Showing 69001 words to 72000 words out of 77995 words
nufosu kuwa sukayi gum daga sambatun surutun dasukeyi tun d'azun akan ya Umar.
Hannu sukaita basu ana gaisawa, duk jikinsu yayi sanyi, yazeed yamik'a musu fodiyo, to 'yan uwa gafa Usman fodiyo, ankawoshine shida madam domin Susanya albarka awajen dadynsa Umar daya gyara.
Kalan kallon aka fara, salman d'aya kar6i fodiyo yayi murmishin takaici, aransa ya ce, ''gashi k'yak'yk'yawa kuwa.
Asma'u ta ce, "ya gajiyarku ya iyali? Idan bazaku damuba muna gayyatarku walima ta mik'a godiyarmu ga ALLAH akan ni'imomin daya azurtamu aciki, ga d'aya daga cikinan shine gyara mall d'inmu daya dawo kamarma wuta bata cishiba, na biyu shine ku6utar kayan ya Fharuk daga hannun custom, na Uku shine albarkar haihuwar fodiyo da ALLAH ya azurtamu dasamu.
Yanda take magana adake tayi mugun basu mamaki, shikansa ya Umar kallonta yakeyi cikeda al'ajabi da birgewa, baita6a tunanin matar tasa jaruma baceba sai ayau. Dukda dai yasan dama Asma'u akwai tsiwa, amma azatonsa ta daina.
Muktar da yazeed kam bak'aramin birgesu Asma'u tayiba, Dan sai zabga murmushi sukeyi.
Tana gama fad'a kuwa ta ce, " inafatan zaku amsa gayyatarmu, nabarku lfy, yaya idan kun gama INA mota, tajuya cikin takun girma tabar wajan.
Duk binta sukayi da kallon, saikuma kishi yata6a zuciyar ya Umar, dad'an k'arfi ya ce, "malamai kallon ya Isa haka, ko kun manta matar aurece?.
Ajiyar zuciya suka sauke suduka, kowanne yanamai janye idonsa daga kanta.
Yazeed yamik'a hannu ya kar6i fodiyo dahar yanzu yake a hannun Salman, sai wani k'ara k'ank'amesa yakeyi tamkar nasa.. π
Yana kar6a suka bar wajen, acikinsu Dr jafar babu Wanda ya iya koda kwakwkwaran tari har su muktar suka kai ga mitar Ya Umar.
Asma'u naciki yazeed yamik'a mata Fodiyo, sannan ya ce, " madam sannu da k'ok'ari, aibansan haka kema kikeba da jarumta.
Dariya sukayi gaba d'aya, ya Umar ya ce, "tab, ai dama Husna matsiwaciyace, Ku kawai takema alkunya, koba hakaba tawan? Yafad'a yana d'aga mata gira.
Harar wasa Asma'u tama ya Umar ta ce, ''bandadai Sheri my boss."
Nanma dariya sukeyi sosai.
Su Tasi'u duk suna kallonsu, kuma azatonsu su sukema dariyar, Dan haka duk jikinsu yakumayin sanyi, wasuma harsum fara nadamar abinda suka aikata ayau.
Ya Umar yatada motar sukayi sallama dasu yazeed suka tafi.
Dayazo saitinsu Dr jafar ma saida yad'aga musu hannu, amma ko tari babu Wanda yayi acikinsu, Dan duk sunyi gum, tundasu ya Umar suka bar wajen babu Wanda ya iya cewa A acikinsu, saidai kallon kallon kawai da zare idanu.
Nikuwa na ce, "hummmm.
__________________________
Ahanya ya Umar da Asma'u sai hirar abinda yafaru sukeyi suna dariya.
Dahaka har suka isa gida. Ya Umar yakwashi ledojin itakuma tasa6i fodiyo suka Shiga.
Afalo suka iske su hasiya da inna baito sunacin tuwo.
Bayan sun musu hannu suka zauna, ya Umar ya ce, " inna yau tuwo akamana?."
Wlhy tuwo nayi Umaru, nidai nagaji dacin shinkafarnan.
Aii wlhy inna kin taimakemu, nikaina bawani damuwa nayi da irin wad'annan abubuwan naiba, nifa aka bani tuwo to anmin dai-dai. Amma su o, e, aii ba'aso, saidai kayan kwad'ayi.
Asma'u datasan da ita yakeyi, ta cuno baki gaba amma batace komaiba.
Ya Umar yace nidai kar aji haushina bankira sunaba dai ko Hasiya?.
Oho dai, aikowa yay zagi akasuwa yasan dawanda yake. Cewar Asma'u tana Barin wajen.
Dariya suka rakata da ita suduka.
Ya Umar ma yamik'e yana fad'in inna bara na rage kayan jikina naje massalaci, danyau zaman cin tuwo zamuyi.
To Umar afito lafiya.
To innarmu, gobe iyanzu munyi kewarki wlhy, dama kiyi zamanki taredamu kawai, zamuyi farinciki wlhy.
'Yar dariya kawai inna baito tayi, ta ce, "a'a Umar, mijinafa?.
Saidai kuma haka inna, amma jimuke kamar karki tafi. Dariya kawai inna baito tayi. shikuma yashige d'akinsa.
*_Lubna_*
Zaune take a k'ataccen falonta, ta mik'e k'afafu gabanta kayan fruit ne da aka yanka k'anana, gefe kuma ga farfesun kaza daya gama had'uwa.
Nikaina 'yar rahotonku saida yawuna ya tsinkeπ.
Ahankali takeci tamkar bataso, gefe kuma masu aikintane kemata tausar k'afafunta.
Wayarta dake wringing tamik'a hannu ta d'auka, ganin mai kirannata yasa murmushi fad'ad'a afuskarta.
Hello Hajja Sadiya ykk?.
Daga can aka amsa mata da lfy lau Hajiya lubna, dama kayane suka iso shine nace bara na sanar miki kafin mutane su za6e.
Wani murmushin k'asaita Lubna tayi, tareda danna tsokar nama abakinta, cikin tauna naman ta ce, "OK Hajja sadiya ngd fa, zuwa anjima kad'an zan shigo insha ALLAH, Dan munada biki satin sama.
To shikenan ALLAH ya kaimu lafiya.
Uhum tafad'a tana ajiye wayar batareda ta yankeba.
Kad'an takumacin naman ta tureshi gefe tana yatsine fuska. Bilki akaimin fruit d'innan cikin firij saina dawo zansha. Tayi maganar idonta akan 'Yar aikin dake dama da ita.
Cikin hanzari kuwa bilki mai aiki ta amsa, d'aukatayi tanufi kicin domin cika umarnin madam.
Lubna kuwa d'aki tashiga, aka sake sabon wanka, cikin shiga ta alfarma, saigata tafito rik'eda key n mota, da k'aramar handbag mai azabar kyau. Takun lubna kawai abin kallone, Dan tabbasa 'Yar gayuce ta fad'a da k'ari, komai nata mai ajineπ§.
Motarta tashige sai gidan Hajja sadiya dillaliya, amma mai lasisi, dankuwa kayane Na manyan k'asa take kawowa. babu tambayar miji atsarin Lubna, ayayinda zata anguwa, saidai yazo ya iske bata nan.
Yanzuma tana fita yana shigowa anguwar, yad'anga gilmawar motarta, amma zuciyarsa bata amince itad'in baceba. Saida yashigo harabar gidan ya faka tashi motar sannan yakula babu d'aya daga cikin motocin Lubnar. (Dan kuwa motar Lubna ak'alla takai hud'u agidan, kuma duk Na gararine da nunawa sa'a).
Baice kimaiba yanufi cikin gidan.............
*_(((S))).......2018_*
*_I Love you all my fan's_*
[1/6, 5:08 PM] ~π© ' π― π¦ π· πβ: π©π»βπ».........
π *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* π
*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*
*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_
*_NIKA'DAIππΌ WRITER ASSO.....π_*
*_pageβ73-74_*
..........Babu kowa afalon sai k'arar AC dana TV. Su bilki sunacan kan sauran farfesun da Lubna ta rage sunaci itada saude.
Cikin d'akinta ya k'arasa, ko INA k'al yake, dama a 6angaren tsafta bashida Matsala da Lubna, dukda dai 'yan aiki keyi ba itaba, saman sofa ya kwanta yana k'arema ko INA na d'akin kallo, amma zuciyarsa da tunaninsa nakan ganin da sukaima Umar ayau.
Lallai suma sunsan Umar yagama kama k'asa, kuma kaf d'insu yafisu komai. Dama can yafisu d'in, ayanzuma garashi dayake auren Lubna kud'i sun k'ara zauna masa. To amma aii banasa baneba, dan yamzudai kam Lubna babu abinda bata fishiba, koda kaddarorin data samu a gadonta sun Isa ta keremasa sa'a, shiyyasa yakula take kallon kanta samadashi. Wata kwafa yayi yana kad'a kai, yakula idanfa yatsaya jiran ya huce, tofa rabon wani zai ratsa. Da sauri yatashi zaune, haryanzu yana a duniyar tunani. Tabbas a farko ya auri Lubna ne dansu bak'anta zuciyar Umar. Ammafa ayanzu tunaninsa yafara sauya akalar tafiya wani 6angare. Yatuna da maganar Kabeer alokacin dasuke kulla wazai auri Lubna d'in?.
*_tab wlhy dabadan matana biyuba, kuma ko sati biyu ban k'ullah da k'ara aureba, ga dokar da dady yasamin akan k'aro ta uku, toda wlhy nizan auri Lubna koda Umar zai mutu. Sannan ita kanta saina tatseta tas, dan fak'iriya ta gsk zan maisheta aradu kuwa. Suma aii Tara musu akayi, kunga kuwa nima saina dangwali arzik'i._*
Alokacin Hafiz babu haka kokad'an aransa, da zuciya d'aya ya amsa zai auri Lubna tunda yad'an fisu k'yau da kud'i, kaitsaye zatafi kar6arsa fiye dakiwa a majalissar.
Ya wani mik'e tsaye yana tafa hannaye, _"ni shegiya inji d'an daudu!"_ dazanma kaina sabalula, baijira wani dogon tunaniba yafara bincike ad'akin Lubna, duk wasu muhimman takardu Na filaye da gidaje Na Lubna saida ya lalubesu Tas, k'ananun kawai ya bar mata, yana gama had'awa Yakama hanyar fita, harya kai falo saikuma yadawo, wani tunanine yazo masa, baikamata yakwashe komai lokaci d'ayaba, Dan tabbas zata gane shine.
Saikawai yajuya yamaida komai, takarda d'aya ya d'auka da wasu kud'i 200k daya gani a dirowar gefen gado yafita zuwa gidan Uwargidansa, dama yau itace dashi, yazo yima Lubna sallamane kawai.
Lubna tana zaune dirshen gaban Hajja Safiya, kaya kawai taketa lodama kanta Na garari, Hajja sadiya kam saida dad'i takeji, dama tasan Lubna babu wasa, data saya zata Baka kud'inka, gashi kuma zata yaya dayawa, Dan yanzu batada babbar customer kamar Lubna.
Saida ta Lodi kayan 2millions NATA Na kanta, sannan shima Hafiz ta d'iba masa. (Yo ba ita tataraba, batasan zafinsuba, sanda aka nema tana gado tana barci hankali kwance)π.
Aledoji Hajja Safiya ta jibga matasu, tasaka 'yan aikinta sukaita kaiwa mota, todama kayan bawani d'inbin yawane dasuba, tunda Na 'yan k'aryane, daga less d'in 300+, sai tanfar 200+, hakama gyale dukna manyanne, barema takalma da jaka, ga yari da kayan kwalli, Dan komai Hajja sadiya saidawa takeyi. Amma dukda haka saida bayan motarta da but suka cika taf, Dan Lubna nason kayan Hajja sadiya, tana siyo kaya masu k'yau da Qualities, gasu designers. Shiyyasa bata k'yashin kashe konawane ta kwashi kaya, dama ga kud'in abanza ana gani.
Sallama sukayi da Hajja Safiya taja mota tatafi, sai gida........
'Yan aikinta ta tura suka kwaso kayan amota, ta kalli bilki amintacciyar mai aikinta kenan, bilki my Sugar yazo gidannan kuwa?.
Eh Anty yazo babu dad'ewama yatafi, inaga yagaji da jiran dawowarkine.
Baki Lubna ta ta6e batareda tace komaiba.
Bilki da sauran 'yan aikin suka fice, itakuma tafad'a bathroom Dan tayi wanka........
___________________________
Safwan kaine ka iya tunawa damu agidannan haka? Kodai 6atankai kayine haka?.
Wata 'Yar dariya Safwan dake gaban mom zaune yayi, mom dama kuna raina wlhy, yanzuma muhimmin abune yakawoni gareku, amma saina k'ara hutawa zamuyi maganar.
To shikenan, ainama godema ALLAH dana ganka yanzuma, jeka huta to, bara nasa ashiryamaka abinci.
To mom, amma yanaji gidan shiru? Inasu baby?.
To ka gujemu ina zakasan mike faruwa agidanku, baby da suhaima sunyi aure, yanzu dagani sai su twins agidan.
Kai yanzunan mom su baby sunyi aure?. Amma banji dad'iba da akayi bananan, ALLAH ya sanya alkairi to. Insha ALLAH dukzanje gidajensu. Matar Ameer fa ta haihu?.
Baki mom tad'an ta6e, ta haihu amma 'yar batazo daraiba.
Ayya my bros ALLAH ya canja damai alkairi, itakuma ALLAH ya jik'anta.
Mom dai batace komaiba, amma mamakin canjawar safwan takeyi sosai, dukya canja mata, ga wata k'iba dayayi ta alamun yanajin dad'i.
Shikam d'akinsa yashige yana wata dariyar mugunta, humm mom dakinsan da shirin danazo gidanan, wlhy datuni kin korani baya, ammafa da ikon ALLAH sainaci nasara akanku.....
π¨tofa Safwan dami kazo?.
__________________________
Yanda takeyin komai a kasalance yau kamar mara laka ajiki saita bashi mamaki, dukdadai yasan miya assasa sanyin jikin nata, hakan bai wuce tafiyar da inna baito zatayi yauba.
Itako bama tasan yanayiba, idonta na kan Fodiyo dake shan nono shima yana kallonta.
Inna baito dake kallonsu ta ce, "ALLAH yaronnan kukayi wasa k'iywa zaiyi nan gaba, jibifa ko wata 2 bai cikaba amma yafara sanin fuskar uwarsa.
Asma'u ta duk'ar dakai k'asa saboda kunya. Ya Umar kam dariya yayi, inna aii yafara k'iywarma, kikula indai yana hannunta bakajin kukansa, amma inhar wani ya d'aukesa mintuna kad'an zai fara.
Cikin zaro idanu Asma'u ta ce, ''kai ya Fharuk, Dan ALLAH kadaina fad'a, ALLAH wani yaji saiya d'auka hakane.
Yo da k'arya nakeyi?.
Shiru tayi amma tana hararsa ta gefen ido.
Inna baito dai dariya take musu. Hasiya kam tana school dan suna zana exam na S,s,c,e.
Haka sukaita hirarsu, dukwanda tsokana ta juyo Kansa za'ayi. Har zuwa la'asar da inna baito ta fara shirin tafiya. Yanzu kam hak'urin Asma'u yazo k'arshe, sai hawaye takeyi, daga inna baito har ya Umar dariya suke mata.
Suduka suka shirya har Hasiya data dawo gidan, inna baito sukaima rakkiya har gida da shatara ta arzik'i. Godiya sosai inna baito tamusu sannan sukai mata sallama suka taho cikeda kewarta.
Daganan gidansu ya Umar suka nufa.
Cikin farin ciki mama ta tarbesu, Rafi'a kam kamar ta tashi sama dan farin ciki.
Suna nan zaune anata hira saiga ya Abubakar, kallo d'aya zaka masa kasan abirkice yake, baya cikin nutsuwarsa.
Suduka da kallo suke binsa, bayan an gaggaisa Asma'u ta zame jikinta tabi su Rafi'a dake d'aki suna magana itada Hasiya, inaga sunayine akan Sadam k'anin Muktar.
Mama ta kalli ya Abubakar cikin kulawa sosai, Abubakar mike faruwane haka? Naga tamkar bakada wadatar lfy?.
Idanunsane suka cika da kwallah, yasharesu yana fad'in mama Sakina tagama dani wlhy.
Sakina kuma? Ya Umar da mama suka fad'a atare.
Ya Umar ne yay k'arfin halin fad'in wai Maman Jameela?.
Kansa ya d'aga ahankali.
Mama ta ce, "tomiya kuma had'aku yau?."
Hummm mama dama asheni aikin banza nakeyi, Kullum Sakina cin dunduniyata takeyi, sakina taruguzani, kullum na ajiye kud'ina danufin tari saitabi ta kwashe, ga shagon ya durk'ushe saboda ragad'ar sa datakeyi.
Jiya na had'a kud'i har 1 .5million zanje kasuwa yau shine Sakina ta kwashesu tas, sannan yau dasafe ta titsiyeni saina saketa, hardacewa idan nahaifi cikin uwata na saketa.
Nikuma raina ya6aci na saketa, ni bansan ta kwashe kud'inba saida ta tafi sannan naduba kud'i sukace na d'aukesu Inda na ajiyesu.
Ina k'ok'arin kiranta sainaga wannan takardar awajen data d'auki kud'in. Yafad'a yana mik'ama ya Umar dake kusadashi takardar.
Rubutune d'an kad'an awajen.
β
_Abubakar bazan iya cigaba da zama dakaiba, Dan kaima nakula *Karayar arzeek'i* na haskoka, gwamma kafin ka durk'ushe kazamemin kaya na kama gabana, nakuma yagi rabona, nidai nayi gaba, 'ya'yanka kuma idan kanaso kazo gidanmu ka kar6a._
Iya abinda ta rubuta kenan, ya Umar yafad'a yana kallon mama dake saurarensa.
Ajiyar zuciya mama ta sauke ta ce, "ALLAH ya k'yauta to."
Cikin ma rairaicewar murya ya Abubakar ya ce, "abinda kawai zakice kenan mama?."
To, mikakeso nace Abubakar? yarinyarnanfa matarkace, abayama nunamin kayi tafini muhinmanci arayuwarka, watsar da kowa da komanka kayi sai sakina. Sai abinda tace shi zakayi, Toni kuwa yanzu miye NAWA?, wanan ai fad'an masoyane.
Kuka Abubakar ya fashe dashi, tamkar wani mace, ya rarrafa gaban mama yana rok'onta gafara da bata hak'uri. Wlhy mama Sharrin shaid'anne dana zuciya, amma tun bayan bikin mufida nayi nadama, Umar Dan Girman ALLAH katayani bawa mamanmu hak'uri, natuba wlhy, kaima ka yafemin abinda namaka, tundaga kan biya maka kud'in asibiti daduk abinda namaka abaya.
Wlhy nayi nadama kunji na rantse muku.
Ya Umarne yataso ya rungumesa, yana fad'in nidai wlhy na yafe maka ya Abubakar, dama can ban rik'eka arainaba.
Ngd Umar, kaidama mai sauk'in kaine, ALLAH yak'arama rayuwarka albarka. Ya nusanta shaid'an daga tsakaninmu.
Ameen ya Umar yafad'a sannan yajuya kan mama yana taya ya Abubakar Neman gafara. Suna cikin haka saiga Abba yadawo.
Yatanbayi ya akayi? Ya Umar yamasa bayanin komai.
Abba ya ce, "kai ALLAH ya k'yauta mana wannan duniya, lallai na tabbata alhakin Umaru ne ke bibiyarmu, Dan ALLAH umaru ka gafarcemu, wlhy yanzu haka Nima cikin iftila'in nake, Dan ALLAH kamana afuw......
Da Sauri ya Umar ya ce, " wlhy Abba na yafe muku, dama can ban rik'eku arainaba.
Kuma nayarda dak'addara k'yak'yk'yawa kokuwa mummuna.
To mungode Umaru, ALLAH yayimaka albarka kaida iyalinka, Yakuma kareku da sharin duk wani mai sharri.
Amen Abba.
Dak'yar suka shawo kan mama ta yafema ya Abubakar, itama ta rok'i gafarar ya Umar d'in, duk ya ce, ''ya yafe musu shikam."
Bayan lafawar komai Abba ya ce, "ai aturama Sakina 'yan Sanda kawai.
Ya Umar ne ya ce, " a'a Abba kubarta, aii duniya makarantace, Wanda baizobama jiransa takeyi. Kubarta taje taci aizasu k'are.
A take anan yayma ya Abubakar alk'awarin kud'i domin yatada jarinsa. Kallonsa sukeyi cikeda mamaki, Dan sunsandai shima bashidashi.
Kallon dayaga suna masane yasakashi yin murmushi, yagyara zamansa sannan ya zayyane musu komai danganeda alkairin yazeed agareshi, dakuma Wanda Alhaji mai kano yamasa shima, har dawowar kayansa Wanda custom suka kama, har bud'e mall d'insa zuwa yanzun.
Rungumeshi ya Abubakar da Abba sukayi, mama kam harda kukan dad'i,