Showing 3001 words to 6000 words out of 77995 words
Kafin suyi magana mama ta cafe, a'a yabazasu rainakaba? Tunda kagaza yimusu maganin abinda yadamesu.
Ajiyar zuciya yasauke, idanunsa harsun canja kala, ya ce, ''kiyi hak'uri mama abubuwane sai ahankali, kinsan dai halin Dana tsinci kaina aciki, inda Dane kobasu tambayaba zan basu, amma wlhy yanzu banida sh......
Kai dakatamin!!!, mama takatsesa cikeda tsawa, harni zaka bud'e baki kacema bakadashi, koma kunyar yin k'arya bakaji?, shekaranjiyafa kasiyar da gidanka miliyoyin kud'i amma har bakinka yafurta bakadashi, duk dai Wanda yagaza godema ALLAH to zai godema azabarsa.
Wani yawun 6acinrai ya had'iye, muryarsa cikeda girmamawa agareta ya ce, "kiyi hak'uri mama, wlhy kud'in gidannan acikinsu aka cire aka sayi gidan damuka koma, sauranne kuma zanje nayi gyaran shaguna nana, bammayi zaton kud'in zasu kaini ko inaba.
Hummm tonaji baban tsari tashi kabani guri, kama gyara duniya dasu ba shagunaba, itadai rayuwa duk Wanda yakedashi yagaza taimakon d'an uwansa aiyayi asara....
Da sauri Umar yad'ago yana kallon mahaifiyar tasu, idonsa yayi jajur, Rafi'a ma kuka takeyi, tana mamakin hali irinnan mahaifiyar tasu, kwatakwata mutumce dabata godiyar ALLAH, atunaninta ya Umar yafi k'arfin cin fuskarta kodan k'ok'arinsa nason k'yautata mata, duk cikinsu babu mai hak'urinsa dakuma kula da iyayensu, amma tunda iftila'in nan yasamesa 'yan gidan suka fara canja masa........
Maganar ya Umar ce takatse mata tunaninta, rissainawa yayi ya ce, " sai anjima, ALLAH ya huci zuciyarki, yakalli su Harris ya ce, "zantura muku insha ALLAH.
baki suka washe suduka harda mama, ko kaifa d'an nan to ALLAH yayi albarka kaji, ameen yafad'a ala6ansa.
Suma su mufida sai zabga godiya sukeyi, shidai ficewarsa yayi.
Koda yashiga mota saiya fice daga gidna, tafiya yakeyi amma zuciyarsa namasa zafi, gefen titi yasamu yay fakin, yakifa kansa jikin sitiyari yana duk addu'ar datazo bakinsa, wlhy yana mamakin hali irinna mahaifiyarsu, alokacin da yakedashi tafi kowa sonsa da tattalinsa, kullum addu'a take masa dafatan alkairi dagamawa da duniya lfy, amma abin mamaki tunda komai yak'are masa saita fara canjawa, yanzu babu Wanda tatsana samadashi, batada magana saita ya Abubakar da Anty Sa'a da Harris da mufida, suma Kansu 'yan uwansa sun canja masa gaba d'aya, anty sa'a ce kawai da Rafi'a suke sonsa, yasa handky yana share hawayen dake kwarara a kumatunsa.
Yakai tsawon lokaci awajen sannan yabirka motar yanufi kasuwa.
Alhmdllh aiki yayi nisa Dan anata kwashe tokar gobarar data k'ona shagunan, ganin komai natafiya dai-dai saiya shiga mota yanufi majalissar abokansu.
%%%%%%%%%%%%
Zazzaune suke sunata kwasar hira da dariya, motar Umar tatsaya.
Motsowwww ga k'aban nan cewar Hafiz.
Waye k'aba?, Salman yatambaya idonsa akan hafiz?.
Umar mana, kokai bakada ganewane, cewar Tasi'u.
Al'kasim yata6e baki kaini wlhy fa banason yana ra6armu karya goga mana talauci.
Ashe kagane d'an uwa, yanzufa d'angidan dayake mana tak'ama dashifa ya saidashi.
Kai Dan ALLAH kabeer dagaske kakeyi?.
Wlhy kuwa Hafiz da gsk, nima jafar take bani labari jiya, kunsan shi kunya bazata bari yafad'a manaba.
Tofa, yanzu to ina Yakoma?.
Wani kangon gida yasiya... Dariya suka shek'e da ita, Al'kasim ya ce, "su k'aba anji yaji........
Umar dake tsaye duk yana jinsu yagirgiza kansa tareda musu sallama............
Afurgice suke kallonsa, duksun tsargu kardai yaji firar tasu?, dansu basusan yama iso inda sukeba.
Kowa yakama 'yan kame-kame.
Hannu yamik'a musu suka gaggaisa fuskarsa d'aukeda murmushi, suna gama gaisawa ko zama baiyiba ya ce, " bara nawuce, Dama nabiyo gaishekune.......
*_(((S)))....2017_*
*_luv you all my fan's_*๐ป
[11/20/2017, 6:20 PM] ~๐ฉ ' ๐ฏ ๐ฆ ๐ท ๐ญโ: ๐ฉ๐ปโ๐ปtyping..........
๐ *_KARAYAR ARZEEK'I!!._*๐
*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*
_Sadaukarwa_
*_miss Xoxo na_*
*_Zarah bukar_*
*_Ayusha muh'd_*
*_NIKA'DAI๐๐ผ WRITER ASSO....๐._*
*_pageโ4_*
..........ah mungode angon Asma'u da uwargida Lubna.
Baice komaiba sai murmushin takaici dayayi yajuya yashiga motarsa, suduka binsa sukayi da kallo, kai jama'a Kodai yaji mimuke fad'a?.
Kai baiwani jimuba, idanma yaji saime kune kukejin tsoronsa.
Mtsowwww miye abin tsoro a can?, mutumin da duk talauci ya gwaguyeshi, ni gwarama dabai zaunaba......
Umar da takaici yacika yana shiga motarsa yabar wajen zuciyarsa namasa k'una, waishi kowa ke gudu tamkar wani mai mugun hali, babu komai yagodema ALLAH, komai na duniya fararrrene kuma k'ararrene, zaiyi hak'uri insha ALLAHU, hak'uri irinna bayin ALLAH, hakadai yayta tunani harya isa gidansa, tun ak'ofar gida yaga motar mahaifin Lubna, cikeda mamaki yake kallon motar, tokodai Lubnace tazo da ita?, yatambayi zuciyarsa.
Ajiyar zuciya yasauke tareda fitowa daga motarsa yashiga cikin gida, ganin takalma reras ak'ofar falon yatabbatar masa da babu lafiya.
K'uru yayi yashiga da sallama, abin mamaki mahaifin Lubna ne da Mahaifiyarta, sai yayunta biyu da suhaima k'anwarta, Asma'u na tsigunne agefe da'alama kuka takeyima.
Dukda babu Wanda ya amsa gaisuwarsa haka yak'arasa cikin falon, yarisina yana gaida iyayen nata, fuska babu yabo babu fallasa suka amsa, yad'ora dafad'in Abba lfy kuwa?.
Lfy lau sai alkairi, Ameer yayan Lubna yafad'a amasife.
Yawu Umar ya had'iye na 6acin rai, amma baice komaiba.
gyaran murya mahaifin Lubna yayi, ya ce, "Umar nasan zakayi mamakin ganina agidanka?, toba abin mamaki baneba, baby ce takai k'ara akan bazata iya zama awannan kangon gidan nakaba, shiyyasa nazo ni dakaina na shaida maka nima banyarda d'iyata ta zauna anan ba, alfarma d'aya zan maka shine nabaka d'aya daga cikin gidajena kakoma kaida baby amma banda waccan sai farar k'afar, yanuna Asma'u.
Sai yanzu Umar yad'ago yana kallonsa, yayi wani d'an murmushi sannan yamaida kansa k'asa.
Duk azatonsu yaji dad'in k'yautarne shiyyasa ya murmusa, amma sai furucinsa ya tabbatar musu da sa6anin haka.
Ya ce, " ngd sosai Abba da wannan k'yauta, saidai inamai baka hak'uri dabazan kar6aba, wannan shine gidan daya kasance dai-adai k'arfina, idan Lubna tana sona tayi hak'uri muzauna anan, danni gsky babu inda zan koma.....
To aiko wlhy Umar saidai kasakeni........
Maganar Lubna takatseshi.
Shiru yayi baice komaiba, Safwan ya ce, "tokaji fa, saika za6a sakinta kokuwa bin abinda takeso?.
Kuyi hak'uri ya Safwan bazan iya sakintaba, kuma bazan koma ko inaba.
To aikuwa zakaga sammaci, Dan yarinyata bazata zauna awannan kangonba tanacin gabza.
Mom Dan ALLAH kuyi hak'uri, kufa iyayenmune baikamata irin wad'an nan zantukan suna fitowa bakinkuba.
Mtsoww to ubana gayamin yanda zanyi?.
Shiru Umar yayi Dan yasan wacece Mahaifiyar Lubna, masifaffiyace dama tafad'a aji.
Mik'ewa sukayi suduka har Lubna d'in, kawai saiyajin anci kwalarsa.
Cikeda mamaki yake kallon Lubna daketa girgiza jiki, ta ce, " wlhy saika sakeni.
Tsawa yadaka mata ke banason iskanci sakemin Riga.
Bazan sakiba wlhy saika bani takardata, kuma saki uku nakeso.
Zuciyar 'yan mazan tazo kusa, aiko ya sharara mata mari..... Baisauke hannunsaba Mahaifinta shima yamareshi.
Umar kana haukane?, agabana zama mari yarinyata, wlhy saikayi nadamar hakan, baby sakesa idan bai bayar da arzik'iba, aizaibada datsiya akotu.
Sakinsa Lubna tayi suka fice suduka.
Binsu kawai da kallo Umar yayi.
Asma'u kuwa dama tun d'azu kuka takeyi, suna fita tashige d'akinta da gudu tana kuka.
Itama binta kawai yayi dakallo.
Zubewa yayi ak'asa yana sauke numfashi da hawaye, shikenan Dan *_KARAYAR ARZEEK'I_* tasamesa sai kowa yatsanesa?, shin shiya d'orama kansa?, miyasa mutane basa ganewa?, ya ALLAH kabani ikon cinye jarabawarka, ALLAH ka k'aramin hak'uri da Wuyan d'auka, yadad'e awajen zaune abin tausayi, dak'yar ya rarrafa yabar falon Yakoma d'akinsa.
%%%%%%%%%%%%
Bayan kwana biyu da faruwar hakan, ya Umar dukya k'ara ramewa yafita hayyacinsa, abincima sai Asma'u tasaka masa kuka yakeci, baya fita ko ina, yama tsaida aikin shagunan nasa, kud'in da k'annansa suka buk'ata yabasu.
Yauma haka yatashi yanajin jikinsa duk babu dad'i, yasan tabbas da likita zai gwadasa saiyaga jininsa yayi hauhawar farashi zuwa dubu k'arewa 180+, yanzuma zaune yake afalo Asma'u ta ajiye masa abinci amma yakasa ci.
Sallamar dasukajice tasakasu kallon k'ofar suduka, har Asma'u tamik'e ya ce, "tazauna yaje.
Hannu yabama bak'on nasa suka gaisa, Umar ya ce, " kayi hak'uri ban wayekaba.
Eh bazaka sannuba, sunana Ahmad ilyasu daga kotu aka aikoni nabaka wannan, yamik'a masa zungureriyar farar takarda.
Jiki asanyaye Umar yakar6a, sallama yamasa yatafi, shikuma yajuya cikin gidan.
Asma'u tabishi da kallo, tasan ko tambayarsa tayi dawuya ya amsa mata Dan haka taja bakinta tayi shiru.
Zama yayi ya warware takardar ya karanta, girgiza Kansa yayi yana cije le6ensa, waishi Lubna takai kotu akan ya saketa?, tamanta da alk'awarin dasukaima juna?, tamanta da soyayyar dasuka Gina atsakaninsu?, tamanta hidima da k'aunar daya Nuna mata?, tamanta?, tamanta?, dayawa.
Ninke takardar yayi yasaka aljihun jallabiyarsa.
Yasakko yazauna ak'asa yaci abincin sannan yatashi yakoma d'akinsa yakwanta.
Asma'u kam shiru tayi tana mamakin komi takardar ta k'unsa oho.
%%%%%%%%%%%%
Bayan kwana hud'u ya amsa kiran kotu.
Bayan kammala wata shari'a aka fara tasu.
Tashin farko lauyan Lubna yanemi takardar saki dabin kadin hak'in Marin da Umar yayma Lubna ranar.
Umar ya ce, "shifa bazai saketaba, mari kuma it's tajama kanta.
Alk'ali yaci kud'i, Dan haka yace tilas Umar yayi saki Dan Lubna tace yana barinta da yunwa, babu sittirar kirki, sharridai sosai suka shirya masa wad'anda dole suka tirsasashi yamata saki d'aya.
Tayi tsalle tadire ta ce, ''uku takeso, Alk'ali ya ce, " yacika biyun.
Ran Umar yakai k'ololuwar 6aci musamman da Lubna taci kwalarsa acikin kotu gaban d'unbin mutane, cikin 6acin rai yacikashe uku amma yace tabasa 'ya'yansa, nanma ta ce, "bai isaba tabada 'ya'yanta mayya tarainesu.
Indai tak'aice muku tilas Umar yahak'ura, alk'ali yasashi biyan Tatar Marin dayayma Lubna, dakuma kud'i milyoyi akan rainon yaransa.
Kukane kawai Umar baiba amma tuni duniyar tafara juya masa, a take anan yamata transpar d'in kaf kud'insa na Account zuwa Account d'inta, bai barma kansa ko nera d'yaba.
Suna fitowa daga kotu yashiga mota yay gida ransa a6ace.
Sukuwa su Lubna da 'yan uwanta sai farin cikin samun nasara sukeyi.
Umar natsaida motarsa yafito, dak'yar ya iya shiga cikin gidan yana dafeda k'irjinsa, dak'yar ya iya sallama yashiga falon, aiko yana shiga ya yanke jiki yafad'i...............
๐wayyo ya Umar Fharuk๐ฅ.
*_(((S)))....2017_*
*_luv you all my fan's_*
[11/21/2017, 4:33 PM] ~๐ฉ ' ๐ฏ ๐ฆ ๐ท ๐ญโ: ๐ฉ๐ปโ๐ปtyping..........
๐ *_KARAYAR ARZEEK'I!!._*๐
*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*
_Sadaukarwa_
*_miss Xoxo na_*
*_Zarah bukar_*
*_Ayusha muh'd_*
*_NIKA'DAI๐๐ผ WRITER ASSO....๐._*
*_pageโ5_*
........da sauri Asma'u da Rafi'a sukayo Kansa, jikinsu sai rawa yakeyi, summa rasa taimakon dazasu bashi, Rafi'a ce tai k'ok'arin fita waje da gudu, cikin sa'a tayi gamo da mak'ocin ya Umar d'in zai fita.
Kuka tasaka masa tana nuna masa cikin gidan, amma takasa magana.
Ya ce, "yammata lfy kuwa?, fad'amin mike faruwa ne?.
Dan ALLAH ka tai makemu ya Fharuk karya mutu....katai makem.....
Ai baima bari tak'arasaba ya afka cikin gidan.
ALLAH yasa ya iya mota, Dan danan suka taimaka masa suka d'akko ya Umar dayayi jagaf tamkar gawa.
Rafi'a tafad'a musu asibitin datasan ya Umar d'in yana zuwa shida iyalansa harma dasu yakansa akaisu idan basuda lfy.
Suna zuwa asibitin Rafi'a ta ce, " sukaishi office d'in Dr jafar.
Babu marasa lfy ak'ofar office d'in Dan haka suka sami damar Shiga kai tsaye, Dr Jafar nazaune yana rubuce-rubuce jin anshigo ko sallama babu yasakashi d'agowa yaga wanene.
Kafin yayi magana,... Rafi'a ta ce, "Ya Umar muka kawo Doctor pls ka taimakemu karya mut......
Kafin takai k'arshe anshigo da ya Umar, doctor yatashi ya taimaka musu aka d'orashi ad'an gadon da'ake d'ora marasa lfy.
'Dan duddubashi yayi sannan yadawo ya zauna yana kallonsu Rafi'a.
Ya ce, " miya sameshi?.
Fad'uwa yayi.
Numfashi doctor yasauke tareda fad'in ALLAH ya sawak'e.
Ameen, Asma'u da Rafi'a suka fad'a.
Doctor yacigaba da fad'in, gsky bazan 6oye mukuba Umar yana cikin matsala, yanzu haka sai mun kwantar dashi sannan musan taimakon dazamu basa, zakuje kubiya kud'in gado dasauran Mayan aiki.
Da sauri Asma'u ta ce, "doctor nawa ake buk'ata?.
Uhmm kamar 100k insha ALLAH zasu isheku komai harma da canji.
Idanu suka zaro waje harda had'a baki wajen fad'in 100k fa doctor?.
Eh, haka nafad'a, aikunsan asibitin kud'ine wannan.
Rafi'a ta ce, " to doctor tunda ya Umar abokinka ne kumasa duk abinda yadace idan yadawo hayyacinsa saiya Baku.
Kai yagirgiza mata, bazai yuwuba aii, shima yasan dokar asibitinmu aii, kuma ma idan nace zanyi k'uri namasa komai idan yatashi yanada abin biyanane?, kuma kunsan Umar bashida ko sisi yanzu saidai yazamemin kaya, so kuke kawai kunemo kud'i kunga yana cikin danja.
Wash hawayene masu zafi sukrbin kumatunsu Asma'u, sudai sunsan doctor Jafar aboki ya Umar ne nakusa, Wanda sunada tabbacin yana cikin jerin wad'anda sukaci gajiyarsa da dukiyarsa fiye da kowa, amma yau danyaga bayidashi shine yake furta wad'an nan kalamin akansa.
Asma'u tadurkushr masa yana kuka da rok'on doctor jafar, amma yay kunnen uwar shegu da ita, saga k'arshema masifa yahauyimusu, kai nifa kuna cikamin kunne da 6atamin lokaci, idan kunada kud'in daza'a lura da Mara lafiyarku kubada, idan bakudashi kud'aukeshi kukaisa asibitin gwamnati.
Ran Asma'u ya6aci sosai, dama ita akwai zuciyar tsiya, mik'ewa tayi fusace taja hannun Rafi'a suka fita.
Saida sukaje harabar asibitin Rafi'a ta tirje tana ad'in Anty Asma'u wai ina zamujene?.
Hawaye Asma'u tashare, ta ce, "Rafi'a kirakani inda ake sqida wayoyi, zansaida wayata, nasan insha ALLAH ko 25k zatayi.
Ajiyar zuciya Rafi'a tayi ta ce, "to kije shagon su labaran na anguwarku, nikuma sainaje nafad'ama su mama king a yakamata su sank ko?.
Eh hakanma yayi, saimun had'u to.
Saga nan kowa yanufi inda zashi, sukabar makwafcin nan nasu tareda ya Umar.
Shagonsu labaran Asma'u take, babban shagone da'ake saida wayoyi daduk abinda yashafi hakan, had gyara sunayi, matasane sunkai Bihar masu tsaron shagon, kowa da abinda take kula dashi.
Asma'u tashiga da sallama, wani matashin saurayi ya ce, ''yammata kina buk'atar wani abune?.
Fuskarta takuma tamkewa damage Asma'u babu damace wajen rashin walwala.
Ta ce, " inaso na said a wayane.
OK to naga wayar.
Wayarta taciro tamik'a masa.
Yakar6i wayar yana jujjuyawa tareda d'agowa yana kallonta.
Ganin kallon mamakin dayake binta dashi yasata fad'in malam lfy kuwa?.
Eh to Hajiya dadai sauk'i, amma tsakaninki da ALLAH wayarnan takice?.
Cikeda mamaki take kallonsa, tagyara tsayuwarta sannan ak'ufule ta ce, "namaka kama da a6rauniyane?.
A'a wlhy Hajiya ko d'aya, kinsandai rayuwarce sai'a hankali kawai, amma idan ranking ya6aci kiyi hak'uri.
Idanma ban hak'uraba dukanka zanyi, kashiga cikin wayar sosai insha ALLAHU zakagane idanma tawace ko akasin haka.
Shawararta yabi yashiga bincike awayar, tabbas tatace Dan hotunantama dake kai sun Isa shaida, yad'ago yana kallonta to Hajiya nawa zaki sayar?.
Kasiya yanda yadace, nidai ina rok'onka kamin adalci kawai, nima dolece tasakani saida wayar badan nasoba.
Jinjina kai yayi, ya ce, "nasiya 150k.
Idanunta tazaro waje, kai malam kallifa da k'yau kaga wayar dake hannunka.
Murmushi yayi Hajiya nagani sosai, wlhy nama saya da daraja aii.......
Kafin tayi magana wani dake kusadasu yana sayen waya ya ce, " gsky kacuceta Dan wayarnan bata sha wahalaba.
Asma'u da mamaki yakashe ta ce, nifa duk bamma fahimci inda kukadosaba, wayar dabata wuce 25k ba kuke kira mata 150k?, ahankama har ana fad'in an cuceni?.
Wanda yasaka musu bakin ya ce, "Hajiya amma dai bake kika sayi wayarnanba?.
Eh bani nasayaba, yayanane yasiyamin.
Haba shiyyasa bakisan kud'intaba, wannan wayar dakike gani, ana saidata 400k wlhy.
Idanu sosai Asma'u ta kwalalo waje, sai maimaita yawan kud'in take azuciyarta, dubu d'ari hud'ufa?, tabd'ijan, lallai ya Umar yayi k'ok'ari......
Tunaninta yakatse yayinda taji maganar labaran abayanta.
A'a Asma'u lfy kuwa?.
Lfy lau wlhy Labaran, nazo nasaida wayane.
Tofa ina wayar?.
Kaganta nan, tayi maganar tana nunama masa wayarta dake hannun saurayin.
Hannu yamik'ama saurayin yabashi wayar, saida ya rissina sannan yabashi alamar girmamawa.
Labaran yakar6i wayar ya jujjuya sannan ya ce, " nawa kasiya?.
In ina saurayin yafarayi alamar rashin gsky, labaran ya girgiza kai kawai danyasan halin yaran shagon dason zuciya.
Baice komaiba yak'irgo kud'i masu yawa yabata, Asma'u ga 330k kiyi hak'uri datayin farko dayayi mini.