Showing 63001 words to 66000 words out of 77995 words

Chapter 22 - karayar arxiki COMPLETE

12 Jul 2024

9242

wani salon kallo, saikuma tarufe idonta, Dan taji kunya.
Yasauke ajiyar zuciya yana murmushin shima, mik'ewa yayi ya ce, " ina zuwa."
Ganin yanufi hanyar bayi ta ce, ''yaya mukam tafiya zamuyi kafin mama tafarga bama nan."
Juyowa yayi ya kalleta, babu wani mama taga bakwa nan, to tayaya kuka fito yanzu.
Yaya wlhy barcifa takeyi, kuma nasan zata iya tashi tunda bata kwanta gaba d'ayaba.
Dawowa yayi yana dariya, ya d'auki fodiyo ya manna masa kiss, my son kafad'ama kakarka iyayenkafa suna buk'atar jin d'umin juna.
Idanu Asma'u tazaro waje tareda mik'ewa zumbur, yaya wa kake gayama hakan?.
Dabaki yanuna mata fodeyo.
Kanta kawai ta jinjina tana fad'in kaga banishi mutafi, saida safe.
Bai bata fodeyon ba, amma yad'an rage fara'a, towai saurin mikeyine? Koma maganar dana kiraki Dan ita bamuyibafa, jiba agogo ko tara batayiba.
Asma'u ta langa6e kai gefe, kai yaya ka tausaya mini plss, ALLAH inajin kunyar mama ainun.
To naji muje falo muyi maganar saiki tafi.
Babu yanda zatayi dole tabishi falon dantaji maganar dazasuyi d'in...........










*_(((S))).....2018_*
*_I love you so much my fans_*
[1/2, 7:48 PM] ~πŸ‡© ' πŸ‡― πŸ‡¦ πŸ‡· πŸ‡­βœ: πŸ‘©πŸ»β€πŸ’».........



πŸ’Ž *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* πŸ’Ž


*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*


*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_


*_NIKA'DAIπŸ‘ŒπŸΌ WRITER ASSO.....😜_*

*_page→67-68_*


..........Su Uncle Abdullahi sunyi bincike akan mazajen nasu Suhaima, duk dadai binciken yad'an nuna musu matsaloli.
Dan haka suka kira mom dasu Lubna suka shaida musu. Lubna da suhaima suka bad'ama idonsu toka babu kunya sukace sudai zasu auresu ahaka. Babu yanda su Uncle habeb suka iya dasu Dan aganinsu auren yafi yawon gararin dasukeyi.
Cikin sati d'aya komai ya kammala, antsaida biki sati biyu kacal. Sai alokacin Ameer yaji labari, masifa yaytayi, ya ce, "kuma babu abinda ya shalleshi. Ransa a6ace yatashi yana fad'in mom dama nazo na sanar miki jiddah ta haihu d'azun, amma 'yar batazo bada raiba.
Baki mom ta ta6e ta ce, " ALLAH ya k'yauta gaba."
K'ala baice da itaba yakad'e rigarsa yafice.
Suhaima & Lubna suka raka bayansa da harara suna zagi. Mom bata hanasuba, Dan itama yanzu haushi. ameer d'in takeji ainun, musamman yanda ya janye kansa daga garesu, komai saidai matarsa.........




β˜…β˜…β˜…

Afalon suka yada zango, ya Umar yazauna saman 2sita, ita kuma Asma'u tanufi kujera mai kallonsa zata zauna.
Hannunta ya kamo, tajuyo tana kallonsa, da ido yay mata nuni da gefensa. Itafa harga ALLAH fitinarsa take gudu bawani abuba, amma babu yanda zatayi dole tazauna kamar yanda ya umarceta.
Juyowa yayi yana kallonta sosai, itama saita nutsun, ya sauke ajiyar zuciya yana murmushi.... Kuma yak'i magana.
Ganin haka Asma'u tad'ago ta kalleshi, muryarta a sanyaye ta ce, ''Yaya ina saurarenka.
Kauda kansa yayi daga gareta yana dariya k'asa-k'asa, zuwa can ya ce, "to abani abinci mana."
Batareda ta tanka masaba tasauka k'asa ta shirya masa abincin, Dan tasan yafison cin abinci ak'asa.
Fodeyo ya mik'a mata sannan ya sauka k'asan.
Anutse yakecin abincinsa, lokaci-lokaci yakan d'ago yakalleta yana murmushi. Itakuma ta zun6ura baki gaba tana nuna masa agogo, dan bata k'aunar mama tagane tannan.
Ga ya Umar yanata wani cin abinci a yangance tamkar mace.
Yana kammalawa tafara gyara wajen, kwanukan ta kwashe tafita dasu zata kai kicin sukai karo da mama a babban falo.
Kallon tuhuma tabi Asma'u dashi, itakuma tayi k'asa da kanta tashige kicin, duk kunya ta rufeta.
K'in fitowa tayi, har saida tajiyo mama tashiga d'akin ya Umar sannan. A hanzarce tashige d'akinta. Hasiya tabita da kallo tana fad'in yaya Asma'u lfy kuwa?.
Bata bata amsaba tashige cikin bathroom.
Dariya ta kufcema Hasiya, ahankali ta Ce, "ALLAH yak'ara muku aii."
Har mama tadawo d'akin d'aukeda fodiyo Asma'u takasa fitowa daga bathroom. Itama mamar batabi ta kantaba ta kwantar da yaron ta kwanta.
Saida Asma'u tagaji Dan kanta sannan tafito cikin sand'a tayi shirin barci ta kwanta, dama mama afalo take kwana..........


*_bayan kwana biyu_*
Bayan kwana biyu akasha suna. Anrakwashe an kwalle kuwa, munsha bidiri harda bired'e.
Mama kuwa tunda daddare tagudu, aka maye gurbinta da inna baito k'anwar maman.
Asma'u taji dad'in hakan, Dan Dama tana tsoron ya Umar gsky. Kar ganin babu kowa agida yamata aika-aika, gata da d'inki ajikiπŸ€ͺ.
Zuwa dare taron suna yatashi lafiya, su Asma'u sun samu alkairi sosai, fodiyo yayi goshi.




β˜…β˜…β˜…
Su Lubna ma anata shirin biki na garari, tamkar wata budurwa🀭.
Hakama mom bikin ake shiri sosai, aranar alhamis aka sakasu a lalle, juma'a sukayi kamu, ranar Asabar d'aurin aure.



____β˜…______β˜…______β˜…_____
Ranar juma'a da daddare ya Umar yana gidansa wajen 8pm. Yabarsu Harris a shago Dan harsun dawo sunbar muktar da yazeed a mall, saikuma ma aikata sababbi da aka zuba masu dutyn dare.
Asma'u da Hasiya, inna baito duk suna afalon, ya Umar da inna baito dai hirarsu sukeyi akan rayuwa. Asma'u da Hasiya kam hankalinsu nakan kallon film d'in Kalan dangi, sai dariya suketa zubawa.
Fodeyo na goye abayan Hasiya, tunda aka masa wankan yamma yaketa barcinsa.
Sallama suka jiyo daga k'ofar falon, ya Umar ya amsa tareda bada Umarnin shigowa, Dan yaji muryar Sadam Ce.
Sadam yashigo ya gaida inna baito, ya gaida ya Umar da Asma'u.
Hasiya ta gaidashi.
Wata farar βœ‰ ya mik'ama ya Umar, Yaya gashi wanine yakawo yamzu wai abaka.
Ya Umar yakar6i yana jujjuyawa cikeda mamaki, shikam wazai kawo masa letter yanzu?.
Sadam yaymusu sallama yakoma shago.
Ya Umar ya ajiye takarda yacigaba da hirarsa da inna baito. Saidai k'asan zuciyarsa nata zungurarsa akan ya duba. Warwarewa yayi yabud'e saiga IV ya fad'o, yazaroshi yafara dubawa.
Murmushin takaici yad'anyi Dan ganin sunan Luban da Hafiz ajiki, wai harma gobe d'aurin aure su.
Acan k'asan zuciyarsa kam abin ya k'ona masa ransa. Amma yadake, Dan bayaso su Asma'u su fahimci komai.
Tundaga nanma saiyaji hirar ta gunduresa. Sallama yayma inna baito yashige d'akinsa.
Asma'u kam tuni ta karanto damuwa afuskar mijin nata, tunda aka kawo masa takardar dama hankalinta na kansa, so take tabishi dantaji matsalarsa, amma kunyar inna baito ta hanata.
Inna baito babu ruwanta, bakamar mamaba, bakomai take saka musu idoba. Saidai idan taga rawar kan Asma'u tayi yawa saita taka mata birki, ta hanyar tuna mata takula da kantafa. Wannan yakansa Asma'u kama kanta.

Ya Umar kam yana d'akinsa cikin damuwa, da bak'in cikin abinda Lubna da Hafiz sukai masa. gawani k'arin bak'in ciki Asma'u bata shigo d'akinba har yanzun. Yaja wani dogon tsaki, tareda kai dubansa akan agogon dake manne a bangon d'akin.
Wayarsa ya d'auka yafara Neman layin yazeed. Saidai harta yanke ba'a d'agaba, tsaki yakumayi Dan yasan shegen saurin barcin yazeed, duk inda 9 tayi saika sameshi a gado nad'e......
Wringing d'in wayar tasane takatseshi daga dogon tunanin, ganin yazeed ne ya d'auka da hanzarinsa. Kai kasa halan kanacan kana barci?.
Dariya yazeed yayi, cikin sigar zolaya ya ce, "malam wanefa barci, inadai shan sharafin soyayyane."
d'an iska naji, ya Umar yafad'a cikin 'yar dariya.
Shima yazeed dariyar yayi, o namantafa Ashe kai yamzu gwaurone, karna tada maka da hankali.......
K'atseshi ya Umar yay saurin yi, malam saurareni ba wannan bane agabanani.
Cikin dariya yazeed ya ce, "to miye agabanka Alhaji?.
Ya Umar yashiga zayyanema yazeed zancen iv da aka aiko masa. Wata dariya yazeed ya k'yalk'yale da ita, saida yayi mai isarsa sannan ya ce, "haba abokina, kaifa jarumine, yanzu wannan d'an abinne yatayar maka da hankali? Miye Hafiz balle Lubna?. Kaida ALLAH ya azurta da samun nitsatstsiyar mata kyakykyawa, gashi har ALLAH ya baku k'yautar fodiyo. Ai kamata yayi wannan sak'on yabaka dariya ba 6acin raiba.
Nidai nasan waye Hafiz, kuma tabbas dawata manufa yakeson auren Lubna, humm itama bazan tayata jajeba Dan ta had'u da daidai itane.
Ajiyar zuciya ya Umar yasauke, murya a sanyaye ya ce, "ngd yazeed na fahimta."
Yauwa abokina, yanzu abinda nakeso dakai, ka shirya cikin wanka iyaka wanka mu halarci d'aurin auren gobe, kasanarma muktar shima.
Sannanfa lokaci yayi dazaka fito kanunama kowa kaima kaine. Dan duk wani 6oye-6oye yakamata yak'are hakanan.
Gsky ne yazeed, nima nayi wannan tunan.
Hira suka cigaba dayi, yazeed ya kwantar masa da hankali, ahaka har suka koma hirar kasuwancinsu kuma....
Sai wajen 11 ya ajiye wayar, bayan yakira Muktar shima ya sanar masa. (Dan yanzu sun k'ulle tamau su ukunnan, komai nasu tare yake). Harya kammala wayar Asma'u bata lek'oba.
Itakam alokacinma tuni tayi barcinta.
Abin yabashi haushi, yay shirin barci ya kwanta.....




β˜….....β˜…......β˜….......β˜….......β˜…
Washe gari wajen k'arfe sha biyu ya Umar yashigo gidan, daga shago yake.
Asma'u da Hasiya ne kawai a tsakar gidan, Hasiya tanadaga kicin tana girki, Asma'u kuma tana zaune akujera 'yar tsigunno tana d'auraye kayan fodiyo.
Hirar Fatee sukeyi suna dariya ya Umar yashigo gidan. Asma'u tamasa sannu, amma saiya d'auke kansa yashige.
Ta cije le6enta na k'asan, Dan ita batasan laifin dataima ya Umar ba, tunda safe yaketa wani ciccije mata, lafiya lau yake magana da kowa agidan amma banda ita.
Cigaba tayi da wankinta batareda tabi takansaba.
Wani haushine yakuma turnik'e ya Umar, haryayi wanka yafito Asma'u bata shigoba.
Inna baito ce talek'o daga windown falo takira Asma'u.
Asma'u ta amsa tana mik'ewa, hannunta ta d'auraye aruwa mai k'yau sannan taje.
Inna baito ta mata dak'uwa, kinci gidanku Asma'u, yanzunan mijinki yashigo amma bazakizo kiji matsalarsaba.
Baki Asma'u ta d'an turo gaba, amma batace komaiba. Inna baito ta nuna mata hanyar d'akin ya Umar tana mata fad'a, kudai yaran yanzu saiku haihu goma amma babu hankali ajikinku?, badole kusa mazanku 'yan kalle-kalleba awaje. Yo ALLAH natuba aii yanzu ake gidadanci agidan aure ba daba.
Itadai Asma'u tanajiyo mitar inna baito amma tashige d'akin ya Umar.
Abakin gado ta iskeshi yana shafa mai.
Ko motsi baiyiba barema yad'ago ya kalleta. Tana nan tsaye harya gama shafa mansa, shiri yafara cikin wata dakakkiyar milk d'in shadda wadda tasha Brown d'in sirfani, sabuwa dal, yad'akko sabon takalmi sau ciki Brown ya saka, hularsa zanna Bukar itama Brown da ratsin milk ya kwama, bak'aramin k'yau na d'aukar hankali ya Umar yayiba, yana cikin fesa turare Asma'u tamatso kusadashi, ta madubi ya hangota, Dan haka yakuma tsare gida.
Matsawa tayi kusadashi ta amshi turaren zata fesa masa, amma saiya kauce, idonta cikeda da kwallah tarik'o hannunsa, yafara k'ok'arin kwacewa tasaki kuka. Tsayawa yayi cak amma bai juyoba, cikin muryar kuka ta ce, "haba ya Fharuk! Laifinmi namaka haka da zafi? Dahar na cancanci irin wannan hukuncin daga gareka?.
Ni bakimin laifin komaiba, yafad'a yana k'ok'arin zame hannunta daga nasa. Kuma rik'ewa tayi sosai tana kuma k'ara sautin kukanta.
Bayason jin kuka ta ko kad'an, amma dolene ya nuna mata kuskurenta kodan gaba ta gyara.
Kuma k'ok'arin zame hannun nasa yayi, tayi saurin k'ank'amesa ta baya. Ya cije le6ensa sannan yajuyo da ita gabansa, cikin tsare gidan nasa ya ce, "keda laifin, amma kinfi kowa raki?." Kinga kibarni natafi, su muktar na jirana ak'ofar gida.
Nidai saika fad'amin laifina.
Hummm tom kibari idan nadawo saimuyi maganar, yanzu d'aurin aure zamuje kuma bani kad'ai baneba, gashima sai cud'emin kaya kikeyi ni.
Kuma narkewa tayi ajikinsa tana raira kukan.
Yasan halin kafiyar Asma'u sarai, rungumeta yayi cikin sigar lallashi ya ce, "tom kiyi hak'u idan nadawo zan fad'a miki laifinki, kuma nayimiki hukumci, yanzudai kimin uzuri na tafi kimji my Queen. Yay maganar yana d'ago fuskarta, Sumba mai k'yau yabata akumatu da goshinta. Dak'yar tayarda tabarsa yatafi.
Afalo sukayi sallama da inna baito, yafice sai zabga k'amshi yakeyi abinsa.
Sun halarci taron d'aurin auren, Wanda mutane da dama suka halarta. Amma wannan karon akwai banbanci, babu manyan mutane kamar lokacin aurenta da ya Umar, dakuma na Ameer. (Kunsan yanzu rayuwar wani abumma na ganin ido akeyi, dak'asa tarufe idonka wani ya shafeka a babin sabgoginsa kenan). To su Lubna dai sunga dahir, Dan duk manyan k'asarnan abokan mahaifinsu awannan karon babusu kwata-kwata.
Ahaka aka shaida auren Lubna & Hafiz, Suhaima & Ramadan.
To ALLAH yabada zaman lafiya.

Lokacin da aka kammala d'aurin auren, ya Umar, Yazeed, muktar, suka doshi gungun na abokansu, wato Hafiz, salman, Dr jafar, alkasim, Kabeer, Tasi'u dadai sauransu, suna tsaitsaye sunsha anko cikin faraen shaddoji, su adole abokai masu had'inkai da k'ud'i...............


Nikam bilynku nace hummmm. 🀫shiiiiiiiiii!!!!!!!.







*_(((S))))........2018_*
*_Luv you all_*
[1/3, 4:10 PM] ~πŸ‡© ' πŸ‡― πŸ‡¦ πŸ‡· πŸ‡­βœ: πŸ‘©πŸ»β€πŸ’».........



πŸ’Ž *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* πŸ’Ž


*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*


*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_


*_NIKA'DAIπŸ‘ŒπŸΌ WRITER ASSO.....😜_*

*_page→69-70_*


..........Assalamu alaikum.
sallamarsu ya Umar tadaki kunnuwansu Dr jafar daketa kwasar dariya suna tsokanar Hafiz ango.
Kusan atare duk suka juyo, mamaki, al'ajabi, razana duk tasaukar musu alokaci d'aya. Cikin murmushi su ya Umar suke mik'a musu hannu. Haka suka dinga basu hannayen tamkar sokaye.
Tabbas ganin ya Umar cikin shiga ta kamala da dattako ta razanasu, hakama ganin muktar da ya Umar tare yakad'a hantar cikinsu, saikuma ga yazeed ma, towai yaushema yazeed yasamu Umar? Amma ko'a wancan satin yazo majallissa haryake tambayarsu babu labarin Umar dai har yanzu ko?.
Sukuma suka shiga gulmar Umar d'in alokacin.
Amma yaukuma saiga Umar da yazeed, harda Muktar Wanda basu ta6a tunanin yama had'a iri da ya Umar ba.
Sudai su ya Umar ALLAH Sanya alkairi suketa zubawa.
Ya Umar yasauk'e kwayar idonsa cikinta Hafiz, fuskarsa d'aukeda wani murmushin mugunta, angon Lubna kasha k'amshi! ALLAH yasanya alkairi abokina, inatayaka farinciki gsky....
Yana gama fad'ar haka yad'auke idonsa daga kan Hafiz. Sosai jikin Hafiz yayi sanyi, gawata kunyar Umar d'in ta baibayesa. Can ya tsinkayi muryoyin su Umar suna musu sallama zasu tafi. Bai fargaba saida ya hango ya Umar zaune a mazaunin direba, yazeed na gefensa, muktar na baya, duk cikinsu babu mai irin kwatankwacin motarcan......
Dr jafar ne yafara jan tsaki lokacinda motarsu ya Umar ta shillah sukabar wajen.... Mtsoow wai wancan wawan waya bashi motane?.
Salman yaywata dariyar mugunta, yo kaimadai Kasan ta munafikin canne yazeed, kokuma wannan dasuke tare, muktar yake kowama? Mtsoww.
Kabeer yay kwafa yana fad'in aikin banza kawai, Dan anbashi aron kaya da mota, shine zaizo yana mana wata burgar banza. Dabamusan asalin balbelaba, dasai tace mana daga masar take.
Tasi'u dayay shiru yana jinsu, danshi tabbas jikinsa yayi sanyi, cikin sanyin murya ya ce, "kai abokaina, anya kuwa Umar bai warkeba? Idan mumce Aron mota da kaya aka bashi, to kwanciyar hankalin dake tartare dashifa?. Kunga kuwa yanda Umar yayi k'iba da haske? Wlhy fatarsa har wani walk'iya takeyi. Nikamarma yafini k'yan jiki, nidake kwana na tashi a AC.
Zasu hayayyak'oma Tasi'u, alkasim ya dakatar dasu, kai kutsayafa, wlhy maganar Tasi'u gsky ce, tabbas akwai wani Abu ak'asa dangane da Umar.
Hafiz dai yakasa cewa komai. Suma sauran kowa yayi gum yana dogon nazari........


Na ce, " hummm, kowadai yadaka rawar wani, aiya rasa turmin Daka tasa.....



β˜…
Acan kuwa su ya Umar tunda suka tafi suketa shek'a dariya. Cikin dariya Muktar ya ce, "wai kunga idanun Hafiz kuwa, kuru-kuru... Hhhhhhhhhhh!!!.
Suka tuntsure da dariya, yazeed ya ce, ''ai duk mamaki ya kashesu k'ananun 'yan iska kenan. Wani abuma sai sunganka a kasuwa Umar. Hhhh
Ya Umar yay dariya harda dukan sitiyari, wai nifa abinda yabani dariyama shine kallon da Tasi'u da Alkasim sukemin, kaikace yau suka fara ganina. Ina kalon salman harda ta6a gefen rigata yaji wace shadda na saka.
Haka sukaita hira suna dariya, daga nan gidan yazeed suka wuce. A can sukaci abincin rana mairai da lafiya Wanda matar yazeed tadafa, Dan yanzu Alhmdllh ta iya girki, yanda su ya Umar sukaita Santi sai yazeed yaytajin dad'i aransa, lallai shawarar Umar d'in tamasa amfani,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login