Showing 57001 words to 60000 words out of 77995 words

Chapter 20 - karayar arxiki COMPLETE

12 Jul 2024

9245

d'an k'aramin tsaki yaja yashige d'akinsa, shima kansa d'akin a harmutse yake, yakai kwana biyar rabonsa da shara. Ananma tsakin yaja mai k'arfima kuwa, Dan har Asma'u tana jiyo sautinsa saboda gidan yakasance babu kayan dazasu hana girmamar sauti komai k'ank'antarsa.
Runtse idanunta tayi Dan harcikin ranta tsakin yashigeta sosai. Tashi tayi akasalance tad'an fara aikin, da k'yar tagama gyaran d'akinta, shima ko morphing bata gamaba taji k'irjinta yafara zafi.
Ajiye morpher d'in tayi tazauna dafeda k'irji. Abaya batama tuna tanada ciki inba fad'a akayiba. Amma acikin watannan ko kad'an batada cikakkiyar lafiya, dauriya kawai takeyi, ciwon k'irji da kasala suke addaba mata, gashi yanzu tadainama yawan barcin bakamar daba dasaita wuni tanayi bata gajiba.

Shigowar ya Umar yasakata d'ago kanta da sauri, kallo d'aya taima fuskarsa ta maida kanta k'asa.
Tunkafin ya tuhumeta tafara magana cikin rawar murya, Yaya kayi hak'u wlhy k'irjina ciwo yakemin.......tak'arasammaganar tana dafe cikinta da k'irjinta dake zafi.
Tausayi tabashi, Dan yagane balaifinta baneba, shi abinda yabashi haushi dabata nuna k'azantar na damunta.
Durk'usowa yayi gabanta yadafa bayanta yana shafawa ahankali, sund'an ja lokaci ahaka kafin yad'ago fuskarta datayi sha6e-sha6e da hawaye.
Gogemata yashigayi amma baiyi maganaba, itakuma tamkar yana zugata sai kuma matso wasu takeyi.
Ganin haka ya Umar ya ce, "kukan ya isa haka kuma malama."
Sassauta kukan tayi saida ajiyar zuciya lokaci-lokaci.
d'agota yayi suka koma bakin katifar, saida yaga tanutsu sannan yay gyaran murya, idonsa akanta ya ce, "zansa asamo miki mai aiki kawai, Dan bazai yuwu mucigaba datafiya ahakaba gsky, inada k'yank'yami Husna kema kinsan haka, kokad'an banason k'azanta.
Amarairaice take kallonsa, muryarta adashe ta ce, " a'a Yaya nidai banason mai aiki. Saidai idan Rafi'a ko Fatee da Hasiya cikinsu wata tadawo nan.
Hannunta yakamo ya rumtse anasa, idonsa nakan fuskarta, husna bazai yuwu mud'aukema mama Rafi'a ba a irin wannan lokacin, kinsan yanzu babu mufida, Fatee kuma tana sana'a itama zamu takurata gsky, saidai idan Hasiya, itama sai idan baba ya amince yabamu tunda dolene tazauna harki haihu, kinga kuwa wata wajen hud'u kenan zuwa biyar.
Kanta ta jinjina tana godiya.
Yad'an murza yatsunta yana murmushi, to amin dariya mana, wannan d'aurewa haka.
Dariyace ta su6ucema Asma'u, tarufe fuskarta tanayi.
Jawota yayi jikinsa ya rungume shima yana murmushi, hannunsa nakan cikinta yana shafawa, murya k'asa-k'asa ya ce, "ALLAH dai yasa kada yarona ko yarinyata suyo gadon wanan saurin kukan naki.
Kanta na bisa cinyarsa tayi 'yar dariya tareda turo baki gaba, tokaima dai karsuyo halinka d'innan na mazurai.
Dariya yayi sosai, cikin dariyar ya ce, " nihar wani mazuraine dani?.
Tab ya Fharuk aii wlhy idan kad'aure d'inan yanda kasan wani soja haka kake.
Yatsansa yasa ya d'alli bakinta yana fad'in mashe ranciya kawai.
Da sauri tasaka hannu tadafe tana fad'in wayyo zafi. Fuskarsa d'aukeda murmushi ya janye hannunta daga kan bakin, o sorry, namanta zan fasa d'an bakin rage zafin.
Hararar wasa tasakar masa, ta yunk'ura zata tashi, ya maidota, sorry my Queen.
Baki tabud'e zatayi magana ya manna nashi.
🚶🏻‍♀


_______________________
Tare suka wuni agida suna shan sharafin soyayyarsu, da k'yar Asma'u ta lalla6a ya Umar yakaita gidan bikin, yanzuma amotar jiya suka tafi.
Asma'u tayi masa tambayar duniya akan motar wage? Amma yak'i yabata amsa, saidai ya ce, "takice."
Daga baya saita tsuke bakinta.
Ak'ofar gidan Mufida ya sauketa, tareda gargad'in da anyi magriba zaizo sukoma gida.
Ta ce, "to."

Sanda tashiga gidan cike yake da danginsu, Dan harsunzo walima.
Gaisuwa taitayi da dangi, wasu har tsokanarta sukeyi wai sai yanzu take zuwa?.
'Yar dariya kawai takeyi cikeda jin kunyarsu.
Ahaka harta k'arasa d'akin Mufida, a can ta iske Anty Saratu da Anty Sa'adatu.
Bayan sun gaisa, Anty sa'a ta ce, ''o ke ma'u sai yanzu kike zuwa? Halan Umar ne?....
Hannu tasa ta 6oye fuskarta tana fad'in a'a fa Anty, banajin dad'ine.
Dariya duk 'yan d'akin sukayi, mufida dake zaune taci kwalliya da'akasan amarya dashi ta ce, "a'a Asma'u fad'i gsky dai, jiyafa agabana yakiraki, runda ya d'aukeki bamu sake ganinkiba dagake harshi bakuje dinner ba.
La'ilah, Anty Mufida munfaje.
Fatee ta ce, "ki rantse kunje Anty Asma'u!." 'Inafa kallonku kuka tafi amota.'
Hararta Asma'u tayi, to 'Yar saka ido anji.
Yanzummadai dariyar akayi.
Haka akacigaba da gudanar da biki, manyan iyaye irinsu inna sunacan suna rabo, su Asma'u kam ana d'aki anashan shargalle.
Shaf tamanta da sharad'in oga, saida taji anata kiraye-kirayen sallar isha'i sannan ta tuna. Jikinta har rawa yakeyi tajawo Handbag d'inta tafara laluben wayarta. Wayyo ALLAH ni Asma'u naga banu, tafad'a yayinda idanunta suka sauka akan screen d'in wayar. Missed call d'in ya Umar har 7.
Anty Saratu dake gefenta ta ce, "k lafiyarki kuwa?."
Yaya Saratu inafa lafiya, ya Fharuk yacemin da anyi magriba zaizo mu wuce gashi har isha'i tayi. 'Ashe kuma yamin kira har 7 ban d'agaba.'
Yanda tarud'e saitabama Anty Saratu tausayi, duk mace tasan tashin hankalin da ake shiga idan kashiga irin wannan k'angin.
Wayar Anty Saratu ta kar6a, itadai Asma'u tayi sagale tana kallonta. Anty Saratu ta kira ya Umar sau uku amma bai d'agaba, tunawa tayi ko yana masallaci, saita d'an dakata da kiran.
Ana idar da sallah takuma kira, shima saida rakira sau biyu sannan yad'aga. Bata bari yayi maganaba ta ce, "Assalamu alikum, yaya ina yini."
Kamar bazai amsaba, saikuma ya ce, "lafiya."
Tundaga yadda ya amsata tasan akwai Marsala. Amma saita dake zuciyarta ta ce, "dama sonake naji kokun tafine? Asma'u ce ta manta da wayarta awajena, kuma tunda aka kira magriba tafito dankarkaita jiranta.
Ta fito!? Zuwa ina?. 'Ya Umar yay tambayar.'
Jin muryarsa tad'an sassauta Anty Saratu ta gyara zama, k'ofar gida tafito, saidai ban saniba kotana tsakar gidan, danni ina d'aki.
Ajiyar zuciya ya Umar ya sauke, Dan d'azun ransa amatuk'ar 6ace yake, azatonsa Asma'u tak'i d'aga wayarne saboda batason tataho...... Ya ce, " kifito tsakar gidan ki dubamin ita, ganinan zuwa gidan.
To. Anty Saratu ta fad'a tana murmushin nasara.
Asma'u ta rungume Anty Saratu dantaji komai, ngd yaya Saratu, wlhy kin taimakeni, ya Umar d'an barazanane sosai.
Dariya kawai Anty Saratu tayi, ta ce, "kinga tashi muje k'ofar gidan yasamemu a can kawai.
Asma'u taima kowa sallama, sannan suka fito k'ofar gida.
Suna zuwa ya Umar na isowa kuwa. Asma'u ta shagwa6e fuska, kai yaya ina kashige inata zaryar lek'oka tun d'azun kamar nayi k'arya.
d'an hararta yayi ya ce, ''ai ita kika zura, dakina lek'owa dabaki ganniba, tunkafin magriba nazo wajennan inata kiranki amma baki d'agaba.
Lah namanta wayarne awajen yaya Saratu, kumani ALLAH ban gankaba.
To naji shiga mutafi nagaji nikam.
Motar tashiga sukayi sallama da Anty Saratu akan saitazo.
Ya Umar ya harareta, wato haryanzu kina yawon tsiyar nan naki ko Saratu.
Anty Saratu tad'an Sosa gefen wuyanta, ALLAH yaya banayi, zanzo zumincine kawai, nakwana biyu banzo mungaisaba shiyyasa.
To shikenan, kigaida yaran. Yabata dubu biyar.
Godiya tamasa sannan takoma cikin gidan, shikuma yaja motar suka tafi.





________________________
Haka rayuwa tacigaba da shurawa, tun bayan bikin Mufida Hasiya tadawo gidansu Asma'u tanad'an taimaka mata da ayyuka.
Asma'u anata jan ciki, saidai ad'an tsakaninnan tana d'an wahala Dan yanzu ita take nata laulayin cikin.
Sosai take samun kulawa daga ya Umar da danginta, hakama Anty Saddiqa tana iya k'ok'arinta.

Akwana atashi babu wuya, yanzu Asma'u kam tashiga watan haihuwa. Zuwa yanzu tazama alalla6a, sai shagwa6a da rakin tsiya, Abu kad'an sai kuka, wani lokacinma dariya take bama ya Umar, kullum tunaninsa randa Asma'u zata tsinci kanta ad'akin haihuwa.
Yasandai zasusha raki ainun....
A6angaren mall nasa abubuwa nata tafiya dai-dai Alhmdllh, har yanzudai baya zuwa sai lokaci-lokaci, shima saiya faki idanun mutane.
Komai yazeed yatsaya akai, gakuma muktar dasu Harris.
Yanzukam kud'i nashigo masa Alhmdllh.
A6angaren haihuwa kam yatanadi komai, har kayan gado yasiyo da kujeru daza'a zuba agidan, amma Asma'u bata saniba, dan bai kawosu gidanba.

Aranar wata Alhamis da yamma Asma'u tafara nak'uda.
Ya Umar na shago Hasiya taje a hargitse.
Hasiya lafiya kuwa?.
Yaya Anty Asma'u ce, gatacan tan.....
Baibari tak'arasaba ya afako cikin gidan.
Sosai Asma'u tafara jigata, hakan yasa baisaurari komaiba ya sungumi kayansa yakai mota. Hasiya ce tai k'arfin halin d'akko akwatin dasuka shirya kayan haihuwar.
Suna isa asibitin aka kar6esu da gaggawa.
Dr Al-ameen sai kwantar masa da hankali yakeyi.
Wasa farin girki, har wayewar garin ranar Asma'u bata haihuba, sai bak'ar wahala datakesha, duktayi laushi ko nishi bata iyawa.
Zuwa sannan 'yan uwa duksun cika asibitin, hardasu mama, dayake yanzu ta canja hali sosai.
Ya Umar kam aii kamar shima nak'udar yakeyi, dukaya fita hayyacinsa.
Ganin yanda Asma'u ta jigata ko motsin kirki takasa Dr Al-ameen yabada shawarar amata CS kawai.
Kowa yabada goyon baya, ya Umar yasaka hannu a takardar.
Babu 6ata lokaci akayi shirin shiga yima Asma'u theater.
Addu'a da fatan nasara 'yan uwa suka bita dashi. Ya Umar kam saiyayi Alwala yashige masallacin dake asibitin, alkur'ani yad'auka yayta karatu da mik'ama ALLAH kukansa...............



*_Asma'un ya Umar! ALLAH yasa afito lafiya kihaifama ya Umar d'inmu d'a ko 'ya maikama dashi😥._*
Ameen

_kowa yay shiru na second 1 Dan nuna jimami😂_








*_(((S)))........2017_*
*_Luv u all._*
[1/1, 3:05 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻.........



💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* 💎


*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*


*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_


*_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO.....😜_*

*_page→63-64_*


..........Sai wajen 1:30pm su Dr Al-ameen suka fito, kowa yana yarce gumi. 'Yan uwa sukayi Kansu suna tambayar Asma'u harma da abinda ta Haifa.
Hannu kad'ai Dr Al-ameen ya iya d'aga musu, cikin hanzari yashige office d'insa. Ya Umar dake binsa abaya ya ce, "Dr matatafa?.
Karka damu, muna fatan nasara, amma muna neman jini da gaggawa.
Dr kud'ebi nawa kawai. Ya Umar yay maganar cikeda hanzari.
Wasu Abubuwa Dr Al-ameen ya d'auka suka fice, kai tsaye wajen d'ibar jini suka nufa. Cikin amincin ALLAH jinin yazo d'aya kuwa, d'iba akayi aka tace sannan cikin hanzari Nurse d'in tad'auka ta kaima Dr Al-ameen......

Yamzuma saida suka kwashe kusan minti 40 sannan suka fito. Yanzukam akwai canji dan fuskokinsu a sake suke.
Duk mik'ewa sukayi ayanzunma, tunkafin suce wani Abu Dr Al-ameen ya ce, "Alhmdllh congratulations, ansami baby boy." 'Yay maganar yana matsawa gefe, Nurse d'in dake d'aukeda babyn ta bayyana.'
Gaba d'aya sukayi cahhh akan Nurse d'in, kowa nafad'in Alhmdllh.
tamik'a musu k'aton jaririn Wanda kallo d'aya zaka masa ka gane dolene yabama mamarsa wahala saboda girmansa. 'Yar rige-rigen d'auka akeyi, ALLAH dai yabama mama nasarar amsarsa.
Ya Umar kam wajen Dr Al-ameen yamatsa, Dr matatafa?.
Murmushi Dr Al-ameen yayi masa tareda dafa kafad'arsa kwantar da hankalinka baban baby, madam ma tana lafiya, yanzu haka anashirin maidata d'akin hutune danta huta.
Ajiyar zuciya ya Umar ya sauke, Ahankali yafurta Alhmdllhi Ala kulli halin. Dr zan iya ganinta kuwa?.
Babu damuwa muje narakaka dai ka ganta, inaga hankalinka zaifi kwanciya.
Ya Umar baice komaiba sai murmushin dakan k'awata fuskarsa dayayi.
Atare suka shiga d'akin da akakai Asma'un, su hud'une ad'akin, ya Umar yama sauran sannu sannan yak'arasa gaban gadon da aka kwantar da Asma'u.
d'aure take da bedsheet fari sal, said'an d'igo-d'igon jini dayad'an 6atashi, amma ansaka mata k'aramin hijjabi shima fari, idanunta biyu kuma tana iya magana, Nurse natsaye agefenta tana saka mata jinin da aka d'iba ajikin ya Umar Dan k'ara mata.
Ya Umar yak'arasa gaban gadon, yaja farar kujerar dake gefe ya zauna, hannun Asma'u yakamo yarimtse anasa, my Asmah sannu kinji.
Bata iya amsashiba, saidai idonta na kansa, sai hura hanci takeyi. Yamatso sosai yashafa kanta yana fad'in ALLAH yayi miki albarka kinji. Kad'an tad'aga masa kanta, muryarta can k'asa-k'asa take magana. Bayajinta, Dan haka yamatso da kunnensa kusada bakinta.
Ta ce, ''Yaya k'afata nanan kuwa? dubamini."
Murmushi yamata, yakuma shafa kan nata, k'afarki nanan My Husna. bakijintane?.
Yanzuma saida yamatsar da kunnensa sannan yaji mitake fad'a. ALLAH jinake kamar babu k'afar.
Ya Umar ya kalli Dr Al-ameen dake tsaye yana gyarama Nurse d'in yanda zatayi.
Dr kaji wai jitake kamar k'afarta bata a jikinta. Ko akwai matsalane?.
No, babu wata matsala, allurar da akamatace takawo hakan, zuwa safiya zatajita daidai insha ALLAH.
Ya Umar ya ce, "tokinji."
Nanma kanta tajinjina tanad'an lumshe ido.
Dr Al-ameen ya ce, "mubarta inaga zatayi barcine".
Ok ya Umar yafad'a yana mannama Asma'u kisses agoshi. Sannan suka fice.

Zuwa yanzu kowa yad'auki baby daketa barcinsa, suna zuwa mufida amarya ta mik'ama ya Umar babyn tana fad'in Yaya ga bak'on duniya.
Murmushinsa ya fad'ad'a, yakar6i yaron maicikeda lafiya, kiss uku ya manna masa afuska sannan yarungume abinsa yanajin wani farinciki na ratsa dukkan ga6o6in jikinsa.
Yakai minti kamar 5 ahaka, kowa yanata kallonsa cikeda tausayi, sunsan yanadason yara, amma aka rabashi danasa.
Bakinsa ya manna akunnen yaron yaymasa hud'uba, a la66ansa ya furta ALLAH ya raya *_Usman Fhodeeyo_*.

🤗nikad'ai najishi, Dan haka na ce, " Ameen ya Umar🤓.


Babu Wanda aka bari yashiga gunta har magriba, bayan magribane kuma ya Umar ya ce, "duksu tafi hakanan."
Badan sunsoba suka fara shirin tafiya, Anty Saratu, Anty Sa'a, mufida, Anty Saddiqa, fatee, Rafi'a, hasiya.
Mama kad'ai za'a bari anan, Rafi'a da hasiya ance subi fatee gidan inna, Dan ita batazoba, tama mama kara.
Kowa yaje yaga Asma'u dahar yanzu take barcinta sannan suka tattafi.


9:30pm
Mama ta kalli ya Umar da Harris, muktar, Sadam, yazeed da matarsa dasukazo suma tun bayan magriba, ta ce, "yakamata kutafi hakanan dare yayi, bakamar su yazeed kuda kuka baro yarama.
Yazeed yay murmushi mama aisuna tareda mai aiki babu damuwa.
Eh dukda hakadai yakamata kutafi, ALLAH yasaka da alkairi, yabada ladan zuminci.
Gaba d'aya suka amsa da Ameen.
Muktar yamik'ama mama jaririn daketa barcinsa nannad'e a showal. Sallama sukai mata suka fice, amma dana kalli fuskar ya Umar sainaga bahaka yasoba. Amma babu yanda ya iya, dan maza basa jinyar mata awajen, saidai mace 'Yar uwarka. Shima namiji haka.
Saidasu yazeed suka tafi sanan suma suka shiga mita suka tafi......
Ya Umar duk saiyaji gidan babu dad'i, amma fuskarsa cike take da fara'a na farincikin k'yautar da ALLAH yamasa yau. Aikam kusan kwana yayi yana sallah da mik'a godiyarsa ga sarkin sarakuna.




★★★

Washe gari tundaga sallar asuba ya Umar ya koma gida yay wanka a gaggauce yay shirin tafiya asibitin, kai tsaye asibitin yanufa. Saida yafara zuwa suka gaisa da Dr Al-ameen sanan yatafi d'akin da aka kwantar da Asma'u.
Tana zaune akan gadon, tajingina da filon wata Nurse tana taimaka mata wajen bama babyn nono.
Mama kuma na zaune akan kujera tana shan shayi (su mama babu juriyar yunwa😉lol).
Kamshin turarensa yacika d'akin, Asma'u dabatasan da shigiwarsaba tad'ago kanta. Murmushi yamata Wanda yasakata jin wani sanyi aranta, saima tadainajin zafin shan nonon da yaron keyi.
Rissinawa yayi yagaida mama sannan yakoma yabi sauran gadajen suma yana gaishesu.
Abakin gadon yazauna kusada k'afafun Asma'u, yad'auki yaronsa da'aka kwantar agefe bayan yasha nono yak'oshi. My Husna! Ya jiki?.
Cikin sanyin murya ta ce, "Alhmdllh, ina kwana?."
Lfy lau, kuntashi lfy?.
Kanta ta jinjina batareda tayi maganaba.
Ya Umar yamaida kallonsa kan mama yana fad'in mama babu dai wata matsala ko?.
A'a wlhy, lafiya lau muka kwana, shima yaron yanata barcinsa, yanzuma yatashi babu jimawa yad'an fara kuka, saikuma ga Nurse take kowa?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login