Showing 45001 words to 48000 words out of 77995 words
na firgita!.
Murmushi yayi yana kuma jawota jikinsa, hum kudai mata kuncika tsorone kawai, yanzu hakama agida d'aya aka ta6ayi amma kunzo kunata cancana magana a chatting.
ALLAH yaya dgsk anayifa. Bakamar gidan amare, da ankai amarya sai 6arayi suje satar kayan lefefa.
Lallaikam to ALLAH yatsaremu da tsarewarsa.
To amen ya rabbi.
Sannu da zuwa.
Yauwa ya gidan? Ina Anty Sa'a d'in.
Tab wannan aitadad'e da tsufa agida, saboda kar yara sutaso daga school su tarar bata nan tatafi. gashi zata biya gidansu mama.
Okey.
Asma'u tayunk'ura zata tashi daga jikinsa yakuma rik'eta da k'yau. Ina zuwa kuma?.
Yaya kofa ruwa ban bakaba bare abinci.
Murmushi yayi ya ce, " to aii banajin yunwa. Nidama wani k'aton albishir nazo miki.
Da Sauri ta ce, "goro fari k'al yayana."
A'a saifa kin bani.
Shiru tayi alamar tunanin mizata bashi to? Zuwa can tad'ago tana kallonsa, yaya komai nabaka yayi?.
Kansa ya jinjina mata batareda yayi maganaba.
Hummm babbar magana. Ya Umar bai tsammaci haka daga Asma'u ba, Dan baita6a tunanin zata iyaba, musamman idan yay la'akari da kunyarta dakuma tsoro. Amma abin mamaki saiga bakinta cikin nasa.
Wani salon kissing take masa wanda shikansa daya d'orata ahanya baisanshiba.
Dandanan jikinsa yasaki, (kundai San su ya Umar sai a slowly😉).
Shima ruk'ota yayi sosai suka zube akatifar yana bada gudummawarsa, dukda jikinsa babu wani kwarin kirki.
Suntafifa basajin kira, Dan haka sad'af-sad'af nafito nida gayyata.
♥
Saida suka kwashi wani d'an lokaci sannan nalek'asu. Hangosu nayi sunfito daga wanka. Nazaro idanu waje dan mamaki😳, yanzunan daga albishi har an zarce?.
Ta6d'i itamafa Asma'u nakula tafara zama 'Yar hannu.
Asaman katifar suka zube, Asma'u na lafe jikinsa ya Umar yabata labarin kiran da yazeed yay masa..
K'ank'amesa tayi tana kukan farinciki da kwararo addu'oin alkairi ga ya yazeed da dukkan ahalinsa.
Shikansa ya Umar saida 'Yar kwalla ta tarumasa agen ido.
Sund'an dad'e suna tattauna lamarin kafin daga bisani Asma'u tabashi hak'uri akan fishin dayakeyi da ita. Murmushi yayi mata, cikin rad'a ya ce, "aikin wanke laifinki tas my Asmy, ALLAH yayi miki albarka, yabamu zuriya tagari."
‘Ameen yayana.'
Daga nan suka cigaba da hirarsu har barci yay awon gabadasu.......
*_____________________*
Yanzu baby bazakuyima kanku fad'aba akan wannan yawon gantalin dakukeyi keda Suhaima? Kince karatu zaki koma bazakiyi aure yanzuba, amma kosau d'aya baki k'arama dadynku maganar karatunba.
Shekaran jiyafa a club Safwan yacemin ya ganku. Anya wannan hanyar kuna ganin zata 6ille daku kuwa?.
Baki Lubna taturo gaba itada Suhaima, Lubna ta ce, "yo momy shida yakawo miki gulmar ganinmu a club shi miya kaisa club d'in? Kodan gwano bayajin warin jikinsane? Zai take laifinsa yahango nawasu. shimafa Safwan d'innan magulmacine, shiyyasa nakeson Ameer, arayuwa bashida saka ido akan abinda babu ruwansa wlhy.
Suhaima ta ce, " aii indai ya Safwan ne haka ya iya gulma tamkar mace wlhy, ke yamafi wata macen narantse. Shi sau nawa muna ganinsa a inda bai daceba amma bama fad'a, Dan kawai ya gammu a club zaizo yana gulmarmu. Naga miye aibun club Dan ALLAH? gurinefa kawai na hutawa bawani abuba..........
Ke dallah yimini shiru anan shashar banza, kemi kika sani dangane da duniya?.
Kucigaba karku fasa, aii duniyace, Wanda baizobama jiransa takeyi. Tana gama fad'a tabar musu wajen.
Suduka baki suka murgud'a. Lubna ta ce, "kaini wlhy watarana momy saitaita Abu kamar bata wayeba. Dan ALLAH miye aibun club?.
Humm kemadai k'ya fad'a, amma balaifinta baneba, wancan algunguminne yahad'a, shibaiga abinda yake aikatawaba saimu?, ALLAH ranar har kwalbar *_Guilder_* Nagani a d'akinsa.
K da gsk?.
Wlhy kuwa baby da gsk nakeyi, amma kinsan dana tambayesa miya cemin?.
Girgiza kai Lubna tayi alamar a'a.
Suhaima tacigaba dafad'in, saboda ya rainamin hankali cewa yayi abokinsane yasha bashiba.
Dariya suka shek'e da ita. Lubna ta ce, " k'arya yakeyi, bayaso kifad'ama dadyne. Shiyyasa Ameer yake birgeni shida lamarinsa babu wani 6oye-6oye, komai afili yakeyinsa kowama yagani. Amma kinga Safwan... Hummm mai fuska biyu kenan.
Dariya suka shek'e da ita, harda tafawa kamar wasu k'awaye.
Suhaima ta ce, "yaya zamuje casun Mufy ne?.
Tafd'i yo mizai hana, ba'a gayyacemubama munje balle Abu namu maganin a kwa6emu. Aii zuwa kobabu tayar gaban mota, bikin birthday d'in aminiya aidole saidamu awajen zai k'ayatar.
Gskyne babyna, shiyyasa nakesonki fiye da kowa agidanan. ammafa Umar yaso ruguzamu wlhy, kai ALLAH yataimakeki ya ku6uto mana dake. Inaji ajikina dankibar gidanan ALLAH ya talautar da Umar.
Dariya suka koma sakawa. Lubna ta ce, " k'aba, yanzudai kam nasan aii yagama Fita hayyacinsa, dagashi har shegiyar yarinyarnan maikamada ojuju.🙃.
Hhhhhhhhh kai baby bakida damafa kema.
Kinsan dabaku rabuba k'ila dayanzu kinmasu Amrah k'ani ko k'anwa.
Tab, keni barima jinginani dashi, har abada nashafeshi daga rayuwata. Kisaka aranki bamma ta6a Sanin wanishi Umar ba arayuwata.
Suhaima ta ce, "k'aba kenan?."
Ke aii Umar yawuce k'aba wlhy, saidai yanyan!. Mtsooww.
Nikoma hirarsa banaso matsiyaci kawai, haka zai k'are rayuwarsa a talauci...........
Na ce, "Hummm....
Yeeeeeeeeeeee💃🏻💃🏻💃🏻, ankwana ana mana ruwa.
ALLAH mungode da tarin ni'imominka garemu, kana bamu badan halinmuba, ALLAH ka k'arama ANNABI fadila da wasila🙏🏻.
*_((((S)))........2017_*
*_I Love you all_*
[12/21/2017, 6:47 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻💻.........
💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* 💎
*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*
*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_
*_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO.....😜_*
*_writer's kuna ina!!?._*
_masu zaginmu dacin zarafinmu mungode sosai, kuna aiko mana da addu'oin alkaba'i da kiranmu jahilai. Hum jahilci! Jahilci!!....wannan kalmace data dace ga Wanda baisan kansaba, mai ilimi shine keyin gyara ba zagiba. Amma yau harmu wata take kirada mazinata marasa tarbiyya, Fasik'ai, wai har kinacewa ALLAH ya wargaza rayuwarmu😭, kekuma takin rayuwarfa? Mi ALLAH zai mata?. maganar gsky shine bamu yafeba, duk Wanda yaymana wanan sharrin, sharrin zina bala'ine masifane._
_wlhy tallahi bazan yafeba nidai, ya ALLAH kayi gaggawar sakamana akan Duk wanda yayi wani mummunan lafazi akanmu, mubazamiyi masa mummunan furiciba, amma indai munada hakk'i agareshi ALLAH kayi gaggawar fidda mana._
_ALLAH kaine shedarmu bamu ta6a rubutaba books dan lalata d'an waniba, amma akace aikinmu kenan, ya ALLAH ka saka mana da sakamako mafi cancanta._
_Kowacece munbarki da ALLAH, shine zai zaka mana, kuma insha ALLAH duk addu'ar dakikayi agaremu koke wacece ALLAH ya maidata agareki, yanda kikaci zarafinmu kema ALLAH yamiki daidai da abinda kika aikata mana._
_Duk Wanda yakaranta Novels idan ALLAH yabashi fahimtar abinda writers suke nufi Dan fad'akarwa falillahi hamdu, idan ka kasa fahimtarmu kuma harka zagemu ALLAH yasaka mana._
_ALLAH ya Isa wlhy, ALLAH ya isa, ALLAH ya Isa!!😭._
*_Banta6a kuka akan rubutuba sai yau, ya ALLAH ka sakamana, kaikafi sanin dukmasu zaginmu da abinda suke aikatawa agaremu, wlhy koda uwarmu d'aya ubanmu d'aya bazan yafe mataba, da aurenmu ake kiranmu mazinata😭, da tarbiyyarmu ake kiranmu marasa tarbiyya!, da imaninmu ake kiranmu fasik'ai, baki sanmuba bamu sankiba, bamu taka mikiba bamu karya mikiba kike addu'ar ALLAH ya wargaza mana rayuwa, Narantse bamu yafeba._*
_Da duk yawun marubutan online nake wanan maganar, bamu yafeba, bakuma ZAMU ta6a yafewaba, ALLAH yasakamana._
*_Kince daga k'ungiyar shiriya ta mata daga jihar kano?._*
_Wannan k'aryane, idanma daga k'ungiyar kike kekika sani, amma kije ALLAH yaymiki abinda kikaimana._
_ALLAH yayi mana maganinki jahila kawai, munbarki da ranar k'arshe ALLAH yamana hisabi😭._
*_Duk wata writer datasan kanta koda bata karanta posting d'inan da akayi zagi akanmuba tota mik'a kukanta ga Ubangijin Al'arshi akan yasaka mana, kullum sai anfito da Sabon salon cin zarafinmu, idan aka zagi wannan writer yau gobe sai a koma kan waccan, haba jama'a kuji tsoron ALLAH wlhy. Writers kufad'a a sujudarku, mufad'a a cikin kowacce sallar farillah data nafila, insha ALLAHU, ALLAH zaimana sakayya._*
Kije keda ALLAH, shine zaimana maganinki, ALLAH ya shiryeki, kuma kikoma islamiyya danneman ilimi akan hak'ik'in Dan Adam a musulince, damunin fad'ar mummunan kalma ga musulmi.
Kema kifara gyara kanji kafin kigayara wani, kuma kema kinada damar rubuta tarihin Nana Aysha (RA) harmu karanta mu amfana kamar yanda kika fad'a. Tunda mu bamuda ilimin addini rubutawa.
Kai kai kai ALLAH ya Isa tunda kika dangantamu da zina.
😭😭😭😭😭😭
*_page→51-52_*
..........Alhamdullahi abubuwa sunata gyaruwa, riba sosai su ya Umar suka samu akan kayansa, wayyo zokaga farinciki wajensu.
A 6angaren gyaran mall NASA kam aiki yayi nisa, yanzu hakam fenti akeyi. Mutanedai sai zind'e da dariya sukeyi wai ya Umar ya saida mall d'insa, musammanma abokansa. masu k'aunarsa Dan ALLAH kuwa bak'inciki sukeyi dak'ara tausayinsa, Dan azatonsu yasayard'in da gsk.
Muktar yana zaune amota yana kallon masu aikin Fentin, fitowarsa kenan daga wajen bayan yagama duddubawa.
Sallamar da akai masace tasakashi d'agowa, matasan samarine su biyu, d'aya aciki ya ce, "sunana Tasi'u, wannan kuma Salman, idan bazaka damuba kazomuje can mana, suka nuna majalissarsu, munga kullum kazo saidai kaita zama a mota, wanan ba girmanka baneba.
Murmushi Muktar yayi, Dan dukansu yaganosu abokan Umar ne.
OK babu damuwa ngd sosaifa. 'Yafad'a yana fitowa'.
Yana kallon sanda Salman da Tasi'u suka kalli juna suna murmushi. aransa ya ce, " Niba Umar baneba, wuju-wuju zan muku wallhy.
Har majalissar suka k'arasa, dukyabama sauran hannu suka gaisa, yasami guri a zauna, hira akacigabadayi cikin raha, zuwacan Hafiz ya ce, "kai ammafa wajennan yayi k'yau wlhy, kunyi k'ok'ari wajen gyarashi, daga gani ya lashe miliyoyin nairori gsky.
Murmushi Muktar yayi, wlhy d'an uwa yaci kud'i kam, bak'aramar 6arna wutar taima wajenba, shiyyasa nake tausayama wannda yakeda wajen.
Aidolene a tausaya MASA Cesar Kabeer yana turo baki gaba alamar zund'e, to amma shine yasayar maka da wajen?.
Saida muktar ya kallesa sannan yasaki wani murmushin mugunta, eh shine ya sayarmana, amma da sainaji kamar ance bokinkine.
Kamar antsikari Dr jafar ya ce, " eh adakam abokinmune amma yanzu ko Inda yake bama musaniba, ranar wani abokinmu harda zuwa nemansa, inagadai baisan yanzu yazama karfaba.....
Gabad'aya suka bushe da dariya amma banda muktar daya tsaya kallonsu, k'asan zuciyarsa kam yanajin wani d'aci. Shimamakima yakeyi yanda Dr Jafar d'in bai ganeshiba.
Haka sukaita tattaunawa da zagin ya Umar, shidai Muktar suna bashi mamaki, sai gab da magriba yamusu sallama yatafi gida cikeda mamakin halin d'an Adam.
Koda wasa Muktar baita6a bama ya Umar labarin yanda sukayi dasu Hafiz ba, amma kullum yana nusashsheshi akan yadage da addu'ar Neman tsari, Dan tabbas yana zagaye da mak'iya, kuma komai zasu iya aikatawa akansa idan sunga ALLAH Yakuma d'aukakashi.
Sosai YA UMAR yakar6i shawarar Muktar, haka suka duk'ufa addu'a shida matarsa, yanzu sundage tashi duk dare suyita nafilfili da mik'a kukansu ga ubangijin talikai, ga azumin litinin da alhamis sunatayi, sadakama ba'a barsu abayaba.
Duk hidimarnan da akeyi babu Wanda yasan abinda ke faruwa a family d'in ya Umar. Inna Ce kawai tasan komai.
Itama kuma tayi gum abinta.
Ranar ya Umar yaje gaigaida iyayensa, yana zaune ak'asan kafet yayinda mama take saman kujera, sai cika take tana batsewa. Kan ya Umar na ak'asa.
Mufida da Rafi'a sunama islamiyya.
Cikin masifa mama ta ce, "Umar ni wacece awajenka?.
Saida yad'ago yad'an kalleta sannan ya ce, " mahaifiyatace!."
Inafa mahaifiyarka Umaru!, aidaka d'aukeni matsayin mahaifiyarka dabaka saida shagunankaba harka kasa fad'amin. Wato kamaidani lasha money ko?.
Ajiyar zuciya ya Umar ya sauke, murya a sark'e ya ce, "kiyi hak'uri mama, koda nasayar aii bama abani kud'inba, sunce saisun gama gyarashi sun tabbatar babu matsala sannan subani kud'in, shiyyasa Nima na 6oye miki, nafison da anbani kud'in sainazo na nuna miki saikinfi yin farinciki.
Mama tagyara zama tana k'ara washe hakwara, eh kumafa da gskyarka Umaru, dama kaga gashi ansaka bikin mufida wata biyu kenan, yanzu saura wata uku, ninasan mak'on Abubakar bazai barsa yaymata kaya masu tsadaba alkur'an kuwa. Inadai fata kafin bikin kud'in namu sun fito ko?.
Kai kawai ya Umar ya iya jinjina mata saboda 6acin rai, uwa uwace babu mai canjata, shibaisan wane irin haline da mamaba........?.
Maganartace takuma katse masa tunani.
Yauwa Umaru ALLAH yayi maka albarka, ammafa kayi hak'uri ankgaya maka maganar bikin Mufida amakare, wlhy Abubakar ne yahana afad'a maka, kasandai halinsa na nunkufurci......
Da Sauri ya Umar ya ce, " babu komai mama, nibara nawuce, inaso nad'anyi wani aikine.
To...to....to Umarina, amma bazaka tsaya ko d'an wani Abu kaciba?, inada wani dambun nama kuwa zauna kaci.
Mama kibarsa kawai, ina saurine aii.
A'a aiba'ayi hakaba, bara na k'ulla ka kaima d'iyata Asma'u. Tana maganar tana shiga d'aki.
Ya Umar yagoge wasu 'yan kwalla da suka tarumasa agefen idonsa:- dawanine yafad'a masa akwai iyaye masu irin halin mahaifiyarsu walhy dasai ya k'aryata, da'a film yagani saiyace wasan kwaikwayone, da a Novel yakaranta dasaiyace k'aryace kawai da wasa da hankalin mutane irinna marubuta. To amma gashi ra'ai-ra'aini yana gani. Ya ALLAH ka shiryi irin wad'annan iyaye!.......
Yauwa Umarina gashi, mama tamik'o masa bak'ar leda wadda aka k'unshe k'aramar roba a ciki.
Kar6a yayi yaymata godiya sannan yatafi.
Yana fita mama tafara rawar murna, kai ALLAH mungode maka kud'in zasu shigo, wlhy dama inata tunani akan yanda zanyi shagalin bikinnan Dan nasan Abubakar da shagen mak'o, k'ark'ari yabani dubu hamsin, amma kinga Umar konawa nace inaso wlhy yaronnan zai bani.
Kai talaucima baiyiba wlhy, aigarama daya saida shagunan koba komai aii zamud'an shana kwana biyu.
_Humm kai jama'a wanan wace irin uwace? kamata yayi tayi bak'inciki dayima ya Umar fad'a akan miyasa ya sayar, amma kuduba murna takeyi akan zasu sami kud'i, bata kallon halin dayake ciki da Wanda zaishiga nan gaba, a'a ita burinta kud'i, gashi tanata bin matakan dazata raba zumincin 'ya'yanta, yau ta nuna tafison wanan, gobe kuma tafison wancan, kaiconmu da masu hali irinna mama, wlhy iyaye kugyara, shikenan da 'ya'yanka sunfara girma saika d'auki duk nauyinka ka maida akansu, wlhy hakan yana kawo raini tsakanin 'ya'ya da iyaye. Indai d'a yakasance nakwarai kuma d'an halak bazai manta da halaccin iyayeba, bazai manta da gwagwarmaya irinna iyayeba musamnamma uwa, kahanata barci tun kana acikinta, kahanata cin abinda take so tun kana acikinta, kahanata sukuni tun kana acikinta, ta haifeka cikin magagin wahala, ta raineka, idan bakada lafiya kana kuka tanayi, idan kaji yunwa tabaka kaci koda ita bataciba, tagoyaka, ta wanke kashinka, idan anta6aka ranta ya6aci, konawa tasamu zata kashesu akanka dankayi farinciki, katuna gwagwarmayar da mahaifinka yakeyi wajen nema muku abinda zakuci da kud'in makarantarku Dana asibiti._
_Amma dan rashin tunani harka iya kasa k'yautata musu sai sun rok'eka, kai wlhy kaicon wad'annan 'ya'ya. Iyaye mugyara, 'ya'ya mugyara Dan ALLAH._
Koda ya Umar yafita saiya samu adaidaita yashiga zuwa gida. Zuciyarsa namasa ciwo da tunanin hali irin na mahaifiyarsu, amma kokad'an abinda take masa bai gutsiri ko kwayar zarrah daga k'aunar dayake mataba irinta d'a da uwa, yanason mahaifiyarsu, akullum kuma yana mata addu'ar neman shiriya wajen ubangiji.
Har suka iso baimasan sunzoba, saida mai Babur yata6ashi sannan yakawo nimfashi, kud'insa yabasa yay masa gidiya.
Shago yafara Shiga suka gaisa dasu Harris sannan yak'arasa cikin gida.
Idonsa nakan Asma'u dake a kwance a tsakar gida bisa tabarma, agogon hannunsa ya kalla 5:13pm. Ya girgiza kansa, afili ya ce, "yarinyarnan bazaki daina wanan barcin la'asar d'inba dakika koya ko?. Narasa mike damunkine haka?.
Yana maganar yana tafiyane gareta, harya k'araso yazauna Kusada ita. takalmin k'afarsa yafara k'ok'arin cirewa yana fad'in Husna! Ke Husna! Tashi mana.
Asma'u batada nauyin barci sosai tabud'e ido ahankali, ganin ya Umar zaune Kusada ita yasata yunk'urawa ta tashi da k'yar. yad'an juyo ya kalleta ya kakka6e safar daya cire. Waini barcinnan dad'i yakemikine dakika kasa dainawa? Magana tanawa nayi miki akan barcin la'asar?.
Hamma Asma'u tayi tanad'anyin mik'a, kayi hak'uri Yaya wlhy nima bansan sanda barcin ya sacenibamafa, zaune nake ina kallo awaya.
Takalmansa yagyarama zama, yad'ora safar akansu sannan yamatsa baya sosai ya zauna tareda jingina da bango.
Jawo Asma'u yayi kusadashi. Husna kodai akwai abinda ke damunki? Wanana barcin naki yafara yawa,