Showing 123001 words to 123632 words out of 123632 words
ita, shima Ayaan tarewa yayi a gidan dudda baya wani samin daman ganinta dan dakin Mami aka mata masauki ga uban yan barka. Da sati ya zagayo kuma akai suna nagani nafada yara suka ce sunan Fareed da Fareeda. Ayaan wani irin son yaranshi da Maman su yake har dan raman kewanta yayi, dazaran bakowa adakin zai sabe ya shigo yadan rage zafi ta hanyar bata hot romance, taita mishi dariya, watanta biyu cs din ya warke kaman ba'a yiba hakan yasa Baaba tabijiro maganan tafiya da ita gida Mami da Pops sukai na'am, Ayaan kam kunyan Baaba yasa kawai bai hanaba amma kaman ya mutu dan bakin ciki gashi bai samu dama sunyi sallama bama har suka tafi, gyara aka shiga yimata a zaria ba kadan ba kullum suna makale awaya da Ayaan dan ita kanta tai kewan shi bana wasaba, watan ta uku Ayaan kaman zai haukace, da kanshi yazo ya dauke matarshi nan fa suka koma gidansu. Ranan wlh har kuka saida tayi sabida yanda ta mugun wahala a hannunshi lallai ko yay kewanta gashi tasha gyaran matsi, da kyar da yara na kuka yabari ta basu nono suna gama sha sukai bacci da kanshi ya karbesu ya kwantar dasu akan gadonsu yakara jawota kuka yadinga mata bil hakki yana mesa ta barshi har tsawon wata biyar rabonshi da ita, bubbuga bayanshi tayi tace "haba ZUMANA bagani ba yanzu am all yours" lallabashi tayi ta dage ta faranta mai rai sosai ta mantar dashi komi.
Ahaka rayuwa ta cigaba da tafiya da kanshi yamata family planning dan yanason Spacing yara at least Fareed da Fareeda suyi shekara biyu ko uku kafin takara daukan wani cikin, yaran ko kadan basu da rigima dan har anfara basu abincin yara wani zubin da safema kwashe su yake ya kaisu wajen Mami da Pops yadawo gida su cigaba da gashi shi shida Bilkisu.
Akwai wata rana da ya hadu da Meram awani supermarket taci attachment ga tabon ruwan zafin har yanzu a kafadar ta tana tare da wani gaye arne dauke kai yayi yana kara nadaman dabi'un shi nabaya babu abinda yafi matarka ta sunna, ta halas tafi Zaki, tafi dadi, tafi gardi, tafi dumi, gata akillace takace kai kadai abinka, babu wanda ya isa ya ketare wanan gonar, abincin babies dinshi dayazo siya ya siya Garber rice ya saima Bilkisu snacks da abubuwan datake so yafito abinshi yawuce gida.
Big Mom rayuwa tai mata kakide kakiden ma daskararre, wuya takeci a prison bana wasaba ga hannu daya gawasu irin kuraje dasuka feso mata kaman gyanda suna ruwa, tai nadama har ba'a cema komi.
Rayuwa da masoyi dadi gareta, Ayaan na Bilkisu, Bilkisu ta Ayaan kaman su cinye junansu haka sukeji. Fadawa tayi jikinshi tana sanye dawani shegen jean bomshort black an jera stones agefe da yar white armless shimi, manna kirjinta tayi a jikinshi tana shafa kanshi, iska ta huramai a idonshi dake a lumshe dan bacci yake tace "wake up Zumana cinyoyina are aching" wani irin numfashi yaja sabida turaren datasa dake fizgarshi sosai, bude ido yayi ahankali ya daura akanta batare dayace komiba, wani parr tamai da ido ta langabe kai tace "please Zumana zafi yakeyi" tai maganan tana wani irin shafo santala santalan cinyoyinta, wani irin fizgota yayi ya nakata akan gadon yana wani irin murmushi, dariya tayi tace "kai Zumana wat are you doing, tausa fa nakeso" kafeta yay da ido saikuma yay murmushi ya kamo soft hand dinta ahankali yace "i love you Baby na" cuddling dinshi tayi tightly ahankali tace "and i love you more Zumana!".
*END!!!*
_Alhamdulillah anan nakawo karshen littafinan mai suna *SANGARTATTCE*, kuskuren danayi Allah ya yafemin sai kunjini a littafina nagaba mai suna *BOYAYYEN MUTUM*._
Duk wacce ta karanta littafin nan batare da tabiya ba itada Allah.
Zaku iya tuntubana ta watsapp number na 07012181461.