Showing 30001 words to 33000 words out of 77995 words
Saina dawo yafad'a yana k'ok'arin ficewa.
Adawo lafiya sukafad'a suduka, shikuma yafice.
Yana fita Maman Faisal tashiga yima Asma'u fad'a (Dan ta girmeta gsky, zata iya zama sa'ar Anty saratu ma). Haba Asma'u yanzunan mijinki zai fita bazaki masa rakkiyaba? Idanfa kika saka wasa wata zatazo ta kwace miki miji. Nakula kinada sakaci sosai. Hakamafa d'azun abirkice kika fito, kamar wadda taje wajen dodo. Kodai akwai matsalane?.
Girgiza kai Asma'u tayi, Dan aganinta baikamata tabama Anty Saddiqa labarin abinda yafaru itada ya Umar ba.
Maman Faisal tacigaba da fad'in to gsky ki gyara kinjiko. maza sunason ana kula dasu tamkar kwai a cokali. Indai kinama namiji haka to tabbas zai koma miki tamkar jinjiri wlhy.
Hakane anty amma wlhy ya Umar daban yake, yacika tauri dayawa. Wani lokacinma dolene kiji matuk'ar tsoronsa.
Hummm Asma'u kenan, duk taurin namiji mace saita sakashi laushi. Shawarar dazan baki ki fara karatun Hausa Novels, insha ALLAH zaki k'aru matuk'a da ilimin zama da miji. (Musamman idan kin had'u da buk d'in marubutan dasuka san Kansu) akwai wasu buks dana karanta na bilyn Abdul, na tabbata zaki k'aru acikinsu.
To a ina zan samu?.
Bak'yayin charting?.
Inayi da, amma yanzu banayi.
Tom Indai ba mijinki ya hanakiba kikoma yi zan baki no. d'inta.
To Anty ngd sosai.
Maman Faisal tamik'e dak'yar saboda tsohon ciki datakedashi, haihuwa yau ko gobe, bara naje gida, nasan sunacan sunamin 6arna tunda sukak'i dawowa.
To Anty ngd.....
..................................
Su Lubna anata hidimar biki, shiri sukeyi na garari Dan bikin namasu akwaine babu k'arya.
Komai awadace yake tafiya, party kam aii anshirya yafi kala 10, su Lubna sune amarori k'irjin biki.
Yau kamu Dan haka sukaci uwar kwalliya nawani sky blue d'in less itada Suhaima, sai walk'iya sukeyi, idan kagansu kai kace sune amaren, bakowa zaiga Lubna ya ce, "ta ta6a aureba bareba harda yara biyu.
Harabar gidan suka fito inda abokan Ameer suke birjik, duk sunci wankan bak'in wando da yellow d'in Riga, wanan shine kwalliyar kamu na maza.
Matankuwa yellow d'in wando da bak'ar riga. Sudai su Lubna basu sakaba.
Wani abokin Ameer ya ce, " kai yarinyar canfa tawuce dani wlhy, wai k'anwar Amee CE?.
Inaganin k'anwarsace, ammafa in k'aramar tafimin k'yau, kasanni ko aure zanyi banason yar 20+ gsky. Nafison daga 16 zuwa k'asa.
Dariya abokin yayi, ya ce, "humm aikai mugunta kakeji.......
Wucewarsu Luban tagabansu tahanasu cigaba da hirar. Sukam basusan sunayiba, sun wuce sun barsu da k'amshinsu.
Mota suka shiga, Lubna tajasu suka bar gidan.
Kaitsaye hall d'in daza'ayi kamu suka nufa. Dangin amarya Suma sunyi shirinsu sosai, amarya tad'auki k'yau, naira tayi kuka agidannan. Su Lubna sai nan nan akeyi dasu, sukuma suna fankama da Nuna isa, su adole dangin miji.
Babu dad'ewa su Ameer suka iso. Ba awani tsaya 6ata lokaciba aka fara gudanar da kamu Wanda yak'ayatar.
Sai wajen 9pm aka tashi, ansha casu kam babu k'arya. Idan kuga yanda Lubna tadage tana rawa saikusha mamaki......
____________________
Tunda Anty Saddiqa tafad'a mata idan tana sakaci wata zata kwace mata miji tashiga damuwa, tana matuk'ar son mijinta, tanajin ya Umar yafi sauran maza awajenta, idan akace wata zata iya kwaceshi agareta takanji tamkar an soki zuciyarta da mashi.
Wasu zafafan hawaye suka gangaro bisa kumarunta. Bata sharesuba, saima cigaba da matso wasu datayi.
Duvanta takai ga agogon d'akin, karfe 9:23pm amma har yanzu ya Umar bai dawo gidanba, tun fitar d'azu da yamma. Tana mamakin ina yajene har zuwa wannan time d'in?.
(Zuciyarta ta ce, ''yaje tad'i.") Rushewa tayi dawani kuka mara dalili....
Ni dariyama tabani aradu😂.
Tana nan tana kukanta saitaji motsin bud'e k'ofa, da sauri tad'ago tana kallonsa. Ya Umar ne sanye cikin kayan barci, da'alama ma yadad'e da dawowa gidan.
Shima kallonta kawai yakeyi amma fuskarsa ko kad'an babu walwala. Cikin d'akin yak'araso, yaja tum-tum yazauna har yanzu idanunsa akanta. Itadai nata na k'asa, ga hawaye sha6e- sha6e a fuskarta.
Ahankali ya firzo huci daga bakinsa yana mai kauda kansa daga gareta. Ko kad'an bayaso yaga mace na kuka. Shi mutumne mai tausayi sosai musamman akan mata.
Yakuma dawo da kallonsa gareta, kukan mikikeyine? Ko har yanzu bakida lafiyar?.
Shiru tamasa, bata d'agoba, bakumata tanka masaba. Dan zuciyarta wani irin zafi takeji, gani takeyi kamar da gsk daga tad'in yake.
Cikin d'an fad'a-fad'a ya ce, "wai bakijinane!!?.
Da sauri tad'ago takalleshi, ganin yanda yakuma tur6une fuska sai tsoronsa yakuma kamata. Bakinta na rawa ta ce, "bakaine kaje tad'iba."
Tad'i!?. ‘ya Umar yafad'a cikin sigar tambaya da mamaki.’
Itama kanta tad'a tana wani kumbura baki.
Siririn tsaki yayi, amma batajiba. Ya ce, "kewaye yagaya miki naje tad'i?.
Gabantane yafad'i, dan kuwa dai zuciyartace ta sak'a mata, bawanine yafad'a mataba.
Shima ganin haka sai kawai ya girgiza kai. Yakuma yin k'aramin tsaki tareda fad'in kinga ni bar wannan banzan shirmen naki gefe, magana nazo muyi. Tashi kije ki wanke fuskarki kidawo.
Ahankali tamik'e kamar wadda kwai yafashema aciki tashiga bayi. Fes tawanke fuskarta sanan tadawo gareshi.
Saida sukaja wasu 'yan mintuna sannan yay gyaran murya:- inaso kibani hankalinki nan muyi magana. Kanta ta jinjina masa alamar to.
_d'azu fitar danayi naje office d'in su muktar ne, dama tun kwana hud'u daya wuce munyi magana, ya ce, " nabada takarduna zai kaima ogansu yanemamin aiki. Dafarko ban aminceba Dan narigada na fidda raina ga aikin. Amma saiya nace sosai da magiya da kawomin hujjoji akan fa'idar Neman aikin harna amince.
Jiya yakai takardun, yaukuma ogan nasu saiya buk'aci ganina. Shine Muktar yakirani ina shago yasanarmin. Wanna dalilin yasa nashirya naje.
Tom saidai kuma abinda yagirgizani shine ogan su muktar abokine ga dad (mahaifin Lubna) akwai dangantaka mai k'arfi a tsakaninsu ta kasuwanci gsky, Dan sanda ina k'arkashinsa yasha aikena awajensa.
Abu na biyu kuma shine Alhaji Ahmad mai kano yad'aukeni aiki ak'ark'ashin kamfanin nasa, ya ce, "kuma yana buk'atar bayani daga gareni akan abinda yasa muka rabu da mahaifin Lubna.
Yabani dama daga nan zuwa gobe, idan nafad'a masa yace zuwa Monday zan fara aiki.
Yakika gani nafad'a masa gsky?, kokuwa na hak'ura da aikin kawai?. Ban fad'ama kowa maganarnanba saike, koshi Muktar baisan yanda mukayiba.
Asma'u tasauke ajiyar zuciya sanan ta gyara zama. Yaya nidai abinda nake gani kafad'a masa kawai, Dan ALLAH yagani bacin amana ko cutarwace taravaku da mahaifin anty Lubnar ba, yanzu kuma aiki za'a d'aukeka idan kayi kuma za'a biyaka, kaga kuwa guminka zakaci bawai a k'ark'ashin wani zaka zaunaba.
Kuma ina ganin koda kafara aiki tom nikuma saina cigaba da lura da shagon harmuga abinda ALLAH zaiyi.
Sosai ya Umar yagamsu da bayaninta Dan haka ya jinjina mata kai alamar gamsuwa, gawata k'aunarta na ratsashi, wani lokacin idan tayi Abu tamkar wata babba. Idan shirmen yamotsa kuma sai an sauke masa cikin tirela😂.
Asma'u tayi murmushi mai kwantar da zuciya, ya Fharuk natayaka Murna, ALLAH yabada nasara da sa'a.
Ameen Husna ngd.
Filo yajawo ya kwanta.
Gaban Asma'u ne yafad'i, karfa asake irin ta ranar.
Kamar yasan tunanun datakeyi saiya mik'e zaune yana fad'in yau baza'a bani abinci bane?.
Da sauri Asma'u tamik'e, Dan danan tacika gabansa da kulolin abinci, tashi yayi zaune tazuba masa komai.
Yanzukam babu laifi yad'an saki fuskarsa, Dan yanacin abinci yana satar kallonta. Sukan had'a ido lokaci-likaci, ganin haka ya Umar yad'auke idonsa gaba d'aya daga kanta yamaida ahankali kan cin abincinsa.
Kamar daga sama yaji Asma'u ta ce, "ya Fharuk inada tambaya?."
Idanunsa masu haske yad'ago yana kallonta, saida ya had'iye abincin bakinsa sannan ya ce, ''ina saurarenki?."
Shiru nawani lokaci tanata juya maganar a zuciyarta, kamar tayi kamar kartayi, can wata zuciyarta na angizata akan ta tambayesa da ace tazauna cikin duhu.
Jin tayi shiru yace yadai? Kokin fasane?.
A'a. Dama inason tambayarka minene maganin mata?.
Sosai ya ware idanunsa akanta. Aransa yace mike damun kan yarinyarnan?. (Inhar bai mantaba Lubna ta ta6a fad'a masa kayan k'arin ni'ima sune ake kira Maganin mata. Dan yata6a rutsata tana sha saiya tambayeta maganin minene wannan?. Dayake Lubna macece da batada kunyar Abu kai tsaye, musamman ga mijinta, sai takecemasa maganin k'arin ni'imane)..........
Ganin yayi shiru yadaina cin abincin, kuma gashi ya tsura mata idan ko k'yaftawa bayayi saitasha jinin jikinta. ad'arare ta ce, "ya Fharuk akwai matsalane?.
Girgiza mata kai kawai yayi yacigaba dacin abincinsa, Dan aganinsa dawata manufa daban tamasa tambayar, ashema k'aryar gudunsa takeyi, tasan komai, tana raina masa hankaline kawai.
Wani d'an murmushin gefen baki yayi, shikad'ai yasan miya kitsa wa zuciyarsa.
Asma'u kam tayi gum, Dan sosai tasha jinin jikinta akan tambayar.
Harya kammala cin abincin babu maicewa da d'an uwansa k'ala.
Bayan ta gyara wajen ta kwashe kwanikan tadawo d'akin. Inda tabarsa anan ta iskesa.
Ya ce, " kinason amsar tambayarki?.
Kanta ta jinjina da sauri.
Yalumshe idanunsa yana wani murmushi na musamman Wanda Asma'u bata ta6a gani daga gareshiba.
Zan baki amsar tambayarki amma nima zan tambayeki Abu biyune, idan kinsani bazan amsa mikiba. Idan baki saniba zan had'a duka nabaki amsa, amma bayauba, zan baki amsar Abu d'aya a daren yau, biyun kuma saida safe.
Bata kawo komai arantaba ta ce, "to ina saurarenka.
Mizakiyi da maganin mata?. Na biyu:- miyasa kika tambayeni.
Gefen wuyanta ta Sosa Dan batasan amsar dazata bashiba.
Ganin haka ya ce, "shikenan, tashi kiyo alwala zan baki amsar farko dakika tambayeni...............
_kuyi hak'uri danifa, yanzu bakwajina yanda ya kamata, wlhy nayi matuk'ar busy ne kawai, kutayani da addu'ar samun nasara kawai._
*l Love you all*😍
*_((S)).....2017_*
*_luv you all_*
[12/12/2017, 10:20 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻💻.........
💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*💎
*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*
*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_
*_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO........😜_*
*_page→37-38_*
..........Bata kawo komai arantaba tatashi zuwa Bathroom, babu dad'ewa tafito d'aureda alwala.
Ya Umar baya d'akin, da alama shima yaje d'auro Alwalane.
K'ok'arin canja zanin sallah tafara, saigashi yashigo. Babu Wanda yace da d'an uwansa k'ala. Ya Umar yad'auki sallaya ya shimfid'a musu guda biyu.
Sallah suka gabatar raka'a biyu. Ya Umar yadafa kanta yay addu'a kamar yanda addinin islama ya koyar mana. Sai ayanzu wani tunani yazo zuciyar Asma'u. Gabanta yashiga fad'uwa da dukan tara-tara. Duk addu'oin dayaketa kwararawa bata fahimtar komai, kawaidai tad'aga hannunta samane. amma ko ameen tagagara furtawa. Nashiga uku ni Asma'u! Shin mi ya Fharuk yake nufine? Nidai nasan wannan sallace da MAZON ALLAH (SAW) yakoyar damu muyi aranar da aka kawo mace amatsayin amarya. To amma shi ya Fharuk miye tasa manufar?. ‘wani ras gabanta yafad'i yayinda zuciyarta tabata wata bahaguwar amsa.’
Bata dawo hayyacintaba taji ya Fharuk na girgizata. "K!. Tunanin mi kikeyine haka?.
Firgigit tadawo hayyacinta, sai mazurai takeyi da idanu. Murya na rawa ta ce, " ya Fharuk mizai farune?."
Kallonta yayi kamar zaiyi magana, saikuma yafasa ya mik'e, saida yazauna abakin katifar sannan ya ce, "mizai faru, kamarya?.
Shiru tayi Dan gane kato6arar datasoyi. Baikamata ta nuna masa tama fahimci wani abuba, tunda yamaidata k'aramar yarinya. Itama bara zata nuna masa tanada wayo fa.
Bai kuma cewa da ita komaiba taga yad'auki keys d'in shago yafita. Ta k'ofar cikin gida yabud'e, mintuna kad'an yadawo hannunsa d'aukeda yogot mai sanyi.
Sau d'aya takalleshi ta kauda kanta. Shima zama yayi da yogot d'insa ahannu. Husna bani kofi biyu.
Tashi tayi tamkar mara laka ajiki tafita batareda tayi koda tariba.
Ya Umar yabita da kallo yana murmushin mugunta, 'Yar rainin wayo zaki fad'a musu yau da bakinki. Kigama wani langa6e-langa6en jikinki yau babu fashi saina mire sadakina.
Haka Asma'u tadawo da kofuna jiki duk a sanyaye. Tanata tunanin abinda zatayi Dan ku6ta daga tarkon ya Fharuk.
Kofunan yakar6a a hannunta, yazuba musu yogot mai dad'i, sai k'amshi yakeyi tamkar na kwakwa da abarba. Yacika Kofi d'aya sannan yamuk'o mata. Bismillah.
Fuska ta yatsine sosai, kaikace batada lafiya. ya Fharuk nak'oshi, ni koma abincin dare banciba saboda cikina yanamin ciwo sosai.
Dariyace taso kwacema ya Umar Dan ganin yanda Asma'u tawani narke fuska da narke jiki, amma dayake jarumin kamewane saiya dake, aransa ya ce, "zaki fad'a musu yarinya, ak'alla nabaki shekara 15 a duniya, duk wani shirinki a tafin hannuna yake. Amma afili saiyayi murmushi, ayya Husna sannu kinji, kar6a kisha kida kad'anne saina kawo miki magani. Ciwo bayason zama da yunwa aii.
Shiru tayi tana satar kallonsa, kardai yagano shirinta shima?.
Jin sanyi a hannunta ya katse mata tunani, kofin yogot d'inne yasaka mata ahannnu. Suka had'a ido, yad'age gira d'aya yana kallonta da ido d'aya, kona baki da kainane? Naga kamar kinajin jiki sosai.
Ahankali ta kad'a kanta alamar a'a.
Shima murmushi yayi yaja Kofi yazuba nasa. Hankali kwance yakeshan abinsa.
Itakam Duk a d'arare take. Dukma zamansa a d'akin ya gundureta, tak'agara yagama yatafi. Amma amamakinta koda ya kammala saitaga yayi mik'a tareda zamewa ya kwanta akatifarta yana fad'in Alhmdllh.
Tana nan tana cancana yogot d'in tamkar maiba yaron goye abinci har nawani adadin mintuna.
Ganin shan yogot d'innata bana k'are bane yasa ya Umar mik'ewa yafita. Kamar yasan mitake shiryawa a zuciyarta yacire key d'in k'ofar yatafi dashi.
Yana fita ta tashi da sauri danufin kulle k'ofa amma saitaga wayam babu key. Wani haushi da tsoro suka kamata lokaci d'aya, afili ta ce, "wayyo ya Fharuk dama mugunta ka shiryamin? Sai hawaye sharrrrr akumatu. Ganin kuka bazai mataba ta tuna dawani d'an kwalbar turare da Anty Saratu tabata ta ce, " tayi amfani dashi Daren farkonta bazata sha wahalaba. Cikin saurinta kuwa tafara lalubarsa, ALLAH kuwa yabata sa'ar ganinsa harma dawasu daban, bata ta6a amfani dako d'ayaba. Shid'in kawai ta d'auka sai wasu turare guda biyu masu fitinannen kamshi. Da hanzari tad'auka tashige bathroom. Duk yanda Anty Saratu ta koya mata haka tayi bayan tayi brush ta matsa ma bakinta wani Abu maid'an karan k'amshi. Sosai tagyara jikinta dukda tanata addu'ar ALLAH ma yasa karya dawo d'akin. Rigar barcin data d'akko maid'an kauri tasaka saboda yanayin sanyi da'ake ciki.
Agurguje tagama tadawo d'akin, katifarta ta haye, yau babu zancen doguwar addu'ar barci. Dandanan ta kammala taja bargo ta k'udundune har kanta, ita adole barci takeyi.
Shiru har minti kusan 20 suka shud'e kamar ya Fharuk bazai dawoba. Harta fara murnar rashin dawowarsa taji anturo k'ofa dawani fitinannen turare. Tasan ya Fharuk a 6angaren k'amshi babu sanya. Dukda k'irjinta na dukan uku-uku saida tayi murmushin jin dad'in k'amshin mai saka nutsuwa da farinciki...........
Jin shigowarsa bargon gabanta yasake sabon salon lugude. Da Sauri tamatsa danjin ya mannata da jikinsa. Murya a raunane ta ce, ''ya Fharuk! Lafiya kuwa?."
Lafiya k'alau, miya farune?.
Um....um...dama naga kazo nanne, yau bakajin barcine?.
Inaji mana Husna!, bagashi Nazo zanyiba.
Idanu ta kwalalo waje, kasancewar akwai wuta, kuma baikai ga kashewaba yaganta sosai yanda take zare ido kaikace taga wani ojujune. Ya Fharuk kana nufun anan zaka kwana?.
Umm. Kenifa kincikani da surutu. ranar dabakinki kikacemin kinajin sanyi, damma Nazo na taimakeki shine zakimin salo?.
Baki Asma'u ta turo gaba, afili ta ce, "yo aii ranar kace, nikuma yau sumul nake, babu abinda ke damuna.
Humyim dama d'azu k'arya kika zabgamin wai bak'yajin dad'i ko abinci bakiciba cikinki na miki ciwo?. Asmah arink'adaijin tsoron ALLAH. k'arya batada k'yau.
K'ara turo baki tayi gaba. Shikuma yasaka d'anyatsa ya d'alli bakin. Da sauri tadafe bakinta hannu tana kukan ta6ara wai zafi.
Baikuma bi takantaba harya mik'a hannu yakashe fitilar d'akin.
Asma'u batason duhu, shima kuma sarai yasani amma yakashe Dan Neman magana.
Tana ganin duhu tak'ank'amesa da sauri. Wayyo ya Fharuk kataimaka ka kunna, ALLAH bazan iya barci cikin duhuba.
Kunnenta yalaluba, ahankali yake mata magana. Karki damu da duhu My Noor, kid'auka nine fitilarki, zakiga haske ya mamaye d'akin..
Yarrrrr tsigar jikin Asma'u