Showing 63001 words to 66000 words out of 123632 words

Chapter 22 - SANGARTATTCE complete by Maman Abd Shakur

04 Jul 2024

33733

kanshi daidai saitin fuskarta yayi ya huramata iska a fuska hakan yasa takara kankame idanunta, hada forehead dinshi yay da nata yana goga hancinshi akan nata dudda haka taki bude idon, murya chan ciki yace "hey open ur eyes" kin bude idon tayi sai numfashin da take da sauri da sauri, kara daura hancinshi da kyau yay kan nata yana shakan numfashin ta itama nashi na shiga nata, batare daya raba fuskar nasu ba ya mikar da hannunshi yana lalubo nata, akan cinyarta yaji hannun nata hakan yasa ya rike ya bude tafin hanun yana murza tsakiyan dake jike da zufa yana kallon fuskar ta ganin taki bude ido yasa murya chan kasa yace "alright u asked for it" chakulkuli yamata da sauri ta bude ido tana neman yin dariya amma ta daure ta hana kanta dariyar, fuskarta yabi da kallo kafin yatashi daga gadon ya sunkuceta sukai bayi, nanma suka kara bata lokaci dan saida ya gasata sanan sukai wanka bayan yay wasa da ita son ranshi, kafin su fito ya zaunar da ita abakin gado yana goge jikinshi da towel sanan ya zauna agefenta yana kallon fuskar ta yanda idonta ke kasa sanan ya kalli gashinta daya hargitse ahankali yace "jeki shirya mufita Mami na jiranmu" yay maganan calmly, tashi tayi daga kan gadon ahankali tana tafiya kadan kadan sabida zafi tafita daga dakin dan lumshe ido yayi kafin ya mike yay wajen wardrobe.

Tana shiga daki tafara share hawaye da kyar tai salla sanan tai parking hargitsassen gashinta da ribbon, wani hadadden lace ta dauko royal blue tasaka an mata dinkin riga da skirt daya mata chas chass ajiki ta zauna akan stool ahankali, tajawo hoda ta shafa ta rangada kwali a idonta da har yanzu basu gama washewa ba tsabagen kuka, ta shafa lip gloss a lips dinta dasuka sa lips dinta yay wani irin kyau pink din yafito sosai bakin ma haka abin saiyay kaman tasaka janvaki, tai carving giranta da brush sanan ta tadau dan babban mayafinta black mai shegen kyau tasaka takalmi medan tsini kadan black shima sanan tadau jakarta data saka wayarta kadai aciki ta zauna abakin gado, ko minti daya batayi da zama ba shima ya shigo sanye da royal blue shadda gizna sai kyalli take yamata dinkin half jumber yasanya black cover shoes mai masifar kyau hakanan yau yaji yanajin saka manyan kaya bakaramin kyau yayiba ya tsaya abakin kofa turus yana kallonta hanunshi rike da tea dayan hanun kuma tablet yarike, dan murmushi yayi ganin yanda taketa wasa da bakin gyalen ta, ya shigo dakin yazo kusa da ita ya zauna har jikinsu na gogan juna yana kallon fuskarta yabata tea ahankali yace "sha mutafi" karba tayi hanunta na rawa takai baki tasha kadan tacire abaki, saida tasha kusan rabi sanan ya saka mata maganin abaki ta hadiye sanan ta shanye sauran tea ya karbi cup din kafin ya mikar da ita tsaye yana kallonta, hanunta yarike sanan yajata yanabinta ahankali suka fita daga dakin da sukazo wajen stairs da kanshi ya dauketa sukai kasa bayan ya ijiye cup din a kitchen yafito da ita ya kulle gidan har compound, saida ya bude bangaren ta yasaka ta ciki sanan ya rufo ya zagaya ta dayan side dinshi ya shiga motar ya kunna suka fita daga gidan, wakar celine dion na if walls could talk ke tashi a motar sai binta yake kaman shiya raira wakar kana ganinshi kasan yana cikin nishadi haka sukakai har gaban babban gidansu horn yayi yana rage karan music din sabida kiranshi da akai a waya, daukar Wayan yayi da hannu daya ya kara a kunne yana tuki da hannu daya ya shiga cikin gidan nasu bayan anbude gate.

Tun kafin yay parking take kallon daya daga cikin securities din gidan data ganshi kusa da flowers din gidan ya tsugunna ya rike wasu maguna masu kyau farare guda biyu, kana ganinsu kasan yarane ba'a dade da haihuwar suba ya kafa kansu acikin wata yar karaman bowl suna lasan madara daya dama musu, parking yayi a inda ake parking motoci ya kashe motar har lokacin waya yakeyi wacce bamatajin abinda yake fadi sosai bata damuba tabude kofar motar tayi ta sauka, ko rufe kofar batayi ba tana tafiya ahankali tana dan dingisawa ahakanma wai ta saita tafiyan sosai tai wajen magunan yabita da kallo ta madubin mota, tsayawa tayi agaban security dake basu madaran tana kallon fararen magen tana murmushi ahankali tace "naka ne? Sunada kyau" security dasai a lokacin ya lura da ita dan hankalinshi yay nisa akan magunan yace "barka da zuwa madam" ganin magen taketa kallo yasa yay murmushi ya shafa kan daya daga cikinsu yace "kin gansu nan Mamar su itake tayani gadi duk randa nake duty shine fa last week data haifesu ta mutu wlh banji dadi ba" kaman zatai kuka tace "to ka saka musu suna?" girgiza mata kai yayi hankalin shi nakan wacce tadena shan madaran, da sauri tace "ka samusu Sameer da Sameera tunda naga ai mace da namiji ne ko?" dago kai yayi yasake kallon fuskar ta yana murmushi yace "eh" ganin yanda gabaki daya hankalin ta yana kan magunan yasa yace "kozaki dauke sune" da sauri ta gyada mai kai tana murmushi ta mikomai hannu tace "dan Allah kaban daya natafi da ita gida" daidai lokacin shima ya mikomata magen harta daura hannunta tadaura akan magen gyalenta ya sauka daga kanta yakoma kafada sabida iskar dayakada kawai karan saukan mari sukaji, Ayaan ya tallama security wani hadadden Mari wanda yasa shi sakin magen arude da sauri ta rike magen karta fadi kasa ta karye jikinta na rawa ganin tsantsan bala'i a idonshi, kama kwalan rigar shi Ayaan yayi yana jijjigashi "dan ubanka ubanwa yabaka izinin magana da Matata eh" arude security kanshi akasa yace "sorry sir" tureshi Ayaan yayi da karfin tsiya saida yakusa fadi ya nunashi da yatsa da tsanin bacin rai yace "u are fired kabar gidan nan yanzun nan" security nabashi hakuri ko kallonshi baiyiba yajuyo ya kalleta da jajayen idonshi, gabaki daya jikinta rawa yake, fizgota yayi da karfin bala'i yana maida gyalen da sauri ta saki magen tai tsalle ta shige cikin flowers shikuma yay hanyar shashin Mami rike da hanunta, arude tace "dan Allah kayakuri karka koreshi" wani irin mugun kallo yamata zuciyar shi natafasa dan jiyake zai iya kashe koma waye yaga yana kallonta koyi mata murmushi (to fah, mutumin naku wanan kishi haka).
Fashewa tai da kuka sosai ganin yanda yake kallonta kaman zai daketa, dunkule hanunshi yayi ya daki jikin bangon daya jinginata akai kafin ya daka mata tsawa. "shut up and wipe those tears" da sauri ta share hawayen tass sanan yarike mata hannu suna tafiya ahankali ya bude kofar suka shiga ciki ganin kowa na falo zazzaune akasa anata hira, ana ganinsu kowa ya washe baki yana kallonsu yasa tafara kokarin fizge hanunta sabida tsananin kunya da nauyin su Abba datakeji shiko ko ajikinshi saima tafiya daya fara ahankali sabida ita sukai cikin dakin itama tabishi ta daddage iya karfin ta ta saita tafiyar ta sabida kar agane, daidai wajen Mami yasaki hanunta ganin wani irin kallo datake mai da sauri ta tsugunna ta wajen kafan Mami dake kan kujera tana gaida kowa kanta akasa.
Sun jima afalon suna hira itadai tana kusa da Mami kanta akasa shiko yana jikin Abba sai shagwaba yake zubawa, Abba na wani irin riritashi kaman kwai, akai akai yake satan kallonta. Big Mummy ne ta tashi bayan wayarta yay ringing ta kalli Mami tace "Munari ta iso bari naje" murmushi Mami tamata tace "tadan huta tukun anjima na shigo mu gaisa nima" to Big Mummy tace tafice daga dakin sai Mami ta kalli Bilkisu datai shiru ita kadai ganin mazan duk sun natsu kallon news suke yasa Mami tace "tashi muje sama daughter" ahankali ta mike Mami ta kama hanunta da kanta dan tun shigowan su tagane komi sama sukayi yabisu da kallo asace.
Suna shiga dakin Mami tai kasa zata zauna hararan ta Mami tayi tace "kinga zamu batafa in kinamin wanan kunyan niba maman ki bane?" gyada mata kai tayi tana dan murmushi gado Mami ta nuna mata tace "to tashi daga kasa ki zauna akan gado" ahankali ta tashi ta zauna Mami kuma tafita daga dakin tace "ina zuwa" Mama Jummai tabama kudi ta aikata wani wuri cikin minti talatin saiga Mama Jummai tadawo da sakon karba Mami tayi takoma daki ta shiga bayi tahada mata ruwan zafi sosai dawasu magunguna aciki sanan tafito ta kalleta ahankali tace "daughter shiga bayi ki zauna a ruwan dana hada miki ina zuwa" Mami tafita daga dakin dan tabata sarari, kaman zata nutse da kunya haka takeji mikewa tsaye tayi da kyar ta shiga bayin kaman yanda Mami tace ta shiga ruwan bakaramin dadi tajiba ko, tadade aciki sanan tafito daure da alwala ganin ankira la'asar tana fitowa tazo tayi, ta zauna akan gado daidai lokacin Mami ta shigo ta mika mata wayarta tace "ga Baaba" cike da farin ciki ta karbi wayan Mami tajuya tafita, sun dade suna magana da Baaba kafin Baaba ta mikama Raiyana dake kusa da ita dukta dameta, da sauri Raiyana ta karba tai uwar dakan Baaba tace "Anty Baby labari zan baki" dariya Bilkisu tayi sosai tace "ina jinki bani nasha" Raiyana cikin murna tace "Anty Baby kinayin aure nafara samari daban daban amma duk cikin su nafison copper dake koyarwa a school dinmu kuma yazo wajen Baba yace zaima jirani har nagama ss3 kafin nan yagama service dinshi yasamu aiki, wlh Anty Baby ina sonshi" hanun mutum dataji akan cikinta yasa ta daga kai a tsorace wani irin kallo yake mata hakan yasa takasa magana ta sauke idonta kasa Raiyana tace "hello Anty Baby" zama yayi kan gadon ya dauketa yasata ajikinshi tareda daura kanshi ta wajen wayan, Raiyana tace "hello Anty Baby kinji labarin kuwa" da kyar tace "eh" kafin ahankali tace "ke kinji dadi ai kinsami wanda kikeso Baba kuma zai hadaki dashi, niko saidai naji sabon zance ranan bikina" da sauri ta share hawayen daya zubo mata ahankali tace "ki gaidamin da Mama da Umma" ta katse wayar da sauri tana wasa da yatsun ta kama hanunta yayi yana kallon fuskar ta yace "ke" kin dago kai tayi hakan yasa ya daura fuskar shi akan nata yana mata wani irin kallota yace "ke" bude kofar da akayi yasa yadago kai Mami ce ta shigo dakin dauke da tray ahanunta na abinci da sauri ta tashi daga kan jikinshi shima ya mike tsaye ya karbi tray yana kallon fuskar ta ahankali yace "sannu da aiki Mami na" nunamai Bilkisu tai tace "abincin tane" sai a lokacin ma ya kalli plate din tuwo ne da miyan kuka dayasha namomi tabe fuska yayi ya ijiye mata agaban ta, tana ganin abincin batasan lokacin data saki murmushi ba daya lobar da dimple dinta numfashin shi yakusa ya tsaya, ta kalli Mami data bude wardrobe kaman tana neman abu tace "nagode Mami na" yunkura wa tayi zata sakko kasa da sauri ya riketa dauke kai tayi ya saukar da ita kasan, zama tayi akasan ahankali ya dauko tray ya ijiye mata agabanta, shikuma ya kwanta akan gadon Mamin, wanke hanunta tayi da ruwan da Mami tasako mata atray din sanan tafara ci har wani lumshe ido sabida dadi gashi harda man shanu a kukan, juyowa Mami tayi ta kallesu kafin ta mayar da hankalin ta duka kan Ayaan dake kallonta kaman zai cinyeta itako bama tasan yanayi ba, dan gyaran murya Mami tayi tace "bakai da Abban ka zaku kai Baba Sulaiman airport bawai kazo ka kwanta anan?" dan sosa kai yayi yamike tsaye yace "na manta ma" fita yayi yadan saci kallonta sai tuwonta takeci.

Bayan sallan isha suka dawo gidan shida Abba side din Big Mummy yayi shikuma Abba yawuce bangaren shi dan adakin Mami yake yau, yadade a side din big Mummy l yana hira da big Mummy da bakuwar ta Munari dataxo daga giada sanan yamusu sallama yafito yay part dinsu, tana kwance kan gadon Mami sanye da doguwar rigan da Mami ta bata daidai jikinta na atampa sai hira suke ita da Mami tuni ta saki jikinta tajita garau, da sallama ya shigo dakin yadan saci kallonta kafin ya zauna agefen Mami yana mata murmushi yace "Mami na nadawo" murmushi tamai tace "akawo ma abinci" girgiza kai yayi yace "naci a part din Big Mum" ya kalli Bilkisu datun shigowan shi tai shiru kaman ba ita ke surutu ba yace "tashi mutafi" wani kallo Mami tamai tace "kutafi ina? Tana nan babu inda zata zatamin kwana biyu tukun" duk wani walwala da murmushin dake kan fuskarshi bacewa yayi kaman zaiyi kuka yace "Mamiii" gyada mai kai tayi tace "am serious fa" tashi yayi yafita daga dakin azuciye tundaga bakin kofa yake kwalama Abba kira. "Pops, Popsy, Pops" arude Abba yafito daga dakinshi shigewa jikin Abba yayi Abba dukya rude ya dafashi jin yanda kirjinshi ke bugawa yace "menene Boy waya batama rai haka heart dinka ke beating fast?" kaman zaiyi kuka yace "Mami ne wai bazan tafi da matata ba" "tace hakan?" Abba yay tambayan ranshi abace, gyadamai kai yayi, Abba yay kwafa yace "je mota ka jirata gatanan zuwa kutafi, ai kafin kai auren tafi kowa damun mutane yanzu kuma dakayi zata dauke ma mata, tafi mota abinka gatanan zuwa" juyawa yayi ya sauka downstairs rai fess yay waje abinshi, Abba ya bude dakin Mami ya shiga ko Mami bai kalla ba ya kalli Bilkisu yace "yar arziki tashi kije mijinki na jiranki a mota kutafi gidan ku" dukar dakai tayi sabida yanda takejin nauyin Abba ta sauko tadau hijabin ta da jakanta ta saka, Mami tace "Allah miki albarka zan kiranki gobe kinji" gyada ma Mami kai tayi tana kokarin hadiye hawayen dakeson zubowa wlh batason gidan, Abba dai juyawa yayi yafita da sauri tafada jikin Mami ta rungumeta ahankali tace "Mami zakizo kiduba ni gobe?" dan dariya Mami tayi jin yarinyar take har ranta kaman yar da ta haifa, hakan yasa ta gyada mata kai tace "eh oya tafi kinga goma saura" sakin Mami tayi tafita daga dakin ahankali har tsakar gida yana tsaye a parking lot jingine da motar shi hanunshi zube cikin aljihu tunda tafito yake kallonta harta karaso wurin motar batace mai komiba ta tazo zata wuce ta gabanshi ta zaga ta dayan side din ta zauna ya kamo hanunta, ahankali yajawo ta yasata ajikinshi ya rungumeta wani irin siririn kuka tasaka mai, ajiyar zuciya yasauke sanan yadan duko dakai yakawo shi daidai saitin kunenta yace "kina son ki zauna da Mami?" gyada mai kai tayi hakan yasa yasake sassauta murya yace "ok next time dazamu zo saiki kwana, now stop crying" cirota yay daga jikinshi hannunshi daya abayanta yarike kwankwason ta yasa dayan hanun yaciro handky daga aljihun shi mai taushi da kamshi ya daura akan kuncinta ya share mata hawayen dayabi ya bata mata fuska yana kallon idonta yanda tai kasa dasu taki bari su hada ido, maida handky yayi a aljihu sanan ya dawo da hannun ya daura akan kumatun ta kafin yadaura forehead dinshi yahada da nata har numfashin su nahadu wa murya chan ciki yace "ke look up" dago dara daran idanunta tayi ahankali ta sauke su akan nashi wani irin kasala da gajiya ne yaji ya sauka akanshi, ahankali yafito da tongue dinshi ya lashi lips dinta kafin yasake mannota ajikinshi sosai murya chan kasa yace "jekima big Mum sallama am waiting for u" sakinta yayi tareda karban jakan hanunta yana kallon fuskar ta jiki asanyaye ta juya tai bangaren Mami shikuma ya bude kofar mota ya shiga ya zauna yana kokarin ciro wayarshi dake ringing.

Sallama tayi daga barander amma ba'a amsaba hakan yasa ta bude kofa ta shiga ciki babu kowa akatafaren falon, hakan yasa tai stairs tafara takala matattakala jin alamun magana amma kasa kasa, ahankali tai sallama agaban dakin big Mummy amma shiru hakan yasa ta tsaya tana waige waige corridor din toko tana part din Mami ne? A'a Mami ai tace tai bakuwa, tuna bakuwa yasa ta mike corridor din dan zuwa guest room da tun kafin takai takejin muryoyin su na tashi kasa kasa suna hira harta daga hannu zatai knocking kofar saita tsaya sabida sunan Ayaan dataji Big Mummy tafada so kawai take takarajin halin mugun nan da kyau saisa batai knocking ba tai shiru tareda kara kafa kunne ajikin kofan.

Big Mummy tace "saisa nakiraki kizo sabida na aiwatar da plan dina, abubuwa da dama sun faru bayan kin tafi nijar, kinsan ko lokacin nan da Alaji yatashi wai duka kamfanin shi zai maida sunan Ayaan, manyan kamfani fa Munari, kina ganinshi haka yanada jirgin ruwan tsatso mai daga ruwa, idan aka tsatso man chan kampanin shi dake calaba ake kaiwa suna sarrafa man acire crude oil, acire kerosine, acire diesel, acire petrol, da sauran abubuwa kinsan kudin Alhaji kuwa Munari? Mutumin dahar shugaban kasa yasan da zaman shi wanima shugaban kasa har aksashen waje ma fa, shine yatashi wai zai mayar da komi sunan Ayaan zai bashi duka dukiyar, hankalina yatashi nace wlh baza ai hakaba, idan Alhaji yamutu fa yanzu Firdausi da danta Ayaan ne zasu kwashi kusan komi na gadon shi saidan kasona danni banda da, ai wlh bazai yuba, shine bayan kwana biyu nacemai inada biki a kaduna inaso naje, yabarni harda min kyauta banzame ko inaba sai gidan bokan da kikamin kwatance nan nace mai inaso ahaukata yaron sanan bayan ya haukace akada shi yabar gidan bama gidan kadai ba yabar kano gabaki daya ta yanda kinga idan yaron yabace ai bazai maida dukiyar sunanshi ba, sanan dazaran Ayaan din ya haukacen zansan yanda zanyi da Alhaji kasheshi ba abu mai wuya bane, yariga ya tsufa dama, mutuwa yau ko gobe, amma kinsan abinda Alhaji yayi kuwa? Dudda yabace saida ya maida sunanshi hankalina yatashi sosai shikuma yaron bayan wata daya dayan kwanaki sai gashi yadawo ya warke wanan yar iskan matar tashi damuka gani dazu damuka shiga shashin Firdausi ubanta ne yamai addu'a ya warke, banda hakama yanzu yamai na tsari kome namai baya kamashi wlh, amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login