Showing 42001 words to 45000 words out of 77995 words

Chapter 15 - karayar arxiki COMPLETE

12 Jul 2024

9239

Shago yafito, Harris nata kaikawo saboda masu sayen abubuwa musamman 'yan makaranta. Dan akwai wata Secondary acan samansu, kuma tanan 'yan makaranta sukebi su wuce.
Kujera yaja ya zauna yana binsu da kallo d'aya bayan d'aya.
Saida Harris yagama sallamarsu duka sannan ya zauna suka gaisa da ya Umar.
Lallai Harris nagafa alama babban d'an kasuwa za'ayi anan. kadage sosai.
Dariya Harris yayi yana Sosa kai, Yaya damacan shashancine yasa ban maida hankaliba. Amma yanzukam nagane saikanadashi akeyi dakai a wanan duniyar.
Murmushi kawai ya Umar yayi, amma baice komaiba.
Suna nan saiga Muktar yafito zaikai su Faisal makaranta.
Duk yaran suka gaida ya Umar da Harris. Shima Muktar suka gaisa.
Ya Umar yahad'a musu kayan kwad'ayi na yara aka sakama kowa a cikin lunch box d'insa. godiya sukayi. Muktar ya ce, ''gsky abinnan yayi yawa Umar, wanan aiisu Faisal aka bud'ema shagon.
Gira ya Umar yad'age ya ce, ''ko."
Eh mana, kullumfa saisun cinye ribar.
A to kai ina ruwanka, shagonsune aii, idan bazaka iya ganiba kabar shigowa.
Dariya kawai Muktar yayi, ya ce, "to ALLAH yasaka da alkairi, ya k'ara bud'i. Bara nakaisu School nazo nawuce aiki kada na makara.
OK saika dawo to.



*_9:00am_*
Sai k'arfe tara Asma'u ta farka, waige-waige tafara na Neman ya Umar, amma saitaga wayam. tashi tayi a sanyaye tashiga bayi domin yin wanka. Batawani jimaba tafito, 'yar kwalliya tayi daidai misali tashirya cikin siket da Riga na atanfa. Haka tagyara gidan duk jikinta asanyaye, agurguje tahad'a break mai sauk'i.
Na Harris ta had'a tanufi shago kaimasa Dan batayi zaton mai gayya mai aikin ya Umar yana canba.
Sallamarta tasakasu d'agowa suduka biyun. Harris yay saurin tararta yana fad'in kai k'anwata yau kad'an garage nafara kukan yunwa.
Murmushin yak'e tamasa, kayi hak'uri ya Harris namakarane yau. ‘tayi maganar tana satar kallon ya Umar daya canja fuska tunda yaji sallamar Asma'u.’
d'auke idonta tayi daga kallonsa ta cema Harris ina kwana.
Lafiya lau Asma'un Yaya. Kin tashi lafiya?.
Alhmdllh.
Kanta ak'asa ta ce, ''ya Fharuk ga Break.
Saboda Harris yadake ya ce, " ina zuwa."
Batace komaiba takoma cikingidan tana mamakin ya Fharuk d'in nata.

Ganin har wasu mintina bai shigoba tazauna tayi tagumi.
Talula sosai duniyar tunani taji sallama. Afirgice tad'ago danjin an jijjigata.
Anty Sa'a ta ce, "Asma'u lafiyarki kuwa?."
Ajiyar zuciya ta sauke mai k'arfi, fuskarta d'aukeda murmushin yak'e, ta tatshi ta k'ank'ame Anty Sa'a tana mai farincikin ganinta.
Itama Anty sa'a saita rungumeta.
Bayan ta shimfid'ama Anty Sa'a tabarma ta zauna ta ce, "Anty inazuwa."
Kai kawai Anty Sa'a ta iya d'aga mata, amma sai binta takeyi da kallo. Sosai Asma'u ta rame mata. Aranta ta ce, ''tomike damun yarinyarnan ne haka?......
Tana cikin zancen zuci Asma'u tadawo d'aukeda ruwa da kayan break d'inta dabataciba.
Anty Sa'a bismillah.
A'a nikam ak'oshe nake ma'u, baradai nasha ruwan kad'an tunda rana tad'aga, sanyin yad'an rage kafin yamma.
Fuska Asma'u ta shagwa6e kai Anty Sa'a Dan ALLAH kici ko kad'anne.
Ganin zatayi kuka Anty Sa'a ta ce, "to naji maida hawayen zanci. Murmushi Asma'u tayi, yauwa Anty babba.
Itamadai Anty Sa'a murmushin tayi. Sai sannan Asma'u ta gaisheta. Ta amsa cikeda fara'a. Ta d'ora da fad'in Ma'u! Shin bakida lafiyane? Kika rame haka?.
Sunkuyar dakai Asma'u tayi k'asa, cikeda jin kunya ta ce, " a'a lafiyata k'alau Anty.
Kai Asma'u ban yardaba, kinga kuwa yanda kika rame?, damacan gaki babu auki kamar a hure.
Kodai Umar ne yake takura miki? Dan nasansa wata sa'in akwai fad'a.
A'a Anty babu komai wlhy, kawaidai idonkine yake nuna miki na rame.
Humm Asma'u kenan, saikace wadda tafara saninki yau. Sati Ukufa dasuka wuce na ganki, kuma da k'ibarki kodai cikine dake?.
Da sauri Asma'u tad'ago tana kallon Anty Sa'a, suna had'a ido tamaida kanta k'asa cikeda kunya. Murya can k'asa ta ce, a'a Anty banida komai.
Ajiyar zuciya Anty Sa'a ta sauke, tasan akwai abinda ke damun Asma'u zahiri. To amma tak'i fad'a.
Shiru nawani d'an lokaci babu Wanda yasake magana.
Can Asma'u ta ce, "Anty ya yara?.
Suna lafiya, duksun tafi school.
Lah Anty harda Abba?.
Eh shima aii ansakashi wata kusan 1 kenan.
Eye yakaga abbati a school.
Dariya Anty Sa'a tayi kawai.

Shigowar ya Umar yasakasu kallon k'ofa suduka.
Suna had'a ido da Asma'u ya harareta.
Anty Sa'a ta ce, " d'an k'anina kadawo?.
Eh wlhy Anty, saukar yaushe?.
Yanzu babu dad'ewa nazo aii. Nalek'a shago naga sai Harris kawai, ya ce, "min kaje nan k'asan layi wajen wani.
Wlhy kuwa, sannu dazuwa, ‘yafad'a yana zama.’
Yauwa kaima sannunka.
Gaisuwa sukayi irinta wad'anda suka shak'u d'innan. Daga nan akahau hirar yaushe gamo.
Asma'u dai batacewa uffan, daga bayama saita tashi tsaye tana fad'in yaya abincinfa?.
Kansa ya girgiza mata alamar a'a.
Mikewa tayi a sanyaye tabar wajen tashige bedroom d'inta.
Daga ya Umar har Anty Sa'a da kallo suka bita, saida ta 6acema ganinsu sannan ya Umar yata6e baki. Anty Sa'a kuma ta ce, " Umar da matsala ko?."
Kallonsa ya maido gareta ya ce, "Anty matsalar mi?."
Kaida Asma'u mana.
Kansa ya girgiza alamar a'a, amma baiyi maganaba.
Hummm kaima haka zaka cemin kenan?.
Ita mita gaya miki?.
Yanda kafad'amin mana, ta ce, "babu komai, nayi tambayar duniya tace babu komai. Ni nazatama batada lafiya ko cikine?.
To ammafa naga kana harararta, kuma yanzu tace ga break. Kace ka k'oshi.
Kodai bakaso nasan matsalar gidankane?.
Bahaka baneba Anty, gsky muduka muka fad'a miki babu komai.
To kudai kuka sani, dukda nasan ayanda akayi aurenku kaida Asma'u babu wani shiri ko shak'uwar soyayya, amma yakamata zuwa yanzu komai yazama tarihi. Musamman yanda Asma'u tayi halacci agareka. Bata zama mai rama alkairi da muguntaba. Kaikaga yanda tashiga Rud'ani alokacin dabakada lafiya? duk Wanda yaganta yasan tana tsananin sonka. Kadaure kaima Umar kanuna mata soyayya, karungumi matarka kusami zuria mai albarka, tunda an rabaka da *_Afrah & Amrah_* kanaji kana gani.
Ajiyar zuciya ya sauke, tuni zuciyarsa tafara bugawa da sauri-sauri. Harga ALLAH yanason 'ya'yansa, kullum dasu yake kwana yake tashi. Rana d'ai-d'aine baya mafarki dasu........
Anty Sa'a takatseshi dafad'in kayi hak'uri bawai natunomaka dasubane dan katashi hankalinka, ALLAH yana sane da kowa. Amma ka gyara mu'amullarka da matarka kuma 'yar uwarka.
Karki damu Anty Sa'a komai yawuce wlhy.
To shikenan, yamzu bara nakirata tabaka break d'in ko?.
Kansa kawai ya jinjina mata.

Babu dad'ewa saiga Asma'u da Anty Sa'a sun fito.
Abinci ta shirya masa kamar yanda Anty Sa'a ta fad'a mata.
Duk tsoronsa ya mamyeta.
Zata koma d'aki Anty Sa'a ta ce, "tadawo tazauna suyi hira.
Babu yanda zatayi tadawo ta zauna. Sund'an ta6a hira sannan ya Umar yafita saboda kiran da Yazeed yay masa na gaggawa.

Bayan tafiyarsa Anty Sa'a tatsare Asma'u da tambayoyi cikin lallashi da lalama.
Haba Ma'un inna, kobaki d'aukeni amatsayin yayarki bane? Indai har zaki iya fad'ama Saratu damuwarki aii nima d'aya nake nida saratun. Kokuwa bahaka baneba?.
Hakane Anty, ‘Asma'u tafad'a murya na rawa kamar zatayi kuka.’
To kinga fad'amin na taimaka miki koda da shawarane inma bazan iya maganin matsalar takiba.
Asma'u tayi shiru tana tunanin ta fad'a kotayi shiru? To amma aii koda shawara Anty Sa'ar ta taimaketa aii kamar yanda tafad'a. To aii kuma wanan sirrintane, kuma ALLAH ya tsinema mai bayyanashi. Kai itakam yazatayine?. Gsky tana cikin matsala, Dan inhar bata fad'ama waniba ya taimaketa da shawarar yanda zata kula da mijinta tofa tabbas tana cikin matsala, koda yaushe aurenta zai kasance cikin yin rawane.........
Anty Sa'a ta katseta da fad'in kinyi shiru Asma'u. Kokin gammace kita zama cikin matsala keda mijinki?. Kowacce mace batada fadar farinciki irin gidan mijinta. to amma ke kin gwammace yazamemiki gidan wak'afi!!??.
Girgiza kai Asma'u tayi tana zuraro da hawaye.
Tabama Anty Sa'a tausayi, Dan haka tarungumota jikinta tana share mata hawayen. Fad'amin kinji Asma'u zakiji sassauci azuciyarki....
Cikin shashshekar kuka ta ce, "ya... Fha...ruk... ne."
To miyayi miki?.
Shiru nawani d'an lokaci, sannan Asma'u tafad'i abinda zata iya.
Shiru Anty Sa'a tayi tana tausayin Asma'u. Baiwar ALLAH shiyyasa dukta rame, kai aii fitinannen miji saimai hak'uri da juriya, amma insha ALLAH zata taimakawa k'anwar tata kodan taku6uta wajen damk'e mijinta ahannunta gam-gam.
Karki damu Asma'u, indai akan wannanne Umar bazai sake fushi dakeba saidai ya sanya miki albarka. Ki kwantar da hankalinki, sannan kidaina nuna masa kinajin tsoronsa aduk lokacin daya bukaceki kinji, idan har kika cire tsoro da fargaba tom zaki zama jaruma insha ALLAH.
Yanzu idan yadawo kuma kibasa hak'uri, insha ALLAH zai hak'ura.
To Anty duk zanyi, ngd sosai.
Karki damu Anty Sa'a ta fad'a tana shafa kan Asma'un.

Anty Sa'a batabar gidanba saida takoyama Asma'u dabaru kala-kala, sannan ta ce, ''tajira sak'o nanan zuwa gareta, zatabama Rafi'a takawo mata, zata rubuta mata bayanin komai.
Godiya sosai Asma'u tama Anty Sa'a, sanan suka shiga shago wajen Harris, bayan and'anyi wasa da dariya Anty Sa'a tatafi da tarin alkairi da Harris ya had'a mata bisa Umarnin ya Umar.



Ya Umar kam koda yafita sai office wajen Yazeed.
Kamar yanda suka saba suka tari juna cikeda farinciki, bayan d'an barkwanci irinna abokai suka shiga abinda ya kawosu.
Yazeed ya ce, "abokina albishirinka.............






*_tofa masu karatu, wane albishir yazeed zaima ya Umar Fharuk ne?._*
*_kubiyo ni mata agidan Abdus'salam danjin yanda zata ritata👌🏼😉_*





*_(((S)))........2017_*
*_I Love you all._*
[12/20/2017, 6:27 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻.........



💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* 💎


*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*


*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_


*_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO.....😜_*


*_ina kuke masoyan Karayar Arzrek'i? ku marmatso-ku marmatso, yaufa shafin da gaisuwar fatan alkairin duk nakune, ina godiya da nuna soyayyarku gareni, inamai kuma baku hak'uri darashin posting d'ina akoda yaushe, alkairin ALLAH ya tabbata agaresu aduk inda kuke, banida damar ware sunan wani bansa nawaniba, amma duk kuna raina, masu kira a waya, damasu toromin sak'o, kai harma wad'anda ban saniba, ina alfahari da masoyina akowane lokaci, nagaisheku da k'yau abokan tafiya._*
*_Hakama ya Umar & Asma'u suna mik'o gaisuwa._*
_I love you so much💋_


*_page→49-50_*


..........Goro fari k'al abokina.
Yazeed yayi murmushi tareda mik'ama Umar wani file.
Ya Umar yakar6i file d'in zuciyarsa cikeda tunani. Bud'ewa yayi yahau dubawa.
Cikin maruk'ar farin ciki ya rungume Yazeed yana fad'in Alhamdulillahi ya Ubangijin talikai.
Yay hanzarin sakin yazeed yashige bathroom d'in dake office d'in, mintuna kad'an yafito d'aure da alwala. Yazeed dai sai kallonsa yakeyi yana dariya. Ya Umar bai kulashiba ya d'auki abin sallah ya shimfid'a a office d'in.
Sallah yayi raka'a biyu, yadad'e awajen sujuda bai d'agoba, yanata mik'a godiyarsa ga ALLAH, harda kukan farin ciki.
Yabama yazeed tausayi sosai.
Saida yadad'e yana addu'oi sannan yatashi yadawo Inda yazeed yake. Tsirama yazeed ido yayi tamkar mai Neman wani abu, a jikinsa........zuwacan kuma yaja wata sassanyar ajiyar zuciya!....Abokina.........
Yazeed yay saurin d'agama ya Umar hannu Alamar baya buk'atar godiya.
Shiru kuwa ya Umar d'in yayi, yakulle bakinsa yana cigaba da kallon yazeed.
Shima yazeed d'in shiyake kallo, saikuma sukaima juna murmushi, yazeed ya ce, "abokina natayaka murna matuk'a wlhy, amma tabbas akwai lauje cikin nad'i dangane da rik'e kayanka, saidai koma waye shida ALLAH kawai.
Ajiyar zuciya ya Umar yasauke, tuni idanunsa sunyi jajur, cikin muryar 6acin rai ya ce, " nadad'e ina zargin hakan, tun lokacin da akaita min yawo da hankali Dan Neman ku6tar kayan. Amma babu komai, koma wanene nayafe masa, ALLAH kuma ya shiryesa.
Ameen namijin duniya. ‘yazeed yafad'a yana sarama Umar.’
Ya Umar yayi murmushi mai k'ayatarwa, murya a sanyaye ya ce, "yazeed kahana namaka godiya, bansan miya saba?."
Bana buk'atar godiya Umar, inhar kad'auka nida kai 'yan uwan junane, to karka godemin.
Humm yazeed kenan, wlhy tunbama yauba dama kallon d'an uwana najini nake maka, akullum darajarka k'aruwa takeyi bisa mizanin zuciyata, ALLAH yajik'ansu Abba da rahma, ALLAH yaraya zuri'a, ALLAH yayi maka sakayya da mafificin alkairi, yanda kayi sanadin dawowar farinciki agaremu kaima ALLAH yasaukar da farinci wa rayuwarka mai albarka har Abadan.
Ameen Abokina ngd sosai, ALLAH yabarmu tare.
Sundad'e suna hira abinsu cikeda farinciki da k'aunar juna.
Sun yanke hukuncin raba kayan na ya Umar gamasu buk'atar sari, shikuma kafin ya kammala gyaran mall d'insa sai ayi k'ok'arin shigo dawasu kayan.
Wannan shawara tayima ya Umar dad'i, Dan haka ya rungume yazeed yana kwararo addu'ar alkairi agareshi.
Daganan sallama sukayi ya Umar yatafi gida........



•∆•
Tunda Anty sa'a ta tatafi Asma'u tatashi takuma gyara gidan tsaf, abincin rana tayi na musamman Dan sotake su shirya da ya Umar d'in.
Taje ta tsala wanka, yaukam hardayin kwalliya, abinda baicika damun Asma'u ba. Ita da'ayi kwalliya Dakar ayi duk d'ayane agareta. Yaudai haka tayi mai sauk'i amma Tamata k'yau.
Zani da Riga tasaka na lemon green d'in shadda, tayi d'auri mai k'yau tareda feshe jikinta da turare mai dad'in k'amshi.
Faisal tabama abinci yakaima Harris da Sadam a shago.
Tana zaune ad'aki tanata latse-latsen waya ya Umar yashigo gidan da sallama.
Babu kowa a babban falo Dan haka yawuce d'akinsa abinsa. Wani ni'imtaccen k'amshine yaratsashi kamar na falon, shak'a yayi ya lumshe idanunsa yana sakin murmushin jin dad'i. Ahankali ya furta ALLAH yay miki albarka my Asma'u husna!.

Nikam danake a la6e nida su Manshat mukace amin.

Yana Shiga bathroom yatarar dawani abin mamakin, ruwan wankane na musamman aka had'a masa. Baimayi niyyar wankanba, yashigane domin sauke nauyi🤐, to amma ganin ruwan wankan yasakashi sha'awar yi.
Aiko yatu6e ya zabga wanka abinsa.

Duk shagalinnan da ya Umar keyi Asma'u batasan yadawoba. Tanacan tana zabga charting da 'yan *_TASKAR LITTATAFAN HAUSA_*😻, su o e sai zabga mata surutu akeyi🙄bandai fad'i sunaba ehe😏, amma nasan kun gane aii😜

*_Ina sonku da Alfahari daku 'yan group d'ina, taskar littatafan Hausa, I love you so much my Darlings._*💋❤❤

Saida yashirya tsaf cikin doguwar riga mara nauyi ash color sannan yanufo d'akin Asma'u. Azatonsama barci takeyi.
Yadad'e tsaye abakin k'ofa yana kallonta amma batasaniba.
Gyaran murya yayi wadda tasaka Asma'u razana tajefar dawayar gefe tareda kwalla k'ara.
Yanda tatsorata sosai saiya bama ya Umar dariya, aiko yashiga tuntsura dariya tamkar bashiba.
Jin dariyarsa yasaka Asma'u dake shirin shigewa bayi Dan Neman gurin 6uya ta tsaya cak. Wata wawuyar ajiyar zuciya tasaki tana fad'in kai ya Fharuk! Wlhy kabani tsoro ainun, kaji kuwa yanda zuciyata ke bugawa da k'arfi?.
K'arasowa yayi inda take, har yanzu dariyar yakeyi, itama zuwa yanzu tafara darawa, yakama hannunta suka koma gefen katifar suka zauna.
Kai Husna dama haka kike matsoraciya? Kinga kuwa yanda kika birkice? Hhhhhhhhh!!!!! Yakuma saka wata dariyar harda kwanciya akan katifar.
Baki Asma'u ta tunzuro gaba, kai yaya kabani tsoro kuma kadawo kanamin dariya. Nidai kabari plss.
Tashi yayi zaune, to aiked'ince kamar farar kura. Kai ammafa kin iya gudu zazuuuu! kenan. ‘yay maganar yana rungumota jikinsa.
Itama k'ank'amesa tayi tana 'Yar dariya k'asa-k'asa.
Ya Umar ya ce, "to azatonki wanene zai shigo d'akinki idan baniba?.
Kasanine wlhy banji koda motsin dawowarkabane, kuma yanzu hira mukeyi a group wai ana shiga gidan mutane da ranar ALLAH sata, wani lokacinma har fyad'e akema matar gidan ko idan sunada 'yammata. Tofa shine nikuma kawai naji gyaran murya batareda sanin shigowar mutumba. Aikaga dolene

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login