ya Abubakar da mama suka d'ago suna amsa MASA babu yabo babu fallasa, durk'usawa yayi yana gaida mama, ta amsa MASA kadaran kadahan, hannu yamik'ama ya Abubakar shima suka gaisa, suna gama gaisawa ya Abubakar yamik'e, to Mamana bara nawuce gida saikuma gobe, babudai abinda kike buk'ata ko?.
A'a Sadiq d'ina bana buk'atar komai wlhy kawadatamu dakomai saidai nace ALLAH yayi maka albarka yak'ara arzik'i.
Ameen Mamana saida safe.
ALLAH yakaimu ka gaidamin 'yan jikokina da d'iyata.
Zasuji insha ALLAH.
saida yaje bakin k'ofa sanan ya ce, " o Umar sorry fa namanta kananan bamuyi sallamaba Ashe, saida safe konace saiwani jik'on danku kunyi wuyar gani yanzu.
Ya Umar dakansa ke a duk'e tun d'uzun yana sauraren tad'in Nasu mama, ya d'ago idanunsa dasuka fara canja launi zuwaja saboda 6acin rai, yasan sarai habaici ya abubakar yamasa amma ko kad'an fuskar jarumin naku bata nunaba, fuskarsa shimfid'e da murmushi ya ce, "babu damuwa ya Abubakar saida safe agaida iyalin, ficewarsa yayi batareda ya amsaba.
Ya Umar yadawo da kallonsa ga mama datake k'irga kud'in da ya Abubakar yakawo mata yanzu sai murmushi takeyi ana dangwalar yawu da k'ara Tisa k'irgar, baice komaiba yamaida Kansa k'asa yana jiran takammala.
Saida tagama tsaf sanan yad'ago ta kalleta, gabad'aya fuskarta ta canja yanzu babu walwala, amma kuma idonta na kan ya Umar d'in.
Muryarsa a raunane ya ce, " mama dama Nazi nasanar dake yanda mukayi da Lubna ne.
Baki mama ta ta6e amasife ta ce, "Umaru kaini rabani dawata lubna tunda kud'in ubanta basu ammfaneka da komaiba, idanda su wasu mutanene arzik'ine Aida sun taimakeka kodan ganin halin masifar dakake ciki, amma mutanannan sunyi funfurun fus saboda bak'in ciki irinna mai arzik'i dabayaso talaka yasamu, wace irin wahalace bakaima ubantaba fisabilillahi amma yamzu suka watsar Sakai, kofa dubaka basuzoyi asibitiba harkayi kwanakinka kagama jinya....
Shidai Umar tunda mama tafara sababinta baice komaiba kansama na k'asa, saidai zuciyarsa tana mamakin halin *_MANTA ALKAIRI_* irinna mahaifiyarsa, koba komi iyayen Lubna sun taka rawar gani akansa, kuma har gobe yana ganinsu da mutunci bakuma zai manta da karamcin dasukai masaba a baya......
Jin mama tayi shiru yagane tagama NATA, muryarsa a tausashe ya ce, "tom mama kiyi hak'uri amma bawannan maganarce dama kawoniba.
Tsaki mama tayi ta ce, " kaji zancen banza to miya kawoka!?".
Saida ya had'iye wani yawu k'irjinsa yana dukan uku-uku ya ce, ''mama na saki Lubna tunkafin na kwanta a asibiti".
Ba mamaba har Mufida da Rafi'a dake k'ok'arin shigowa saida suka daskare awajen, maganarsa ta razanasu.
Cikin tsawa mama ta ce, "Umaru bakada hankaline!!?, kokuwa kafara shaye-shaye bansaniba!!?".
d'ago jajayen idanunsa yayi yana kallonta, cikin girmamawa ya ce, " wlhy mama bana shan komai, amma idan kin bani dama zan fad'a miki dukkan abinda yafaru harna saketa.
Wani huci mama tasauke harda hura hanci ta ce, "ina jinka.
Ya Umar ya sauke ajiyar zuciya sanan cikin nutsuwa yafara zayyanama mama komai, Rafi'a da Mufida sai hawaye sukeyi, mama kanta jikinta yayi sanyi, wani k'auna da tausayin d'an nata suka ratsata, tabbas tana matuk'ar son 'yayanta mafisifar son kud'i da hange-hangene kawai suke dakusheta, ya Umar yayi shiru ayayinda yakai karshe, zuciyarsa sai zafi takeyi da rad'ad'i, jiyay k'irjinsa yafara nauyi, addu'arnan ta yaye bak'inciki da tafiyar da k'uncin zuciya yafara ambata.....
*↓*
*_“Allahumma inni abduka ibnu abdika ibnu amatika, naasiyatin bi yadika, maadhin fiyya hukmika adlun fiyya k'adha'uka as'aluka bi kullis min huwa laka sammaita bihi nafsaka au anzaltahu fiikitaabika au allamtahu Ahdan min khalk'ika awista' asarta bihi fii ilmil gaibi indaka an taja'ala k'ur'ana rabii'a k'albii, wa nuura sadrii, wa jalaa'a huznii wa zahaaba hammi”._*
_(ya ALLAH ni bawankane kuma d'an bawanka, kuma d'an baiwarka, makwarkwad'ata a hannunka take, hukuncinka zartaccene akaina, kuma k'addararka gareni mai adalcice ina rok'onka dakowanne suna Naka, Wanda ka ambaci kanka dashi, koka saukar dashi acikin littafinka, koka sanar dashi ga wani daga halittarka, koka ke6ance kanka da saninsa acikin ilimin fake da ke wurinka daka Sanya alkur'ani ya zama kaka ga zuciyata, da haske ga k'irjina, da kwaranyewa ga bak'in cikina, dakuma mai tafiyar da damuwata)”._
*↓*
*_“Allahumma inni a'uzu bika minal hammi wal huzni, wal ajzi wal kasali wal bukhli wal jubni, wadhal'id daini wa galabatir rijaali”._*
_(ya ALLAH! ina neman tsarinka daga damuwa da bak'in ciki, da gajiyawa da lalaci, da rowa da ragwantaka da nauyin bashi, da rinjayen mazaje)._
Ahankali k'irjinnansa yafara rage nauyi, zuciyarsa yafara sanyi, wata nutsuwace tafara riskarsa babu abinda yakeyi sai sauke ajiyar zuciya, da sauri Rafi'a tabud'e firij ruwa tad'akko batareda ta nemi kofiba ta mik'a masa, shima bai tsaya tambayar kofinba ya 6alle murfin yana kwankwad'awa cikinsa, saida yashanye ruwannan tas sannan yadire gorar, dama k'aramar gorace, kansa yad'ora jikin kujera yana sauke numfashi ahankali, bayan wasu 'yan mintuna nutsuwarsa tadawo gaba d'aya, har bak'in cikin da mutane suka cusa masa d'azu wajen neman aiki dukya kwaranye, saima wani nishad'i da farinciki daya mamayesa.......
Maganar mamace ta sauka a kunnensa, cikin tausayawa ta ce, "ALLAH ya k'yauta, saikadage yanzu kafara neman aiki da takaddunka, dama kaine kak'i aii tuni, yanzu da aikin kayarda ya samama maka alokacin daya baka za6i aikaga da haka bata faruba ko?........
Kallon mama yakeyi k'ur da mamaki wai ita har yanzu batayi laushi bane?, wai sai yaushene mahaifiyarsu zata daina wanan masifaffen son kud'in nata da hange-hange, (wata zuciyarsa ta ce, " addu'a kawai zakucigaba da mata").
Yananan zaune harta gama surutanta, jin ankira sallar isha'i yamik'e yamata sallama.
Awaje yatadda k'annen nasa mata duksunyi tagumu, yata6a Mufida dake kusadashi, "k! Lfyarku kuwa?".
Figigit suka dawo hayyacinsu, babu komai yaya. Okey tomni nawuce saida safe.
Lah yaya munfa kusa gama abinci katsaya kaci mana.
No ngd saida safe... Yafad'a yana fita.
Rafi'a da Mufida suka bishi da kallo cikin tausayawa.
Kai tsaye gidansa yanufa, baishigaba saida yayi sallar isha'i a masallacin anguwarsu sannan yashiga gida. Tun a tsakar gida yaga canji Dan yau gidan yasha gyara, yana shiga abban fallo wani k'amshi mai dad'i yabigi hancinsa, dukda babu komai afalon sai agogo amma yasharu tas sai k'amshi ke tashi, jin tafiyar abayansa yasakashi d'agowa da Sauri..............
*_(((S))).......2017_*
*_I Love you all my sweet fan's_*💋
[12/2/2017, 4:11 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻💻.........
💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*💎
*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*
*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_
*_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO........😜_*
*_page→27-28_*
........Asma'u ce sanye cikin doguwar riga ta atanfa, kayan sunyi bala'in zama ajikinta d'as, taci kwalliya ta alfarma sai bulala k'amshi takeyi, cikeda yanga tak'araso gareshi, shikam tsaye yake gingiringin tamkar wani gunki, harta k'araso gareshi amma bai motsaba.
Cikeda mamaki Asma'u take kallonsa, miya samesa haka?, kokuwa kwalliyar tatace batayibane?, shiga tayi bin jikinta da kallo tamkar mai Neman wani wani Abu, can tad'ago tana kallonsa itama, ya Fharuk lfy kuwa?.
Firgigit yadawo hayyacinsa tareda sauke wata nannauyar ajiyar zuciya!, 'yan kame-kame yafara na basarwa, no. babu komai yafad'a yana nufar d'akinsa.
Binsa da kallo tayi saikuma ta tab'e baki, kadaiji dashi tayi maganar tana masa gwalo😜.
Ya Umar nashiga d'akinsa yazube bisa katifar datasha d'an karan gyara, lumshe idanu yayi yana murmushi, yadad'e baiji farinciki irinna yanzuba, a 'yan watannin nan yama manta shi macene kokuwa namiji?, kwata-kwata bayajin wata sha'awa ko son kasancewa da mace, damuwa ta mantar dashi farinciki da nishad'i, yaukam Asma'u ta tunatar dashi koshi waye, Dan kwalliyarta tasakasa begen wani Abu, babu k'arya yarinyar tanada jiki irinna mata masha ALLAH, hannu yakai yashafa sumar Kansa wadda ba gayubane yasakashi tarata, a'a damuwace kawai da rashin lokacin kai, tashi yayi zaune yanamai bin ko'ina na d'akinsa da kallo, komai tsaf kamar ba d'akin daya zama bolaba acikin kwana hud'u dasuka wuce.
Ajiyar zuciya ya sauke tareda furta *_“Alhamdllh alaa kulli hallin”._*
A gaggauce yatashi yacire kayansa, wanka yashiga sauri-sauri ya kammala Dan yana burin sake ganin Asma'u da k'yau, baiwani d'auki dogon lokaciba yagama shiryawa cikin wando iya gwiwa da k'aramar Riga mara hannu, turare yafesa sanan yasaka silifas yafito babban falon dayake tamkar zaure, babu kowa afalon Asma'u takoma d'akinta, shima d'akin nata yanufa, tana a falonta zaune kan tabarmar data shimfid'a waya taketa latsawa tana kallon hotunan ya Umar sannan yana Umar Fharuk d'insa, tana murmushi, Dan sanda akayi hitunan yana wasa da nairane, shikansa yana son hotunan sosai, yad'an dad'e tsaye yana k'are mata kallo, ganin batasanma yanayiba yay mata gyaran murya.
Jikinta har rawa yakeyi wajen 6oye wayar.
Baice da ita komaiba yazauna kan tabarmar, saida yazauna sanan yamik'a mata hannu alamar tabashi wayar yagani.
Idanu ta kwalalo masa waje, ya Fharuk bafa wani Abu baneba. Uhm nasani, kibani dai. Marairaice fuska tayi tamkar zata FASA kuka Dan batason yaga mitake kallo, ALLAH ya bawani abun ashsha bane hotuna nake kallo.
Hotunan waye?, yay maganar cikeda cin magani.
Uhm uhm namunefa nidasu Hasiya da Fatee....... Batama bari ya tanka ba tamik'e tafita Dan kawo masa abinci.
Binta yayi da kallo, dukda bai yarda da itaba.
Yana nan zaune tashigo da tiren abinci, kallon tiren yayi dake d'aukeda komai sabo, kuloli Kofi cokula filet duk sababbi, kallonta yayi da k'yau yanzukam fuskarsa amatuk'ar d'aure take, ayatsine ya ce, "wad'annan abubuwanfa INA kika samu kud'in siyensu?.
Ad'arare ta kallesa muryarta na rawa ta ce, " uhm ya Fharuk sauran kud'in wayarnanne dama nabama Fatee tasiyo mana saboda naga ko kofin shan ruwa babu agidannan, dama sonake ka kammala cin abincin namaka bayani amma kayi hak'uri nayi Abu batareda Neman shawararkaba.
Ahankali ya furzo huci daga bakinsa yana kauda kai daga gareta.
Jiki a sanyaye tahad'a MASA abincin agabansa, tuwon masarane daya tuk'u da k'yau saikuma miyar k'u6ewa d'anya dataji d'anyen kifi da daddawa sai k'amshi ke tashi, a jok d'in kam zo6one shima sai k'amshin kayan yaji yakeyi.
Tunkafin yafara cin abincin k'amshin yawunsa keta tsinkewa, sosai ya k'agara yafara saka lauma, amma jinkai da k'asaita irinta mazaje yasakashi mazewa harda kauda kai gefe.
Cikin sanyin Murya Asma'u ta ce, "ya please kaci abincin, Dan ALLAH kada kamin horo akan hakan."
Tausayi tabashi Dan muryarta har rawa takeyi, amma baice komaiba, hannunsa takama tasaka acikin ruwan data aje arobar wanke hannu, Fes ta wanke hannun yana jinta, bai ankaraba yaji hannunsa acikin miyar, kallonta yayi da sauri, ta langa6e kai gefe tamkar zata FASA ihu, kona baka da kaina?, tayi maganar hawaye na zurara akumatunta.
Kad'an yarage ya fashe da dariya amma saiya gimtse ya antaya mata hararama.
Tashitayi tamkar Mara laka tashige bedroom, shikuma yaraka bayanta da murmushi, tana shigewa yafara saka lauma yana lumshe ido saboda dad'in da tuwon kemasa.
Saida yaci yak'oshi sanan ya wanke hannunsa, tuwon yad'iba a filet yatafi d'akinta danyasan itama bataciba, kwance take akan katifa rubda ciki da alama ma kuka takeyi, aransa ya ce, "idon kuka kenan".
Zama yayi abakin katifar yana ambatar sunanata, Husna tashi kici abincin. shiru tamasa batayi koda motsiba.
Ganin haka yakamo hanninta yana murzawa ahankali, zumbur Asma'u ta tashi zaune tana muzurai, wani yarrrr! Taji yayinda yake Mirza tafin hannunta, batareda yace mata komaiba yad'ora filet d'in abincin saman cinyarta, maza kicinyeshi tas.
Fuska ta shagwa6e tana turo baki nima na k'oshi tunda kaima bakaciba, ido d'ya yad'age yana kallon shagwa6a, saikuma yayi murmushin gefen baki yana fad'in waya gaya miki banciba?, saida nakusa cinyewama nakawo miki sauran.
Ya Fharuk da gsk?.
Kansa ya jinjina mata.
Bismillah tayi tafara cin tuwonsa, shikuma cikin dabara ya d'auki wayarta yafara bincike, ganin hotunansa take kallo d'azu yasakashi sauke ajiyar zuciya, tayi sagare tana kallonsa Dan mamakin wannan ajiyar zuciya, saida tagama tsaf taje ta wanke hannu sannan tadawo ta zauna abakin katifar hannunta d'aukeda kud'i masu d'an yawa har kashi biyu.
Naminene?, yafad'a batareda ya kar6aba.
Zan maka bayani aii.
Yau bayan fitarka Inna tazo gidannan, takawo mana kayan abinci, sannan tace nabaka wad'annan kud'in tanuna masa kashi d'aya acikin kud'in, wad'an nan kuma na sauran wayatane, saidai kayi hak'uri nata6a wasu aciki.
Amma ya Fharuk nayi wani tunani. Mizai hana shagonnan na k'ofar gida kazuba kayan provisions acikinsa har muga abinda ALLAH zaiyi akan Neman aikin naka.
K'yawawan idanunsa ya tsura mata yanamai kallonta cikeda so da tsananin k'auna, tun Asma'u tana yarinya yake sonta amma wasu abubuwa suka hanashi nunawa dakuma soyayyar Lubna data rud'eshi kasancewarsa mutum maison wayayyar mace. jiyake tamkar ya rungumeta. amma bazaiyi hakaba Dan gudun karta rainashi.
Jin yayi shiru gashikuma ya tsura mata idanu ta ce, "ya Fharuk! Mike faruwane?. Ko shawarata batayi daidai baneba?.
Ajiyar zuciya ya sauke, a'a Husna shawararki tayi, amma kibari zanyi tunani. Kud'in inna kuwa gsky bazan amsaba, za'a maida mata abinta, idanni har ban bataba, amatsayinta na uwa agareni, tom baik'yautu na kar6a daga garetaba.
Humm yaya kasandai halin Inna sarai, wlhy na tabbata bazata amshi kud'innanba, tunda har tayi niyya. Amma kagwada kagani, Dan kunfi kusa.
Hararta yayi, kokina kishine?.
Asma'u tazaro idanu waje, ya Fharuk nikam kishinmi zanyi dakai? bayan inna tabamu labari tunkan tasamemu kaine d'anta, yanzukuwa danta samemu bazata ta6a had'a soyayyarka da tamuba. Tokaga idanma nayi kishin, ainayi abanza. Ammafa inad'anyi kad'an. ‘tayi maganar tana dariya damasa gwalo.’
Shima murmushin yayi, yamik'a hannu zai cafkota ta zulle. Filo yad'auka yajefeta dashi, wlhy nakula yarinyarnan kinrainanifa.
Hannu tasa takare kanta daga filon, cikin dariya ta ce, "ALLAH niban rainakaba." ‘ashagwa6e take masa magana.’