Showing 51001 words to 54000 words out of 77995 words

Chapter 18 - karayar arxiki COMPLETE

12 Jul 2024

9240

suke nunawa kenan, had'arin yafarune a hanyarsu ta zuwa legos daga nan kano.
Mama ma sai jikinta yayi sanyi tatsaya sagare tana kallo.
Bak'aramar tarwatsewa jirgin yayiba, ga mutanenan kwance, wasuma Kansu yacire, wasu k'afa, wasu hannu, wasuma babu ta yanda za'a shaidasu dan duk sun canja kamanni. d'aya bayan d'aya akebi ana nunasu dan ana kwashe gawawwakinne da duba masu rai, dukda babu alamun akwai wani mahaluki dake numfashi acikinsu. gawar mahaifinsu lubna aka nuno, cikin amincin ALLAH shikam kamanninsa na nan, saidai jini dukya 6atashi, sannan hannunsa d'aya yafita.
Ya Umar yaruntse idonsa hawaye na kwarara, mama kanta kuka takeyi, (bak'aramin abune yake raunana jarumtar gwarzo namiji irin ya Umar ba) zuciyarsa da kwakwalwarsa suka Shiga tuno masa waye dady?, mutumin kirki maison talaka da son k'yautata masa, ya tuno ranar daya fara ganinsa shida direbansa, alkairin daya masa ya d'aga darajarsa fiyema da 'ya'yan cikinsa, wasu zafafan hawaye suka k'arayo ambaliya akumatunsa.
Mamace tayi k'arfin halin kama hannunsa ta zaunar akujera, a hankali take shafa kansa tana lallashinsa, ita kanta tasan miye matsayin dady azuciyar ya Umar, kosu sukace sun manta da halaccinsa akan d'ansu sunyi butulci ba k'aramiba.
Lallashin ya Umar takeyi sosai Wanda yake kuka harda shashshrka, kansa yana saman cinyar mama.....Umaru yanzu ba kuka yake buk'ataba, yana buk'atar addu'a ne daga garemu, babu abinda zamu sakanka masa dashi aduniyarnan inba addu'aba, Wanda ya haliccesa shine ya kar6i abinsa, muma nan duk irin wannan ranar muke jira Umaru...... Da ire-iren wad'annan maganganun ta kwantar masa da hankali.
Ahankali yafara sassauta kuka nasa saidai ajiyar zuciya, haka su Rafi'a suka dawo daga gidan inna suka samesu.
Suma sungani agidan inna dan haka basa buk'atar k'arin bayani, saidai ya Umar yabasu tausayi ainun.
Baibar gidanba saida aka kira sallar magriba.


Atsakar gida yatarar da Asma'u zaune saman kujera 'Yar tsugunno. Ta rabga tagumi.
Ko motsin shigowarsa batajiba barema sallamarsa, shima bashida k'arfin mata magana, saikawai yajingina da bango yazuba mata idanu tamkar mai nazarin wani abu.
Sunkai minti20 ahaka sanan ALLAH yabama Asma'u ikon d'agowa danjin kamar alamar mutum tsaye akanta.
Tarazana sosai, dan haka tayi shirin takewa da gudu, muryarsa a sanyaye ya ce, "Asma'u ninefa."
Gabantane yay azabar fad'uwa danjin muryar ya Umar dakuma sunan daya kirata dashi, Wanda zata iya rantsewa bata ta6ajin sunan abakinsaba sai yau.
Ya Fharuk lfy kuwa?.
Ajiyar zuciya ya sauke wadda yayita sau babu adadi, muryarsa hard'an rawa takeyi ya ce, "dadai sauk'i Husna."
Shiru tayi tana nazarinsa, saikuma yabata tausayi, gashi sunyi azumi, takama hannunsa suka shiga ciki.
A babban falo ta zaunar dashi bisa tabarmar data shirya kayan shanruwan.
Baice mata komaiba, tazuba zo6o mai sanyi tamik'a masa, kai ya girgiza mata alamar a'a ya k'oshi. Tuni idanunta suncika tab da kwalla, ganin haka sai kawai ya kar6a ya shaya kusan rabi, daganan yajingina da bango yay shiru.
Itama Asma'u shiru tayi, tasan bak'aramin abune yata6a zuciyar mijin nataba.
Haka sukaita zaman shiru har aka kira sallar isha'i.
Bai iya fitama masallaciba yayi sallar agida. itamadai Asma'u tayi tata sallar.
Har k'arfe kusan goma babu Wanda yazubama cikinsa komai. Cikin Asma'u ne yafara kiran Ciroman yunwa, dama 'yan kwanakinnan bata iya jure zama da yunwa saboda cikinta yafara girma, azuminma dak'yar take kaishi aduk ranar litinin da alhamis dasukeyi yanzu.
Zamewa tayi ta kwanta akan abin sallar, ya Umar yabita da kallo saita bashi tausayi daya tuna bafa ita kad'ai baceba, gakuma azumi dasukayi.
Tasowa yayi daga inda yake zaune yadawo kusada ita, ya had'a shayi mai kauri akofi, yazuba soyayyen dankali afilet da kwai (dan yanzu alhamdulillahi, basuda Matsala a a6angaren abinci. Ko abayama dasuka Shiga halin ha ula'i suna samu suci koda baikai yanda suke soba).
batareda yamata maganaba yakamata yatayar zaune, jinginata yayi da jikinsa sannan yad'akko kofin shayin daketa turiri kad'an-kad'an yakai bakinta.
Kauda kanta tayi gefe alamar bazata shaba. Bayason yawan magana yanzun amma yakula saita sakashi yayi akan dole. muryarsa asanyaye ya ce, "kidaure koda shayinne kisha mana, kinga bake kad'ai baceba.
Itama idanunta tad'ago tana kallonsa, yaya Indai kanaso naci to saidai muci tare. Ahankali ya girgiza mata kansa alamar shi ya k'oshi.
Itama saita kauda NATA kan ta ce, " Nima nak'oshi, tayunk'ura zata tashi daga jikinsa.
K'ara rik'eta yayi dak'yau dukda jikinsa babu kwari, kinga to zauna zanci.
Babu musu tazauna da k'yau, yana bata tana bashi harsuka d'anci babu laifi.
Asma'u tagyara wajen tsaf, lokacin data dawo yashiga d'akinsa, itama saita wuce NATA d'akin cikeda tunanin mike damun ya Umar ne?.
Saida tayi wanka tai shirin barci, zaman jiransa ta zaunayi, ganin lokaci yanata tafiya kuma ko alamarsa babu yasakata mik'ewa takashe komai tafice, tasaba kwanciya ajikin ya Umar dan haka bazata iya barciba ayanzu idan baya a kusada ita.
d'akin tatura tashiga da sallama, turus tayi dan ganin ya Umar kwance bisa katifa a yanda yashigo, ko Riga bai cireba barema asaran yayi wanka.
Jikinta asanyaye tak'arasa gareshi, jin motsinta da k'amshin turarenta yasakashi tashi zaune.
Idanu yakafa mata kamar mai hango wani Abu, tazo ta zauna ajikinsa tana tambayarsa abinda ke damunsa.
Awanan karon bai 6oye mataba yafad'a mata komai.
Itama har kuka tayi dukda bawani saninsa tayiba sosai, ranar ma dasukazo da family d'insane har ya Umar yamari Lubna, aranar tafara ganinsa. tundaga ranar kuma bata kuma ganinsaba.
Daga k'arshe sai ya Umar ne Yakoma lallashinta.
Ta ce, "ALLAH yajik'ansu yagafarta musu ya yafe musu.
Ameen ya Umar yafad'a yana kuma rungumeta da k'yau........




_____________________
Washe gari yazeed yazo sukaje gaisuwa shida abbansu dakuma baban Asma'u, da muktar, Harris, Sadam.
Sun sami gidan cike da al'uma kala-kala, dan yaune ake jana'izarsa, sarakuna, 'yan siyasa, 'yan kasuwa, masu madafun iko a gwamnati, harda mutane daga k'asashe daban-daban. Dan shi d'an kasuwa babu inda babushi, musammanma irinsu dady dasuka zama manya dolene adama dasu ako ina.
Suma su ya Umar anyi jana'izarsa dasu, sai yamma lik'is suka sami damar ganinsu safwan, sannan mutane sunragu sosai.
Har cikin gidan akai musu iso sukayi gaisuwa, saidai su ya Umar basuga Lubna ba. Amma ya hango 'yan biyu ajikin momynsu Lubna d'in.
Ko magana basuyi masaba dan ayanzukam summa manta dashi. Shima baice dasu komaiba tunda ana cikin rud'anine.

Kwana uku suka jera suna zuwa kullum.
Sai'a rana ta k'arshene ya Umar yaga Lubna tsaye aharabar gidan tayo rakkiyar wasu 'yan uwansu dazasu tafi.
Sanye take da dogon hijjabi mai hannu haryana Jan k'asa, balaifi tarame sosai dan mutuwar tarazanasu ainun, tanata jan carbi.
Suna had'a ido da ya Umar gabanta yafad'i, shima kansa saida yaji wani Abu.
d'auke kanta tayi daga garesu, tamaida hankali wajen yin sallama da 'yan uwan nasu dasuka shiga mota. Saida motocinsu suka fice sannan tajuya zasu koma itada Suhaima, da Jiddah matar Ameer.
Yazeed ne yay k'arfin halin kiran lubna d'in.
Tatsaya cak itasu Suhaiman, amma babu Wanda yajuyo acikinsu saidai Jiddah.
Su yazeed basu damuba, dan yauma subiyune kawai, dagashi sai ya Umar.
K'arasawa sukayi inda suke. su ya Umar suka gaishesu tundasu sungaza gaisheau. Jiddah ce kawai ta amsa da arzik'i, amma Suhaima da Lubna sai wani yatsine-yatsine sukeyi.
Sudai su ya Umar basuwani biye musuba sukai musu gaisuwa.
Fuuu suka shige ciki, jiddah kuma tatsaya ta amsa musu harda musu godiya da fad'in ALLAH yabada ladah.
Haka sukabar gidan, tsakanin ya Umar da yazeed babu maicewa uffan. Har k'ofar gidan yazeed ya sauke ya Umar, sukayi sallama.
Yazeed ya ce, "yakamata kashirya gobe idan ALLAH ya kaimu muje wajen saida motoci Umar. Baikamataba ace kacigaba dayawo hakaba.
d'an murmushi ya Umar yayi, karka damu yazeed kasan abinda yasa kaga inata zamewa gameda sayen motarnan, kayi hak'uri na kwantar dawata k'ura sannan, kasan babu Wanda yasan halin da ake ciki har yanzu.
Hakane kuma, namaka uzuri, ALLAH yakaimu lokacin, ubangiji yagyara mana komai cikin hikimarsa da ikonsa.
To ameen ngd sosai abokina, ka gaidamin madam da yara.
Zasuji insha ALLAHU, Nima ka gaidamin madam.
Sallama sukayi yazeed yaja mota yatafi, shikuma yashiga cikin gidan.
Asma'u na kichin tana k'ok'arin had'a kayan bud'a baki. Jin motsinta akichin shima saiya nufi can. yad'an zaro idanu waje dan ganin tana cin k'osan datake soyawa, madam ina azumin?.
Hannu tasa tarufe fuskarta tana murmushi, ALLAH yaya na karya, jinayi bazan iyaba, ga cikina yanata juyamin.
d'an murmushi yayi, dan yau babu laifi yad'an saki jikinsa, sa6anin kwana biyu dasuka wuce bashida walwala ko kad'an.
Yakuma matsowa kusada ita yana fad'in lallai kinzama ragguwa to.
Yaushe kika karya?.
ALLAH yaya ba ragwantaka baceba, tun sandasu Rafi'a sukazo.
Sune suka sakaki kika karya kenan?.
Idanu tazaro lah bafa subane wlhy, kayarda dani ALLAH.
na yarda dake, cigaba da aikinki to, k'osan zai k'one.
Da sauri takoma kan aikinta tafara kwashewa danya soyu.

Yaukam babu laifi bayan shanruwa ya Umar yazauna sunyi hira, acikin hirar tasunema yakecewa tadakata da azumin tahuta hakanan.
Ta ce, "aii zata iya, yau d'inma dan and'anyi ranane.
A'a kibarshi haka, dama inada niyyar tsaidaki saboda babyna baya samun isashshen abinci awajenki.
Hannu tasa tarufe fuska tana fad'in kai yaya.
Dariya yayi yana kwanto da kansa bisa cinyarta tareda tura hannunsa arigarta yana shafa d'an matashin cikin NATA dayayi d'as ajikinta, ya ce, " my baby ALLAH yakawoka, ko yakawoki duniya lafiya. Kullun mafarkin isowarka nakeyi.
Asma'u dai shiru tayi tana kallonsa yanda yake magana da ciki tamkar maiyi da mutum............



_kunjini shiru. Babana ne babu lafiya wlhy, amma Alhmdllh jikin da sauk'i, muna buk'atar addu'oinku plss._πŸ™πŸ»






*_(((S))).......2017_*
*_I Love you all_*
[12/27/2017, 4:01 PM] ~πŸ‡© ' πŸ‡― πŸ‡¦ πŸ‡· πŸ‡­βœ: πŸ‘©πŸ»β€πŸ’».........



πŸ’Ž *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* πŸ’Ž


*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*


*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_


*_NIKA'DAIπŸ‘ŒπŸΌ WRITER ASSO.....😜_*

*_page→57-58_*


..........Bikin Mufida ya kankama sosai, hidima akeyi babu kama hannun yaro.
Ya Umar dai baice dasu komaiba, ko kwayar shinkafa baikai gidanba, dukda mama tamasa magana.
Cemata yayi baida kud'i, kuma ba yaya Abubakar duk yace zaiyibane?.
Shiru tayi dantasan inda maganar tasa tadosa.

Har ana gobe d'aurin aure babu wani abin arzik'i daya sauka gidan.
Babu kayan miya bare nama kokuma wanidai Abu daya danganci abinci har hud'u na yamma kuwa.
Ana nan zaune jigum-jigum.
Kowadai yasan al'adar makwafta da danginka nakusa sukan shigo domin rage aiki ana gobe d'aurin aure.
Gakuma gida cike damk'an da dangi na nesa wad'anda tun ajiya suka fara sauka gidan.
Ana nan zaune jigum-jigum kowa yana raba idanu yaga ta inda abinda ake jiran zai 6ullo. Cikin amincin ALLAH saiga yi anfara shigowa da kayan gado na Mufida.
Nan take kallo yakoma sama, mamaki al'ajabi yacika mutane, kayan gadone irinna da-da d'innan, kuma kallo d'aya zaka musu kagane tsofaffine akaima kwaskwarima kawai. abin mamakin baigama k'arewaba saida aka dire rabin kwandon tumatur, da attarugu da tattasai acikin yellow d'in leda mai layi-layi, sai alayyahu buhu guda maicin arba'inπŸ™Š.
Saikuma ga garin tuwon dabai wuce kwano ashirinba, gefe kuma da shinkafa 'Yar Hausa mai tsakkuwar tsiyarnan dabata wuce kwano ashirinba itama.
Kowa yayi cirko-cirko yana kallon ikon ALLAH, Saiga ya Abubakar yashigo saiwani bud'awa yakeyi yana washe hakwara, shi a adole yayi abin arzik'i yau.
Sai gaida mutane yakeyi washeda baki, amma ganin kallon dasuke masa saikuma jikinsa yayi d'an sanyi.
Yakai dubansa kan mama da inna, sumadai kallonsa sukeyi cikeda mamaki, amma a can k'an zuciyar inna tana fad'in ALLAH ya k'ara.
Inda suke yak'araso, har yanzu bakinsa awashe yake, dukda jikinsa yayi la'asar. Mama inna! gafa kayannan sun iso, kunata kirana mutane suna jira sufara aiki ko?, wlhy inacikin kasuwa nayi matuk'ar busy, gashi dak'yar nasami motar data d'akko yakayan gadonnan, kiranma dakukemin yasakani azamar tahowa, kaji na nan za'a kawo guda Biyar manya-manyanema wlhy.
Inadai fata komai zai wadatar da kowa?, kuzo kuduba kayan gadonma, kafintan ya iya aiki wlh...........
Hannu mama tayi saurin d'aga masa dan surutunsa yafara addabar kunnenta.
Hawaye suka zubo bisa kumatunta, cikin shashshekar kuka ta ce, "Amma Abubakar kaji haushin rayuwarka, kaje, nidai kawulak'anta ko? babu komai ngd.
ALLAH sarki Umaru ALLAH yayi maka albarka. Basai mutum yamutuba ake tuna alkairinsa.
Dama duk Wanda yagaza godema ALLAH na tabbata zai godema azabarsa.
Banga laifinkaba abubakar saidai nawa, yau ga abinda halina ya jazamin, ALLAH kamin ni'ima maimakon nagodemaka saina butulce, ya ALLAH ka gafarceni, natuba ALLAH, wlhy natuba.
BakI ya Abubakar yata6e waike mama miya kawo wad'annan surutan ne haka?.
Ubankane yakawosu matsiyaci kawai.......
Bata k'arasaba inna ta to she mata Baki tareda janyeta suka koma baya saboda idon mutane, ya Abubakar baifasa bin bayansuba. Shima ya Umar saiya biyo bayan ya Abubakar dan shigowarsa gidan kenan shima, amma yaga dukkanin kayan dake zube a tsakar gidan, harma yayi gamo damai kawo kaji ak'ofar gidan.

Lafiya kuwa inna? Maganar ya Umar tadaki kunnuwansu.
Atare suka d'ago suna kallonsa, mama tasake fashewa da kuka tana koroma ya Umar bayani dalla-dallah.
Shiru yayi yana saurarenta, tausayinta yacikama masa ciki, kafin ya ce, " wani abu saiga Abba yashigo shima afusace.
Ganindai komai zai kwa6e agaban mutane inna ta ce, ''sushiga d'akin Abba.

Zaune suke suduka a falon Abba, wannnan karon harda Harris da mufida da Rafi'a.
Inna ce tayi magana duk tana bin kowannensu da kallo.....
Ita gsky d'ayace, kuma daga k'inta said 6ata, lallai inamai jaddada muku Abubakar bashida wani laifi, laifinkune wanan, tunda tun farko kune kuka d'ora yarannan akan wannan mummunar tarbiyyar.
Kuna Nuna banbanci akan 'ya'yanku saboda wane yanadashi, wane bashidashi. Kund'auki dukiya tamkar itace jigon rayuwa. Kudubafa halin da Umaru yashiga a watannin baya, amma acikinku babu Wanda yata6a waiwayarsa yasan yaya yaci, balle ya yaciyar da iyalinsa. Bak'aramin tashin hankali yaronnan yashigaba, badan mai tawakkali bane Aida yanzu an mance kamanninsa ko?.
Amma maimakon kujawoshi jikinku, kuringa kwantar masa da hankali, saikukayi watsi da labarinsa kuka kama Abubakar mai kud'i kuka rik'e ko?.
Wannan wace iriyar rayuwace haka?, aurenfa mufida aka saka agidanna amma Umaru baison komaiba akai saboda son zuciya irin naku. Kuji tsoron had'uwarku da ALLAH mana, kufa iyayene masu tarbiyyantarwa bamasu ruguzarwaba, ALLAH fa baya d'orama bawansa abinda bazai iyaba.
Shin ku'a tunaninku kunada wata dabara ta gujema talauci kenan?.
Hummm shidai Ubangiji aiba abokina wasan wani shege bane.
Ai yanzu ba tsinar Abubakar zaku hauyiba, hak'uri zakuyi da abinda yakawo ayi bikin haka, arurruma akaita kowa yahuta......
A'a inna idan ya Abubakar zaibani rancen koda dubu d'ari biyarne sai ayi komai yanda suke buk'atar d'in......
Carab ya Abubakar ya kar6e zancen, a INA naga wata dubu d'ari Biyar in? Kokuwa kud'in kasuwata zan gird'e nabaka rance saboda kanaso ayi biki waje-waje?.
Wlhy Umar kafita idona narufe, yanzu wannan siyayyar dakuke rainawa tawajen dubu d'aricefa. Ko kayan gadonnan hallidu kafinta a dubu arba'in da Biyar yayimini su babu Ragin ko sisi wlhy.
Ince yanzudai inna tagama wa'azi akan rashin godiyar ALLAH ko?....
Ba godemakane ba a yiba ya Abubakar, kawaidai INA buk'atar rancenne.
To banidashi d'an jonin masifa, kaid'in baca akayi ka saida mall d'inkaba? Ina kakai kud'in? In ba neman alagidigo da hankalin mutaneba kakeyi?.
Ajiyar zuciya ya Umar ya sauke, ya marairaice murya, (amma a can k'asan zuciyarsa dariyace ke bal'in cinsa, daurewa kawai yayi ya gimtseta) ya Abubakar bawai inayin Alagidigo da hankalinku baneba, har yanzu wad'anda suka sayi wajennan basu bani kud'in baneba.
Amma munyi alk'awarin nanda wata shida zasu bani adunk'ule, dan banason kud'i gutsin-gutsin.........
Kai dallah sauraramin, wlhy Umar kafita sabgata nasha iska, inbanda raini taya zanyi nad'auki dukiyata nabaka har tsawon wata shida, nikuma nazauna fanko, saboda inajin tsoronka, angaya maka nid'in sallamammene ko shashasha?........
Mamace tak'atse musu zance cikin raunin murya, kabarsa Umaru Shiba sallamamme baneba, nasan babu yanda za'ayi nunkufurci irinna Abubakar yabarsa baka bashi.....kuka yahanata k'arasawa.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login