Showing 33001 words to 36000 words out of 77995 words
yatashi saboda salon da ya Fharuk yake mata magana akunne. K'ok'arin barin jikinsa tafarayi. yakuma ruk'ita da k'yau yanda bazata guje masaba.
Fitinannan k'amshin jikinta yake sunsuna. Wannan wane irin turarene kika saka Husna;?. βyay maganar murya asark'e, tamkar mai shirinsa yin kuka.β
Itama cikin Rawar murya data jiki ta ce, " turarene kawai yay.........."
Batakai ga k'arasawaba ya manne bakinsu waje d'aya. Itakuma rawar jikintane yak'aru, dukda jikinta yana kar6ar sak'onninsa 100%, amma zuciyarta na razanar da ita wahalar dazata sha. Wannan yasa tafara kuka wuywuy da mutsu-mutsun kwace kanta.
Gogan naku kam aii abin nema yasamu, aikin gabansa kawai yakeyi, yanda yake cikurkud'a Asma'un kaikace baita6a kusantar wata maceba a duniya.
Nidai bilyn Ku sim sim nafito gudun aikata laifin kallon k'urullaπΆπ»ββ..............
_kuyi hak'uri da wannan_.π»
*_Nagaisheku da k'yau 'yan group d'ina, ALLAH yabarmu tare.ππ» irin tamau-tamau d'innanππ»._*
*_(((S)))........2017_*
*_Luv you all_*
[12/13/2017, 8:38 PM] ~π© ' π― π¦ π· πβ: π©π»βπ».........
π *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*π
*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*
*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_
*_NIKA'DAIππΌ WRITER ASSO........π_*
*_pageβ39-40_*
..........Idanun Asma'u biyu aka kira sallar Asuba. Amma koda motsin kirki takasayi daga inda take. Ciwon jiki da zafi a k'asanta duk sun addaba mata, sun taru sun zubar matama da zazza6i. Ga kukan datasha adaren jiya.
Ya Umar kuwa barcinsa yakeyi sosai, shima barcin baiwani dad'e da d'aukarsaba saboda kukan da Asma'u takwana tanayi. Shikuma yana aikin lallashi. Sai wajen k'arfe 3 da 'yan mintuna barci ya saceta, shima yasamu yayi nasa. Ita dayake barcin wahala tayi, saita rigashi farkawa da wuri.
Har aka fara kiran sallar farko ya Umar bai motsaba, itama Asma'u barcine yasake saceta.(kunsan dai aikin shaid'an).
Wannan barcine yakaisu har 6:48 na Safiya. Ya Umar ne yafara farkawa ayanzunkam. Ganin haske ya yawaita, yasakashi mik'ewa zumbur, bakinsa d'aukeda addu'ar tashi barci. Innalillahi yashiga ambata Dan ganin agogo. Baima bi takan Asma'u ba yashige bayinta, wanka yayi agaggauce yad'auro alwala yafito. Jikinsa sai rawa yakeyi, arayuwa yana matuk'ar shiga damuwa idan lokacin sallah yawucesa. Hakan na 6ata masa rai. Anutse yagabatar da sallar Asubahi, yanamai cigaba daneman gafarrar ALLAH na jinkirta yinta akan kuskuren barci.
Saida ya kammala hankalinsa ya kwanta yadawo kan Asma'u.
Dubansa yakai gareta, anyi sa'a kuwa fuskarta tana fuskantarsa. Wani k'asaitaccen murmushi yasaki yana wani lumshe idanu, ahankali ya furta Husna daru kenan!, ALLAH yay miki albarka, ya dawwamar da ruhinki cikin farinciki, kamar yanda kika sakani adaren jiya.
Nidake la6e agefe na ce, "ameen ya Umarin mu."π€Έπ»ββπ»
Tashi yayi daga kan sallayar yakoma kan katifar ya zauna saitin fuskar Asma'u. Sosai ya tsira mata idanu tamkar yau yafara ganinta, jiyake wata k'aunarta naratsa 6argonsa da jinin jikinsa. "ada yaso Lubna harma yake ganin bazai ta6a son wata mace bayan itaba, amma zuwa wannan ranar labarin yasha banban, dankuwa jiyake abayama baiyi wata soyayyaba, yanzune zaisan miye soyayyar, yanzune zai amayar da ita inda yadace, yanzune zaisan miye farinciki acikin soyayya. Ahankali yakai hannunsa saman d'an bakin Asma'u daketa barcinta. Zagaya d'an yatsansa yakeyi akai cikeda shauk'i.
Sannu ahankali Asma'u tafara motsawa harta bud'e kumburarrun idanunta akansa. Suna had'a ido tamaida nata idanun tarumtse gam.
Murmushi yayi tareda fad'in haba my Husna! bud'e idanun mana. bud'e ki kalleni da k'yau ni nakine ke kad'ai, zan kasance dake har Abadan Hayatee na.
Wani sanyin dad'ine ya kwarara azuciyar Asma'u, itakam yau wace irin godiya zatama Ubangijin talikai mai sassauya al'amura. Yanzunan ya Umar ne dabakinsa yake furta mata kalmomin nan? Ya Umar d'innan mai tsada da aji mijin Anty Lubna? Ya Umar d'innan da sonsa yazama garkuwar farincikinta tun tana k'arama? Ya Umar d'innan da takema kallon Wanda yafi k'arfinta abaya? Ya Umar d'innan daya mallake zuciyarta da dukkanin komai nata batareda yasan tanayiba? Ya ALLAH kaine Sarki mafi Girman iko da Rahma, ALLAH Kaine kake bayarwa ka k'ara batareda ka k'osaba.........hawaye sosai keta kwarara a kumatunta.
Ya Umar yakuma matsawa gareta zuciyarsa dukba dad'i, azatonsa har yanzu kukan abinda yay mata takeyi. Rungumeta yayi tsam ajikinsa, murya a raunane ya ce, "kiyi hak'uri my Husna! nasan ban k'yautaba amma ki gafarceni." ALLAH yay miki albarka, kisaka azuciyarki Umar Fharuk nataredake har Abadan. Yanda kika saka ruhina da zuciyata acikin farinci kema ALLAH ya dauwamar danaki Ruhin a farinciki. I love you so much my Husna.
Aii Asma'u batasan sanda tak'ara k'ank'amesaba tana zubda hawayen farinciki. Shikuma yana aikin shafa kanta da lallashi.
Saida tayi mai isarta sanna yad'auketa cak zuwa bathroom.
Ananfa akeyinta Dan Asma'u bazata iya tsayawa ya Fharuk yamata wankaba.
Tun yana had'a ruwan zafin daya d'akko daga kichin tagwada fita daga bathroom d'in, amma kamar yasan mitake nufi ya dinkare ko'ina na k'ofar.
Da d'an zafi sosai yahad'a ruwan zafin sannan yadawo da kallonsa ga Asma'u. Suna had'a ido tayi k'asa da kanta tana hawaye. Murmushi yayi ahankali yamatso gareta, murya k'asa-k'asa ya ce, " my Husna kincika shagwa6a. Kodai nakira Inna ko mama?.
Sosai tawaro idanu akansa. Saikuma wasu hawayen suka kuma gangarowa.
Tunawa batayi sallar Asubaba yasakashi sungumarta yasaka arobar daya had'a ruwan zafin, dama daga Ita sai riga iya guywa.
Wani zallo tayi tareda k'ank'amesa tana kuka. Wayyo ya Fharuk wlhy akwai zafi. Innata kice yabarni wayyo ALLAHNA.
Sake dannata yayi da k'yau yana murmushin wannan kuka. Afili ya ce, "Husna karfa kisaka gaban inna yayta fad'uwa, tun jiya kiketa kiranta. Ya Isa haka kada ki k'aremin sunan Innata!.
Zuwa yanzu tad'an daina mutsu-mutsun tashi, saidai hawayen dasuka kasa k'arewa. Saida ruwan yahuce yakuma zuba ruwan zafi, baibartaba saida ya tabbatar tagasu dak'yau sannan ya ce, "kin iya wankan tsarki?.
Kanta tad'aga masa kawai, har yanzu hawaye takeyi. Baifitaba har saida yaga yanda tayi, ya tabbatar tayi dai-dai sannan yanad'ota a tawul ya d'akkota kamar wata jinjira.
Akatifar yadireta, yagoge mata jikinta yasaka mata kayan data ware domin yin sallah. K'ara d'aukarta yayi yakai inda abin sallar yake.
Baibar wajenba saida ta kabbara sallar.
Dawowa yayi inda katifar take, yacire bargon. Ido yazaro waje Dan ganin yanda zanin gadon yad'an 6aci kad'an. Mamakine yakamashi, dama bakowace macece ake ganin jini a Daren farkontaba? Yasan Lubna tagirmi Asma'u amma ita jinin data zubarma har tsoro yabashi a lokacin. Saikuma gashi Asma'u ita babu sosai. Ubangiji mai iko, matanma akwai banbanci atsakaninsu kenan?.
*_hattara samari, kudaina d'aukar cewa dolene sai kunga jini adaren farkon matanku zaku yarda takawo budurci cikakke gareku. Mata kala-kalane, bakowacce bace ake ganin jini adaren farkonta. Mutanen da, suna aurar dayara suna k'ananane, shekara 12-13-14 kaga kuwa wad'annan yarane d'anyu dolene a iya ganin jinin. Kuma alokacin matan basa yawan yin abubuwan dazai saka burcinsu yin rauni._*
*_ayanzunkam bahaka bane, mafi yawanci ana aurar da mata 18-19-20-21-22+ ne, gakuma abubuwan 'yan matan kanyi dake saka buducinsu yin rauni batareda sun saniba. Yawan d'aukar Abu mai nauyi, horo da ake bama yara a makaranta, hawa mashin, tsallaka kwata, yawan tsalle-tsalle, musamman dayanzu 'yammata suka lalata kansu wajen rawa. Irin wad'annan abubuwan da dama dawad'andama ban lissafoba duk suna saka budurci yin rauni koda mace takasance ma'bociyar kamewa. Mata saimu kula. Kukuma maza Ku fahimcemu, bawai ganin jini face-face agado bane alamar mace takawo cikakken budurci gidan miji. ALLAH yasa mugane, ameen._*
Yaye zanin gadon ya Umar yayi zuciyarsa fes babu wani wasiwasi akan Asma'u, domin kuwa shine sheda akan tsam yasameta, bama k'aramar wahala yashaba wajen fasata. Lallai yakamata sauran maza irinsa su fahimci haka suma.
Asma'u kam tuni ta idar harta kwanta awajen.
wani zanin gadon yasake, dukda wannand'in bai 6aci dayawaba, amma baidace abarsaba. Yana canjawa ya d'akkota yamaida saman katifar dan barci takeyi sosai.
Zanin gadon yakai bayi yasaka a bokiti ya wanke tas yaje waje ya shanya. Yana gamawa yadawo d'akin yakwanta tareda rungume abarsa suka koma barci mai dad'i.
*_1:4pm_*
Sai k'arfe d'aya da minti hud'u ALLAH yabasu ikon farkawa kusan atare, amma Asma'u tariga ya Umar tashi, motsin tashintane ma yatadashi.
Tanajin motsin tashinsa ta lafe ita adole barci takeyi.
Murmushi ya Umar yayi tareda yimata cakulkuli.
Dariya sosai tazo mata, dukda zafin datake d'anji idan tayi motsi babba hakan baisaka ta dainaba.
Ganin yanda take dariya yasaka ya Umar dariyar shima. K'ank'amesa tayi sosai tana cigaba da dariyarta dafad'in ya Umar yi hak'uri Dan ALLAH, ALLAH kuwa abinnan babu dad'i.
Daina yimata yayi, yajawota jikinsa ya rungumeta tsam zuciyarsa fal farinciki.
Sunkai 30minutes ahaka yana gaya mata dad'ad'an kalamai wad'anda suka sakata k'ara ganin kimarsa a idonta. Dama can ita bataji haushinsaba, aganintama hakan zai iya zama sanadin dazaisa ya sota. Sa6anin da da ita keta fama da dakon sonsa a zuciyarta.
Bayan wani lokaci yad'auketa cak sai bathroom. Zille-zille tafarayi ita adole bazatayi wanka dashiba.
Shikuma yace bata isaba, aii daga yau tarema zasu ringa wanka, danshi hakan yana cikin tsarinsa. Ganin zata fita yad'ebo ruwa yazuba mata ajiki. Dole tatsaya awajen cak, shikuma yashiga yimata dariyar tsokana. Ta6ara tafara zuba masa shikuma yana lallashi har aka kammala wankan yad'akko kayarsa kamar d'azun.
Da k'yar tasamu ya yarda yatafi d'akinsa yabarta ta shirya itama.
Kowa shirinsa yayi mai k'yau.
Asma'u tad'an daure tagyara d'akinta da babban falo sannan tashiga kicin Dan nema musu abinda zasu saka abakin salati.
Ganin rana tayi sosai sai kawai tad'ora jalof d'in taliya da dankali. Tasaka busashshen kifin da ya Umar yasaya musu shekaran jiya. Cikin 'yan mintuna k'alilan gidan yacika da k'amshi ainun. Dama Asma'u gwanace a wajen abinci.
Ya Umar daya tsaya had'a wasu takardu yay shirinsa tsaf cikin shadda fara tas, dakakkiyar shaddace 'Yar ubansu, yad'inkata tun yana shanawa da naira. Shaddar d'inkin zamanine fetet, tayi masa k'yau aynun, yad'akko bak'ar hula yasaka, yasaka safa da takalmi bak'i sau ciki. Wayyo masu karatu tamkar ba ya Umar dake cikin k'angin rayuwaba. Idan kagansa zaka d'auka har yanzu ajik'e yake da laimar kud'i.
Fitowa yayi yanata bulbula k'amshi, tamkar Wanda yay wankan turare. Yalek'a d'akin Asma'u bata nan. Jin motsi akicin yasakashi nufar can.
Asma'u dake jera abinci akan tire Dan ta kammala komai tajiyo k'amshin turaren ya Umar ya yawaita awajen.
Lumshe idanu tayi ahankali tabud'e akansa, bak'aramin tafiya da ita wankansa yayiba. Shima tayi masa k'yau sosai. K'arasowa yayi cikin kichin d'in ya rungumeta, cikin kunnenta yarad'a mata, haba My Husna! Waya gaya miki amarya na aikin a irin wannan ranar?.
Fuskarta tashiga sinnewa a k'irjinsa ita adole kunya. Yad'ago fuskar tata a acikin tafukan hannunsa, idanunsa suna yawo bisa k'yak'yk'yawar fuskarta. Kiss ya manna mata agishi da hanci, ahankali ya furta ALLAH yay miki albarka my Husna. Ina k'yaunarki sosai.
Saida ta k'ara sinne kanta a k'irjinsa sannan ta ce, "nima haka yaya ina k'yaunarka."
Rungumeta yayi tsam yana juyi da ita Dan murna. Sundad'e ahaka sannan yad'auki tiren abincin sukaje falo.
Tare sukaci abincin dukda Asma'u akunyace take, ko ido batason suhad'a dashi.
Bayan sun kammala yatayata suka gyara wajen sannan ya ce, " bara yaje wajen Alhaji mai kano, dama k'arfe biyu yace yadawo.
Addu'ar fatan nasara da dawowa lafiya tamasa.
Shikuma ya ce, "taje ta kwanta tasake hutawa Dan anjima za'a k'ara irin amsar jiya.........
Aibata bari ya rufe bakinsaba takwasa dagudu zuwa ciki.
Dariya yafita yanayi da jinjina shirme irinnna Asma'u............
*_(((S)))........2017_*
*_Luv you all_*
[12/14/2017, 8:28 PM] ~π© ' π― π¦ π· πβ: π©π»βπ».........
π *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*π
*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*
*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_
*_NIKA'DAIππΌ WRITER ASSO........π_*
*_pageβ41-42_*
..........Itama daida tashiga ciki gudun nata yabata dariya, Dan haka tayi dariya sosai harda rik'e ciki. ALLAH nagode maka daka nuna min wannan rana mai cikeda tarin farinciki. Wai yau nice da ya Fharuk manne da juna, yana gayamin kalamansa masu dad'i da tsada. Ya ALLAH ka d'orar mana da wanan farinciki har k'arshen rayuwarmu....
Ameen Asma'u.
____________________
Su Lubna ansha shagalin biki, kud'ikam sunyi kuka abikinnan, komai anyishi asarauce. Su Lubna kam ashiga wanan afita wanan. Dama d'inkuna sukayi na garari itada Suhaima.
Zuwa yanzu kam amarya tazo gida. Taroma yatashi kowa yakama gabansa. Su Lubna suna d'aki anata zabga barcin gajiya, gidan tsit kamar babu bil'adam acikinsa.
Sai can nad'an jiyo hayaniyar su twins ad'akinsu.
Can na nufa danna ganema idanuna. Aiko sune suketa tsalle-tsalle agado, duksun hargitsa d'akin. Babu laifi yaran sunyi girma sosai, ga kamanninsu da ya Umar sunfito sasai. Saidai Hassana farace. Usainace dai komai na ya Umar bata bariba, har dariya idan tayi kamar tasa...
Barisu nayi nafito Dan inada abunyi.....
____________________
Alhamdulillahi ya Umar yayima Alhaji Ahmad mai kano bayani gamsashshe akan rabuwarsa da mahaifin Lubna.
Dayake mutumne mai fahimta, saiya gamsu da komai, yakuma bama ya Umar hak'uri.
Kayi hak'uri Umar, da abinda suka aikata maka. Amma inada tabbacin babu laifin Alhaji awannan lamarin, saidai idan matarsace tazugashi. Nasan halinta batada kirki kokad'an, bataso kowa yara6i Alhajin Dan aganinta za'a k'are musu dukiya.
Murmushi Ya Umar yayi ya ce, ''to ALLAH ya kiyaye."
Ameen dai Umar.
Yanzu zaka iya fara zuwa aiki daganan zuwa Monday.
Alhamdulillah ngd sosai Alhaji, ALLAH yak'ara bud'i na alkairi.
Ameen Umar..
Daga nan Ya Umar yatafi sai kuma gidan inna.
Babu kowa a tsakar gidan, sai kaji da su Inna ke kiwo sunata kaida kawo. Yakuma yin sallama ak'ofar d'akin da takalma suke birjik har wajen k'afa shidda. Kusan atare suka amsa. Sannan yashiga.
Sannu da zuwa suka shiga yimasa da gaisheshi, yayinda shikuma idonsa kebin Harris da kallon mamaki. Dama yana zuwa gidannan?.
Shima kansa Harris d'in yalura da kallon da yayan nasa kemasa, Dan haka yay k'asa da Kansa alamun jin kunya.
Inna duk tana kallonsu. Ya Umar yaje kusada inna ya durk'usa cikeda ladabi ya gaidata.
Cikin fara'a ta amsa masa da tambayar lafiyar iyali?. Ya ce, komai Alhamdulillah. Asma'u ma na gaishesu.
Muna amsawa.
Kallonsa yamaida ga Anty Saratu, ya ce, "sarkin yawo kenan, kekam kina iya sati d'aya bakizo gidannanba?..
Kanta ak'asa ta ce, " ya Umar wlhy har sati uku inayifa."
Harara ya balla mata, a'a har shekara kinayi, inna ba kwana hud'u dasuka wuce Nazo gidannan natarar da yarinyarnan ba agidannan?.
Dariya inna tayi, wlhy hakane Umar, nima yanzu babu jimawa nagama mata fad'an yawo, dan ba abune mai k'yauba.
Ya Umar yakuma harararta, mijin nakine sakarai dayake barinki, ke ko saboda yara yawon baya damunki?. To daga yau karna sake ganinki agidannan sainan da wata uku. Idan bahakaba kuma ranki zai 6aci matuk'a.
Gyad'a kai tayi dukda hukuncin NASA bawai yamata dad'i baneba, Dan Anty Saratu akwai d'ambazan yawo kamar taci k'afar kare. (Shima mijin NATA bayaso, amma saboda yana matuk'ar sonta saiyake barinta)..
Daga nan hira akad'an ta6a, wadda ya Umar bawani saka musu baki yakeyiba sosai, garama idan inna tayi magana.
Zuwa can ya ce, "inna Nazo wajenkine."
To yaron arzik'i, nima kuwa dama ina nemanka.
Saratu da Hasiya, fatee kufita. Amma Harris yatsaya.
d'agowa ya Umar yayi ya kalli Harris d'in da yay k'asa da Kansa, Dan bak'aramar kunyar ya Umar yakejiba.
Bayan fitarsu Inna ta kalli ya Umar. Umaru! Inaso kabani Aron hankalinka nan, mufara maganar da Harris yazo da ita, dukda nasan bakazomin da sakaren maganaba kaima, amma na Harris ma yanada matuk'ar muhimmanci.
To inna ina saurarenku.
Inna ta kalli Harris daya marairaice fuska tamkar zaiyi kuka. Harisu taso kazo nan.
Jiki a sanyaye Harris yataso, yazo kusada ya Umar yazauna. Inna ta nuna masa ya Umar da ido.
Zamansa ya gyara muryarsa na rawa ya ce, "yaya Dan Girman ALLAH kayi hak'uri, ka yafemin duk abinda namaka. Wlhy na tabbata duk gidammu babu mai mana Abu tsakani da ALLAH kamarkai. Abunda yafaru abayama sharrin shaid'anne. Ka gafarceni, insha ALLAH bazan sakeba. Wlhy yanzu ina tareda kai 100%.......
Ya Umar yakatseshi da