Showing 39001 words to 42000 words out of 77995 words
daddad'an girki datayi.
Girgiza kanta tayi, idanunta ak'asa, a'a ya yazeed ngd basai kabani tukuyciba. Banmmasan zakuzo tareba da anmaka na musamman aii.
Kai aii wlhy wanna danacima na musamman ne. Ke dai kawai ALLAH yak'ara dank'on k'auna keda abokina. Ngd sosai..
Asaman kafet d'in ya ajiye suka fita..
Godiya sosai tamasa, da sak'on gaisuwa ga iyalinsa sannan takoma ciki, tana mamakin yazeed. Dama akwai irin wad'annan mutanen har yanzu adoron k'asa?.
A can kuwa ya Umar yarakashi har mota yana k'ara masa godiya da k'yak'yk'yawar addu'a shida zuriyar sa. Saida yaga yabar Layin sannan yashigo cikin gida.
*_(((S))........2017_*
*_Luv you all_*
[12/18/2017, 4:29 PM] ~π© ' π― π¦ π· πβ: π©π»βπ».........
π *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* π
*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*
*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_
*_NIKA'DAIππΌ WRITER ASSO.....π_*
_gaisuwar da shafin duk nakine dear Zarah Bukar. barkakanki da dawo online, Alkairin ALLAH ya iso gareki aduk inda kike._
Luv you sosai-sosaiπ»
*_pageβ45-46_*
............A falo ya iske Asma'u tsaye tanata k'ara mamakin halin kirki irinna Yazeed.
Sallamar dayayi ta amsa. Yad'ora dafad'in Husna uana ganki atsaye, lafiya kuwa?.
Lafiya lau yaya, kawai ina mamakin halin kirki da dattako irin na ya yazeed ne. dama har yanzu duniya tanada mutane irinsu acikinta?. Yaya 10millions fa 1 time, batareda tunanin komaiba.
Murmushi ya Umar yayi, my Husna hakane, yazeed ya cancanci yabo ainun, tunda k'addarar nan ta sameni babu Wanda yata6a taimakamin dako sisi dagake sai innata, saiko Anty sa'a. Abokaina, wasu daga cikin 'yan uwana duksun gujeni saboda banidashi yanzu. Atunaninsu zan zame musu nauyi, naringa binsu inacewa subani. Humm lallai naga rayuwa, ALLAH ya shirya zukatanmu.
Shikam yazeed aibammasan mizance akansaba, saidai kawai naita masa k'yak'yk'awar addu'a shida zuri'arsa daganan har k'arshen numfashina.
Gsky ne yayana, Nima zan tayaka insha ALLAHU.
ammafa gsky su ya Yazeed sunada kud'i.
Sunada kud'i sosai Husna, mahaifinsu yatara musu, kuma yakoyama kowa yanda zai nemi nasa, kina ganin yazeed nan bak'aramin d'an kasuwa baneba.
To ALLAH yasakanya masa da mafiyin abinda yabamu. ga wad'annan suma.
Ameen ya rabbi husna, amma wad'annan nakine, kije ki ajiye abinki. Nida akabama 10millions niyakamata nak'ara mini aii ko?.
A'a yaya, Dan ALLAH karik'e, ni babu abinda zanyi dasu, aii komai nawa nakane.
Murmushi yayi yana d'aga mata gira, hakane kuma sarauniyata. To yanzu ki ajiyemin su zan kar6a kinji.
Kanta ta jinjina a sanyaye.
Ya Umar yakamo hannunta yana fad'in yauwa wana kama?. d'azu wakikema dariya?.
Dariyarce takuma zuwama Asma'u alokacin da tatuno jambaki a la66an ya Umar. Takuma shek'ewa da dariya harda rik'e ciki.
Ya Umar tsayawa yayi kawai yana kallonta. Saida tayi mai isarta sannan tadaina tana sauke numfashi.
Humm kingama? Ya Umar yatambaya yana matsowa gareta, itakuma tana matsawa baya, har suka dangane da bango. Sosai idanun Asma'u sunfito waje. A yanzukam sai tsoro ya kamata Dan ganin yanda fuskar ya Umar tasauya.
Hannunsa yadafa ajikin bangon yamda babu ta inda Asma'u zata tsere masa.
Yatsirama fuskarta idanu. Na ce, "kingama min dariyar?. d'ago idanunta tayi suka had'a idanu. da Sauri ta janye nata. Muryarta har rawa takeyi, ta ce, " kayi hak'uri bazan sakeba."
Yanda tayi magana a sanyaye saita bashi dariya. Amma saiya dake, yasa hannu yad'ago ha6arta. Maimakon ta kallesa saita lumshe idanun ta.
Ya ce, "bud'e idonki ki kalleni.
Girgiza kai tayi alamar a'a.
Shikenan za6i hukunci dazan miki da kanki, ga za6i biyu. Kodai kimin abinda namiki harna d'ebo janbaki a bakinki, kokuma ak'ara abinda yafaru jiya............
Aii baima k'arasaba tawaro manyan idanun ta a kansa. Yanzukam yakasa daurewa saida ya murmusa. Saikuma ya gimtse fuska ya ce, " wanne kika za6a?."
Asma'u ta marairaice fuska tamkar zatayi kuka. Murya na rawa ta Ce, "aii gwamma na d'azu d'in.........
Jin ankwala kiran sallar magriba yasakashi k'yaleta yanufi d'akinsa, yana fad'in kishirya kafin nadawo.
Da gudunta tashige d'akinta harda saka key. Aii yaya nariga nasha. Saidai kanemo mai maka kiss. Wayyo, ALLAH ya Fharuk ma ya iya rashin kunya. Da INA ganinsa shiru-shiru kamar bazai iya wani abunba amma shimafa A ne.
Ya Umar nayin Alwala masallaci yawuce.
Koda aka idar da sallah baishigo gidaba, saiya tsaya shago wajen Sadam k'anin Muktar. Dama shine yakad'an zauna idan babu makaranta.
Sadam yagaida ya Umar da tambayarsa ya aikin?.
Murmushi ya Umar yayi, Sadam aii bama afara aikinba ko? Ya kasuwar taka?.
Alhmdllh yaya, saidaifa yogot ya k'are.
"o namanta nace kaje wajen Sabi'u ka kar6o, jiya da yamma nakai masa kud'in, amma aii yakamata yau yama aiko dashi koba'a jeba.
To k'ila baidawo daga kamfani dawuriba.
Ito dakuma wannan Dan wanan.
Kashiga gidato kahuta, saina k'arasa.
Lah a'a yaya, wlhy kayi tafiyarka wajen Anty Asma'u, kasanfa tace in bana barinka Shiga gida da wuri zata hanani Rafi'a.
Dariya ya Umar yayi, ya ce, "lallai kaikam aiki yasameka ashe.
Shima Sadam dariyar yayi. Ya ce, " aii shiyyasa zan Dage da k'yau Dan kar a hanani
fita sukayi suna dariya Dan gabatar da sallar isha'i.
Bayan an idar ya Umar yadawo shagon, d'an abin motsa baki ya d'aukama Asma'u, sannan yatambayi sadam ko Muktar yadawo?.
Eh yadawo tun d'azun, amma naga sun fita shida kawu labaran.
Okey, tobara nashige ni saida safe.
ALLAH yakaimu yaya, agaidamin da auntyna.
Zataji insha ALLAH.
____________________
Tunda Asma'u ta idar da Sallah taketa hanzarin yin kaye-kayen kaya, tasan yau ya Umar bazaici abincin dareba tunda sunci abinci da yamma lik'is, shiyyasama batayi yink'urin dafa komaiba.
Sokawai take tagama k'imtsa gidan tashige d'aki ta kulle kanta Dan tasan ya Umar akwai fad'a da cikawa.
Tana Shiga d'aki yana shigowa, gabantane yafad'i tafara k'ok'arin son kulle d'akin. Saidai ta makaro Dan harya Shiga.
Kallonta yayi, miya baki tsoro haka?.
Cikin in INA ta ce, babufa komai.
d'an murmushin gefen baki yayi, tareda d'age gira d'aya yana kallonta da ido d'aya, kin tabbata?.
Kanta ta jinjina masa, amma k'irjinta sai dukan hamsin-hamsin yakeyi.
Shimadai yafahimceta, Dan haka ya ajiye ledar hannunsa yazauna bakin katifar. Zonan.
Wayyo ALLAH kamar tafasa ihu hakataji, amma yazatayi? dole ta k'arasa garshi, tana niyyar durk'usawa k'asa yajawota saman cinyarsa.
Humm Husna yaushe kuma aka fara zama shiru-shiru? Ko yanzu Sabon hankali yazo mikine?.
Itadai shiru tayimasa, sai tsoro fall ranta. Wlhy duk son datakema ya Umar bazata iya k'ara bashi kantaba a yau. Yanzu haka dauriya kawai takeyi...
Jin tayi shiru ya girgizata, inafata kina tunanin abinda kika za6ane.
Kai yaya baka mantaba.
Kema dazakiyi baki mantaba bare nida za'ayimawa.
Shiru tayi tana tunanin dabarar dazata masa.......
Muryarsace takatseta....
Ya ce, "kin shirya?."
Yatsine fuska tayi kamar wadda batada lafiya.
Ya kuma fad'in yadai?.
Kaina yake ciwo.
Dariya yayi aransa, afili kuma saiya rungumota da k'yau yana fad'in o ni Umar Fharuk ALLAH yabani mata raguwa. Kafin tace wani Abu, saijin bakinsa tayi acikin nata. tuni zaman ya gagaresu ya mirginata suka fad'a saman katifar sosai.
Hummm bara na cika rigata da iska.
πββ
____________________
Amma Alhaji kana ganin bakayi wautaba wajen d'aukar yaronan aiki kuwa?.
Alhaji mansur wautar mi kenan?.
Hummm wauta saboda Alhaji Ubangidansa nada.
Eh to Alhaji Mansur, mutane zasu iya kallon hakan akan abinda bai daceba, to amma idan akaduba halin da yaron yashiga sai a tausaya masa. Musamman danaji cikakken bayani akan abinda yarabasu da Alhaji. Yaron yanada hankali da nutsuwa wlhy, kokad'an bashida damuwa gakuma rik'on amana.
Alhaji Ahmad duknaji bayaninka, kuma na gamsu, amma tabbas akwai damuwa. Inaga gara kawai kabashi wani taimako yaje yayi wata 'Yar sana'a, ALLAH shine maiyi, saiya sake d'agashi idan yaso.
Amma kabi komai asannu, karka aikata abinda zaidawo yadami kowa Company d'innan.
Ajiyar zuciya Alhaji Ahmad ya sauke, harga ALLAH yana tausayin Umar, kuma har a zuciyarsa yaso ya taimaka masa. Amma shima haka ya kwana jiya zuciyarsa na tunane-tunane akan abinda zaije yadawo gameda d'aukarsa aikin. Dukda yasan halin Alhaji mutumne mai sauk'inkai. To amma bazaiji dad'iba aii.
Haka yakwana yana tunani, hardai matarsa ta fahimta da safe ta tambayesa damuwarsa. Bai 6oyemataba ya sanar mata komai. Ita kanta ta jinjina lamarin, kuma ta tausayawa Umar. Amma irin shawarrar databasa, irintace yanzu Alhaji Mansur yake basa.........
Alhaji Mansur yakatse masa tunani dafad'in yakagani?.
Ajiyar zuciya Alhaji Ahmad yasauke. Shikenan nayarda da shawarrar ku, zuwa anjima zankirashi har gida namasa alkairi tunda nayi niyyar taimakonsa.
To haka yafi sauk'i kam. ALLAH shima yabasa nasa.
To ameen.
Ya Umar kam yau tunda suka tashi sallar asuba baidawo gidanba yana shago Sadam yawuce makaranta. Asma'u tagama had'a break fast tagyara gidan tsaf.
Wajen k'arfe 10 tad'an lek'a shago, saita hango ya Umar tareda Mukhtar.
Sallama tayi tanadaga cikin gida, suka amsa, ta gaida Mukhatar da tambayar yara suntashi lafiya?.
Cikin fara'a ya amsa mata kamar yanda yasaba.
Ta kalli ya Umar dake jera yogot a firij. Ya Fharuk break fa?.
d'agowa yayi yana kallonta cikeda so da k'auna, keda nace kiyi barci ki huta shine kika kama yin aiki?.
Fuska ta shagwa6e amma batace komaiba.
Shima saiyayi murmushin nasa na k'asaita. to jeki kawo.
Cikin gida takoma, Dan danan saigata da tire. Baibari tashigoba yatareta ya kar6a, ahankali ya ce, "I Love you my Husna."
Itama cikin nata salon ta ce, "Love you more my boss."
Murmushi yakumayi, yajuya cikin shagon yana maimaita sunan aransa, my boss!.
Yasaki murmushi akaro na babu adadi.
Muktar dake kallonsa ya ce, "lafiyarka kuwa?."
Murmushin yakumayi, babukomai mikagani?.
A abubuwa dayawa mana. Muktar yafad'a cikin tsokana.
Hummm kadaiji dashi, zomuci abinci...........
________________________
Bayan sati d'aya.
Abubuwa dayawa sun faru acikin sati d'ayannan, ciki harda kiranda Alhaji Ahmad mai kano yayma Umar.
Bai nuna masa k'iri-k'iri baizai d'aukeshi aikiba. Amma cikin hikima irinta manya yayma Umar bayani yanda zai fahimceshi.
Ya Umar yace wlhy babu komai Alhaji na fahimceka. Kuma ngd sosai da irin kulawar daka nuna akaina, ALLAH yak'ara bud'i na alkairi. Ngd ngd.
Babu komai Umar, amma ina k'ara baka hak'uri, ga wanan kaje kaja jari.
A'a alhaji wlhy basai kabani komaiba.
Karmuyi haka dakai Umar, ninayi niyya aii, kuma babu mai maida alkairi sai shaid'an nasan kasan haka kuma.
Hannu biyu ya Umar yakar6a yayma Alhaji godiya sosai sannan yatafi gida.
Naira Million 1 Alhaji Ahmad yabama Umar. ranar harkuka ya Umar yayi. Ashe dama mutane na sonsa har yanzu?. Alhaji Ahmad yasha addu'oin alkairi kam.
Abu na biyu kuwa shine shige da fici da yazeed ketayi akan kayan Umar su fito daga hannun custom.
Na uku kuma ya Umar yasa Muktar agaba wajen gyaran mall d'insa daya k'one, aiki akeyi tuk'uru, ankwashe sauran tokar, harma Anfara d'ora ginin inda ya rushe. Aiki sosai yayi nisa, fatansu ak'arshen sati amaida rufi kawai.
Na ce, "ALLAH ya taimaka ya Umar d'inmuππ€Έπ»ββ.
Tunda aka fara aikin abokansa suke mamaki, dan majalissarsu kusada Mall d'in take.
Nan suka fara Gulma wai kodai ya Umar ya saida wajen ne. Harda dariyar mugunta sukeyi, wai lallai maza anji yaji.
Duk abinda sukeyi Muktar yana kallonsu idan yaje duba aikin, kuma yana kawoma Ya Umar labarin komai. Ya Umar bayacewa komai, saidai yayi murmushi da fad'in ALLAH ya shryesu.
Na hud'u kam ko kusa ko kad'an bainunama kowa acikin family d'insaba yasamu wata waraka, dagashi sai Asma'u sai inna. Ko Harris baifad'amawaba duk da ayanzu Harris d'in yana bayansa d'ari bisa d'ari, Dan yanzuma shine yake zama ashago.
Ya Umar kam koda yaushe ya manneda Asma'unsa suna shan sharafin soyayyarsu. Sosai yake nuna mata k'auna itama a 6angarenta hakane. Duk abinda mijinta yakeso shitake masa, soyayya kam nuna masa takeyi k'uru-k'uri afili.
Idan kagansu tamkar zasu cinye juna sabida so da k'auna. Abu d'ayane takasa sabawa dashi ga ya Umar, shine fitinarsa, ko kad'an takasa zama jaruma awannan fannin. to shima dai yana tausaya mata, Dan haka yakan d'an d'aga mata k'afa awasu lokutan koda yakasance amatse.
Yazeed kam yanzu kullum anan gidan yakecin abinci. Dan girkin Asma'u yana masa dad'i.
Tun lamarin baya damun matarsa harya fara tada hankalinta matuk'a. Ayanzukam tak'udiri aniyar shiga makarantar koyon girki, duk da batasan inda yake zuwa cin abincibama.
Yauma kamar kullum Asma'u da ya Umar suna kwance ad'aki kasancewar safiyace, ga garin antashi dawani d'an karen sanyi. Sunacikin bargo manne da juna kamar masu tsoron kar a rabasu.
Ya Umar yaja hancin Asma'u daketa faman lumshe idanu tana k'ara nanewa ajikinsa.
Kalli yanda kiketa nanemin duk kinbi kin d'agamin hankali. Yanzu kuma danace inaso kihau raki.
Asma'u tad'an janye jikinta tana fad'in yi hak'uri nidai Dan ALLAH.
maidota yayi jikinsa yakuma rungumeta, murya k'asa-k'asa tamkar mairad'a ya ce, "zanyi hak'uri idan anbani."
Wata zabura tayi kamar wadda aka fad'ama mutuwa, murya na rawa ta ce, ''kai ya Fharuk kofa awa 1 bakayi dayiba. Dan ALLAH ka tausaya min.
Tausayi tabashi, to amma shimafa bawai laifinsa baneba, inhar zaiga Asma'u akusadashi tofa sai hankalinsa yatashi (yatuno Lubna, itakam tanada juriya tanan 6angaren, inhar zai nemeta bazata ta6a masa gardamaba balle nuna gajiyawa. Duk lalacinta da rashin son aiki bata masa awajen sunnah).
Jin yayi shiru yasaka jikin Asma'u yin sanyi. Bada sonta take bijire masaba, fitinar ya Umar d'ince tayi yawa. Saboda fa wanan abun saiya baro shago sau wajen uku arana. Dukta rame saboda yawan yi dayakeyi, itakuma ga tsoro, data gansa agida sai tsoro ya mamayeta. Amma harga ALLAH tanaso tazama jaruma wajen kula da mijinta. Bataso sanadin ragwantakarta yafara tunanin kaucema UBANGIJIM AL'ARSHI. Dan rashin samun had'in kanta zai iya jefashi cikin tarkon ZINA. (wa'iyazubillah. ALLAH ka karemu muda zuriyarmu da al'ummar MANZON ALLAH (S,A,W) gaba d'aya).
Jikinta a sanyaye tafara masa abinda tasan yanaso. Amma amamakinta saitaji ya ture hannunta, ya juya mata baya.
Hankalinta yakai k'ololiwar tashi. Jikinta na rawa takoma inda yajuya. Saiya k'ara juyawa d'ayan gefe. Ganin haka sai kawai ta rungumesa ta baya ta rushe da KUKA..........
π€Έπ»ββπ€Έπ»ββkunjini shiru?, munasha bikine o.
Ina fata kuna cikin k'oshin lafiya kuda family's naku??.β€β€π
*_(((S)))).......2017_*
*_I Love You all my Fan's._*
[12/19/2017, 4:59 PM] ~π© ' π― π¦ π· πβ: π©π»βπ».........
π *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* π
*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*
*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_
*_NIKA'DAIππΌ WRITER ASSO.....π_*
*_pageβ47-48_*
..........Sosai kukanta kecin zuciyarsa, amma saiyayi burus da ita. Saida tayi mai isarta sannan barci 6arawo ya saceta. (Wanan halin Asma'u ne, Indai har zatayi kuka, to k'arshe sai barci kuma).
Jin shiru dakuma alamar jikinta yad'an saki, yasaka ya Umar juyowa yana fuskantarta. Girgiza kai kawai yayi tareda rungumeta. Wata sassanyar ajiyar zuciya ya sauke, aransa kam tausayintane ya mamaye zuciyarsa.
Saida ya tabbatar barcin nata yayi nisa sannan yazare jikinsa ahankali yamaye gurbinsa da filo. Kwanciyarta ta gyara tacigaba da barcinta.
Shikuma saiya nufi d'akinsa yay wanka ya shirya tsaf cikin ka'nanun kaya, bak'in wando da farar riga mai layi-layin bak'i, sosai yayi k'yau sai zabga k'amshi yakeyi kuwa kamar shagon my Abdul d'ina na turarurrukaπ lol.
d'an lek'ata yayi yaga haryanzu barci takeyi. Aransa ya ce, "kasa kenan."