Showing 66001 words to 69000 words out of 77995 words

Chapter 23 - karayar arxiki COMPLETE

12 Jul 2024

9244

danshi ya ce, ''yasakata makarantar koyon girki. Gashi kuma shawararsa tayi musu dad'i su suka, Dan yanzu ko yawan fad'an nan basayi da ita.
Saida sukayi sallar la'asar a masallacin anguwar su yazeed sannan muktar da ya Umar suka taho sukabar yazeed a gidansa.
Da sallama yashigo gidan nasa, ganin takalma reras ak'ofar falon yasashi jan birki, Dan muryoyin mata yake jiyowa dayawa sunata hira da dariya.
Harya juya zai koma saiga inna baito tafito daga band'akin tsak'ar gidan.
A'a Umaru kadawo?.
Eh wlhy inna, ya gidan?, wani biki ake haka?.
Dariya inna baito tayi, ta ce, "a'a su Sa'adatu nefa.
Kallan takalman yakumayi, ya ce, " inna amma naga talkalmane reras, harsu nawane?.
Su 6 ne, fatee, Rafi'a, kaltume (d'iyar inna baito Ce), Sa'adatu, saikuma Saddiqa matar muntari.
O wlhy nama zata wasu bak'ine daban.
Shida inna baito suka shiga.
Saddiqa naganinsa tatashi tana musu sallama, dantasan itama nata mijin ya dawo, gaisawa sukayi da ya Umar tatafi.
Shima ya zauna suka gaggaisa, Anty Sa'a ta ce, "Umar wannan d'aukar wanka haka? Daga ina?.
Shafa kansa yayi yana dariya, idonsa akan Asma'u dake tsiyaya masa ruwan sanyi a cup, ya ce, " Anrty Sa'a d'aurin aure mukaje wlhy."
Tofa, waye yayi aure a irin wannan time d'in haka?.
Ya Umar yakar6i ruwan da Asma'u take mik'o masa, yad'an ta6e bakinsa sannan ya ce, "wani banzane,.... saida ya shanye ruwan sannan yajuyo yana kallon su Anty sa'a dasuka had'a baki wajen fad'in banza kuma!!?.'"
O sorry, wani abokina zance mukufa.
To ALLAH ya sanya lkairi suka fad'a atare.
Ya Umar yamik'e tsaye batareda yace aminba.
Asma'u ta ce, "Abincifa?."
Shiru yayi yashige d'akinsa.
Anty Sa'a ce ta ce, "mata tashi kibishi d'akinsa, waya gaya miki ana tambayar miji yanason Abu acikin mutane? Asma'u nakula sainayi training d'inki gsky akan kula da miji."
Shiru Asma'u tayi tamik'e zuwa d'akin ya Umar, tanata tunane-tunane aranta, ita kanta tana ganin wataran kamar batayin abunda yakamata wa mijinta, to amma tayaya zata gyara? Gsky itama tanason taga suna rayuwa da mijinta kamar yanda akeyi acikin Hausa novels, abin Na birgeta sosai, musamman data kula ya Umar d'an son soyayyane. Itama tanason soyayya, to amma saita rasa yanda zata nunama ya Fharuk d'inta, Dan ita mutumce mai kunyar tsiya, dukda tad'anyi karatunta har zuwa diploma, yakamata kuma ace kanta yawaye, amma matsalar da'aka samu shine harta gama karatunta batada wata k'awa, k'annenta sune k'awayenta, wannan yasa batasan wasu abubuwanba dayakamata mata tanayima mijinta danya zama NATA ita kad'ai.
Kamar yanda Anty Sa'a ta ambata to zata nutsu danta samu training d'in kama ya Umar d'inta ahannu ita kad'ai..........
Tunda tashigo yake binta da kallon mamaki, shin mike damun matar tashine haka? tana tafiya tana tunani?.
Shigowarta takai minti 15 a tsaye, amma alamu sun Nina masa bamata tareda duniyarsu baki d'aya, hankalinta yatafi zuwa wata duniya tadaban. Ya girgiza Kansa tareda tasowa har zuwa Inda take atsaye tana cigaba da sak'a wasik'ar jakuna.
Bata ankaraba saitaji an d'alli bakinta. Cikin Sauri tasaka hannunta tadafe bakin, tareda kai dubanta gamai mata wannan aika aikar haka.
Ya Fharuk ne tsaye agabanta, yacire kayansa dagashi sai best da gakeren wando, ya hard'e hannayensa ak'irji idonsa k'ur akanta.
Ta sauke ajiyar zuciya ahankali sannan takauda kanta.
Ajiyar zuciya ya sauke shima tareda warware hannunsa, Asmah kinada gyara sosai ta hanyar kula dani wlhy, akwai abubuwa masu yawa dakikemin inajin dad'insu dakuma yaba miki.
Akwaikuma masu yawan gsky da idan kikaimin suna 6atami6n rai, nidai asanina mace kullum k'ok'arinta yanakan tarairayar mijintane, ammafa ke agareki Bahaka baneba. Tabbas abinda nagaza samunsa abaya sanda inatareda Lubna nasamesu agareki, harma mafiyansu, saikuma abinda nake samu ga lubna kekuma bakiyiminsu.
Asma'u ni mutumne maison zama da wayayyiyar mace, bawai wayewa ta rashin kunyaba, wayewa irinta zamantakewar aure, nifa a ganina idanhar mace tanason mijinta yazama NATA 100% tofa saita zama Mara kunyar k'arfi da yaji.KeKekuma kunyarki tanad'an cutar damu gsky..

Duk wannan magamar da ya Umar keyi Asma'u natsaye idanunta Na zubar da hawaye, tabbas tasan akwai gazawa a al'amuranta Na kula da mijinta, amma tana buk'atar shawara.
Suduka kowa yayi shiru, ita tana kuka, shikuma yatsura mata idanu yana kallonta, amma yakasa wani yunk'urin lallashinta.
Sunkai tsawon minti 7 ahaka sannan ya Umar Yakama hannunta suka koma bakin gado suka zauna. ganin kukan NATA bamai k'arewa bane yasakashi jawota jikinsa ya rungumeta sosai yana shafa bayanta alamar lallashi, amma uffan baiceba.
Nanma saida sukaja wasu lokuta sannan Asma'u tad'ago tana kallonsa, ya Fharuk Dan ALLAH kayi hak'uri zan gyara, Nima kaina inaji a raina akwai abubuwan danakeyi ba daidaiba, amma rashin nunawarka yasa bana fahimta sosai balle na nemo hanyar gyaran.
Murmushi ya Umar yayi yana kamo hannunta, to yanzun Na nuna da kaina my Asmah, saiki gyara ko? Namiki hakane saboda kar agarin sakakinkifa Na hango wata awaje ta kwace miki ni. Yay maganar cikeda zolaya yana d'age gira sama.
Bakinta ta turo gaba, ni wlhy kabar fad'a, ALLAH banason kishiya.
A indaifa kina sakaci da rik'ona aiko zata kwankwaso miki k'ofa, dama ga d'aki nan inadashi. Jibafa tun kayan danatafi nabarki dasune ajikinki, tunfa na wankan safene, nasan kuma bazaki ciresuba sai wankan barci, amma sanda kina amarya bakyayin wannan kazantan? tundagadai cikin fodeyo kika fara wannan abun, gashinan yanason zame miki jiki.
Shiru tayi tana kallon hannayensa masu laushi da santsi dake rumtse da nata, tasan gsky ya Umar duk yake fad'a mata.
Ganin tayi shiru yad'an girgiza hannunta, kifayi hak'uri badan cin fuska nake fad'a miki hakaba, inaso kigyarane Dan nazama naki kekad'ai da yaranmu my Husna, inasonki dayawa, shiyyasa banason wani Abu yazo yasaka sonnaki yin rauni azuciyata kinji, tunkina 'Yar k'aramarki nake sonki har kika girma.....
Da sauri Asma'u tad'ago tana kallonsa, yamata murmushi, baki yardaba ko?.
Shiru tayi batace komaiba, ya matsa hannunnata, takuma d'agowa tana kallonsa. Muryarsa can k'asan mak'oshi ya ce, "nasan kema kina sona aii, amma kikaita 6oyewa, amma ni tuni naganoki. Ban gaskata hakanba sai aranar da aka sakamin rana da Lubna. to karki damu, yauga Umar fharuq mallakinki ke kad'ai da fodiyonmu. Ammafa idan kika cigaba da sakaci zai samo miki mai tayaki kula dash....
Ai bata bari yak'asa fad'aba tafad'a jikinsa ta k'ank'amesa tareda sakin wani kukan shagwa6a.
Shima saiya rungumeta yana dariya, 'yammata bimin kanki ahankali karki 6allomin ruwa d'inkin yafarke nashi 12. yakamatama nakira Dr Al-Ameen naji yaushe zamuje a kwancene?.
Itadai tana lafe ajikinsa tana shashshekar kuka.
Cikin 'Yar dariya ya ce, ''nasan inda wannan kukan yadosa da abinda kikeso, bara kigani namiki kar asaka uwata awak'a.
d'agota yayi ya manne bakinsu waje d'aya. Tun Asma'u na mutsu-mutsin kwacewa hartayi lif itama tafara bada gunmawarta....


Hummm masu karatu! Wata sa'in muma matafa akwaimu da gulmar tsiya araduπŸ€”πŸ€ͺ.



♣♣♣.
Tundaga ranar Asma'u da ya Umar suka shirya, yanzukam abubuwan datasan yanaso komai kunyar datakeji haka take dannewa tamasa. ga Anty Sa'a daga gefe tana koyar da ita wasu darussan. hakama inna baito, tunda ta fuskanci Asma'u sokuwace saita d'auki d'ammarar kowa mata yanda zata kula da mijinta.

Ayanzukam shikansa ya Umar yaga canji sosai, farinciki yacika zuciyarsa, wani son Asma'u nak'ara ratsa jijiya da 6argo zuwa jininsa. Shima tattalinta yakeyi sosai. Yakaita asibiti an kunce d'inkin CS d'inta, Dr Al-ameen kuma yabasu shawarar yanda zata kula da kanta batareda samun matsalaba, yakuma bata wasu magunguna.
Har harabar asibitin yarakosu hannunsa d'aukeda fodiyo, yanata yaba k'iba da lafiyar yaron, gashi masha ALLAH k'yak'yk'yawa son kowa k'in Wanda yarasa.

Gaban Dr jafar yafad'i Dan hango su Umar tsaye sunata dariya shida Dr Al-ameen cikeda nishad'i. Ga Asma'u agefensu cikin k'yak'k'yawar shiga ta alfarma, shikansa ya Umar d'in sanye yake da wata d'anyar shadda blue sai maik'o takeyi, tad'inku da d'inkin zamani, ga hularsa k'ube ya Murza mai adon farin zare da ratsin blue. Sai annurin farin ciki da kwanciyar hankali suke fitarwa.
Ganin ya Umar yakar6i Fodiyo daga hannunta Dr Al-ameen, Dr jafar ya ce, "kai, dama matarsa ta haihu?. Dukda sunad'an nesa dashi yana hango k'yak'yk'yawar fuskar fodeyo, da a ka masa kwalliya da milk d'in kayan sanyi na alfarma, ya sauke wata ajiyar zuciya alokacin da ya Umar yabud'ema Asma'u mota tashiga, ya rankwafa ya saka mata fodiyo akan cinya, wannan yarufesu yadawo sukai sallama da Dr Al-ameen shima yashiga motar suka tafi.

Jikinsa har rawa yakeyi yashiga motarsa shima sai majallissa kai rahoto, Dama yatashi daga aiki Dan yamma tayi............

🀣🀣🀣🀣🀣.



*_Amarya Lubna_*
Su Lubna amarya, antare akatafaren gidan data samu gado, Dan tace bazata zauna gida d'aya da matar Hafiz ba, a gidanta zata zauna. Babu musu ya yarda kuwa.
Komai na alfarma tazuba agidan, kud'inta kam bak'aramar girgiza sukayiba, ga 'yan aiki data Loda agidan, kowa da aikinsa, harda masu yimata tausa daban.
Amarci kam itada Hafiz ana dirzarsa, jitake kamar yanzu tayi auren farko.
Tamanta da kowa da komai, komai NATA sai Hafiz.
Shikam tarairaya iya tarairaya yake Nuna mata, matarsama ko lokacinsa bata samu, barema 'ya'yansa da iyayensa. Danginsa kam babu Wanda ke zuwa gidan, Dan Lubna tasaka dokar batason had'in gambiza.
Dayake lalla6ata yakeyi saiya yarda da zancenta, babu kuwa mai zuwa musu gida, shikam aii yazama mijin Hajiya, danko kwayar gero baita6a ajiyewa a gidanba, komai da kud'in Lubna akeyi tunda ta nuna tanadasu. Suci mai k'yau su saka maik'yau, suyi barci amai k'yau, dama su Amrah awajen mom aka barosu dansu d'ebe mata kewa....


*_Suhaima_*
Itadai Suhaima akwai banbanci da Lubna, Dan ita amarcin NATA yazo da gargada.
Ashe Ramadan d'an talakawane lik'is, irindai matasannanne masu son k'arya da burgar tsiya, shine Aron kaya shine na mota, dawannan abubuwan yabige tunanin suhaima harta amince ta auresa, Dama kuma tun awaje suke shek'e ayarsu.
Sai lokacin da'aka kaita taganta awani d'an gida kamar BQ d'in gidansu, aiko ranar kwana sukayi tafka bala'i.
Dole washe gari ya yarda suka koma gidanta data samu agadonta itama.
Hakan yamasa dad'i kuwa, Dan kobabu komai ansamu cigaba, dama wancanma babansane Yakama masa Hayar, Dan Ramadan baya aikin komai sai tsalle-tsallen 'yanmata. Sune samarin shaho na wannan zamanin.
('Yammata sai ayi hattara da samarin shaho, Dan akwai irinsu Ramadan dayawa suna yawo cikin duniya).








*_(((S)))......2018_*
*_Luv you all_*
[1/4, 4:45 PM] ~πŸ‡© ' πŸ‡― πŸ‡¦ πŸ‡· πŸ‡­βœ: πŸ‘©πŸ»β€πŸ’».........



πŸ’Ž *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* πŸ’Ž


*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*


*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_


*_NIKA'DAIπŸ‘ŒπŸΌ WRITER ASSO.....😜_*

*_page→71-72_*


..........Kiyyyyyy!! Yaja wani wawan birki agabansu. duk arikice suke kallonsa, Salman da shima isowarsa kenan yasa k'asan rigarsa yana toshe hancinsa saboda wata k'ura da Dr jafar ya tayar awajen.
Ganin yanda yafito abirkice yasaka sauran mik'ewa gaba d'aya, har sassarfa yakeyi yana had'a k'afa kamar zai kifa Dan k'ok'arin k'arasawa inda suke zaune.
Saidai kuma yana zuwa garesu kallonsu yacanja akala daga gareshi zuwa bayansa, Hafiz da Kabeer hard'an tureshi gefe sukeyi danson kallon abinda suka gani sosai.
Shima sai kawai ya waiga domin bawa idonsa abinci.
Motar ya Umar ce ta tsaya awajen, gaba kad'an da motar Dr jafar. Fitiwarsace taja hankalinsu wajen kallon mamaki agaresu. Shikam koma Inda suke bai kallaba, ya zagaya inda Asma'u take yabud'e mata k'ofar, fodeyo tafik'o masa, yakar6eshi hannu biyu yana murmushi da fad'in yauwa my dear son! Yau kanashan yawo ko?.
Asma'u tafito tana murmushi, yaya shima aii gara yasan gari ko?.
Cikin kallon k'auna ya ce, ''Kodai ke kinaso kiga garin? yafad'a tareda lakace hancinta.
Dariya sukayi gaba d'aya sannan suka jera atare suka nufi ainahin cikin mall d'in, ya Umar na rungume da fodiyo, ga Asma'u a gefensa cikin farinciki.
Su Hafiz kuwa tamkar sokaye haka suka dafama su ya Umar baya da kallo.
Tun a k'ofar wajen masu bud'e k'ofa suka fara rissinawa suna kwasar gaisuwa wajen uban gidansu.
Shikam cikeda fara'a irinta sanin hak'k'in d'an Adam yake amsawa, da nuna musu iyalinsa. Sunajin haka suka rissinawa suna gaida Asma'u itama.
Acikima bata canja zaniba sai rissinawa ma aikatan sukeyi suna kwasar gaisuwa.
Masu siyayya kam sunyi tsai tsaye suna kallonsu ya Umar d'in.
Wasu 'yammatanma harsun k'yasaπŸ˜‰. (Kunsandai rayuwarnan indai kanada 'Yar daud'ar duniya, to yanzu zakaga 'yan mata Na rawar kai akanka). ALLAH yasa mudace.

Da Sauri sadam yataso ya tarbesu, kar6ar fodiyo yayi daga hannun ya Umar tareda gaishesu.
Cikin zolaya Asma'u ta ce, ''lallai Na Rafi'a dolene kuyi Fari kaida ya Harris, Ashe kullum cikin Ac kuke wuni?.
Dariya sadam yayi, kai antymu kin iya Sheri wlhy, amma nidai bazance komaiba harsai kin bani Rafi'a zakiji bakina.
Dayawan mutanen dake gurin saida suka dara, Asma'u ta birge dayawan mutanen wajen, Dan da watace matar mai irin wannan wajen ai da irin shegen mai girman kannan za'ayi, da d'aukar kai, amma jiba yanda take wasa da dariya da ma'aikatan wajen. Dukdadai da alamar sanayya tsakaninta dashi, amma ta birgesu gskiya.
Ya Umar dake musu dariya ya kamo hannunta, kinga my Husna bar shiriritarnan idan kunje gida kwayi, muje kisayi abinda zaki saya mu wuce.
Kallonsa tayi cikin langa6e kai, yaya sayafa? Muda shagonmu?.
Cikin tsokana ya ce, "kema saikin biya aii".
Juyawa tayi tana kallonsu Harris da hankalinsu gaba d'aya yake kan Fodiyo suda wasu ma'aikata, Baki tad'aga zata kira Sadam, ya Umar yasa hannunsa ya toshe bakin. K lafiyarki kuwa? Mizakiyi?.
Kiransu zanyi naji waye ya kafa dokar?.
Cikin dariya ya Umar ya janye hannunta suka shige wani d'an d'aki, Ashe Office d'insane awajen. K'ofar yamaida yarufe yana dariya, kai my Husna ALLAH ya shiryaminke?.
Itama dariyar tayi tanabin ko'ina Na falon da kallon.
Manya-manyan hotunansu guda biyar tagani a kowace kusurwa ta office d'in, itadashi da fodiyo, akowace kusurwa, saikuma asaman tebur d'in an ajiye wani madaidaici itadashi nanma da fodiyo.
Kallonsa tayi, shikuma ya d'aga mata gira yana murmushi.
Itama ta sakar masa da murmushin tareda zuwa ta rungumeshi, hannu biyu ya kar6eta shima ya k'ank'ame kayansa, burinsa kullum yaga Husnarsa cikin farinci, yarinyar data masa hallacci alokacin damutane masu yawa da muhimmanci arayuwarsa suka gujesa, yarinyar dake sonsa Dan ALLAH badan dukiyarsaba, yarinyar data sadaukar daduk wani farincikinta domin NASA ya inganta, yo idanma yagaza Nuna mata k'auna aii yayi butulci mai yawa.....
Asma'u tad'ago tana kallonsa, amma fuskarta tad'an sauya, cikin langa6ewar kai ta ce, "ya amma banga su twins ba?."
Shima fara'arsa ya rage, sannan ya kauda zancen ta hanyar cewa muje yamma nayi karmu kwasarma fodiyo sanyi yazo yana mura.
Komawa tayi takuma k'ank'amesa, yaya kabani amsar tawa tambayar mana.
Wannan ba maganar nan bace, bari saimunje gida.
Baijira amsartaba yafice abainsa.
Itama dolene ta take masa baya Dan tasan halin kayanta sarai.
Ak'ofar office d'in tasameshi yana jiranta, ahankali suketa zagayawa suna d'aukar abinda suke buk'ata, dawanda fodiyo yake buk'ata, harda Hasiya da inna baito dazata koma gobe idan ALLAH ya kaimu.
Sosai suka Lodi abubuwan buk'ata, suna gamawa wani ma'aikaci yazo ya kar6i kayan, wajen kashiya's yaje Harris da sadam suka kar6a akai total.
Amamakin Asma'u saitaga ya Umar yaje yabasu ATM d'insa sun cire kud'in, aranta ta Ce, "Ashe da gsk yaya yakeyi.
Bayan sungama komai tsaf suna shirin fita saiga Yazeed da Muktar sundawo daga wajen aiki, dama haka sukeyi, idan suka dawo saisu lek'o suga yanda komai yake tafiya kafin sutattafi gida.
Juna suka rungume suna murna.
Muktar ya ce, " mutumina kace soyayya kafito?.
Dariya ya Umar yayi tareda fad'in ALLAH yashiryaka Muktar.
Ameen suka fad'a cikin dariya.
Asma'u ta gaidasu da tambayar aikinsu, duk suka amsa cikin fara'a sannan yazeed yakar6i fodiyo yana fad'in kud'an rakamu wani waje mana kaida madam.
Ya Umar ya ce, ''to aja zuga!, ina kuma zaka kaimi? Mudake shirin tafiya gida?.
Kudai kubiyoni kawai.
Haka kuwa suka rankaya suka tafi, Asma'u Na a bayansu.
Ganin inda suka dosa ya Umar yaja tunga. Cikin had'e fiska yazeed da Muktar sukace babu jayayya a tsakaninmu.
Ya Umar baice komaiba yakad'a kai suka cigaba da tafiya har majallissarsu Dr jafar.
Suna ganin sun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login