Showing 6001 words to 9000 words out of 77995 words

Chapter 3 - karayar arxiki COMPLETE

12 Jul 2024

9252

Babu komai tafad'a tana murmushi, ngd sosai labaran, amma Dan ALLAH kozan samu memory nakwashe abin kan wayar?.
Babu damuwa, idan nakwashe zanbama Rafi'a takawo miki.
To ngd sosai labaran.
A babu damuwa Asma'u.
Agurguje tafice tasamu adaidaita cikeda kwarin guywa suka nufi asibitin..........







*_(((S))).......2017_*
*_luv you all my fan's_*
[11/21/2017, 4:33 PM] ~๐Ÿ‡ฉ ' ๐Ÿ‡ฏ ๐Ÿ‡ฆ ๐Ÿ‡ท ๐Ÿ‡ญโœ: ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿปโ€๐Ÿ’ป.........




๐Ÿ’Ž *_KARAYAR AZEEK'I!!_*๐Ÿ’Ž


*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_


*_NIKA'DAI๐Ÿ‘Œ๐Ÿผ WRITER ASSO......๐Ÿ˜œ_*


*_pageโ†’6_*

.......Anshigar da ya Umar babu dad'ewa su mama suka iso, suduka sukai kan Asma'u suna tambayar jikin ya Umar d'in?.
Jikin Anty sa'a tafad'a tana kuka, wannan yasa suka k'ara rud'ewa.
Makwafcinsune yamatso, cikin hikima yamusu bayani.
Godiya sukai masa sosai, daganan aka koma zaman jigum-jigum.

*_3h...ago_*
Dr yafito shida Nurse's dasuka taimaka masa.
Shimadai rufuwa akansa sukayi suna tambayarsa jikin ya Umar.
Yabuk'aci ganin wasunsu a office d'insa, amma babu Wanda zaya iya hak'uri abarsa abaya, Dan haka suka tafi suduka.
Dr bai hanasuba saima gurin zama daya nuna musu.
Kowa yasamu waje yazauna yanajiran bayani, bayan Dr yagama 'yan rubuce- rucensa yad'ago yana kallonsu, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce, "Alhmdllh, gsky Ku k'ara godema ALLAH akan taimakon daya bama Alhaji Umar danba kowane yake irin fad'uwarnan yatashi dai-daiba, amma shi Alhmdllh babu wata Marsala, saidai yana cikin matsannanciyar damuwa wadda saida taimakonku aikinmu zaikai ga nasara, yanzudai yasamu barci kuma bazai farkaba harsai nanda 24h Dan munaso zuciyarsa tasami Hutu sosai.
Yanzu ga wannan zakuje kubiya kud'ad'en sannan kuma asayi wad'annan magungunan kafin ya farka.
Atare sukace to Dr mungode sosaifa.
Karku damu aikinane.
Godiya suka masa sannan suka fita.
Suna fita Mama ta kalli ya Abubakar, ta ce, " Abubakar saika amshi takardun kaje kabiya kakuma sayo magungunan ko?.
Fuska ya murtike tamkar zai fasa kuka ya ce, "to kuzama shaida idan yatashi zai bani kud'ina Dan na kasuwane.
Asma'u da Anty sa'a, mufida, Rafi'a duk kallon mamaki suke masa, shikansa ya fahimci haka amma saiya basar yamik'ama Asma'u hannu alamar tabashi takardun.
Kanta ta girgiza ta ce, ''ya Abubakar kabarsa akwaima kud'i awajena kuma insha ALLAH zasu ishemu komai.
Babu kunya ya washe bani yana fad'i a to kinyi k'yankai Asma'u.
Babu Wanda yatanka masa acikinsu, Asma'u da Anty sa'a suka tafi wajen da Dr yafad'a musu.
Sunbiya kud'in komai sannan sun sayo duk magungunan da ake buk'ata, dawowarsu babu dad'ewa ya Abubakar yawuce kasuwa akabarsu mama anan.
Sumadai zuwa dare duk suka tafi akabar Asma'u kawai awajensa, da mamace zata tsaya Asma'u tace taje tahuta ita zata zauna dashi, dak'yar tayarda saida su Anty sa'a suka saka bakima.
Bayan tafiyarsu Asma'u tayo alwala tashimfid'a sallaya, sallar isha'i tagabatar tayi addu'a sosai darok'on ubangijin al'arshi akan yakawoma mijinta d'auki da sassaucin halin daya tsinci kansa aciki, tashafa addu'ar tanamai zubar da hawaye, bayan kammalawarta saman kujerar dake d'akin tadawo ta zauna ta talsurama k'yak'yk'yawar fuskar ya Umar idanu, duniyar tunani tafad'a wa rayuwarsu tabaya maicikeda abubuwa na ban mamaki, ban haushi, al'ajabi, tausayi, farinciki, da jarabawoyi kala-kala...........



*_SHEKARUN BAYA DASUKA SHU'DE_*๐Ÿค”
Malam Tsalha baduku tsohon kirki mai mata d'aya da 'ya'ya uku aduniya.
Hajara tsohuwa mairan k'arfe uwargida kuma amarya agidan malam Tsalha baduku, ta haifamasa yara uku 2maza 1mace.
Usman, Kabiru, Binta.
Sun rasu suduka tun shekarun baya dasuka shud'e.
Usman yanada mata d'aya da yara Uku shima, Mero itace matarsa suna kiranta da mama, malam Usman mutumne mai hak'uri da kawaici, yanada son 'yan uwansa sosai dakuma iyayensa, bawani mai k'arfi banebashi amma mutumne mai Neman nakansa cikin tsaftatacciyar hanya, akwaishi da wadatar zuci dakuma Nuna godiyar ALLAH kan abinda yabashi walau kad'an kokuma mai yawa.
Saidai Bahaka bane ga matarsa Dan itakam akwai hange-hange da son kud'i damai kud'i, Indai Kanada naira tokuwa kai abokin tafiyane, idankuwa babu to kana gefene awajenta.
Yaransu uku Sa'adatu, Abubakar, Umar Fharuk.
Sai kuma Kabiru matarsa d'aya wasila amma basu ta6a haihuwaba.
Halin Kabiru shima yasha banban Dana malam Usman dankuwa shimadai akwai son 'yan canji, toshikam babu laifi yanada d'an hali danyafi malam Usman arzik'i.
Sai Binta itamadai tayi aure harda yaranta, halintakam irinna malam Usman ne dantanada hak'uri sosai da kuma zafi idan ka k'ureta.
Yaranta hud'u duk mata, Saratu, Asma'u, Fateema, Hasiya.
ALLAH yayima malam Usman rasuwa tunsu Umar suna k'anana danshi bama sosai yasanshiba, bashida wayo sanda yarasu.
Bayan Rasuwar malam Usman rik'on yaran yacigaba gudana hannun mahaifiyarsu mama, ta taka rawar gani sosai wajen kula dasu har bayan shekara uku da rasuwar malam Usman sai kawu Kabiru yazo da buk'atar auren mama abisa shawarar da inna binta k'anwarsu tabashi.
Dagudu kuwa mama ta yarda Dan tasan Kawu Kabiru yanada d'an abin hannunsa gashi kuma baita6a haihuwaba, ba'a wani 6ata lokaciba aka d'aura auren, anan gidan tacigaba da zama, cikin ikon ALLAH kuwa saiga ciki, wayyo zokaga murna wajen kawu kabiru da family gaba d'aya, tattali sosai yakema mama, ciki yanakai wata Tara da wasu kwanaki ta sunkuto d'anta Namiji Wanda yaci suna Usman suna cemasa Harris, shekarar Harris biyu mama takuma haihuwar mace Mufida, daganan sai Auta Rafi'a.
Rafi'a nada shekara biyar aduniya Anty sa'a tayi aure bayan ta kammala karatunta na Secondary, taso cigaba da karatu amma hakan bai samuba, shima Ya Abubakar a daddafe da buga-buga yakammala Diploma d'insa, daganan yay aure yanad'an sana'ar saida kayan provision awani shago dake k'ofar gidansu.
Bata sake zaniba akan Umar Fharuk dan shimadai duk ajirgi d'aya suka sauka, bayan kammala secondary yafara karatun nasa a B,U,K saboda k'yawun result d'insa kai tsaye degree suka basa, dahad'a gabas had'a yamma aka kammala, ALLAH yabashi nasarar fita da result mai k'yau, yayi farinciki sosai hakama 'yan uwansa musamman ma mama Dan aganinta itamafa karan 'ya'yanta yakai tsaiko yanzu.
Umar yadawo zaman gida babu aikinyi, tun zaman yana masa dad'i harya fara gundurarsa, tuna maganarnan ta hausawa dasukance babu maraya sai rago tamasa allurar tashi domin Neman abinyi, duk abinda yasan zai rufa asirinsa yinsa yakeyi babu sanya ko girmankai irinna 'yan bokon nan, ana haka wani abokinsa yay masa hanyar Babur na adaidaita sahu, sosai Umar yaji dad'in wannan taimako, cikin farin ciki yazoma mama da kawu Hamidan wannan labari.
Hummm, amma saisuka gwaleshi da nuna masa wannan k'ask'ancine, yaza'ayi kamarsa dayakeda kwalin degree yak'are da tuk'a babu, gsky yacanja shawara amma ba wannanba.
Wannan lamari ya6ata ran Umar sosai, Dan haka ransa a6ace yanifi gidan inna binta.
Tarba sosai yasamu agurinta Dan d'an gatantane.
Inna tasaka Fatee takawo masa abinci da ruwa, saida yaci yak'oshi sannan yakwashe komai yafad'a mata.
Itama ranta ya6aci sosai Dan haka taita fad'a kamarsu mama na gabanta, takuma kwantar masa da hankali akan zata samesu, shikuma yaje yakar6i adaidaita sahud'in yafara aikinsa.
Yaji dad'i sosai Dan haka yayta mata godiya, daganan hira maidad'i suka cigaba dayi Dan akwai shak'uwa tsakaninsu sosai.
Sallamar Asma'u da Hasiya ne yasakasu katse hirar suka amsa.
Asma'u tazube littatafanta na islamiyya tana fad'in wash inna wlhy nagaji yau.
Binna ta ce, "to sannu ragguwa, amma bakiga yayankiba.
Idanunta tad'ago ta kallesa, saikuma ta kauda kai tace ina yini.
Bai amsataba saima hararta dayakeyi, takuma fad'in inayini, Dan ita azatonta baijibane, d'an yatsine fuskarsa yayi sannan ya amsa, yamaida kallonsu ga Hasiya da itama take gaidashi, ya ce, " Autar inna ya islamiyyar?, kinadai yin k'ok'ari ko?.
Hasiya ta jinjina kai ta ce, "eh yaya munayi, yanzu hakama ina ajin sauka nida yaya fatee, yaya Asma'u kuwa sune manya Dan sune 'yan ajin hadda.
d'an satar kallon Asma'u yayi, suna had'a ido ya kauda kai.
Asma'u tad'an ta6e baki tareda mik'ewa tashige d'akinsu tana k'unk'unai Dan haushin ya Umar takeji saboda abinda yay mata shekaran jiya, tana hira da saurayinta ya koreshi, abin bak'aramin haushi yabataba.
Bata k'ara fitowa falonba saida taji yatafi sannan tafito.
Inna tabita da kallo, kekuwa Asma'u mikikeyi ad'aki tun d'azun?.
Kanta tad'an sosai ta ce, "inna ina wayane da Anty saratu fa.
Inna batace komaiba ta mik'e, saida takusa zuwa k'ofa sannan tajuyo tana kallon Asma'u, ta ce, "idanma laifi kikaima Umar to wlhy kiyi gaggawar bashi hak'uri Dan kinsan Sam banason raina nagaba.
Asma'u ta kwa6e fuska kamar zatayi kuka, nifa inma ban masa komaiba.
Ohodai nidai nafad'a miki, inna tafad'a tana ficewa daga falon........







*_(((S)))......2017_*
*_Luv you all_*
[11/22/2017, 1:23 PM] ~๐Ÿ‡ฉ ' ๐Ÿ‡ฏ ๐Ÿ‡ฆ ๐Ÿ‡ท ๐Ÿ‡ญโœ: ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿปโ€๐Ÿ’ป.........



๐Ÿ’Ž *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*๐Ÿ’Ž


*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*


*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_


*_NIKA'DAI๐Ÿ‘Œ๐Ÿผ WRITER ASSO........๐Ÿ˜œ_*

*_pageโ†’7-8_*

......Umar kam tun aranar yaje yakar6i Babur d'in Adaidaita sahu, kuma aranar yafara aiki, ganin alkairin daya samu yasakashi farinciki sosai tareda samun kwarin guywa.
Bai sanarma kowa yafara aikiba agidansu saida inna tazo washe gari sukai magana dasu mama, badan mama tasoba ta amince, amma babu yanda zatayi Dan tanason inna binta sosai kodan k'aunar datake nunama 'yayanta, ta taka rawar gani sosai akan karatun Umar Dan d'an gidantane.
Tundaga ranar Umar yacigaba da hayar adaidaita sahunsa, dukda mama bata nuna farincikinta aikai hakan bai hanashi yimusu hidaimaba da d'an abinda yasamu, babu yabo babu fallasa suke kar6a, shikam Umar ko kad'an hakan baya damunsa harkokinsa kawai yakeyi.

Ana haka sai wani al'amari yafaru a wani daren Juma'a ranar alhamis kenan da daddare.
Bayan Umar yagama aikinsa misalin k'arfe 11 saiyayi harama tafiya gida.
Yana cikin tafiya saiyaga ana d'aga masa hannu tundaga nesa, lamarin yabashi tsoro Dan azatonsa 'yan fashine ko 6arayin Babur, haka yak'arasa wajen guywarsa asage yanata ambatar duk addu'ar datazo bakinsa.
Yataka birki agaban dattijo da wani matashi daketa k'ok'arin tsaidashi, matashin saurayinne yayma Umar magana.
Abokina Dan ALLAH kozaka kai alhaji gyad'i-gyad'i?.
Shiru Umar yayi na 'yan sakwanni zuwacan yasauke ajiyar zuciya tareda kallon agogon hannunsa, ya ce, "abokina darefa yayi duba kagani, gashi kasan akwai tazara daganan zuwa gyad'i-gyad'i.
Nasani abokina amma Dan ALLAH ka taimaka, wlhy daga airport na d'akko mai gidana saikuma mota tamana tsiya, tun d'azun muke tsumayen abin hawa amma bamu samuba.
Kafin Umar ya ce, " wani Abu dattijon Alhaji yalek'o yanafad'in yaro kadauro Dan ALLAH, wlhy nagaji sosai burina kawai nahuta.
Ajiyar zuciya Umar yasauke tareda gyad'a kai ya ce, "shikenan shigo mutafi baba.
Alhaji yaji dad'i sosai, Dan haka yashiga sakama Umar albarka, kayansa direban yakwaso zuwa adai-daitar sukaiyi sallama Umar yaja suka tafi.
Tunda suka tafi babu maima wani magana, Umar yana tuk'i yana tunanin rayuwa da yanda take tafiya, Alhaji kam yayi shiru abaya saboda gajiyar zaman jirgi dake nuk'urk'usarsa, saida suka isa gyad'i-gyad'i sannan Alhaji yanuma Umar layin dazasu shiga.
Ak'ofar wani katafaren gida suka tsaya, Umar yajinjina kai azuciyarsa yana fad'in wani kaya sai amale.....
Alhaji yakatse masa tunani da mik'a masa kud'i masu yawa Wanda shima baisan adadinsuba.
Umar ya yakalli kud'in ya kalli alhaji sannan ya ce, " baba 350 ne kud'inka aii.
Murmushi alhaji yayi ya ce, "d'ana karka damu kaidai kar6i.
A'a baba ngd kabani iya hak'k'ina kawai, girgiza kai Alhaji yayi dakuma ajiyema Umar kud'in akan cinyarsa, babu yanda Umar ya iya dole yakar6a yay godiya sannan yatafi gida da addu'ar ALLAH yakaisa lfy.
Inda yake kai adai-daitarsa yanufa, yasamu guri yay fakin, abinda yake lilli6eta yajawo zai rufe sai idanunsa suka sauka akan wani d'an k'aramin akwati, shiru yayi yana nazarin kowaye ya manta?.
Wata zuciya ta ce, " masa Alhajin Daka sauke yanzu.
Afili ya ce, "hakane kuma, ya kalli agogonsa saiyaga har 12:36, gsky yanzu yana tsoron sake hawa titin nan, kuma idanma ya iya komawa yanada tabbacin za'a barsa yashiga wannan gidan a irin wannan lokaci?, d'an tsaki yaja tareda d'aukar akwatin yana fad'in insha ALLAH gobe idan ALLAH ya kaimu da sassafe saina kai masa.
Da wannan shawarar yanufi gida, dama kullum shine k'arshen dawowa gida shiyyasa yake rik'eda key d'in gidan guda d'aya, bud'ewa yayi yashiga sannan yamaida yarufe tareda addu'ar rufe gida, d'akinsa yashiga yay wanka da shirin barci sannan yay nafilfilinsa kamar yanda yasaba ya kwanta.

_washe gari_
Tunda yatashi yay sallar asuba bai koma barciba dama shi haka yake bai iya barcin safeba kullum yana dawowa daga masallaci zai d'auki alkur'ani yahau karatu, saida gari yay sha sannan yay addu'oi yatashi, wanka yashiga.
Shigarsa babu dad'ewa mama ta shigo d'akin, idontane yasauka akan bak'uwar jakar mai k'yau, jikinta har rawa yakeyi tabud'e jakar, idanu tazaro amatuk'ar razane Dan ganin mak'udan kud'in dake cikeda d'an akwatin duk daloline sababbi k'ar.
Razanuwa da ganin kud'in yasa takasa aikata komai har Umar yafito daga wanka, shimadai bak'aramar razana yayi dagani kud'inba, Dan yauce rana ta farko daya fara ganin zunzurutun kud'i tsirara agabansa masu yawan haka.
Jikin mama amace ta ce, " Umaru INA kasamo wad'annan kud'in haka?.
Zama yayi abakin katifarsa, yajanyo jakar yana rufewa mama ba nawabeneba, wanine nad'auka jiya da daddare shine yamanta da jakar.
Mama ta washe baki tana fad'in Umaru aii yamzun sunzama naka tunda tsuntuwa kayi, lallai kagodema ALLAH da wannan arzik'i daya yimaka, dama masu iya magana necewa dare d'aya ALLAH kanyi bature.
Kallonta kawai yakeyi damamakin ganin rikicewar datayi Dan kawai taga kud'i, shi rabonma dayaga fara'ar mama agareshi harya manta wlhy, amma duba daga ganin kud'i dukta rikice, ya kauda Kansa saboda 6acin rai, amma kasancewarsa jarumin 6oye sirrin zuciya sai fuskarsa bata nunaba ko kad'an, cikeda ladabi ya ce, "mama zan maida MASA kud'insa ne, Dan zan gane gidan Dana saukesa insha ALLAHU.
6ata rai mama tayi, ta gallama Umar harara to Uban masana basaikaita maidawarba, idan banda ga6anci ALLAH yabaka irin wannan dukiyar har kayi tunanin maidama mai ita?, shi Kasan ta hanyar daya samu?, k'ilama 6arawon gwamnatine.
Kiyi hak'uri mama ALLAH ya huci zuciyarki, abinda zaki duba wannan kud'i ba hakkina bane, koma tayaya maisu yasamesu wannan shiyya d'aukarma Kansa kaya, inada damar maida masa kud'insa, to aii gara na maida domin ubangijinafa da barci ko gyangyad'i baya d'aukarsa yana kallona, kuma baya yafe hak'k'in wani akan wani face kanemi gafarar Wanda ka zalunta, tonikuwa mizaisani butulcema ni'imar da mahalliccina yay mini? na tsarkakakkiyar zuciya.
Mik'ewa mama tayi a fusace tafice tanata masifa.
Umar ya girgiza Kansa tareda sauke zazzafan huci, afili ya ce, " mama ALLAH ya shiryeki.

Niko bilyn Abdul sai na ce, "ameen ya Umar๐Ÿคท๐Ÿฝโ€โ™€.

Koda Umar yagama shirinsa yanufi d'akin mama Dan mata sallama kamar yanda ya saba.
Da sallama yashiga falon, babu kowa sai Mufida da Rafi'a dake break fast kowanne sanye cikin kayan makaranta na gwamnati.
Gaisheshi sukayi, ya amsa yana tambayar ina mama?.
Mufida ta ce, "tafita makwafta yaya.
Makwafta kuma?, yanzu da sanyin safiyarnan?.
Shiru sukayi basuce komaiba, ya ce, " to kutashi mutafi idan kun gama?.
Rafi'a ta ce, "yaya bazakayi kari ba yau?.
A'a Rafi'a yau ina saurine, kudai kutashi muwuce, to suka fad'a suna mik'ewa, kowa yad'auki jakarsa ta makaranta suka fice.
Atsakar gida suka gamuda kawu, Umar yadurk'usa har k'asa yana gaida shi, Abba ina kwana.
Lfy lau Umaru anfito?, eh Abba mun fito, to wannan akwatinfa haka?, Abba wlhy wanine ya mantashi jiya dana d'akkoshi shine zanje na mayar masa, tofa yo kai Umaru banda abinka aii wannan tsintuwace, karik'e abinka kawai mana, nasandai bai wuce kaya bane aciki?, murmushi Umar yayi yanamai jinjina halin iyayen nasu aransa, ya ce, " karka damu abba nasan gidansa zankai masa dan takardune aciku, aikin 6ur inji tusa, a'a jeka kakaimasa abinsa, mizakayi dawasu tarkacen takardu dadai kud'ine ko kaya saika rik'e, nanma murmushi kawai Umar yayi harsu Mufida na tayashi.
Rafi'a da Mufida ma suka gaidashi, suma amsawa yayi cikeda fara'a.
Sallama sukai masa sannan suka fice, wajen adaidaitarsa sukaje, saida ya goge sannan suka shiga, makaranta yafara saukesu daganan yanufi gyad'i-gyad'i.
Da gyar ya iya gane layin, yatsaya adaidai inda yasauke dattijon Alhaji, gidan dayaga alhajin yashiga yake kallo, shi saima yanzu yaga gidan sosai, katafaren gidane na mai jida 'yan canji, komakaho yashafa katangar gidan yasan mai gidan ya shahara kuma yagama jik'ewa da data.
Yad'an dad'e atsaye yana tunanin yanda zai shiga gidan, baigama tunaniba yaga an wangale k'aton gate d'in gidan, wata dalleliyar motace tafito bak'a wulik sai d'aukar ido takeyi, k'arfin hali Umar yayi yamatsa kusada motar yana d'aga masa hannu.
Ahankali aka sauke bak'in Gila's d'in motar, wani matashin saurayi dabaifi sa'an Umarba ya bayyana.
Umar ya ce, "sorry Dan ALLAH inada

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login