Showing 75001 words to 77995 words out of 77995 words

Chapter 26 - karayar arxiki COMPLETE

12 Jul 2024

9243

sunan riba, a lokacinma damuke samun nasa kullum zancensa bai wuce mijirasaba dai.
Gsky mom nafarajin tsoro.
Hummm baby wlhy bake kad'aiba, nikaina a tsoracen nake. Amma lfy naganki da kaya haka?.
Mom Hafiz ya sakeni.
Saki kuma baby? Miyayi zafi haka?.
Mom bar matsiyaci, tunda Safwan yatafi mana da kud'i 'yan kud'in dake hannuna suka k'are Hafiz yafara canjawa, idan Na tambayesa kud'i bazai bani isashsheba, saiyace aibani kad'ai baceba yanada wata matar harda 'ya'ya. nidashi kusan kullum dambe, yoni mom ina ruwana da matarsa ko wasu 'ya'yamsad'in wofi.
Jiya dasafe muntashi ko kayan abinci babu agida sainace yabani kud'i naje nasayo. Shinefa yad'auki 50k yabani, nikuwa uwarmi 50k zatamin, ko a sayen naman gidan bata k'areba. Nace masa sunyi kad'an, shikuma yacemin bashida wasu, haushi yakawoni wuya Na zageshi, shine ya mareni, aikuwa naita danna NASA ashar yabani saki uku.
Ayau Na saida gidan anjima kad'anma zasu turomin kud'ina.
Kuka mom tasaka tana fad'in lalai baby Na k'ara tabbatarwa bakida hankali wlhy, yanzunan saboda kud'in cefane kuka kashe aurenki? To ina motocinki?.
Yo mom run yaushe Na saidasu, d'ya kawai taragemin wadda nake shiga, itama bawani lafiya tacikaba.
Kuka sosai mom takeyi, lubna kam ko'a jikinta, Dan bataga a in kukaba anan. Saga k'arshema 'yayanta tad'iba suka fita. Urban shopping tayo musu mai yawa sannan suka dawo gida.

Turus tayi Dan ganin Suhaima zaune tana rabzar kuka, dukta rame ta lalace, said urban ciki rindimeme.
A sanyaye Lubna tazauna tana fad'in Suhaima kekuma lfy? King a kuwa yanda kuka koma Lamar matar k'auye?.
Kuka Suhaima takuma fashewa dashi tana fad'in badole kiganni hakaba baby, Ramadan ya niyyar kasheni da raina. Kiduba duk alaccin danaima Ramadan arayuwa bai ganiba, dukda nagane bashida komai nayimasa sutura Na zauna dashi. Yau kusan wata biyu kenan yamin wayau da dad'in baki yakar6i 'yan sauran kud'in hannuna way zai fara kasuwance, nikuma daboda yarda danayi dashi Na d'auka Na bashi, Ashe tikitin iskanci da karuwai a hotels yabud'e da kud'in ban saniba. ahankali yabi duk ya said a motocin gidan, Ashe hard a gidan ban saniba. Yau dasafe saiga wad'anda suka sati gidan sunzo wait sun bamu notes nanda gone my kama gabanmu. Ina cikin tararrabi da jiran Ramadan saiga ta karda ya aikomin wai ya sakeni kuma nafara zuwa ganin likita saboda shi an tabbatar NASA yanada HlV😭, Yakima tabbata Nina INA tareda iya, tak'are maganar da rushewa da matsanancin kuka😫.
Data mama har Lubna ma kukan sukeyi, su twin's dai said kallonsu sukeyi da 'yan aikin gidan.

Yau sukam duniya tamusu gwatson k'yanwa🙁. ALLAH yasa mudace ameen.



*_Bayan wash shekaru._*
Abubuwa sun faru dayawan gsk, ciki harda ciwon 6arin jiki data kama mom, sakamakon Nina Safwan da akayi ankamashi da hodar iblis shida wasu abokan kasuwancinsa su takwas. Harma an Yankees musu hucin Lisa ta hangar harbewa, wannan yasa ta yanke jiki ta fad'i awajen, tundaga nan babu wani sashe Na jikinta take mitsi.
Wannanne yasa jinya tazamema Lubna biyu, damage ga Suhaima kwance waken shekara d'aya kenan, tuni ta haihu mace, yarinyarma hartayi wayo, abaya tana shan magani dad'n kukad'ad'en dasuka rage musu, dawanda Ameer take taimaka musu, Dan yanzu shikad'aine mad'an a in hannu acikinsu. Shiyyasa yad'ik'e matarsa GAM, Dan itace sila ta zamowarsa Na gari harya iya rik'ekansa, yanzuma yaransu biyu.
Suhaima tana ganin tasamu lafiya tafara wasa da shan magani, shinefa ciwo ya dirkusar da ita.
'Yan aikinsu kuwa aituni kowa ta gudu ta barsu. Abinci Kansas badan Ameer ba dabasuciba kuwa, duk wata yana k'ok'arin kawo Mayan abinci gidan.
Su 'yan biyu kuwa dasuka zama 'yammata aii saidai add'a kawai, damage dance yaro yana koyine da abinda yagani anayi agidansu, yanzu haka saisu had'a kwana biyu NASA gidan, sunacan yawon gantalinsu.
Kuban tayi kuka harta rasa hawaye. Said yanzu tunanin ya Umar me addabarta,Neman ganinsa takeyi ruwa a jallo amma tarasa hangar hakan........



★★★★★
Su ya Umar kam aii saidai muce Alhmdllh, k'ofofin arzik'i sun kuma bud'ewa tako ina, dagashi har Asma'unsa sun murje sunzama manya ababen Alfahari ga dangi.
Yanzu haka yaransu uku, bayan fodiyo ta haifi mai sunan inna Binta kenan, amma suna kiranta Batul, sai kuma mai sunan ya Umar, wato Umar Fharuk, shima suna kiransa Affan.
Tuni ya canja musu gida mai k'yau da tsari, rayuwarsu sukeyi cikin soyayya da k'aunar juna, ga 'yan 'ya'yansu ababen sha'awa da birgewa, dolene ka gansu su baka sha'awa.
Fatee, Rafi'a, Hasiya duksun haihu, suma anatashan soyayya suda mazajensu.
Hakama 6angarensu inna dash mama, komai Alhmdlh, Anty sa'a da anty Saratu, da mufida sumadai komai normal, kiwa yana cikin kwanciyar hankali.
Abotar yazeed da ya Umar da Muktar kam said abinda yay gaba, sun k'ulle kansu tsam, basa sakeda wata kwafa dazata rusasu, hakama matansu da 'ya'yansu......




★★*★★*★★*★★
Amrah da Afrah na zaune afalon k'asa, duksun baje kayan sweet da samarinsu suka siya musu. Lubna dake zaune agefe tana d'urama mama ruwan tea Dan shine kad'an yake wucewa, shima saida cokali ake d'an zirara mata, lubna dukta lalace tayi bak'i Lamar ba Lubnar nan 'Yar gayuba, tafita hayyacinta sosai, ayanzuma saita had'a kwana hud'u batayi wankaba saboda damuwa da tashin hankali dasukai mata yawa.
Mama ma dake kwance wadda idontane kawai ke aiki, tanata kallonsu Amrah da hira ta kaure a tsakaninsu kowa Na kid'a saurayinta yafi Na 'Yar uwarta.
Da k'yar Suhaima dake kwance gefe ta ce, "Afrah tazo tabata ruwa tasha".
Baki Afrah ta turo gaba tana k'unk'uni, dak'yar tabata ruwan tana yatsina fiska Dan k'yank'yaminta sukeyi yanzu. Hawayene ya ziraro a kumatun Suhaima, tatuna kanta ada, dayanda tayi holewar datafi tasu Amrah. Amma gayanda rayuwarta takoma?.
Lubna ta harari Amrah, itako babu tsoro tarama tana fad'in kijimin momy, minamiki zaki harareni?.
Afrah ta ta6e baki tana danna sweet abaki.
Itadai Lubna batace komaiba.
Saican kamar an tsikari Afrah ta ce, " momy! Yau munga wani abin mamaki wlhy.
Kamar lubna bazata tankaba, saikuma zuwa can ta ce, "nami?."
Humm mall d'in da guys d'inmmu suka kaimu dayagama had'uwa, wlhy momy komai akwai awajen, Raine kawai ba sayarwa, yafa had'u sosai.
Amma kinsan mi muka gani?.
Hoton wani k'yak'yk'yawan mutum shida matarsa da yaransu uku, shine mai wajen, wlhy abin al'ajabi tana masifar kama da Amrah.
K'armin d'ansa kuwa kamar ni nahaifeshi saboda kamar damukeyi. Tab ai kamar ta 6aci.
Amrah ta kar6e zancen dafad'in aii wlhy Afrah har mukazo gida inata tunaninsu. Nidai haka kawai naji ajikina munada dangan taka dash.
Gaban Lubna ne yafad'i.
Da sauri ta ajiye kofin tea d'in datake bama mom, ta ce, ''ya sunansa?."
Ummmm anfa rubuta ajikin pic d'in. Afrah yama? Nikam Na manta.
Da sauri Afrah tace, matardai sunanta Asma'u, shikuma mutumin Umar Fharuk, sai yaranau Usman fodiyo da batul, Affan......
Zumbur Lubna tamik'e tana fad'in kutashi muje Ku nunamin wajen.
Wani kallon sama da k'asa sukai mata, sai kuma suka bushe da dariyar shak'iyanci. Cikin dariyar Amrah ta ce, ''gaba momy ahaka zaki bimu wajen kamar an kwatoki daga bakin kura?.
Inama laifin kid'anyi wanna ki canja kayannan.
ALLAH mom tsamimafa kikeyi, yau kwananki uku bakiyi wankaba, shiyyasa ko kusadake banason zama.
Hawaye suka cikama Lubna ido, wai itace yau 'ya'yanta kekiranta da tana tsami? Lallai rayuwa kenan, ta tababata alhakin Umar kad'ai ya Isa tatsinci kanta fiyema da yanda take ayanzu.
Haka tatafi tayi wanka, sannan tazo suka tafi, suka bar mama da Suhaima agida, Dan harda Habiba d'iyar Suhaima suka tafi.



Hankalin Lubna yatashi sosai daganin hoton ya Umar da Asma'u. Da alama 'ya'yansune taredasu ahoton.
Jiki a sanyaye suka k'arasa indasu Harris da sadam ke zaune.
Bayan Lubna ta gaishesu Dan Amrah da Afrah babu wannan atsarin tarbiyyarsu, NASA Haida kowa, ko gidan Ameer sukaje haka sukeyi. Lubna tafara tambayarsu ko Alhji Umar nan?.
Sudai su Harris kallonsu kawai sukeyi, Dan kokad'n bai gane Lubna ba, shidama Sadam bai santaba, amma idonsa nakan su Amrah daketa taunar cingam k'as-k'as, kamarda Amrsah takeyice da ya Umar tabashi mamaki, hakama Afrah da Affan.
Harris ne yay k'arfin halin fad'in baya nan yaje gida yanzunnan kai yara.
Da sauri Lubna ta ce, "kozaku bamu kwataccen gidan Dan girman ALLAH?.
shiru sukayi suduka, Dan sukam bama su yards dasuba, kowadai yasan yanda rayuwar ta lalace yanzu.
Lubna ta rissina kamar zata duk'a tana k'ara rok'on Harris, Dan itama bata ganeshiba.
Sadam ya ce, ''baiwar ALLAH kekam miyasa kike son ganin ya Umar.
Dak'yar ta iya had'iye yawu ta ce, " ni tsohuwar matarsace, wad'annan kuma 'ya'yansane. Ta nunasu Afrah.
Idanu Amrah da Afrah suka zari, suna fad'in 'ya'yqnsa!!?.
Can kuma Harris tayi wani uban zallo shima yana k'qrema lubna da twins kallon mamaki.
Tabbas alamu dayawa sun nuna gskyar Lubna, musammanma kamainnin Amrah da ya Umar.
Cikin masifa yakirasu waje, ana cikin haka saiga yazeed, yatanbayi abinda ke faruwa Harris yafad'a masa.
Hannu Yazeed yad'aga masa ya ce, "a'a daina korarsu.
Kushiga Mora na kaiku.
Badan Harris yasoba yazeed yad'auki su Lubna amotarsa sai gidan ya Umar.
Afrah dake gaban mota tuni har zuciyarta ta k'yasa yazeed😨🤣.



-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-
Asma'u dake zaune Afalo taci wwalliyarta, gefenta masu aikintane suna zaune sai hira Duke zuba mata tana dariyar. It's babu ruwanta da German kan nan irinna hajiyoyi.
Da gudu fodiyo da Batul suka shigo falon suna kiran Ammi! Ammi!! Mundawo mundawo.
Itama cikin azama tamik'e ta taresu Rana farincikin dawowar 'ya'yanta ababen alfaharint.
Suna cikin murnar saiga ya Umar yashigo d'aukeda Affan ahannu, shima sanye cikin Mayan makaranta.
Shida Affan d'in tahad'a ta rungume tsam ajikinta, shima ya Umar k'yak'yk'yawar tarba yamata tareda manna mata Sumba agoshi.
Affan ya ce, ammi yau antynmu tace Nafi kiwa kokali a class d'inmmu.
Masha ALLAH autana, haka nakeaonji.
Ya Umar ya ce, ''autan lfy hajiyata, idanmma zaki dage ki Dage, autana bai zoba har yanzu, shine zaizama k'anin Affan na tara.
Sosai Asma'u tazaro ido, gaba ya Fharuk rufamin asiri mana, ukunnan ma aii ansha fama kafin suzo.
'Yar dariyar ya Umar tayi, ya ce, "ahaka kuma nake jiran tara nan gaba.
Habadai wasa kakeyi wlhy.
Said a suka zauna sannan yace babu wani wasa da gsk nakeayi.
Shiru tamasa taje takawo masa abinsha, sannan tafara cirema Affan Mayan makarantar.
Suma su fodiyo duksun cire, kowa yama k'ok'arin nuns mata homework d'in da aka basu, sukaji sallamar yazeed.
Yaran kowa ya yard a abinda ke hannunsa suka kwasa da gudu suna fad'in oyoyo dady.
rungumesu yazeed tayi, shima yama fad'in oyoyo yarana.
Ya Umar da Asma'u dai kallonsu kawai sukeyi suna dariya.
Lubna dasu Amrah kam suna baya said kalle-kalle sukeyi agidan.
Saima yanzu su Asma'u suka gansu.
Ko kad'an Asma'u bata gane lubna ba bare su Amrah.
Amma kuma kamar dasukeyi dashi yasakata taura musu idanu.
Shikam ya Umar suna shigowa yaganesu suduka, Dan d'azu yaga Afrah da Amrah a mall d'insa tareda wasu samari biyu. Kuma yaji ajikinsa 'ya'yansane. Har hawaye saida tayi alokacin, yana k'ara yima Lubna ALLAH ya Isa, Dan asanadinsa yaransa suka lalace, shidai bai ta6a Yar kowaba tunyana saurayi bare yanzu.
Amma gawasu suna lalata 'ya'yansa ta dalilin halin ma haifiyarsu.
Yazeed ne yacema su Lubna su zauna.
Duk suka zazzauna.
Asma'u takawo musu abubuwan motsa Baku.
Ran ya Umar a6ace yatashi zaibar falon. Da sauri yazeed yarik'e hannunsa yana fad'in karfa ka manta, a tsakaninmu babu jayayya.
Idon ya Umar yayi jajur saboda 6acin rai, yajuyo yana kallon yazeed, kayi hak'uri d'an uwana, wannan jayayyar tasha banban da wadda bakaso.
No Umar duk d'ayace, Dan ALLAH kayi hak'uri kazauna plss.
Saida ya Umar yay kwafa sannan ya zauna. Amrah da Afrah kam aii tuni sun nutsu, Dan basuga wajen wargiba.
Sudai su fodiyo suna tsaye agefe suna kallon iyayensu.
Lubna ta Haida ya Umar, bai amsa mataba. Bata damuba itama, ta kalli Afrah da Amrah tace augaidashi.
Amamakinta saigashi sun gaidaahi, harma da Asma'u.
Sumad'in bai amsa musuba, saima cikin tsawa ya ce, "Lubna! Miyakawoki gareni? Dawane shiri kuma kikazo yau?.
Tsawar babu Wanda bata razana a falonba, Affan ya k'ank'ame Asma'u yana kuka, Dan basu ta6a ganin baban nasuba a irin wannan yanayinba.
d'aukarsa tayi tana lallashi, fodiyo da Batul ma duksun mak'ale jikin yazeed.

K'asa Lubna tadiro tana kuka da neman gafarar ya Umar.
Ka gafarceni nida iyayena da 'yan uwana Umar, wlhy duniya takoyar damu hankali, munyi nadamar abinda mukaimaka. Umar yanzu bamuda abin jayayya Sakai, dukiyar damuke tak'amar da ita tak'are. Ciwo da bak'in cikin rayuwa sune suka maye gurbin arzeek'inmu.
Umar kayi hak'uri, ga 'ya'yankanan zan maido maka, Dan ALLAH karkace bazaka kar6esuba, Umar wlhy nasan nikaina ina gab da kamuwa da wani ciwonne, rayuwar dasu Amrah da Afrah suka saka kanau kawai ta Isa lafiyata baraza......
Da sauri ya Umar yad'aga mata hannu a hasale, yana fad'in suka saka kamsu, kokuwa kika sakasu ciki. ALLAH shine zaidata van ta6a zina da 'Yar kowaba amma ta sanadinki ga 'ya'yana sunayi. Lubna kin cuceni, kin zalinceni, yama za'ayi Na yafe miki?, kin rabani da 'ya'yana Ashe badan ki kula dasuba? Saidai ki watsa musu rayuwarsu? Wata 'yan kwallah ta taru masa a gefen ido......
Yazeed da Asma'u ne suka saka baki wajen taya Lubna Neman gafara.
Dak'yar ya hak'ura, Afrah da Amrah aukazo suka rungumeshi suna kuka suma. Yauce rana tafarko dasuka gane kuskuren dasukaso tafkawa rayuwarsu, ALLAH ya taimakesu ya tsaresu basuta6a bama wani saurayi kansuba, saidai soyayyar shan minti da romances da samarin sukanyi dasu.
Shima ya Umar rungumesu yayi, yau ga 'ya'yana sundawo gareshi, bayan kwacesu da akayi daga hannunsa Na tsawon shekaru.
Daga nan wajen Asma'u sukazo itama suka rungumeta, basu manta da itaba, suka rungume 'yan kannensu dabasu sansuba.
Lubna sai dad'i takeji, ga hawauenta sunk'i tsayawa, ta rungume su fodiyo itama tanajin dayanzu k'ila itace ta haifesu, amma San zuciya da rud'anin duniya yahana tsaida zuciyarta waje d'aya. Aigatanan a makarantar nadama.......

Anan tabarsu Twins kamar yanda Asma'u ta buk'at.
Aiko hakan yamusu dad'i, saijan 'yan k'annensu sukeyi ajiki, suma dayake sunada saurin sabo harsun saki jiki dasu.

Washe gari, ya Umar yaje har gidansu Lubna d'in yad'auki mom da Suhaima yakaisu asibiti.
Mom sai kuka takeyi, babu bakin magana, hakama Suhaima tanata kuka da Neman gafarar ya Umar, tasanar dashi sune itada mom sukaita zuga Lubna, akan tarabu dashi, run bata aminceba harta amince.
Ya Umar saidai kawai yayi murmushi ya ce, ''ya yafe musu.


*+++++++++++++*.
Cikin wata biyu jikinsu mom da Suhaima yayi k'yau, Dan yanzu mom nad'an iyayin magana kad'an ², dukda dai bata fita sosai, hakama Suhaima alhmdlh, jikin nata yayi, k'yau.
Mom sai sakama Ya Umar albarka takeyi da k'ara Neman gafararsa.
Koda yaushe yakance ya yafe musu.
Asma'u kam bata ta6a gazawa wajen kawo musu abinciba kullum safe da yamma.
Duk sanda Lubna ta gansu dasu da 'yan 'ya'yansu saitayi kuka, da nadama, mai makon Umar yayi baya, kullum saima gaba yake k'arawa. Tagujeshi saboda *,"karayar arzeek'i"_* yau gashi shine yake taimakonsu da dukiyarsa.
Tayi kuka harta godema ALLAH, tayi nadama rayuwarta, shiyyasa akace idanu gemun d'an uwana Yakama da wuta to yayyafama naka ruwan. Idanu kuma ALLAH ya jarabci bawansa badan bata sonshi baneba.
Itakam taga zahiri akan Umar.
Itada 'yan uwanta kam duk ga yanda tasu rayuwarsu tak'are, sun rasa alokacin Dana Umar yadawo.
ALLAH ka shirya zukatanmu, ka ganar damu gsky.

Ni bilynku nace ameen😭.


Alhamdulilahi.


Anan nakawo k'arshen wannan d'an littafi NASA mai suna *_KARAYAR ARZEEK'I_* abinda nafad'a saidai, ALLAH kabani lada, Wanda nati kuskure ALLAH ka yafe mini.

Ina godiya ga d'umbin masoyana, musamman masu bibiyar buk d'innan Na *_karayar arzeek'i_* ngd sosai, ALLAH yabar zuminci, Nina INA k'aunarku da alfahari daku aduk India kuke.

*_Writer's 'yan uwana kuma inata mik'o godiya agareku, ALLAH yabarmu tare, yak'ara dank'on zuminci, ALLAH yak'arama kowa baseeer da hak'urin typing._*


Bilkisa Ibrahim
Bilyn Abdul.

Marubuciyar.
_rashin Sani_
_auren k'addara ko biyayya?._
_k'anwar uwace ko kishiyar uwa?_
_nida aminiyata_
_kukan kurciya_
_sabon al'amari_
_nawaff_
_ban saketa ba_
_Abdul-maleek bobo_
_karayar arzeek'i_


*_Sharhin littatafaina 10 nanan zuwa agareku insha ALLAHU_*


_NGD SOSAI, ALLAH YABAR ZUMINCI._


*_BILYN ABDUL CE._*👌🏼😁





*_(((S))))........2018_*
*_I love you more...._*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login