Showing 18001 words to 21000 words out of 77995 words
baya buk'atar maganar, ganin haka kowa ya daina tambayarsa Lubna.
Yauma duk suna asibitin har kawu kabiru da babansu Asma'u, 'Yar hira akeyi da raha irinta family idan an had'u, ya Umar kam shiru baya cewa da kowa k'ala, Harris ya kalli ya Abubakar ya nuna masa ya Umar da baki (zind'e kenan, kuma babu k'yauπ.)
Baki ya Abubakar yata6e shima suka had'a ido da matarsa Haleesat.
Asma'u duk tana kula da abinda sukeyi, hakama Anty Sa'a, hawaye yacika idon Asma'u tamik'e ahankali tafice.
Ya Umar dake kallon duk wani motsin kowa, har abindasu ya Abubakar sukeyi masa, yabi Asma'u data fita tana kuka da kallo, ahankali yalumshe idanunsa yanamai jin tausayinta, shima sakkowa yayi daga gadon yanufi hanyar fita.......
Inna ta ce, "Umar ina zuwa kuma?.
d'an shafa kansa yayi, idonsa ak'asa ya ce, " inna zand'an tattaka ne, na gaji da kwanciyarne".
To aii dakayi magana sai ko Harris ya taimaka maka, kaida bakajin k'warin jikinka".
A'a inna yayi zamansa zan iyama, nafison nayi dakaina.
To shikenan, jeka, idan kagajidai kadawo kaji.
Kansa ya jinjina mata tana murmushi, sannan yafice.
Asma'u na zaune akujerun dake jere a tsakkiyar reception d'in asibitin, kanta a duk'e yake shiyyasa ya Umar baiga halin datake a cikiba, takawa yayi zuwa gareta.
Da sauri tad'ago danjin mutum ya zauna a Kusada ita.
Had'a ido sukayi da ya Umar, sai kawai tad'auke kanta, tamaida k'asa tana k'ara share hawayen dasuka silalo mata yanzun, girgiza kansa yayi tareda kamo hannunta ya rumtse anasa, yaarrrrr tsigar jikinta ta tatashi, yauce rana ta farko da ya Umar yata6a rik'e hannunta amatsayinta na matarsa, ta rumtse idanunta harda cije le6e.......
Bata gama dawowa dai-daiba taji muryarsa na kuwwar fad'in Husna!.
K'ara rintse idanunta tayi sosai takuma kasa amsashi.
Shima baya buk'atar amsar tata Dan haka yacigaba da fad'in, Husna shin bazaki zama jaruma baneba?, kina ganin rayuwa zata cigaba da tafiya komai da kuka?, Husna bamusan randa rayuwa zata canja bafa, kenan hawayenki basuda ranar k'afewa?, kinga d'ago ki kalleni.
Shiru Asma'u takasa d'agowa, amma tana sauraren dukkan maganganunsa.
Ya kuma fad'in husna kalleni mana.
d'agowa tayi cikeda kasala, suna had'a ido tayi azamar janye nata, yad'aga baki zaiyi magana Anty Sa'a tak'araso wajen.....
A'a d'an k'anina mikuma kukeyi anan wajen?.
Baice komaiba saidai nuna mata Asma'u da kanta ke k'asa yayi.
Anty Sa'a tad'anyi murmushin takaice tareda zama Kusada Asma'un suka sakata tsakkiya itada ya Umar.
Itama dafa kafad'arta tayi, cikin sigar lallashi ta ce, "Asma'u kik'ara zama mai hak'uri da jarumta dukda nasan kinadasu, kicigaba da yima mijinki kuma yayanki addu'oin fatan alkairi, kizama mai k'arfafa MASA gwiwa kinji?.
Karki sake damuwa da abinda wasu suke masa barema harya sakaki kuka, ALLAH daya basa shiyya kar6i abinsa badan baya son Umar ba, sanda ya azurtasa baiyi shawara da kowaba, hakama yayin amshewa, suma basufi karfin ya kar6e daga garesuba.
_antambayi Mazon ALLAH (s,a,w) waye talaka?._
_sai ya ce, "Wanda zaitashi ranar k'iyama babu komai na aikin alkairi a gidauniyar ayyukansa._
To Ashe talaucin duniya bashine talauciba, dukiyar duniya ba itace arzik'iba, Dan *_KARAYAR ARZEEK'I_* ta riski Umar ba hakan na nufin ALLAH baya sonsa baneba, ya jarbceshine Dan kawai yaga nauyin imaninsa, wannan itace *Kaddararsa* Dan haka bashida ikon tsallakewa, inhar d'an Adam bazai iya gujema kaddarar ranar mutuwarsaba, to tabbas bai Isa gujema duk wata k'addara a yayin rayuwarsaba, kibar kuka kinji.
Jin jina kai Asma'u tayi, cikin raunin murya ta ce, " Anty sa'a ngd da tunatarwarki agareni, ALLAH yak'ara bamu jarumtar cinye jarabawarsa, Ameen ya rabbi Asma'u, ALLAH ya albarkaci rayuwar aurenku.
Murmushi Asma'u tayi, azuciyarta ta ce, "Ameen Anty Sa'a".
Ta juya tad'an kalli ya Umar, muryarta kasa-kasa ta ce, " ya Fharuk kayi hak'uri da d'aga hankalinka danayi harka taso kafito, insha ALLAH wannan shine na farko kuma na k'arshe.
Mik'ewa yayi yana fad'in ni bakimin laifin komaiba dama.
Daga Asma'u har Anty Sa'a da kallo suka bishi harya shige d'akin dayake jinya.
Asma'u tajuyo tana kallon Anty Sa'a, kanta a langwa6e ta ce, "ya Umar yanada wuyar sha'ani anty".
Murmushi Anty Sa'a tayi tareda fad'in duk taurinsa kece zakisakashi yayi sanyi k'anwata, nakumasan zaki iya saboda jarumtarki...
Itama tana kaiwa k'arshe ta tatashi tabar wajen.
Da kallo Asma'u tabita harta shige, ta sauke ajiyar zuciya tana wani murmushi da juya maganar Anty sa'a a zuciyarta, indai hakane to tabbas zata zama zaruma wajen maida ya Omar sanyi kamar yanda Anty Sa'a tafad'a, tabbas tanason ya Umar sosai kuma zata zauna dashi aduk halin dayake ciki, itama mik'ewa tayi tashiga d'akin
Da sallama tashiga, wad'anda sukaji suka amsa, tanemi waje kusada Fatee ta zauna, data d'ago ido saita kama ya Umar na kallonta, Anty sa'a na kallonsu tana dariya ciki-ciki.....
_____________________
Kwana biyu tsakani aka sallamai ya Umar suka tattara sai gida, duk dangi sun musu rakiyya zuwa gidan nasu.
Wani abun mamaki tundaga babban falo suka fara gani, kaf abinda ke falon an kwasheshi babu komai sai agogon dake manne abango, kallon-kallo aka koma kowa yayi cirko-cirko kamar zakaru na shirin fad'a, Asma'u ce tayi k'arfin halin d'aga k'afafunta tashiga cikin falon sosai tana kalle-kalle.
Babu Wanda ya iya cewa Uffan aduk taron, Dan Ya Umar baibama kowa damar hakanba, hasalima d'akinsa yashige yabarsu anan, a falon nasama abin mamakin ya tarar Dan nanma komai babu sai agogo dawata kujera guda d'aya dayakan zauna domin hutawa, sai tebiri agefenta Wanda yakan d'ora abubuwa, dak'yar yaja k'afarsa zuwa cikin bedroom d'in zuciyarsa cikeda tunani kala-kala, nanma dai bata canja zani ba Dan babu komi sai katifa da jibgin sutturunsa akai, saikuma tarkacen daba'a rasaba, jin hajijiya na neman d'ibarsa ya dafe bangon d'akin, cikin zuciyarsa yake tunanin wayayi masa wannan aikin?, badai za'a danganta ta'asarnan da 6arayiba Dan babu abinda 6arawo zaiyi da katakai, zuciyarsa tafara rawa akan ina Asma'u tasamu kud'in biya masa asibiti?, can wata zuciyar ta ce, "ita ta saida kayan gidan kenan?. Damm gabansa ya fad'i yay shiru batareda iya koda kwakwkwaran motsiba, yama rasa wane tunani zaiyi akan Lamarin........
A 6an garen Asma'u madai tunani take yaushe ya Umar yay cinikin kayan gidansu?, kanta bai ida kwancewaba saida tashiga nata d'akin, babu komai an kwashe sai katifa, hattada akwatinanta na lefe ankwashesu kaf, sai kayan datazo dasu daga gida aka zube a katifa, innalillahi wa'inna ialaihirraji'un kawai take iya amabata, yaraf tazube bisa katifar tana sauke numfashi, wai miya shiga kan ya Umar ne haka?, Dan kawai *KARAYAR ARZEEK'I* ta riskeka sai komai daka mallaka yazama hajar rabawa a kasuwa?, haba wannan wace iriyar rayuwace?.......
6angaren dangima dai kowa lamarin yagirmi tunaninsa, amma babu halin magana, dansu duk tunaninsu su ya Umar sun saida kayan gidanne dan nema masa lfy, wannan yasa tausayinsu ya d'arsu a zukatan wasunsu, Anty sa'a ma kasa zama tayi ta tattara 'ya'yanta suka tafi tana kuka da tausayin k'anin nata, ganin haka sauran sukaima Asma'u sallama suma suka tattafi.
Daga Asma'u har ya Umar sun riski kansune a halin shiru da zargin juna, kuma har zuwa yammaci babu Wanda ya iya neman d'an uwansa balle tambaya agareshi, ganin agogo ya nuna 3:45pm yasaka Asma'u tashi tafito da k'yar saboda jin cikinta yafara kiran Ciroma tasan kuma ga ya Umar ma hakane.
Kicin tanufa da nufin dafa musu komi yasamu su zirarama hanjinsu, mamaki al'ajabi da tsinkewar zuciya duk suka risketa alokaci guda, wayam babu komai akicind'in koda kuwa cokaline, hakama sitod'in babu alamar kwayar gero acikinsa, ta nisa tareda sauke numfashi, tama rasa abin fad'a Dan haka tafito zuwa d'akin ya Umar.
Tofa. ta ambata yayinda tayi tozali danasa d'akin shima wayam, ta hard'e hannayenta ak'irji tana k'ara raba idanu akan komai, shin kuka zata fasa kokuwa kururuwa?, da sauri tafito zuwa d'akin Lubna, nanmadai an kwashe komai ko tsinke ba'a bariba, nasu d'akunan yafi dama-dama tunda anbar musu katifu da agogunan kallon lokaci.
Ayanzun kam ba tsinkewar zuciyace kad'ai ta risketaba harda tsinkewar 'Yar hanji da daskarewar jini, da k'yar taja k'afafunta takoma d'akin ya Umar, masu iya magana kance ta inda aka hau aii tanan ake sauka.
Bedroom d'insa takutsa kai batareda neman iziniba bare tsoron shiga, babu kowa ad'akin saidai k'arar ruwan wanka daga bathroom d'insa, wannan yasa tazauna abakin katifar tanabin tulun kayansa dake jibge bisa katifar da kallo...............
*_luv you so much my sweet fan's, ALLAH yabar zuminci, inata godiya da k'aunarku gareni, wlhy nima ina matuk'ar k'aunarku aduk inda kuke alkairin ALLAH yakai mukuπ»π»π»π»β€β€β€β€β€β€π€π._*
*_(((S))).......2017_*
*_Luv you all_*
[11/29/2017, 2:40 PM] ~π© ' π― π¦ π· πβ: π©π»βπ».........
π *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*π
*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*
*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_
*_NIKA'DAIππΌ WRITER ASSO........π_*
_Na gaisheku my Deexerh da Billy S Fari & Deejerh, alkairin ALLAH yakai muku aduk inda kuke, ina alfahari daku._π»π»π€π
*_pageβ23-24_*
.......Yana fitowa tamik'e zumbur tamkar wadda aka tsikara, da sauri tafice a d'akin, shikuma ya rakata da kallo, baice komaiba ya zauna yana shafa mai, duk jikinsa babu k'arfi yake jinsa, jallabiya kawai ya zura yafito domin tafiya masallaci sallar la'asar.
Afalonsa ya tadda Asma'u, harzai wuce saikuma yajuyo ya kalleta, itama shi take kallo, amma suna had'a ido tajanye nata, ya ce, "lfy kuwa?".
Tashi tayi tsaye tana tura baki gaba, muryarta na rawa ta ce, "ya Fharuk miyasa zakayi haka?".
Kallonta yakeyi sama da k'asa Dan baisan inda maganar tata ta dosaba, hasalima shiyya dace yamata wannan maganar saboda saida kayan gidan datayi.
Ganin kallon dayake mata yasaka jikinta yin sanyi. shima juyawa yayi yafice abinsa batareda yasake cewa komaiba.
Dak'yar ta iya jan k'afarta takoma d'akinta, itama sallar ta gabatar, tana nan zaune akan sallayar cikinta na k'ugin yunwa taji alamar shigowar mutum, kafin tayi wani yunk'uri k'amshin turarensa ya sanar da ita shine, sosai yake bin d'akin da kallo, jiyayi wani haushi yakuma turnik'e zuciyarsa, to aii 6annar tayi yawa, kujerun babban falo kad'ai zata iya saidasu sama da dubu d'ari biyu, amma shine hardana d'akinsa Dana d'akinta?, afusace ya ce, "k! Waimike damunkine?.
Asma'u tad'ago tana kallonsa, tuni tsoronsa ya tasirantu azuciyarta Dan ganin yanda idanunsa suka kad'a sukayi jajur.
Muryarta na rawa ta ce, "yaya babu abinda ke damuna fa"......
Wata Uwar harara ya galla mata wadda tasakata saurin tsuke bakinta, Yakuma Daka mata tsawa ubanwaye yasakaki saida kayan gidannan!?.
Cak jikin Asma'u yatsaya daga rawar dayakeyi, sosai take kallonsa dakuma mamaki, shi Kansa ya lura da hakan.
Ta d'auke idonta daga kansa tana fad'in niban saida ko cokaliba agidannan, nima kuma d'azu maganar danaje yimaka kenan, dai-dai da kicin ba'a bar komaiba hakama d'akin Anty Lubna babu komai........
Shiru yayi yana kallonta, zuwa can kuma ya ce, " to idan bake bace wanene?, kinsandai 6arawo bazai saci katakai yabar kayan sakawaba?, shin inama kika samu kud'in biyamin asibiti?.
Zuwa yanzun kam zuciyar Asma'u tafara tunzura, Dan haka tafara maganar dad'an karsashi, wayata nasayar nayi hidimar asibitinka, Dan alokacin banida abinda yawuce wayar saikuma kayan lefena Dan sukad'ai na mallaka agidannan, sukad'ai kuma zan bigi k'irji nace nawa, ko a shekaranjiya danazo gidannan komai yana nan, na tabbata duk Wanda yay wanan aikin ajiya yayishi.... Fuuuuu tashige bathroom batareda tajira cewarsaba.
Cikeda mamaki yabita da kallo, dama yasan tuni Asma'u tanada tsiwa daga bayane tabari saboda tana shakkarsa, fita yayi zuwa d'akin lubna danya gaskata maganar Asma'u.
Ilai kuwa babu komai acikinsa, kamarma ba'a ta6a ajiye wani Abu daya danganci mutumba, can jikin k'ofar window ya hango wata farar takarda, ahankali yataka ya zareta tareda bud'ewa, anutse yafara karanta takardar, baikai da zuwa k'araheba yasaketa awajen yana ambatar addu'ar da akeso musulmi yayi yayinda al'amura suka tsananta a gareshi.
β
*_βAllahumma laa sahla illaa maa ja'aaltahu sahlan wa anta taj'alul hazna izaa shi'ita sahlanβ._*
_(ya ALLAH! babu wani Abu mai sauk'i, sai abinda kasanyashi yazama mai sauk'i, kuma kai kana Sanya tsanani idan kaso yazama sauk'i)._
Haka yayta maimaita wanan addu'a ahankali nutsuwa tafara zuwa agareshi, d'aukar takardar yayi yafice daga d'akin Yakoma nasa.
Asma'u dake la6e tana kallon duk abinda ke faruwa takoma baya da sauri Dan ganin zai fito, koda yashiga d'akinsa saiyayi wurgi da takardar a katifar, shima yafad'a saman kayan ya kwanta domin samun sauk'in zafin da yakeji.
Asma'u nanan zaune afalo shiru saiga Rafi'a da abinci, sosai tayi murna da hakan, bata 6oyema Rafi'a damuwarta tasanar da'ita komai. sosai lamarin ya girgiza Rafi'a.
Asma'u tamik'e takaima ya Umar abincin, tadad'e akansa tana masa magana amma ko motsi baiyiba bare tayi tunanin zai amsata, hakan yasa tadire abincin tafitowarta.
++++++++++++++++
Haka rayuwar gidan tacigaba datafiya cikeda k'unci da damuwa, babu mai shiga harkar wani acikinsu, gaisuwa kawai take had'asu saikuma kaimasa abinci Wanda Rafi'a tajuri kawowa kullum bada sanin mamaba.
Ranar yashirya fita, tsaf yafito yanata zabga k'amshi, idan baka saniba bazaka ta6a cewa yana cikin wata damuwaba, fuskarnan fayau sai Annurin hak'uri ketashi, saidai duk Wanda yasan ya Umar ya kalleshi a yanzu yasan ya rame sosai, sai dogon hancinnan dayay ziri-ziri, jin k'amshin turarensa ya yawaita awajen yasaka Asma'u dake kwance d'agowa tana kallonsa, tashi tayi zaune.
Shima sai binta yakeyi da kallo, gani yake dukta canja masa, kamarma tayi bak'i, tausayinta ya d'arsu azuciyarsa, zama yayi abakin katifar kusada ita, cikin taushin murya ya ce, "Husna bakida lafiyane?.
Kwalla suka cika mata idanu, kanta ak'asa ta ce, " a'a lfyta k'alau".
Shiru yayi yana nazarinta, zuwa can yasauke numfashi, d'aya daga cikin wayoyinsa yazaro saga aljihu, yacire sim Cart d'insa sannan ya kalleta, ina cim cart d'inki?.
Yana nan, tafad'a kanta ak'asa.
"d'akkomin".
Tashi tayi tamkar kazar da k'wai yafashema aciki, yabita dakkalo sanye take cikin sket da Riga na shadda ruwan ak'asa mai turuwa, ada kayan sunmata kad'an amma yanzu data rame sunmata yawa.......
Katse masa tunani tayi da mik'a masa sim Cart d'in, baice komaiba ya kar6a ita kuma takoma inda takeda ta zauna.
Saka sim Cart d'inta yayi a wayar ya sassaita mata abubuwa sannan yamik'a mata yana mik'ewa.
Galala take kallonsa da waya a hannu, ganin haka ya d'ora mata bisa cinyarta, ya ce, " zanje wani waje yanzu Dan inaso nafara Neman aiki.
Muryar Asma'u a sanyaye ta ce, "ALLAH yatsare yabada sa'a".
Amin yafad'a yanamai jin dad'in addu'arta har cikin zuciyarsa.
Tunda yafice taketa juya wayar a hannunta tana murmushi, aranta ta ce, " ko wayarnan takai nawa?, Dan tabbas daga ganinta an sayeta da kud'i masu nauyi. Ta sumbaci wayar tana murmushi tareda shak'ar daddad'an kamshinsa dake tashi a jikin wayar, ahankali tafurta ALLAH yabarmu har Abadan my Umar Fharuk!, abinsona, farincikina, Nusfulhayat d'ina, hawaye suka gangaro abisa fuskarta.......
Kamar wadda akaima magana akunne tamik'e zummbur tanufi d'akinsa, takardar ranar tafara bulayin nema, amma duk inda take zatonta babu ita, tacije le6e tana yarfe hannun jin bak'in ciki, harta kama hanyar fita saikuma tadawo, bai k'yautu ace tacigaba da Barin d'akin da kayansa akan katifarnanba, komawa tayi tazauna ahankali tafara ware gogaggu da wankakku wad'anda babu guga, harma damasu daud'a aka had'a awajen, zagewa tayi sosai tagyara d'akin tsaf, tad'akko zanin gado ta shimd'a, kamar ance tad'an d'aga katifar saiga takardar ranar, wani murmushi jin dad'i tasaki, ta d'auki takardar ta ajiye gefe saida tagama gyara komai tsaf sannan tafice zuwa d'akinta cikeda son ganin abinda takardar ta k'unsa.......
Ya Umar kam koda yafita ak'ofar gida sukaci karo da makwafcinsa, hannu yabasa suka gaisa, ya Umar yamasa godiya sosai akan taimakon daya masa ranar, babu komai d'an uwa aii anzama d'aya, amfanin makwaftakar kenan.
Hakane gskyarka ngd sosai ALLAH yabar zuminci, saidai bansan sunankaba.
Murmushi makwafcin nasa yayi ya ce, "hakane. Ni sunana Muktar".
Masha ALLAH malam Muktar, nikuma sunana Umar Fharuk.
Masha ALLAH Umar, daga yau ina fata zamu zama abokan juna, matanmmuma zasu zama k'awaye.
Babu damuwa Muktar ALLAH yabarmu tare, suma saimuyi k'ok'arin had'asu.
Sund'an dad'e suna hira, sannan Muktar yamasa sallama yakoma wajen aikinsa, dama yayi mantuwane yadawo d'auka.
Ya Umar ma mashin ya tsaida yahau suka nufi inda zaije........
*_(((S))))......2017_*
*_Luv you all_*
[11/30/2017, 3:19 PM] ~π© ' π― π¦ π· πβ: π©π»βπ».........
π *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*π
*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*
*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_
*_NIKA'DAIππΌ WRITER ASSO........π_*
*_pageβ25-26_*
........Jikin Asma'u har rawa yakeyi wajen bud'e takardar, ta jingina da k'ofa bayan ta rufe tafara karantawa.